Kasuwanci Na Hausa Novel Complete

Barka da zuwa shafin hausanovelsdoc inda muka kawo muku littafin kasuwanci na hausa novel complete wanda Asmabaffa ta rubuta takuma wallafah.

Kasuwanci Na Hausa Novel Complete

COPY BY ZAINAB BUTALAWA

   KASUWANCI NA

kasuwanci na hausa novel complete


Kasuwanci na 1-10

Official

By

AsmaBaffa

BISMILLAH


Alhmdllh fans Allah ya kara kawo mu sabon Novel dina KASUWANCI NA da fatan zaku bibiyeni muji yadda zai kasanceFatana Allah yasa mu karu da junaAllah yasa masa Albarka ya fadakar ya kuma nishadantar dakuina matukar Godiya masoyanamasoya novels dinamasu sharhi musamman AsmaBaffa fans clubTaskar fiddausi sodangida kuma House of Hausa Novels ina miko dubun gaisuwa ta gareku na gode da Sharhi

       

   Da fatan zaku ci gaba da Sharhi a kai Kai sabo da shine yake guiding writer ta rubuta muku me dadi da maanaidan ba Sharhi baya tafiya dai daiDan Allah a dinga Sharhi fans ana nishadi musamman yan gp na

    Akwai gps da dama da basa Sharhi ko tnx baza suyi ma bazaka ta musu posting shurusai ranar da ba ayi posting ba sai a fara neman novel ci gabaduk gp din da basa cewa ko Hi zan daina musu posting wlhda nayi daya biyu naji duf to shike nan sai suji duf nima




      Wannan page na farko na Sadaukar dashi gareki sweet frnd FLOWER

Kudin cinikin awarata nake irgawa duk da ba kudin arziki bane amma dukkansu daga yan goma sai yan biyar sai ko ashirinkanwata na shiga kwalawa kira MEENAT wai baza ki fito ba sai na shigo na marekiMaganar AMMA naji tana daga gefena a kwance saman yar tabarma tace Haba MUFEEDA ta wannan wacce masifa ce haka dan Allah ki dinga dagawa yaran nan kafa kannenki ne faAmma kina dai jin tun dazu nake jiransu su fito su tafi Islamiyya amma sai nauyi sukeyi kuma sun San cewar anjima zan soya Awaragashi gobe zasu zo suna takura mana a basu kudin Break to ai sai bisu a hankali dan Allah kinga ni ba lafiya ce dani ba kece komai nasu kece uwarsu kece Ubansu Mufeeda kece komai dinmuZuciyata ce tayi rauni nace to Amma ba komai na Dena kiyi hakuri Allah zai baki lafiya kinjiga kudin nan Amman mu bari na gyara gidan na daura mana tuwo naga muna da ragowar garin masaraMurmushi Amma tayi tare da kallona tace Mufeeda Allah ya miki albarka Allah ya baku miji na gariya baku yara su rama muku abinda kukayi mana na alkhairiMufeeda yau shekarar babanku Sha uku da   bacewahar yau ina Sa ran watarana zai bayyana da Zanfi kowa murna ya ganku Ku uku kun Zama yan mata gaku kyawawan gaske kamar indiyawamusamman ke Mufeeda kunfi kama da Shuwa sosai mahaifinku kika biyo domin shine fari kamar balarabe haka yake har kin fishi Hasken fata masu kuma su Meenat sune masu kalata wato su ba farare ba su kuma ba wanda zai kira su bakake duk gaku Allah ya bani Ku kyawawa farare daku amma duk kyan nan sabo da talauci ko Sallama ban taba ji ance ana sanku bawanda na tabbata da masu kudi ne komai muni auruwa sukeyimusamman ke Mufeeda kin kai har 16yrs amma nafi so na aurar dake tunda ba makaranta kike zuwa baBaki na turo gaba tare da sakin shagwaba ina shure shure kamar yarinya ina kukan sangarta Allah Nidai Amma bana son aure kuma ma nawa nakehmmm Mufeena Mufee tawa ai gashi nan kin fara girma har da Irgan dangiAmmah mene Irgan dangi tace gasu nan a kirjinki Kin fara Nono Mufeeda akwai maganar da za muyi anjima idan yaran nan sunyi baccikunya ce ta kamani nace to Ammah Allah ya kaimu bari na gama aikin ko kina da bukatar shiga bayi na taimaka miki Ae rikeni muje Mufeedata Allah ya miki albarka


kama Ammah nayi da kyar tana rike da sandar karfe wacce a asibiti aka bata ita na kaita har bayi ta tsuguna tare da Dafe jikin bangosai na fito bayan ta gama abinda zatayi ta kwala min kira na koma nace Ammah ko na goyaki Dariya tayi tare da cewa na gode Yata baki ji me Doctor yace bana dan dinga takawamurmushi nayi wanda yasa hakorana kanana farare suka bayyanadimple dina ya lotsa riketa nayi muka fito taresai Lokacin kannena MEENAT da MAEESHAH suka fito cikin shirin makarantar Islamiyyana kallesu cikin tsafta kayansu yasha gugasun bani shaawa naji inama nima haka nake zuwa kullum amma ina bazan samu dama baamma Alhmdllh tunda kannena suna zuwa ba matsalaAmma ce ta kalleni cike da tausayawa tace Mufeedata Da sauri na dawo daga tunanin dana lula na kakalo Murmushin dole nace Ammah ki huta bari na gama aikin naje na siyo kayan alewar madarakinga gobe kuma da safe Kosai yana jira shimaamma ni naga awarar tafi riba maAmmah tace Mufeeda wannan satinfa naji zuku yi Allurar polio vaccine da kukewa yaraMufeeda tace wlh Ammah ba sauki abin ni haushi na ma gidan masu kudi kantama kantama na GRA Ammah ayi ta wulakanta mu da kyar mukeyi muna Shan wahalawani gidan ma kafin ka shiga tashin hankali ne ko ina securities neaikina naci gaba da yi muna hira da Ammah mahaifiyarmusaida na gyara gidan tas na kunna turaren Wutar kamshi duk da gidan ba wani me kyau bane amma ita tsafta bata buyaAllah ya haliccemu da tsananin Tsafta wanda duk Balain mutum bazai ce gidanmu akwai digon wani abu na kazanta ba haka muke gaba dayanmumiyar Kubewa busashiya na kadana tuka tuwon masara na kwashe cikin wata tsohuwar Cooler dunmunayi wanke wanke da wanka na shirya cikin kayan gwanjo na Riga blue me layi layi na faritare da skert shima ruwan gorofarar Powder na shafa da Vaseline a lebenaHijab me hannu nasa wanda ya wuce gwiwata nace Ammah bari na siyo kayan nan nazo na fara soya Awarar dare kinga magriba ta gabatoFadada murmushinta Ammah tayi tace a dawo lfy Allah kiyaye hanya


    Ameen nace tare da fita waje ina dan wasa da kudin dake hannuna cikin unguwarmu layinmu na bari nayi tafiya me Nisan gaske Allah yasa ma ba rana sai da na gaji sosai kafin na karasa wata yar kasuwa karama da ake saida kayan abinci da fruits etc inda na saba siyen waken kosai da sauran kayan Sanaa ta na karasa da faraa dukkanmu munyi sabo da juna sabo da yau da kullumkudin na mika ina bi ko wanne layi duk na hada abinda nake bukata kaf aka hado min a wani katon buhun bacco na fito da kyar nake dagawa ina nishi haka nake tafiya a hankali wani dattijo ne yace yarinya kawo a daura miki a kai ai zaifi ko Murmushi nayi masa ya amsa ya daura min na masa godiya naci gaba da tafiyata da kyarsai da nayi nisa na shiga wani layi wanda manyan gidajen masu kudi ne na gani na fadaGRA ce ta masu kudi nabi ta ciki sabo da kullum ta hanyar nake wucewa ko sabo da nasha kallon hadaddun gidaje tare da Lambu masu kayatarwa duk kuwa da cewa na saba shiga sabo da rigakafin polio na nake aikin dole muna neman Izni mu shiga sabo da tare da masu Unguwanni muke yin rigakafin dole su yarda a shiga ko Police su kama me gidan haka aikin yake


    Wasu motocine a kalla sun kai guda takwas a jere dankara dankara ban taba ganin irinsu ba sai yau da suka shararo da uban gudu kamar zasu tashi sama cikin layindai dai wani gida suka Parker wanda gidan yafi kowanne kyau a layin da gudu na matsa tare da rakubewa a jikin ginin gidan ina kallon ikon Allah 


da sauri naga sojoji sun fito daga sauran motocin tare da zagaye wata uwar shahararriyar mota me kyau da tsada na fitar hankaliwani dattijo ne ya fito fari kar dashi yana sheki da Alama kudi sun ratsashi a matukar hasale ya fito daya bangaren ma wani wani mashahurin matashi ne ya fito da sauri a matukar hasale cike da isa hade da Izza Saurayin kamar balarabe ko Bature haka yake duk Haske da kyau na da ake fada sai naga wannan ya wuce nawa ya zartani a komai nan take na raina kaina musamman yanda na kalli shigata babu maraba da Almajira mara gata


    Saurayin bazai wuce 35years ba ya kai karshe a haduwa gashinsa abin kallo kansa style din askinsa abin kallo ne abin birgewa da shaawaidonsa ya budeban San sanda nace wow a raina ba idonsa kamar madara yana wani lumshewa gasu Dara Daragirarsa har kamar zata hadega wani dan saje da gemu masu matukar kyau da suka kawata fuskarsahancinsa me matukar kyau kuma baiyi tsini da yawa badan bakinsa wow masha Allah ga wasu pink lips duk da cewa nima bakina kamar cokali bazai shiga ciki ba gashi lips dina jajir dasu amma sai naga wannan kam nasa sunfi nawa komaikuma sai na tashi me duhu a kansa ko dan shi Hutu da Naira sun ratsashi ne oho Kana nan kayane a jikinsa wandon pencil Jean brown colorrigarsa fara tas da top Brown ya daura sama takalminsa fari half cover flat shoeshi ba gajere ba shi ba dogo da yawa bahaka ba ramamme ba kuma bame kiba bakai mashaAllah da a mafarki na ganshi ba shakka Aljani zance


     Dattijon cikin farar shadda kar cike da Fada yake magana da alama da Saurayin yakeAAYAN  will u hear me out plsda sauri Saurayin ya bata rai cike da fushi yana shagwaba kamar dan yaro cikin muryarsa da ta girgiza ni sabo da dadinta yace pls Abbi I knew it just leave me alone For God sakeHajja she is ur mother not mine so Abbi kaine ya dace kabi Umarninta ba ni bataya zata dinga takura min ni kadai ne jikanta gasu nan da yawa maza da matako kawai dan ni bani da Mahaifiya bata rayesannan mahaifina bashi da lafiya bakwa kaunata shi yasa ni kadai ake ma haka yanzu ina Abuja kace dole sai na dawo Kano da Zama kusa da Kuban taba wani rayuwa a kano ba ka sani sabo da kana matsayin mahaifina nake maka biyayyasabo da gudun saba maka na bar muku gidankubana amfani da sisin kudinkaAllah ya bani nawa Abbi har na fika ma maybe kudinBut why mewhy are u doing this to mekowa a Family kaf maza da mata nine ba a so me nayi musuidan sabo da Umma ne bata raye sai na hutaAbbi ban shirya aure ba kunsa nayi ba muguntar da ba ayi min bahaka mun rabukun kara aura min wata itama mun rabu sabo da matsalar dake damuna na rashin lafiyar haihuwa Abbi kun San bani da lfy bazan iya Rayuwar aure da mace ba akan me zaku ce na kara auro wata so kuke mata su kasheni bazan iya musu amfanin komai badalilin bacin rannan da nake Sha kasan yanzu Hawan jini gareni me karfin gaske ko wanne lokaci zan iya rasa rainasannan kasan Ina da diabetes dalilin Hawan jini yasa ya kamani tawakali da addua nakeyiAbbi why not bakwa tausaya minbakwa tausayin rayuwata tun tasowata a wahala na tashi a duniyawannan yasa na tsani mata wlh Bana kaunar duk wata budurwa komai kyau da hankalintadalilin haka bana Hulda da kowa family da frnds etc ni kadai nake rayuwata sabo da bakin ciki da halin da nake ciki shi yasa nayi nesa da kowagwiwoyinsa ya  dire a kasa hawaye na kwarara a idonsa kamar ruwa tare da rike kafar dattijon yace Abbi ka fadawa Hajja zan zauna daku amma pls kar ayi min aure again ko me kuke so wlh zanyi amma yanzu banda aureAbbi ka tuna kusan mutuwa nayi yanda mata suka ci min mutunci


    Kallonsa Dattijon yayi tare da cewa tashi Aayanzan yi shawara da yan uwana muyi deal duk abinda mukace zakayi ka yarda Ba tare da yayi tunanin komai ba Yace ae Abbi na yarda indai bazanyi aure ba shike nanAbbi yace an gama ko ka samu Lfy kana haihuwa sai na yarda zakayi aure ka tabbatarKuma ko kaga wacce kake so baza ka aureta ba har sai in mune muka yardacike da murna yana murmushi ya daga kai alamar yes ya AminceAbbi yace Good for ukar kaga bani na haifeka ba kace zaka min butulci zan iya yi maka abinda baka tunanika dinga tunawa da halina kasanni sarai zan iya yi maka ko mene ne ba ruwanaShi dai Bayan murna yake yace ya yardaTashi muje daga yau ka dawo Kano gida daya zamu zauna sai dai jefi jefi kaje Abuja harkokin business dinka shima sai idan da yardata idan kuma kaki zan iya haram tama Business dinka gaba daya kasan nasan komai akan hanyoyin da zan lalata duk dukiyar daka mallaka


Aayan ne yayi murmushi tare da cewa Abbi matukar baza kuyi min aure na zauna da mace ba zan iya mallaka muku komai nawana tsani mace a duniya ni bana son Zama dasu wlh ko yan uwana bansokallon tsana Abbi yayiwa Aayan tare da cewa dan kawai baka da lafiya ne Man amma wa yaki mataai mata sune jin dadin duniyakaga duk son kudinaSaurayin ya daga kai yana murmushin takaiciAbbi yace to duk kudin da nake nema sabo da mata nake nemansumata mutanenmu in ba su mene amfanin kudi

   Kai Aayan baka da amfani a duniya fa da kai da gawa daya kuke Banga Amfaninka ba samto kai baka haihuwabaka iya Yiwa mace komai me kakeyi kake wahalar da kanka wajen neman kudigaka a haka kamar Namiji Amma na tabbata in dai ba mune muka zaba maka mace ba irin almajira ko talakawa sune suke neman kudi sune yan wahala sune wahalallu wanda basu san kansu babasu san me duniya ke ciki babasu da wani amfani da irinsu ya dace a nema a aura maka sune watakil ka samu me son kudi tayi kasuwanci da kai ta samu kudi ta zauna da kai da hakuri


    Aayan yaji matukar zafin kalaman Abbi wanda gaba daya ji yayi kamar ya mutu Sabo da bacin raihaka ya hakura ya danne bakin cikinsa Amma idonsa ya kada yayi jajirsai da Abbi ya gama gasa masa bakaken maganganu masu zafi sannan yace tashi muje ciki kasa a kawo ma motocinka kasan ko aron nawa ko na gida babu me baka kamar yanda kace kowa yayi amfani da kudinsaAayan yace ai duk new nayi Order an siyar da wancen saban yayi za a kawo min  gobedariyar mugunta Abbi yayi tare da cewa kana kokari fa wlh ni da kai da gawa haka nake kallonka baka da amfani a duniya me zaka amfanawa waniko mace baka amfana mata komai ba sai wa Bakin ciki ya tokare zuciyar Saurayin yana tsaye a gate har Abbi ya bawa Sojojin da suke can gefe dasu Umarnin su shigo da motocin gidanan suka bar Aayan wanda ya dafe saitin zuciyarsa da hannunsahar suka shige da motocin gidansuna rufe gate din ya fadi a wajen ya sankame kamar ya mutugashi unguwar shuru ba kowa bare a taimaka masa


    Ni da nake Rabe ina jin komai da Sauri na jefar da kayan dake kaina nayi kan wannan Saurayi cike da tausayawatunani na sumewa yayina rasa ya zanyi na tasheshi robar ruwa dake hannunsa na Eva na fisgo da Sauri hannuna na rawa na bude tare da kwara masa a fuska Amma shuru bai tashi bahannayena biyu na daura saman kirjinsa ina dannawa kamar yanda nake gani likitoci nayiyi kawai nakeyi ba ji ba gani danna kirjinsa nakeyi sosai ina nishia rude na kara kwara masa ragowar ruwan na sunkuya a kansa kamar zan shige masa cikikamshin turarensa yasa kamar na sume Sabo da dadifatarsa laushi kamar auduga lumiswukil naga ya bude ido mun hada ido dashi kafin na kifta ido naji an sharara min uban Mari sai da na daina gani na wasu yan lokutakafin na dawo hayyacina yasa kafa ya harbar dani da mugun karfin da sai da nayi uwar Sufa na tuntsira naci ta ka na kife can gefe yarafnan take lebena ya fashe fuska ta ta kumburasabo da rashin Imani bai kyaleni ba takowa yayi har inda nake ya kara Sa kafa yayi ball dani sai da kaina ya bugu da wata yar bishiyakafa yasa ya take hannuna dake yashe kasa ya murzaidonsa yayi ja da hannu daya ya damki wuyana ya shake tare da rabani da kasa ina kakariMari ya shiga yarfa min ban san iyakacinsu ba sannan ya jefar dani kasa kamar wani kayan wankiKuka me karfi na saki duk dauriyata ban san inda kaina yake batunani na mahaukacine dama asheina ta kuka a wajen Fuskata ta kumbura sosai jikina duk wani wajen ya farfashe Sabo da ball da ya dinga yi danitsorinsa ya shigeni ina nan wajen har ya shige cikin gidan da motoci suka shigaAllah ne ya taimakeni wani dattijon kirki yazo wucewa a motarsa yace yarinya motace ta bigekiBan san me zance ba kawai sai nace kare ne ya biyoni shine na dinga faduwamutumin bai yarda ba Amma ya Kira Driver dinsa yace ka dakko mota ka kai yarinyar nan asibitina ka samu Sajeeda tayi mata dressing ka maidata gidansu kayi Sauri dare ya faragodiya nayi masa ina kwance a kasa ina tunanin zalincin da Saurayin nan ya gwada min tare da rashin Imani daga taimako sai naci Dukan tsiya

haushinsa naji sosai a raina ga tsoronsa da ya dasu a Cikin raina bana fatan sake ko kallonsa Sabo da tsoronsa nake ji yanzu


   Ina tunani a kwance Dattijon Driver ya karaso tare da bude min mota da kyar na iya shiga motarDriver ya saka min kayana a Cikin motar wanda na siyo a kasuwawani hadadden asibitin kudi ya kaini nan take akayi min komai da ya dace aka bani magunguna da Alama asibitin dattijon mutumin ne da ya Bada motarsa a kaini gidaDriver na gwadawa gidanmu ya kaini har kofar gida sannan ya miko min dubu biyu yace na sha Maltina inji Alhaji me gidansada kyar na yarda na karbashima sai da Driver ya nuna baiji dadi ba sannan na karba tare da zuba godiya na dauki kayana na shige gidanmu shi kuma yaja mota ya tafiina shiga gida Kannena Meenat da Maeeshah har sun yanka awarar suna jirana da gudu suka taso suna Sister Mufee me ya samekilfyhatsari kikayi ko motace ta kadekikinga yanda kika koma kuwaDa Sauri Ammah ta fito da Rarrafe kamar zata kifa Sabo da rudewa tana Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun shine Abinda Ammah ke furtawa tana Hawaye tare da cewa me ya samu MufeedataMe ya samu katangarmu Kuka na fashe dashi me karfi tare da Rungume Ammah ina cewa ba komai Ammah a wani layi ne kare ya biyoni na dinga gudu na fada cikin kwalabati da kyar wani ya taimakeni ya kaini asibitinsa kinga an bani magani harda kudi dubu biyu na shan Madara da MaltinaAmmah tace wannan waye me kirki hakaWlh Ammah wani  ne Doctor ne Babban mutum ya sa Driver dinsato ku dai kiyaye da mazan zamani a tsare mutunciAlhmdllh tunda komai yazo da saukiMeenat ki dafa mata ruwan zafi ta gasa jikinta taci abinci tasha maganin ta kwantake Maeeshah jeki kofar gida ki fara soya awarar kafin yan siya su fara taruwa mikewa mukayi tare da aikata abinda Ammah ta ce

Karanta: Nihaad Hausa Novel Complete


    Bayan nayi wanka na gasa jikina Mai na shafa sannan na Sa doguwar riga mara nauyi itama yar gwanjo ceabinci na dauko tuwon da nayi dazu naci na koshi domin ni cuta bata hanani cin abincikomai rashin lafiya sai naci na koshi nayi lufbayan naci Ammah ta dinga ballo min maganin tana bani ina sha har na gamatace kawo na shafawa na shafa mikiAmmah zan shafa ki barshi kinga ke ba lafiya gareki ba bayan na shafa jikin Ammah na koma na kwanta ina tunanin Saurayin dazu tare da maganganun da naji sunyi nake ta faman tunani shi kuwa mene tarihinsa me mutanen nan suke nema dashi ne hakatunowa da nayi irin rashin Imaninsa nan take na firgita tsoronsa ya kara shigata na kankame Ammah har bacci ya kwashe ni Washe gari da asuba da kyar na tashi na gabatar da Sallah tare da Azkhar kamar yanda muka saba gaba dayanmuBayan gari yayi haske naje da Sauri na hada wutar  itace na daura ruwan zafi yana tafasa na dama koko sannan na kafa daya kaskon gefe daban na fara suyar kosan siyarwa taana sallama ana siya sai kuma ruwan zafi ya tafasa na kwalawa su Maeeshah kira suzo suyi wanka su wuce schlda Sauri sukayi wanka suka shirya tsab cikin Uniform dinsu wanda yasha wanki da gugaKokon dana dama musu suka eba tare da kosan suka ci suka koshi sannan suka kaiwa Ammah nata itamaNima ina aikin Suya kosan siyarwa ta ina shan koko da kosai na Sister ya jikin naki gashi kumburin ya bajemurmushi nayi tare da cewa Alhmdllh kuje kar kuyi late ayi karatu da yawa banda wasabani da burin da ya wuce naga kunyi karatu sisters ku dage cikinku mu samu lauya da Doctor dariya suka dingayi Ammah ma tana tayasu cike da tausayawa Mufeedakudin Break na mika musu nace gashi yau ba ashirin za a baku ba Hamsin Hamsim zan baku kuci me dadimurna suka dinga yi suna tsallen murna tare da godiyaNace kuje mana Gashi karbi Meenat kece babba kuyo mana Cefane muyi miyar egusi da tuwon shinkafa ki taho da nama na dari Uku muma muci dadi ko Ammah Murmushin farin ciki Ammah ta saki tare da kallona tace Allah ya muku albarka dai yaran nan


bayan sun tafi na gama siyar da kosai na ya kare kaf ina ta faman murna na lallaba jikina na gyara gidan fes na tattaro kayanmu har na Ammah da kannena na wanke su fes na shanyaAmmah wacce ta rarrafo ta zauna saman tabarma tace Mufeeda me za a dafawa yan makarantar ne yau Na gaji taliya zan dafa da mai da yaji kafin dare sai muyi tuwoneh hakan ma yayi ai tunda muna samun na sawa a bakin Salati ba kamar lokacin baya batashi ki kokarta ki gama ke ma ki kwanta ki huta idan sun dawo yau ba Islamiyya sai suyi girkin darenamsawa nayi da to na mike nayi abinda ta Umarcenina hada mata ruwa na kamata har Nayi tayi wanka fes na koma na riko ta muka dawo naa tayata shiryawa tsaf muna hira 


ina gamawa na hada yaji me dadi yasha hadi na soya manjana gyar dan kitchen dinmu wanda yake na karfen langa langa neAmmah na zubawa na kawo mata tare da ruwataimaka mata nayi ta zauna nima nasa hannu muka ci muka koshi muna Bada dunkulen Maggi starSallah muka gabatar ta Azaharsai ko mukaji Sallamar Yan makaranta su Meenatda gudu suka shigo suna sallama suka rungumeniIdo na waro mene hakan Sis wlh wani ne yace yana son Maeeshah mu kuwa muka zabgo da guduke kin ganshi wlh in banda wari ba abinda yakeyi wai yanzu Ammah duniya ta lalace me kudi bazai Hulda da talaka ba komai kyanka indai ku talakawa ne babu me kulaka sai talaka dan uwankaAmmah tace ai duniya haka ta koma idan da gate a gidanku to me mota ne zaizo idan babu kuwa sai dai dan uwanka talakaYanzu kalli irin kyawu da Allah ya zuba muku Amma babu me zuwa wajenku talakan ma ya gagara sabo da talakan ma gudun talakawa yake Allah kayi mana maganidan baki na na turo Ammah ke komai kice aure wai shekarunmu nawadan gidanku gata nake nema muku yanzu ko idan da kunyi aure ai kuna da yancinku ko ba komai sai kiga kun huta shine burinaAmmah wa zai kula dake to aini aure bai taso ba a wajena Ammah wlh Bazan iya aure na barki a haka ba ko da kuwa zan dawwama ba aure ne a duniyaki daina zancensa indai kina so hankalina ya kwantaMaeeshah tace Sis manya bari muyi girkinmuharararsu nayi nace kuje dai ku cire Uniform kuci abinci kuyi sallah ku huta sai kuzo ku fara aikinni yanzu kun san kasuwa zanje siyo kayan da nake siyarwa cittakaninfaribarkonowakekanwaSabuluomomaggi kala kalahar su Aya duk siyarwa nakeyi duk wasu kana nan Abu na amfaninmu kayan girki ina siyarwa a gidanmuhaka ina saida su Ayaridikantualewar Madaraalbishir etc su Maeeshah nake sarowa suna Tafiya min dasu makaranta su siyar minina kosai na siyarwada rana na siyar da su Zobo kunun zaki da dare kuma nayi Awaraina kitso da zanen lalle sosai kudi idan sunzo zanyi na karbi kudinasannan ina cikin masu polio rigakafiduk wani neman kudi na Sanaa kanana na gida ina yikusan komai ma siyarwa nakeyikullum bani da lokaci bana zama sam sai neman kudi dashi muke ci muke shamuke Sutura tare da makaranta


biyawa Ammah kudin maganiyanzu kasuwanci a duniya shine buri na wanda har ya kai ga dasa min matsiyaci son kudi tare da tattaliiya lissafi da planningsabo da yawan Hulda da mutane yasa na kara gogewa na waye sosaiakan kudi ba mutunci ko bashi ya shiga tsakanina da mutum akan dan Kasuwanci na to fa zan iya rufe ido dole a bani makamar zanyi sata haka nake matukar neman kudi


    Yau Monday Su Meenat suna schl na gama komai na fita naje wajen saro kayan Yara na shaina siyowa kala kala har su tuwon madara na wuce schl na kaiwa su Maeeshah domin su siyarina zuwa na hango Malam ya sa Maeeshah kamun kunne ya hanata ko shiga aji wai sun makara


    Ina matukar Jaje gareku fans da raguwar shekaru da muka samu domin ba karuwa shekarunmu suka yi ba raguwar suka yiana ta happy new year a daina addua ya dace muyi Allah yasa mun shigeta a Saa tazo lfy ta wuce lfyAllah yasa ta Zama shekara me amfani a Rayuwar muta zame mana farin ciki da samun ci gaba a cikintaAllah ka kara mana lfy da Nisan kwana me amfaniAllah ka kara mana imaniAllah yasa muyi karshe me kyau idan tamu tazoAllah ya azurtamu da mutuwar shahadaAllah ya rufa mana asiri duniya da lahira Ameen


AsmaBaffa


KASUWANCI NA

Kasuwanci na 21 to 30  25


Official


By

AsmaBaffi

  Wannan page naki ne HUMAIRA Allah ya bar kaun

       Wajen malamin naje da kyar na rokeshi ya kyaleta yace tayi Sauri ta karbi sakon ta shiga aji nima ina mikata mata na kama hanya sai gidawashe gari kuwa da sassafe na shirya na barwa su Maeeshah suyar kosai da Komai nayi shirin Tafiya rigakafin Polio dama indai ina rigakafin nan to dole  Meenat ce zata zauna tayi dukkan abin da nake siyarwa har na gama Polio sannan taci gaba da zuwaSabo da Ammah bata yarda da talla ba shi yasa Sam bama fita talla a gida muke sanaarmu     Maeesha kadai ke zuwa yanzu kafin na gama Vaccine


     Inda muke haduwa da maaikatan unguwar da mukeyi naje na samesu cikin Napep na sauka cike da faraa da murna muka gaisa da junasannan na dauki akwatin da kwalaben Allurar suke ciki ga kuma supervisor dinmu da sauransusabo da box carrier ce ni ba a biyanmu da yawa dubu hudu da dari biyar muke dauka idan an gamabani da ilmin da za bani Babban matsayihaka mune da wahala mune muke daukan kudi kadana kafa muke Tafiya muna shiga gidaje ana house markingsai 2pm muka tashiwashe gari ma bangaren unguwan da mukaje dabana kwana na Uku kuwa da muka fara GRA din nan da na taba ganin Saurayi Aayan ya zaneni yau gidajensu zamu shiga aikin Vaccine duk da cewar ban taba shiga gidan baamma bana fatan shigarsaina ji ina gani muka zo jikin gate dinsu


takadda aka rubuta sannan akayi knockingSojoji sunfi  biyar ne suka fito kamar zasu masgemusai da aka basu takardar cewar yan Polio ne suka zo ga me unguwa a tsaye kuma dole sai an digawa yaro dan kasa da 5yearstakardar suka karba sannan suka koma ciki zasu nunawa me gidansutunda suka shiga muna tsaye a wajen gate har sai da suka kwashe fin hour guda sannan suka fito sukace ance mu shigamaaikatan sai murna suke zasu gano haduwar gidanni kam cikina ya duri ruwa bana fatan shiga Amma ba yanda zanyi haka na fara binsu kamar kwai ya fashe min a ciki sanye nake da red hijab dina me hannu har kasa duk da cewa nayi kyau Amma sam na raina kaina


   Muna shiga muka firgita domin maaikata da Securities ne ko inagidan ko ina kamshi ke ratsowa yana shekiga wasu motoci sunfi ashirin a gidan lafiyayyuhar round ne a gida kamar wani Babban titi tsakiyar youturn din ruwa ke tsiri sama yana shararowa a kasa kuma yana komawa kasan yana fesowaa film ake ganin irin wannan gida jencan gefe ga wasu sweeming pool har kala biyuko ina flowers ne a gidanduniya guda ce a gidan domin wani part din ma ya dace ka hau mota sannan ka Isa in kuwa ba haka ba zaka gajiwani soja ke mana jagora muna binsa a baya har muka zo wani garden ba abinda babu a garden din nan domin har da filin ball da Sauran wasanni iri irikida ne na wakokin Naija ke tashi har tsakiyar kai a manyan speakersyan mata su Uku kyawawa yan gayu ne sanye cikin English wears Wando short da yar vest suna ta faman taka rawa hannunsu rike da kantama kantaman wayoyigefe wasu Yara ne sunkai su hudu mace daya da Maza su Uku sun sha kyau cikin kana nan kaya yan yayi suna ta faman buga ball abin mamaki ko kallon inda muke basuyi ba kamar ma basu san mutane sun wuce ba haka muka ci gaba da Tafiya muna yin gaba kadan sai ga wasu Maza zaratan samari suma hadaddun gaske baza su wuce 29 yrs ba su uku suna zaune a wasu kujeru masu malafa a sama game kawai suke bugawa suna dariyako wanne yasha kyau cikin kana nan kaya kamar a Englandkaina nidai yana kasa Amma suma samarin inda muke ma basu kalla ba balle musa rai za a kula mutafiya dai muke muna bin Soja can wani wawakeken fili ne fetal yasha tsari da haduwa carpet dan gaske ne a kasan wajen da wasu manyan pillows ko ina yasha flowers ga wasu grass carpet wata mashahuriyar Dattijuwa tsohuwa tukuf muka hango kwance tayi kwanciyar Isa kamar sarauniya fatarta lumis fara kar duk da cewa ta tsufa Amma akwai hutu kayan marmari sun ratsata


    Mu matan da muka shigo dama mu Uku neda hannu tayiwa Soja Umarni nan muka ga yace gasu nan yayi gaba abinsahar kasa na durkusa na gaisheta cike da girmamawasu kuwa sauran matan cewa sukayi ai maaikata ne wlh baza su durkusa ba duk wulakanci da akayi musu ba wanda ya musu ko sannu bare kallon arzikigata ita wannan ta tsufa ma Amma bata saduda da duniya ba har wani jin dadi take


   Kallonmu tayi tsohuwar ko amsa gaisuwata bata yi ba tana yatsina fuska tana kebe baki tare nuna Isa ta fara magana kuje dan Allah kun tsaya min a kai wari yana hawa min kaida mamaki muke kallon ikon Allahcan ta jawo waya ta danna kira tana jan tsakisai ga wata da Alama yar aiki ce harda Uniform dinta dauke ta fito da ruwan roba tare da wani liquid soap me kamshi tace kuzo muje ku wanke hannunku sai a diga musu polioTsohuwar nan cike da izza tace wlh badan Hukuma da suke hadawa da ita ba baza a digawa jikokina ba samkazanta abinda ana kaisu asibiti ayi musu me kyau ko kasar wajene ma sai suje a diga musu Amma a dinga turo mana kazamai gidaje jasu can kujeina jin haka na daga kaina ina kallon sararin samaniya tare da kallon tsayi da girman building din nasu kamar baza a mutu ba katanga ma tayi tsiri sararin samaniya kai kace Malaikan daukan rai bazai iya tsallakawa baa raina nace to yaje har fadar shugaban kasa ma ya dauke Yar Aduayau Ina sani Abacha 

 

      Ina wannan tunani sai ga wasu dattijan Maza farare suma su Uku sun fito harda Abbi wanda na taba gani zama sukayi kusa da tsohuwar suna maganalokacin mu kuma an jamu part din yan aiki nan aka dinga dirje mana hannu sannan suka fito damu wajen yaran dake Garden tare da yan matan nan masu rawa da Wando 3qtr muka komanan fa da kyar aka jawo mana yaran ana cewa Hajja ce tace ayi musu suka bude bakin su tas dasu cikin taka tsantsan na diga musu yanda akeyi sannan nace to Alhmdllh mun gama mun godeme rubutu ta cike talley sheet dinmuna jiranta tana rubutu yan matan nan dake rawa dauke da cup a hannu suna shan lemo suna rawa suna bige mu Amma ko kallon mu basayi bare mu Sa ran ko Sorry zasu cegefe dasu muka matsawata ce ta fito cikin shiga ta alfarma zata kai 40years da Alama da yaranta a ciki domin munga suna daga mata hannu bye Mumtayi murmushi Tare da shigewa mota Driver ya jata ta daura kafa daya kan daya tana karanta JaridaNumfashi ne ya kusa daukewa sakamakon wasu motoci da suka keto cikin gidan a kalla sun kai guda biyar suka Parker zunzurutun Securities ne suka fito tare da zagaye motar kamar wani Shugaban kasa ne zai fitobude motar sukayi muna tsaye muna shan kallo Wani arnen takalmi ya zuro waje nan take kamshinsa ya cika gidan me dadiya dan jima a haka kafin daga bisani ya fito cike da takama kamar wani Sarkicikin kana nan kaya yake yau ma farin Wando  pencil sosai rigarsa Silver color da Golden rubututakalminsa Silver yasha masifar kyauduk wanda ya ganshi zai rantse ba mutum bane Sabo tsabar baiwar sura da kyauga iya daukan wanka yanda yake matukar kyauyan matan nan ne muka ji sunce Hi Ya Aayanko kallonsu baiyi ba sai ma wani kallon Banza da muka ga ya watso musu kamar yaga kashisabo da nima gwanar mugunta ce a raina nace Allah ya kara shegu ga ubanku a girman kai gwara haka


    Matar da muke aiki da ita wato Salima itace ta kalli yan matan tayi dariya wai irin ta tura musu haushiai kuwa ba zato muka ji karar Mari a fuskata domin suna rawa tunaninsu nice na musu dariya shine daya a ciki kawai ta daukeni da shegen mari wanda ya jawo hankalin wannan Saurayin da Sauran Maaikata kainaKuka na fashe dashi a wajen nan take na fadi a wajen na dinga shure shurewanda muke Polio ne suke bani baki kan nayi shuru mu taficikin kuka nace Wlh sai na rama mikewa nayi a hasale na cakumo daya a Cikin yan matan wanda ban san wace ta mareni ciki ba nidai na kama daya tare da makalkaleta na cisgo gashinta na murde na ja da karfisannan na dalla mata mari har biyu na sake ta na zura da gudu domin sunyo kaina da kwaben lemon me tsada da suke sha zasu fasa min a kaidaya ciki ta jawo Hijab dina ta bayaSecurities sun taho Saurayin nan ya dakatar dasu cewar a kyalesusuna kallo sun rike min Hijab na sunkuya tare da zare Hijab dina na bar musu a hannunsu na Arce jikin gate ina rokon a bude minSaurayin nan yace kar wanda ya bude minHar yan matan nan suka zo kaina na kara runtumawa da uban gudu amma saida suka kamani suka rufarmin suka dakeni sosai naji jiki sai da suka gaji dan kansu sannan suka tafi ina yashe a kasasai Hawaye nakeyi abokan aikina suka dagani da kyar sannan naga wannan Saurayin yace a bude mana mu bace a ganinsa ya tsani mata ko da yan uwansa ne baya kaunar ganinsusai da na tabbatar an bude mana nasa kafa ta daya ciki daya waje sannan nace kai yan mataduk kuwa suka juyo suna kallona nace Allah ya Isa kuma sai na rama watarana idan kanwata ta zama Doctor ko Lauyakallon banza suka min tare da tabe bakinace zaku gani wlh kyaleki nayi dan ba a kan KASUWANCI NA kuka tabo ni barigimar ba akan kudi bace Amma da akan kudi ne ai da sai da a mutu a gidan nan shegutsinannu tambadadduarnajahilaidabbobi kuma dukkan yan gidan nan na zaga na nuna Saurayin nan dake tsaye nace harda kai da wannan tsohuwar dake zaune a carpet a sanar mata dazagina da iyayenku baki dayasannan kuma ina tunatar muku Malaikan mutuwa na nan zuwa wataranasojoji ne suka yo kaina na Arce da uban gudu tare da cewa Allah ya isa dana gaishe da tsohuwar nan kekakashashiyana dinga zura uban gudu Allah yasa time din tashinmu yayi kawai na fada Napep ina haki sai gida tazarce kawai tun daga Cikin gidan nake gudu har nazo bakin titi na hau Napepsu kansu abokan aikin nawa dariya suke min da kyar wani cikin wanda ke jiranmu a waje ya karbi box din hannuna Sabo da uban gudun da nake kamar na fanfalaki


     Bayan na koma gida sallah na gabatar tare da fara harkar kasuwancina har Awara nayi ta dare bayan na siyar na gyara komai tare da irga kudin na cire ribar na zuba cikin asusun da nake tarawa Ammah kudin asibiti na magani tare da ware na gida da yan abubuwawashe gari haka muka je wata unguwar mukayi polio abokan aikina su Salima sun sani gaba suna min dariyar abinda ya faru damu a gidan masu kudin jiyasai dariya muke muna Bada labarinSalima tace ammafa sun hadu da yawa a gidan kowa me kyau ga iya kwalliya musamman dan Iskan da yasa aka dakeni domin ni tunanina shine yasa a Zane ni tunda shi ya hana a bude min gateSalima tace lalle Mufeeda ashe haka kike da rashin kunya idan an tabo kikina da Silent falava wlhu like too much falavamurmushi nayi kawai domin bana jin wani turanci ni kamkaratun Hausa da Arabic kawai na iya Amma Ilmin turanci sai dai kalmomi dai dai domin bani dashih akan ma don ina dagewa ne su Meenat suna koya min amma da ba karamar dakikiya za ayi ba ni kam

Karanta:
The Sexy Boss Hausa Novel Book 2

      Yau cikin nishadi muka gama Polio na dawo gida da Sauri naci abinci na shirya sai kasuwa siyayya ina tsoron bi ta cikin GRA Kawai sai na hau Napep naje na dawo lfy bayan mun gama suyar Awara mun siyar wanka muka kara yi tare da Sallar IshaSu Meenat Assignment sukayi na schl tare da karatu nima na zauna suna koya min karatun turanci da rubutu haka Arabic ma duk da ina da Ilmi domin Uzu na ashirin cif haka wasu litattafan duk nayi wanda Kannena su Maeeshah sunyi Sauka tuni littafin da suka sani kam ko kafarsu ban kama ba danma ni gwanar jin waazi ce nasan duk wasu hukunce Hukunce na addini da dama Amma su suke koya min karatunda badan haka ba da anyi kungurmar Jahila ni


      Part of speach suke koya min common adjective sun sha fama dani kafin na iya fada Sabo da ba laifi kwakwalwata da saukin ja tunda ni dai iyakacin Jss 2 makaranta ta gagareni Allah ma yasa Makarantar Arabic da boko mukeyi a hade shi yasa muke dana addinisu Meenat kuwa ai akwai Ilmishi yasa da munyi fada zasu ce to Sis me kika sani ma in ba neman kudi ba musamman Meenat uwar iyayi da son kwalliya domin duk wata kwalliya ta yan Zamani ta iya ta komai nata na harkar son gayuMaeeshah ma haka suyi ta faman iyayi ni kuwa sai dai na siya musu kayan yi suyi ta zuba kwalliya ina kallo tunda har cosmetics na talakawa ina siya musu iri irikayan wanke gashi na talaka ni dai barni da jarabar tsafta amma ba ruwana da wata kwalliya gani nake bata lokaci ce kawai kudi nake nema dan mi tsira da mutuncinsu

 ni kullum sai da na labta Hijab na fita neman kudi ba sauki wanda yanzu Unguwarmu sun samin suna Yar Kasuwasabo da bani da lokaci sai na neman kudi akan kudi ba daga kafa


   Duk inda naji wata Sanaa ko harkar samun kudi to fa yanzu zan cusa kaina ciki dole sai na samu domin mu samu na ci da sha tare da Suturaina da karancin wannan shekarun Amma na shaku da kudiyanzu abinda ya dameni bai wuce kai Ammah Hospital ba domin dubu Sittin da biyar zamu je da ita za ayi mata wani aiki a Ciwon dake kugunta zuwa kafafunta shi yasa na gigice yaki Halak yaki Haram haka nake tara kudin

    Akan wannan yanzu kam na koyi hainci a Sanaa ta domin Awara da ina yinta me kyau da dadi Amma yanzu dan na samu riba da yawa na daina alkintata idan na tashi tacewa Bazan matse ruwan da yawa bakadan nake dan matsewa kana ci zaka ji ciki lumtsum da ruwa da maihaka yajin na daina me dadi sai na gabza uban gishiri a ciki dan yayi yawahaka ake siye Sabo da tsaftarmu Amma sun daina karba da yajinmuhaka kosai na ma da wata taba da hainci ya taso min sai na siyo garin kwaki tare da jar kala bayan na dauko markaden saina zuba garrin kwaki a Cikin markaden waken kosan nawa tare da jar color yayi wani jajir sannan kosan ya kumbura yayi sutu sutu dan na samu riba na samu kudi sai kiga ana ta siye Malam kosai yasha kayan miyar color gashi har wani Danko yake Sabo da yaji garrin kwaki ciki ba a sani ba ayi ta siye ina samun riba tunanina dai dai duk kuwa da cewar nasan ba kyau sai da nayi Istngifari domin ko Ammah da kannena basu san tabar da nake aikatawa ba gara awarar gida idan zan soya musu daban nake tace ta tas tsam ba ruwa sai su zata ma wacce ake siya haka take


    Hattana Alewar madarata dasu kwakwimeti tare da kafi tsire in dai zanyi sai na san tabar dana yi a ciki Sabo da kawai na samu riba me yawagullisuwa idan zanyita sai na tankade garrin masarara me Laushi na kara a cikin Madarar Sabo da tayi yawahaka ma Zobo na siyarwa sai na samu jar color na tafasa zobon kadan na narka uwar Color a ciki nayi hadinsa a ganshi kamar gaske ayi ta zuka ba a san rabi color ce kawai da ruwa bakuma bana sa sugar dan zaki wato sugarin nake dan yafa kadan sai kaji zaki cai


     Ina zaune kusa da Ammah ina tufke mata gashinta muna sauraren Radio kawai sai muka ji cewar Gomnati zata raba tallafi ga marasa karfi Naira dubu sha biyar biyar tare buhun shinkafa da taliya sugar da man gyada tare da waken Suya a ja jarinan take na mike zumbur naji kudiAmmah ta kalleni tace sarkin neman kudi dan Allah ki hutawa kanki zafin nema baya kawo samu haka duk kin damu kanki Allah yana rufa mana asiri dan Allah ki rage takurawa kanki ayi amfani da abinda ya samubaki na turo Ammah kina gani kudin maganinki har yau basu hadu ba fato ta wacce hanya zaki bi ki samo mana tallafin Ammah wajen counsilor din Unguwarmu Adamu zanje na nemi Alfarma ya nemo mana hanyaai yana da kirki Amma fa kija mutuncinki duk da nasan irin tarbiyyar da nayi muku ki kiyaye Mufeedata sannan kinga girma ya fara kamaki idan kika bari Namiji ya rike miki ko yatsa shike nan kinyi ciki an gamada Sauri na zaro ido waje a tsorace nace Ciki Ammahae ai indai Namiji ya rike maka ko farcene to shike nan ciki ya shigada tsoro na firfito da ido wajenace Ammah su Meenat nake tsoro bari su dawo na fada musu gaskiya kar suje su yarda da Maza su rike musu hannu


    Su Meenat suna dawowa na taresu da Sauri tare da jansu dan Bedroom dinmu nace dan ubanku karku bari Namiji ya rike ko yatsankuMeenat tace Sabo da meba kyau kuma Ammah tace ciki ake daukaDariya naga Meenat ta kyalkyale tare da cewa Allah ya bamu kudi Sis ki koma schl kema wlh ba haka bane ke baki da labarin abinda ake a aure ana samun cikiai Ammah wayo ta miki kar mu kula Maza mu lalace shi yasa ta fada haka Sabo da taga mun fara girmashuru nayi ina Nazari Amma naki yarda da Meenat Sabo da nasan Ammah baza ta fada mana karya bakyalesu nayi kawai na fita abina naci gaba zuba kwakwimeti na  ledabayan na gama na fara daura su citta dasu kanwakaninfari etckusan duk makwaftanmu a wajena suke siyen kayan miyaidan suka siya kawai sai su zauna a gidanmu suce bari su daka kayan miyar ko jajjage da sun shiga gida kawai sai da su fara girkisabo da son kudi na nace to daga yau na kafa doka cewar ko wacce idan zata yi daka a turmin gidanmu to sai ta bayar da Naira goma kudin turmiganin haka yasa Bazan basu tabarya ba sai an miko goma shike nan suka daina daka a gidanmuMuna da wata Kura da yake gidan mu akwai rijiya idan guganmu ya fada da ita muke amfani mi Ciro guganmutane suna zuwa aro sosai nan ma nace kudin aron Kura Naira talatin wasu haka dole suke bayarwa suna dauko GugaAmmah ta hanani Amma naki jisu Meenat ma dole suyi abinda nace ko bana nan idan aka zo to fa sai an Bada kudin nankomai nawa idan zaka taba na kudi ne


     Haka na kama kafa naje har gidan Adam counsilor neman Alfarma a sani cikin masu tallafiyace Mufeedata ki Makara wlh an gama daukan sunaye amma na miki alkawari akwai na wani watan kizo Office ki sameni a secretariat zan sa sunanki a wasu da za fara bayarwa na manomaban kawo da wata manufa ba kawai na dinga Murna ina godiya cewar zanje in Sha Allah 


    Bayan kwana goma Zaune muke gaba daya tunda anyiwa Su Meenat hutun schl muna ta Hadin Zobo nan nace suje su ebo robobi a wanke suna Tafiya na watsa Maroon color tare da makawa Zobo ruwa na hadashi da su Flavour yasha uban Barkono a cikisabo da aji yaji sosai sai na zuba citta da kaninfari kadan na ebi Barkono na watsa a ciki na tafasa dashi Sabo da aji yajin ya fito sai ka rantse yajin cittane da kaninfari me uban yawagaskiya na iya taba sosai ni kaina ina jinjinawa kaina yanda nake tabka tsiya a sanaoi na ba a magana watarana nakanji haushin kaina nima ba da son raina nakeyi ba Amma Sabo da neman rufin asirisu Maeesha suna kawo robobi Meenat tace sis wannan uban zobon fa dazu fa dan kadan ne bai kai rabin botiki ba amma yanzu ya cika botikiMaeeshah ma tace nima haka na gani kamar na AljanuHarara na zabga musu sannan sukayi shuru


abin takaicin da kyar na hada dubu Sittin da Bakwai kudin Ammah na asibitihaka nace su shirya mu tafihar kofar gida na kira Napep muka hadu tare da daukan Ammah muka sata cikin Napep muka kulle dan gidanmu da yar kofar da ta kusa ballewa ma haka na zarge ta muka shiga Napep Sai Asibitin Murtala na cikin KanoMunje  Dr Naseer ya duba lafiyarta ya dinga fada me yasa ba a kawota da wuri ba tuntuni yace a kawota ayi aikin to gashi ciwon nata ya kara karfi yanzu dole wasu magunguna zasu rubuta mana mu siya na dubu Hamsim da biyar sannan idan ta shanye bayan sati Uku mu dawo da ita za ayi mata aiki


    Bakin ciki da tsoro tare da firgici suka kamamu gaba dayanayi Zuru Zuru kamar wacce ta shekara taana zawo haka na koma nace Doctor yanzu nawa ne kudin aikin Yace ai kudinku da yawalikitan da zaiyi mata aikin nan baya zama a kasar nan sam Sabo da aikinta zaizo yayi mata ya komadon haka idan yayi muku sauki ku biya dubu dari takwas da  Hamsim domin ciwon ya girmada ace tun farko kun kawota da tuni baifi ku kashe dubu dari ba Amma yanzu danma da wannan Doctor dinne Amma wannan aikin kasar waje muke tura mutane masu irin cutar ayi musu aikin anfi dacewaa nan kuwa sai dai mu dage da adduakuje ku dawo lallai nan da 3wks tare da kudade in ba haka ba kuna kallo wlh zata kasa ko motsa yatsa dake gabarta nan gaba sankamewa zatayi ku daure ku dawo ayi mata aikin kunji


   Likita na bayani Hawaye na sintiri a fuskata tunanina ina zan nemo kudin nan ko kaina zan siyar wlh bazan yi wannan kudin baInnalillahi nake maimatawa Doctor kuma na kwantar min da hankali yana cewa cuta jarabta ce daga Allahidan Allah ya jarabceka sai hakuri aci gaba da addua Amma tana cikin hadariMeenat dake kusa dani itama Hawaye takeyida kyar na Lallashi kaina nice babba Amma kuma nice me raguwar zuciya bana iya rike Hawaye na saurin kuka gareni ammafa a bangaren abin tausayiko ya naga abin tausayi yanzu zan yi kukakanmu da Ammah nake tausayawa kawaiMeenat karki fadawa Ammah me Doctor yace kawai kiyi shuru da bakinki Sabo da bana so hankalinta ya tashimuce kawai aiki za ayi mata nan da 3wks sai kudin zamu fada mataamma karki fada mata Doctor yace zata iya rasa ranta ba lallai ta tashi ba kinjiok Sis Bazan fada ba cewar Meenat dake sheshekahawaye na share mata nace muje kawai muk ayiwa Dr sallama muka tafiMaeeshah da Ammah suna jiranmu a can waje magunguna muka siya sauran kudin na siyo mana wasu kayan abinci da CefaneSu Meenat kuwa tuni na hadasu tare da Ammah nace suje gida zanzo daga bayaIna cikin Napep kawai tunani nake ta ina zan samu kudin nanlallai Zafin nema baya kawo Samugashi dai na gama Haincina a sanaata na cuci mutane da dama ta hanyar siyar musu da gurbataccen abun ci kuma karshe kudin anfaninsu kadan ne a wajenmu abinda nayi don shi ba a dace baamma duk haka ban hakura ba kuma ban damu ba matukar zan samu kudin da Zan nemawa Ammah lfy


     Tunani nake bana ganin komai bana ji har Napep ya saukeni a gida na shiga da kaya Niki nikiMeenat ta karba ta shigar dasu cikitsabar bakin ciki da muke ciki yau bamu iya daura kaskon Awara a kofar gidanmu baduk muna zaune kowa da tunanin da yake banda Maeeshah da yake ita ba wani girma da hankali tayi ba sosai bacci ma takeyiabincin da muka dafa ba wanda ya iya kai ko loma daya bakinsamusamman ni gaba daya na rude na rikiceidan kuka ya taho min sai na shiga toilet naci uban kuka na wanke fuskata na fito haka na kwana inayi kafin Safiya tayi idona ya kumbura yayi jajir ga addua muna tayi mura ta kamani muryata har ta dashe Sabo da Hawaye na kawo Mura yawan kukada sassafe kamar me aikin Gomnati 8am nayi shiri da kumburarren idona tare da jansa na maka hijab kowa ya ganni yasan ba lfytunani nake ina zanje neman kudi Office din yan siyasa ko gidajen masu kudiko kuma kasuwa zanje wajen masu kantinadomin   banyi tunanin kaiwa gidan Radio ba ko wani wajekaf makwaftanmu haushina sukeji Sabo da kan Sanaa ta ba mutunci idan maganar kudi ce ba kawaici don haka ba da wanda muke shiri sai da daiku duk sunfi jin haushinadon haka babu me bamu shawara ko gidan Radio ko wani waje to idan ba business ba babu abinda ke hada mu dasu Sabo da ba a kula mu ance dan munga muna da kyau sai mu dinga yanga mu ba yayan uban kowa basannan tunaninsu ma ni yar Iska ce Sabo da yawan fita da nake kullum ina gantalin neman Kudi tunaninsu ai iskanci nakeyi kullum ina titihaka suke zagina ba abinda ba ce min


    A fusace na fito daga gida ka Rantse  mutanen garin ne suka min abin haushi domin kowa haushinsa nakeji kamar zan make mutane haka nake tafiya fuuuuuuu fuska ba annuriduk motar dana gani sai na harareta na harari na ciki dake tuki irin ga mutane da kudi ba taimakocommon arna ko church kaje a tallafa ma amma musulmai ko a masallaci basa iya bada Sadaka me tsoka sai biyargomaashirin katon me kudi kaga ya mika Hamsimmafi akasarin Hausawa haka suke bare har wani ya dauki nauyin karatun wasu ko ci da Sha bare na magani sai dai dai ake samun masu hakaamma arna sai kaga mutum daya ya kwashi yan unguwa da yawa ya fitar dasu kasar waje karatu etc 

   






AsmaBaffa

11 1020 PM Asmabaffa 



    KASUWANCI NA







             610








Official







By

AsmaBaffa








        AUTA kema wannan page Sadaukarwa ce gareki








             Tafiya nake ina tunani har na Isa bakin titi ina jiran na shiga Napep shuru shuru ba taxi ba Napep kowacce a cike sukewata dalleliyar motace tayi parking a gabana tunanina Namiji ne irin samari yan iska masu ragewa mata hanya a nemesu nan take na kara tamke fuska na dauke kaina na kalli can gefen hanyawani kamshi naji ya cika wajen sakamakon bude murfin motar dake Saitina da akayi sai lokacin na kalli me fitowar ba kowa bane face yan matan nan na gidan Saurayi Aayan wanda suka min dukan tsiya sune su biyu suka fito a zafafe kida na tashi a motarsu sunci uban kyau ko ina zasu je ohoina cikin wannan tunani sai ji nayi an sharara min ruwa a jikina me sanyia firgice na kallesu da mamakinan suka sheke min da Dariya dayar ta fusgo min Hijab tare da shakenidayar ta duro min ashar tare da cewa ubanwa kika zaga har gidanmudama nace wlh duk ranar dana ganki sai kin San wa kika yiwa rashin kunya wato har iyayenmu ko


     Dayar data shakeni ta tsandara min mari tace Wai ke face to face harda zagin ya Aayan ke din banza kucaka yar matsiyata kin San su waye ubanmu har zaki bude rubabben bakinki ki zagi kakarmu who are u me kwakwalwar dusa banza gaja


  Wani bakin ciki da bacin rai ya taso min duk saurin kuka na haka na danne shidama cikin haushin masu kudi nake ga bacin ran halin da muke cikinan take na kasa hakuri nima nace kune dai gajoji yan iska tsinannu na shaki wacce ta shakeni nima na zuba mata Mari me lafiyanan take ta shakeni tare da Dafe kuncinta dayar ta taso a fusace kafin ta karaso na tsuguna tare da kwaso kafafunta ji kake Tim ta fadi gefen titina bita kuwa tare da jawo kafarta kaiiiii kowa yana kallo ina janta a kasa tana ihuna hau kanta tare da Zama daram na rufeta da duka tako inawacce na mara kuwa da sauri tazo kaina itama ta hau dukanamuna ta faman yiga yara da mutane sun taru ana kokarin rabamu amma Sam munki Hakura yi kawai mukeyi

    Wata motace dalleliya ta kara parking a gaban ta yan mata wata budurwa itace wacce muka samu tare suna rawa ranar da muka je gidan Polio da gudu ta taho tana yiwa yan Uwanta magana Ku kyale matsiyata Ku zo mu tafi pls wannan ba Class dinku bace Ladies plsbabu wanda ya kulata da takalminta me shegen tsinigani tayi babu me hakura kawai ta daga waya ta kira Babansu tare da fada masa Address din inda mukeNan take sai ga arnayen Motocin Aayan sunyi parking sun kai su bakwai da securitiesyana zuwa ya fito cikin Takun mashahurin Namiji yau sanye yake cikin farar shadda dinkin fitted dai dai jikinsa ya dau matukar kyau ga wani arnen glass  Brown a fuskarsa ba karamin kyau yayi baganinsa yana tahowa nayi matukar firgita kamar zanyi fitsari sabo da na tsorata bazan manta da dukan da yayi min baban San sanda na hantsilar da dayar daga jikina ba na tashi daga kan dayar da nake zaune na gyara hijab dina na kwashe da uban gudu kamar zan tashi samaina danyin nesa dasu na tsaya ina maida Numfashishi kuwa baima tunani ba Sam bai gane ni ba amma ya tabbata ya sanni

 

    Ina kallonsa ya karasa wajensu ya kama yan matan nan ya dinka kwada musu mari ba ji ba gani yana ball dasu sai da ya canja musu kamanni sannan ya fada mota yace Securities su kamo nibanyi tunanin wajena zasu zo ba ina ta kokarin tare Napep amma babukawai sai motoci na gani sun zagayenikafin kace me Sojoji sun zagayeni ba hanyar guduwa

Post a Comment

0 Comments