A RUBUCE TAKE Hausa Novel
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
A RUBUCE TAKE !!!
(K'addarata)
Free page 01
Babban falo ne,wanda yake malale da marron din carfet mai taushi da kuma saitin kujeru kalar labulen wadanda suka yiwa falon qawanya,a tsare falon yake,ta yadda duban farko kuma kai tsaye ba zaka dauka falon tsohuwa bane,saboda ya wadata da kayan alatu na rayuwa bakin gwargwado.
Daga tsakiyar falon,mamallakiyar falon ce zaune saman carfet din,babbar macace wadda gashinta mai tsaho da kuma santsi ya fara bayyanar da furfura saman sumarta,kana iya hangen hakan sakamakon gocewar daurin dankwalin dake kanta,fara ce sol har yellow takeyi,tsufanta bai boye kyan siffa da take dashi ba,wanda da alamu ta sameshi ne tun daga zamanin quruciya kawo yau,kana kallonta kasan ba cikakkiyar bahaushiya bace,hakanan kammanninta bana fulani bane.
Daga gabanta kuma wata matar ce da suke diban kamanni da ita,saidai nata shekarun gaba daya ba zasu rufa talatin ba,ita dinma fara ce sol kamar matar dake zaune kusa da ita,wanda kana dubansu zakasan cewa 'ya da uwa ne,yaro ne saman cinyarta tana shayar dashi,dattijuwar mahaifiyar tata kuma tana daga kayan dake gaban nasu
"Duk da kayan sunyi kyau humaira,amma gaskiya nafison wadanda sukafi wadan nan tsada,Banason siyawa widad kaya masu sauqin kudi,gwara masu dan tsada da inganci" mai da dubanta halimatu tayi ga kayan tana sake qare musu kallo duk kuwa da cewa itace ta siyosu da hannunta,kayan irinsu ta siyawa yaranta,ta siyama widad din irinsu ne a nata zaton shine qarshen abinda zatayi ta burge ummu,saita maida dubanta ga dattijuwar
"Ummu,yanzu duk kyan wadan nan kayan basuyi miki ba?" Kai ta girgiza
"Basuyimin ba,kuma tunda nace basuyimin ba ai sai a canzo ko?,tunda dai kudina na saka zan siya,ba kudin wani bane" baki halima ta tabe tana sanya hannunta guda daya tana tattara kayan gefe,zuciyarta cike fal da bacin rai,akwai maganganu da yawa a ranta,amma tasan bata isa ta fadesu ba,yanzu yanzu rai zai iya baci indai akan widad ne
"Kin karba min kudin a wajen yaayan?"
"Yace sai ya dawo zai bayar na ajiye miki" sake baci ranta yayi,wannan karon ta gaza boyewa
"Uhmmm,Allah sarki,to Allah yasa suna da rabon saka ankon" kallonta ummu tayi ba tare da tace mata komai ba,idan da sabo ta saba da irin wadan nan dabi'un,ta rasa me yasa suka gaza fahimtarta,tana ganin son rai ne kawai da son kai irin na dan adam.
"Latifa!" Ummu ta waiwaya bayanta inda qofar kitchen dinta yake ta qwala kira,daga ciki aka amsa sannan mamallakiyar sunan ta fito,wankan tarwada ce,mai matsakaicin jiki,a nutse ta qaraso
"Gani ummu"
"Shiga dakina saman pillow akwai purse dita ki daukomin" amsawa tayi da to sannan ta juya.
Saidai bata ko kai ga isa dakin ba,ihu ya karade gidan cikin wata siririyar murya,ihu ne sosai hade da kuka.
Da sauri Latifa ta dakata da tafiyar,sannan ta waiwayo tana duban ummu,itama ummun ita take kallo,fuskarta cike da tsoro
"Ummu kamar muryar widad fa" kai ta jinjina da sauri
"Haka nake shirin fada nima"
"Yo wace idan ba ita ba?,kaf gidan nan waye yake wannan tabarar idan ba ita ba?" Dauke dubanta ummu tayi daga kan.haliman zuwa ga ladifa,wadda tuni ta fara nufar qofa
"Yawwa,dubamin ita don Allah latifa"
"Yanzu kuwa" ta amsata tana ficewa daga falon.
Yaronta halima ta kwantar a gefe sannan ta miqe itama tabi bayan latifan tana qunquni cikin ranta.
Babbar harabar gida ne wadda ke dauke da interlock shimfide a ko ina,duk da irin girman harabar gidan,jikin kowacce katanga data zagaye gidan dake dauke da sassa sassa guda biyar shukoki ne da.flowers da sukabi bangon gidan suka zame masa ado.
Daga bakin daya daga cikin sassan gidan wasu daga cikin ma'aikatan gidan ke tsaye,daga inda kake kana iya hangota,yarinya ce da duka duka ba zata wuce shekara goma zuwa sha daya a duniya ba,farace sol,irin farin nan me cakude da surkin jaa,ma'abociyar yalwatacciyar suma me santsi data sauko har zuwa bayanta ta kuma bazu har saman kafadunta saboda tsallen da take faman yi tana kuma dage maroon din doguwar rigar dake jikinta,manyan idanunta cike da hawaye da suke saukowa saman kumatunta wasu na zirara har gefan dogon hancinta da ya gauraye da majina da hawayen
"Babu komai fa widad,na gaya miki na cire shi tun dazu" wata mace dake tsaye a gafe sanye da riga da zani na atamfa ta fada tana qoqarin riqe yarinyar.
Dai dai lokacin latifa ta qaraso halima na biye da ita
"Meye haka?,me ya faru?" Yayi tambayar tana nufar widad da keta zabga tsalle da kururuwar kuka
"Tana tsaka da barci a falona bayan sun gama guje gujensu,kawai ina kitchen ni da marka na jiyo ihunta,da nazo sai tace wai kyankyaso ne ya shige mata riga,dana duba sai naga ashe qwaro ne dan qarami,na daukeshi aka fitar dashi,amma tace kyankyaso ne,nayi duban duniya ban ganshi ba" tsaki halima taja
"Iskancin banza da wofi ne da zallar tabara data yi mata yawa,wuce mu tafi kafin na tsitstsinka miki mari" ta fada cikin tsawa
"A'ah dakata a duba matan halima" latifa ta fada tana tsugunna wa gaban widad din,ta dage rigar tata da kyau sannan tace
"Kalli ki gani,babu komai a jikinki" cikin tsoro dubi fararen qafafuwanta,ganin ba komai din kamar yadda latifa ta fada,saita gyada kanta,saidai kuma har yanzu batabar kukan da take ba.
A gaba halima ta sanyata tana ta faman sababi m,wannan ya sake tunzura kukan widad din,har suka isa qofar falon ummu.
"lafiya ko?,me akayi mata?" Ummu ta fada idanuwanta da hankalinta gaba daya yana kan widad,tambayar data yi mata sai ya zamana kamar an tunzura ta,cikin sassarfa ta shige falon,tana kuma isa ta fada jikin ummun tana sake sakin kukan.
"Me kuwa akayi mata banda tsoron banza da wofi da take dashi,wallahi ummu sakalcin yarinyar nan ya fara yawa,haba" halimatu ta fada cikin huci tana neman saman kujera ta zauna kamar zata fashe
"Kin taba gani haka kawai mutum yana kuka ne?,ke me yasa kike haka?"ummu ta fada tana jifanta da harara
"Kyankyaso ne ummu yabi ta jikinta,an cireshi amma ta dauka bai fita ba" latifa data shigo ta sake yima ummu bayani tana dosar kitchen.
Waiwayawa ummun tayi tana jifar halimatu da harara
"To kinji,amma shine zakice kukan banza takeyi?,bayan kinsan widad da tsoro,kinsan kuma halittarta ce a haka?"
"Da sakalci wallahi ummu,haba don Allah,ko nabiha da take qanwarta bata wannan abun sai ita shafaffa da mai"
"To anji,saiki rufawa mutane baki hakanan" ummun ta fada tana maida hankalinta ga widad dake kwance saman cinyarta tana share hawaye
"Sannu kinci abinci?" Kai ta girgiza alamun a'ah
"Anty madina ta zuba mana,sai nayi bacci"
"Shikenan,tashi maza kije latifa ta zuba miki,idan miyar tayi miki yaji ta zuba miki wadda takeyi yanzu tunda naji kamar ta soyu,ki biya bandaki ki wanke fuskarki,bazan sake bari kije ko ina cikin gidan nan ki kwanta bama bare irin haka ta sake faruwa" miqewa widad tayi a hankali ta soma barin wajen,sai data shiga dakin ummun ta wanke fuskarta kamar yadda tace matan,ta cire rigar jikinta saboda jiqewa da tayi ta saka wata,riga da zani ne,da qyar ta iya daura zanin saboda rashin iyawa da rashin sabo sannan ta wuce kitchen wajen latifa.
"Halimatu,banason irin wannan dabi'ar nasha gaya miki,idan baku tausayawa widad ba bai kamata ku sata a gaba ba"
"Nifa ba a gaba na sakata ba ummu,sakalcinta yayi yawa ne,fisabilillahi duk cikin gidan nan wace ake nunawa gatan da kike nuna mata?,ai ba ita kadai bace jika a gidan,sannan ma girma takeyi fa,nan da shekara uku tsaf xa'a iya tayar da batun aurenta,niba tsangwamarta nake ba,so nake naga ta gyara" ido ummu tadan zuba mata na wani lokaci kafin ta janye dubanta daga gareta,ta fuskanci ba zata gane ba
"Allah ya kyauta" kawai ta sake cewa,tasa hannu ta janyo purse din da latifa ta ajjiye mata,ta bude ta fidda 'yan dubu dubu ta lissafa ta miqa mata
"Gashi,ki lissafa ki cire kudin da zaa qara na kayan da zaki canzo din,ragowar ki siya ma yaran sauran abinda ya rage" hannu biyu tasa ta karba tayi mata godiya,duk daba haka taso ba,ta rasa me yasa ummun take kasa dai daita widad da sauran jikokinta.
Sanda ta shiga kitchen zamanta tayi wajen latifa bayan ta zuba mata abinci,tana ci suna hira,sai ka rantse da Allah ba ita ta gama sambada ihun ganin kyankyaso ba,tana ta zubawa latifa surutu ita kuma tana biye da ita,wannan yasa akwai shaquwa sosai tsakaninsu,kusan tana daya daga cikin wadanda basuson kukanta cikin gidan.
Sai data cinye tas sannan ta ajema latifa kwanon ta sauka daga kujerar data hau kai ta zauna
"Kizo ki wanke hannunki mana kafin ki fita" latifa ta waiwaya tana ma widad magana,wadda tuni ta kusa qofa tana sude hannu
"Ina zuwa,zan wanke a wajen anty madina,na manta na baro alawar madarata dazu a can,Allah yasa su faruqu basu shanyemin ba" bata ko sake tsaiwa sauraron latifa ba tayi qofa abunta.
Su uku ne yanzun zaune a falon sabanin dazu,anty halimatu,ummu da kuma wani baqon daban.
Matashin saurayine fari ne shima kamar yadda na lura da kusan mafi yawa na launin fatar jama'ar gidan farare ne,yana da sassalkan gashi mai santsi gami da duhu,kamar yadda sumar qabilar larabawa ko buzaye suke da ita,sanye yake da shadda dinkin zamani da ya zauna masa sosai a jikinsa,kanshi babu hula,hannunsa riqe da wayarsa yana dannawa,gefe daya kuma suna hira da ummu da anty halimatu.
Turus widad tayi tana kallonsa,ta tsareshi da idanu duk da babu wanda ya ankara da fitowarta a cikinsu,dubansa take tana jin wani haushi yana cikata,tsaki taja a hankali don kada su jiyota,sai kuma ta tura baki gaba kamar zata saki kuka.
,juyawa tayi kamar zata koma cikin kitchen din,amma kuma saita sauya shawara,saboda tasan indai ta koma din ummu tasan tana can kuma zata kirata ta fito,abinda bata so din kenan,sai ta dawo tana duban bayan kujerar falon,akwai hanya da zata sadata har qofar falon,don haka ta duqa ta fara tafiya a durqushe ta bayan kujerun,gabanta yanata faduwa,fatanta Allah yasa kada ummu ta ganta.
A hankali ummu ta waiwaya zuwa sashen kujerun,motsi take jiyowa,saita sauke idanunta zuwa qasan kujerun,fararen qafafuwan widad ta hanga,dariya taso subuce mata amma saita danne,ba tare da kowa dake wajen ya ankara da abinda ke faruwa ba tace
"Widad!" Idanunta na kan qofar falon,ba zaka zaci ta ganta ba,cak widad ta tsaya tana zare manyan idanuwanta waje,gabanta yana faduwa,tana jin kamar ta juya ta koma,amma kuma idan tace zata koma din asirinta zai tonu
"Widad,ko bakya jina ne?" Ummu ta sake kiranta tana kallon sashen da alamu suka nuna a nan take a tsaye,saddaqarwa tayi,ta tabbatar ummu ta ganta,don haka sai kawai ta miqe tsaye,fuskarta a daure,ta tattare dan qaramin bakinta ta turoshi gaba,sannan ta fara takowa zuwa inda suke.
Dukkansu suka bita da kallo,halimatu ta tabe baki tana dauke kanta,haushin widad din yana sake kamata,ummu kuwa girgiza kai kawai tayi,cikun zuciyarta tana cewa
"Allah ya kyauta aikin quruciya".
Ta bangarenshi kuwa da kallo ya bita,ya kafeta sosai da idanuwansa,irin kallon da sautari abokansa kan masa dariya,su kuma ce sukam basuga abun kallo ga qwaila kamar widad ba,tun tana tsumman goyonta Allah ya jarabceshi da soyayyarta,har yau kwanan gobe kuma babu abinda ya canza a zuciyarsa game da ita,saidai ita din da baiga alamun koda sakewa dashi tattare da ita ba bare akai ga zancan soyayya,soyayyar da yake da yaqinin bata santa bama,batasan kuma mece ce ita ba,shi yake saka ran ta koya daga gareshi,saidai bata sakewa dashi bare ta bashi wannan damar,tako ina bashi da matsala,yasan zaya sameta za'a bashi ita kamar yadda yake muradi,amma kuma babbar matsalar daga gareta ne.
"Bakiga mutane ba ba zaki gaishesu ba?" Ummu ya fada tana hade fuskarta tsam waje daya,duk yadda takai ga gantanta widad da nuna soyayyarta a gareta,amma bata da sassauci wajen tarbiyya.
Kamar wadda aka sheqawa mari haka ta waiwaya gareshi
"Yaya mahfood ina yini?" Tattausan murmushi ya saki yana kallonta,kanta babu dankwali kamar yadda ya santa,bata qaunar daura dankwali sam
"Lafiya lau widadun ummu,ya makaranta?" Bata amsa masa ba,saita juya ga ummu tana bata rai
"Gani ummu" ummun na shirin miqewa tsaye tace
"Bani nake nemanki ba" saita miqe a abunta tana riqe da hijabinta a hannu
"Muje ki gyaramin wardrobe dita kafin ki wuce gida" ummu ta fada tana yin gaba.
Miqewa halimatu tayi ta saba yaronta a kafada tabi bayan ummun tana cewa
"Har yau ita widad din dana koyawa yadda akeyi bata koya din ba kenan?"
"Nidai ba wannan na tambayeki ba,in zakimin kimin,idan kuma fashin baqin naki zakiyi ki barmin kayana,ko intisar tazo sai tayimin" jin ummun ta fara mita saita tsuke bakinta,tabi bayanta kawai din kawai,sai falon ya rage saura su biyu.
*_DOGUWAR TAFIYA CE,WADDA KE QUNSHE DA TARIN DARUSSA,TAFIYA CE MAI DAUKE DA WANI IRIN SALON KISHI,GOGAYYA CE DA FAFATAWA TSAKANIN MABANBANTAN MATSAYI BIGIRE GAMI DA MATAKI NA RAYUWA_*
*_Ta fita zurfin karatu_*
*_Ta fita yawan shekaru_*
*_Ta fita wayo dabara da siyasa_*
*_GOYON KAKA CE_*
*_SAKALTACCIYA_*
*_ME QANANUN SHEKARU K'WARAI_*
*AKWAI TAZARA MAI TARIN YAWA A TSAKANINSU,KWATANKWACIN SAMA DA QASA*
*AMMA DUK DA HAKA TA CITA DA YAQI*
*GARIN YAYA?*
*_Kin karanta HANGEN DALA?,to ba shakka wannan tafiyar ta fishi zafi darussa da kuma ilimi a cikinta(in sha Allah)_*
*_ku taho kawai muje,kuyi jumurin bibiyata,kamar yadda aka saba har kullum,babu gaggawa cikin tafiyata_
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
Free page 02
*MAAB LUXURY HOME*
*_idan kaji gangami akwai labari_*
*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*
Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane
nasan zaku tambaya ina ne nan?
MAAB LUXURY HOME
Kai daga jin sunan ma babu tambaya
____________________________
waiwayowa yayi yana dubanta bayan ficewarsu gaba daya,maficin da ummu ta tashi ta bari ne riqe a hannunta tana tsige adon jiki,fuskarta a dinke tsaf,yakanyi.mamakin yadda take masa,kamar wata qatuwar budurwa,ya rasa dalilin da sam bata son su zauna waje guda ko su hadu,saidai har yanzu zuciyarsa na bashi nutsuwar cewa quruciya ce kawai da rashin sanin ciwon kanta,da zarar ta sake hada hankalinta zata fuskanceshi?
"Amma sai yaushe?,lokaci qara quracewa fa yake" zuciyarsa ta gaya masa,sai ya dan gyada kai
"Soon in sha Allah" ya fada yana bawa kansa qwarin gwiwa,qwarin gwiwar da kusan kullum itace madogararsa
"Widad" ya kira sunanta
"Na'am" ta amsa a cunkushe ba tare data kalleshi ba,murmushi yayi
"To kidan kalleni mana?,ummm,ke da zaki zama matata?,so nake ki saki jiki da yayan naki" manyan fararen idanuwanta ta daga tana kallonsa,wani haushi da kuma tsanarsa suka saukar mata,lallai yaaya mahfood ta tabbata dan iska ne,ita yakewa zancen ta zama matarsa?.
Yadda ta zuba masa fararen idanuwan nata sai yaji dadi cikin ransa,don takan jima bata tsaya ta kalleshi ba,wannan ya bashi qwarin gwiwar janyo ledar daya shigo da ita wadda ke shaqe da kayan kwalliya,kasancewar ya santa da son kayan ado da gayu ya tura gabanta
"Ga kayan kwalliya nan 'yammatan ummu,sai ayita shafawa ko?" Dauke idanunta tayi daga kansa ta mayar kan kayan,saita dalla wa kayan harara,ita zaiwa wayo?,ya dauka bata da hankali kenan,haka kawai,bayan ummu tasha gaya mata ko zama tayi kusa namiji ciki zatayi,shine zai wami bata kayan kwalliya?,to bai isa ba,tana gama wannan tunanin ta miqe abinta ta nufi qofa da saurinta.
"Zo mana widad.....widad"ya fara qwala mata kira,gudun kada latifa ko ummu dake daki su jiyo shi,su kuma sanyata dawowa dole saita fella da gudu ta qarasa ficewa,don ta lura shi kadai ne zaifi mata saurin barin sassan.
Bata tsaya ko ina ba sai sassan anty madina,taja birki tana zabga haki,dai dai lokacin da dukka yara yaran gidan da suke da shekaru irin nata ke zaune a falon anty madina,kaf cikin matan gidan ta fisu qarancin shekaru,tana da faran faran da son mutane,tana yawan jansu a jiki gami da biyewa shirmensu,wannan yasa kafatanin yaran gidan kowa ke sonta,yake kuma son zama a sassanta.
Dago kai tayi tana duban widad,muhassana ce kwance a cinyarta diya ga qanwar mahaifin widad tana mata tsifa
"Lafiyarki widad?,irin wannan cin burki haka?" Guri ta samu kusa da khalisa ta zauna tana maida numfashi,sai kuma ta bata rai, idanuwanta sukayi rau rau suka ciko da qwalla
"Yaya mahfood ne"
"Mahfood kuma?,biyoki yayi?" Kai ta girgiza tana turo baki gaba,ita sam sam ma batason maganarsa,yanzu su mahassana zasu fara tsokanarta
"Wai cemin yayi matarsa" tana fadin maganar qwalla na gangaro mata,qaramin murmushi anty madina ta saki,ta rasa wanne irin rashin haduwar jini ne haka tsakaninsu,duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda mahfood din ke qaunar widad,hakanan kowa yasan yadda take gudunsa,bata qaunar hada inuwa dashi
"To banda abinki mene ne don yace miki matarsa iyi widad?,bakiga su zahira ba aure za'ayi musu?,kuma daga su sai ku?" Kafin anty madina ta kammala bayaninta widad din ta saki kuka harda turje qafafu,baki anty madina ta sake tana kallonta gami da jan salati,yayin da su muhassana suma ke kallonta suna dariya
"Tsaya,bakya sonshi ne shi yayan naku?" Kai ta gyada
"Wallahi ni bana sonsa Allah"
"To ya isa,ki share hawayenki,an gama maganar,ba wanda zai baki shi" dif kukan ya tsaya,ta tashi ta zauna dai dai tana goge qwallarta tana kuma hararar su khalisa kan dariyar da suke mata
"In sha Allahu sai su abba sun baku dauda" dariya sosai anty madina ta tuntsire da ita,duk da quruciyarta wani lokaci idan tayi wani abun kamar babba,dauda shike wankin gidan,na kowanne sashe,daga qauye yazo a gidan aka riqeshi
"Bakinki ya sari danyen kashi" khalisa ta fada tana dariya
"Saidai naki bakin" widad ta fada tana sake harararta,dole anty madina ta shiga fadan ta raba,ta kuma janye musu hankalinsu da wani abu na daban.
Qememe taqi komawa sassan ummun,duk da ummun ta aiko latifa har kusan sau uku amma taqi komawa,zatonta mahfood yana nan bai tafi ba,wayo ummun keso tayi mata don ta dawo,har abbanta yazo ya tafi bata koma din ba,son samunta ma tayi kwananta nan wajen anty madina cikinsu farisa,amma kuma tana tsoron kyankyaso,kada yayi mata irin yadda yayi mata daxun,har sai data fara barci sannan latifa tazo ta tafi da ita bayan ta tasheta ta sakata a gaba.
Tana shiga dakin ummu ta haye gadonta taja bargo ta duqunqune sosai harda cusa kanta cikin pillow,tun tana kasa kunne taji shigowar ummu har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari ummun bata ce komai da ita ba,saidai ta bata ledar kayan kwalliyar tace ta dauketa taje ta adanata,aifa kamar jira take,saita dire cup din da take shan tea dashi ta saki kuka
"Allah ni bana so,banaso ummu" tana turje qafarta a qasa
"Hukumullahu" ummun ta fada a ranta tana zuba mata idanu,wannan abun na widad din kuwa na qare ne?,kullum abu kamar ma sake ci gaba yakeyi?,kafin takai ga sake cewa komai akayi sallama falon,ta dauke kanta daga widad ta maida gareshi taba amsa sallamar.
Babban mutum ne ko ace magidanci,wanda kallo daya zaka masa kasan danta ne daga tsatsonta ya fito,a nutse ya qaraso falon yana kallon widad da fuskarta tayi sharkaf da hawaye
"Ke kuma da baki rabo da rigima me akayi miki?" Ya fadi yana neman wajen zama,baki ummu ta tabe tana girgiza kai
"Don anyi maganar mahfood ne" saita zarce da gaya masa abinda ya faru jiya.
Maida dubansa yayi gareta yana nazartarta na wasu daqiqu,shima kallon quruciyarta yakeyi,yasan ita ke dawainiya da ita,don idan a wani gidanne ko zancan aurar da yayunta da za'a aurar yanzu ba'a fara ba bare ita,to amma haka tsarin yake,a haka kuma dukka suke tafiya
"K'aniyarki" abba ya fada yana tsuke fuska
"Don gidanku mahfood ba babanki bane kike masa irin wannan?,maza tashi ki dauki kayan ki adana su" fuskarta jiqe da hawayen ta miqe ta dauki ledar,sai tayi hanyar fita da ita
"Ina zaki?,nan ne dakinki?" Cikin muryar kuka ta waiwayo
"Anty madina zan kaiwa...."
"Eh itace ke iya jurewa shirmensu ai" ummu ta karba zancan tana qarashewa abba bayani,sai baice komai ba,wannan ya bawa widad damar ficewa.
Tana tafe ita daya tana sharar qwalla,maimakon sassan anty madina,sai tabi siririyar hanyar da zata sadata da parking lot na gidan,tasan can ne babu kowa,don duka samarin gidan masu fita kasuwa kawo yanzu sun fita din,sai su 'yan makarantar da suke shirin komawa ranar litinin,sune daliban da aka yaye daga primary school zasu wuce zuwa qaramar secondry jss one.
Dan bencin da ake ajewa a wajen lokaci lokaci ta haye ta zauna a kai,sai a sannan ta buda ledar tana duba abinda yake ciki,kayan makeup ne sosai irin wadanda takeso,batayi mamaki ba,don uncle mahfood din ya jima da sanin zabinta da kuma duk wani abu da takeso.
Sai data fiddosu tsaf ta qare musu kallo,sai kuma ta tabe baki,motsin da taji daga parking space din ya sanyata fara tattara kayan cikin hanzari,tana gudun ko abba ne ya fito zaya tafi,ta tabbatar idan ya ganta a wajen fada zata sha.
Wanda ta gani a wajen yana niyyar fitowa daga motar tasa ya sanyata sauke ajiyar zuciya,tasan cewa kome zatayi ba kulata zaiyi ba bare ya hanata,don kuwa tsahon tasowarta ta sanshi amma ba zata iya tuna rana daya da magana ta taba shiga tsakaninsu ba.
Kamar yadda ta zata din kuwa,ko a yanzun ma dauke kansa yayi ya soma rufe motarsa sanna ya jefa key din a aljihu ya kuma soma takawa yabar wajen.
Da kallo ta bishi tana tabe baki gami da jifansa da harara,har sai da ya bacewa ganinta sannan ta dauke dubanta daga wajen,a hankali take tattare kayan tana maidawa cikin ledar,qasa qasa take magana ita daya
"Wallahi banaso,bayarwa zanyi,ni ba wani aurensa da zanyi,dan iska kawai" dif maganar tata ta yanke,sai kuma tahau zaro idanu cikin tsoron kada wani ya jita,sai data tabbatar babu motsin kowa sannan ta qarasa kwashe kayanta ta kuma fito.
Isowarta farfajiyar gidan yayi dai dai da budewar gate din gidan,qaramar motar qirar 406 ta danno kai ciki,sai ta dakata daga yunqurin isa sassan anty madinan tabi motar da kallo,sai kuma ta saki murmushi har dimple din dake kwance saman kumatunta hagu da dama ya lotsa,saita cilla da gudu gudu sauri sauri zuw wajen motar,cike da zumudi da kuma murna.
Sanda ta isa daura da motar tuni mamallakiyar motar ta kasheta tana yunqurin fitowa
"Anty dina sannu da zuwa" waiwayawa tayi sashen da widad din take tana niyyar dauko jakarta daga back seat na motar
"Widad rigimammiyar ummu,ya na ganki a gida kuma?" Murmushi tayi tana leqen cikin motar da alama akwai abinda take nema
"Anty secondry zamu tafi fa,muma mun zama manya kin manta?"
"Au anyi haka fa,kice zamu sake samun qarin 'yammata cikin gidan namu....."
"Anty wai ina aysar ne?" Ta tambayeta cikin katsar numfashinta
"Gashi nan a daure" ta fada tana nuna mata shi a kujerar dake kusa da tata cikin baby car seat,zagayawa tayi da hanzari
"Don Allah anty kwantomin shi"
"A'ah widad......ke kanki yaushe ummu ta daina goyaki?, barshi yanzu zan fito na kunceshi" bata rai tayi,wai me yasa kullum suke maidata baya,bayan ita kanta tasan girma take?,to idan ma har yanzu yarinyace ita a wajensu me yasa suke mata zancan uncle mahfood?,dole daga bisani anty dina ta ciro yaron ta miqawa widad shi,sannan suka nufi sassan mahaifiyarta tana ankare da widad din.
"Ke kuma wanne tsautsayin ne ya sanyaki daukar yaronki ki bawa wannan yarinyar?" Cewa momma mahaifiyar anty dina bayan shigarsu babban falon sassan nasu.
Kafin anty dina tace komai widad din ta rigata magana
"Momma Allah na iya fa,gash.i nan ma ni na daukoshi tuyn daga parking space" ta fada tana turo baki,wanda ke sake nuni da zallar quruciyarta,abinda ya sake batawa momma rai,taja tsaki tana miqa hannu gami da yunqurin karbar yaron
"Miqomin shi nan,me kika iya?,yarinyar da ko pant dinta har yanzu batasan ta wanke ba" momma din ta fada tana jifanta da harara,zallar quruciya ya hana widad fahimtar kuma,bugu da qari kuma,akwai wata irin wankakkiyar zuciya da take da ita,ba kasafai ta fiya damuwa da abubuwan da suke faruwa cikin gidan ba,duk da ta soma girma,hankalinta ya fara fahimtar wasu abubuwan
"Allah na fara koya momma"
"Naji,jeki da Allah" ta fada tana sake harararta kamar idanunta zasu fado,sai dauke dubanta daga fuskar momma din tana nufar hanyar kitchen dinta.
Wata tsawa ta kwatsa mata,wadda sai data sanyata ta kusa tuntube da kujerar dake gefanta
"Ina kuma zaki?" Ta fada tana fidda idanu
"Wajen Aafiya zani"
"Kiyi mata me?" Ledar hannunta ta daga tana nuna mata
"Kayan kwalliya na kawo mata ta zaba"
"Uhnnnn,salon kije kisa ta bata aikin dana sakata,to zauna nan har sai ta fito,kada ki shiga ku hadu ayimin shirme" narkewa tayi tana duban momma din,da alama tanason ta roqeta ne ta barta ta shiga,tana kuma tsoron tsawarta,don ba abinda ta tsana sama da tsawa da kuma fada.
"Ki barta mana momma,idan yaso tana shiga saita fito kada ta zauna" dina ke fada qasa qasa,saboda tausayi da widad ta bata,waiwayowa momma tayi ta kalleta tana dan juya aysar a hannu kamar zata masa rawa
"Wannan yarinyar?,tsab zasu iya barnatar min da guri,kuma baka da damar yi maya fada balle duka,tunda tana da uwa a bakin murhu"
"Kiyi haquri momma,yanzu zata fito"
"Naji,amma indai ta shiga din duk barnar da tayimin ke zaki biya"
"Na yarda" sai.anty dina din ta daga kai ta dubeta
"Shiga kikai mata kizo na aikeki sassan anty madina"
"Tohm" ta amsa da zumudinta tana shigewa,deena ta bita da kallo,bata fiya yin fushi ba don mutum ya bata mata ko ya tsangwameta,bata sani ba ko tsabar quruciya ce?,ko sai nan gaba zata fahimta komai idan hankali ya gameta?
A RUBUCE TAKE!!!
(k'addara ta)
Page 03
Koda ta shigan bata zauna ba kamar yadda anty deena tace tayi sauri,ta sameta tana yankawa momma albasa,sai zabga gumi taje gami da hawaye,duk da cewa kitchen din kitchen ne irin na zamani,da ya wadatu da iska da manyan windows,dukka a qoqarin momman na koya mata girki,kada ta tashi kamar widad,wadda bata cas bare as a gidan,abinda ya damu wasu cikin gidan,yake kuma basu haushi sosai,suna gajun gatan da ummu ke nunawa widad din yayi yawan da ya kamata ta rageshi ta sanwa wasu cikin jikokinta.
Budewa Aafiya kayan tayi tana cewa
"Zabi duk abinda kikeso a ciki" kanta ta leqa cikin ledar tana cewa
"Ummm,yar gatan ummu,inda nice nace mata ta siyon kayan nan qi zatayi,sai tace naje na tambayi yayuna maza"
"Yaaya mahfood ne nima ya kawomin" daga kai tayi ta kalli widad,dududu itama Aafiyan ba zata wuce sa'ar widad din ba,saidai ta danfi widad din girman jiki kadan
"To me yasa ba zakiyi amfani dasu ba?" Tura baki tayi tana tsuke fuska
"Banaso,ni bana son sa,banason ana min zancensa,ki dauka anty deena zata aikeni" ido ta fidda
"Yaushe tazo?"
"Yanzu" saita ajjiye wuqar tana zura hannu a ledar,ta zabi abinda takeso tana cewa
"Aiko na godde wlh,bari nayi sauri na gamawa momma aikinta na fito" tana dan lila ledar ta fice abinta ba tare data tsaya sauraronta ba,ta samu anty deena a falo,ta bata leda tace ta kaiwa anty madinan,ta amsa ta fice da dan guntun gudunta.
Ta dan samu yaran sassa sassan gidan da dan dama a sashen anty madinan,kasancewarta mai fara'a haba haba dasu da jan kowa a jiki,kowa nata ne,hakanan kowa yana jin dadin xama dasu,bayan sa'anninta masu kamar shekarunta data samu,harda yayyensu da ake dab da bikinsu,kuma suna tare da anty madinan,da alama akwai abinda take koya musu,sauran sa'annin nata suna daga gefe sun buda tasu chamber din.
Bayan ta miqa mata ledar sai ta kalleta
"To wannan dayar kuma fa?"
"Kayan kwalliya ne na kawowa su rafi'ah"
"A ina kika samu kayan kwalliya masu yawa haka?" Basma cikin 'yammatan dake shirin amarcewa ta fada tana dubanta bayan ta dago kanta daga danna wayar da takeyi,kanta tsaye ba kwana kwana ko damuwa tace
"Yaa mahfood ne ya kawomin"
"Shine kuma zaki rabar?" Anty madina ta tambayeta tana bada hankalinta sosai a kanta,kamar zata saki kuka tace
"Banaso anty wallahi,ni banaso"
"Barta don Allah ta rabar,miqomin na zabi nawa" basman ta sake fadi tana miqa hannu,ba wani damuwa tattare da ita ta miqa mata ledar ta qara gaba tana cewa
"Anty basma idan kun gama su na'ima zasu zaba" anty madina data bita da kallo tana kallon zallar quruciya ta saki ajiyar zuciya
"Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi,baaba mahfood dai kam to"
"Uhmmm,wai laifin widad kuke gani?,ni nafi ganin laifin baaba mahfood din ai,kamar maye,yarinya tun tana 'yar tamilo kake faman mata hidima,jikinka da aljihunka basu huta ba,ta fara wayo ta nuna baka so basai ka haqura ba,dui gidan ita dayace 'ya?,ko ita kadai ce jika?" Kai anty madina ta girgiza
"A'ah fa basma,har yanzu widad akwai quruciya tattare da ita,ai ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare"
"Uhmmm,anty madina,yarinyar nan fa daurin gindi ta samu,Allah kuwa,kuma sai yaushe?,bayan mu kadai ne muka haura zuwa SS,mu dinma gashi SS one kawai aure ya tashi,bare su da jikinsu da alama mai saurin girma ne,Allah yasa su gama JS ma"
"Allah ya shiga lamarin" anty madina ta amsa mata
"To Ameen"basman ta fada tana maida kanta ciki ledar,don tuni marwa ummee da nujood suka gama zabar nasu,anty madina nata musu tsiyan girma ya fadi,raqumi ya shanye ruwan 'yan tsaki,su da za'a kawo musu akwati me zasuyi da toshin qanwarsu.
Widad kam bata sake bi takan kayan ba,a nan suka gama gantalewa,duka ta rabar,dan abinda yayi saura ya gangarar dashi anan wajen anty madina,tayi komawarta sassansu.
Sanda ta koma tuni abbanta ya tafi,sai ummu kawai
"Ina kikakai kayan?" Ta tambayeta tana tallafe da kuncinta tana dubanta,maimakon ta amsa saita narke fuska,ta kuma shige cikin kujera abinta ta lafe taba mus mus da baki,juyin duniya ta gaya mata inda takai kayan taqi,dole ga qyaleta,tasan indai cikin gidanne zata ji.
Tun tana zaman likimo har bacci yayi awon gaba da ita,bata tashi ba sai kusan azahar,sanda latifa ta kammala abincin rana,ta kuma tattaro panties da undies din widad din zata wanke.
Sai datayi sallar azahar kamar yadda ummu ta horar da ita,ta karba abinci,saita zagaya baya inda latifan ke mata wankin,ta zauna tana ci suna hira da latifan...
***********
Kamar kowacce safiya a ranakun makaranta,school bus din gidan ke tattara kan duka yaran gidan zuwa makaranta,wanda kusan yawancinsu makaranta daya suke zuwa,wadanda kuma suke mabanbantan makarantu sai ta miqa su sannan ta dawo gidan zuwa lokuttan tashinsu.
Daga can sassan ummu widad ce zaune saman kujera,sanye da sabbin uniform dinta kamar yadda komai nata a ranar yake sabo a matsayinta na dalibar da ta shiga secondry school a ranar,ummu na zaune daga qasan carfet hannunta riqe da plate tana miqawa widad din plantain din ciki
"Maza maza kici kafin 'yan azalzalar nan su biyo sawunki,idan ba haka nayi miki ba haka zaki tafi,yanzun latifa zata kawo miki lunch box dinki" fuska a nake a kuma sakalce take duban ummu
"Wallahi na qoshi ummu,ya isa haka"
"A'ah,qarashe wannan dai" ta fada cikin nuna kulawa,hakanan ba don taso ba ta daga cup din hannunta dake cike da tea tana shanye ragowar na ciki,dai dai lokacin basma ta shigo,sanye take da kayan gida,kasancewar ita din a yanzun sai daina zuwa,saboda kusantowar bikinsu,bawai don sun gama bane,haka al'adar gidan take,alhajin salim mai fata tsoho mai ran qarfe,kaka kuma uba ga ahalin gidan wannan sbine tsarin da ya dora dukka yara da jikokinsa,mutane da yawa 'yan bani na iya da kuma 'yan gaza gani kance
'Gidan me fata ai da wuri suke aurar da yaransu,da sun ga mai kudi sai su cire yarinya daga makaranta,basa ko gamawa,don sunga suna samun masu danshi ne,suma masu kudin da shegen kwadayi,suna ganin kyawawan mata sai su rude' duk da wannan jita jita na dawo musu kunne amma sunyi banza da zantukan mutane,abu daya tsoho kuma dattijon ya sani shine,mutuncin mace dakin mijinta,hakanan duk wadda tayi katari da samun mijin dake da ra'ayin karatu tana ci gaba da karatunta ne cikin dakin mijinta.
"Goyon kaaka,sai a fito ko?,kin tsaida mutane kina bata musu lokaci" ta fadi tana harararta,ganin yadda ummu ta zauna dafa'an tana bata abinci kamar wata yarinyar goye,waiwayowa ummun tayi tana danqara mata harara
"Ke kuma da bake za'ayi tafiyar wa ya sakoki a maganar?"
"Yo fisabilillahi ummu saita makarar da kanta fa makarar da wasu?" Tayi maganar tana miqa hannu gami da fusgar sabuwar school bag din widad din dake ajjiye kusa da ita,kafin su sake cewa komai.muryar dattijon ta ratso falon
"To....to,ya akayi?" Ya fada yana qarasowa a hankali zuwa cikin falon,kafin ya samu waje ya zauna yana dubansu.
Russunawa basma tayi ta gaidashi,dai dai lokacin latifa ta qaraso dauke da lunch box din widad din
"Gashi an gama" ta fadi tana ajewa gabanta
"Ko muje motar na rakaki dashi" latifan ta sake fada tana kuma dauke lunch box din daga gabanta,tabe baki basma tayi sannan tace
"Tabdi!,gigin primary,kina shiga dashi ansan burbushin primary ce,meye hadinki da wani lunch box tsabar sangarta?,Allah latifa ke kike sake taya ummu ana sakalta yarinyar nan" ta qarashe maganar tana hararar widad din
"Wato kedai anyi babbar banza ko?" Alhj salim ya fada yana duban basma
"Allah alhaji bata sanin ta fara girma"
"Wuce ku tafi ga iliya can yana horn" ya fada yana daga musu hannu,sai a sannan widad ta sauko daga kan kujerar,ta maida takalmanta suka fice ummu tana muta addu'ar dawowa lafiya.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tabbatar da fitarsu,ta maida dubanta ga alhj salim din
"Yaran nan sam basu da zurfin hankali,ta yaya zan banzatar da widad ta gaza samun kulawata?,yarinyar da tun tana watanni a duniya mahaifiyarta ta tafi ta barta?,idan ban kula da ita ba waye zai kula da ita?" Murmushi dattijon yayi yana qarashe janye ragowar carbin da ya rage a hannunsa sannan ya ajjiyeshi gefe
"Iya tasu fahimtar kenan,amma duk da haka saboda gudun ci gaba da samun sabani da yadda suke jin haushinta ganin kamar kinfi sonta,kiyi qoqarin boyewa da rage wasu abubuwan"
Dan sunkui da kanta ummu tayi
"In sha Allah" ta amsa masa cike da ladabi,duk da bata da tabbacin yiwuwar hakan.
"Kunun za'a kawo maka ko dumame?"
"A fara kawomin kunun da qosai tukunna" ya amsa mata yana gyara zamanshi sosai saman kujerar,ta yunqura ta miqe zuwa kitchen da kanta,duk da tsufanta hakan bai hanata yi masa tasa hidimar da kanta ba,koda zata bawa latifa tata hidimar tayi mata,amma ta alhajin ita keyi.
Awannin da tayi a makaranta a ranarta gane banbamcin secondry school da primary,sosai makarantar tayi mata dadi,lokacin tashinsu da yayi tun a cikin motar suke hayaniya,labarin sabon aji da kuma sabuwar makaranta
"Don Allah kuyi mana shuru,kun cika mana kunne ha'an" ramziyya wadda take cousin a wajen widad ta fada,ita din gaba take dasu,don a qalla ta basu shekara kusan biyu,ita dinma wannan shekarar ta shiga js three,kuma akwai yiwuwar shekara mai zuwa a karba kudin aurenta kamar 'yan uwanta,dole suka rage hayaniyar,saita maida hankalinta ga iliya driver
"Ko ka wuce damu gidan baaba mahmud?,muga lefen najwa tunda yau babu islamiyya"
"To shikenan,babu laifi" ya amsa mata.
Kicin kicin widad tayi,ko kusa ko alama bata qaunar zuwan gidan nasu,koda hutun makaranta akayi kuwa,gidan ba gurin zuwanta bane,zata iya cewa banda mahaifinta bata da kowa a cikinsa,sai yayanta wanda.ba kasafai kake samunsa cikin gidan ba,yawancin lokutta yana makaranta,duk da yadda mahaifinta ke nacin ta dinga zuwa din amma ummu ta hana,idan ta kama saidai ta wuni ta dawo.
Tun daga harabar gidan matan gidan suka fara jiyi hayaniyarsu,babu wadda ta motsa,don kowacce dan data haifa kadai shine nata,har suka qaraso cikin ainihin babban falon gidan
"A'ah,kada dai kucemin daga makaranta kuke?" Ta tambayesu tana tafa hannuwa cike da yaqe da kuma riya,saboda mai gidan na nan,daga inda yake din kuma zai iya jiyo komai
"Ga alama kuwa umma" najwa dake fitowa daga dakinsu ta fada tana dariya gami da qoqarin daura dankwalinta
"Lefe mukazo gani" widad ta fada tana dan dariya,ganin yau yau umman ta sake mata fuska,ramziyya ta harareta
"Shegen son kallon kayan lefe,caraf ta bada amsa"
"Da gaskiyarta,gaba su za'a kawowa ai" umman ta amsa bayan ta qwalawa me aikinta kira kan ta zubo abinci, murmushi widad tayi maganar tana bata mamaki da dariya,yanzun wataran itama sai a ciko akwatuna da kayan lefe ace nata ne?.
A nan suka ci abincin rana suka kuma baje suka kalli kaya son ransu,alhaji mahmud ya fito a shiryensa,suka hau gaisheshi ya amsa musu cikin fara'a da jin dadin ganin 'ya'yan 'yan uwansa,ya bisu da kyautar dari bibbiyu sababbi,duka harda widad din bai banbantata da kowa ba a cikinsu,sannan ya fice yabar gidan.
"Ni kunzo a dai dai ma,ku taimakamin na fidda kayan da zan kai dinki" ramziyya ce ta dinga tayata zabin,widad na hade mata su waje daya
"Basuyi yawa ba wadan nan kayan anty najwa?, duka zaki kai dinkin?" Inji widad dake zaune daga gefe
"Saina ma qara wasu,kin manta haka amare keyin dinki da yawa?" Kai ta jinjina kawai tana ci gaba da kallonsu,bayan sun gama najwa tace
"Ki kwana anan widad,saiki rakani nakai dinkin,gobe saina maidaki gida".
Cikin murna da zumudi ta amsa da to,ko ba komai zata yita kallon kayan lefen dake burgeta sin ranta,don haka ta baiwa su Aafiya jakarta suka wuce mata gida da ita.
Sanda ummu taji shigowarsu sai tayita sanya idanu taji shigowar widad din amma shuru,har ta gaza daurewa ta aika latifa sassan su marwa ko sassan anty madina ta dubo mata widad din me ta tsaya yi bata shigo taci abinci ta sake wanka ta canza kaya ba.
Da latifa ta dawo mata da batun sun barta gidan baaba mahmud shuru tayi,cikin ranta duka babu dadi,don bataso ko kadan widad din tayi nisa da ita,to amma tasan mawuyacine itama ta yarda ta kwana din,ta tabbatar da wahala bata nema a kawota gida ba.
Sanin hali yafi sanin kama inji hausawa,don kuwa tun bayan sallar magariba bayan sun dawo daga wajen dinkin ta lafe a kujerar falon gidan tana raba idanu,ta cika tayi fam,gida kawai takeson komawa,har umma ta fahimci haka,itama hakan ya mata dadi,don duk randa yarinyar ta kwana a gidan ko yaya ne sai sunga wani abu na bacin rai daga mai gidan dangane da yadda yake nuna mata kulawa
"Rabu da ita umma,kin ganta fa ta fara girma,Allah har qirga dangi naga ta fara,amma.har yanxu bata girma da kwana a bayan ummu ba,yau dai a gidan nan zaki kwana,idan bikin nawa yazo ma ba zaki iya kwana ba kenan?" Itadai batace komai ba har zuwa sanda baaba mahmud ya dawo,tare suka zauna da ita suna cin abinci amma sam taqi sakewa,qarfe takwas na dare ta fara musu hawaye,dole ya tashi driver ya maidata gida
"Maidata,kada ta hanamu barcin dare" cewar abban nata.
Karfe tara saura suka isa gidan,sanda motarsu ta tsaya daidai sanda motar uncle haisam abban su marwa qani ga mahaifinta ta tsaya
"Aah,wa nake gani haka da daren nan kamar widad?" A ladabce drivern ya amsa shi
"Itace,taqi zama ne abba yace a dawo da ita"
"Ikon Allah,to muje ciki" ya fada yana kulle motarsa,sukayi sallama da drivern yabi widad din zuwa sassan iyayensa.
Ummun da kuma alhaji suna falo a zaune,sai a sannan yake cin abincin dare sunadan taba fira sama sama da ummun.
Bataji sallamar widad ba sai fadowarta jikinta data ji,tana shirin dagata sallamar uncle hisham ta biyo baya
"Tare kuke ne?" Ummu ta jefa masa tambayar,yana rage tsahonsa gami da neman wajen zama yace
"A'ah,can na ganta drivern gidan yaaya mahmud ya sauketa"
"Yar nema,shine kike biyo dare kika gudo?,ba zaki qyalemin mata dai ta huta ba kenan?"cewar alhaji yana tsokanarta,daga ummu tayi tana turo baki
"Bakaji dadin gani na ba?,bayan ko cigiyata ma bakayi ba..... shikenan" tayi maganar tana miqewa daga jikin ummu tana wucewa daki
"Ahaf......me kika sani banda takura?". Bata ansa ba har ta isa daki ta tura ta shige abunta,dariya suka saka gaba daya, alhaji ya girgiza kai
"Quruciya me dadi" ya fada a hankali,sai ya maida dubansa ga hisham yana tattara hankalinsa zuwa gareshi.
*
HUGUMA
A RUBUCE TAKE
(K'addara ta)
Page 04
Alhaji salim musayyib mai fata shine cikakken sunan,mazaunin maiduguri da wanda aka haifa a can,ya taso ya girma ya kuma yi gwagwarmayar karatunsa dukka acan din,nau'in jinsin nan da mutane ke kira da suna SHUWA_ARAB,saboda asalin iyayensu da kuma kakanninsu dukka ba'a maiduguri aka haifesu ba,ba kuma anan sukayi rayuwarsu ba,rayuwar da sukayi a maidugurin duka duka 'yar taqaitacciya ce,sanadin kasuwanci,asalin tushensu sun fito ne daga qasar mali zuwa yemen,kuma har yanzu danginsa da tushensa suna can gaba daya ko nace mafi yawa daga cikinsu,iyali ga mahaifinsa musayyib suke ta yado a nan,da kuma nashi ahalin shima daya tara.
Matan aurensa biyu dukka 'yan asalin qasarsa wadanda suka hada masa tarin zuri'a da kuma yara masu yawa,dansa na farko da matarsa ta fari wadda ta kasance balarabiyar qasar yemen shine mahmud,wanda yake mahaifi ne ga widad data kasance ruwa biyu,balarabiyar mali kuma bafulatanar usul daga katsina ta gefen mahaifiya,wannan shi ya taru ya bata wani irin sassanyan kyau daya banbanta da kyawun dukka cousin dinta da kuma sauran 'yan uwanta,domin ita daya mahaifiyarta ta haifa ta barta a gidan,sai tarin 'yan uba da kuma cousins da take dasu.
Yanayi na rayuwa da kuma kasuwanci ya maido alhaji salim qasar kano da zama,ya fara tara iyalinsa shima,bayan ya aurar da mahmud arziqinsa ya qara ninkuwa fiye dana da,wanann ya siya manya manyan filaye ya hadesu waje guda,ya kuma yanki wani sashe na gidan ya fara ginin matsugunnin da zai zauna da matansa da kuma yaransa,bayan ya kammala suna gab da tarewa matarsa ta biyu ta rasu,sai mahaifiyar mahmud ce kawai Allah ya qaddara mata zama a gidan.
Mahmud ne kawai ke rayuwa a wajen gidan,girman gidan ya sanya duk yaronsa daya tashi yin aure,za'a fitar masa da tsarin ginin da zai dace da gidan a gina masa ya tare a ciki,wannan yasa sannu a hankali gidan ya zama babban family house dake dauke da sassa sassa guda biyar,kuma kowanne sashe cike yake da albarkar zuri'a wadata da kuma kwanciyar hankali.
Widad ta kasance ta musamman a wajen ummu,saboda ummun ta bude idanu ta gani a matsayin uwa kuma mahaifiya a wajenta,don itace ta raineta tun tana tsumman goyonta har kawo yanzu da shekarunta suke goma sha daya da watanni a duniya.
Soyayyar da ummun itama kewa widad din ta banbamta data kowa,saboda itama tana jinta da matsayi biyu ne a wajenta,d'iya kuma jika,ta manta da raino sanda ta amshi widad da nufin rainonta,don a sannan ta aurar da autarta ma anty halima tuni,kasancewar su din basa zurfafawa karatun boko,kina gama primary ma kika samu miji to tabbas alhaji salim zai bada aurenki ne, matuqar ya yarda da addinin mutum da kuma mutuncinsa,ruwan miji ya barki kici gaba,ruwansa yace a'ah.
Ko kadan rashin uwa bai wani taba widad ba,saboda ta samu dukka kulawa da 'ya ke samu ga mahaifiyarta daga wajen ummu.
Mahfood d'a ne ga baaba maisara,wanda suke 'ya'yan wa da 'ya'yan qani da mahaifin widad,tun kafin ta kawo haka yake nuna yana da interest a kanta,amma ko daya widad din taqi sake masa balle ya samu fuskar da ko hira ta zauna tayi dashi,saboda ita din wata irin mutum ce,tana da wahalar sabo,hakanan idan kanason ganin kazar kazar dinta da hirarta to cikin gidansu ne,musamman sassan ummu ko na anty madina,indai akace maka baqon guri ne zaka tsammaci cikakkiyar magana ma bata iya ta ba.
Abu na biyu tana da masifar tsoron maza,saboda kullum hudubar ummu shine,idan ta sake ta yarda ko hannunta namiji ya kama zatayi ciki,idan kuma ta samu ciki mutuwa zatayi,wannan yasa sam sam bata yarda ko inuwa su hada,bama shi ba,dukka samarin gidan da suke a matsayin yayye a wajenta haka dabi'ar ta take.
_wannan kenan_
*Bayan shekara uku*
Tun daga daren juma'ar da ya kama gobe sallah gaba daya yanayin gari ya canza daga yanayin azumi zuwa yanayin daren sallah,ko ta ina al'ummar musulmi sai hada hada ake,tituna zuwa layuka,gidajen kitso qunshi zuwa shagunan masu dinki ko ina cike yake danqam da jama'a kamar rana.
Haka ce ta kasance gidan alhaji salim musayyib,babban gidan dake dauke da family masu yawa,a dabi'ar gidan babu tsawwalawa,koda salla ce kowanne sashe yana yin kalar girkin da mace ko matan sashen suka tsara yi,saboda kowanne part akwai store da kuma kitchen din su tare da me aikinsu,saidai idan an gama ranar sallah dukka suna zubawa abincin mai dan dama su aike sashen surukarsu hajiya ummu,duk da ita dinma ba zama take ba, takanyi abinci har kusan kala biyu,sabida karbar baquncin jikokinta dama surukanta matan 'ya'yanta maza guda biyar da Allah ya bata,su da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wajen diyarta halimatu,hakanan su kansu jikokin dake cikin gidan suma kusan a nan suke zuwa su karba nata,sukance yafi dadi.
Karanta: Namijin Duniya Book 2 Complete
0 Comments