Barka dazuwa wannan shafin namu na littafan Hausa novels inda muka kawo muku tubali hausa novel complete book 2.
Tubali Hausa Novel Complete Book 2
Tubali Hausa Novel Complete Book 2: A Jikinta ya manna kanshi da cikinta kana kuma ya cusa fuskarshi acikin jikin nata
Tare dasa hannunshi na dama ya dame mararshi
Gaba aya jikinshi rawa yakeyi tamkar mazari wani irin ciwo cikinnasa keyi masa wanda har hakan yasa numfashinsa ke kokarin kwacewa
Hannunshi na hagu yasa abayanta ya zagayeta tare da rie ta gamgam cikin gigitan ciwo da fitan hayyaci
Hakan kuwa yayi masifar gigita Jannart wanda gaba daya jikinta ya dauki rawa kamar yadda nashi jikin ke rawa
Kana ya kwakumeta ya kanainayeta ya hanata wawaran motsi
Jannart kuwa Ganin hakan yasa cikin firgici ta bue baki murya na rawa ta fara cewa
Innalillahi wa innailaihi rajiun Mamy Mamy Mamy Kalli yadda yakeyi fa
Yayinda ita kuwa Mamy cikin tsananin tashin hankali da kidima ta fara juyawa tsakiyar falon cikin rashin sanin abinyi taketa rabkawa Ramadan kira
Ramadan Ramadan Kazo Rayyern ba lfy
Dr Sulaiman ne wanda shi ya dawo da Rayyern din ya turo ofar da hanzari
baishigo da wuri bane kuma saboda ya tsaya fadawa Baba Mauo cewar ciwon Rayyern ne ya tashi
A hanzarce ya fao cikin falon
Baba Mauo na biye dashi a baya
Yayinda sukabar Hadi da Ari mai gadi kuwa tsaye a harabar gidan sunyi jugumjugum domin duk mai imani muddin yasan yadda ciwon Rayyern ke yi in ya tashi tamkar zai tafi da ransa to tabbas zai cika da fargaba
Hakan ne ma yasa Hadi zaro wayarshi ya kira Abba yana agawa cikin yanayin tashin hankali yace
Alhaji jikin Rayyern fa ya tashi
Cikin kidima Abba ya kalli mutanen da yake tare dasu tare da miewa tsaye yace
Rayyern ba lfy
Yana fain haka ya fita daga falon da bisa alamu duk mgnar sirri yakeyi
Yana katse kiran Hadi ya kira Ramadan yana agawa yace
Kai Ramadan kana ina
Da sauri yace
Abba ina Minjibir ne Lfy kuwa
Cikin bada umarni da tashin hankali yace
Maza ka wuce kayi gida yau kuma cikin Rayyern ya tashi
Cikin tsananin tashin hankali Ramadan ya mike tare da barin duk wani abu da yakeyi hankalinsa amatukar tashe yace
innalillahi wa innailaihi rajiun Jikin Hamma Rayyern ya tashi Yanzu Abba Hamma Rayyern din yana ina
Abba dake tsaye cikin alhini da fargaba yace
Yana gida kayi sauri kaje
Yana gama fadin haka ya katse kiran
Kana yaci gaba da tuin da yakeyi
Shi kuwa Ramadan a kidime ya kalli Riyyamnsra dake cewa
Hamma Ramadan meya faru
Ya are mgnar yana firfito da idanunsa
Idanu Ramadan din ya rumtse da karfi cike da alhinin abunda Abban ya gaya masa ya kamo hannun Riyyamnsra tare da jansa suka nufi parking lot hankalinsa atashe yace
Riyyam mu tafi gida yau kuma ciwon cikin Hamma Rayyern ya tashi
abunda yafi shekara biyu ya kusa shekara uku bai tashi ba amma yau gashi ya sake tashi mishi
Innalillahi
shine abinda Riyyamnsra ke ta maimaitawa
Daidai lokacin da suka shiga mota
A 360 Radaman ya figi motar yana cewa
Yah Rabbi Yah Allah ka bawa Hamma na lfy gaba aya mun sakankance da cewar ya worke tunda mukaga yayi shekaru bai tashiba
A nan gidan kuwa
Cikin yanayi tashin hankali Mamy ta kamo hannun Dr Sulaiman a gigice ta jawoshi zuwa gaban Jannart da Rayyern ke kwance kanta irin kwanciyar nan ta rubda ciki
Murya na rawa Mamy tace
Sulaiman duba min Rayyern yana raye kuwa duba minshi kaga fa baya motsi
Ta are mgnar wasu irin masifaffun hawaye na kwaranyo mata
Yayinda sai a lokacin kuma Jannart ta sunkuyo da kanta ta zuba mishi ido tabbas kuwa ya daina motsi duk rawa da karkarwar da jikinshi keyi ya bari
Wani irin zaro ido tayi tana kallon Mamy dake cewa
Innalillahi wa innailaihi rajiun Sulaiman ka duba min Rayyern kada ya tafi ya barmu akwai nauyinshi da bamu sauke a kanmu ba
Shi kuwa Dr Sulaiman kamo hannunta yakeyi yana son zaunar da ita amman ina gaba daya ta gama gigicewa ga hawayen dake ta Kwarara acikin Idanunta
Baba Mauo kuwa da sauri ya matso gaban Jannart ya tsuguna cikin kuma tashin hankali yasa hannunshi akan wuyan RAYYERN sabida a kife yake murya na rawa dattijon ya fara kiran sunanshi
Rayyern Rayyern RAYYANU Muhammad Muhammadu tashi
Bue idanunka Mauona
Ya are mgnar hawaye na kwaranyo mishi
Wanda ganinsu ne kuma yasa hawayen idanun Jannart tsinkowa
Tausayin tsohon da Mamy ne sukayi masifar raunata mata zuciya
A fili zaka gano tsananin tashin hankali da kidimar da suke ciki kana da tsananin sonshi dake cikin kwayar idanunsu
Shi kuwa Rayyern da yakejin kansa acikin wata duniya mai dauke da tsananin azaba gami da radadi samasama haka yake jiyo muryarsu
Saidai kuma bazai taba iya amsawa ba duk da yana jiyo kiran sunansa da Baba Mauo keyi saidai baya da hakikanin cewa ko yan siraran labban bakinsa zai iya motsawa saboda tsananin ciwon da yakeji
Dr Sulaiman kuwa cikin samar da kwanciyar hankali wa Mamy ya samu ya ajiyeta bisa kujera kana a hankali yace
Mamy Rayyern yana numfashi fa babu abunda ya samesa Dan Allah ki kwantar da hankalin ki Insha Allah zai samu lfy na mishi allura tun a asibiti yanzu haka ciwon ya fara lafawa Insha Allah gaba daya zai daina
Dr Sulaiman din ya kare maganar cikin kwantar da murya da kuma son samawa Mamyn nutsuwa
Daidai lokacin ne kuma Abba ya shigo
Da sauri ya iso tsakiyar falon
Sai kuma ya iso gefen Baba Mauo a kidime ya fara kiransa
Rayyern
Sai kuma ya juyo da sauri jin Dr Sulaiman na cewa
Abba dan Allah ku kwantar da hankalinku ku barshi zuwa anjima kaan zai iya amsa muku nayi masa allura Insha Allah zai samu sauki
Wani irin dogon numfashi Abba ya sauke kana ya koma ya zauna bisa kujerar dake gefensa
Yayinda Mamy kuwa har yanzu ta gaza tsaida hawayenta
Gaba daya hankalinta yaki kwanciya tsoro takeji kada wani abu ya samu Rayyern din badon komai ba kuwa saidan sanin da tayi cewar ciwon cikin baya taba yi masa da sauki idan ya tashi
Jannart kuwa da tayi kasa da kanta tana jin yadda Rayyern din ke kwakume da ita da masifar arfi yanayin rikon da yayi mata dinne kuma yasa kugunta ya soma sarawa saboda ba wai riko ne na wasa yayi mata ba rione na neman mafita
Ramadan da Riyyamnsra kuwa kusan a jere da sassarfa suka shigo cikin falon kowannensu hankalinsa amatukar tashe
More especially Ramadan da yasan irin yanda ciwon keyiwa Hamman nasu idan ya tashi
Da sauri suka nufi kanshi saidai basu karasa ba kuma suka tsaya saboda ganin su Abba duk suna zaune
Baba Mauo na zubda hawaye Mamy ma haka kana Jannart da yake kwance lib a cinyarta kamar matacce itama hawayen take tsiyayarwa
Abba kuwa habarsa ya tallafe saidai kallo daya zakayi masa ka karanto tsananin tashin hankalin dake kwance akan fuskarsa
Ganin hakanne kuma yasa zuciyar Ramadan wani irin harbawa lokaci daya kuma gaba aya jikinsa ya fara tsuman tashin hankali dan su a zatonsu Rayyern din ya rasu ne
Cikin wani irin tashin hankali rauni gigita da kuma kidima
Riyyamnsra ya saki wani irin raunataccen kuka tare da zamewa ya zauna aasa ya kife kansa bisa sawun Rayyern cikin rauni murya na rawa kuka na danne abinda yake faa yake cewa
Innallahi wa innailaihi rajiun Mammy mutuwa zata hanani cika miki burinki
Wayyoooooooo Allah na Mammy na inama kina kusa kizo kiga halin da tsatsonki yake ciki Mammy wlh shine wlh sune
Su Abba kuwa tsananin tashin hankalin da suke ciki yasa gaba aya basa iya fahimtar kalaman Riyyamnsra asalima basa jin me yake faa da kyau
Sai dai shi kuwa Rayyern da tunaninsa ke kokarin gushewa a sama sama yake jiyo kukan yaron da kuma abinda yake fai
Duk da bawai yana fahimtar kalaman sosai bane amma yaji wasu daga cikin maganganun wanda ayanzu baya cikin Lfy da kuma hayyacin da zai iya nazari ko hasashen kalaman
Dr Sulaiman ne ya matso kusa da Riyyamnsra ya jawoshi jikinsa ya zaunar dashi tare da cewa
Kai Riyyamnsra kabar kuka bafa rasuwa yayi ba ciwon ne ya fara lafawa kaga Abbanku ma yayi shiru
Sai alokacin Ramadan ya sauke wani irin numfashin daya sakar masa da wani nannauyan abu mai kama da dutse daya tsaya a irjinsa
Sabida gaba aya ya fara rasa numfashin sa
Shi kuwa Riyyamnsra cikin kasa danne kukan sa yace
Yah Sulaiman da gaske kake Hamma Rayyern dina yana numfashi
Kai Dr Sulaiman ya jinjina kana cikin sauri yace
Eh Riyyamnsra bai rasuba gashi yana numfashi nanda yan mintuna zai tashi insha Allah
Ajiyan zuciya suka saue baki ayansu
Sai lokacinne kuma Mamy ta iya tsaida hawayenta
Yayinda Baba Mauo Kuwa sam hawayen shi ya gaza tsayuwa
Hakan kuwa shi yasa Jannart ta gaza tsaida hawayenta saboda acikin rayuwar ta akwai rauni sosai matukar zata ga hawayen Babba To Lallai zuciyarta saita karye ba kuma zata iya lallashin kanta ba
Kasuwanci Na Hausa Novel Complete
Ganin duk sun dan nutsu ne kuma yasa cikin sanyi Dr Sulaiman ya samu ya zauna tare da dgo kansa ahankali yayi gyaran murya kana anutse yace
Kwata kwata abun bai wuce 30mnt da fara mishi ba domin tun da ya fara mishi na fahimta saboda naga yana ta haa zufa kasancewar alokacin muna cikin meeting ne da sauran Doctors din mu
Akan wani course da muke son wasu daga cikin Doctors in namu suje suyi a Mascow
So dana fahimci cewa ciwon cikin nasa nason tashi ne sai na bukaci da mu tashi taron amma sai yaki bani dama to kafin mu gama ma abin har ya fara tsanan ta
Idanu duk suka tsurawa Dr Sulaiman din saboda Jin abunda yake fada
Shikuwa Dr Sulaeman gyara zamansa yayi tare da fuskantarsu cike da son sake samar musu nutsuwa yace
Insha Allah Rayyern zaiji sauki domin muna fita a meeting din nayi masa allura saidai kafun nan ma tuni abin ya gama tashi shiyasa ya an wahal dashi amman Alhamdulillah bayan 50mn idan alluran ta fara aiki zai dan ji saui wanda kuma zuwa yanzu inada yakinin fara aikin allurar Dan shiyasa ma kukaga yayi shiru jikin ya daina bari
Cikin gamsuwa Ramadan da Abba suka gyaa kai saboda wannan bayanine da likitocin suka saba yi musu sudai fatansu shine samun saukin Rayyern din
Baba Mauo dake zaune kuwa ahankali yasa hannunshi ya shafa kan Rayyern din zuwa wuyansa
Kana ya mie tsaye
Tare da sharce hawayen sa
Cikin tausayawa yace
Toh Alhamdulillah Allah ya bashi lfy yasa zakkan jikine Allah ya daga kafadunsa
Ya are mgnar yana nufar hanyar fita
Cikin saue numfashi Riyyamnsra da Ramadan suka bishi da ido da kuma wani kallo mai cike da wani irin so na musamman
Abba da Mamy kuwa
Numfashi suka fesar tare da cewa
Amin ya Allah baba Mauo
Shi kuwa Baba Mauo yana fita
Hadi da Ari sukayi kanshi cikin girmamawa da kwarjinin dattijon suka hada baki wurin cewa
Allah rene ya jikin nasa
A hankali yace
Alhamdulillah jiki da saui
Allah ya kara sauki
suka hada baki wajen fada
Shikuwa Baba Maudo
Amin ya Allah
Yace yana mai wucewa cikin an side insu
Kai tsaye Bathroom ya wuce alwala yayi kana yazo
Ya dauki Kurani ya fara karatu wai ko zaiji sanyin zuciyarshi da wani nauyi daya danne mishi ahon zuciyarshi
Amma ina hakan ya gagara
Hawaye kuwa tamkar an bude bakin famfo
Allah ya sani yana jin wani irin azabebben son yaran a zuciyarshi
Baya son gani ko jin duk wani abu da zai cutar dasu duk kankantarshi da yanada hali da ko kuda bazata sauka kan Rayyern ba
Da ya dauka kawai dan kyautata mishi da sukeyi ne kuma dan kasan cewarsu yaran uban gidansa
Toh amman zuwan Riyyamnsra yasa ya fahimci kawai yana son duk wani abinda ya shafesu ne
Wasu lokutan yakanyi tunanin ko dan kamar da Riyyamnsra din yakeyi da Rayyern ne yasa yake masifar sonshi ma din
Hannun shi ya daga sama yana mai yiwa yaran addua
A nan cikin falon kuwa
Shiru Jannart tayi ta sunkuyar da kanta asa
Yayinda hawayenta keta kwaranya ba aautawa
Tana ciwo amman bata taa ganin irin wannan tashin hankali a fuskar Daddy kamar yadda ta gani a fuskar Baba Mauo da Abba ba
Bata taa ganin makamancin gigitar da Mamy tayi a fuskar Mom ba
Duk da tasan mom tana masifar sonta
Wannan kawai ya isa shaidar son uwa da banne a duniya
Mamy kuwa numfashi take ta saukewa kawai
Riyyamnsra kuwa miewa yayi ya haura sama
Yana shiga kuwa ya kira Mammyn sa
Abba kuwa cikin saue numfashi ya tallabe haba
Tare da cewa
Ramadan dagashi a kanta
Sai ka gyara mishi kwanciyarsa
Cikin sauri Dr Sulaiman yace
Aa Abba barshi shida kanshi zai tashi in allurar ta gama ratsashi
Cikin sanyi Mamy tace
Ai kuma Jannart din zata gaji
Kai ya dan juya tare da cewa
Bazai dadeba zai tashi
Shiru sukayi
Kana shi kuma Dr Sulaiman miewa tsaye yayi tare da cewa
Toh Abba ni bari in wuce gida anjima zan dawo
Toh mun gode Dakta
Abba ya faa yana mai gyara zamanshi
Shi kuwa Dr Sulaiman Ramadan ya kalla tare da cewa
Kasan idan ya tashi zai tashi ba arfi illar alurar kenan shiyasa baa cika son yawaita yiwa mutum itaba
Zaijishi duk ba arfi so dole sai an taimaka mishi ka sani
Kai Ramadan ya jinjina tare da cewa
Eh na sani
Daga nan ya sallamesu ya tafi
Su kuwa shiru sukayi suka zauna jugumjugum
Ganin kuma yamma lokacin daura girki yayine yasa Mamy miewa a hankali ta nufi Kitchen
Bayan ta cire lallenta ne kuma ta fara aiki
Ita kuwa Jannart gaba aya ta kasa kwakwaran motsi
Sabida masifar kunya da nauyin Abba da takeji kana ga kuma nauyin zaratan namiji dake kanta
Wanda agaba daya rayuwarta bata taa fuskantar makamancin hakan ba ga wani irin masifeffen amshin jikinsa dake narkar da jikinta tattausan sumar kansa da sajensa ta zuwa idanu
Yanzu kusan 50 minutes kenan suke a hakan
Yayinda kuma har yanzu hawayenta kedan disowa kadankadan
Suna mannewa ajikin gashin idanunta
Shi kuwa Rayyern dake kwance a hankali ya an ja numfashin wahala tare da fesar dashi
Kana ya rumtse idanunshi da arfi tare da taune lips inshi duka biyu saboda so yake ya tashi amman gaba aya jikinshi daga kugunsa zuwa sawun takawarsa sunyi lakwas
Wannan abun shiyasa baya son allurar
Dan muddin akayi mishi ita sai yayi kusan mako guda karfinsa bai dawo daidai ba
Da sauri Ramadan ya matso kusa dashi
Daidai lokacin kuma Riyyamnsra shima ya sauko asa
A tare suka an sunkuyo kanshi ahankali ya bue idanunshi jin muryar Abba nakiran sunansa
Rayyern Rayyern
Cikin wata iriyar sassanyar murya can asan maoshi yace
Naam Abba
Jin Rayyern din ya amsa ne kuma yasa Abba cikin jin dai yace
Alhamdulillah Alhamdulillah
Rayyern kuwa cikin arfin hali da jarunta ya tattaro ragowar kuzarin sa baki aya
Ya yunura alamun zai tashi
Da sauri Ramadan yasa hannunsa zai tallabeshi
Cikin sanyin murya yace
Barni zan iya
Cike da rauni Ramadan yace
Hamma Rayyern bazaka iyaba
Karkar haka jikinsa ke rawa
Lokacin da ya samu ya juyo ya ago kanshi
Da sauri ya rumtse idanunshi ganin kamar kan Jannart yake
Haka yasa ya miawa Ramadan hannunsa
Da sauri ya kamoshi kana ya yunura ya zauna
Lokacin Mamy ma ta iso cikin jin dai tace
Alhamdulillah sannu ko Babana
Kanshi ya gyada mata
Ita kuwa Jannart a hankali ta mie tsaye
Cikin son tsaida hawayenta ta nufi Kitchen
Tashinta ne yasa Abba matsowa kusa dashi
Hakama Mamy nanfa sukayi ta mishi sannu
Ita kuwa Jannart tana shiga Kitchen aikin da Mamy ta fara taci gaba da yinsa
Su kuwa A falon cikin arfin hali ya maida kansa ya jingina da jikin kujera kana a hankali ya fara yunurin tashi tsaye
Da sauri Abba ya tallabeshi gefen damanshi
Kana Riyyamnsra ya tallabe gefen hagunshi
Ramadan kuwa da Mamy ido suka zuba musu sunaga yadda yake taka kafafunsa da suke karkarwa
A hankali suka fara take steps din da taimakon su Abba ya samu
Suka haura
Kai tsaye Bedroom dinsa suka wuce dashi
Suna shiga suka kwantar dashi
Sanin kuma allurar zata sashi bacci ne yasa Abba juyawa ya fita
Shi kuwa Riyyamnsra gefensa ya zauna
Yana gyara masa pillow
Rayyern din kuwa yana kwanciya lokacin aya bacci ya fara fuzgarshi
Ramadan ko ganin sun haura sama ne ya sashi fita kaitsaye kuma Mainasara pharmacy ya nufa inda yaje ya dauko magungunan da Rayyern din Kesha Idan ciwon ya tashi
Ita kuwa Mamy Kitchen ta koma nan sukaci gaba da aikinsu ita da Jannart
Bayan sallan ishai
A hankali Jannart ta dan juyo tana kallon kofar babban falon
daga nan cikin falonta
Da sauri kuma ta mie jin muryar mutumin nan da taji ana kiransa da Baba Mauo yana sallama
Da alamun kuma babu kowa a main falon
Da sauri ta mike ta nufo falon
Baba Mauo Kuma tsaye yake bakin ofar ya an turota yana sallama da an buga kofar
A hankali tace
Wa alaikassalam Baba ka shigo mana
Daidai lokacin kuma Mamy ta fito daga side insu
Cikin girmamawa tace
Aa Baba Mauo ka shigo mana
Cikin kamala yace
Toh
Kana ya shigo
A hankali Jannart ta dan rusuna tare da cewa
Barka da dare Baba
Juyawa yayi ya kalleta cikin wani irin mamaki da nazarin fuska da kammanin muryar yarinyar yace
Barka dai Ya mai gidan naki da jikin
Cike da girmamawa tace
Alhamdulillah jiki da saui
Masha Allah Allah ya ara mana sauki
Ya faa yana mai juyowa yana kallon Mamy dake cewa
Bismillah mu isa yana sama Abbansu ma yana can
Hakan ne yasa ya nufi saman
Ita kuwa Mamy juyowa tayi ta kalli Jannart da idanunta suka dan yi ja cikin kulawa tace
Kinyi salla ko
Kai ta gyaa mata alaman eh
Ita kuwa Mamy
Ba tare da tace mata komaiba ta nufi Dinning area
Foodflask ta auko wanda tasa mata
Abincin da sukayi sakwara ce da miyar agushi
Mia mata tayi tare da plate da spoon tace
Gashi ki zauna kici abinci ki kuma bar zubda hawayen nan haka kinji ko Mamana
Cikin sanyi tace to
Kana ta amshi kular ta wuce akinta
Ita kuwa Mamy Kitchen ta koma tazo ta shiryawa su Ramadan nasu ta kai musu falon sama
Anan ta samesu
Baba Mauo da Abba Kuma suna cikin dakin Rayyern in
Ganin har yanzu bacci yakeyi ne yasa suka fito
Ita kuwa Jannart ajiye kular tayi a falon
Ba tare da tayi niyar ciba ta kwanta a asa bisa carpet din tana rike da wayarta
Sam ta rasa me take tunawa
saidai kawai ta fahimci cewa yau gidan babu dai dan ciwon Rayyern in
Sabida su Ramadan masu ebe mata kewa da Riyyamnsra mai sata farin ciki duk yau basa da Gud Mood
Tana nan kwance ahaka har tayi bacci
A folon kuwa suna fitowa suka samu Dr Sulaiman ya iso
Nan Abba ya koma dashi ya an ara dudduba shi
Kana ya sallamesu ya tafi
Haka dai su Ramadan suka tafi dakinsu
Mamy kuwa falon Jannart ta lea ganin tana bacci ne yasa ta wuce side insu
Dan tasan yau Abba a dakin Rayyern zai kwana
Haka
Hakan kuwa akayi
Rayyern kuwa baccin yayi mai zurfi sai karfe uku da rabi ya farka
Abba da kanshi ya hada masa ruwa yayi wonka
Kana yayi alwala
Yana fitowa yayi ramuwar sallan magriba da ishai sannan ya dan sha tea in da Abba ya hada masa da kansa
Toh kuma daga nan sai idonsa ya an bushe
Sai da akayi sallan asuba
Kafin ya koma wani baccin
Koda Abba suka dawo masallacin sun sameshi yana bacci
Nan suka fito
Mamy da Jannart kuwa Kitchen suka shiga dan haa breakfast
Kasan cewar yau in asabar ce ba aiki
Yasa Riyyamnsra da Ramadan ma basu tashi da wuriba
Sai karfe tara suka fito
dakin Rayyern suka shiga
Zaune suka sameshi bisa carpet ya jingina jikinsa da gado
Mamy da Abba ne zaune agabanshi
Mamy na haa mishi tea
Abba Kuma da kanshi yake zuba mishi ferfesun jan nama da Jannart tayi mishi yayi laushi tibis
A hankali ya an juyo ya kalli Radaman dake cewa
Hamma ya jikin naka
Cikin saue numfashi yace
Alhamdulillah
Riyyamnsra kuwa matsoshi yayi da kyau tare da cewa
Hamma Rayyern Mammy ta gaishe ka da jiki
Zaiton ma tace in gaisheka da jiki
Cikin sanyi yace
Ngd
Ganin kuma alamun bai son surutune
Yasa suka sauo asa
Abba kuwa cikin kulawa yace
Rayyern kaci abincin tunda uminsa kaji
Cikin sanyi yace
Abba na gaji bazan iya cin nama da sassafen nan ba
Da sauri Mamy tace
Rayyern yayi laushi sosai fa
Cikin narke fuska yace
Bani tea in kawai is okay
Haka suka hakura suka barshi
Tea in yasha
Kana Abba ya kuma hada masa ruwan wonka yayi
Koda ya fito daga wankan wasu tausassun riga da wondo yasa wanda Abban ya fito masa dasu
Mamy kuwa tuni ta sauko kasa
aasan ta samu su Ramadan da Riyyam nsra a dining area suna zaune Yayinda Jannart ke zuba musu abinci
Da sauri Mamy tace
Kai kun kai abincin su Baba Mauo kuwa
Kai Riyyamnsra ya gyaa tare da cewa
Eh Mamy nakai musu yanzu ma na dawo
To yayi
Mamyn tace tare da zama gefensu nan sukayi Karin kumallon
Wunin ranar dai haka sukayi shi a gida gaba dayansu
Alhamdulillah kuma jikin Rayyern da sauki sai dai rashin karfi da rashin cin abinci dama kuma da rashin son mgn da bayayi dama kuma shi ba gwanin surutu bane balle kuma yanzu ga halin ciwo
Washe gari ranar lahadi ma
Haka suka wuni
Duk da surutun Riyyamnsra ya rage
saboda jikin Hamman nasa
Da yamma kuma Nasir Ahmad yazo ya duba Rayyern din da jiki
Bayan sun dan taba hira shida Riyyam nsra ne kuma yayi musu sallama daga nan kuma gidan Malam Mainasara ya wuce
Nan yake sanar masa abinda ke faruwa
Jannart kuwa tun ranar tun lokacin kuma bata sake ganinsa ba ko jin muryarsa
Yayinda Mamy kuwa duk a zatonta Jannart din duk safiya tana zuwa duba jikin Rayyern din
Washe gari Ranar Monday Alhamdulillah jikin da sauki sosai domin karfinsa ma ya an fara dawowa
Bayan sunyi breakfast ne kuma Ramadan ya tafi asibiti
Hakan yasa Jannart da kuma Riyyamnsra sai kuma Mamy ne ke zaune afalon
Dago kai Riyyam nsra din yayi tare da kallon Jannart dake rie da wayarsa tana kallon comments in followers insa akan wata wakar fullancin daya bibiya
jin wayar tasa tana ringing ne kuma yasashi kallonta tare da dan gyara zamansa yace
Aunty Jannart Waye
Mammy ce
Ta bashi amsa tana mio masa wayar
Da sauri ya amshi wayar tare da amsa kiran
Assalamu alaikum yah Mammy
Jim ya anyi na tsawon kusan daiu 2 kana a hankali ya mie tsaye tare da fara haurawa sama yana cewa
Afwan Mamma wlh shine baya son surutu ko wayarsa bai amsa kira tun ranar nake son hadaku toh ganin baida lfyarne yasa nai shiru
Ya are mgnar yana ida hawa saman
Kai tsaye dakin Rayyern in ya nufa da sallama a bakinsa
A falon kuwa cike da mamaki Mamy ta bishi da ido
Zuwa yanzu ta fara tsoron wani alamarin to wai ma ya akayi bata taa tunanin Riyyamnsra ya nuna mata hoton Mammansa ba
Tayi wannan tunanin
Jannart kuwa da sauri ta juyo ta kalli wayarta dake gefenta cikin mamaki ta zubawa wayar ido ganin number dake kiranta
Shi kuwa Riyyamnsra a hankali ya isa gaban Rayyern dake zaune bisa kujera
Yasa system in shi a gaba da alamun aiki zaiyi dan yanzu ya bue ta
Idonshi ya ago ya zubawa Riyyamnsra su
Shi kuwa Riyyamnsra cikin karya wuya
Da rauni ya iso garesa murya a raunace yace
Ayyah Hamma Rayyern dan Allah ga waya kayi mgna da Mammy na tun shekaran jiya take cemin in hadaku ta gaidaka da jiki taji muryarka
Ya arashe mgnar yana karya wuya
Ga mamakin Rayyern kuwa sai ga hawaye na zubowa a fuskar yaron
Shi kuwa Riyyamnsra cikin yin raurau da ido
Ya mia masa wayar tare da cewa
Dan Allah Hamma Rayyern kada kace aa
Ya rigada ya gama karya mishi zuciya da hawayensa
Duk da ko mgnar yayi sai yaji ya gaji shiyasa baya son yawan mgn
A hankali yasa hannunshin ya amshi wayar
Cikin nitsuwa ya manna wayar a kunneshi tare dasa kafaarsa ya makale wayar
Murya a sanyaye yace
Assalamu alaikum
A can asar Ethiopia kuwa
Wani irin lumshe ido Mamma tayi tare da jan wani irin dogon numfashi kana cikin tsananin harbawar da zuciyarta keyi tace
Wa alaikassalam Mauo am
Wani irin rumtse idanu Rayyern yayi da azaban arfi tare dasa hannunshi y
Sabbin Hausa Novels Zafafa na 2023
Albishirinku Maaurata GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku maaurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MAAURATA
NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara Kullum dai magana daya ce akan maaurata fada rashin jituwa mutuwar aure akan kuskure kalilan rashin kula rashin yi wa juna uziri Toh wai duk me ya janyo hakan Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take Shin yaruwa ke macece amma kin san wacece mace ku Kin san me ake kira mace kuwa Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango sanyin idaniyarsa ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da niimar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su
Wannan ita ce mace Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace kaya ne da suke taimakawa sex hormones dinki
Misali kina kallon India hollywood Asian film kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu
Saboda me hakan Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da niima cike da tsukewa kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haine na ingantattun itatuwa da yayansu
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki
Zo ki ji yaruwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace Gubar ciko gumbar tsalle dole gubar da baa baiwa mai kishiya garin mai garin mallaka tsumin goron tula tsumin tsartai tsumin maratsi palapala butar sirri kwanon kasaitacciyar mace furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu
Ina mata masu fama da sanyi Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan
Ina da ciccibi mai kyau Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya
Akwai daya bangaren wato KAMSHI
Kimarki gyaranki da kamshinki Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta akwai shuumar humra sayan na gari maida kui gida banda karanta yayin gyara Hajia
Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zainki ko karin bayani zaki tura kuin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn
Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
GARKUWAR MAAURATA
By
GARKUWAR FULANI
22122021 1945 Ya dafe ahon zuciyarshi sabida wani irin masifeffen harbawa da yaji tayi da azaban arfi
Yah salam
Shine abinda ya iya fada cikin zuciyarsa
Yayinda Riyyamnsra kuwa ya zauna a kasa a gabanshi tare dasa hannunshi duka biyu ya tallabe Fuskarsa kana ya zubawa Rayyern in idanu kamar mai kallon madubi ko TV
Shi kuwa Rayyern wani irin sakewa yaji jijiyoyin kanshi zuwa zuciyarsa sunayi
Suna bada sautin
Rasras yayinda duk kofofin gargasar jikinsa suka fara amsa amon muryar baiwar Allah nan
Yayinda can wurin Mammy ma haka abin yake
Dan Tuni ita wasu hawaye na ke tsiyayo mata Yayinda takejin zuciyarta nayi mata ani irin duka
Cikin rumtse idanunta tace
Maudo ya jikin naka
Idanunsa ya dan lumshe cikin kuma jin wani sabon bugun zuciya yace
Mammmmmy jiki da saui Alhamdulillah
Riyyam nsra kuwa dake gefe wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo daga cikin idanunsa wanda sukafi kama da hawayen farin ciki
Yayinda shikuwa Rayyern meda kanshi yayi ya jingine jikin kujerar yana mai amsar saon da jijiyoyin jikinsa suke bashi
Cikin kasala kuma ya motsa lips insa tare da cewa
Amin Mammy
Ya fadi hakanne kuma saboda adduar da Mammyn tayi masa
Mammy kuwa Idanunta ta lumshe cikin kuma danne abunda takeji yayi tsaye acikin zuciyarta ta soma yi mishi adduan samun lafiya tare da sa mishi albarka
Sai kuma ta daura da cewa
Ina Ramadan
Cikin saue numfashi Rayyern din yace
Ya tafi wurin aiki
Daga can bangaren Mammy kuwa Kai ta jinjina tare da soma tambayan shi akan sauran ahlin gidan nasu
Shikuwa Rayyern duk yanda yakejin mood dinsa na sanjawa amma anutse yake amsa mata kana kuma
Cikin girmamawa
Kamar da wasa kuwa shida Mammyn saida sukayi mgnar mituna shida kana sukayi sallama
Bayan ya zare wayar akan kunnensa ne kuma ya mikawa Riyyam nsra
Cikin sauri kuwa Riyyam ya karbi wayan tare da mikewa tsaye direct ya koma dakin Ramadan
Ganin fitan Riyyam dinne kuma yasa Rayyern jingine kansa da jikin kujera tare da rumtse idanunshi
Asanyaye kuma cikin tausasshiyar muryarsa yake fadin
Yah ilahi ya mujibaddaawati
Ya salam
Sune abunda yake fada yana mejin
tamkar kanshi zai juye abubuwa da yawa keyi masa yawo acikin tunanin sa
Maudona
Ya maimaita kalmar da yaji ya tsaya mai arai dan sai yakejin tamkar ya taba jinta
Idanunshi ya bue kana a hankali yace
Toh ko dai Baba Mauon da nake jine yasa naji kamar nasan kalmar ada can baya
Saurin girgiza kanshi yayi tare dasa hakwaransa ya cije lips dinsa
Take kuma ya fada dogon nazari wanda hakan yasa ya gaza ci gaba da aikin da yake son yin
A can falon kuwa cike da mamaki Jannart ta zubawa wayarta ta ido
Taki amsawa
Jannart ba kiranki akeyi ba ki amsa mana
Mamy ta fada tana kallonta cikin kulawa
Jannart din kuwa cikin yanayin nazari tace
Mamy numbern ba suna ban san waye bane
Ta ida mgnar tana jawo wayar jin da tayi sako ya shigo mata
Toh ki amsa mana ai zakiji waye ne
Cewar Mamy
Jannart din kuwa kai ta ago daga duba sakon tare da cewa
Lah ashe ma Aunty Dijat ce
Ganin kiran ya kuma shigowa ne yasa ta amsa kiran
Tare da kara wayar a kunne
Da sauri tace
Abba kaine
Gyara zama Barrister Kabir yayi tare da cewa
Eh nine dai Jannart na fahimci
Daddynki yana iya zargar wayata da bin diddiginta ne yasa na kiraki da wayan Khadija
Cikin gamsuwa tace
Ayyah Daddy na
Miewa Mamy tayi ta bar wurin
Sabida ta barta ta an sake
Ta sake din kuwa ganin Mamyn ta tafi cikin nitsuwa tace
Abba ya lbrin su Daddyn ya Mom tayi ina Yah Azeez na
Da sauri yace
Me ruwanki dasu
Shiru tayi cikin sanyi jiki ta mie ta nufi falon ta
shi kuwa Barrister Kabir cikin kulawa yace
Kina lfy ko
Lfy lau Alhamdulillah Abba
Ta bashi amsa tana zama
Gaba aya jiya ke nai ta tunawa da sanyin nan ki kula da kanki sosai kin san irin wannan sanyin arshen hunturun yafi miki illa da tada ciwonki kiyaye shan ruwan sanyi da AC sannan kike rufe Windows inki duka sabida hazo kinji ko
Cikin nitsuwa tace
Toh Abba
Juyowa yayi ya kalli Dijat dake ta son ya Bata wayar suyi magana da Jannart din kauda kanshi yayi daga kallonta tare da cewa
Gidan naku duk lfy ko
Gyara labulen window dake kusa da ita tayi kana a hankali tace
Uhumm shine dai baida lfy tun ran jummaa wai ciwon cikinsa ya tashi sai ka gani Abba kamar zai mutu fa
Ta kare maganan cikin dan nuna tausayawa
Abba Kabir kuwa da sauri yace
Subahanallah Rayyern din
Kai ta gyaa kamar tana gabanshi
Sai kuma ta daura da cewa
Eh Mamynsa nata kuka da Baba Mauo
Innalillahi Jannart meyasa baki gaya min ba
Cikin sanyi tace
Abba na manta ne
Cikin faa yace
Jannart ki mance ciwo da lfyar mijinki Kada ki sake yin haka kul kinji ko
Cikin biyayya tace
Toh Abba
Barrister Kabir din kuwa dan gyara zamansa yayi tare da cewa
In sha Allah da yamma zan zo akwai wani abu da kike bukata ne
Kai Jannart din ta jinjina kana cikin sanyin murya tace
Aa Abba babu abunda nake bukata
To shikenan sai nazo
Daga haka sukayi sallama
Bayan ya katse wayarne kuma ta mike tare da fitowa waje suka shiga Kitchen da Mamy
Da yamma misalin arfe biyar da da rabi na yamma
Abba da Barrister Kabir din Suka shigo a jere
Kasancewar shigowar Barristern ya samu Abban a wurin Baba Mauo ne
Ganinsu ne kuma yasa Mamy yin murmushi fuska asake tace
Sannu da zuwa Barrister
Shidin ma Barrister Kabir din murmushi yayi kana cikin mutuntaka yace
Yauwa sannu Hajiya fatan na sameku lafiya ya mai jiki
Lafiya kalau Barrister jiki kuma Alhamdulillah dan yana ta samun sauki ya iyalai
Masha Allah Iyalai Alhamdulillah
Ya fada adaidai lokacin da yake zama akan kujera
Yayinda ita kuwa Mamy juyawa tayi kaitsaye ta nufi dakin Jannart tana cewa
Jannart ga Abbanki yazo
Jin abunda Mamyn ke fadane yasa Jannart dake zaune saurin mikewa tsaye tare da nufo falon tana gyara mayafin doguwar rigar jikinta
Murmushi Mamy tayi tare da juyowa
Ta nufi falon ita kuwa ta rufa mata baya
Suna fitowa ta nufi kusa da Abban tana murmushi
Abba sannu da zuwa
Tace tana zama agefenshi
Yayinda ta hango Abban Rayyern kuma yana haurawa sama
Mamy kuwa Dinning area ta nufa
Goran Ruwan sanyi dana Nutri milk tasa a an ma daidaicin tray da cup kana Akan santer table in dake gabanshi ta ajiye tray tare da zama bisa kujera
Sannu Barrister Bismillah ga ruwa
Ta faa cikin kulawa
To nagode
Barrister Kabir ya amsa
Tare da daukan ruwan ya dansha kadan
Jiyo alamun ana sauowa ne kuma yasa Mamy maida kallonta ga stairs din
Ganin kuma Rayyern ne yake takowa a hankali yana sanye da wata tattausar jallabiya baa mai masifar shei
Irin mai guntun hannu ne jallabiyar
gabanta kuma ta sama ankawatasa da aninaye
Abba na biye dashi a baya
Sosai ya an rame duk da jallabiya ce a jikinsa kuwa amma ramarsa ta an fito sai wani irin fari da yayi yayinda sajenshi yake an hargitse
Cikin jin dai Mamy tace
Alhamdullahi lallai yau kam jiki da saui tunda har Babana zai sauo asa
Jin hakane yasa Barrister Kabir juyowa ya kalli gefen damanshi ganin Rayyern ne da yadda yake tafiya a kasalance alamun ba isashen arfi ajikinsa ya sashi cewa
Ayyah Alhaji da ka barshi ai Idan yaso ni saina haura in ganshi gaskiya yaji jiki
Daidai lokacin kuma suka iso kan steps in arshe
Cikin yanayin gajiya da maida nufashi ya zame ya zauna kan step na biyu tare da jingina kansa da jikin arafunan gefe da gefen steps din cikin lumshe ido yace
Abba na gaji
Ya are mgnar yana kallon tsakiyar falon
Ita kuwa Jannart jin muryarsa ne da kuma abinda Mamy da Abbanta suka fadane yasa ta ago kanta tare da ware manyan idanuntata kalli hanyar sauowan
Wanda yanzu kusan satinta uku a gidan amman bata taa zuwa ko kusa da wurinba
Ido cikin ido sukayi dashi
Wanda hakan yasa tayi maza tayi asa da kanta
Tare da lumshe idanunta tabbas ya rame sosai fuskarshi tayi wani irin haske
Sajenshi ya hargitse kaan alamun babu isasshen arfin jiki da nitsuwar lfya
Dibdabdibdab haka taji bugun zuciyarta na harbawa
Shi kuwa Rayyern fuskarshi ya tsuke tare dayin mgnar zuci
Eh dole mana a Barka ka haura sama tunda gaka ubana kasan da ka gani ka karanta duk bai isheka ba ai sai kaga makwancina
Mtswwww yaja an gajeren tsaki cikin bakinsa
Mamy kuwa cikin jin dai tace
Sannu ko Babana
Kai ya gyaa mata cikin sanyin jiki
Abba kuwa gefenshi ya an ratsa tare da cewa
Toh huta sai ka araso ko
Kai ya kuma gyaawa
Barrister Kabir kuwa gyara zamansa yayi tare da cewa
Rayyern ya jikin naka
Da sauri yace
Alhamdulillahi ni nama worke
Murmushi Barrister yayi domin ya gane cewar
Har yanzu DrRayyern bai yarda dashi ba asalima zarginsa yakeyi
Cikin kulawa yace
Masha Allah Haka ake so
Allah ya ara lfy da karfin jiki
A takaice yace
Amin
Shi kuwa Abban Rayyern da Mamy cikin jin dai sukace
Amin Amin Barrister mun gode matua Allah ya bar zumunci
Amin yace yana mai kallon Jannart data sunkuyar da kanta asa tana wasa da wayar hannun ta
Miewa tsaye yayi tare da cewa
Toh Alhaji bari in wuce gida Allah ya ara saui
Miewa shima Abban yayi tare da cewa
Amin Amin Barrister mun gode sosai
Daga nan suka fita tare
Suna fita itama Jannart ta mie ta nufi akinta
Da wani irin masifeffen kallo Rayyern ya bita dashi kallon da yafi kama da harara
Mamy kuwa shi in ta zubawa ido Jin ana kallonsa ne kuma yasa ya an juyo ya kalli Mamy ganin yadda ta tsareshi da ido ne yasashi kwae fuskarsa tare da miewa ya dawo kan doguwar kujera
A hankali ya kwanta tare da aura kafa aya kan aya kana
Yace
Mamy Riyyim fa
Numfashi ta sauke tare da cewa
Ya tafi yi mana cefene shida Hadi
Kai ya gyaa tare da fuskantar TV
Ita kuwa Jannart tana shiga part dinta
Wonka tayi tare da alwala kana ta fito dan magriba ta gabato
A falon kuma a tare Ramadan da Riyyamnsra da Abba suka shigo
Gaba ayansu rie da manyan ledodi
Kitchen suka wuce
Kasan cewar kayan miyane
Yasa duk suka diresu nan
Kana duk suka je sukayi alwala
Shi kuwa Rayyern dama ya koma akinsa dan yin wonka
Bazai iya zuwa masallaci ba dan dan haurowan da yayi duk jikinsa rawa yakeyi
Haka yasa yayi salla a akinsa
Su kuma suka wuce masallacin
Basu dawoba saida sukayi ishai
A haka dai Rayyern yayi jinyar an motsawa kaan da ciwon cikinsa yayi
Cikin ikon Allah cikin mako aya ya samu lfy sosai yanzu arfin jikinsa ya dawo
Yau Monday har asibiti yaje sai dai sam bakinsa ba dai shi yasa bai iya cin abinci
Jannart kuma bata wani ganinsa bare wata mgn ta haa su
A can sashin Alhaji idi Saleh Dakata kuwa
Duk yadda Barrister Kabir ya zaci takun yayan nasa ya wuce zatonsa
Hakan yasa ya tsananta matakan irin bi diddigi
Da taimakon Baba Ado da Ashiru
Duk yadda yaso gano ainihin zuciyar yayan nashi ya gaza ganewa
Yah Azeez kuwa sosai ya shiga tashin hankali
Wanda saida yayi jinyar ciwon da tashin hankalin yasakar masa
Mom da Abdul kuwa gaba aya gidan ya juye musu
Domin abun ya musu yawa ga Daddy da hawanjininsa ke yawan tashi binibini ciwon kai an tafi asibiti
A can tashar Arewa 24 TV kuwa
Gaba aya Aisha Lawal da Aunty Fauziyya D Sulaiman da Hajia Rabiah dama sauran maaikatan hankalinsu yayi matuar tashi da jin labarin acewar Jannart
Musamman Salman da gaba aya ya gigice ya imauce
Dan abun ya daki zuciyarsa sosai hakan yasa ko aiki yanzu ya dena zuwa dan shi a zatonsa akan shirinsu aka sace ta sai yake gani shine next target din masatan
Ganin tashin hankalin da yake cikine kuma yasa
MD neman Barrister Kabir yayi mishi bayani
Dole yazo har gidansu shida MD
Nan sukayi mishi duk bayanin abinda ke faruwa
Toh Alhamdulillah ya samu nitsuwa sai dai kuma ya shiga ruani
Nan MD ya gyara zamanshi tare da cewa
Yanzu dai sai ka kwantar da hankalin ka
Ka fara zuwa aiki
Da sauri yace
Toh Ni da waye zamuyi aikin
Cikin saue numfashi MD yace
Yanzu zamu bawa Asiya rion kwaryar shirin zuwa lokacin da komai zai daidaita
Cikin tarin ruani yace
Toh ita Jannart fa
Da sauri Barrister Kabir yace
Kada ka damu da mgnar Jannart komai zai daidaita da izinin ubangiji
A hankali yace
Toh Allah ya yarda
Amin Amin sukace kana suka sallameshi suka tafi
A gajiye ya dawo cikin gidan
Ko yanzun fitowarsa kenan daga cikin mota Yayinda Usman PA ke rie da marfin motar
Cikin kulawa yace
Sannu
Kanshi kawai ya gyaa kana ya raa ta gefen Usman ya wuce
Shi kuwa Usman binshi a baya yayi rie da jakar laptop dinsa da aya wayarsa sai wasu files dake hannunsa
A hankali ya kalli Baba Mauo dake yi masa ya jiki fuska ya an sake tare da cewa
Jiki da sauki Baba Mauo
Masha Allah Allah ya ara sauki
Amin Amin
yace tare da wucewa
PA na biye dashi a baya
Wa alaikassalam
Mamy tace lokacin da suka shigo tare da sallama a bakinsu
Masha Allah Babana sannu da dawowa ya Office
Mamyn ta Kuma faa
Shikuwa Rayyern numfashi ya an fesar tare da cewa
ALHAMDULILLAH Mamy
Juyowa tayi ta kalli PA dake gaidata tare da ajiye kayan uban gidan nasa agefenta
Lfy lau Usman ya Umma da jiki
Mamyn ta amsa masa tana dan murmushi
Jiki da saui tace ma in gaidaki
Ya faa yana kallon Rayyern in daya nufi Dinning area
Kai ya an juyo tare da cewa
Riyyam fa nasan Ramadan kam mun barshi a asibiti
Riyyam yana sama yanayi musu gyaregyare
Murmushi Usman yayi tare da cewa
Toh wai sai yaushe zai koma ne yanzu fa yafi wata aya da zuwa har ya shiga na biyu kuma banga yana wani aikinba
Da sauri ya kalli Riyyamnsra dake saukowa yana cewa
Toh PA ko dai korata zakayi ne wai dan Allah ma me na tare maka ne nafa gane tun a jirgi ba sona kakeyi ba to yawo nazo ko kana da mgna
Ya ida mgnar yana turo baki
Dariya sosai PA yayi domin dama akwai yar tsama tsakaninsu cikin dariya yace
Aa ni kuma in koreka to a kaina kake ne
Cikin tae bakinsa da salon an samarin TIKTOK da sukafi kama dana an daudu yace
Toh waya sani
Murmushi Usman ya kumayi tare da cewa
Mamy ni bari in wuce gida
Toh ka gaida Umma ko Usman
In Sha Allah zataji
Ya bata amsa
Har yaje bakin ofar fita kuma ya juyo tare da cewa Riyyamnsra
Nest week fa zamu wuce China dan haka ka shirya mu saueka a asarku
Ya are mgnar cikin tsokana
Shi kuwa Riyyamnsra murmushi yayi tare da cewa
Ayyah to dan Allah ka bari in zamewa Hamma Rayyern PAnsa mu tafi tare
Dariya Usman yayi kana ya juya ya fita
Shi dai Dr Rayyern bai kulasu bama
Shi kuwa Riyyamnsra System in da wayar ya auka ya koma sama dasu
Mamy kuwa shiru tayi ta kasa kunneta can kitchine dan tasan Jannart na ciki taga kuma Rayyern ya nufi can
A hankali ya sako afarsa ka step in Dinning area
amshin da yake jin ya an shaa
Ba tare da tunanin komai ba ya kutsa kai cikin Kitchen din
Ita kuwa Jannart dake tsaye miyar taushe da man shanu take haawa Yayinda tamaida gaba daya nutsuwarta ga aikin da takeyi din wanda hakan yasa ita sam bata ma lura da shiba
Shi kuwa Rayyern yana shigowa cikin kitchine din idanunsa suka sauka akan bayanta
Wanda dogon gashin kanta ya sauko har tsakiyan gadon bayan ta kasancewar kuma turkish gown ne ajikinta shiyasa tayi kyau sosai yaudin duk wani kuruciya da yarintar ta I mean innocent dinta ya bayyana
Kallo daya yayi mata ya dauke kansa tare da tabe bakinsa batare kuma da ya aiwatar da abunda ya shigo dashi cikin kitchine dinba ya juya tare da ficewa Kai tsaye ya nufi falon Abbansa
Da sallama a bakinsa ya shiga
Gefen Abban nasa ya zauna
Bayan sun gaisane kuma ya an gyara zamanshi kana cikin nitsuwa yace
Abba batun tafiya ta China fa na gama komai Insha Allah Ranar Monday mai zuwa zamu tafi
Cikin zuba mishi ido Abba yace
Rayyern bazaa bariba kuma sai ka kara samun lfyar jikinka
Dan guntun murmushi Rayyern din yayi tare da gyara zamansa yace
Abba ba komai nayi sauki ai zan iya zuwa kaga in mun je in ma ba dadewa zamuyi ba dududu bazan fi kwana ashirin ba zuwa da biyar zan dawo
Dan jim Abban yayi kana cikin shakka yace
Kai gsky ni dai ban gamsuba
Da sauri yace
In sha Allah Abba ba komai fa zanje lafiya nadawo lafiya
Kai Abban ya an jinjina tare da cewa
Kayi shirin tafiyar ne
Da sauri yace
Ai na gama komai ma nida Usman zamu je
Akaro na barkatai Abban ya sauke numfashi tare da cewa
Toh Allah ya kaimu ya kuma bada saa
Amin Amin yace
Jin an fara kiran sallan magriba ne kuma yasa duk suka mike sukayo alwala suka wuce masallaci
Yau jummaa Bayan an taso sallan jummaa ne kuma suna zazzaune a falon suna cin abinci
Dan duk basu ci abincin rana ba
Sabida gudun kada su makara
A nitse ya turo ofar falon ya shigo
Tare da sallama a saman lips inshi yayinda Usman PA kuwa ke biye dashi a baya
Riyyamnsra ne ya fara mgn ba tare da ya haiye danwaken da yasa a bakinshi ba yace
Hamma Rayyern Mammy tace in gaisheka da jiki
Cikin alamun gajiya da an yunwa ya gyaa kai
Yana mai kallon Mamy da Usman da suke gaisawa
Kana Mamy na sawa Usman din danwaken a plate
Shi kuwa Usman kanshi ya an juyo ya kalli Jannart dake bare dafeffen kwai
Hajia Barka da yamma
kasa ta danyi da kanta batare kuma da ta dago ta kalleshi ba cikin mutumtawa tace
Barka dai PA ya gida
Tayi maganan tana bare kwan tana sawa a plate din da Mamyn ta turo mata
Kana ta mia mishi
Ramadan kuwa baki ya an bude tare da an yin shishitan yaji yace
Kai yajin nada zafi my Aunty ara min salat da tumatur da kwai in zai an kashe yajin
Ya are mgnar yana turo mata plate din murmurshi tayi tare da cewa
Toh sha ruwa kafin nan
Ba musu ya auki cup din ruwa dan suna masifar tsoron yaji
Riyyamnsra kuwa sai ci yake yana tande baki kamar era a gari
Shi kuwa Rayyern a hankali ya an muskuta tare da kwae fuska
Ido Mamy ta zuba mishi
A hankali yasa hannunshin ya shafa cikinsa kana yace
Yunwa
Yayi mgnar can asan makoshin sa
Kai ta jinjina tare da jawo plate alamun zata zuba mishi
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da nuna mata Ramadan daketa shishitan
Abu sai kace cimar Mayumutun yanaci yana gigicewa
Ai ni in nasa wannan a bakina suma zanyi Mamy
Yayi mgnar yana miewa tsaye
Murmushi Mamy tayi
Ita kuwa Jannart lips inta duka biyu ta hae ta ciza
Saboda yayi mgnar da arfi kuma da gayya
hakan yasa acikin ranta tace
Uhum ni dai ba mayya bace ato
Shi kuwa fara haurawa sama yayi tare da cewa Mamy
Please Mamy abu mai an ruwaruwa
Ba tare da ta kulashi ba
Ta kalli Jannart tare da cewa
Kici mana Jannart
Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa
Na koshi Mamy sai anjima
Juyowa sukayi suka kalli ofar akin
Jin ana bubbugawa
Da sauri Riyyamnsra dake ta hanyar kofar ya mike tare da zuwa ya bue
Fahad ne telan Mamy da ta bawa kayan Jannart
Cikin sauri Riyyamnsra yasa hannunsa ya amsar masa jaka aya tare da cewa
Bismilla shigo ciki Mamy Fahad ne
Yayi mgnar yana shigowa Fahad na biye dashi a baya yana dariya tare da rufe ido
Da sauri Mamy ta juyo tana kallon Fahad tare da cewa
A Allah mai iko alawarin tela bai zuwa masallaci nanfa ace min mako biyu har zance yayi yawa ma amma nai shiru sai gashi kuma sai yau ka bullo
Dariya mai sauti Fahad din yayi tare da ajiye jakar hannunshi
Kusa da inda Riyyamnsra ya aje na hannunsa
Kanshi ya an shafa tare da zama gabanta kana anutse yace
Wlh akasi aka samu zazzai ne ya
Da sauri Ramadan ya katseshi da cewa
Dan Allah kada ka daurawa kanka ciwo Fahad kai dai kawai kayi shiru
Dariya yayi tare da cewa
Toh Hajia buesu ki ganima zaki sha mamakin kyansu da tsarinsu
Murmushi Mamyn tayi tare da cewa
Toh Jannart tattare plates din nan
Murmushi Jannart din tayi tare da fara tattare wurin
Ita kuwa Mamy Fahad din ta zu bawa danwaken tare da sa mishi duk kayan hai
Gyaran zamanshi yayi tare da fara ci
Yayinda Jannart kuwa ta gyara wurin
Riyyamnsra kuwa kayan ya fara jawowa da sauri Fahad yace
A kai malam dakata ya kake figosu haka a dinke a goge suke da ko wanne yana hae da an uwansa cikin leda
Ya are mgnar yana matsar da plate din gabanshi ya matso
Kana ya fara fito dasu daya bayan daya saida ya fiddasu kab kala ashirin da biyar
Shadda biyar lace biyar atampa biyar material biyar shadda lace biyar
A hankali ya fara ware inkin wata shadda pink color wacce akayiwa inkin fent wok mai masifar kyau dan doguwar rigace
Masha Allah gsky inki yayi kyau
mamy ta faa tana kallon rigar atamfar da ya kuma warewa
Irin in kin nanne na duwatsun shuwariski masu masifar kyau da akabi da kelleyen kolliyar
Kasan cewar atampar koriyace sosai take daukar ido
Medata yayi ya ninke tare da jawo wani shadda lace mai azabar kyau pink and purple mai an karen tsada
Sai wani lace ya kuma fiddasa kalan yellow and orange anyi masa inkin gariyar mata mai masifar kyau
Ita kanta Jannart kai ta jinjina dan ta gamsu da kalar kayyakin da zafafan inkuna na zamanin da suka samu
Cikin jin dai Mamy tace
Kai sannu da aiki Fahad na huce dan gaskiya kamana dinki mai kyau ninkesu kawai medasu leda dama
nasan inkinka ai babu haifi
Murmushi yayi cikin jin dai kana ya medasu cikin leda
Tare da ci gaba da cin danwaken
Cikin jin dai Jannart tace
Gsky inkuna sunyi kyau
Allah ya saka da alkhairi Mamy
Amin Amin tace tare da kallon Riyyamnsra tace
Yauwa auki kayan kai matasu Bedroom in ta shigo sai ta kimtsasu
Da sauri yace
To
Kana ya fara jidansu
Ita kuwa Mamy cikin kula tace
Nawane sauran kuinka Fahad
Gyara zama Fahad din yayi tare da jinjina kansa yace
Ba ranan Hadi ya kai min 70k ba da fari kuma kin bani 50k
Yanzu saura 30k kenan Hajjajo
Cikin dariya Mamy tace
Aa fa Fahad kuke jin tausayin mutane mana kana nufin dubu dari da hamsin kenan a inki kala ashirin da biyar
Da sauri yace
Allah ko Hajjajo an ma kece kuma nasan ba adawo dasu da wuriba
Kai ta jinjina tare da cewa
Toh ba matsala Ramadan yi mishi transfer
Cikin sauran an shishitan yace to
Kana shi kuma Fahad ya fara gaya mishi ac no dinsa
Haka dai yayi mishi send 30k din kana yaci yayi hanian kafin ya sallamesu ya tafi
Usman ma tare suka fita
Shi kuwa Ramadan anan ya mia sai bacci
Mamy kuwa cikin alamun baccin itama tace
Yauwa Jannart jeki kimtsa kayanki
Sai kizo ki samawa mijinki wani an abu mai saui
Kai ta jinnina kana ta mie
Riyyamnsra na cewa
Yauwa kiyi ki fito my Aunty zan tayaki
To tace kana ta wuce daki
Itama Mamy dakin ta wuce
KARANTA: Nihaad Hausa Novel Complete
0 Comments