SAKON so Hausa Novel M SHAKUR

 

SAKON so Hausa Novel M SHAKUR

SAKON so Hausa Novel M SHAKUR

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan kuna kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da Episode biyu

SAKON so Hausa Novel EPISODE 1️

~Masjid Ibn Taymiyah~ Aka rubuta ajikin babban masallacin dake cike makil da jama’a kowa yaci manyan kaya manyan shaddoji da kanagani kasan daurin aure ake shirinyi, wani matashin saurayine ke sanye da manyan kaya dakuma babban Riga na shadda datasha aiki yana tsaye daga ta wajen masallacin yana kallon agogon hannunshi da alamu lokaci yake dubawa chan kuma yadago kanshi yana leken kan titin da masallacin ke kai, tabashi akayi daga baya dayasa dasauri ya waigo wani matashin saurayine yatabashi shima yana sanye da manyan kaya yasha hula kube, cikeda damuwa yace “he’s 20minutes late Arif kazo mutafi koda na’ibin limamum masallacin nanne ya karba maka Auren, duk an taru mutum daya ake jira haba mana is not cool” girgizamai kai wanda aka kirada Arif yayi yace “I know he will come let’s just give him some time, Uncle Hamma is just…..” dasauri abokin yace “sociopath” wani mugun kallo Arif yamai zaiyi magana daidai wata Babban jeep na parking abangaren masallacin dayadan sami space na parking, wani kalan walwala ne ya bayyana akan fuskan Arif baisan lokacin dayabar abokin nashi yafice daga cikin premises  na masallacin dasauri ba dudda jama’a na kwalamai kira ta ko’ina suna ango ango baibi takansu ba yay wajen motan dayake nan bamaka ganin kowa na ciki sabida tinted glass ne duka kuma arufe, ahankali yasa hannunshi batare daya jiraba yabude gaban motan bangaren mazaunin direba tareda tsugunnawa har kasa cikeda girmamawa batare dayama kalli fuskan mutumin dake cikin motanba yace “barka da zuwa Uncle Imran” wani magidancin mutum ne zaune cikin motan da akalla zaiyi 48/49yrs yana sanye dawani soft milk yadi daya haska bakar fatanshi dake bala’in sheki tsabagen hutu.

Yanada cikan gashin gemu sosai gasunan baki sidik masu tsayi kadan dawasu sirarren saje dakenan a kwance suma lublub, ga cikan gashin gira dakuma suman kai dudda lafiyayyan hulan minister na kanshi hakan bazaisa kagane cewa yanada cikan sumaba, yanada wasu kalan kananun yet manyan idanu idan ya zubamaka su idanba ka natsu ka kalleshi ba zaka dauka idanun nashi a lumshe suke amman abude suke ras kwayan idanun farare fat, hancinshi dogone sosai kuma siriri sai lips dinshi dakenan jazur, kallo daya yama Arif dake tsugunne kanshi akasa babu wani murmushi ko fara’a akan fuskanshi sannan kuma babu wani bacinrai ko wani yanayi akan fuskanshi saima fuskanshi dake nan adake dake lullube dawani kalan warm rahama akai, kaman baiso yay magana yace “Arif” wani kalan murmushi Arif din yasaki cike da mugun girmamawa yace “na’am Uncle Imran” tareda dago kanshi yadan kalleshi saikuma yasake sauke kan nashi kasa dasauri baitaba ganin mutumin dake tattare dawani kalan mugun kwarjini dakuma haiba irin na Uncle Imran ba, duk yanda kakai ga bushewar idanunka baka iya kallon tsabaragen idanun Uncle Imran kamai, Ahankali kaman baiso yay magana cikeda wannan natsuwan yace “get up kayanka will get dirty” tashi Arif yayi babu gardama still kanshi na kasa hakan yasa anatse ya sauko daga cikin motan yafito ya tsaya kusada Arif duk tsayin Arif akafadar Uncle Imran yake dan Uncle Imran giant ne sosai, dudda babba ne shi ya manyanta amman jikinshi da gabobinshi gabaki daya atsaye suke tsaf kana ganinshi kaga wanda yake gyara jikinshi ta hanyar cin lafiyayen abinci dakuma excercise, yana sanye da babban riga dake kyalli da wandonshi daya tsayamai a daidai idanun sahu, kafanshi na sanye da ankle sock dake cikin wani givency covershoe dake sheki sosai, juyawa yayi yadauko wani bakin glasses dan idanunshi basason haske sosai yasaka sannan yakalli Arif dakanshi ke kasa yace “muje ko”? Gyadamaikai Arif yayi yace “to bismillan mu Uncle” yay maganan suna jerawa tunda yake baitabajin mutum dake kamshin turare kwatankwacin irin turaren Uncle Imran ba, turaren Uncle Imran nada bala’in dadi gasu da sanyaya rai, tun kafin su karasa cikin masallacin mawaka da maroka kemai wake wanda ko kadan bayaso hakan yasa baice musu komiba koyabasu kudi ba yawuce suka shiga masallacin nan da nan abokin Arif yace “waliyin Arif ya iso” karasawa sukayi cikin aka zazzauna nan da nan aka daura aure tsakanin Arif da Salma akan sadaki 500k wanda Uncle Imran yabiya mishi akai addu’a ana gamawa ko sec daya tal bai karaba yamike yajuya Arif yatashi dasauri yabishi abaya, abokin Arif yataba wani abokinsu da duk sukabi Arif da Uncle Imran din dasuka fice daga masallacin da kallo yace “dan Allah jibi Arif saikace yaga God” dayan abokin mai suna Muhammad yace “to ai kusan hakane wannan Uncle din nashi shiyamai komi aduniya tundaga primary school konine abinda yafi hakama zanmai wlh Aliyu tunda mahaifinshi ya gudu yabarsu bai kuladasu ba” tabe baki wanda aka kirada Aliyun yayi yace “bakasan waye mutumin nan ba idan kasan irin kalan bakin girmankan dayake dashi saikai mamaki bakaga yanda babu wanda yagaida a masallacin nan ba sai uban dingile wando shi adole ustazu da ijiye gemu” wani kallo Muhammad kema Aliyu yace “waikai Ali me mutumin nan yamaka ne danni wlh banga aibunshi ko daya ba”? Mugun kallo Arif yama Muhammad yace “bazaka gane bane waini mutumin nan zai hana aiki sabida wai inashan taba yay rejecting application dina a company shi, shi wayasan kalan abubuwan dayayi lokacin dayake matashi yana soja kafin yay retire”? Kalan kallon da Muhammad kemai yasa yace “me to ai gaskiya nafadi ni to even tell you the truth gwara dabai daukeni ba dan ance mahaukaci ne tuburan tuburan saidai in alluran sojojinshi basu tashi ba wlh bakaga saisa har yanzu babu wacce ta yarda ta aureshi ba sai tsufa yake agidan tsohuwarshi” wani mugun harara Muhammad yamai yace “kainedai kaga tsufan dan ni bangani ba wlh ko mahaifin Arif daya girma yafishi tsufa, haushin shi kawai kakeji sabida yahanaka aiki dayayi, kuma aure dabaiyiba shine baiyi niyya ba tunda akazo har gida aka kashemai mata da yara biyu” dasauri kaman jira Aliyu yake yace “kasan shekara nawa yanzu da mutuwansu? This is the 13th year amman har yanzu bai kara aure ba, wlh basabida mutuwan matanshi bane ba, matsalan haukanshi yasa babu wacce ta yarda ta aureshi” zai cigaba da magana ganin Arif na tahowa wajensu yasa yay shiru yamike tsaye yana kakkabe rigan jikinshi. 

SAKON SO M SHAKUR

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu

Sakon so Hausa Novel EPISODE 2️

Tunda yashigo cikin estate dinsu yahango wani magidancin mutum tsaye agaban wani dankareren gida da sojoji guda uku ke tsaye wajen taredashi, kana ganin mutumin kasan zasuyi age mate saidai shi mutumin yafishi tsufa sosai dan ga furfura ko’ina akan fuskanshi, dan ijiyan zuciya yasauke sannan yakarasa gaban gidan batare daya kashe motan ba yasaukar da glass din motan kasa hakan yasa sojojin wajen suka sassaramai Sir! Gyadamusu kai yayi a natse batare daya amsasu ba sannan yasauke idanuwanshi kan mutumin daya taho wajen motan dasauri fuskanshi babu alamun rahama akai baiyi wata wataba babu gaisuwa ko sannu cikeda masifa yace “Alhaji Imrana nagaya maka karabun mini da d’ana kaki I agree cewa lokacin nan nagudu na barsu Kaika sashi a makaranta da sauransu yanzu I am back yarona don’t want anything to do with me, imagine ni mahaifin Arif ina masallacin nan amman ko kallo ban isheshi ba sabida kai sai rawan jiki yake yana binka kaman yaga sarki, karabun mini da dana allow me to be his father” tunda yake maganan kallonshi yake saida batare da yanayi kokuma wani abu na fuskanshi ya chanza ba yagama tsaf sannan yace “nabarka lafiya Baban Arif” tareda maida glass din motan sama aka bude mishi gate yawuce yashiga cikin katafaren gidanshi yabar mutumin awaje yana nuna kanshi yace “ni zaka gwadama miskilanci”? Duk maganganun dayake sojojin kallonshi suke so suke suje su bubbugeshi amman kallon da Oga kadai yamusu is kallon kar wanda ya kula bakona cikinku yagama duk abinda zaiyi yatafi.

Wajen jerin motocin dasunkai kusan 12 acikin gidan yayi karasawa yayi da motan yana tafiya very slow yay parking sannan yakashe motan yakai kusan 5min zaune a motan kaman bayaso yafito sannan yabude kofan ahankali yafito sannan yamaida kofan yarufe yajuya yafara tafiya yana dumfaran cikin gidan ma’aikatan cikin gidan dake aikace aikacen su na gaidashi da kai kawai yake amsa musu yakarasa gaban babban durmemen flat daya rak dake cikin gidan dakeda girman gaske yabude kofan ahankali yashiga wasu yan kananun yarana su biyar da dukansu bazasu wuce shekaru 3, 4, 5 hakaba suna tsalle tsalle suna ganinshi duk kowa ya natsu duk suka zauna akasa atare cikeda gwaranci irin na yara sukace “Abee Assalamu Alaykum” maida kofan yayi sanan yajuyo yabi yaran da kallo dayar karaman murmushi daya bayyana akan fuskanshi a natse yace “wa’alaykumus salam Children” sannan yashigo cikin katafaren falon dawani katon family picture frame ke bangon dake dauke dawata tsohuwa da akalla zatakai 70yrs sai shi yana tsaye agefenta daga yanayin yanda fuskanshi yake ahade zaka gane ko kadan bayason hoton sai wasu manyan mata dasuma sun manyanta masu kama dashi su uku, saikuma wasu maza su biyu dakana gani zakasan kanninsu ne saikuma yara dayawa a frame din, zama yayi kan kujeran sannan yabi yaran da kallo daduk suke kallonshi sai yanzu yama tuna baitaho musu da komi ba this is so not like him saurin dayake yasa yamanta, wannan karan dan murmushi kadan yayi sannan yamike musu hannu yace “kuzo nan” kaman jira suke dawani kalan gudu suka taho murmushi yayi anatse yace “zan dauki kowa one after the other okay” gyadamai kai duka sukayi babban cikinsu dake 5 yafara dauka yace “Muhammad” yaron ya kyalkyace da dariya sannan yadauki na biyun yace “Faisal” yadauki macen yace “Nana” sanan ya ijiyeta yadauki dayan macen yace “Miemie” sannan yadauki karaman dake 2yrs yace “Anees…….” Shiru yayi sabida zafi dayaji ajikin yarinyar hakan yasa yakai hannunshi dasauri yataba goshinta jin dumi yasa yakalli Muhammad yace “call Aneesarh Mom” dasauri yaron yajuya yay kitchen, ko 1sec Muhammad baiyi da shiga kitchen ba wata Yar Babban mace tana kamadashi tafito da apron ajikinta dasaurinta tace “Yaya Imran kadawo”  kafin yay magana wata yarinya Yar budurwa fara da akalla zatai 21yrs tafito daga kitchen din da gudunta tana wani kalan mugun murna dudda akwai Aneesarh ajikinshi saida tazo ta gefenshi tawani kalan rungumeshi tace “Abee Assalamu Alaykum” dan murmushi kadan yamata tareda daga kanshi yakalli fuskanta yace “wa’alaikumus salam Kausar, ina dan kwalinki”? Yay maganan yana kallon kanta dababu dan kwali tayi tsifa rabi tabar rabi, dan zaro idanu tayi sannan tajuya da gudu tai sama binta yayi da kallo sannan yadawo da hankalinshi kan kanwarshi yace “why is Aneesarh body hot”? Kaman Maman zatai kuka tace “wlh babu yanda banyi da itaba takishan maganin Ya Imran” kallon fuskan Aneesarh yayi dake kan jikinshi daketa kallon fuskanshi sannan yakalleta yace “kawomin maganin” dasauri tai sama tana murmushi sosai bata taba ganin mutumin da yara ke bala’in so kuma suke tsoro kaman Ya Imran ba dazaran yashigo kowa zai natsu sannan kowa yayta murna suna kallonshi saukowa tayi da ibuprofen na yara a hannunta tazo har gabanshi ta tsaya ta bude maganin ta debamai a marfi 5ml tabashi tace “Allah sa tasha ni karma ta amayo makashi Ya Imran tabata maka jiki” karba yayi sannan yakalli Aneesarh dake kallonshi yadan mata murmushi ahankali yace “haaaaaammmm” yabude bakinshi kadan hakan yasa dasauri yarinyar tabude bakinta tace “haaaaa” samata maganin yayi abaki ahankali with so much care and love kaman yana handling Yar kwai dasauri yarinyar ta shanye murmushi yamata yace “good job Aneesarh” yay maganan tareda sakata ajikinshi tai lamo yana caressing nata sannan yadago kanshi yakalli mahaifiyarta dake kallonsu tana murmushi sosai yace “su Hajiya basu dawo daga gidan bikin ba”? Gyadamai kai tayi tace “eh amman yanzun nan mukai waya suna hanya, harda Anty Binta itama dazu ta iso da mijinta” gyadamata kai yayi batare dayace komiba hakan yasa tace “nakawo maka tea ko coffee Yaya” girgiza mata kai yayi yace “no anjima” gyadamai kai tayi sannan tajuya tawuce kitchen dan karasa girkin daidai nan itama Kausar ta sauko tana sanye da hula tana kallon mahaifin nata tace “Abee nasaka” kallonta yayi sannan ya Gyadamata kai tawuce kitchen tana murna Maman Aneesarh dake sauke tukunya daga kan wuta tace “mehaka”? Dariya tayi takaraso kusada ita tace “murna nake Abee yadawo kinga zai tayani karasa tsifan” hararanta Maman Aneesarh tayi tace “ke wai bakisan kin girma bako Kausar kullum Babanki zai fita yaje aiki yadawo inhar yashigo gidan nan saikin sakashi yamiki naki aikin bakiji abinda Hajiya tagaya miki bako kina wahalar mata da dand’a” turobaki tayi ashagwabe tace “nikuma ai Babanane” yanda tayi abinma dariya yabama Maman Aneesarh tace “Allah ya shiryeki ina Abdallah baitashi daga lectures din bane”? Dasauri Kausar tace “4-6 yakedashi aini bazan iya Medicine ba ko kadan wlh wahalallen course” ahaka suka cigaba da hiransu suna girkin gwanin ban sha’awa.

Yana rikeda Aneesarh a hannunshi yana caressing nata ahaka bacci yay awon gaba da ita, haka yake inhar zai dauki yara su dan jima awajenshi duk rigiman yaro saiyayi bacci, tashi yayi yana rungume da ita a kirjinshi har gaban kitchen din yaje batare daya shiga cikiba yace “Kausar” dasauri  Kausar dake kwashe shinkafa a flask tace “Na’am Abee” tasaki spoon din tajuya tafice daga kitchen din dagudu ganin Abee agaban kitchen din rungume da Aneesarh datai bacci yasa tace “Abee gani” ahankali yace “jeki kawo zani ki goyata” gyadamai kai tayi dasauri tace “to” tabi tagefenshi tai bene tafara hawa dagudu anatse yace “what did Abee said about running”? Daina gudun tayi dasauri  tai piki piki da ido tace “no running” tana tafiya tai sama bata jimaba tadauko zani tazo har gaban kitchen din ta duka gabanshi tace “Abee samin ita” ahankali yazare ta daga kirjinshi sannan yasamata ita abaya ahankali tareda karban zanin yadaura mata akai itakuma tamike tana gyara zanin tace “Abee goyon yayi”? Ahankali yana kallonsu yace “eh” sannan yajuya yayi stairs yawuce sama itakuma Kausar tawuce tashiga kitchen din suka cigaba da aiki.

Babban sama ne gidan akalla akwai dakuna dakuna sunkai kusan ashirin ko da biyar dan irin babban family house din nan ne, asaman ma wani kebentaccen bangare yawuce da kofanshi ke cikin lungu sannan yabude kofan dakin ahankali yashiga da sallama ko kadan dakin babu wani hayaniya ko tarkace aciki lafiyayyen gadone aciki dake shimfide da white sheet ga white bargo akai an gyarashi tsaf saikuma study da akayi agefe daya da shelf’s na bango dake cike da littatafi sai desktop akan table da kujera saikuma wasu dakuna biyu wanda day bathroom ne daya kuma closet, bathroom nashi yashiga wanka yayi sannan yafito yashiga closet ta shirya cikin wata faran jallabiya mai haske agoge kar yana wani kalan kamshi yasaka wani farin hula kwankwasa kaji hadisi din nan gemunshi na kyalli fuskanshi na annuri ga tabon salla ijiye wayanshi yayi akan gado sannan tazura wasu flat takalma na gida yafito tun kafin yakai wajen stairs yakejin hayaniyan su muryan Hajiya haryakai stairs yafara sauka yanabin kowa na falon da kallo.

Wata har tsohuwar mata ce kan doguwan kujera tana sanye dawata atampa mai kyau anmata dinkin bubu da zani irin dinki tsofaffi dai kana ganin matan kasan ta kwan biyu aduniya dan akalla zatai 70yrs, saikuma wata mata dake zaune akan lallausan carpet akasa tana sanye da lace na alfarma tana kasa su dibla da alkaki da nakiya a babban tray yaran duk sun zagayeta kowa na Mama bani nawa, ga Maman Aneesar dakuma da Kausar suma kowa na jiran nashi, ga wasu manyan mata biyu suma kana ganinsu kasan da mai rabon dasu duka yan uwa ne Zainab da Sajida saikuma wasu maza dasuka zazzauna kan kujera suna danne dannen waya kowannensu na sanye da shadda, yanda yake tafiya ko kadan bazakaji karan sahun tafiyanshi ba amman kamshin turarenshi daya fara isowa falon yasa jikake falon yay tsit kowa yadago kanshi yakalli stairs Anty Binta dake kasan su alkakin ne tai wani kalan murmushi tace “Yaya Imran” dan murmushi kadan yayi anatse yace “Fatima ina mijinki”? Murmushi tamai tace “yaje gidansu anjima zaizo” gayadamata kai yayi yakalli maza biyun dasuke azaune dazu daduk sun tashi tsaye kowa kanshi akasa anatse sukace “Ya Imran ina wuni” gyadamusu kai yayi yace “mutafi masallaci” sannan yajuyo da kanshi yakalli mahaifiyarshi da tunda yafito shi take kallo ahankali yace “Hajiya barka da dawowa” ahankali tace “Imrana aiko su Umman Arif sunce amaka godiya sosai sunyi murna” Anty Binta tace “eh wlh, musamman aka bamu Leda cike dasu cincin da alkaki da nakiya da nama akace mu kawo maka, Sajida ina yake nashi”? Dasauri Sajida tashiga kokarin bude wani jakan hannunta dan yatsine fuska yayi yace “baranci ba” Hajiya tace “batun dazu nagaya muku Imrana bayacin duk ire iren shirmen nan ba saidai su Ibro da Hamza kubama su Ibro wannan kusai kuraba wannan” tai maganan tana nuna kannenshi dasukai gaba sannan tace “wai haryanzu jama’a jikana Abdallah bai dawo daga boko ba” Anty Binta dake bama yara kasonsu tace “Hajiya nakirashi yana hanya” wucewa yayi yafice abinshi hakan yasa Hajiya itama tamike ahankali tace “kuwuce kowa yaje yay salla” karasa bama yaran nasu tayi itama Kausar ta karbi nata tawuce daki ta ijiyema su Abdallah da Ibro da Hamza nasu.

SAKON so Hausa Novel EPISODE 3

Koda aka idar da Magrib gyara zama yayi dan yaji ta’aleem wanda dama shi haka yake sai bayan yay isha’i yake komawa gida, yana zaune inda yake wani yaro dan matashi haka dabazai wuce 22yrs ba yay kamadashi kaman yay kaki yatofar yazo kusadashi ahankali ya zauna tareda daura hannunshi kan nashi warmly yace “Abee” dagoda fuskanshi yayi yadaura akan fuskan yaron asanyaye yace “Ya school”? Murmushi yaron yamai yace “fine Abee yanzun nan nadawo nashigo masallaci dannai salla bari naje gida nai wanka naci abinci Abee I am hungry” gyadamai kai Abee yayi hakan yasa yatashi tareda wucewa yafita daga masallaci mahaifin nashi nabinshi da kallo ganin yanda gajiya ya nuna afuskanshi karara.

Sai bayan sallan isha’i sannan suka  fito daga masallacin dashi da kannenshi biyun maza Hamza da Ibro sai Abdallah, magana yayi da Ibro dazai wuce gidanshi dan yanada mata gidanshi babu nisa da nasu shima a estate din yake zaune da matanshi da yaranshi Mata guda biyu hakan yasa shida Hamza da Abdallah dakemai hira sukai cikin gida ko kadan baida magana amsanshi baya wuce uhnnn u’u, suna shigowa falo akan lumtsetsen one sitter kujera yazauna dake facing wanda Hajiyanasu ke zaune akai 2 sitter, idanunta kyam akanshi tace “an dawo daga masallacin”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya” murmushi tayi tace “to Madallah kowa yaci abinci jeka dinning kaci naka kaima” dan yatsine fuska yayi tareda girgiza mata kai kaman wanda akace yay wani mugun abu ahankali yace “coffee kawai zansha Hajiya ankaimin daki”? Tabe baki tayi tace “ai tuni diyar nan taka mai rawan kai takaimaka daki” tashi yayi yace “to saida safen ku” tashi shima Abdallah yayi yace “Inna nima nagaji bacci zan gobe inada 6 nasafe, good night” binsu Hajiya tayi da kallo saikuma tai shiru murmushi Hamza dake kallon Hajiya yayi yazo kusada ita zama yayi yatasata agaba kuri yana kallo hararanshi tace “me kake kallona kaikuma”? Murmushi yamata yace “Hajiya kinga kiragema kanki wannan damuwan ko dazu saida Anty Binta tamiki fadan nan, kirage damuwan nan kan Yayanmu ba yaro bane he can take care of himself, kowa yasan Yaya baida yawan cin abinci idan yaji yunwa dakanshi zaisa akaimishi” baki tabude zatai magana daidai akai sallama tareda shigowa falon wani magidancin mutum ne wanda akalla zaiyi sa’an Abee washe baki tayi tace “surukina oyoyo Mustafa” murmushi yayi yataho da sauri har gabanta yaje ya tsugunna yace “ina yini Hajiya mun sameku lpy” murmushi tayi tace “Alhamdulillah dan nan yakuma zaman jidda? Ya fama da abincin larabawa mara magi sai uban kanunfari su masoro da sauransu”? Murmushi yayi yace “Alhamdulillah Hajiya” gaidashi Hamza yayi daidai nan su Anty Binta da kanneta duk suka fito gaidashi sukayi Ya amsa tashi Anty Binta tayi zata kawomai kayan kwalama yace “ina Imran Wife”? juyowa tayi takalleshi tace “yana dakinshi” tashi yayi dasauri harzai wuce Hajiya tace “Mustafa” dawowa yayi dasauri gabanta yace “na’am gani Hajiya” dan ijiyan zuciya tasauke baki tabude zatai magana saiga hawaye Hamza dake kusada ita yace “kinfara ko Hajiya”? Dan murmushi Mustafa yayi taredakai hannunshi yakama na Hajiya anatse yace “zan mishi magana Hajiya Dan Allah kidena kuka” bakin zaninta takama dasauri takai kan idanunta ta share tass sanan takalli Mustafa tace “Mustafa dole na koka Imrana shine yarona na farko wannan wani kalan kaddaran rayuwane, shine uban duka yaran nan nawa, ganida yara mata, yanzu nan nan Rahama uwar Aneesarh tadawo gida da yara biyu mata mijinta yarasu, idan wani abu yafaru shi za’a nema shine me tsaya musu, bama wanan ba at least wayannan su kannenshi uwa daya ta haifesu yaranshi daya haifa fa iyye? Yaran cikinshi fa Kausar da Abdallah? Yazaci su basu damu kullum suna ganin ubansu haka bane? Nasan yawahala arayuwan nan na………” “Hajiya!” Mustafa yakira Hajiya ahankali dayasa ta kalleshi murmushi yamata yace “in sha Allah zanyi magana dashi yau bari naje” tashi yayi ahankali yay sama sukuma duka yaran har Anty Binta sukazo suka zagaye mahaifiyar tasu kowa yay zugummm kunsan ance yara mata dabanne akwaisu da tausayi da jinkan mahaifiyarsu duk lallashinta suka cigaba da yi kowa na bata baki.

Yana zaune agaban study desk dinshi har lokacin yana sanye da jallabiya ya kunna desktop dinshi ga coffee a mug yana kurba yana aiki akai knocking kofar dakinshi tareda bude kofan gabadaya aka shigo hakan yasa yadaga kanshi dasauri yakalli kofar danko Hajiya bata shigomai daki kai tsaye batare daya bata izinin shigowa ba balle kuma wani na gidan, ganin Mustafa yasa yasaki wani kalan coool smile taredajan kujeran dayake kai baya yamike tsaye yakaraso inda Mustafa ke tsaye gaban kofan yana murmushi yabashi hannu tareda cewa. “Wata sabon gani” murmushi Mustafa yayi yakarbi hannunshi yace “I missed my best best besssst friend my one and only childhood friend, Imrana waikai baka tsufa ne for God sake look at me look at you, jibeni kaman wani yayanka”?Dan murmushi yayi akunyace yace “common don’t start with this your blabbing mushiga ciki wants some coffeee”? Ciki  babban dakin suka shiga Mustafa yazauna kan lallausan carpet din dakin dakeda wani kalan shegen taushi kaman gado shikuma Abee yawuce dauko flask na coffee da mug Mystafa nabinshi da kallo yace “jibeka kaman yayan Abdallah ba Babanshi ba” tsiyayamai coffee yayi yabashi batare dayace komiba hakan yasa ya amsa yana kallonshi yakai baki yadan kurba sannan ya ijiye, ahankali Abee yace “Ya Jiddarh how is the course going”? Dan yatsine fuska yayi yace “nima wlh retire zanzo nayi kwanan nan kaman kai, aikin soja barinma na Nigeria is exhausting and energy draining, you know what they say problem no dey finish for naija” murmushi dukansu sukayi atare Abee yakai mug na coffee bakinshi yanasha ahankali shima Mustafa yanasha yana kallonshi 1yr kenan da tafiyanshi Jiddah one year kenan rabon dayasashi a idanu gani yayi Abee yawani kara kyau wlh kaganshi zaka dauka matashi ne dake tsakiyan lokacinshi kawai maturity da yanda yake daukan kanshi ne zaisa kagane Babba ne mutumin nan ya kwan biyu aduniya but other than that yamafi wani lafiyayyen matashin kyan gani da kyawun jiki kaman daga sama yaji saukan tambayan Mustafa akunne shi. “When are you getting married again Imran”? Chak ya tsayar da mug din dayakai bakinshi zai kurbi coffee yakai kusan 2min ahaka ko motsi baiyiba sannan gently yazare mug din ya ijiye ahankali kan tray din kafin yamike tsaye Mustafa nabinshi da kallo yawuce gaban desk dinshi yaja kujera yazauna yacigaba da aikin dayakeyi acikin desktop din batare dayace uppan ba, dan murmushi Mustafa yayi ajiyan zuciya yasauke yakarasa shanye coffee cikin mug dinshi sannan ya ijiye cup din yamike tsaye shima ahankali yakaraso tsakiyan dakin ya tsaya anatse yace “kayi avoiding this question for good 13yrs but this time Imran ko bakaso you must answer me” yay dan shiru yatako zuwa bayan kujeran dayake zaune ahankali ya tsaya taredakai hannayenshi yadafa kafadanshi yace “duk wanda yashigo cikin gidanku abu nafarko dazai gani shine one bigggg happy family, ga Hajiya da yaranta dakuma jikokinta sun cika gidan leaving happily kansu ahade but trust me that still person dayayi tunani u people are happy family will take him just a day to realize you guys are not happy, dan behind that happiness is one huge big sorrow dayay surrounding zuciyan kowa all because of you Imran, kowa is not happy, your family supported you throughout the difficult time dakai going through arayuwanka, everything, kullum suna cikin battling da PTSD dinka, burinsu yanzu daya ne kasami mata kai aure ka natsu yaranka su sami uwa eh Imran” dan lumshe idanu Abee yayi sannan ahankali yabudesu tareda juyowa hada idanu yayi da Mustafa dake kallonshi kaman yaune yafar ganinshi, wani abune yaji ya tsayamai azuciya hakan yasa yasake lumshe idanu kawai yay shiru ahankali Mustafa ya tsugunna agabanshi tareda kamo hannayenshi yarike hakan yasa yabude idanunshi ahankali, ahankali Mustafa yace “talk to me I am your friend, I am here for you, talk Imran” kadawa idanunshi sukayi sukai jaaaa kaman bashiba ahankali muryanshi harta dishashe yace “I don’t wanna get married again! I don’t want tooo” yay shiru tareda sake lumshe idanunshi dan murmushi kadan Mustafa yayi ahankali yace “bakason kasake wani aure because you feel you are betraying Muna (Maimuna)”? Murya chan kasa yace “kowa knows how deeply you love Muna Imran, soyayya kukai kaida muna soyayyan da tun kuna yara tun bakusan ciwon kanku ba, soyayya ce dakuka farata tun baby class, primary school har secondary school, kaida Muna are just like Zara da wata, duk inda aka ganka anga Muna akaga Muna anganka, I remember lokacin nan kuna kare secondary school aka muku aure sabida kun ishi mutane da soyaya” Mustafa yayi murmushi ahankali murya chan kasa yace “is not easy to loose the love of one’s life along with 2 of your beautiful children Abdulhamid da Asiya, I know you are suffering I know your heart is shattered but trust me Imran this is not what Muna wants for you kana wannan miserable life din rayuwan kadaici kullum daga office sai masallaci sai gidan Hajiya for the past 13yrs kana tunanin Muna and your two marigayun yara wants that?” Wani kalan gaggauran ijiyan zuciya yasauke har lokacin idanunshi a lumshe dazaka iya dauka ko bacci yakeyi, ahankali Mustafa ya matse hannunshi yace “13yrs kenan da aka kashe maka mata da yaranka biyu tun kana shekaru 36yrs yanzu you are 49 Imran me kake nufi you will not move on ahaka zaka karasa rayuwanka kana zaman kadaici kullum mahaifiyar ka your old mother cikin kuka take kullum kanninka su Binta cikin kunci suke yaranka ma haka all because of you shin kamusu adalci kama dattijuyar 70yrs old Mom naka adalci da at this stage babu abinda take bukata banda farin ciki, kama Muna adalci datake sonka sama da rayuwanta eh Imran”? Wani kalan ijiyan zuciya mai zafi ya fuzar sannan yabude idanunshi ahankali yakalli Mustafa murya chan kasa yace “kowa zan aura Musty kasan cutar da ita kawai zanyi, my heart my soul my whole body and everything belongs to only one woman which is Muna, bazan taba iyason kowace mace ba kuma arayuwana, I cannot love again, kota Auren gangan jikina kawai aka aura, I can’t love again, bazan taba samun wata kaman My Muna ba” murya chan kasa Mustafa yace “kai Allah ne? Kasan gaibu ne? Did you know what tommorow holds for you don’t say that Allahn daya baka Muna can give you wacce tafi Muna” ajiyan zuciya yasake saukewa murya chan kasa still Mustafa na kallonshi yace “how are you even surviving Imran all this years? Tayaya kakai har war hakama bakai aure ba? Imranan dana sani dakenan duk shakara Muna ke haihuwa, I remember lokacin damuke trainning na sojoji a chan jaji kusan duk bayan 2days kake sabewa tabayan katanga kadawo gida just to come and ease yourself da iyalanka eh? I know you best friend naji bazaka tabaso wata ba but you are punishing kanka, grieving Mamaci daban sannan halittun da Allah yamana ajikinmu daban, yudaya baya hana daya grief Muna as much as you want but you are suffering, for the past 13yrs rabonka da wata mace idanba kanason kai loosing sanity naka loose focus bane kanemi mata kai aure” fuzar da iska yayi ahankali yace “I am sorry Musty but bazan taba iya neman wataba, and the suffering I am suffering lemme suffer it I deserve it, bayan aurenmu danake cema Muna I want to become a soja bataso she stop me but nakiji sabida it has been my childhood dream nazama soja, Muna was always scared idan aka turamu for assignment kada akashe mata ni not knowing bani Zaa kashemata ba itane za’a kashemin, had it been I listen to her I went for another course instead of becoming a soja da yanzu My Muna na raye, so lemme suffer I deserve it I have been selfish and stubborn and a bad husband to her” baki Mustafa yabude zaiyi magana Abee ya nunamai kofa da hannu kai tsaye yace “leave me alone Musty leave my room” kallonshi Musty yayi idanunshi sunyi jajir yasan idan ya tsaya zai iya sawa yanzun nan ya birkice kuma yau ya birkice babu wanda zai runtse agidan nan ga Dr shi baya Nigeria yayi dan tafiya hakan yasa ahankali yadaga hannunshi yace “okay I rest my case best friend saida safe” yajuya yay kofa yabude Anty Binta yagani gaban dakin idanunta sunyi jaaa maida kofan yayi yarufe kaman jira take kawai tafada jikinshi ta kankameshi tana kuka ahankali janta yayi saida sukai wajen bene sannan ta tsayarda kukan tareda dago fuskanta tashare idanunta ahankali tace “please kada kagayama Hajiya yanda kukayi wlh zuciyanta zai iya bugawa” Gyadamata kai yayi tareda murmushi yace “I know wife muje” sauka sukayi zuwa dakin Hakiya dake nan akasa a falo dan bata iyawa da benen nan tana ganin Musty cikeda murna tace “yakukayi dashi Mustafa ya aminci zaiyi Auren”? Dan murmushi Musty yayi yace “eh Hajiya amman yace adan bashi lokaci ya kammala project dindayakeyi a company shi” dan murmushi Hajiya tayi one thing is dudda tsufanta babu wanda yakaita sanin halayen yaranta kawai tasan bahaka sukai dashiba ne amma she knows what to do.

SAKON so Hausa Novel EPISODE 4️

4:30 yabude kofar dakinshi yafito sai zuba uban kamshi yake kana ganin kasan yay wanka dan yasaka wata milk jallabiya gogaggiya mai bala’in laushi yasaka hula fara kwankwasa kaji hadisi, dakin Hamza yafara shiga yatadashi sannan yashiga dakin Abdallah yatadashi yace yay maza yay alwala kafin yagama tada mutanen gidan, fita yayi yawuce dakin Kausar, ahankali yabude kofan da sallama yashiga yakai hannu yakunna wutar dakin tana kwance kan gado ta kudundune cikin bargo tana shargan bacci karasawa gaban gadon yayi ya bubbuga mata katifa ahankali yace “Kausar” bude idanunta tayi cikin muryan bacci tace “Abeeee” hannunshi yamika mata yace “get up and pray” gently tasa hannunta takama nashi hakan yasa yadagota ahankali ta tashi zaune sannan takarasa yaye bargon tamike tsaye tawuce bayi, fita yayi ya tsaya gaban dakin da Maman Aneesarh ke ciki yay knocking yace “Rahama” cikin muryan bacci tace “natashi Ya Imran” knocking dakin da Anty Binta tasauka yayi itama tace ta tashi sannan yasauka kasa direct dakin Hajiya yayi tunda ya hango wuta dakin yasan ta tashi amman dudda haka sallama yayi yabude yashiga zaune take kan lallausan dadduma da charbi ahannunta hannu tadagamai alamun addu’a take mikewa yayi yafita daidai Hamza da Abdallah sun sauko kasa suka wuce masallaci.

Karanta: Auren Sha'awa Hausa Novel

Hamza da Abdallah sun rigashi dawowa daga masallaci danshi dama yana tsayawa yay azkar sannan yagaisa da mutan unguwa idan ana bukatan wani abu a masallacin ya saya, wajajen 7 yashigo gidan da sallaman shi chan ciki, gabaki dayan yaran gidan na falo dukansu an musu wanka looking neat dukansu sun saka kayan makaranta little Aneesarh ne kawai bata fara school ba, kuma duka yaran dsame school suke duk sun zauna suna jiran breakfsat dan iyayensu na kitchen, zama yayi akan kujera one sitter wanda wajen kusan shine wajen zamanshi na ka’ida duka yaran tahowa wajenshi sukayi sannan suka duka atare sukace “Assalamu Alaykum Abee good morning” dan murmushi ya sakan musu yace “wa’alaykumus salam children morning” daidai nan Abdallah shima yashiga saukowa kana ganinshi kasan yay wanka yasa kananun kaya masu kyau da sneakers akafanshi dawata jaka na LV abayanshi sai key mota kaganshi sak ubanshi yana zuwa gaban Abee yace “good morning Abee” “morning Abdallah what time kakeda lectures yau” yana gyara agogon hannunshi yace “Abee by 8 ne yanzu 7 harda minti goma bari nai sauri idan lecturer ya shiga baya kara bari wani yashiga” yay maganan yana mikewa zai wuce Abee yace “go and have breakfast kafin kafita” strictly Abee yay maganan daidai nan Hajiya tafito tace “Alhamdulillah ai yau uban naka nagida naga ta yanda zaka tafi makaranta bakai kari ba yaro kwata kwata bayason cin abinci” turo baki yama Hajiya yajuya yawuce dinning danyi kari Abee yadauke idanunshi daga kanshi yajuya yakalli Hajiya data zauna kan 2 sitter dake facing nashi ahankali yace “ina kwana Hajiya” “mun tashi lpy Imran” ahankali yace “Alhamdulillah Hajiya” yadanyi shiru sai chan yakalleta yace “me kuke bukata agidan”? Anatse Hajiya tace “fruits ne kawai babu amman akwai kayan abinci da komi lastweek ai kasa Hamza yayo chefene” gyadamata kai yayi yace “magungunan kifa”? Tana kallonshi tace “basu kareba har yanzu” daidai nan su Anty Binta suka fito daga kitchen zasu fara jera abinci a dinning Hajiya tace “ku kawo nan muci anan dan Allah ni wlh bason cin abinci wajen nan nakeba” kawo abincin sukayi duk suka gaida yayan nasu Sajida yafara kallo batare daya amsa gaisuwanta ba yace “when are you going back to your husband house”? Murmushi tayi tace “Yaya dazaran yadawo daga lagos zaizo yadaukeni next week yace zaizo ni wlh banma gaj…..” mugun kallon daya mata yasa tahadiye maganan yakalli Zainab kafinma yayi magana da sauri tace “Yaya Imran ni sai ranan Friday kaga yau monday” dan dariya Hajiya tayi tace “yara duk sun zo sun taremini gida sun hanani sakat” turo baki Zainab tayi tace “bamason rabuwa dake Hajiya” dasauri Hajiya tace “aure kam yagaji haka ingayamuku” daidai nan Anty Binta takalli Abee tace “mezan zuba maka akwai waina da pepper soup na cowtail, saikuma chips da egg, akwai kuma dumamen tuwo da kuka sai shayi da kunun gyada” ahankali yace “I want masa da shayi” murmushi tayi tashiga zubamai daidai nan Hamza ya sauko ya shirya cikin suit yayi kyau Hajiya dake kallonshi tace “kai lpy kaci suit yau”? Murmushi yayi yakalli Ya Imran da ake bama abinci yace “yau zamuyi baki a office za’a kawo wasu yan makaranta excursion suga company namu idan Ya Imran yayi welcoming nasu nine let’s just say tourist dinsu to kinga I need to look good” tabe baki Maman Aneesarh tayi yadaga mata gira daya Hajiya ta kalli Abee daya fara kurban shayi ahankali anatse tace “zakuyi baki shine kai me kampani gabaki daya ko shiryawa bakayiba” ahankali yazare kofin shayin daga bakinshi yace “idan nagama zan shirya” zama Hamza yayi yakarbi abincin da Anty Binta ke bashi yace “wlh yaran nan naku suyi sauri inba hakaba babu makarantan dazan kaisu saidai ku ku kaisu” Hajiya ta dubi Anty Binta dake bama yara abincin tace “wai ina jikata Kausara ne jama’an gida”? Dan dariya daga Binta, Sajida, Zainab da Maman Aneesarh sukayi, Maman Aneesarh tace “Hajiya kin manta shiryawan Kausar ne” Zainab tace “manyan yammata yan 100 level JJC saida gayu” daidai nan Abdallah yatashi daga dinning yace “nina tafi” atare kowa na dakin yace “Allah kiyaye hanya, Allah bada sa’a Doctor” karasowa wajen Abee dahar lokacin shayi yakesha baima taba wainar da aka zubamai ba yace “Abee natafi” hannu Abee yasa a aljihu 10k yaciro yabashi dasauri yakarba yana murmushi yace “thank you Abee” ahankali yace “drive safe” murmushi yayi yace “I promise Abee” yajuya dasauri yawuce daidai nan Kausar ta sauko tana sanye da doguwan rigan atampa mai kyau tasaka bakin safa akafanta da flat shoe sannan tarike milk hijabinta ahannu, da dankwalinta a hannu, da jaka da ribbon a hannu tana shigowa ajiyesu tayi akan kujera tazo wajen Abee da sauri tabashi ribbon din tace “Abee kamamini gashin” baki Hajiya tasake tace “yanzu kiwuce duka matan dake dakin nan kitafi wajen ubanki yamiki parking gashi dakecin abinci” turo baki tayi tawuce tabama Zainab tace “samin Anty” murmushi tayi takama gashin da baida wani tsawo tace “kawo kallabin na daura miki shima kawowa tayi tadaura mata sannan tazauna tana breakfsat dasauri sauri hada ido tayi da Abee dake kallonta, kallon daya mata kadai yasa ta faracin abincin ahankali anatse dan yahanata cin abinci da sauri adolenta ta natsu ta cinye tass sannan ta tashi tasaka hijabinta itada sauran yaran sukabi Ya Hamza dazai kaisu sukabar gidan.

2 slice na waina yaci acikin hudun da aka sakamishi sannan yatashi yawuce sama dan shiryawa, tsaf ya shirya cikin black suit dayasaka wata farar Riga aciki mai shegen kyau, baisa boturin jacket na suit dinba hakan yasa kana iya ganin farin, yasa black Wandon suit din daya tsayamai a idon sahu as usual yanda tsayin wandunanshi suke, covershoe yasaka na gucci dake wani shining, wannan karan babu any hula akanshi hakan yasa gashin kanshi yay wani kalan kyau ya kwanta lub sai kyalli suke, ahankali yake saukowa rikeda wata jakan laptop a hannunshi daga Hajiya har duka matan ta duk suna falo da Matan Ibro itama yanzun nan tashigo tanacin ragowan waina dan tsohon ciki ne da ita bata iyacin abincin data dafa, ganin Abee yasa akunyace ta sauke kanta dan kowa nauyin Abee yakeji cikeda kunya tace “ina kwana Abee” kallo daya yamata yadauke kai yace “Alhamdulillah” yakalli Hajiya yace “natafi Hajiya” dan murmushi tasakin mai tace “ubangiji Allah yabada sa’a yakara daukaka” ahankali yace “Ameen” su Anty Binta atare sukace “Allah bada sa’a Yaya” bai amsasu ba yafice suna sonshi bana wasaba Ya Imran shine komi nasu, ci sha sutura, duka kanninshi dukansu duk wata kowacce yana bata kyautan kudi hatta matan Ibro, banda Ibro da Hamza da suma tunda sun gama makaranta duka yasasu a company shi duk suna aiki awajen, school fee na marayun yaran Maman Aneesa na kanshi magani komi, sai su Abdallah da Kausar dake university Kausar this year tafara tana 100level tana karantan Mass com, shikuma Abdallah na 300 level medicine, Abdallah nada bala’in kokari da kwazo ga natsuwa da tausayi da kirki saisa Abee yabashi motan kanshi dudda he’s 22yrs dan yawanci early morning lectures yake kuma bayida gara gara, itama Kausar tana kokari ba laifi amman ba kaman Abdallah ba randa sukeda lectures lokaci daya da Abdallah shi yake wucewa da ita idan kuma ya bambamta Hamza ke kaita.

SAKON so Hausa Novel EPISODE 5️

Ahankali cikin muryan bacci wata kalan siririyan murya mai shegen dadi da zaki tace “Gwaggo yunwa” shiruu kakeji banda sound na munshari dake tashi acikin duhun dakin, cikin wani irin raw voice din nan dake nuna bacci mutum yake ko cikin bacci mutum yake maganan tace “Gwaggooooo yunwaaaaaa!” Firgigit munsharin dake tashi daga dakin dakeda duhu nan ya tsaya kaman anyi ruwa an dauke karan hannu kawai ketashi daga dakin dake nuna ana tattaba gadon alamun abu ake nema sai chan aka kunna wani bright torchlight daya wani kalan haska dakin bauuuu kaman wutan lantarki, wata tsohuwar mata ce da akalla zatai 70 kokuma 72 haka kwance kan wani makeken gado mai kyau tana sanye cikin riga bubu da zani na atampa gefenta kuma wata yarinya ce mai jiki sosai kwance ta kankame Yar tsohuwar kaman zata koma cikinta idanunta akulle tana daure da wani pink towel, kallon fuskanta yar tsohuwan tayi tace “Ohh ni Safara’u Allah ubangiji ka nunamin ranan dazanyi bacci tundaga farkon dare har karshe batare da wannan fitinanniyan yarinyar ta tadani tanajin yunwa ba, Ya ubangijin sammai da kassai Ya ubangijin dake busa numfashi rokonka nake Allah ka kawomin ranan nan da gaggawa” cikeda takaici tace “aisai kitashi ga shayinki chan cike a flask, namanki da somasa nacikin kula, buredi ma na wajen idan kuma harda shinkafa zakici to wlh dakanki zakije kitchen kidebo dan kin ganni nan ban barin gadon nan Lulu” still cikin baccin batare data bude idanunta har lokacin ba tace “Gwaggo wlh ki kawomini nan” tai maganan kaman mai shirin kuka dayasa babu shiri Yar tsohuwan takai hannayenta ta kabarda hannunta dake kan jikinta tace “aisaiki sakeni intashi yarinya kaman jikan mayu” tashi daga kan gado tayi tasauka tawuce wajen da flask da wata katuwar kula da cup da duk suke kan faranta ta duka da kyar ta dauka tazo gaban gadon ta ijiye sannan ta kalleta still idanunta arufe suke tace “tashi to kici” kaman jira take ahankali ta tashi zaune idanunta still arufe tana rike da gaban towel dinta dake shirin zamewa sannan ta gyara daurin zanin da kyau tana turo baki tashiga bude idanunta ahankali, wasu hadaddun kitson kalaba ne kan yarinyar dasuka zubo mata har tsakiyan baya an jera beads a bakin kitson kaman wata Yar yarinya, wani kalan kibane da yarinyar bana wasa ba, irin asalin yaran nan ne da ake kira da chubby, idan kaga jikinta zaka dauka she’s about to burst ne dankoni dazu dana ganta kwance kan gadon nadauka Babba ne sai yanzu dana kalli fuskanta Nagane yarinya ce da duka duka bazata wuce 19-20yrs ba, wasu kalan cat sexy eyes gareta dayasa idan ka kalli fuskanta saika kasa janye idanuwanka akanta for some seconds sabida kyawun idanunta, tanada cikan gira kuma baki sidik hakama gashin idanunta da dan siririn hancinta, tanada kumatu rubu rubu dasu that looks super cute on her dawasu kananun succulent pink lips da kana kalllonta yana bada all this kananun jariran yaran nan dakeda kiba din nan sosai, skin dinta is like butter ne ko milk banmasan yanda zan siffanta muku ba but kaganta zaka dauka idan ka latsa jikinta jini zai fito ne, everything about her is chubby harta yatsun hannuwanta dana kafafunta burbur dasu kaganta kaman zata fashe, sauka tayi ahankali daga kan gadon tana kara gyara daurin towel dinta da kyau sannan akan soft carpet din tana bude flask din ahankali duk cikin bacci itakuma Gwaggo tawuce tabude bandaki tashiga. Shayin tazuba cikin wani babban cup dayaji madara da Milo yana tururi sannan tabude babban kulan samosa ne kusan 20 aciki da naman kaza da akai pepper chicken dasu guda 5 da sauri tashigaci tass ta shanye shayin kofin takara bude flask tadeba tacika tacigaba daci itakuma Gwaggo tafito ta shimfida dadduma kawai tahau tass ta shanye shayin da samosan da duka naman gyatsa tayi sannan ta tashi tahau gado ta gyara kwanciya ta kwanta murya chan kasa cikin bacci tace “Gwaggo kizo mukoma bacci” hararanta Gwaggo tayi tace “nafila zanyi gwarama kiyi baccin ki dan kinsan da asuba zan tadaki yau monday zakuje iskuko oho dai amakaranta” dan gajeren tsaki yaja tanajan bargo ahankali akuma shagwabe tace “ni bazanje ba Mandawari na zaiyi live broadcast karfe shadaya na safe yau” hararanta Gwaggo tayi tace “asheko dake da shegen gantalallen Mandawarin daharyau baimasan ko akwai mai kamanki aduniya ba babanku zai hada yaci ubanku” murguda baki tayi tareda lumshe ido kafi kacema bacci yay awon gaba da ita ganin haka itama Gwaggo ta kishingida da bango danta dan runtsa kadan tasan inhar batahau ba nan bada jimawa ba zata tashi da kanta dan Lulu bata iya bacci bataji ta rike mutum ba tun tana yar kankanuwan ta take haka.

5 na asuba tabude ido ahankali takalli inda Gwaggo take kan dadduma sannan ta tashi zaune ahankali tana jaye zanin gadon tana murmushi tasauka dagakan gadon da sauri tawuce bathroom na cikin dakin da ruwan zafi tai wanka tai brush sannan tai alwala tafito daure dawani towel din bayan ta wurga wanda tacire kan washing machine tazo dakin bataga Gwaggo awajenba hakan yasa tadauki wani dogon hijabi tadaura akan towel na jikinta tahau kan dadduma, tana sallame sallan ta tashi batare datayi azkar ba tawuce tafita daga dakin tashigo falonsu wani chocolate dake kan center table na cabry diary milk tadauka da sauri tana budewa tai wajen kofa daidai nan Gwaggo tafito daga kitchen tace “ina kuma zaki gari bai gama wayewa ba Lulu”? Batare data kalli Gwaggo ba tace “wajen Ya Samira zani” baki Gwaggo tabude zatai magana amman tuni tabude kofan tafice Gwaggo tabita tana kwalamata kira tace “bazakizo kisa kaya ba da asuban nan kina yawo daga ke sai tawul babu dan kwali akanki Lujain” ko juyowa batayi takalli kakartata ba saina kara sauri datakeyi zuwa babban flat din gidan tana tafiya kaman Kazan agric dataci takoshin nan tana tafiya da kyar tana tafiya tana ballan chocolate din hannunta tanaci, gidan dan Babba ne ba laifi kana ganin yanayin tsarin gidan kasan ba laifi gidan masu rufin asiri ne daidai gwargwado, bude kofan flat din tayi tashiga dakin tsaf tsaf sai kamshi yake babu kowa afalon direct tawuce wani daki dake corridor dataji hayaniya budewa tayi tashiga da sauri tana murmushi, yammata uku ne acikin dakin dake dauke dawani babban gado na daidai rufin asiri ga daddumai da hijabai akasa kana ganinsu hancinsu zaisa kagane sudin duka sisters ne saidai su kaf dinsu black beauties ne kuma ko kadan basu da jiki kaman ita su sirara ne yammata sosai, duk kallonta sukayi suka watsar amman ko ajikinta wani kalan murmushi tayi tamaida kofan tarufe takaraso cikin dakin tana kallonsu daya bayan daya, Babban cikinsu wacce akalla zatayi shekaru 23 ne da waya ke kunnenta tace “Baby ina zuwa zan kiraka” sannan ta katse wayan takalli wacce ta shigon tace “Lujain ba jiyan nan da daddare Baba yagama miki magana kan zama da towel dakuma rashin daura dankwali ba” dan yatsine fuska tayi kaman zatai kuka ashagwabe tace “mancewa nayi ban daura dan kwallin bafa Ya Samira” dasauri wacce takira da Ya Samira tace “to towel dinfa” dan turobaki tayi tace “wlh zafi nakeji idan nasa kaya” daya daga cikin sauran biyun matan ne taja tsaki tace “yarinya gabaki daya Gwaggo tamaidata mara saiti, ba dole kidingajin zafi idan kinsa kaya ba, jibeta kaman buhu” da normally ne da yanzu tai kuka da aka kirata da buhu but yau she’s extremely happy hakan yasa tace “wlh banda lokacin ki Ya Abida amman gobe ki tareni ki kirani buhu kiga abinda zai faru” yunkurowa Abida tayi kaman zata daketa hakan yasa da sauri Lujain din takoma baya Abida tace “maimaita abinda kikace”? Dauke kai tayi dayan sister da tundazu batai magana ba tace “Ya Abida inba so kike yau duk mutafi school da bakin ciki ba kada kitaba yarinyan nan yanzu dan wlh bamuba har Baba da Mama ransu yau saiya baci akanta kindaisan fitinan Gwaggo sarai” kaman jira Lujain din take jin ankira Gwaggo  kwafa tayi tace “barta ta tabani ma tagani Ya Habiba” ganin rikici zasuyi yasa Samira tace “ni dan Allah ku kyaleta zonan kifadamin meya kawoki wajena da asussuban nan keda nasan war haka baki tashi ba” murmushi tayi ta harari Abida da Habiba tawuce wajen samira kaman maison gulma tace “ni akunnenki zan gayamiki” kunnen Ya Samira tabata magana tayi mai tsawo sannan ta tashi wani mugun kallo Samira tamata tace “chabdi wlh bazan baki ba hakanan” kaman zatai kuka tace “please Ya Samira kome kikeso zan miki Allah” shiru Samira tayi tana kallonta hakan yasa tace “wlh kuwa” murmushi Samira tayi tunawa da wani abu tace “inhar kin yarda zaki fasa asusun ki kibani duka kudin ciki zan baki wlh dama banda kudin ankon Aisha kinga nasamu” kaman zatai kuka tace “kai Ya Samiraaa duka fa kikace” hararanta Samira tayi tace “ashe baki cika crush din Mandawari ba, ni wlh idan inason wani celebrity babu abinda bazan iyayi akanshi ba, kikasan ma ko a live din dazaiyi yau yaraba ticket na zuwa kallonshi a stadium idan zai buga kwallo basaikije ba, kuma yana ganinki zaice yana sonki kinga yanda kikeda kyau ne” wani kalan mugun murmushi tayi dayasa kumatunta ya lotsa abin kaman wani machine ne awajen ya bala’in haska fuskanta, Abida dakejin firansu ne ta tsoma baki tace “Ya Samira stop deceiving this girl for your personal interest, international player irin Muhammad Mandawari kyakkyawan footballer hadadde ga kudi bazai taba cewa yanason wannan buhun yarinyar ba ko itace last woman on earth wlh” wani abune yatokarema Lujain wuya tajuya tana kallon Abida dake kallonta hararanta Abida tayi tace “yarinya abincin dazataci dukanmu nan bamu iya cinshi, tsakar dare kaman diyar aljanu dansu ke fatin abinci tsakar dare haka itama ketashi taci nata, Gwaggo kawai tabude mata ciki, tayaya ma Mandawari zai dauketa? Wlh tafi karfinshi” daga Abida har Habiba suka kwashe da dariya itakuma Samira tarike nata dariyan dan tana hango samun da zatayi, Habiba dake dariya tace “Mama ma tace babu wanda zai taba cewa yana sonta balle harma Ya aureta bakiga ba duka yan class nasu nada saurayi ita mazan ajin ko kallonta ma basayi bata burgesu everybody gets irritated with cin abincin Lujain da kibanta” juyawa Lujain tayi fuuu zata fice dasauri Samira tariketa tahararesu tace “don’t mind them yan bakin cikine Mandawari will acknowledge you one day as his die hard fan sannan zai soki harma ya aureki” sosai hawaye yacika mata idanu ahankali tace “are you sure Ya Samira bazaice nacika kiba ba” murmushi Samira tamata tace “ai kiba halitta ce kuma shi so comes from heart inhar na gaskiya ne ko kinfi kowa kiba aduniyan nan he will love you and cherish you, now smile for me muje mukarasa deal din inhar zaki kawo kudin yanzu zan baki wayan ki kalli live dinshi idan nadawo daga school na karbi wayata kin yarda” dasauri ta gyadakai murmushi Samira tayi tace “to jeki kawo kudin kafin nan nagama waya da Baby” da sauri tajuya tafita su Abida suka bita da harara sukace “wawiya kawai tama dawo ta dauke ledan chocolate din nan data ijiye mana anan dan nan ba dakin kakarta bane data maida bola ba”.

ZA KU SO KU KARANTA WADANNAN LITTAFAN:

1. The Virgin Maid Hausa Novel Complete

2. Nakasa Ba Kasawa Bace Book 3

3. Tarihin Hannatu Musa Musawa

4. Soldiers Family Hausa Novel

Post a Comment

0 Comments