Barka Da Zuwa Wannan Shafin Namu Inda Ayau Muka Kawo Muku Cikakken Tarihin Hannatu Musa Musawa.
Wacece Hannatu Musawa?
Hannatu Musawa Lauya Ce, 'yar Siyasa, Kuma Marubuciya Daga Najeriya. A Halin Yanzu Tana Aiki A Matsayin Mataimakiyar Kakakin Jam’iyyar All Progressives Congress (Apc).
Hannatu Musawa Wacce Ta Fito Daga Jihar Katsina A Arewacin Najeriya, Diyar Fitaccen Dan Siyasa Alhaji Musa Musawa Ce.
Hannatu Musawa Kwararriyar Lauya Ce A Ingila Wales, Burtaniya, Sannan Kuma Lauya Ce A Kotun Koli Ta Najeriya.
Ina Muku Maraba Da Zuwa Wannan Shafin Inda Zaku Karanta Duk Wani Abu Da Ya Shafi Hannatu Musawa, Wanda Yahada Da Tarihin Rayuwarta, Dukiyarta, Shekarunta, Iliminta, Yanayin Asalinta, Siyasarta, Aikinta, Mijinta, Mahaifinsa, Da Dai Sauransu.
Tarihin Hannatu Musa Musawa
An Haifi Hannatu Musawa 1 Ga Watan Nuwamba A Shekarar 1974 Wanda Shekarunta Yakama 49 A Shekarar 2023.
Hannatu Musawa 'yar Asalin Jihar Katsina Ce Daga Arewacin Najeriya, Kuma Mahaifinta Gogaggen Dan Siyasane Wanda Akafi Sani Da Suna Alhaji Musa Musawa.
Ta Kasance Kabilar Hausa/Fulani Kuma Musulmace. Hannatu Musawa Ta Samu Digiri Na Shari'a Daga Jami'ar Buckingham A Burtaniya. Tana Da Digiri Na Biyu Na Master's A Fannin Shari'a Na Daga Cardiff Jami'ar Wales.
Suna: Hannatu Musa Musawa
Shekaru: 49
Jinsi: Macce
Jihar Asali: Katsina
Kabila: Hausa/Fulani
Anan zamu dakata da wannan labarin akan hannantu musawa. Muna kan tattara karin bayanai game da wannan baiwar Allah.
Ku kasance da wannan Shafin namu a koda yaushe. Mungode
Karanta: Tarihin Sheikh Abubakar Giro Argungu
0 Comments