Alkawarin Zuciya Hausa Novel By M Shakur

 

Alkawarin Zuciya Hausa Novel By M Shakur

Alkawarin Zuciya Hausa Novel By M Shakur

      PROMISE OF THE HEART 

          M SHAKUR

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Alkawarin Zuciya Hausa Novel By M Shakur Page 1

UK

Tundaga nesa take leke babban building din datake dumfara tana bin uban tulin cars din wajen da kallo kaman akwai abinda take nema kafin daga bisani idanuwanta su sauka kan wata white Bentley car gashinan kar kar ko alamun a single dust babu ajikin motan ajiyan zuciya tasauke ahankali murya chan kasa tace Alhamdulillah hes still around sanan tashiga sauri takarasa gaban wajen da ake kira da Cozy harzata saka hannu tabude kofan tashiga tadanyi jim tsaya kafin ahankali tabi jikin ta da kallo tana sanye dawani white jeans daya kamata tsam dawata yar dark blue top mai shegen kyau wacce da kadan tasauka daga kan cibiyanta saidan gyalen data yana kanta white shima dayamata kyau sai gashin kanshi dakenan kusan rabi awaje anmata kalaba da attachment kanana dayamata kyau shima hannunta rikeda wasu books guda biyu dakuma phone nata kirar iPhone 13 sai wata yar karaman jakan datake rataye da ita ajiyan zuciya takara saukewa kana ganinta kasan shes nervous sanan ahankali tasa hannu tabude kofan wajen tashiga ciki



Hadaden eatery ne and bar mai shegen kyau babu wasu mutane dayawa awajen wayanda suke wajen yawancinsu turawa ne fararen fata maaikatan wajenma fararen fatane hakan yasa zaka gane wajen na bature ne ahankali take tafiya tanabin wajen gabaki daya da kallo da gefen idanunta kafin takarasa gaban kanta taja kujeran wajen ta zauna sanan tasauke books dinta agabanta da wayanta daidai baturen Bar attendant din yakaraso yana kallonta yace what can I get you miss dan waigawa tayi kaman tana neman abu awurin tace Pierre Zro Ros please two shot ganin duk tana maganan ne batare datama kalleshi ba yasa yace gotcha sanan yajuya yakoma yadauko wine din datai order yazuba mata a cups guda biyu sanan yadawo gabanta ya ijiye yace here we go dan juyowa tayi da sauri takallai sanan tasauke jakanta da sauri tadauko kudi taba shi tace keep the change kafin ma yay magana tasake juyarda kanta tana bin mutanen wajen da kallo one after d other



Kai Zayn look wani hadadden chocolate guy daga tachan karshen babban falon wajen da aka cikada kujeru ne kowa na zaune yana abinda yake yataba wani kyakkywan thick farin guy dake zaune kan kujera ya lumshe idanu pipe din shisha na bakinshi yana zuka yana fitarda hayakin ta hanci yana sanye da riga da wando both black na LV farine shi kal yanada cikan jiki dayake rigan dayasa short sleeve ne hakan yafito da kakkauran murdadden hannunshi irin guys dinan ne masu manyan gabobi dakuma murdadden jiki dudda idanunshi a lunshe but idan ka kalleshi bazaka so kadauke idanunka ba dan yanada wani irin kyau kaman mace lips dinshi sunyi wani kalan masifan ja kodan shishan dayake shane oho yanada dogon hanci siriri dayazauna akan fuskanshi gwanin ban shaawa sai gashin giranshi baki sidik kuma acike yanada tabon salla agoshi sai gashin kanshi baki sidik shima dake kyalli sun nannade kaman na buzu sanan gawani kwantaccen saje a fuskanshi Masha Allah koda ace shiyay kanshi bazaiyi kanshi da wanan kyau dinba ballema bashi yayba


Ganin baida niyyan amsashi yasa Mamu ya fizge pipe din shisha dake bakinshi yace kafara ko ina maka magana kamin banza ahankali yabude idanunshi dasuka wani lumshe sukai yaushi da idanda zai kalli mace dasu sai lissafinta yarikice sanan yazubasu kan Mamu kaman ance yay magana dan dole yace what Dan murmushi Mamu yayi da hannu yamai alamu yace look over to the counter ga budurwanka chan stalker dinka tazo sai kallon ka take wlh haba Zayn kaiko bazakaji tsoron Allah ka kula yarinyar nan koda sau daya bane tunda dai ta kasa maka magana for morethan 2months yarinyar nan kullum binka take tana stalking naka tana kallonka u know she really really likes u waikai maisa kacika wulakanta mata ne eh Anyway I dont blame you ni wlh in mace ne banmaga abin so ajikinka ba mutum dukgaka nan kalan asibiti farin fata kalan cuta duk baku da karfi dan murmushi yayi dan yasan Mamu so kawai yake yajashi suyita surutu this afternoon shikuma baida time dinan hannunshi yamikamai alamun yabashi shishi shi ijiye pipe din shishan Mamu yayi kan table din gabansu yace Ya isheka hakanan gashinan duk idanunka sun chanza launi munada lectures yanzun nan fa I think in the next 5min dan tsaki yaja yasa hannu yadauki pipe din shisha yacigaba dasha abinshi yana daddanna wayanshi yana hura hayakin ta hancinshi batare dayama daga kai ya kalli inda Mamu yacemai yarinyar nan takeba Mamu nabinshi da kallo yarasa yanda zaiyi yaraba Zayn da shisha shima bawai bayasha bane no but occasionally yakesha shiko Zayn zai iya wuni yanashan shisha hakanma yasa baya iyacin abinci sosai ganin yasake lumshe idanu yasa Mamu yaja tsaki yamike tsaye yace dalla Malam wuce mutafi bude idanunshi yayi dasuka dan kankance sukaija sanan ya watsama Mamu harara kafin ahankali ya ijiye pipe din yamike tsaye dogon namiji ne nagaske budadde sanan kuma cikakke irin mazan nanne da ake kira da burin mata car key dake kan table din yadauka yana rikeda wayanshi yay gaba abinshi batare daya cema Mamu komi ba yay hanyar kanta



Tundaga nesa ta hangoshi ya dumfaro gaban kanta duk taku daya dazaiyi saita jishi har kirjinta yana amsawa tun kafin ya iso wajen wani kalan kamshin dayakeyi dayake neman sata ta haukace sabida sonshi ya lullube mata hanci ganin koina najikinta yadau kyarma yasa ahankali tasa hannu tadauki cup na drink dinta takai bakinta still tana kallonshi ta gefen idanunta daidai ya iso ya tsaya dab da ita dasauri bartender din yazo yace u done sir bai amsashi ba yasa hannunshi a wandonshi yaciro wallet dinshi yabude yana kokarin zaro kudi ko kadan batasan drink din yamakai saman hancinta ba tsabagen yanda take kallonshi kawai numfashin dazata shaka ta shaki wine din wani irin mahaukacin shakewa tayi dabama tasan lokacin data saki cup din akasa ba tana wani kalan mahaukacin tari wine nabin hancinta suna fita idanunta sunyi ja kwalla yacikasu dawani kalan sauri daga Bartender din harshi suka juyo suna kallonta dasauri Bartender din yataho ta saitin gabanta yace sorry Miss dudda tarin datake kokarin danne tarin take tana kakalo murmushi dan wanan kwafsin haka har ina baki tabude zatai magana wani tarin yakara sarkaketa wine din na fitowa daga bakinta yana diddiga akan white wandonta duk yay staining sabida Jan wine ne kaman daga sama taga wani clean white handky agabanta kamshin da ajikin mutum daya tall a duniyan nan takejin kamshi taji yana fitowa daga hanky ahankali tadago kanta sama tanabin Tundaga handkerchief din dakallo harzuwa white hannun dake rikeda shi zuwa kan fuskan Zayn dake kallonta in the eyes wani sabon bugawa zuciyanta yashiga yi hannunta har rawa yake tasa takarba zatakai kan fuskanta dan sharewa shikuma yajuya ya ijiye kudaden dayariga yaciro daga wallet dinshi yadaura kan kantan yajuya yawuce batare daya kara bata second look ba ahankali ta janye handky dagakan bakinta tabishi da kallo harsaida yabace ma ganinta sanan tasauke ijiyan zuciya kafin ahankali tasauke kanta tana kallon handky din ko kadan tama manta inda take rungume handky tayi akirjinta tana murmushi sosai.


ALKAWARIN ZUCIYA 2

Murmushi Bartender din yayi inda sabo yasaba yasan yanda yarinyar nan ke crushing on that guy like hell not just her da many other ladies ma sabida guy dinan cinikin dasukeyi yanzu a eatery dinan is mind blowing dazaran ansan yana ciki yammata zasu fara tururuwa suna shigowa from no where so koshima hes happy for her at least yau yakulata he hope suyi relationship dudda guy din dumping yammata yake anyhow kaman trash kuma ko ajikinshi dan yasan yanda suke binshi he just hopes wanan will not be one of his victims dan yana using babes kaman yanda yake using pen na rubutu idan yagaji da wanan ya yar yadauki sabo



Tadade awajen ita kadai sai murmushi take tana daddaura handkerchief din akan fuskanta tanajin dadi daga bisani wayanta yashiga kara dasauri ta kalli wayan ganin Juliana Munari ke kiranta yasa dasauri tadauka tana murmushi sosai tace Hi Babe ya daga tachan bangaren wata yarinya tace ina apartment dinki amman bakinan Ayshu where are you Ba tundazu muka gama lectures ba murmushi tayi sosai tace ina Cozy dan jim Jully tayi tace for Godsake Aisha when will u get sense Eh look at the way Kabeer ke binki Ayshu yaron nan loves you like a mad man amman kina nan kina stalking wanan heartbreaker da the worst part baimasan kina existing ba dasauri Aysha tai fari da ido tace says who wayace miki baisan ina existing ba Wlh yasani infect right now ma yanzu haka handkerchief dinshi nake kallo a hannuna it feels warm and smells succulent OMG it smells just like him wlh I feel kaman Zayn dina ne anan wajen shiru Jully tayi saikuma chan tace Ayshu I am ur friend and I will always tell you the truth forget that guy hes nothing but a dream and face the reality face wanda ke sonki ba wanan ba da kowa in our university sunsanshi ba wajen using yammata yay dumping nasu Ayshu enough of this stalking sabida yaron nan kin chanza gida kin dawo apartment din dayake kin biya kudi double of the normal amout sabida acire tenant din dake zaune adakin dakenan directly opposite nashi kinyi parking kin koma compund din Aysha sabida yanda kike stalking guy dinan kinsan karfe nawa yake tashi karfe nawa yake fita gym karfe nawa yake shiga school sau nake yake da lectures kinsan all his spots grades dinki kullum low suke karayi sabida soyayyan wanda baisan dakeba ke gabanki kum Jully please enough allow me to leave my life ana so by force ne banson KB ki rabudani da maganan shi kuma zaki gani Zayn will notice me and I will date him dasauri Jully tace dating Ayshu bakince min Islam dating babu kyau ba dan yatsine fuska tayi tace Jully is because bakisan guy dinan bane saisa irinsu idan kika basu kanki ne kawai zasu zauna dake dan gayu ne nafitina kaman ba muslim ba boko tashigeshi I want him to be addicted to me kaman yanda yakenan addicted to shisha I am ready to give him anything wlh Ina balain sonshi just wait for me ki dafa mana abinci gani nan zuwa

tana maganan ta katse waya shiru Jully tayi at this point zubama Ayshu ido zatayi dan Allah yama Ayshu taurin kai batajin shawara kuma yaron nan will only break her heart she will only chop breakfast a hannunshi a nothing will happen yaron da har lecturorin su mata crushing suke akanshi anyway she just hope for the best




Wuraren 6 ta shigo gidan kana ganin gidan kasan na mugun yaran masu kudi ne elevator ta shiga zuwa floor dinsu sanan tawuce Dakinsu tana kallon nashi dakin datana gani tasan baidawo ba daman baya dawo da wuri kullum sai 11 ko 12 nadare kuma kullu yaumin bata iya bacci saitaga dawowanshi wata rana tai kuka duk randa zai dawo da mace wata tana kuma tai murmushi the truth is baifiye neman mata ba wani zubin zaiyi 2month baidawo dakowace mace ba wani zubin kuma saiya dawo da mace zasuyi kusan kwana uku ko hudu tare saikuma shikenan bata kara ganinta dudda batasan dalili ba but kawai haka take gani kuma baka taba ganinshi da babe din dabataci sunanta babe ba duk tana tunanin nan tana tafiya ne tana kaiwa gaban Dakinsu tabude kofa tashige ciki tana ihu kitchen tafada tawani irin rungume Jully tana nuna mata handky tace Jully look murmushi Jully tayi tana kallon handky sanan tace Ya akayi yabaki handky shi  nan tabata labarin from A to Z tana murna murmushi Jully tayi tace nidai jeki wanka kizo muci abinci dan Jerry zaizo yadauken gira daya Aysha tadaga mata tace Iyye love birds tai maganan tana wucewa bedroom nata tashiga sanan ahankali ta ijiye handky kan pillow dinta tareda shafawa sanan tawuce ta shiga wanka agurguje tana fitowa tazo sukaci abincin tare sanan Jully ta shirya ta wuce abinta komawa tayi ta kwanta kan gado tadauki handky tana kallon shi kafin ahankali tace Zayn I love you so very much Zayn rungume handky tayi akirjinta tsamtsam tanaji kaman shita rungume ahaka bacci ya kwasheta 11 dot na bugawa ta bude idanunta tsam shi kanshi gangar jikinta yasaba da stalking nashi fitowa falonta tayi tai hanyar window ta ta tsaya dayake wutan dakin akashe ne ta tsaya tana kallon kofarshi tana tsaye awajen kam wajejen 1130 saigashi ya shigo yana tafiya nan cikeda isa akuma hankali tundaga wajen saida kamshin dayake yadaki hancinta bude kofanshi yayi ya shiga sanan ya maida yarufe kafin ya kashe wutan falon murya chan kasa tace good night My love asuba tagari sanan ahankali tasauke window blind din tajuya takoma daki ta kwanta saikuma kaman wani abu yafado ranta dasauri ta tashi tadauki handky tafada bayi ta wan ke shi tsaf sanan ta shanya tafito tazo ta kwanta shida dot tabude idanuwanta agurguje tafada bayi tadauro alwala tafito sallan ma agurguje tayi bama ta tsaya cire hijabin ba tafito ta daga window blind ta tsaya jikin window dan 630 dot yake fitowa tafiya gym tana tsaye saigashi yafito cikin kayan workout gajeren wando da singiletin Riga da safa da canvas cinyanshi tabi da kallo amunmurde kaman na yan wrestling sanan yaja kofan dayake da pin suke bude kofan yawuce yana jogging yatafi abinshi murmushi tayi ahankali sanan tace good morning  baby na sanan tajuya handkerchief din tadauka tai ironing nashi sanan ta shiga wanka tadade sosai abayin sanan tafito tana ganin 8 saura da sauri tawuce wajen window Wuraren 8 yashigo yana zufa murmushi tayi dasauri tajuya tashiga ciki wani hadaden short gown ta saka daya sauka daga guwiwabta da kadan pink yamata kyau Wanan Karan batasa dankwali ba sai turaren data feffesa sanan tai parking gashin ta in a stylish way sanan ahankali tadauki handky tana kallon kanta agaban madubi ahankali tace Ya Allah kadaurani akanshi sanan ta zura slippers dinta tawuce tafita falo ahankali tabude kofa tafito daga flat dinshi sanan kaman wacce abi yafashewa aciki tai hanyar dakin shi kirjinta na daukan uku uku tawuce gaban dakinshi tadade atsaye kafin ahankali ta danna door bell ankai kusan 5min kaman bazaa budewa farat aka bude kofan gabadaya dasauri tadaga kanta suka hada ido wani irin faduwa gabanta yake tana kallonshi yana daure da bathrobe ajikinshi kirjinshi duka abude gashin kirjinshi akwance ruwa nabi sai karamin towel a hannunshi yana goge kanshi da alamu daga bayi yake da mamaki yadan kalleta batare datai magana ba lips dinta har rawa yake sanan ahankali tadaga hannunta dake rikeda handkerchief din murya chan kasa tace ahhhhhmmm dama dama I brought your handkerchief back ne tai maganan tana wani irin nishi sama sama kaman numfashinta sai dauke kirjinta nawani irin racing this is the first time take ganinshi ahaka ganin still kallonta yake ba yabo ba fallasa kuma bai fasa abinda yake ba wato sharekanshi da karamin towel din dayake rikedashi yasa taji wani balain fargabanshi na cikata jin baice komiba dakyar tadaga hannunta tamai pointing kofan dakinta dake kallon nashi tace actually thats my flat yanzun nan naganka shine nace uhmmm bari nakawo ma dan yatsine fuska yayi amugun wulakance ya kalli handky datake mikamai tundazu har hannunta na neman sagewa yace I dont need it discard it yaja kofan zai maida yarufe da sauri tace uhmmm wait please chak ya tsaya yana kallon fuskanta da fuskanshi dababu alamun rahama akai face dinshi looking kaman zai maketa tagefenshi taleka tana kallon indomie da taga yafito dashi zai dafa yacika ruwa a babban pot yazuba albasa aciki ya fasa kwai aciki ruwan na kumfa sosai dan murmushi tayi cikeda shakkanshi tace are you trying to cook indomie Yana kallonta still a balain wulakance yace uhn kaman dole akace yay maganan murya chan kasa cikeda shakkan abinda zatace tace thats not how to lemme cook it for you pplease wani kalan wahalallan tsaki yaja ko kunyanta baijiba yace banso sanan yay slamming door din on her face batare dayama jira maitake shirin cewaba kuka taji yazo mata wuya tadaure tahanashi fitowa tadade ahaka awajen sanan ahankali tajuya tawuce takoma dakinta zama tayi tana kallon handkerchief din tama rasa meke mata dadi tunda take bata taba shakkan wani namiji ba sai wanan menene shi Jibeta fa tanada kyau babu namiji da bazata iya daukemai hankali ba shi waye enough of all this tashi tayi fuu tai kofan tabude tafice sanan direct tai dakinshi ta danna door bell baa wani dauki lokaci ba wanan karan tabude kofan koyana expecting wani ne oho churus ya tsaya ganin yarinyar dazu wani irin faduwa gabanta yayi ganinshi dagashi sai dogon wando na Jean da Riga a hannunshi dabai Riga yasaba yanada wani irin broad chest ga cikakken shoulder parts garai kasa magana tayi saiwani kalan kallon kirjinshi datake lips dinta na rawa tana kallon dark aroelas dinshi ahankali tace lloveyouZZayn Tundaga sama har kasa yake kalleta sanan yace ke kikama kanki wanan Karan wani slamming kofan yayi on her face saida yataba goshinta ahankali tajuya kaman an kashe mata yaran ciki tawuce side nata ta zauna dirshan akasa tana zaune awajen taji fitowanshi yafice kiri kiri kasa zuwa class din datake dashi tayi sabida yanda komi baya mata dadi


ALKAWARIN ZUCIYA  3


Nigeria

Wata babbar mace ce doguwa chocolate skin tsaye cikin wani lafiyayyen hadadden kitchen ginin zamani tana sanye dawata doguwan rigan Atampa mai kyan balai ga kallabi daure akanta da kana gani kasan daura dankwalin kawai tayi amman hakan baihana kwantaccen black gashinta dake gauraye da farare lekowa ba tana tsaye agaban wani hadadden babban gas a kitchen tanama wata yar aiki dake juya basmati rice a tukunya dawani wood spoon magana sukaji wata zazzakan murya dake ratsa zuciya na ya mace ta kwala ma matar uban kira Mama nadawo nakawo miki wasu kawayena ki gansu wani irin kwashewa da dariya yar aikin dake juya abinci a tukunya tayi takalli Matar da aka kira da Mama datai tsaye kawai tama rasa ta cewa tace Hajiya wlh tun ina iya kirga yawan kawayen Khairy harna bace a kirgan kwafa kawai Matar da aka kira da Mama tayi tace karasa juya abincin sai ki kwashe a warmer Ladid bata idasa maganan ba aka kara rangadamata kira da wanan zakakkiyar muryan kaman ana busa sarewa Mamaaaa kina ina zoki gansu dafa goshinta Matar tayi cikeda takaici tace Allah nagode maka dakabani wanan yarinya ina ganin Ummulkhairy ce zata bani hawan jini aduniyan nan tai maganan tana fitadaga kitchen din ta hanyar bude kofa tafice tana fitowa dining tai kicibus da yammata kusan su tara a zazzaune kan lafiyayyun kujerun falon suna maganganu suna hira suna kallon lafiyayyen hadaden falon dayaji Cubana furnitures ganin Matar da kallo daya suka mata suka gane itace mahaifiyar Khairy yasa duk suka zubo daga kan kujerun cikeda girmamawa duk suka gaidata Mama ina yini Mama barka da rana Mama ina gajiya lafiyayyen murmushi ta sakin musu tana karasowa tsakiyan falon tana bindi da kallo daidai tace Masha Allah sassannunku da zuwa yammata yakaratu Kafin subata amsa wata kyakkyawan budurwa yarinya chocolate skin color yar doguwa bachan sosai ba dabazata wuce 20yrs skin dinta nawani kalan glowing fuskanta babu ko kuraje guda tanada dan dogon hanci yet kuma dan karami dan diss afuskanta but fitacce tanada manya manyan pure white eyes idanunta are very big sunada wani kalan adorable spherical shape that is just damn gorgeous dan kana kallonta the first thing dazasu fara daukan maka hankali a fuskanta are her big white eyes ga eyelash dinta dogaye bakake cikakku hakama gashin giranta tanada goshi wanda kusan yarabu biyu ne rabi duk gashi ne dayake nan baki sidik sun kwanta daya karama fuskanta wani kalan kyau dan zaka dauka buzuwa ce sai dayan rabin kuma fatarta ne dayataho har gira tana sanye da dogon rigan atampa itama da dan kwalinta akanta tawani buga uban ihu da saida falon ya amsa gabadaya Mamaaaa yanda ta kwala mata uban kiran nan yasa  mahaifiyar nata tadago da kanta tareda juyowa ta zuba mata idanuwanta kurii irin na jamaa yaya zanyi da wanan yarinyar ne Wani irin washe baki Khairy tayi cute saitin white teeth dinta suka bayyana tashiga saukowa daga stairs din dagudu kaman ba ita Mamar kema kallon zaki ganeba kawai tawani irin fada jikin Maman nata tana ihu sosai tana rawa ta kankame Maman kamkam Wayyooo Mama wlh nai missing naki inata nemanki nadauka kin fita ne har hankalina yatashi ashe kina kitchen Mama tun safe yau banganki ba awa nawa yanzu bansaki a idona ba karfe biyar fa nai kewanki Maman mu Mamana I miss you Mommy Ummulkhaiyr tai maganan tana kara kankamet Mama cikeda tsananin murna dudda yanda Mama ke mugun kule da ita saida tai murmushi har cikin ranta duk cikin yaranta babu wanda ke sonta kaman yanda Khairy ke sonta idan Khairy tadawo gida batanan wani zubin har zazzabi takeyi Son da Khairy ke mata dabanne gabaki dayan kawayenta baki suka sake suna kallon Khairy yanda ta kankame mamanta cikeda murna tana rawa kaman wata yar karaman yarinya murmushi kawai Maman takeyi ganin yanda kawayen ke kallon Khairy sabida wayan nan wasu new set ne basu saba ganin haukanta agidaba yasa Mama tace ke dalla cikani kije kitchen kitaya Ladidi ku kwaso abinci kiyi serving friends naki kuci sakin Mama tayi ahankali tana murmushi dake balain kara mata kyau tana kallon Mama tace tom Mama sanan tawuce kitchen da ihunta ta shiga kitchen din Ladi kwas kwas Tsabagen yanda Ladidi tafirgita batasan lokacin data saki cokali data rike a hannunta kasa ba kwashewa da dariya Khairy tayi ganin yanda Ladidi tafirgita Ladidi ta watsa mata harara tana dafa kirjinta da hannu jin yanda yake  bugawa tace aniyarki tabiki Khairy bani zaki sawa bugawan zuciya ba wlh dariya Khairy tayi tadauki spoon tazo kusa da ita tana kallon tukunyar tana murmushi tace uhmm smells good lets have a taste abincin tadeba takai baki tana lumshe ido harara Ladidi tabita dashi tana kallon long full lushy eyelash dinta dazakaji kaman ka cire kasama naka sabida kyau dan murmushi tayi tace yayi dadi Khairy Kinga nasa coconut milk dakikace nadinga sawa bude idanu Khairy tayi ta kalleta sanan ta yatsine fuska tace yayi dadi ba laifi amman ba kaman nawa ba batarai Ladidi tayi hakan yasa Khairy tafashe da dariya tace ki zubamana nida kawayena kizo ku gaisa hararanta Ladidi tayi tace Malama ki tsaya ki dauki abincinku ki kaimusu ba inda zani nagaji da gaisawa da kawayenki nibansan ko kamfani gareki na kawaye ba turobaki Khairy tayi tace bakinciki kikemin kinga inada kawaye masu sona ke bakida kawa ko daya dasauri Ladidi tanuna kanta tace ni Khairy bakin ciki ana zaune lafiya kawayenki sunfi dari ni idan Allah yabani kawaye ko sama da biyu ne bansan yanda zanyi dasu ba hararanta Khairy tayi tadauki Baban tray da Ladidi tajera musu different abinci akai a different plate guda 5 tafita dasu taje takai musu sanan tadawo ladidi na kallonta tace yanaga kin dawo akufule tace su tara ne plus ni goma kuma is just 5 plate of food nafita dashi kasa magana Ladidi tayi kawai tashiga zuba wasu sababbi tass abincin yakare Ladidi tace yayyinki suka dawo maizasuci oho ta amsata akufule tafice abinta takaimusu abinci suka shiga ci suna hira shaaaa kakeji sun cika falon da hayaniya kadauka biki ake kowani liyafa aka hada lekosu Ladidi tayi daga kitchen kwafa tayi tace yo wlh ban kara daura wani girkin barima kiga tafiyata zanyi masu gida nakema aiki ba kawayenki ba yarinya kowani kare da doki kawayenki ne mijinki zai sha fama Khairy tai maganan tana komawa ciki hada yan kayanta tayi a handbag dinan sanan tabi takofar kitchen tafice abinta daman inhar tagama aikin yamma indai Hajiya na sama tafiyanta take saidai in tana kasa ne saitaje tamata sallama tawuce



Sai wuraren 6 sanan kawayen nata suka fito bayan takaisu sama sunma Mama sallama har compound tarakosu inda sukai parking motocin su duk suka shishiga daya daga cikinsu taleko bayan tama motarta benz key tace wai Khairy yaushe zaki farajan mota kine eh Gamu duk mu munaja ke kadaine kullum driver ke kawowa kaman zatai kuka tace ba su Mama bane da Baba wai tsoro suke su barni nafara tuki wai nacika rawan kai kumafa na iya wlh Paddy dariya dukansu sukayi wacce ta kira da Paddy tace ke da karfin hali zakisa su barki kifara tuki wlh daukan mota kawai zakiyi wataran ki fice Babe magrib tayi bari muwuce see you tomorrow at school hannu tadaga musu tace see yah girls gateman dinsu yabude musu gate suka fice motoci biyar daidai kuma motocin yayinta na shigowa gida na Baban su biyeda su washe baki tayi tana tafi ahankali tana kallon motar Baban su dake shigowa last tace oyoyo Baba motan na parking tai wajen motan da gudu batare databi na yayyinta da kallo bama.

======================================

ZA KU SO KU KARANTA WADANNAN LITTAFAN:

1. The Virgin Maid Hausa Novel Complete

2. Nakasa Ba Kasawa Bace Book 3

3. Tarihin Hannatu Musa Musawa

4. Soldiers Family Hausa Novel

5. Auren Sha'awa Hausa Novel By Oum Aphnan

======================================

ALKAWARIN ZUCIYA  4

Kafin ma Baba yabude kofa tasa hannu tabudemai kofan jikinta har rawa yake tanajin dadi Baba oyoyo Baba sannu da zuwa wani magidancin mutum ne babba sosai yana sanye da babban riga yanada gemu dayacika da furfura ga kuma katon ciki irin na manya wayanda suka manyanta dinan exactly idanunsu iri daya da ita manya saidai nashi daya soma kankancewa sabida tsufa wani kalan kyayataccen murmushi yasakin mata cikin kamilallen muryanshi irin na magidantan nan yace yarinyar Babanta yay maganan yanajan dan hancinta murmushi tayi sosai tace sannu da zuwa Baba fitowa daga motan yayi yace to akwasomin kaya akai ciki gyadamai kai tayi tace to Baba yawuce yana kallon yaranshi maza su uku da duk suke tsaye suna jiran fitowanshi Manaf wanda yake Babba yanada 27yrs sai Muaz shima 27yrs twins ne shida Manaf saidai ba identical twins ba ko kadan ma basuyi kamaba idan baa gayamaka yan biyu bane bazama ka yardaba Manaf na kama da Mama Muaz na kama da Baba sai Maheer dakenan 24yrs dukansu sun gama makaranta duk a company Baba suke aiki yanzu


Gaida Mahaifin nasu sukayi cikeda girmamawa kana ganinsu kaga yaran dakeda tarbiya dakuma natsuwa Cikin so da kauna ya amsasu yana tambayan kowa ya aiki sanan suka wuce masallaci itakuma kayan Baba su files da wasu yan tarkace tafito dasu daga motan sanan tai cikin gida


Sama tayi direct zuwa lafiyayyen hadadden falon Baba ijiye kayan tayi sanan tajuyo tabude kofa ahankali ganin Mama tsaye abakin kofan kaman ita take jira daman yasa takarasa fitowa tareda maida kofan tana rufewa tana kallon fuskan Mama dake kallonta tana murmushi harara Mama ta watsa mata tace ba murmushi nace kimin ba quietly go to that kitchen kidafa sabon abinci wanda zaaci agidan nan this night tunda wanda aka dafa dake da kawayenki kun cinyeshi tatas dan turobaki tayi dan wlh tagaji ahankali kaman zata rushe da kuka tace Mama maisa Ladidi bata dafa wani ba wlh nagaji school fa naje cikin fushi sosai Mama tace are you stupid Umma Inba so kike na makeki ba kiwuce yanzun nan kafin raina yabaci kije ki daura abincin dazaaci this night I am talking to you kina gayamin Ladidi tadafa kin zaci sabida ke nadauki Ladidi aiki kokin dauka jakace ita batasan ciwon kanta ba dazata zake tai girkin gida keda kawayenki kuzo kutasa abincin agaba ku cinye tas yanzu ina gayamiki kije ki daura wani kina neman kawomin gabli da baadi to the kitchen my friend Mama tadaka mata tsawa kaman zata kurma ihu tawuce hawaye sun cika idanunta tass tai kasa harara Mama tabita dashi sanan takada kai kawai tawuce tashiga dakinta


Kitchen din tashiga tamaida kofan da mugun karfi tarufe kaman zata Balla kofan sanan ta jingina da kofan tana maida numfashi takai kusan 5min sanan tawuce ta kwaso kayayyaki tashiga shirin hada girki



Saida akai Ishai sanan Baba da su Manaf suka shigo gida afalo suka tarda Mama zaune gaidata duk sukayi Mama ta gaida mijin nata zama duk sukayi Maheer yace Mama me aka dafa yunwa nakeji ahankali Mama tace Khairy na kitchen tana girki itada kawayenta suka cinye duka abincin da aka dafa tass shine yanzu dannace taje tadafa wani abincin take kumbure kumbure dan murmushi Baba yayi yana duba wayanshi ganin yanada miss call cikeda kufulewa Maheer yace wlh Mama Allah zan zane yarinyar nan duk randa takawo kuchakun kawayenta tashiga kitchen tamusu girki da kanta ba abincin muba cikin fushi shima Muaz yace ni I dont even know wani kalan brain Khairy keda shi ni tunda nake bantaba ganin wacce takai Khairy yawan kawaye ba kawayenta sunfi dari biyu tamaida mana da gida nanne majallisar kawayenta ai gobe Saturday Allah sa takawo mana wata gidan nan wlh daga ita har kawar saina kakkaryasu Baba daduk ke jinsu yana taba wayanshi wayan ya ijiye yakalli Mama yana murmushi sanan yakalli su Maheer yace ku kyale yarinyar nan shes just a small girl idan making friends makes her happy so be it abincin gidan banike siyaba taita kawo kawayenta sunaci is no big deal and you wife yajuyo yakalli Mama yace idan abincin gida da kawayenta keciki ki kara yawan abinci since kinsan yarki mai mutane ce ta yanda zasuzo suci su koshi sanan muma muzo muci okay tabe baki Mama tayi tace daman babu wanda ke bata yarinyar nan saikai kacigaba Mama tai maganan da fushi dan murmushi Manaf da tuntuni baice komiba yayi ganin yanda ran Mama yabaci yace Mama kudena making issue out of this small thing please bagashi yanzu tana kitchen tana dafa mana wani ba is just friends ta tara bawai wani bad hali ko dabia takeyi wanda yaran yanzu sukeyi ba Mama please ku kyaleta shes still a small girl inda ace bata gama secondary school dawuri ba da har yanzu bamata shiga university ba ballema tazo hartana final year ku barta please Mama ahankali zata gyara murmushi sosai Baba yayi yanajin maganan da Manaf keyi Manaf nada dabiunshi sak ga hakuri ga iya tafiyar da gida gashi da halin manyanta halin Baba amman Muaz da Maheer jin kansu suke kaman saonnin Ummul Khairy Baki Mama tabude zatai magana aka bude kofan kitchen din aka fito Khairy ce tadauko wani hadaden warmer ko kallonsu batayi ba sai uban turo baki take tawuce zatakai warmer dinning Baba yace zo kawo kulan nan Umma anan falo zamuci ahankali tajuyo tazo Muaz da Maheer sai uban ballamata harara suke tana karasowa ta ijiye kulan Baba na kallonta yace yauwa sannu da aiki Yanmata na Maheer dake kallonta yace yi sauri kije ki kawomin plate dina da fork dasauri ta kalleshi da manya manyan idanunta harara ta watsamai wani irin mikewa tsaye yayi kaman zaiyo kanta dasauri tai baya tareda dan sakin ihu Wayyo Ya Manaf kaganshi ko hararanshi Manaf yayi batare dayay magana ba hakan yasa Maheer yakoma yazauna yana kwafa Manaf yakalleta yace go and bring the plate and serve us gyadamai kai tayi tajuya tana turo baki daga Baba har Mama suka bitada kallo bata wani dade ba tafito dauke dawani babban tray da plates spoons bottle water da drinks ke kai sanan takawo tsakiyan falon sanan tabude kulan wani kamshi ne yadaki hancinsu tadafa wani lafiyayyen taliya da nama zuzzubama kowa tayi sanan ta tashi Baba yace ina zaki zauna kici naki ahankali tace nakoshi naci shinkafa dazu wanka zanje nayi Baba nagaji jikiyi yarinyar kirki wucewa tayi sama sukuma sukahau ci saida Maheer yajuya ganin hartama shiga dakinta yasa yajuyo yace at least shes good in one good aspect wato girki murmushi Baba yayi yakalli Mama yace akwai wacce zata zauna da Wife bata iya girki ba ballema yarta murmushi kawai Mama tayi batacemai komiba saida suka gamacin abincin tsaf sanan Maheer ya kwashe komi yakai kitchen kafin su tashi suma iyayensu sallama suka wuce side dinsu



Tashi Baba yayi yana kallon Mama datai shiru yace please kidena sa zancen shirmen Khairy aranki is just like what Manaf said at least friends kawai ta tara bawani mugun hali ba dan ijiyan zuciya ta sauke sanan ahankali tace Alhaji still yawan kawaye basu da amfani wlh ahankali Baba yace I promise duk randa nai sensing wani bad behavior kokuma wani abu nida kaina zan rabata dasu please this matter of her friends shouldnt be an issue again ok Ahankali Mama tace ai shikenan  dama kaine ke bata Umma ai Mama tai maganan tai gaba abinta binta yay abaya yace wifeyyy common bata biyemishi ba tabude kofar dakinta ta shige murmushi yayi kawai aranshi yace I will handle u later sanan yay hanyar dakin Khairy knocking yayi ahankali tareda kiran sunanta Umma jin shiru yasa ahankali yabude kofan dakin dakine nai kyau dakana gani kasan dakin Yar gata ne anyimai Fenti pink dakuma design na flowers everywhere tana kwance kan lafiyayyen gadonta mai kyau tana sanye da dogon gown na bacci tana bacci hankali kwance ga dakin uban sanyin AC tachure alamun sanyi takeji karasowa gaban gadon yayi yace Umma Umma mamar ki dake fada ita batasan rashin jin maganan ta kika daukoba yay maganan yanajan bargon gadon yarufa mata sanan yadau remote don AC yarage AC sosai kafin ahankali yajuya ya kashe wuta sanan yarufe mata kofan yawuce dakin matarshi.


ALKAWARIN ZUCIYA 5


Da asuba kafin Baba yawuce masallaci yashigo yatadata wanda hakan yakeyi kullum

Da farinciki ta tashi yau sosai kaman ba itane ta kwana da fushi jiyaba murna take sosai sabida yau zataje bikin kawarta Zainab


Saida tai salla tai karatu sanan ta gyara dakinta tsaf tafito kasa ta sauka a kitchen ta tarda Mama tsaye zata fara aiki dawani irin gudu taje ta rungume Mama Mama good morning murmushi Mama tasakeyi this is another aspect na halin Umma datakeso ko kadan batada riko tureta Mama tayi tace waike karyani kikeso kiyi dariya tayi tace Mama dadi nakeji yau bikin Zainab Kawata Beaty wacce nai ankon ta kin tuna Baki Mama ta tabe tace ina zan tuna wata Besty Bestotin kin sunfi dari keda kullum cikin bikin kawayenki ake idan babanki ya shigo kije ki tambayeshi izini baruwana da zuwa bikinki  bani tukunya nidai kiga dasauri tadaukoma Mama tukunyar nan suka shiga hada breakfast tanama Mama surutu wuraren 8 suka gama komi suka jera a falo daidai nan su Baba suka shigo gidan duka zama sukai a falo suka shiga kari sai bayan an gama ta kwashe komi takai kitchen sanan tadawo da saurinta tazauna kusa da Baba fuskanta kadai yagayamai dawani abu hakan yasa yace Ya akayi Khairiyya Murmushi tayi tace Baba yau bikin Zainab kawata shine nakeso nagayamaka idanu Baba yazuba mata yace amman kinsan yau yakamata kije gidan Baffan kiko gyadamai kai tayi dasauri ahankali tace Baba gobe zanje gidan tunda yau inada biki please naje Baba  shiru yayi sai chan yace ok kije but by 4 kidawo gidan nan ban yarda kije kai Amarya ba murmushi tayi tace Baba ai daman bazanje ba itada zaakai Kano kumama ana daura aure wai zaa tafida ita kaga kenan kafin 4 nadawo ma jinjina kai Baba yayi yace duk kincikani da surutu okay to adawo lpy ki kama kanki banson kula maza okay dasauri tace to Baba bari naje na shirya to tai maganan tana tashi tai sama tashi Manaf yayi yace bari naje na kwanta Mama binshi Mama tai da kallo yawuce yafita shikuma Maheer da Muaz Kwallo suka kunna a falon suna kallo abinsu Baba kuma na duba wasu files dayasa Mama tadaukomai daga dakinshi




Wanka tasakeyi sanan tashirya cikin wani hadaden ashobe skyblue dogon riga aka mata daya kamata daidai ita ya balain mata kyau yabi jikinta sosai zama tayi gaban madubi tana kallon kanta dan tsaki tayi takai hannunta tana shafa siman rigan da akabi da net da kana iya hango tudun saman boobs dinta ahankali tace I hate style like this dake nuna jikina I will use gyalena narufe Mtsww tasake jan tsaki sanan ta zauna tai wani lafiyayyen dauri dazaka dauka make up artist ce tayi kwalli ta zizara sanan tadau wani lipgloss tasaka dayasa lips dinta shining pink din jiki yafito sosai dazaka dauka janbaki pink tasaka wayanta dake gaban mirror kiran samsung note 22 ta dauka ganin 10miss calls yasa tace OMG guys gani nan zuwa kunata kirana ganin battery ta yay ja yana nuna 10 left yasa takara jan tsaki tace ohhh namanta bansa chaji ba arayuwanta babu abinda take kiwuyan sawa irin chajin waya wani zubin sai wayan ya mutu russ ne shine zata dauka ma tasa a chaji jefa wayan tayi a shinning handbag dinta dake ijiye kan mirror sanan  tajawo wani hill na dolce gabana tasaka sanan tamike tsaye dan karamin gyalenta tadauka ta warware sanan ta yafashi ta gaba tsaf yarufe mata kirji sanan tadauki turarukanta ta feffesa kafin ta maida komi yanda yake tafito lokacin 1248PM



Saukowa tashiga yi daga Mama sai Maheer afalon yana kallon wrestling shima Muaz yatafi ya kwanta kamshin dayaji yasa yajuyo ganin Khairy yasa yasaki baki yace ke kece amaryan Wanan kwalliya haka Wanan ko ranan aurenki banjin zaki irin wanan kyan ba hararanshi tayi takalli Mama dake binta da kallo tace Mama kin ganshi ko hararan Maheer Mama tayi hakan yasa yay shiru itakuma takaraso wajen Mama tace Mama zan tafi ina Baba Ahankali Mama tace Ya kwanta ga kudi ya ijiye miki tanuna mata bandir na yan 200 dasauri tadauka tana murmushi tace Allah sarki Babana hes the best Mama natafi tai maganan tana wucewa zatai kofa Mama tace ke dasauri tajuyo takalli Mama dake kallonta Mama tace kindaiji abinda Baban ki yace ko 4 tamiki agida Umma kuma ki kama kanki baruwanki da maza ko abokan ango saura kuma naji kin wuce wani gantalin daban wlh kika saba any of them bikin dazakije na karshe kenan ban kara barinki fita dasauri tace Mama I promise nida keda bukukuwa I will not jeopardize that Mama bye Mama zan kawo miki alkaki hararanta Mama tayi tace banso wuce Direba na jiranki kofa tabude tafice Already Adamu Direba harya shiga cikin motan ita kawai yake jira wata lafiyayyen bakar Benz tabude baya tashiga sanan tace gidansu Zainab zamu Adamu to Hajiya yay maganan yana tada motan yaja saida sukahau kan titi sanan taciro wayanta dake nuna 9 yanzu sabida uban kiran dasuke mata kafin tama danna wayan wani kira yashigo da suna Zainab daukan kiran tayi tana dariya tace Amarya kinsha kamshi da turare kuma wani gida ne gani ahanya shiru tayi sai chan tace Okk sanan tace Adamu suna gidansu Amal wai ahankali tace to dan babu gidan wata kawarta dabaisani ba tafiya kai nisa sukayi sanan suka shigo wani hadadden estate daya cika da mutane kana gani kAsan biki ake wani Layi daban ya shiga sanan yay parking agaban wani hadadden gida murmushi tayi tace yauwa Adamu bani key motan narike dasauri yajuyo ya kalleta ganin kaman yanaso yaganota yasa tace zan taimaka musu dashine ana kwaso one or two things dazamuyi amfani dashi idan zan dawo zan kiraka saikazo mutafi tai maganan tana mikamai hAnnu ahankali yazari key motan yabata karba tayi tace yauwa katafi to dan sai yamma zan kiraka tai maganan tana fitowa daga motan shima fitowa yayi sanan tarufe motan ta danna lock tawuce cikin gidan abinta shikuma yawuce yatafi zuwa bakin titi ya tsaye abin hawa yahau



Tun kafin tashiga gidan takejin tashin kida murmushi tayi ta shiga gidan an gyara anyi decorating ga yammatan Amarya sai rawa suke suna hangota aka wani hau ihu Khairy Khairy ta iso ke join us wani irin murmushi tayi kaman abinda take jira kenan dasauri tai dance floor din DJ yasakan musu wani mad song rawa sukahau yi suna ihu suna hotuna idan kaga Khairy zaka dauka taje dancing school ne  suna haka saiga Amarya tafito wani mahaukacin ihu sukasa aiko tashigo itama sukahau rawa kaman mahaukata Amaryan ta rungume Khairy tana mata magana a kunne hakan yasa taciro wayanta tana video ganin wayan na nuna mata 1 yasa tai tsaki ta maida bag sanan taciro kudi tana ihu yara sai kallonsu suke taba manna ma amaryan It was fun she love her friends and she loves wedding har buri takeci irin na shagulgulan da zaayi idan bikinta yatashi


ALKAWARIN ZUCIYA 6


Wajajen 3 aka wuce da Amarya Kano ita kanta Khairy saida tadanyi kuka cus Besty tabata tausayi bayan an wuce da ita  tama Maman su sallama tawuce dan zuwa chan gidan dasukai party inda motanta yake a pake ahankali take tafiya ta balain gaji sabida rawan dasuka sha ita kadai kemagana tace yanzu inda Baba yabarni da hardani zaakai Zainab Kano gashi akwai more event a Kano dan murmushi tayi ita kadai tace Allah kaimu bikina wlh 2 weeks zaayi ana event hmm dan murmushi tasakeyi tace nidako saurayi banda shine nake planning biki na ahankali ita kadai tace saikace wata mara farin jini inada samari dayawa but duk mazan Nile ne basu hadu ba gasu yan rainin wayau saisa i dont even talk to them tai maganan tana murguda baki daidai lokacin ta iso wajen motan ahankali tace I want to marry hadadden namiji classic  handsome miji dat will make mata jealous of my catch tsayawa chak tayi takalli motan gabanta yadan fadi saikuma chan tace dont be scared Khairy you have to show Baba u can drive sabida yabarki kidinga jan motarki tana maganan tabude gaban motan tashiga tazauna tana sauke ajiyan zuciya sanan tamaida kofar motan tarufe kafin ahankali tace Ohhkay lets see sitbelt tasaka still gabanta nafaduwa bata taba tuki bafa kawai tasha ganin yanda akeyi sanan Maheer idan tashiga mota dashi yana nuna mata yace kihaka kihaka this and that ahankali tace Bismillahir Rahmanir Raheem sanan ahankali takunna motar gently gabanta na dum dum tashiga yin reverse kadan kadan kana gani kasan wacce bata iya tuki bane acikin motan nan sanan ahankali taja motan tana tafiya ahankali wani irin murmushi tayi cikeda jin dadi tace see ba gashi nan na iya ba ina tuki perfectly like a pro Ahankali takejan motan feeling a bit too sad sabida su Mama basu Bari takai Zainab ba ahaka hartakai gate din estate din tasa kan motarta tafice tana kalle kallen main road din gabanta na faduwa ganin motoci kowa na zuba gudu na wucewa yasa sabida irin karfin hali irin nata tasa motan ta shige cikin titin sanan tafara gudu Adan hankali ganin tana gudu kan titi smooth babu wani tangarda yasa tai murmushi tace wlh na iya sanan tawani kara uban gudu tana murmushi ko kadan bata lura dawani keke napep dake bullowa daga wani layi da mahaukacin gudu ba kawai danno kan keken shi yayi batare dayama kalli titin ba rawa jikinta ya dauka dudda da akwai tazara kadan tsakaninta dashi amman sabida yanda jikinta ke rawa tanason takara kara rage gudun datake kawai ta danna sauri before the blink of an eye jikake kwarap Motanta yadaki bayan keken da balain karfi tacigaba da tura keken gaba jikinta nawani irin rawa tama kasa taka burki Innalillahi wa innailaihi rajiun tafadi arude kaman walkiya sanan ta ci wani mahaukacin burki dayasa dabata saka sit belt ba data buga kanta a siteri ganin motan ya tsaya chak yasa dawani irin sauri ta murza key ta kashe motan gabaki daya tana wani irin sauke ijiyan zuciya da sauri dasauri tana kallon keken dake manne da gaban motanta zufa nawani irin keto mata daga goshi takasa ko motsi still in shock



Dawani kalan sauri direban keke napep din yafito yaci Kwalli a idanunshi yana sanye da Yar singileta daya koma brown tsabagen datti da jeans passengers shi maza biyu suma dake baya duk suka fito yana kallon yanda bayan keken shi yay condemn sauran motoci sukuma sunata wucewa abinsu tunda dai Allah yakawo sauki hatsari ne da babu wanda yaji ciwo to su karata chan anata wucewa ta gefensu



Saida mai keken yagama duba kekenshi tass yakalli yanda duka kwan fitilan dake bayan keken suka faffashe sun fadi akasa sanan ahankali yadaga kanshi yakalli glass din gaban motan ranshi amugun bace yana kallon Umma dahar lokacin takasa motsi sai numfashi datake maidawa ita kadai tasan yanda cikin jikinta ke rawa kafinma mai keken yay magana daya daga cikin passenger yace durun uwanchan amman matar nan yar balain rainin wayau ce Auwal muna tuki abinmu lami lafiya tazo ta dakan mana keke tamana Wanan uban asaran sanan ta zauna hankali kwance a motanta batama fitoba balle ta duba asaran datayi mana ba





Wani hadadden hilux baka dakana ganinta zaka gane da security personnel ne ke gudu akan titin ganin titin is congested go slow yasa yashiga  rage gudu yana kalle kalle wani kyakkyawan saurayi ne ke tukin motar yana sanye da kayan yan sanda daya balain haska farin fatan jikinshi ahankali yake tuki yanabin titin da kallon ganin yanda motoci suka cika hanya tam ga daga chan gefe gefen titi haka  ya hango accident akayi tsakanin keke da wata mota dayaba iya ganin cikin motan cus tinted glass ne ga masu keken sun fito suna duba keken su uku kana ganin yaran kasan irin rascals dinan ne dan tsaki yayi ahankali sanan ya gangara gefe yay parking motan shi murya chan kasa tace I hate this job Dad sanan ya kashe motan yafito yanadan yatsine fuska tareda maida kofan motan nashi yarufe


Cikin wani kalan bakan zuciya mai keken da aka kira da Auwal da idanunshi sukai jajir danshi kadai yasan wuyan dayasha kafin yasami keken nan mezaicema mutanen dasuka bashi haya cikin fushi ya nuna Umma dake kallonsu kuri ta glass din gaban motan da yatsa irin warning dinan yama kasa magana tsabagen zuciya hakan yasa ahankali Umma takai hannunta ta zare sitbelt sanan tabude kofan motan tafito ahankali jikinta na rawa tana kallon gaban motanta itama dayama bare yay kacha kacha saikuma bayan keken dashi ma ya baci wutan duk ya mutu sun faffashe sun fadi sanan takaraso ta inda suke tsaye nesa dasu zata bude baki tai magana Auwal mai keken ya tare mata numfashi yace ke dan ubanki dame kike takama agarin nan dazaki min condem din adaidaita sanan ki zauna cikin motarki batare dakinma fito kin duba barnan dakikayi ba balle kibani hakuri sosai kirjinta kewani kalan dukan uku uku hakuri tai niyyan tabashi amman yanda yazagi Babanta yasa taji ranta yabaci cikin fushi tana kallonshi itama right in the eye tace karka karayin kuskuren zagin ubana again inba hakaba wlh saina wanka maka mari besides ma kai agidanku baa koyamaka kaduba hanya kafin kashigo ciki ba eh Cikeda wata kalan bakar zuciya Auwal yana kallonta da idanunshi da ita kanta taga balain dake cikinsu yace ni kike gayama magana Dakewa tayi dudda kirjinta kaman zai tsage tace ai kai kafara dama ance idan Yaro bai koyi tarbiya agida ba zai koya a titi dan haka from today karka kara ganin mutum kai kuskuren zaginshi ko iyayenshi kafin ma Auwal dake dunkule hannu yay magana passenger sukace ke wai kinada hankali kuwa kin bugemai keke kinmai asara bazaki bada hakuri ba wani mugun kallo tamusu tace kune marasa hankali bani ba kuma hakurin bazan bayarba kuyi yanda zakuyi tai maganan zata juya jitayi an wani irin fizgo bayan riganta fut tadawo baya hartana turgeda kafa sabida heel din data saka wani irin bari jikinta yadauka tana kallon Auwal daya fizgota ganin yadaga hannu zai kaimata mari yasa tawani irin kwala ihu tareda kai hannayenta biyun tana kare fuskanta shiru taji batare dataji saukan Marin ba akan fuskanta hakan yasa ahankali kaman wacce tai sata ta shiga janye hannunta daga kan fuskanta tana nishi sama sama sanan tabude idanunta da kyau tana kallon gabanta inda su Auwal mai keken suke wani mutum tagani dogo fari kal sanye da kayan yan sanda yasha gabanta yana rikeda hannun Auwal daya kawomata mari ya murde dudda bataga fuskan mutumin ba dan yabata baya but she could see yanda bayan shi keda fadi gawani kalan bakin suma dake kanshi sun kwanta suna kyalli sosai zuwa shi wajen yasa wajen yadauki kamshin dayakeyi Daga Auwal har passengers din duka tsurewa sukayi suna mutumin cikin wata kalan kakkausan murya yace how dare you raised your hand zaka daki mace akan titi are u mad Yadakamai tsawa yana murde hannunshi da kyau ihu Auwal yayi jin azaba yace officer dan Allah kayakuri bazan karaba wlh bugemin mota tayi opisa cikin muryan nan nashi nabawasa yace and u dare to lift your hand up zaka daketa cause she is a woman and she is helpless alone Inda kanwar kace fa U deserve to sleep in jail dukan ku the three of you sosai suka shiga bashi hakuri tun tana kallonsu tanajin mesuke fadi har taji kanta nawani irin juyawa kaman tanajin jiri bugawan da kirjinta keyi yay multiplying da kusan dari hakan yasa gently tajuya tana daura hannayenta akan kirjinta tana kokarin ta saita numfashinta dake mata wuyan kamawa tana kokarin tafiya kawai tafiyan taji ya gagareta wani irin zubewa tayi jikin motan Karan faduwanta da bugewa da motan datayi yasa dawani irin sauri dagashi harsu suka kallo inda take ganin yanda take nishi tana beating chest nata tana kokarin numfashi at the same time tana kokarin tashi tsaye yasa dawani irin sauri yasaki Auwal yay inda take

616 755 PM 234 701 275 3212  ALKAWARIN ZUCIYA 



         M SHAKUR



7


Ganin Officer yasaki Auwal yay wurin yarinya datake abu kaman mai aljanu yasa suka juya da gudu suka shiga cikin keken su suka ja suka bace atitin saurama kadan sukara wani hatsarin Allah ya kiyaye

Ahankali ya tsugunna agabanta yana kallonta from head to toe this is the first time yake kallon fuskanta ganin yanda take fitarda  numfashi da kyar yasa yashiga bin jikinta da kallo kota bugene koko tai sustaining any internal injury neor something else but babu any sign ajikinta ahankali yasake maida idanunshi kan fuskarta yana kallon yanda take breathing not knowing exactly what to do da kyar ta iya bude idanunta tana nishi kaman zata mutu dishi dishi take gani sosai but she could see mutum akanta yana kaman yana kokarin karantan wani abu gently taga pink lips dinshi na motsi kaman magana yake mata amman batajin komi tashi yayi da sauri ganin kaman something is stopping her from breathing maybe tanada blockage a airways dinta bude gaban motan yayi ya cire jakanta dake wajen ya wurga kujeran mazaunin direba sanan yadawo inda take zaune akasa ahankali yasa hannunshi yakamo kafadunta sanan gently yadagata yadauketa yakai ta gaban motan yasata aciki yamaida kofan yarufe sanan yazaga ta dayan bangaren direba da sauri daidai ana kiran sallan magrib yabude kofa yana kallon yanda take wani irin dambe da numfashinta da kyar ta iya bude idanunta ta kalli jakanta daya wurga mazaunin direba dayake kokarin daukewa zai zauna ganin haka yasa dasauri yadauki jakan yashigo motan tareda bude jakan cikin zafin nama yashiga ciro abubuwan ciki kayan shafa kudi turare wayanta sai daga dan lungun jakan yaga inhaler

Post a Comment

0 Comments