Akidata Hausa Novel Book 2

Akidata Hausa Novel Book 2


Akidata Hausa Novel Book 2

Akidata Page 46_47

shiru Yusuf yayi yana kallon Widad, yayin da yaji gaba É—aya hantar cikinsa ta kaÉ—a jin abunda Widad É—in ta faÉ—a, ta kalleshi tace

"Ya naji kayi shiru ne? Akwai matsala ne?"
girgiza mata kai yayi yace
"A'a babu komai" Widad tace

"Shikenan, ga Abinci can, kaci seka sha magungunanka ka kwanta"

Kasa motsawa yayi daga inda yake, balle ya aikata É—aya daga cikin abunda tace, sake kallonsa tayi tace "wai ko dai jikin ne?"

Girgiza mata kai yayi yace "A'a jikina ai na warke"

" to ai gani nai duk ka wani koma so silent, shiyasa nayi zaton ko jikin ne, ka tashi zan kwanta "

Yusuf ya miƙe, ya bata guri ta gyara shimfiɗar ta ta kwanta, yayin da ya koma gefe yayi jugum kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa.

A ƙoƙarinsa na kaucewa zargi daga Widad, ya miƙe ya ɗakko Abincin da niyyar ya fara ci, Amma gaba ɗaya ya ya kasa, tunani burjik a zuciyar sa, ga labarin da Saleh ya gaya masa, ga kuma itama abunda ta faɗa masa yanzu, ashe dai da daru a gaba, ko wane irin hukunci zata yi masa idan ta gano shi jami'in sirrine? Gashi zuciyarsa ta riga ta gama kamuwa da tsananin ƙaunar Widad, yana matuƙar jin sonta a ransa, a yanzu haka dama yana ɗar ɗar, saboda yasan bashi da tabbacin idan suka koma gida Widad ta cigaba da zama da Auren sa, dukda a yanzu yana ƙoƙarinya jarraba Widad yaga ko tana son shi, a ƙaddara ma ta yadda da Auren, su cigaba da zama tare, waye yasan Aure suka yi, Saleh ne kawai sheda ta yaya zasu fuskanci mutane suyi musu bayanin wannan rikita rikita?.

   Nan da nan wani irin gumi ya shiga tsasttsafowa Yusuf, lallai akwai Æ™ura a gaba, kasa cin Abincin yayi, dama gashi bakinsa babu É—anÉ—ano saboda zazzaÉ“i, dan haka ya ajiye Abincin a gefe ya nemi guri ya kwanta, sedai kamar yadda beyi tsammani ba, bacci ya Æ™auracewa idonsa se tunani, yanzu meye mafita? Ta ina ze tunkari Widad yayi mata bayanin waye shi, dan kamata yayi ace shi ya gaya mata ba wani ba.

Haka nan jiki a sanyaye ya cigaba da tunani, ya daɗe a zaune ba tare da ya kwanta ba, yana ta saƙawa yana warwarewa.

Muryar Widad yaji tace "Tunanin Meka ke hakane wai?"

Da sauri ya dawo daga tunanin da yake yace "Babu komai karki damu"

"Ko kana tunanin gidane, da Ummanka?"

Murmushin dole ya ƙaƙalo yace "A'a"

"Nasani dole zakayi tunanin gida, nasan baka jin daɗin zaman garin nan, ko baka faɗa ba zaman garin nan ba daɗi, Amma ni ta wani ɓangaren rahama ne a gare ni, bana fargaba ko tashin hankali saboda maƙiyana, ina matuƙar jin daɗin karamcin da mutanen gidan nan suke min, dukda yadda zaman garin ke bani wahala, amma karamcin su da goyon bayanka na ƙara bani ƙwarin gwiwa, tabbas duk wani motsi da zanyi ina tunanin Daddy, ina tunanin wani hali yake ciki, me yake yi? Nasan ina ransa, sedai ina masa Addu'a zuwa lokacin da Allah ze kawo ƙarshen wannan abun in koma gida, kaima kayi haƙuri nasan duk nice silar shigar ka wannan halin"

Ta ƙarasa maganar cikin damuwa. Yusuf yace "bana dana sanin kasancewa ta dake anan, saboda karamcin mahaifinki da yadda da yayi dani beci ace na bar 'yarsa ɗaya tilo ta shiga wani hali in kasa temaka mata ba, sedai dole inyi kewar Ummana, bata da kowa seni, mahaifina ya rasu, gata marainiya ni kaɗai ne a kusa da ita muke rayuwar mu tare, Allah kaɗai yasan irin damuwar da take ciki, dan tunda na tashi ban taɓa nesa da ita ba, nasan tana cikin damuwa "

Cikin tausayawa Widad tace
"Allah sarki, dole zukatan makusantan mu su shiga damuwa, har gara kai wataƙila bayan mamanka akwai wanda zasu damu da halin da kake ciki na ɓatan da kayi, nikam daga Daddy na se Bulama nasan sukaɗai zasu damu, duk wanda yake tare dani, yana tare dani ne dan wannan dukiyar, nasan da babu ita da bazasu nunamin so ba, kuma nasan zagina suke a bayan idona, shiyasa nake wa mutane wani kallo na daban, a da na zata duk mutane miyagu ne, kuma talakawa zasu iya komai akan kuɗi basu da kirki, sedai wani darasi da nayi shine, shi rashin kirki ba'a talaka ne ko me kuɗi ba, a mutum ne kawai, na samu misali akanka da kuma mutanen ƙauyen nan, basu san koni wace ba, amma suna ta kyautatamin"

Yusuf yace "hakane kam, naga kin sake dasu sosai kamar bake ba, kamar ba kece me wannan AƘIDAR ta ƙin mutane ba, me yiwa mutane kallon miyagu ba"

"Hmm ina da dalilin yin hakan, ka kwanta dare ya fara yi, kaga baka da lafiya akwai buƙatar ka samu isashen bacci"

Yusuf yace "Hakane, kema ki kwanta my queen"

'ba zaka dena faÉ—ar wannan sunan bako? "

"Dama bakya son sunan ne? "

"ban sani ba, ai kasan nace maka bana so"

Yusuf yace "ni gaskiya daÉ—in sunan nake ji, My Queen, My life, I love you so much My dearest Queen"

Tsaki tayi, ta canza position É—in da take kwance ta toshe kunne ta, wai danma karta cigaba da jin meze ce"

Yusuf yayi murmushi, ya kwanta sedai fa bacci yaƙi yuwuwa, saboda saƙawa da warwarewa da yayi tayi, akan ya sanar da Widad gaskiya waye shi, kokuma karya gaya mata?

"Barrister Hafiz, kuyi duba a cikin lamarin nan da kyau, ku tsananta tunani kafin yanke hukunci, akwai gwagwaɓar riba da zaku samu idan akayi wannan harƙallar daku, zaku samu alheri fiye da tunaninku, zaku samu arziƙin da baku samu a harkar aiki bama"

Barrister Hafiz ya gyara zama yace "Abunda nake so ku fahimta anan shine, wannan aikin fa hatsari ne dashi, mu sa hannu a siyar da kadarorin Daula, karkuyi mamaki akwai masu bibiyar al'amuran dukiyarsa bamu sani ba, idan abu yazo ya tonu sunanmu ze É“aci, kuma mu rasa aikin mu, sannan mu fuskanci fushin hukuma"

Alhaji Musa yace "Barrister, sha'anin ƙasar nan tamu yanzu kowa mafita yake nemawa kansa, da kayi ƙaramin laifi a kaika prison a banza, gara kayi gagarumi wanda zaka samu mafita a al'amuranka, kuɗi zaka samu manya ba ƙanana ba, wanda baku taɓa zaton samu ba, kuma a yanzu waye yasan inda Daula yake? Idan abubuwan nan suka samu zaku iya barin ƙasar ma gaba ɗaya, dan haka ku san dabarun da zakuyi, kuyi mana wata takarda da zata nuna yayi holan wasu daga kadarorinsa, a bisa farashi me sauƙi ".

Ya kice gumi Barrister Hafiz yayi yace" Yallaɓai akwai buƙatar a ɗan bamu lokaci, zamuyi shawara tukuna "

"Shikenan, amma bama buƙatar a ɓata dogon lokaci, muna sauraren ku"

"Shikenan yallaɓai, sekun jimu"

Hajiya Sarah ce zaune gefen Bulama, yana shan tea yana karanta jarida, tace

"Yallaɓai, dan Allah ka tausayawa Hajiya Halima, kasa baki a sakar mata ɗanta, gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, hankalin ta gaba ɗaya baya jikinta saboda damuwa"

Bulama ya nisa yace "banƙi ta taki ba, amma baki fini son Halima ba, da ina da yadda zanyi da zanyi ƙoƙari in saka a fitar da shi, amma wannan case ɗin ba ƙarami bane, idan na matsa sunana ze iya ɓaci"

"Hakane amma ya kamata kayi wani abu, koda ta ɓangaren kwantar mata da hankali ne, Allah kaɗai yasan halin da take ciki, ba ƙaramin abu bane uwa ta iya jure ɗanta a wani yanayi, idan ka bincika babu lallai ko Abincin kirki tana iya ci"

"Eh to banƙi zancen ki ba, amma Halima mace ce me taurin kai da rashin haƙuri, maimakon tayi haƙuri a bi komai a hankali, amma se azalzala ta take, irin wannan lamarin a hankali ake binsa, amma ita ta fiye garaje, case ɗin nan ba ƙaramin case bane ba, karki manta Daula ne fa aka nema aka rasa, kuma shine yake kula dashi, gaba ɗaya ana saurarar hukuma aji me zasu ce, Amma insha Allah ze fita "

Hajiya Sarah tace " shikenan, Allah yasa amma tana cikin damuwa sosai, Allah ya fitar dashi, dan yaron kirki ne sosai "

Bacci be É—auki Yusuf ba se wajen Asuba, dan haka da Asuba kasa tashi yayi, Widad ce ta fara tashi taje tayi alwala, ta dawo amma be tashi ba.

Hannu tasa tana ɗan dukan ƙafarsa tace " ka tashi ka makara fa yau "

A hankali Yusuf ya motsa yace
"Subhanallah, kuma shine zaki dinga dukana haka da ƙarfi, sekin jimin ciwo?"

"wannan É—an dukan ne zan ji maka ciwon?"

"Eh mana duba gurin kiga, har yayi ja fa, kin zage ƙarfinki kina ta faman dukana"

Dagewa tayi ta ƙara masa wani dukan tace "wannan kuma se kace na karya ka ko?"

Yusuf yace "kai, tabbas idan na riƙe ki se na rama, zan rama wannan dukan da kika yi min" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje domin yin alwala yazo yayi sallar Asuba.

Da gari ya ƙara haske, Gwaggo ta aiko musu da koko da ƙosai, Widad ta zauna ta dinga tsintar ƙosan ta naci, tace bata shan kokon, shikam Yusuf yaji daɗin yadda ta fara sakewa, yanzu tana iya cin Abincin su, dukda a yanzun ma bakomai take iya ciba, amma tana iya cin wasu abubuwan, yanzu wanke wanke ma, ita take abunta ta wanke banɗaki, wataran kuma Hindu ce ke mata.

Yusuf ya kalleta yace "meyasa ba zaki haÉ—a da kokon ba?"

"nifa ba son wannan kokon nake ba, wataran ji nake kamar zanyi amai idan na sha"

Yusuf yace "Allah yasa Baba Hari ta jiki, Kisha faɗa da baƙar magana"

Dariya Widad tayi tace "Aikuwa dai, ai gaba É—aya matar nan comedy ce, komai ta gani se tayi magana, wani abun ina sane nake yi, amma bata ganewa taita faÉ—a"

Yusuf yace "Hmm Allah ya shiryeki to, aini ban san haka kika iya neman magana ba, ganin cewar a baya ko maganar ma bakya son yi, idan anga fara'arki to da magenki ne roux ko kuma Daddy"

"Allah sarki, harka tunamin da sister roux É—ina, nasan tana missing É—ina, maybe ma yanzu sun barta ta mutu saboda yunwa, nasan bame kulamin da ita, nima haushina suke ji balle magena"

Yusuf yace "Eyya Sorry, Insha Allah bata mutu ba zamu koma ki tarar da ita tana nan"

"Hmm is very hard gaskiya, am missing Home Yoseef, ina tunanin dabbobina gaba É—aya nasan suna missing É—ina"

"wai me yasa kikafi son dabbobinki akan mutane, kina ƙaunar dabbobi sosai"

Widad tayi ajiyar zuciya tace "labarin yana da tsayi sosai, Amma tabbas dabbobi sun fiyemin mutane, except in some circumstances, duk abu indai dabba ta shaÆ™u da kai, ba zata yadda a haÉ—a kai da ita a cutar da kai ba, amma dan adam fa yana iya manta dukkan alkhairinka a hada kai dashi a cuceka, shiyasa na zabi rayuwata a cikin dabbobi”

Yusuf yace “hakane maganarki amma sedai ba duka aka zama daya ba, Amma na Allah  ai basa karewa sannan ba yadda zaai ace mutum yayi rayuwa ba mutane"

Widad tace "kai ka ga haka, nikam nayi, kuma yafi kwanciyar hankali"

Yusuf yace "Ai ba ƙaramin mamaki nayi ba, ranar dana ga kina sukuwa akan doki"

Widad tayi murmushi tace "i miss that Moment, ko a England ina wasan polo, ina son tseren dokuna sosai"

Yusuf yai murmushi yace "ko tsoro ba kya ji"

Daga nan  be kuma cewa komai ba ya maida kai yayi shiru yana da  cin abincin a hankali, widad ta kalleshi tace kamar
" akwai Magana abakinka da kake so ka gayamin,naga jiya tun jiya kana ta yawan kallona"

Yusuf yace aini kullum cikin kallonki nake, babu wani abu da nake son gayamiki

"shikenan tunda kace haka,amma gara inda akwai ka gaggauta gayamin, bazan takuraka seka gayamun ba amma nasan akwai abunda yake damunka”

“kinfara samun ido kenan?”

“ba ido nake samka ba, yanayinka ne ya nuna min, amma shikenan ba ina kokarin matsa maka bane, ko son sanin me kake ciki ba, ni bari in tashi in fita in dan sha iska”

Yususf ya kalleta yace “bana son kifita ki barni,ina jin daÉ—in hirar nan da muke”

Yamutsa fuska tayi tace  "ni kuma na gaji da zaman dakin, dan haka waje zan fita”

Yusuf yace “shikenan tunda haka kike so,your wish is mine my queen”

“ka ji dashi dai, inka gama karka manta da shan maganinka" daga nan tai waje abunta

Alhaji Haruna ne shida Alhaji Munir suke cigaba da tattaunawa akan al amuransu.

Alhaji Munir yace "‘anya baka ganin ayi kokari a sakarwa matar nan danta, da yasan inda Daula yake iya azabar da aka gana masa ya isa ya fadi inda yake, amma tunda be faÉ—a ba to tabbas besan inda yake ba, gashi ana batun tafiya kotu, karfa matar nan ta tona mana asiri”

Alhaji Haruna yace “ka kwantar da hankalin ka, hakan ma duk shirine, idan sun tafi kotu, za a dauke hankalin mutane daga wasu abubuwan, da zarar hankali ya dauke ya karkata can, mukuma semu cigaba da barnar mu, kafin a farga mun kwashi abunda muka kwasa koda wancan abubuwan basu samu ba”

“banÆ™i ta taka ba, amma ka gane wani abu guda daya, mudinga yi muna ankarewa da abunda ze biyo baya, yanzun idan aka shiga kotun nan slide mistake ze iya sakawa asrinmu ya tonu, sannan maganar  da muke har yanzu fa babu wanda yasan inda yaran nan suka shiga, tunda suka gudu har yanzu shiru babu labarinsu, babu labarin inda suka tafi, kuma har yanzu basu dawo garin nan ba, gaba daya a tsorace nake, kuma yakamta ace zuwa yanzu shi wannan yaran da muka sa su sace su me adda yake kowa?, yakamata ace basa raye bekamata abarsu suci bulus ba,suma fa hatsarine as garemu”

Alhaji Haruna yayi murmushi yace “Alhaji Munir ikon Allah, kaikam wasu lokutan akwaika da tsoro, munefa masu kasar nan, ko yaya muka ga wani abu na shirin kawo mana tangarda zamuyi maganinsa, mukeda hukumar tsaro kudi da masu mulki, kai a tunnainka har akwai wani wanda ze kawo mana tarnaki ne? ka sha kuruminka, komai a tsare yake, shekara nawa mukayi ana tafiyar nan, ba tare da an samu mtsala ba? Karka manta Alhaji Bukar ma fa namune, kadai mubi komai sannu”

Alhaji Munir yace “ duk nasan da wanan, amma abunda nake so ka sani shine,wannan mahaukaciyar matar fa zata iya komai idan taji za a kaimata danta prison,bafa zata zuba mana ido tana kallo danta ya tafi prison ba”

“karka damu za a san yadda za ayi da ita”

“shikenan, amma nifa kwanan nan na fuskanci wasu halaye da Musa yake yi, sam na kasa gane kansa fa”

“ba kai kadai ba, nima kallonsa kawai nake, kar ace na fiye matsawa ne ko neman rigima shiyasa kawai nake kyleshi”

Alhaji Munir yace “Banda shi mahaukaci ne, wai takara ze fito, ubanwa ze zabeshi bayan bakin tabon da Daula ya goga masa, ai mutane ba mahaukata bane”

Alhaji Haruna yace “kyaleshi ai ya zata mutane basu da hamnkali, a da alokacin da yayi siyasar ma ai farin jinin Daula ne yasa aka zabeshi, ba wai dann ya cancanta ba, mu zuba masa ido ya cigaba da haukansa tunda bashi da hnakali”

“aikam babu alamar hnakli, gara yaje mutane su cinye É—an abunda ya tara É—in ai, se sun talauta shi sannan yazo ya fadi zaben, mutum se taurin kan tsiya, baya É—aukar shawara sam, indai 'yan siysa ne zasu ziga shine, su cinye komai idan ya fadi su gudu su barshi”

Alhaji Musa yace “:ai shiyasa ban damu da in bashi shawara ba gara yaje suma suci rabon su, daga baya yayi hankali ai”

‘shikenan, ni bari in wuce se munyi waya”

“shikenan,semunyi waya”

Daga na sukayi sallama.

Ganin wucewar Hajiya Halima ne yasa Ramlah bin bayanta zuwa dakinta, tana zuwa tace “Mummylafiya kuwa?”

Zama hajiya Halima tayi tace “ina fa lafiya, wai kotu za akai Anwar kotu fa Ranlah”

“mummy wane irin kotu kuma? Ba za bada belin nas ba ?”

“sun hana , sunce ba zasu bada belinsa ba, kuma wadan nan banzayen sunki suyimin komai akai, sun barni se wahala nake nikadai, nikadai na haifeshi nikadai nake wahala ta, dan san abunda ze biyo baya kenan da ban barin Anwar yaje yana wannan wahalar ba, idan yaso ba zagi ba ko tsinewa ce duniiya sumun baze dameni ba,amma ina kallo akaimin da na prison baze yuwu ba, niba abun  in tona asiri ba, nima zan kwana a ciki, da sedai ayi duk wadda za ayi”

Ramla tace ” mummy kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki, idan kika fallasa ba iya asirinsu ba hatta namu muma ze tonu ne, dan haka kiyi hakuri mubi a hankali”

“wani irin mubi a hankali komai yana lalacewa, in zuba ido akaimin É—ana prison sam baze yuwu ba wallahi, ana shiga kotu nasan prion ne zasuce zasu kaimin shi”

“babu me kaishi prison, kidena damun kanki, Anwar ze fito”

Haka taita kwantar mata da hankali.

Tunda widad ta fice tsakar gida bata sake komawa ɗaki ba, tana maƙale da Gwaggo da Hindu tana koyo aikin gida, yayinda gefe guda sunayi suna faɗa da Hari, yayinda Hanne keta jifanta da bakaken maganganu, wani abun Widad ta gane wani ba zata gane ba, dan wata hussar ina tayi tsauri bata ganewa sam, ita dai tafi maida hankali akan ta koyi aikin,Gwaggo bata hantarar ta idan tayi ba daidai ba seta gyara mata cikin ruwan sanyi.

Saleh ne ya shigo gidan, ya tarar Widad zatayi tatar gasara, tanata kokowa da abun tatar Gwaggo tana gyara mata, gashi ta maida duk hankalinta so take ta koya, gwanin ban dariya da tausayi.

Saleh yace "Ina kwana ranki ya dade?”
Dagowa widad tayi ta kalleshi cikin basarwa tace “lafiya kalau”

Saleh yace  “aiki kike ne?’

Gwaggo tace “aikam aiki muke tayi”

”madallah sannu da kokari Gwaggo, ya me jiki kuma?”

Gwaggo tace “jiki da sauki Alhamdilillah”

“mashaallah, bari inshiga in duba shi”

Widad na jinsu tayi masa banza taki kula shi.

Da sallama Saleh ya shiga dakinsu Widad, ya tarar da Yusuf a zaune yayi shiru yayi zurfi a duniyar tunani, Yusuf ya dago ya amsa.

Saleh yace “ya dai ko jikin ne?”

Yusuf yace “ jiki ai naji sauki Alhamdilillah”

“madallah ai haka ake fata, ai can naga mutuniyar taka a tsakar gida tana ta kokawar yin tatar gasara, se barna take”

Yusuf yayi dariya yace “danma baka ga yadda take tankaÉ—e ba, bakaga asarar garin da tayiwa Gwaggo ba, ai Gwaggo ba karamin mutunci take man aba, se fatan Allah ya sakamata da alkairi”

Saleh yace “ai abunma da takaici ace yarinya kamar wanna bata iya aikin gida ba,abun da kunya ai”

“yakamata kiyi mata uzuri da an koya mata da zata iya ai”

Saleh yace “waye ze koya mata, ta dinga hantarar mutum tana masa wulakanci”

Yusu yace “adinga kara mana matata ce fa Saleh”

Sale yai murmushi yace “masu mata manya,to Allah ya bada hakuri, na manta ne, Allah yasa in an tashi komawa a tafiwa da Daula jika”

Shiru Yusuf yayi bece komai ba yana tunani, Saleh yace “lafiya kuwa?”

Yusuf yace “Saleh akwai matsala ina cikn damuwa sosai, har yanzu bata san waye niba, bana son taji a wani gurin tayimin kallon makaryaci, yanzu ban san ta in zan faraba bansa n ya zata kalli abunba, zata iyayimin bore ina tsoron darunta”

Saleh yace “hakane amma ai kai namijine, kuma zuwa yanzu duk ta rage wasu abubuwan ai, ba lallai ta maka wulakanci tunda yanzu ba wanda ta sani se kai”

“Saleh anya ba ka manta wacece Widad ba? Jiya ta gama jadaddamin bata yafiya ga wanda yayi mata karya ko yaci amanarta”

Saleh yace  "Æ™warai na san wacece ita, yadda ta gaya maka hakane bata yafiya ga wanda yayi mata Æ™arya ko yaci amanarta, duk yadda suke da shi kuwa, amma ai kai akwai alaÆ™a me matuÆ™ar Æ™arfi a tsakaninku, zata iya É—aga maka Æ™afa kuma kamata yayi ace kai da kanka ka gaya mata, karka bari taji a waje, idan kuwa ka kuskura ta samu labari a gurin wani akwai matsala, dan bata Æ™i ka tafi prison ba kaima, tace an haÉ—a baki da kai za'a cuce ta, abun da nake ganin dai yafi shine ka sanar da ita kawai, hakan zefi "

"tabbas nasan bata yafiya ga wanda yaci amanarta, nikam Saleh me kayi mata wanda yasa ta kasa duba alkhairin ka se laifukanka? "

Saleh yayi murmushi yace " labari ne me tsawo Yusuf, kuma gaya maka labarin tamkar ƙara wani laifin ne akan laifi, amma ka bari idan tayi niyya zata iya gaya maka komai, nidai shawarata da kai, tun kuna nan ka gayamata waye kai"

Yusuf yaja ajiyar zuciya yace " Inajin tsoro Saleh, harga Allah ni fa ina son Widad ne tsakani da Allah, yanzu idan na gaya mata zata iya ƙina, a yanzu mu tana ƙasa tana dabo ne, dan itafa bata yadda akwai so ba, dan haka bani da tabbacin tana sona, kuma inzo in gaya mata wannan magana, abun ze lalace gaba ɗaya ne fa"

Saleh yace "haba namijin duniya, ai kai kana da jarumrtar da ka cancanci a sara maka, haka nan duka butulcin me butulci dole ya sarawa namijin ƙoƙarin da kayi akan Widad, ni kaina na fuskanci sonta kake, amma dole zata ɗaga maka ƙafa dan baka cancanci ta wulaƙanta ka ba, be cancanci ta manta da alkhairin da kayi maka ba, dukda yarinyar wata irin muguwar bahaguwa ce, amma kayi ƙoƙari kafin ku bar garin nan tasan abunda ake ciki "

Yusuf ya dafe kai yace " Subhanallah, ban san ta ina zan fara ba Saleh, ina tsoron abunda ze biyo baya, ni kome zata yi baze dameni ba, ni fargaba ta karta rabu dani ko tayi min wata mummunar fahimta "

" Yusuf kenan, da alama wannan ne karonka na farko na shiga soyayya ko?"

Yusuf ya girgiza kai yace " Na taɓa soyayya Saleh, har na sawa kaina bazan sake soyayya ba, katsam Widad ta shigo cikin rayuwata ba tare da na warke daga wancan ciwon dake zuciyata ba, kuma har nake jin cewa a yanzu inawa Widad son da banyi wa waccan yarinyar ba"

Saleh yace "lallai kana cikin Jarrabawa Yusuf, ina maka fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya fitar da kai"

Sallamar Widad ce a É—akin ta katsesu, suka amsa mata gaba É—aya, fuskarta duk bushashiyar gasara, kanta babu É—ankwali goshinta duk gumi.

Ta kalli Saleh ha haÉ—e rai tace "Excuse us please"

Saleh yace "to" ya tashi ya fita ya bar É—akin.

Ta kalli Yusuf tace "ka zauna kana ta surutu, baka san lokacin salla yayi bane, har an fara aikowa ana tuna maka, kaje kaja salla"

Yusuf yace  "aini yanzu gaba É—aya kunyar mutanen nake ji".

Widad tace "me kayi musu na kunya?"

Yusuf yace "tunda kika rungume ni a gabansu, indai suka ganni se inga suna wani sunkuyar da kai"

Ɗan guntun tsaki Widad tayi tace "to dana rungumeka a gaban su is it an abomination? Saɓo nayi kome?"

"to ai su basu saba ganin irin haka ba, is against their norms"

Widad tace "to su suka sani, ni wanka zanje inyi, kaje kayi sallar"

Yusuf yace "to bari inje in dawo in rama dukan da kika yi min da Asuba"

"ina nan ina jiranka kuwa, kasan dai na fika ƙarfi yanzu, kai sauro ya zuƙe maka ƙarfi".

"dole kice haka mana, tunda na baki jinina, dole kiyi ƙarfi ai"

Ta kalle shi tace "ji wata magana, jinin naka ma da bashi da kyau, duk ba wasu sinadarai a cikinsa, shine duk ka dameni da ka bani jini, to zan biya ka abunka"

Yusuf yayi dariya yace "kamar gaske"
Yai waje, yana fita ta kintsa ta É—au bokiti ta tafi taje tayi wanka.

Tana zaune tana shafa man zaitun a jikinta Yusuf ya dawo, ta bawa ƙofa baya, farar fatarta se ƙyalli take da ɗaukar ido, ga baƙin gashinta ya kwanta sosai a bayan ta, ƙasansa ya jiƙe da ruwan wanka, ba taji dawowar Yusuf ba se jinsa tayi zaune a kusa da ita, numfashinsa na sauka a jikinta.

Da sauri ta É—ago ta kalle shi tace "meye haka? Ya zaka zo ba ko sallama, ka zauna kana shinshinani"

Seda tasa Yusuf yayi dariyar dabe shirya yinta ba, yace "niba shinshinaki nake ba, se kace wani kare"

"to baga numfashinka nan inaji a jikina ba"

Beyi magana ba, ya kalli hannun ta data tsiyayo zaitun, ya zura nasa hannun akan nata, zaitun É—in wani duk ya zube, ya shiga shafa mata a jikinta.

Ji tayi tsaigar jikinta na tashi, É—an yamutse fuska tayi tace "Yoseef bana so, ka bari in shafa da kaina"

"Ni kuma ina so, ki bari in shafa miki"

Tsaki tayi ta ɗan ɗaga murya tace "nace maka bana so" tai maganar tana ƙoƙarin miƙewa, Amma Yusuf ya riƙeta ya hanata tashi, a hankali yace "yi haƙuri Widad, magana nake so muyi" yai maganar yana sauke numfashi.

Littafin kuÉ—i ne, kuyi magana ta wannan lambar domin siyan littafin
Nagode

Ummee Musa: 48_49

HaÉ—e rai tayi tace "dan za muyi magana shine zaka dinga yimin wannan abun haka, ni bana so gaskiya karka sake yimin"

Maimakon yayi magana Shiru yayi ya sake ƙanƙameta sosai a jikinsa, ya kwantar da kansa a jikinta, ita kuwa mutsu mustu kawai take, so take taga ta ƙwace daga jikinsa, amma abu ya gagara, ya riƙeta sosai ga ƙarfinsu ba ɗaya ba.

A hasale Widad tace "Wai dan Allah Yoseef meye hakane?, ka cikani towel É—in jikina ze kwance fa? Nace maka bana so ka cikani dan Allah, wallahi gaba É—aya ka canza hali, kwanan nan sekai tayi min wasu abubuwa wanda bana so, kuma kana sane"

A hankali ya cika ta, ya kwanta akan katifar yayi shiru tare da lumshe idonsa.

Se kuma ta juya tana kallonsa tace "meye kuma?" ba tare da ya buÉ—e idonsa ba ya girgiza mata kai.

"to me zaka gayamin?"

"bakomai" ya bata amsa

"wani irin bakomai bayan kace magana zamuyi?"

Gabansa ne ya faɗi, yaga be kyautu yayi mata wannan zancen a wannan gaɓar ba data ɗau zafi, dan haka ya buɗe idonsa ya ɗan tsare ta da ido yace dama ba wata magana bace, ina son in sake gayamiki Ina sonki Widad "

Ha É—e rai tayi tace " kaga tasarmin daga kan katifa ta, tunda ba zaka dena wannan shirmen ba, kuma daga yau in ka san wannan shiritar zaka gayamin, karka sake cewa zakayi magana dani na gaya maka, dan bazan saurareka ba"

Yusuf yace "Maganar tawace shiririta? Queen ba shirita bace i mean it, kalmar so ba abun wasa bane ko imagination ba, please my Queen ki yarda ina sonki mana"

Banza tayi masa, ta ɗakko kayanta tana ƙoƙarin sakawa, ya juya mata baya don ta sa kayanta.
tayi ƙasa da muryarta cikin ƙunƙuni tace 'kaji da shi dai, kai ta mun wasu abubuwa amma idan zansa kaya seka wani juya, wai kai gaka na Allah, inma baka juya ba niba abunda ya dameni sa ka yana zanyi'

Bece mata komai ba se dai murmushi da yayi, se data gama sa kayan, ta yunƙura zata miƙe ya sake riƙeta, a fusace tayi niyyar yi masa rashin mutunci, amma ya rungumota ta kasa cewa komai jin ya haɗe bakin su.

Gaba ɗaya Yusuf yafi ƙarfinta, ta kasa gane kansa kwata kwata, kwanan nan se wasu ɗabi'u yake mata wanda bata gane kansu, tana ji tana gani seda yayi me isarsa sannan ya cika ta, ba zata iya ƙwace kanta ba.

Yana cikata bata kuma kallonsa ba, ba tace komai ba rai a matuƙar ɓace tayi waje, kallo ɗaya zaka yiwa fuskar ta kasan a fusace take, ta fita tsakar gida rana ta take, kowa yana ɗaki ta fita ta samu guri a ƙasan bishiya tayi zamanta.

Hakanan Yusuf ya dinga jin be kyauta ba abunda yayi, amma ya zeyi shima bayin kansa bane, mutum ne shima kuma me cikakkiyar lafiya, shi kansa yanzu ya fara É—ar É—ar na zama da Widad a guri É—aya, komai ze iya faruwa.

Barrister Khalil kam tunda yakoma gida yake tunanin hirar da sukayi da Nurat game da mahaifinta, tabbas mahaifin Nurat ba karamin hatsabibi bane ,ze iya aikata komai muddin burinsa ze cika ,amma yayi mamakin yadda Nurat tace masa da saka hannunsa a sace Daula da akayi,abun da mamaki matuka, nan ya shiga nazarin ta ina yakamata yayi wani abu? Amm muddin ya kuskura Alhaji Musa yasan yana wani yunkuri,ko kuma ya gane ya san wani abu akan abunda yake aiktawa,to tabbas ba abunda ze hanashi daukar mataki akansa,dan bashi da Imani sam.

Barrister Hafiz ma tunda ya koma gida yake tunanin batun da aka bijiro masa da shi akan dukiyar Daula,tabbas kudi abun sone,amma meze biyo baya idan suka amince akayi wann aika aika? Idan sukayi aikin nan tabbas zasu samu kudi,amma hatsarin dake cikin hakan shine abun dubawa, watakila idan shi nya amince ba lallai sauran lawyoyin su yadd ba,amm tabbas yana son kudi shima.

Ya yanke shawarar zefara tuntubarsu daya bayan daya yaji opinion din sauran akan lamarin abunda suka yanke shikenan.
  Ya tashi ya dau mukullin motarsa ya fice.

Anwar kuwa gaba daya yayi baki,ya rame saboda zaman gurin nan babu sauki sam, ga sauro ga rahsin kula, ga azabar wahala da ake gana musu akan lallai se sun fadi inda Daula yake, amsar sa dai dayace be san inda yake ba.

Yana zaune a inda suke ajiye yayi shiru yana tunani,s hi babban abunda yake damunsa shine waye ya sace Daula? Wanda ya sace shin yana iya kula dashi?maganinsa ma ko ana kula dashi a bashi oho? Yayi zurfi a duniyar tunani yaji an kira sunansa, a hankali ya daga kai, dan sandan yace

“ka taso kana da bako”

Anwar ya taso ya taho a hankali yana jan kafa,yabiyo bayan dan sandan.

wanda aka nuna masan akace shine me nemansa sam be sanshi ba, dan ko ganinsa be taɓayi ba.

Mutumin ya kalli Anwar yace “kaine Anwar?”

Anwarv yace “Eh nine”

Mutumin ya kalli Anwar yace “ naji ance ranar sha biyar ga wata za a kaiku kotu ko?”

Anwar ya jinjina kai yacec “ eh hakane”

Dukda ban gabatar maka da kaina ba baka san koni waye ba,nima turoni akayi gurinka,kuma ancemin babu bukatar seka san waye ya turoni, yanzua abunda nake so nbda kai shine ina son ka gayamin tsakani da Allah meka sani game da batan Alhaji Nasir”

Anwar ya gaya masa iya abunda ya sani,Mutumin yace  "shikenan karka damu ka kwantar da hankalinka,insha Allah komai zezo da sauki”

Anwar yace  “shikenan nagode sosai”

Mutumin yace “sannan kuma, bana bukatar kowa yasan nazo gurinka ciki harda mahaifiyarka’

Anwar yace “shikenan,Insha Allah babu meji”

Daga nana sukayi sallama mutumin yatafi.

Widad na zaune a gindin bishiya, tana tunanin abunda ya shiga tsakaninta da Yusuf, tai shiru sosai tana tunani, tama rasa me yakamata tayi, haushi zataji kome?, Ganin Widad zaune ita kaÉ—ai a gindin bishiya yasa Hindu tazo ta Zauna a gurin Widad, tace "Amarya me kike anan ke ka É—ai haka?"

"ina shan iska ne kawai" Widad ta bata amsa

Hindu tace "tunda ba abunda kike, É—an koyamin turancin mana"

Murmushi Widad tayi tace "to ta ina zamu fara, bansan a inda kika tsaya a turancin ba"

Hindu tace "ni dai kota ina ne mu fara"

Nan Widad ta shiga koya Mata daga ƙananan abubuwa wanda zata iya riƙewa.

Yusuf ya fito ze tafi Sallar la'asar, ya ya kalli su Widad yace  "karatu ake ne?"

Widad bata amsa ba, Hindu ce tace "eh  wallahi turanci ake koyamin"

Yusuf yace "Masha Allah, Allah ya temaka"

"Ameen" Hindu ta amsa banda Widad data haÉ—e rai.

Daya dawo ma a gurin bishiyar ya tarar da ita, tana cin Abinci.

Yusuf ya Æ™araso ya zauna a kusa da ita yace  "Shine kike cin Abincin babu ko gayyata? Bari inzo muci tare, kin san cin Abinci tsakanin ma'aurata yana Æ™ara danÆ™on soyayya, nikuma ina son Soyayyarmu ta wuce É—anÆ™o ta zama kamar Æ™arfe"

Banza tayi masa taƙi kula shi.

Ya wanke hannu yazo yasa hannu suna cin Abincin, amma Widad taƙi ce masa komai.

Se yanzu Yusuf ya fuskanci fushi take dashi.

Yusuf yayi ƙasa da muryarsa yace "My Queen me nayi miki ne? Se magana nake am kin basar dani, bana jin daɗin hakan fa"

Ƙara haɗe rai tayi, ba tare da tace masa komai ba.

Yusuf yace "Abunda  nayi miki a É—aki ne yasa kike fushi dani ni ko?"

Cire hannunta tayi daga Abincin, taje ta wanko hannunta ta dawo tai zamanta, shiru yayi yana sake binta da kallo.

Hanne ce ta fito, tana ganin Yusuf ta wangale baki tace  "Sannu"

Jiki a sanyaye Yusuf yace "Yawwa Sannunki Hannatu"

Ba ƙaramin daɗi Hanne taji ba jin Yusuf ya kira sunata da Hannatu.

Ta ƙara wani rausayar da kai tana murmushi, ta ƙaraso inda yake zaune kusa da Widad a kan tabarma, tace "bari in ɗauke kwanon, naga kamar ka gama cin Abincin"

Bece mata komai ba, taje ta É—auke kwanon ta kai gurin wanke wanke, ta kawo masa ruwa a buta tace "ga wannan ka wanke hannu"

Yusuf yace "God bless you, Nagode sosai"

Ta jinjina masa kai tana murmushi, Widad ko kallon inda suke ba tayi ba, ta cigaba da kaɗa ƙafarta.

Tana jin yadda Hanne keta wata kwarkwasa, Hindu  dake banÉ—aki ji take kamar ta fito ta shaÆ™e Hanne, ta wani É“angaren kuma tana ganin baiken Widad, data zuba mata ido ta Æ™yaleta.

Yusuf ya tashi ya tafi É—akin su, Hindu na fitowa daga banÉ—aki a fusace  tace  "Hanne gaskiya abunda kike bakya kyautawa, ya zaki dinga shigewa mijin mace a gabanta, dan kawai kinga tana É—aga miki Æ™afa, haba Hanne dan Allah ki dimga tunani mana"

Hanne tace "ba zanyi tunanin ba É—in, ina ruwanki dani? Tunda ita ba zata iya kula dashi ba ai shikenan, mace ba abunda ta iya se girman kai, sam bata da tarbiyya, bata san darajar miji ba"

Widad ta miƙe zata koma ɗaki, sedai babu zato Hanne taji Widad ta shaƙeta da rigar jikin ta, seda idanunta suka yo waje dan azaba, cikin zare ido da ɗaga murya Widad tace

"Am tired, ban taɓa ɗagawa wani mahaluki ƙafar dana ɗaga miki ba, ina ƙyaleki ne saboda Karamcin iyayenki a gare ni, kin san wacece ni? Babu ruwana da alaƙar dake tsakaninki da Yoseef, amma karki sake sakani a irin wannan haukan naki, banda ƙaddara ko a mafarki aka ce ni Widad zan zauna a wannan ƙasƙantaccen gurin zance ƙaryane, saboda kawai ina zaune a cikin wannan jar ƙasar shine zaki dinga gayamin baƙaƙen maganganu? Kin san wace ni, idan kin san wace Widad ko hanya muka haɗa sekin kauce, banda dalilin ƙaddara babu abunda ze haɗanj da daƙiƙiyar baƙauyiya kamarki, hanyar dana sa ƙafata na wuce ma baki isa ki biyo ta ba"

Hanne se kakari takeyi, Su Hari sukazo da gudu amma suka kasa Æ™watar Hanne a hannun Widad, fitowar Yusuf ne yayi daidai da shigowar Saleh, da sauri Yusuf ya Æ™arasa inda dramar ke faruwa, idanun  Widad sunyi jawur, fuskarta sharkaf hawaye tana masifa.

Yusuf ya ƙarasa yasa hannu ya cire hannun Widad daga wuyan Hanne, Hanne ta shiƙi iskar 'yanci, ta koma gefe tana ta haki tana zare ido, kamar an karɓeta daga hannun zaki.

Saleh yace "Wallahi da ta kasheki ta kashe banza, dan babu wanda ya isa ya ɗaukarr miki mataki, kin san wacece kuwa? Kin san' yar waye ita? Ko dan kawai kin ganta a cikin gidan nan a zaune, ina lura da yadda kike mata wasu abubuwan tana ƙyaleki, tunda kika ga nima tana mun abunda taga dama ina ƙyaleta to tabbas kin san ba a banza ba, ƙaddara ce ta kawota zama daku, amma ke a gidan su ko me goge mata takalmi baza'a ɗauke ki ba"

Gwaggo tana jin duk dramar da'ake yi, amma tai shiru a É—aki bata ko fito tsakar gidan ba, saboda tasan abunda ke faruwa, tasan yadda Hanne ne ke wuce gona da iri a wasu lokutan.

Shikan sa Yusuf yasan ba ƙaramin ɗaga ƙafa Widad kewa Hanne ba, a yadda Widad keda izza bata ɗauka raini, amma take sharewa idan ta mata wani abun, lallai haƙurinta ne ya ƙare.

Suka shiga É—aki, Widad se kuka take jikinta na tsuma, ga gumi data haÉ—a.

Yusuf ya shiga share mata hawayen fuskarta  tare da faÉ—in "is ok, kiyi haÆ™uri nasan kina haÆ™uri, Amma ki Æ™ara insha Allah mun kusa mu koma gida"

Kamar wadda aka mintsina, ta miÆ™e daga jikinsa a fusace tace  "dalla ma ni Æ™yaleni, ba kaine kake mata dariya ba, yasa ta rainani takemin wani kallo na daban ba, harni wannan baÆ™auyiyar yarinyar zata kalla ta dinga zagina? Tunda kana mata dariya dole ta Kalleni ta dinga cewa ban iya kula da miji ba se ita, ai seka Aure ta tazo ta kula da kai, wallahi ta kuma yimin abunda bemin ba, sena É—au mataki mafi muni a kanta, zan nuna mata wacece Widad "

From no where Yusuf yaji wani farinciki yana ratsa shi, Widad ta fara kishinsa kenan? Murmushi yayi yace

" Ohh yasalam, shikenan tabbas nayi laifi, dukda badan ina mata murmushi ba, da tabbas ba zata rainamin 'ya ƙwalisar mata ta ba, amma ayi haƙuri zan kiyaye insha Allah, na dena mata dariya amma ayi min afuwa".

"Karma ka dena kai tayi mata, wallahi na dena ƙyaleta"

"Ayi haƙuri dai, kar ayi aika aika, ki dena kuka share hawayen ki maza, mijinki baze sake kallonta yayi mata dariya ba"

Shiru tayi masa ta cigaba da ajiyar zuciya. Yusuf a ransa yace  'insha Allah ko baki son meye so ba zaki sanshi a kaina, kuma ina fatan ki furta da bakinki kina son Yusuf, muje zuwa dai'

Shikam Saleh a tsakar gida ya cigaba da zazzaga musu masifa, akan abubuwan da Hanne ke yiwa Widad, sun sha mamaki jin yace ko za'a tattara kaf ƙauyen da kadarorin da mutanen ƙauyen suka mallaka ba zasu sai gidan mahaifin Widad ɗaya wanda take rayuwa a ciki ba.

Hari ta zaro ido tace  "Wudas É—in?"

"ke dalla ware ai kece Wudas É—in, meye wani Wudas"

Hindu ta yadda da maganar Saleh, saboda sam Widad ba tayi kalar wahala ba.

Ita kuwa Hanne jinsa kawai take badan ta yadda ba, shaƙar da Widad tayi mata tafi komai bata mamaki da ɗaga mata hankali.

Ramlah ce ta shiga falo, ta tarar da Amal a kwance tana kallo, amma hankalin ta sam baya kan tv tunani kawai takeyi, a É—an gigice tace "Amal wai kinji Anwar kotu za'a kaisu next week"

Da sauri Amal ta tashi zaune tace  "kamar yaya kotu?"

"Yanzu Mummy ta dawo take gayamin"

"Dama ana kai mutum kotu, koda ba'a  tabattar da laifin da ake tuhumarsa ba?"

Ramah tace "ya za'ayi in sani? Nifa hankalina ya tashi, ashe abun nayi ne"

Amal tace  "mun shiga uku Ramla, da Æ™yar in aka shiga kotu kiga ba'a kai shi prison ba, yanzu meye abunyi?"

"wallahi nima ban sani ba, gaba É—aya kaina ya gama kullewa, Ga Mummy ta damu sosai, ko Abinci ma ba ta ci fa"

"Subhanallah, Allah sarki Yaya Anwar, yanzu fa da sunje koti se ace se prison"

Ramlah tace "wallahi nima abunda nake tunani kenan Amal, Allah sarki bawan Allah"

Nan suka yi ta jimantawa juna.

Har dare Widad taƙi walwala, ko kula Yusuf ta ƙiyi, yau ko harar da suke a tsakar gida dasu Hansai bata zauna ba, ta gyara shimfiɗar ta zata kwanta, Yusuf yaje kusa da ita yace

"My Queen dan Allah kidena fushi dani, nasan yau gaba ɗaya ranki a ɓace yake, na farko na sake gangancin sumbatarki, ga kuma wancan laifin shima da kika ce nayi, dan Allah kiyi haƙuri bazan iya jure ganinki cikin ɓacin rai ba"

Cunkusa baki tayi, ta cigaba da ƙoƙarin kwanciya.

"Amma inaga dole mu koma kan shawarata ta farko, na yakamata mu raba ɗaki, kinga ni ba waliyyi bane mutum ne kamar kowa, idan muna tare a guri ɗaya akwai matsala, ina gudun wani abu yazo ya faru, kinga na fara gazawa gurin riƙe Alƙawarin yarjejeniyar dake tsakaninmu"

"wallahi bazan kwana a É—akin nan nikaÉ—ai ba, duk inda zaka je sena bika"

"to idan na kuma kissing É—inki kika haÉ—emin rai se nayi abunda yafi haka, kina bani ciwon kai Widad, komai nayi laifi ne a gurinki, ki dinga sassauta min mana, a dinga jin tausayina"

Kwanciya tayi ta juya masa baya, shima kuwa ya kwanta a bayanta, banza tayi masa taÆ™i magana, ta lumshe ido da nufin tayi bacci, a kunnenta ya dinga raÉ—a mata  

"I love you My Queen, ina sonki Widad, and I mean it from the bottom of my heart, i love you"

Cike da ƙosawa Widad tace "Naji amma dan Allah ka ƙyaleni inyi bacci"

"to ba kice komai ba, kin haƙura kin dena fushin?"

"eh na haƙura jeka"

"kora ta fa kike Queen"

"Niba korarka nayi ba, bacci nake ji"

Yusuf yace "shikenan, Asuba tagari masoyiyya"

"kaika santa"

Yai murmushi ya koma kan shimfiÉ—arsa.

Ana ta shirye shirye za'a kai su Anwar kotu domin fara sauraren ƙararsu, akan tuhumarsu da'ake da haɗa baki gurin sace Daula, Anwar ya duƙufa sosai da Addu'oi babu dare babu rana.

Yana zaune da safe wani ɗan sanda yazo ya buɗeshi, aka tasa ƙeyarsa zuwa wani guri, wannan mutumin dai daya zo ya kuma gani, aka bawa Anwar kayansa da aka karɓa.

Mutumin ya miƙawa Anwar hannu suka gaisa yace "masha Allah, you are free now malam Anwar, muje in ajiyeka a gida"

Cikin mamaki Anwar ya kalle shi yace "i am free as how? An game bani da laifi kenan?"

"eh baka da laifi, muje"

Kamar soko haka Anwar yabi mutumin, kuma ya kasa tambayar sa waye shi, ya kai shi restaurant yaci Abinci sannan ya wuce ya kai shi har ƙofar gida.

Mutumin ya kalli Anwar yace "Anwar ina maka fatan Alkhairi, ina maka murnar fitowa da kayi da kuma tsallake tarkon azzalumai, seka kula Allah ya kiyaye gaba"

Anwar yace "sedai ni tunda kake zuwa gurina ban gane ka ba"

Mutumin yace "nasan baka sanni ba, kuma bazaka ganeni ba, sedai nima aikoni akayi ba'a bani umarnin sanar da kai wayeni ba, babu buƙatar hakan Daula yana tare da ubangida na, shiyasa aka ɗauke shi a Asibiti, yana gurinsa dan haka ka kwantar da hankalinka"

A firgice Anwar yace "dan Allah waye uban gidan naka? Daula bashi da lafiya, yana buƙatar kulawar likita"

"É—an samari kai dai ba Ruwanka, koma a wani hali yake ciki tunda dai kai ka fita, maza jeka zan tafi"

Jiki a sanyaye Anwar ya sauka, yana bin motar da kallo kamar wani soko, har motar ta bara layin.

Gate ɗin gjdansu ya nufa, ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, Isa ne yazo ua buɗe ƙaramar ƙofar, yana ganin Anwar ya shiga mutstsuka ido ko gizo yake masa, Isa yace

"Kamar Yallaɓai Anwar nake gani"

Anwar yace  "eh nine Malam Isa"

Buɗe masa ƙofar yayi ya shigo, Isa yace "Yallaɓai an sakoka kenan?"

Anwar yace  "Alhamdilillah Isa an sakoni" nan ma'aikatan suka dinga murna suna taya shi farinciki.

Cikin gidan ya Æ™arasa, yana shiga ya tarar babu kowa a falo, É—akin mahaifiyarsa ya nufa, yasa hannu ya murÉ—a Æ™ofar É—akin yayi Sallama, da sauri ta waigo dan mamar Muryar Anwar taji, aikuwa ba kama bane shi É—inne, ai da hanzari ta miÆ™e, ta nufe shi da sauri 

"Anwar kaine? Garin yaya, ya akayi aka sake ka?"

Rungume ta yayi yace "Mummy ki bari in huta se in gaya miki, duk kin rame Mummy na"
Kuka ta saka tace "ba dole ba Anwar, baka nan na rasa me kemin daɗi, nasan zaman gurin nan sam ba daɗi yake maka ba, nayi zarya harna gaji anƙi a sakeka, ko Abinci bana iya ci, bana baccin kirki"

"shikenan, is over now, ai gani na dawo Alhamdilillah"

Suna nan zaune sega su Amal, dan ta manta ma bata sanar dasu dawowar Anwar ba, nan suka dinga murna suna farinciki da dawowar Anwar, aka shiga yi masa girki, yai wanka ya huta dan ko ina na jikinsa tsami yake masa saboda wahala.

Mummy tace "nikam ka gayamin, ya aka yi aka sako kame?"

Anwar yace  "wallahi Mummy ikon Allah kawai, ina zaune akace in fito, wani mutum ya É—akkoni a motarsa yace bani da laifin komai, ya kawoni har gida ya tafi"

ÆŠan yatsine fuska tayi tace "meye haka sekace wata almara?"

"Wallahi Mummy dagaske nake miki, kiyi waya ki tambaya kiji"

"ikon Allah ko wane mutumi ne wannan oho? Ta be gaya maka waye shi ba?"

"nayi nayi ya gayamin, amma yaƙi sam, be gayamin ko waye shi ba"

Amal tace "Mummy koma dai waye, tunda Allah yasa an sako mana shi ai shikenan, mu dama fatanmu ka dawo gida"

Mummy tace  "Amma da mamaki, ina mamakin waye haka? Dan na san ba'a cikin waÉ—an cam tsinannun bane marasa imani"

Anwar yace "Mummy suwaye kenan kkke zagi haka?"

Da sauri ta wayence tace  "A'a karka damu, 'yan sanda nake nufi, ba irin zaryar da banyi ba amma suka Æ™i bani belinka"

"Allah sarki, ai Abincin su suke karewa suma Mummy, bekamata ki tsine musu ba"

Mummy tace "hakane kam, na dena tsinemusu tunda nidai É—ana ya fito"

Yau Widad har takwas na safe bata tashi ba, tunda tayi sallar Asuba, Yusuf yaje kan shimfiÉ—arta ya riÆ™e hannunta a nasa yana É—an matsawa yace  "My heart, ki tashi baccin ya isa haka, ki tashi kici Abinci"

Motsawa tayi a hankali tayi juyi tace "kaci Abincinka, ni bacci nake ji"

"A'a ni gaskiya bazan iya cin Abincin babu ke ba, ki tashi please"

Shiru tayi ta sake lumshe ido, "zanyi miki abunda bakya so yanzun nan fa"

Murmushi tayi tace "banyi brush ba dai" ta ƙarasa tana dariya, Yusuf yace "aini bana ƙyamar ki, kece kike ƙyamata komai naki ni so nake"

Widad tace "naji, É—akkomin brush É—in inje in wanke baki"

Ya duba inda take ajiyewa, ya É—akko ya bata, tana zaune akan katifar bata tashi ba, Yusuf yace "ya dai? Ko sena É—auke kine?"

Jinjina masa kai tayi alamar eh, aikuwa ya ƙaraso ya ɗauketa cak, dariya take tace "ajiyeni tun kan Baba Hari tamin ba'a ko ace na aikata wani babbam zunubi a koreni daga garin nan"

A tare suka kwashe da dariya, Yusuf yana kallonta cike da farinciki.

Tayi waje, taje tai brush ta dawo suka fara cin É—umamen tuwo.

Yusuf kallonta yake, da alama tana cikin nishaɗi, yanzu ne lokacin da ya dace ya gaya mata abunda yake son gaya mata, yai shiru yana saƙe saƙen yadda ze ɓullo da zancen yaji tace

"Me kake son gayamin ne da yake razanaka har yanzu ka kasa gayamin? Ka gayamin kawai ina saurarenka"

gaba É—aya Yusuf ya É—an ruÉ—e yace "ba wani abu da nake son gayamiki ba fa, kece kike ganin kamar ina son in faÉ—i wani abu ne"

Murmushi tayi tace "Hmm Yoseef kenan, a ɗan zaman da nayi da kai daga lokacin da ka fara min aiki, na fuskanci halayenka da yawa, koba haka ba ina iya karantar abunda ke ran mutum ta hanyar fuskarsa, bana son ƙarya, karka ji wani abu, babu abunda zan maka, se abunda Allah yayi nufin ya faru da kai"

Yusuf yace "dama ina son in gaya miki yau nake son na cigaba da fitane, ina son in sai mana wasu abubuwan na buƙatunmu, wasu abubuwan duk sun ƙare"

Widad tace "Yaushe ka warke da har zaka fara zancen fita? Se kaje ka kuma haɗuwa da wata rashin lafiyar ko? toni babu ruwana, tunda dai ban takura maka nace seka saimin abunda baka dashi ba, ka ƙyaleni komai aka bani zanci, in wanda zan iya cine se inci, in bazan iya ciba kuma se in haƙura kawai"

Sosai ta bawa Yusuf tausayi jin abunda ta faɗa, Yusuf yace " duk da haka Yakamata ace nima ina taɓuka wani abun da kaina, in sauke haƙƙinki da yake kaina, in sai miki abubuwan da kike buƙata koba duka ba"

"Shikenan, amma nidai bance kayi abunda zaka cutu ba koka wahala ba, ka kula da lafiyarka"

Yusuf ya gama shirinsa tsaf ze fita, Saleh ya shigo gidan ya kalli Yusuf yace "Ahh Yusuf ina zuwa haka? '

" zani cin kasuwane Saleh " Yusuf ya bashi amsa

Saleh yace " Haba Yusuf, kasan fa baka da lafiya sosai "

Yusuf yace " shima zaman guri É—ayan babu daÉ—i Saleh "

Harice take a tsugune tana ta tattara ƙwan da kazarta tayi zata bayar akai kasuwa, Yusuf yace " Baba Hari, wannan ƙwan na siyarwa ne?"

Hari tace " Eh za'a akaimin kasuwane"

Yusuf yace "Masha Allah, inba damuwa a zuba na kaji biyar na zabi biyar, a kaiwa Queen idan na dawo insha Allah zan bada kuÉ—in"

Hari tace "meye kuma Kun?"

Yusuf yayi murmushi yace  "A kaiwa Widad nake nufi"

"Awo sekace min Wudas, amma kun ai bazan gane ba idan kace haka"

Saleh yace "Hari baki abun magana, Queen yace ba kun ba, yana nufin sarauniya"

Kwaɓe baki tayi tace "Wace sarauniyar? Sarauniyar fitsararru ba"

Yusuf yace "Ayi haƙuri"

Hari tace "dan dai kaine, kuma ina jin kunyar ka, amma da ita zata siya bazan sayar mata da ƙwan nan ba"

Yusuf yayi dariya yace "ayi haƙuri, A temaka mana"

Saleh yace  "kedai kinji kunya, ki rasa da wadda zaki dinga faÉ—a se wannan Yarinyar"

Widad ta ƙaraso inda suke da kwanukan wanke wankenta a hannu tace
"Idanma baki siyar dan Allah ba, zan buɗe gurin ƙwan ne in kwashi san raina, ko in kama kajin naki in yanka in soye muci nida Yusuf tunda bashi da lafiya dama"

Dariya suka yi, Saleh ya dinga mamaki, dama Widad ta iya magana haka hadda tsokana?

Hari tace tunda Yusuf ne ze sai ƙwan, ya biya kuɗin biyar, ta bashi biyar kyauta, amma bata yarda ya bawa Widad wanda ta bashi ba.

Widad tace "Hari dama kina ɗan dafa ƙwan nan kici, dase kinfi haka ƙiba da kyau, ke kullum cikin neman kuɗi kamar zakiyi ƙwace, kuma na rasa inda kike kai kuɗin"

Hararta Hari tayi taƙi ta kulata, aka ɗakko kwano za'a sakwa Widad ƙwai, Widad tace

"kuma idan kika samun ƙanana bana so, manya za'a bani dan nima ƙatuwa ce"

Haka Widad tasaka Hari a gaba, tana ta zolayarta ita kuwa Hari tunda Widad ta shaƙe Hanne take ɗan shakkarta.

Yusuf yace "Queen zan tafi"

Widad tace "ba zaka soyamin ƙwan ba zaka tafi?" tai maganar kamar wata ƙaramar yarinya tana sa hannu a gashin kanta.

Gwaggo ta sunkuyar da kai tana jin taɓara, Yusuf yace "ki bari in dawo"

Maimakon tayi magana se ta cuna baki tana kallonsa,

Yusuf yace "Shikenan Muje in soyamiki, amma nasan ba iya ci zaki yi yanzu ba, dan yanzu kika gama cin Abinci"

Gwaggo tace "Yusufa jeka abunka, za'a soya a bata kaji"

Widad ta cunkusa baki tace "Ni gaskiya Mama nasa nake so, naga kin fi son Yoseef dani, ni kowa baya sona"

Gwaggo tace "nina isa ince bana sonki, waceni niko nake sonkj, amma ina nema masa Alfarma, a ɗaga masa ƙafa tunda fita zeyi"

Widad tace "shikenan Allah ya temake ka, jeka seka dawo" tai maganar tare da kashe masa ido É—aya.

Hari tace  "A'uzubullahi wannan Yarinyar idan ka zauna a inda take seta karya maka alwala"

Dariya Yusuf yayi sukayi waje shida Saleh, Saleh yace "Salute to you Yusuf, babu wanda ya isa ya biyaka namijin ƙoƙarin nan da kake, kalli yarinyar da take rayuwa kamar wata halitta daban, me gudun jama'a da son rayuwar kaɗaici, amma ita ta sake a ƙauye haka take rayuwarta, cikin farin ciki fjye da wanda take a gidansu da yake da tarin arziki "

" Saleh, ai dama kuɗi dukiya ba sune kwanciyar hankali ba, farinciki zama cikin wanda suka damu da kai shine farinciki, mutanen wannan zamanin muke ganin in kana da kuɗi kana da komai, ka wuce baƙin ciki "

Saleh yace" tabbas hakane maganarka Yusuf, da fa tsakaninta da mutane kallon banza da hantara, amma yanzu kalli yadda ta sake da Gwaggo ta maida ta kamar wata kakarta"

Yusuf yace "sosai makuwa, akwai shaƙuwa a tsakaninsu, Gwaggo nada sauƙin kai, kuma tana janta a jiki, bata hantararta idan tayi mata wauta ko wani abu, shiyasa itama take sonta"

Saleh yace  "hakane, amma ya batun ciwon ta kuwa? Na taÉ“in hankali?"

Yusuf yace "ina doubting akan wannan ciwon da take dashi, ina da question mark akai, amma lokaci nake jira"




"Alhaji Musa, kaji wata maganar banza wai an saki Yaron nan Anwar"?

Alhaji Musa yace "haka nima labari ya isheni, ni kaina abun ya É—auremjn kai Munir, wane mara mutuncin ne haka, waye yayi wannan karambanin?"

Alhajj Munir yace "munyi waya da Bukar, yace ze bincika nima nasa a bincikamin amma har yanzu babu wani labari, an rasa waye yasa a sake shi, wai daga sama aka bada umarni"

Alhaji Musa yace "waye a saman ya bada umarni damu bamu sani ba? Ta yaya ana tuhumarsa da wannan babban laifin za'a sake shi, idan kuwa hakane to tabbas muna da abokan Adawa wanda suke mana zagon ƙasa akan lamarin nan"

Alhaji Haruna da tun É—azu bece uffan ba ya nisa yace "ni kaina gaba É—aya ya kulle, na rasa abunyi semun toshe nan se can ya buÉ—e, na rasa wane banzan ne yayi wannan aikin"

Alhaji Musa yace "tabbas akwai lauje cikin naÉ—i, yanzu abunda ze faru shine, zamu saurari Bukar muji me zece, lallai a binciki wanda yayi wannaan aika aikar, sannan a tabattar an kama yaron nan an maida shi"

"haka ma za'ayi, wannan shine abunda ya dace, akama shi harse an ga Daula"

Anwar yana zaune yana cin Abinci yace "Mumsy kin san wani abu kuwa?"

"A'a seka faÉ—a" ta bashi amsa

"wato bawa baya taɓa gane Allah subhanahu wata'ala yayi masa ni'ima, se yayinda wannan ni'imar ta gushe, kinga ko 'yancin kayi yawonka ɗin nan inda kaga dama, ba ƙaramar ni' ima bace, zama guri ɗaya bala'ine Mum, ga rashin gurin kwanciya me kyau, ba Abinci me kyau, wai danma nine fa wasu haka suke tagayyara a cikin gurin nan "

Hajiya Halima tace " Aini duk zance ya ƙare, tunda Allah ya fito min da kak, Se fatan Allah ya kiyaye gaba"

Anwar yace  "Ameen Mummy, ni yanzu fatana ubangiji Allah ya bayyana Daddy, yasa yana hannu nagari, dan na tsorata da abubuwan da suke faruwa"

Mummy tace "kai kam wannan dashi ya haife ka da an shiga uku, kai har yanzu baka shiga hankalinka ba, ba kaga masifar daka shiga saboda temako ba, still kai tunaninsa ka keyi"
. "Mummy ba zan taɓa iya dena tunaninsa ba, saboda gudunmuwarsa a rayuwar mu"

Wayar Anwar ce ta shiga ringing, ya ajiye spoon É—in da yake cin Abincin ya É—aga wayar yasa a kunnensa.

Lambar Bulama ce, bayan sun gaisa Bulama yace "Anwar ashe ka fito?"

Cike da ladabi Anwar yace "eh Daddy na fito"

Post a Comment

0 Comments