Amfanin Kanunfari ga Maza da Mata
Tags: amfanin kanunfari ga maza, amfanin kanunfari, dabino da kanunfari, amfanin tazargade da kanunfari, maganin infection da kanunfari, amfanin tsarki da kanunfari, matsi da kanunfari
In zaki jika kanunfari at least ki bari yayi 2-3 days kafin ki sha. Kuma ki zuba shine yanda in ya jika ruwan zai koma brown. Babban goran faro ki sa masa cokali uku na kanunfari.
1. Kanunfari Yana taimakawa wurin rage ciwon mara ga mai ciki da kawo haihuwa da wuri.
Wata yar'uwa bayan waccen rubutun ta faÉ—i cewa: "Kanunfari yana hana me ciki ciwon mara kuma yana taimakawa wajen haihuwa da sauri. Ga wani hadin da nake amfani da shi "Ki samu dabino, ki ciccire kwollon ki sa shi a rana idan ya bushe ki daka tare da kanumfari ki rinka sha da madara." Tace "Na yi amfani da shi kuma ya mun sosai wallahi."
Wata itama tace: "Nima na gwada especially idan kika hada kanumfari da minannas, ki samu empty roban swan ki jika da ruwan sanyi ki bar shi ya kwana, sai ki rinka sha da peak milk (madarar ruwa). Ki yi ta refilling (sake cikawa) har kamshin da color brown ya tsane sai ki zubar ki jika wani."
"Tace har tsayin labour (nakudan) ta ya ragu, nan da nan sai ta ga ta haihu sanadiyyar amfani da kanumfari. Wato kenan duk mai ciki in tana amfani da shi zata samu saukin ciwon mara da rage tsahon nakuda.
Domin karin ruwan ni'ima da daÉ—i. In dai mace ta rike wadannan in Allah Ya yarda bata da matsalar ni'ima.
2. Ki samu kanumfari, rake, ginger/ginseng in so samu ne, sai zuma.
Ki dafa rake da sauran kayayyakin amma ban da zuma, na kamar minti 30.
In kika sauke ya huce sai ki murje ruwan raken ya fita jikin shi, ki zuba zuma a ciki, ki rinka shansa. Yana mutukar saukar da ni'ima kuma yana kara sha'awa da daÉ—i.
Wasu ma suna saka mazarkwaila a cikin dahuwan.
3. Ki rinka nika kankana da kanumfari, ki zuba ridi in kina da shi sai ki nika shi sosai. In kin juye sai ki zuba isashen madara ki rinka sha.
4. Yayan goji/kabewa (pumpkin seeds) suna kara wa mace sha'awa da dadi.
Akan busar da shi a daka a rinka sha da madara ko a dafa a sha da madara. Wasu kuma suna daka shi tare da busashen yayan kankana su sha da madara.
Yana wanke duk wani dattin jiki. Sannan ki dafa goji dai-dai wanda zaki iya shanyewa. Sai ki sauke, ki zuba dakakken kanunfari, zuma da madara isashe ki sha da yawa.
Wasu kuma tace ruwan suke su sha wato ki dafa shi da kanumfari sai ki tace ki sha akai akai, duk wanda dai kika ga zaki iya. Yana gyara jiki da fata, yana kara karfin sha'awa da ni'ima da dadi ga mace da na namiji duka.
5. Kankana (watermelon), yana kara sha'awa, ni'ima da dadi.
Ki rinka yanketa har da wurin farin domin akwai sinadarin da jiki ke bukata a ciki. Zaki iya haÉ—a kankana, kanumfari da cocumber ki nike ki rinka sha.
6. Cin kifi da shan farfesun sa yana kara sha'awa.
Ki sanya kayan kamshi sosai a cikinsa (nutmeg, tafarnuwa, kanunfari, ginger, girfa dss) ki ci ki sha romon isashe. Cin nama mai romo-romo amma wanda yaji haÉ—in kaya kamar riÉ—i, kafi malam da nonon rakumi.
7. Tafarnuwa yana sanya mace juriya yayin saduwa.
Yana kashe infection da cututtuka marasa adadi ciki da waje. Yana cleansing cututtukan ciki. Zaki iya sashi a cikin abinci ko ki rinka hadiye shi da yoghurt bayan kin yanka ruwan jikinsa ya dan fito.
Zaki iya hadiye babba guda daya da yoghurt mara sugar duk bayan sati biyu ki sha, sau biyu a wata kenan ko sau uku.
In baki so akwai capsule na tafarnuwa kuma akwai oil nashi. Yana wanke duk cutukan ciki da mara. Don haka kada kiyi sake da shi.
8. Yawan cin ayaba da yin juice dinsa da madara shima yana sanya mace juriya, kuzari da dadi. Abarba yana gyara kamshin sperm da kara lafiya.
8. Yawan cin ayaba da yin juice dinsa da madara shima yana sanya mace juriya, kuzari da dadi. Abarba yana gyara kamshin sperm da kara lafiya.
9. Ginseng kamar citta yake ana siyar da tea nashi a kasuwa wurin masu siyar da tea na kanti kala-kala, kuma ban san sunansa da hausa ba. Yana kara sha'awa, juriya, yawan sperm da dadi. Zaki iya dafa shi da kanumfari. Haka nan in babu shi za a iya amfani da ginger.
10. Nutmeg (gyaÉ—ar miya) ana samun shi wurin masu siyar da kayan kamshi (su kanunfari da citta) A rinka daka shi ana sashi a farfesun da zaki sha. Wadanda suka ji su tafarnuwa, kanunfari da citta. Ki ci naman ki sha romon.
11. Ki siya busashshen dabino, kanunfari, aya, zaki iya hadawa da busashen kwakwa. Ki daka su ko ki kai a nika miki gari kenan. Ki rinka sha da zuma ko madara. Wannan yana dadewa bai lalace ba.
Sannan zaki iya nika su ki sha kamar kunu. Hadin nan yana mutukar wanke koda da kara wa mace daÉ—i da ni'ima. Sannan zaki iya hada aya, dabino, gyadar mata da mazarkwaila ki yi garin shi kina sha da zuma ko madara.
12. Ki rinka shan zuma kada ya rinka yanke miki, haka nan yoghurt/nono. Ki rinka soya kwai amma kada ya soyu sosai da man zaitun da safe.
Ki rinka cin zogale da shan ruwansa, ki rinka yin miyar ugwu leaves ko alayyaho. Ki rinka dafa wake tare da kifi, isashen albasa/ tafarnuwa da ganyayyaki.
Ki rinka yawan yin salad Ko kwaÉ—on duk ganyen da kika samu.
13. Ki rinka yawan shan lemu ko matse ruwansa. Ki rinka yawan cin cocumber yana gyara fata, kara ni'ima da dadi. Ki rinka shan rake mai yawa kada ya yanke miki ko bashi da zaki sosai.
14. Kada ki manta da shan shayin kanunfari, cinnamon (girfa), cardamom (Habhan ko Habbahan), ginseng ko citta, a sa na'a na'a (mint), tafarnuwa dss.
In kina yawan sha ni'ima ba zai yanke miki ba, infection ba zai zauna a jikinki ba, ba zaki rinka warin gaba ba, ba zaki rinka jin kasala ba.
15. Ki rinka shan garin zogale da yoghurt da safe kafin ki ci komai. Yana maganin ulcer yana da kuma sinadarai mai yawa a cikinsa. Ki rinka yawan cin aya kada ya yanke miki.
Da cin kwakwa da dabino ga daÉ—i ga karin ni'ima. Ki rinka shan isashen ruwa da rana, ki rage cin abinci mai nauyi sosai yayin zuwa turaka zai sa miki kasala.
WaÉ—annan kadan daga cikin abubuwan da nake ganin zai amfani mata ne da na rubuta yau. Ki rinka kokarin jure amfani da abubuwa har jikinki yayi adopting ya saba. Akwai abubuwan da aikinsu ba na yanzu yanzu bane.
KARANTA: Budurcina Hausa Novel by Maman Teddy
0 Comments