Auren Wata Tara Complete Hausa Novel

 

Auren Wata Tara Complete Hausa Novel

Auren Wata Tara Complete Hausa Novel

Auren Wata Tara Complete Hausa Novel: Tafiya suke cikin unifoam din Islamiya su biyu suna tafe suna hira kadan_kadan

 Asmy ce ta daddabo Zarah ta ce Zarah gafa mutumin yau ma ya na kofar gidan Ku kuma wlh nasan ke ya ke jira  

Tsaki wacce aka kira da Zarah taja cikin sanyi murya da daman Chan tun asali haka muryarta take komai takeyi zatayishi cikin nutsuwa da sanyi ta ce Aiko bazan shiga gidan yanzu ba Allah har sai ya tafi  sai sannan na Kare mata kallo doguwa Ce mai matsakaicin jiki 


Choculate colour Ce bazaka kirata fara Chan ba haka kuma tafi karfin ka kirata da baka 

tana da round face da dogon hancinta sai dan karamun bakinta da ya dan tsuke ya bada shape din heart Dimple dinta guda biyu dukkaninsu sun lotsa 

wanda tun asali haka suke ko batayi magana ba a lotse wanda suke kara fito mata da ainahin baiwar kyaun da Allah yayi mata Fuskarnan tata fresh ba komai sai kwalli da ta kurtawa idanunta Kadan

Zarah tana da Balain shape Wanda ake kira da shape din CocaCola diri da Zati da Allah yayi mata shine Babban abunda ke Jan hankalin maza gareta Dan Zarah badai diri ba Dan koya tayi tafiya haka zakaga hips dinta na Juyawa 



Wanda saika dauka da gangan ta ke yin hakan alhalin itama Ba so take ba danma koda yaushe cikin hijab take amma dukda manyan hijaban da take sanyawa baya hana bayyanar da surar da Allah yayi mata


 Kama hannunta Asmy tayi cikin Sauri suka shiga gidansu Wanda madaidaicin gida ne Suna shiga Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta ce  Allah yasa mayen bai ganmu ba dafa saiya biyo mu ko


Aiko da ya biyoki wlh da yaga yanda ake Rashin mutunci Dan ni ba ke bace danfa ya ganki haka salo salo ba umm ba umm umm shiyasa ya rainaki wlh Zarah ki rage sanyin nan Lafiyarki tayi yawa haba ayi mutum kullum cikin sanyi dukda wannan halin naki ya sanya har Rabi take maki irin abunda take maki Dan taga bata gamu da yar zamani ba haba ke Ko a makaranta Saidai na shige maki fada to tun wuri ma wlh ki koyi kare kanki haba hakurinki yayi yawa wlh 


Asmy ta karasa fada tana huci Mamanta ce Da ta fito daga kitchen ta na sauraransu ta ce  Zarah karki biyeta kici gaba da yanda kike Allah yanason masu hakuri kowani dan adam yana da nashi kalar jarabawar kinji ke kalar taki kenan kiyi kokari wajen ganin kin cinyeta Allah ya kawo maki sassauci cikin alamuranki ga abinci nan kuzo Kuci kunji


kasa da kanta Zarah tayi tana Goge hawayen da suka zubo mata na tausayin kanta ta ce Insha Allahu Mama  Kallon Asmau mamanta tayi ta ce Karfafa mata gwuiwa ya kamata ki dingayi kullum ba Wai Zuga ta ba kinji gyada mata kai asmy ta yi ta ce Insha Allah Mama  Tuwon Shinkafar da yaji Miyar taushe mai dadi da Mama ta zubo musu suka zauna Suka fara ci 


Bayan sun gama Ci nan suka fiddo Littafansu na Islamiya suka dinga duddubawa Dan yanzu gaba daya hankalinsu ya na Ga saukar da ke tinkarosu Bayan sun gama dibawa jin ana kiran Sallar magriba ya sanyasu tashi Bayan sun gabatar da Sallar magriba Hijab dinta Zarah ta sanya ta ce Bari na wuce gida sai da safe Bankwana tayiwa maman asmy tare suka fito su biyu Kasancewar gida Ukku ne tsakaninsu sai nasu Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ganin Nura baya nan A daidai bakin kofar gidan Asmy ta tsaya ta ce  Sai Gobe Zarah Zan wuce Kallonta tayi ta  ce  bazakizo mu shiga tare ba Girgiza kai Tayi ta ce  Saidai kawai mun hadu gobeto Sai Allah ya kaimu kawata ta fada ta na kutsa kanta cikin gidan cikin siririyar muryarta tayi sallama a hankali 


karamun gida ne daki hudu daya na Mama Rabi daya na Baba sai na ukkun nata na hudun kuma nakannanta  a tsakar gida ta tarar da Mama Rabi tana ganinta ta watso mata wani banzan kallo cikin Masifa ta fara magana da cewa an fake da Islamiya ana yawon karuwanci Dan matacciyar uwarki Da kikaje kika zauna uban wani zai daura miki girkin ne Eh ko kin Aje wani ne a gidangirgiza kai ta fara tuni harta fara hawaye dan a rayuwarta kome Mama Rabi zatayi mata batajin ciwon shi kamar irin yanda take zagar mata Mahaifiya da ke kasa Goge hawayenta tayi cikin muryar tsoro ta ce  Kiyi Hakuri Mama Tsaki Rabi taja tare da mikewa ta ce  Kafin nan da minti Talatin na baki ki gama yimun tuwo da miya Dan uwarkito ta fada gabanta na faduwa tare da shiga kitchen din


murhu biyu ta hura dukda iccen jike ya ke kasancewar yanayin damuna Haka tayi ta hura wutar cikin kankanin lokaci ta na Sauri ta gama Duka ayyukan tukwana ta fito ta yi wanke wanke Su Habiba na Nan zaune suna latsa waya ba Wanda ko tsinke ya kama mata Harta gama komai tukwana ta wuce dakinta Dan hutawa Cire kayan jikinta Tayi Tare da daura zani Dan zafi takeji kodan yanayin garin kamar akwai hadari a kasa ya sanya zafin fitowa tayi a lokacin Mama Rabi suna cin tuwo ita da yaranta Tabe baki tayi tare Jan tsaki ta ce Sai anje an gama yawon ta bugas din azo ana wankan iskanci a gida  Idan da sabo ta saba hakan yasa ko a jikinta harta fito daga bandaki Bayan tayi alwalar isha i dakinta ta wuce tare da shimfida tsohuwar dardumarta ta sanya hijab dinta ta Islamiya ta kabbara salla 



Bayan ta gama isha i tare da shafai da wuriri zaune tayi a wajen ta jima tana nemawa mahaifiyarta gafara a wajen ubangiji ta na hawaye ta ce Allah ya jikanki Mahaifiyata har kullum ina kukan rashinki a kusa dani amma kuma nakanji farinciki idan na tuna da irin mutuwar da kikayi bansankiba ban taba ganinki ba Amma ki sani ina tsananin kaunarki kullum da tunaninki a raina nake kwana nake tashi na tabbatar da kina raye da bazan tsinci kaina cikin wannan kuncinna rayuwa ba amma babu yanda na iya da Lamarin ubangiji haka Allah yaso ya ganni kuma nagode masa Allah yasa kin huta 


ta karasa fada tana fashewa da kuka mai cin rai Hade kai da gwuiwa tayi ta na ta kukan halin maraicin da ta tsinci kanta da tasowarta cikin marassa imaniMalam Yusuf Da ya shigo Yanajin yartashi na yiwa mahaifiyarta addua Saida ya Goge hawayen tausayin yar tashi Shi kanshi idan yana tunowa da Mahaifiyarta kuma  masoyiyarsa Zarah mace mai biyayya da hakuri Sai da ya  Goge hawaye karasowa yayi Tare da zaunawa gefenta ya ce Zahrau Kiyi Hakuri kinji yaci ace kin saba da irin wannan rayuwar kisani komai yayi farko yana da karshe kinji yata Allah yayi maki albarka ya jikan mahaifiyarki ya kara miki hakuri da juriyar zama da rabi sannan ya nuna mun ranar aurenki ni kaina badan naso ba nake ganinki cikin wannan halin  


jin muryar mahaifin nata ya sanyata saurin Goge hawayenta Dan a duniya babu abunda ta tsana sama da tashin hankalin mahaifin ta tare da kirkirar murmushi ta ce Baba ina yini  Murmushin ya mayar mata ya ce Lafiya qalau Zarah ta ya makarantar munyi magana da malaminku yau ya ce Akwai kudin sauka da za a kai me yasa baki fadamun ba tun da wuri Zarah  kasa tayi da kanta ta ce


 Baba naga baka da kudi kuma naga ba dole bane sai anyi walimar saukar da ni tunda Dai na hardace a kaina ai shikenan  girgiza kai Baba yayi yanajin kaunar yar tashi ta daban sosai hankali da hangen nesa irin na Zarah har mamaki yake bashi akwaita da hakuri irin na mahaifiyarta cewa yayi Allah yayi miki albarka yata amma ko zamu rasa abunda zamuci saina biya miki kudin ba dubu goma bane Allah ya horemun kafin lokacin ameeen Baba nagode Kinci abinci dai koeh Baba ta fada ta na gyada masa kai  yawwa to shikenan Sannan ya miko mata dari biyu ya ce Gashi ki boye ki dan dinga kashewa kinji Murmushi tayi tare da amsa hannu biyu ta ce Nagode Baba Allah saka da alkhairi  Ameen yar kirki ya fada tare da yi mata saida safe 


Bayan fitar Baba girgiza kai tayi tana jin kauna da soyayyar mahaifin nata ta musamman tasan Shima ba ason ranshi take fuskantar kalubalen wannan ba Boye kudin da ya bata tayi a akwatin kayanta tare da dauko Alquran mai girma ta fara karantawa cikin zazzakar muryarta tana rerowa cikin kiria mai dadin sauraro a haka har bacci barawo ya kwasheta 


kamar yanda ta saba koda yaushe tun asuba da ta tashi tayi sallah bata koma ba nan taci gaba da aikace aikacen gidan Har Safiya tayi wajen 8 da rabi taga su Habiba sun fito Suna hamma tare da daukar buta Zasuyi Alwala girgiza kai tayi wai ace Sai yanzu zasuyi sallah Kodan yau sunma tashi da wuri su da har 9 kaiwa suke batace komai saboda bata manta ba ranar da ta taba musu magana akan Sallar Safe da suke irin tijarar da suka mata hakan ya sanyata cigaba da Harkokinta Tana cikin dora dumame Khairat ta leko Yarinya ce da bazata wuce shekaru goma sha daya ba kallonta tayi tare da cewa  Ina kwana Aunty Murmushi Zarah ta sakarma kanwartata dan duk cikin gidan itace Ta fita zakka ta ce  


Lafiya qalau khairat Kintashi lfy Alhmdllh ta fada ta na Amsar tukunyar da Take shirin dorawa ta ce  bari na tayaki AuntyA a a ki barshi khairat zanyi Amsa tayi ta ce  Nidai saina tayaki Suna cikinyi Mama Rabi ta leko Dan Safiya ta gulmanta mata Khairat na kitchen tana taya Zarah Aiki wata uwar ashar ta kawo ta lafta wadda saida cikin Zarah ya duri ruwa tuni ta dabarbarce Kafin da dago Mama Rabi ta kife ta da Mari tare da cewa  Dan Ubanki yartawa zaki sanya Aiki tayi maki kama da kalar Aiki Sau nawa zan fada maki Ke kadai zaki dinga aikin gidan nan Eyye tsabar iskanci ma yarda na Haifa itace zatayi maki aikiKhairat ce ta mike cike da tausayin yar uwar tata ta ce Kiyi hakuri Mama Ba ita ta sanyaniba ni naga ya kamata na tayata 


Tsawa ta daka mata Tare da nuna mata hanyar waje ta ce Fice ki ban waje kafin na waiwayo kanki Cikin Sauri ta fita ta bar kitchen din ta na gunguniZarah ko hawaye ne suka zubo mata Inda Mama Rabi ta shiga balbaleta da masifa Inda ta shiga ba ta nan take fita ba amma bata Ce mata uffan ba harta gama fadanta ta fita girgiza kai tayi tare da mikewa taci gaba da abunda ta ke ta na yi ta na hawaye Bayan ta gama aikin Dakinta ta shiga ta share tare da daura towel ta dauki sosonta da sabulu ta fito Ta shiga wanka Bayan ta fito Nan ta iske Mama Rabi da diyan ta suna cin dumamen Tuwon da ta dafa bata bi ta kansu ba ta shige dakinta Tare da Shiryawa cikin Wata Atamfarta da ta dansha jiki jin kukan yunwar da cikinta keyi ne ya sanyata mikewa tare da fitowa nesa da su ta tsaya tare da Kasa da kanta Tayi shiru  


Cikin masifa Rabi ta ce kikazo kikayi mana tsaitsaye Mayya me za a baki Dagowa tayi idanunta na zubar da kwalla tayi maza ta Goge ta ce Daman abinci nazo dauka  Dogon tsaki taja tare da Banka mata harara ta ce Mun cinye mu Kanmu bai ishemu ba  Khairat ce dukda yarintarta ta ce Mama ni bari na bata nawa na koshi Harara ta banka mata tare da dankwashinta aka ta ce inke kin koshi ni ban koshi ba  girgiza kai kawai Zarah tayi ga abinci nan tana gani Bayan ita ta sha wahalar girkawa amma a hanata ga tsabar yunwa da takeji Juyawa tayi ta koma dakinta tare da dauko dari biyun da Baba ya bata ta boye a jikinta hijab ta sanyo tare da Fitowa Tsawa Mama Rabi ta daka mata ta ce Gidan ubanwa kuma zaki 


Fita zanjena nemi abinda zanci ta fada cikin rawar murya koma ciki babu Inda zaki Dan Ubanki so ne kike ki kara jamun Zagi a wajen mutane duk abunda nake ba gani ake ba To ba Inda zakiAmma Mama Ke fa kika hanani Abinci kuma zanje na saya ki hanani fitata fada cikin dauriyaeh bazaki ba ko fada zanyi ki mayar mun


Girgiza kai kawai tayi tana Jinjina Rashin imani irin na Mama Rabi daki ta Koma tare da zaunawa ta rafka ubann Tagumi Hawayen tausayin kanta na zubo mata yaci a ce Inda sabo ta saba da halin da take ciki



muje zuwa fans salon na daban ne Kudai kawai Kuci gaba da bibiyar gawurtaccen labarin da yazo cikin gawurtattu

ta hanyar comment da sharhi ne kadai zai tabbatarmun da labarin ya amshi wajenku ko akasin haka idan kun karanta ku daure  Kuyi comment tare da sharing sauran grps masoyan Asali wannan itace babbar kwarin gwuiwar da makaranci ke bawa marubuci

GAWURTATTU BIYAR TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE 


1 MU GANI A ASA
      _Ummu Affan_

2 ABIN CIKIN WAI
      _Ummu Maher_

3 GUNTUN GORO
      _Mom Islam_

4 GISHIRIN ZAMAN DUNIYA
    _Mrs Bukhari_

 5 AUREN WATA TARA
     _Miss Hajo_


Guda biyar  1k
Guda huu  N700
Guda uku  N600
Guda biyu  N500
Guda aya  N300

DOMIN TURA KUIN KAI TSAYE

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

an asar Niger zasu tura nasu anan

0817 952 3215

Guda biyar  1000f
Guda huu  700f
Guda uku  600f
Guda biyu  500f
Guda aya  300f

TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN 


    Taku har kullum dince dai
          

       _Miss Hajo ce_
821 0818   AUREN WATA TARA 

       MALLAKAR

   Hajara L Sadeq

FREE PAGE

3  4


Tana nan zaune tana jin yunwa har Ukku da rabi tayi cikin Sauri ta mike tare da sanya Hijab dinta Dan daman Allah Allah take lokacin Islamiya yayi turaranta Wanda baiwuce Naira dari Ukku ba ta fiddo ta fesa Dan Ita daman Chan ma abuciyar son kamshi ce 



 Fitowa tayi ganin ba kowa tsakar gidan Tare da barin gidan Gidansu Asmy ta shiga gaishe da mamansu tayi har kasa ta amsa mata cikin girmamawa Babansu ne ya fito Shima gaishesa tayi ya amsa mata cikin sakin fuska Asmy ce ta fito daga palour tare da kallonta ta ce




 Ki shigo yau kece da Shiryawa da wuri Ko yar jarabar bata nan  Dariya Kadan Zarah tayi tare da girgiza kai ta ce Kiyi Sauri dai yanzu  Kama hannunta tayi suka shiga cikin palourn su mai dauke da kujeru matsakaita masu kyau sai madaidaiciyar plasma dinsu dake manne a dakin Suna Kallon tashar arewa24 




ganin ana maimaicin dadin kowa ya sanya Zarah maida hankalinta ga kallon da ake Asmy tunda ta shigo ta lura da Idanun Zarah yanda suka fada tasan bataci abinci ba gashi tasan ko mutuwa zatayi bazata taba cewar bataci ba



 Shinkafa da miya taje ta zubo dukda taci abinci Tazo ta Aje gabanta tare da kallonta ta ce Sauko muci abinci my Besty na koshi Kedai kawai kici mutafiHarararta tayi ta ce Aiko kice yau ba zuwa Islamiya Dan Allah sai kinci abincin nan idan ba haka ba Muyi ta zama a haka Saukowa Tayi Dan tasan kawar tata ta aika Ta ce



 Uwar yan jaraba to muyi Sauri Sai sannan Asmy ta saki fuska ta ce kokefa my Besty wai kinsan Waec dinmu ta fito Kuma alhmdllh Duka na cinye yanzu jiran neco kawai muke tunda ita kikayi  



Cikin farinciki Zarah ta ce Wow alhmdllh sis a Gaskiya na tayaki murna wlh Allah sanya alkhairi kice itama neco tana gab da fitowa muyi ta addua



 Wlhko Besty Kinga murnar da nake Har suka gama cin abincin suna Hira Inda Bayan sun gama sukayi sallah tare da wucewa Islamiya Dan duk shirye shiryen saukar da zasuyi ne nan da sati biyu ake



 Sai wajen magriba suka bar makarantar Inda daga nan kowa yayi gidansu Tun a Soron gidansu Zarah ta farajin muryar Salisu gabanta na faduwa Ji take kamar ta juya Dan tana tsoron mashayin Chan



 dakyal tayi shahada ta shiga tun daga shigarta Salisu dake kan turmi yana busar sigari ya kafeta da idanu har wani lashe harshe yake Itako hade fuska tayi Tam Cikin muryar yan maye ya ce Daman tun dazu nake jiran dawowarki Amaryata  



dogon tsuka Zarah taja tare da Yin hanyar dakinta janyo mata hijab yayi Wanda hakan ya kular da Zarah batasan lokacin da ta juyoba tare da wankeshi da Mari Salisu da saijin saukar Mari yayi a fuskarsa dafe kumcinshi yayi tare da nunata da yatsa ya ce



 Ni kika Mara Aiko yau zakisan kin taba cikakken dan tasha Dan uwarki Dan kin samu ma ana sonki Aiko daga yau bazaki kara gigin Marin wani ba ya fada yana zare belt din jikin wandonshi tuni cikin Zarah ya Dori ruwa Dan ba abunda ta tsana irin a taba lafiyarta Cikin Sauri Ta maza ta Ruga dakinta Tare da sanya sakata ta rufe sai huci take



  Salisu ko tsaye yayi ya na ta banka kofar ya ke kamar zai ballata Rabi ko shiru tayi Dan abunda yasa bata tanka ba Baba na bandaki tun daga Shigowar Salisu Kasancewar Tattare suka shigo da Zara da ido take masa nuni akan ya bari amma sai dura ashar yake ya na cewa yau sai ya raba Zarah gida biyu 



Baba ne ya fito daga bandaki cikin bacin rai irin nasu na masu hakuri ya dakawa Salisu tsawa  Juyowa yayi Dan duk iskancinshi yana shakkar Malam saboda mutum ne mai kwarjini Sosai Malam ya shiga Fada ta Inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sulalewa Salisu yayi ya bar gidan Inda ya koma kan Rabi ya ce



 Wlh nakaraga dan iskan yaron nan ya shigo gidan nan zaki kuka da kanki Marainiyar Allah ku sakata gaba Kuyi ta musguna mata wlh kedai Rabi kiji tsoron haduwarki da ubangiji Dan sanya bakinciki a cikin zuciyar maraya ba karamun Abu bane kina daukarsa wasa hakkin wannan yarinyar kadai ya isa ya hanaki kwanta kabari ko Dan a tunaninki duk abunda kike bansaniba 


ina sane kuma ki kiyayi irin hukuncin da zan yanke nan gaba Dan Zarah ta fiyemun ke da kowa ma  Tsaki Rabi ta ja tare da Barin wajen ta na gunguni Girgiza kai Baba yayi tare da Yin alwala Dan ya wuce masallaci ya Tada musu sallah



Zarah ko ta nan tana hawaye har taji fitar Salisu da yanda Baba yayi musu saitadanji sassauci Amma dukda haka tsoron bude dakin take Dan tasan Rabi duk abunda Baba yayi mata akanta zata huce Ga tana son taje tayi salla ta na tsoro Gashi yau batayi musu girki ba tasan ta bani ta na nan rufe ta kasa fitowa tanajin irin ruwan zagi da masifar da Mama Rabi ke Surfa mata tayi mata banza 



sai da kanta taje tayi girki wajen 11 PM tukwana Zarah ta fito tayi alwala tana sanda ta koma daki tare da hade Sallar magriba da isha i tukwana ta nemu waje ta kwanta



 Dan Daman batasa ran cin abinci ba tama girka sai Anga dama dama ake bata Ko idan Baba na gidan bare ba ita ta girka ba Cikinta na kukan yunwa a haka har bacci barawo ya kwasheta



Washegari Tana kwance da Yamma tana bitar karatun Islamiya kasancewar Alhamis ce suna gida taji yaro yayi sallama tare da cewa ana kiran Zarah a waje 


 Mama Rabi Ce dake waje ta ja tsaki tare da cewa kaje kace bata nan  Baba ne da shigowarshi gidan kenan ya kalli yaron ya ce je kace gata nan 



Fita yaron yayi yayinda Mama Rabi ke cika tana batsewa Kwalawa Zarah kira Baba yayi Bayan ta fito Ya ce Jeki shirya Ana Kiranki kofar gida


 to tace tana kasa da kanta dan bazata iya musu da mahaifinta ba Tare da komawa ciki ta sanyo katuwar hijab dinta Ta fito Mama Rabi na binta da harara Dan tana bakincikin taji ankira Zarah waje zance


kamar yanda tayi tsammani shidinne sanye cikin wani bakin yadi gashi baki ga bakin yadi sai suka saje tsaki taja a ranta tana turo baki harta isa Inda yake tare da ja ta tsaya tana kauda kai 




Nura ko cikin farinciki ya ce  Yakike masoyiyata Yaudai Ranar ta musamman ce a gareni tunda kika amsa kirana Wani banzan kallo Zarah ta watsa masa tare da Jan tsaki ta ce  



Malam idan ka gama zan wuce ina da Aikin da nake a ah yi hakuri gimbiyar mata kinsan ke din ta musamman ce sai ana lallabaki Dan Allah Zarah ki amshi tayin Soyayyata tsaki Zarah taja ta ce  Inma kana wannan mafarkin Ka daina Dan bana sonka na fada maka ba sau daya ba basau biyu ba Amma ka nace ayi mutum ba zuciya ta fada tana Kara Jan tsaki tare da Juyawa ta shige cikin gidan ta na gunguni



 Baba na ganin shigowarta rai bace ya ce Lafiya yar Amanar Baba waya tabamunke naga ranki bace  Cikin shagwabarta da tunda aka haife take da ita  ta ce 



Baba Nura ne kuma nace masa yadaina zuwa wajena yaki dainawa Girgiza kai Baba yayi tare dayi mata murmushi ya ce in banda abunki Zahrau meye aibun Nura yaro mai hankali da sanaarsa da komai  



Zarah ji take kamar tayi kuka ta ce Ni Baba bana sonshi kuma ni da ba Aure zakamun ba Duka nawa nake Dariya Baba yayi ya ce to shikenan yar Baba kwantar da hankalinki ai ba a dole a soyayya Yawwa daman zuwan da nayi kauye jiya na sayar da akuyata Dubu sha Biyu Yanzu haka daga wajen malamin naku nake harma nakai kudin sun bani receipt ya fada yana nuna mata receipt din 



Cikin farinciki Zarah ta dago ta ce Kaii amma nayi farinciki nagode Baba Allah saka da alkhairi ya kara budi nagode Nagode



  Ameen yar kirki ya fada yana Mikewa Mama Rabi Ce ta mike cikin Masifa ta ce


  Amma dai Malam kasan Irin faman da muke a cikin gidannan kullum cikin cin tuwo Miyar kuka muke Maimakon da kudin ko yar shinkafa ma auno mana Shine zakaje Ka biya asara Har dubu koma akan Saukar da bama ta kirki ba aka bibiya izif biyar bazata kawoshi a ka ba wlh abunda kake Malam ba adalci bane na tabbatar cikin yarana Khairat ko Safiya acire Habiba da Salamatu tunda ba yaranka bane  Babu wacce zaka biyawa Har dubu goma idan zasuyi sauka amma ita yar gwal din ka lale Naira na dukan Naira har dubu goma ka biya mata



girgiza kai kawai Baba yayi Dan ba a komai ya fiye mata ba ya ce Suma cikinsu Wata ta dage tayi saukar taga ko sama da dubu goma idan ban bayarba yaran da kin lalata su islamiyar ma na sanyasu amma ba zuwa suke ba Shine har zakizo kina kushe karatun yarinyar da ta shekara da shekaru tana gangariyar karatu ta gama sauka gashi yanzu har tayi harda Wanda iya tsawon rayuwa baxan iya tuna ince ga ranar da Zarah bataje makaranta ba ince Salamatu da Habiba ba sun girmeta ba cikinsu ba mai izif Biyu cikakke gwarama khairat shine zaki hadata da su wannan Abun da kike za a iya daukarsa a hassada ce 



  Sosai maganganun baba suka batawa Rabi Tai masifa ta shiga surfawa Inda ta shiga ba ta nan take fita ba hada kuka wai yayiwa diyanta gori Baba bai kulata ba ya ficewarshi tana ganin fitar Baba ta sauke ruwan masifarta akan Zarah saida tayi mai isarta itadai Zarah bata kula taba sai aikinta da ta kama 



suko su Habiba ko akansu ita da da Salamatu suna Chan suna wayar batsarsu da samarinsu Bayan Mama ta gama masifarta daki ta shiga Inda ta samesu kowanne da earpiece suna Waya sai huci take Salamatu ce ta katse wayar tare da cewa



 kema Mama ki daina tada hankalinki akan komai meye akayi akayi wata banzar Zarah kina da mu  Tsaki Rabi taja ta ce ba dole na damu kaina ba yarinya duk tazo tana neman  muku zarra Kuna nan zaune bakinku primary amma yarinyar nan shegiyar da bala i na da komai Amma saida har ta gama secondry school sannan gashinan har tana hardar alkur ani amma ku shaggun ko izif daya cikakke bana ce zaku kawoshi ba ga shegen farinjini tsiya yarinyar nan Duk ta na neman ta rikitamun lissafi  



Habiba ce ta turo baki tare da cewa kema Mama meye abun damuwa anan har waccen figaggiyar yarinyar yar shekara 16 zata dameki sannan da kike maganar Karatu har wani amfani ke gareshi a zamaninnan Mama Me muka nema muka rasa Muma dai daidai gwargwado muna da namu farinjinin tunda manyan yaran da suke zuwa wajenmu da kudin da ake kashe mana ma kadai ya isa ki gane munyiwa yarinyar Chan zarrah Mama 



Kullum maganar kenan kuna tare da manyan yara yau a sauke ku a wannan mota gobe a saukeku a waccen amma har yanzu an rasa na aure guda daya gaisuwa ma suzo abun ya gagara


Kwana a tashi ba wuya a wurin Allah a yaune ranar saukar su Zarah Duka daliban makarantar sanye suke da ankon atamfa tare da hijab Blue Sabbi sai tag din shaidar su a wuya manyan malamai sosai aka gayyato a walimar 



Wanda wurin ya cika sosai kowa da dan uwanshi iyaye da abokan arziki sunzo Zarah na zaune ita da Asmy Dan Mamansu Asmy ma tayi musu ankon kayan A gidansu Babu Wanda yazo Sai Baba Dan tanajinsu khairat da tace mazatazo Mama Rabi ta hanata 



Hakan bai dameta ba Dan daman ba bukatar zuwan nasu take ba Fuskarta rufe take da nikab nan aka shiga kiraye kirayen dalibai Bayan sunyi karatu a basu kyaututtuka har akazo kan sunanta



 Zarah yusufGaban Zarah saida ya bada daram saboda sosai takejin kunyar ratsa mutanen nan Saida aka kara kiran sunanta sau biyu tukwana ta mike Shima saida Asmy ta zungureta tana mata Dariya kamar wacce batason ta taka kasa Haka take ratsa wajen Wanda duk Inda ta gitta sai an bita da Kallo dukda kwayar idanunta kadai ake gani fuskarta rufe take bai hana Kyaunta bayyanuwa ba 



a haka harta isa kan step din mika mata abun karatu akayi amsa tayi tare da Fara rero qira cikin zazzakar muryarta Mai dadin sauraro tsakiyar suratun bakara take karantawa babu mahalukin dake wajen da zaice karatun Zarah bai ratsa sa ba Mutane har wani lumshe ido suke iyaye da dama sunajin inama yarsu ce jin irin yanda take fitar da tajwidi


 Baba ko wani farinciki da annashuwa ce yakeji na shigarsa yana Godiya ga Allah da ya mallakamai Zarah a matsayin ya tayi minti ashirin tana karatu batare da gargadaba tukwana Aka amshi abun maganar tare da yi mata kabbara 



Duka wajen kabbara ya dauka Inda manya daga cikin baki suka mike tare da Fara yiwa Zarah kyauta Bayan ta amsa tayi musu Godiya Malam ta mikawa jinjina mata Malam yayi da hannu Dan daman sunsan Zarah zata fiddasu kunya a taron nan 



Bayan nan Aka shiga bada kyautar karramawa ga dalibai Inda yawaici Duka Zarah ta amshe kyaututtukan saboda duk fagen da akazo ita dince saida taci kyauta ukku daya ta  wacce tafi kowa kokari a ajin ta biyu kuma Wacce bata fashi ta Ukku nutsuwa da girmama malamai



 itama Asmy ta amshi kyauta biyu daya ta maida hankali a karatu daya kuma ta Rashin makara Bayan nan suma sauran dalibai aka shiga basu nasu kyaututtukan sai around 2pm aka kare taro Bayan baki sun tafi Ya rage daga dalibai sai malamai 


nan Malaman suka bawa Zarah kyaututtukan da ta samu duk a emblem ne wasu Ba yanda batayi ba akan malaman su rike sukace a a a nata ne Sosai Malaman sukeson Zarah saboda kwazo da kokarinta Tabbas Zarah tabar makarantar zasuyi Babban rashi Dan duk musabaqar da ta tashi da ita ake turawa kuma ita ke ciyo musu na daya



Bayan sun taho daga Makaranta kai tsaye gidansu Asmy suka nufa a kofar gida Zarah ta tarda Baba Dan ya rigasu tahowa Wajenshi suka nufa Kallonsu yayi ya ce Allah yayi muku albarka Zarah kedin ya ce ta gari da kowani uba zaiyi shaawar kasancewar ki yarshi ina matukar alfahari dake Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari mai tausayi da jin kai



 murmushi Zarah tayi tanajin dadin adduar Baba ta ce Ameen Baba nagode mika masa kyaututtukan da ta samu tayi  nan ya shiga dagawa emblem na farko kudine tsabarsu dubu Hamsin na biyu kuma turmin atamfa na Ukku alquran ne sai sallaya a ciki da charbiCikin fara a Baba ya ce

Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu su tuntubeni akan number wayata kamar haka 07026166526
Ko masu bukatar shiga grp sharhi ko tambaya  hanya a bude take

GAWURTATTU BIYAR TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE 


1 MU GANI A ASA
      _Ummu Affan_

2 ABIN CIKIN WAI
      _Ummu Maher_

3 GUNTUN GORO
      _Mom Islam_

4 GISHIRIN ZAMAN DUNIYA
    _Mrs Bukhari_

 5 AUREN WATA TARA
     _Miss Hajo_


Guda biyar  1k
Guda huu  N700
Guda uku  N600
Guda biyu  N500
Guda aya  N300

DOMIN TURA KUIN KAI TSAYE

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

an asar Niger zasu tura nasu anan

0817 952 3215

Guda biyar  1000f
Guda huu  700f
Guda uku  600f
Guda biyu  500f
Guda aya  300f

TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN 




   _Miss Hajo ce_
821 1553   AUREN WATA TARA 

       MALLAKAR

   Hajara L Sadeq



5  6

Masha Allah natayaki murna yata  Allah sanyawa karatunku albarka  


Ameen suka fada ita da asmy Mika mata kyaututtukan Baba yayi da niyar ta amsa


 girgiza kai tayi ta ce  a a a Baba banason komai a ciki komai na sama na sameshine ta dalilin tarbiya da jajircewar da kayi a gareni 


girgiza mata kai yayi ya ce  na sani Zarah ta amma Bazan amsar miki Komai ba nasan kina da bukatar abubuwa da dama bakya tambayata Dan haka ki biya  bukatunki dasu 



Girgiza kai tayi ta ce  a a Baba wlh bana bukatar komai kafini bukatarsu Dan Allah ka amsa 


Duk yanda Zarah tayi Baba ya amsa kin amsa yayi saida Asmy tasa baki dakyal ya Anshi Dubu ashirin Inda ya mikawa Asmau  sauran kudin ya ce  


Amshi ku tafi Sannan ya kalli Asmy ya ce kiyiwa mamanki Godiya kice nagode Allah ya saka da alkhairi Tabbas Saratu ta cika yar mutunci kuma ta cika Alkawarin aminiyarta mariganyiya Kinga yarinyar nan saboda kawaici bata fadamun akwai maganar Anko ba Allah sarki ashe har tayi muku saida safe take fadamun angode Allah bada lada



 Murmushi Asmy tayi ta ce To Baba  Barwa Baba sallayar sukayi tare da Quran din Inda suka koma gidan su Asmy sai tayasu murna ake nan yan uwa da abokan arziki suka shiga shigowa tayasu murna da Yamma suma sukayi yar karamar walimar su Wanda mamansu Asmy ce ta shirya hakan


Bayan magriba ishai Asmy ta kalli Zarah ta ce Wai kudinnan sis me za ayi miki dasu ki bawa Mama kawai ni ba abunda zanyi dasuMama ce dake jinsu ta ce Har ance babu abunda za a yi da kudi Zarah zandai Aje miki  


Girgiza kai Zarah tayi ta ce Mama Dan Allah ki rike wlh babu abunda zanyi dasu  ke ai tamkar uwa kike a gareni Dan Allah Mama ki rike  



girgiza kai Mama tayi ta ce a a fa Zarah Aje miki kawai zanyi karki kara cewa wani Abu  


shiru Zarah tayi badan taso ba Dan a abunda maman asmy take mata ko jininta ce ita sai haka 


Asmy ce ta ce  Mama babansu zarah yace nayi maki Godiya girgiza kai tayi ta ce 


 Ai Tsakani na dasu ba Godiya Komai nayiwa Zarah Ban fadi ba irin zaman mutuncin da mukayi da mariganyiya da amintar da mukayi a lokacin bamu da hali amma Matar nan bata ci banci ba akwai lokacin da saimun kwanta bacci haka zata buga mana gida na bude naga abinci ne ta kawomun a lokacin muna cikin wani hali da haka zamu kwana bamuci ba muna halin Rashin babu Amma Matar nan bata taba cin Abu Bancishi ba Munyi zama na amana da mutunci da mahaifiyar Yarinyar nan 



Goge hawayenta tayi ta ce Har yau idan ina tuno da zaharau bazan daina kukan rashinta ba mace mai kirki hakuri da juriya Allah dai ya jikanta yasa ta huta


Sosai sukayi sanyi Cikin kasa da murya Zarah ta ce Ameen ganin ta na shirin yin kuka ne ya sanya Mama barin maganar tare da kama musu hirar duniya Har ta samu ta dan warware


 Bayan sunci abinci Cire kayanta Zarah tayi tare da sanya rigar baccin Asmy Dan daman nan gidan take Aje sabbin kayanta saboda su Habiba suke lalata mata su sanye mata kuma bata isa tayi magana ba hakan yasa take ajewa gidansu Asmy 



nan gidan kawai take samun walwala da farinciki Sai wajen 10pm ta wuce gidansu har bakin kofar gidan Asmy ta rakata tukwana ta Koma Zarah koda ta shiga Zaune ta tarar da Mama Rabi na girgiza kafa tana ganinta ta taso tare da Wanke da Mari Dan da bakincikin kyaututtukan da akace Zarah ta samu ta yini hakan ya sanyata huce haushinta na dalili marar ma ana da tushe  nan tahau dukanta tana bala i tana cewa 



Yar iska tun safe rabonki da gidan nan Sanadin mutane su dinga zagina suna kin lalace a hannu na Bayan duk yanda zanyi inayi iya kokari na Amma kullum baki da aiki sai jamun Zagi cikin unguwa Itakuma saratun in gidanta zaki koma saitazo ta daukeki Dan kazar kazarta kuma daga yau bazaki kara fita ba daga gidan bare ki fake da islamiya na kara ganinki gidan saratu wlh duk tsiyar da na shuka maki ke kikaja shine kikayi zaune gidanta yau babu aikin da kikamun uban wani kike tunanin zai maki aikin gidan Dan matacciyar uwarki  



Zarah kuka take sosai ta durkushe tana bawa Mama hakuri anma bata Rabu da itaba da hannu take jibgarta Baba ne ya shigo tun a soro yaji kukan yar lelen nashi 


cikin bacin rai Baba ya shigo Tare da wanke Mama Rabi da Mari cikin bacin ran da idan kaga yayishi tofa rai ya baci ya ce Duk iskancin da kike kikaga ina kyaleki ba tsoronki nake ba Rabi gudun tashin hankali ne me marainiyar Allah tayi miki da Zaki hauta da duka daman an fadamun irin zalincin da kikewa yarinyar nan idan ba Dan kin sameta mai hakuri bata fadamun shiyasa kika maida ita jakar ki to hakuri na ya fara kaiwa Bango daga yau Zahrau bazata sake Wani aiki a gidan nan ba su diyanki aikinme suke idan bazasuyi aikin ba gidan ya rube karewar kazanta kumasannan daga yau Kika Kara daga hannu kika daki yarinyar nan kin daki igiyar auranki a bakin aurenki 


Nuna kanta Rabi tayi ta ce Ni kake fadawa haka Malam  Amfada maki ko akwai abunda zaki iyajinjina kai tayi ta na girgiza kafa na borin kunya Dan Malam bai taba mata haka ba tasan yakai bango Har ya iya daga baki ya furta mata a igiyar Aurenta tofa ya fara gajiya da ita hakan yasanya ta yin lakwas Dan Tasan ta rabu da Malam asirinta ya gama tonuwa Dan duk cikin mazajenta biyar da ta aura babu mai hakurin Malam bazata taba yarda Auransu ya lalaceba


 wucewa ciki tayi kamar zata tashi sama Baba ko Kallon Zarah yayi ya ce Tashi ki shiga kici gaba da hakuri kinji wataran sai labari  Mikewa Zarah tayi ta ce Toh Baba nagode  tare da shiga dakinta tana hawaye har bacci ya dauketa


Washegari koda ta tashi bata sa ran Bata abinci ba Ta na nan zaune wajen 10 koda ta leka ta tambaya ina abincinta Da masifa Mama Rabi ta korota ta ce Daga yau bazata kara cida ta ba Tunda ubanta ya hanata ta girka to itama bazataci shi ba ta nan zaune ta na hawaye  taga shigowar Asmy dakin maza tayi ta goge hawayenta Murmushi suka sakarwa juna Zarah ta ce 


 yanzu nake tunaninki Bestywlhko nima tunaninki ya sanya na taho ta fada tana zaunawa gefen katifar da take kallonta tayi ganin yanda fuskarta ta kumbura Alamun Tasha kuka kamata tayi ta ce Mai ya faru Besty  kirkira murmushi tayi ta ce Bakomai me kika ganihmmm karkiyimun karya Zarah ina gane halin da kike ciki ko baki fadamun ba nakanji a jikina fadamun meyake faruwa  


nan Zarah ta fada mata abunda ke faruwa Mikewa asmy tayi tare da dura ashar ta ce Wlh iskancin Matar nan yayi yawa bari zan gwada mata ni yar zamani ce 



 ta fada tana niyyar fita kamota Zarah tayi cikin Sauri ta ce ki Rufamun asiri sis Dan Allah karkije ki kara jamun ni komai tayimun na barta da Allah 


dakyal Zarah ta samu Asmy ta hakura Kama hannunta tayi ta ce Taho muje gida ki karya  tare suka fito  Mama Rabi ta bisu da harara da tsaki suna isa gidan su asmy nan Zarah ta karya Dan tare suka shiga kitchen suka dafa indomie Bayan sun karya gadon dakin asmy suka kwanta Dan su huta daman Zarah da gajiyar jiya bata saketa ba Aiko kafin kace me bacci yayi awon gaba da ita itace bata tashi ba sai wajen Azahar


 tana tashi tayi wanka ta sanya kayanta a gidan Anko sukayi da asma u da Yamma Mama ta aikesu gidan babbar yayar Asmy dake Aure wata unguwar Gyara fuskarta Zarah tayi tare da shafa hoda Wanda Asmy ce ta sanyata shafawa Bayan ta sanya doguwar Hijab dinta mai hannu tana shirin daura nikab asma u ta rike tana Dariya ta ce Haba Kinga yanda kikayi kyau kuwa please muje a haka Dan Allah  


tana murmushi ta ce Allahko Besty Eh mana ai nikab bakoda yaushe ake sanya shiba itama kalar hijab din ta Zarah ta sanya Bayan sun fito Mama ta basu kudin napep tare da cewa kar kuyi dare to suka fada tare da fita basu jima ba Suka samu napep koda suka isa gidan Hauwau daman sun saba zuwa tare sai nan nan take da Zarah kamar ma itace kanwartata Zarah ko sai wasa take yiwa karamun danta ganin magriba tana gabatowa ya sanya su mata bankwana Suka fito 


dari biyu ta basu waigawa sukayi unguwar suka ga ba Alamun Abun hawa Tafiya suka fara Kadan kadan parking din mota sukaji daga bayansu hakan baisa sun juya ba saima cigaba da Tafiyarsu da suke Zarah ta ce 


Wannan tafiyar da mukayi ai daman karasawa mukayi a kasa munkusa fa Rabi Wlhko ai inbanda magriba da kawai a kasar muka tafi muka ma sai awara da kudin napep din wlh cewar Asmy  Assalamu alaikum warahmatillahi ta ala wa bara katuhu 


Suka tsinkayi Muryar wani saurayi daga bayansu  Zare idanu sukayi tare da Kallon juna ta wutsiyar ido Asmy ce tayi karfin halin amsa masa sallamar yayinda Zarah ta kara yiwa saurinta mai matashin saurayin ne ya ce  Dan Allah yan mata idan ba damuwa minti biyu zaku bani muyi yar magana 


Asmy ce kamar zata tsaya Zarah ta juyo tare da banka mata harara cikin siririyar muryarta ta ce Kiyi Sauri mana mu tafi  munyi masa kama da matan da za a Tara a titi ta fada tana turo baki Tare da tsaida napep da sukaga zata wuce maza tayi ta shiga Asmy ko girgiza kai tayi tare da Kallon matashin saurayin ta ce  Kayi hakuri Malam ba mutunci bane tsare mace a titi shiyasa 


tana gama fadar haka itama ta shiga cikin napep din Cizon yatsa Hafiz yayi zazzakar muryarta na dawo mashi har tsakiyar kansa kyakyawar fuskarta ce ta shiga yi masa gizau rumtse idonsa yayi da karfi tare da budewa ganin napep dinsu na shirin yi mashi nisa ya sanyashi saurin komawa mota ya tada tare da binsu Dan shifa ya ga Matar Aure

Koda suka isa gida Ana gama Sallar magriba Suna isa salla sukayi Bayan sunbawa mama sakon da itama ta bayar a kawo mata ana ishai nan sukayi sallah Wutar da aka maido ne ya sanya Asmy saurin Mikewa tana murna ta ce  alhmdllh daman yanzu ake tsaka da series din da nake kallo a zeywood 


Ta fada ta na kunna kallo Zarah ko na kwance a doguwar kujera nan Asmy ta zauna tana cigaba da Kallon Indian series din da ake hankalinta duk ya na wajen Zarah da ba kallo take ba Ganin yanda Asmy ta maida hankalinta a wajen ya sanyata Fara kallo Sosai taga ana zuba romance love a film din Tuni taji wani irin feeling ya bijiromata tun daga tsakiyar kanta Rumtse idonta tayi sosai tare da matse cinyoyinta lokaci guda mararta ta fara mata wani irin murdawa 


Cikin karfin hali ta na murya dakyal ta ce Sis ki kashe Dan Allah ki kashe ta fada ta na rumtse idoCikin Sauri Asmy ta kashe shataf ta mance da yanayin kawar tata da bata kunna ba cikin Sauri ta je Wajenta tare da kama hannunta ta ce


 Sorry sis Na manta larurarki ne kuma banzata zaki kallaba shysa  murda kawai Zarah take cikinta na mata wani irin murdawa tuni ta fara shafta uwar zufa cikin kidimewa Asmy ta mike Dan bata mance irin bakar wahalar da tasha ba kwanaki Wanda har saida akaje Asibiti shawarar da doctor ya basu ta fado mata a rai cikin Sauri ta mike tare da

Domin magana da marubuciyar sharhi tambaya ko kuma Karin bayani 07026166536

GAWURTATTU BIYAR TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE 


1 MU GANI A ASA
      _Ummu Affan_

2 ABIN CIKIN WAI
      _Ummu Maher_

3 GUNTUN GORO
      _Mom Islam_

4 GISHIRIN ZAMAN DUNIYA
    _Mrs Bukhari_

 5 AUREN WATA TARA
     _Miss Hajo_


Guda biyar  1k
Guda huu  N700
Guda uku  N600
Guda biyu  N500
Guda aya  N300

DOMIN TURA KUIN KAI TSAYE

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

an asar Niger zasu tura nasu anan

0817 952 3215

Guda biyar  1000f
Guda huu  700f
Guda uku  600f
Guda biyu  500f
Guda aya  300f

TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN 



_Miss Hajo ce_ 
822 1359   AUREN WATA TARA 

       MALLAKAR

   Hajara L Sadeq

TEAM GAWURTATTU BIYAR

7  8

Tare da rugawa Dakinsu maganin baccin da Dr ya basu akan idan ta fara haka a bata zai iya taimaka mata ta maza ta fito tare da bude kwalbar maganin Tado kanta Kadan tayi tare da sanya mata kwalbar maganin a baki



 Saida Tasha kusan rabi tukwana Asmy ta janye Ba ayi minti goma ba wahalallen bacci ya kwashe Zarah Ajiyar zuciya Asmy ta sauke tare da zaunawa gefen kawartata 


Mama ce ta shigo kallonta ta yi ta ce Lafiya asmy naga Zarah kwance kamar bata lafiya  kasa da kanta Asmy tayi ta ce Eh Mama bacci ta ke  Okay ta fada tare da komawa kitchen Dan ta dagosu tunda taga kwalbar maganin bacci hannun Asmy 


zarah ita ce bata tashi ba sai wajen la asr ta na tashi taji sauki

Haka rayuwar Zarah taci gaba da wakana da dadi ba dadi danma yanzu ta samu sassauci tunda Baba yayima Mama Rabi wannan Abun bata Kara yunkurin dukan ta ba


 sannan daman su habiba ba wani harkansu take shiga ba Dan magana ma saita kama take hadasu gwarama khairat itace Dan Safiya ma dukda yarinyartarta ta fara kwatsawa dasu Habiba shekararta 13 amma rannan ta hangota suna tafiya da wani wai Saurayi har yana rike hannunta


 irin dabiar yaran gidan nasu Sosai take mata ciwo dan ma Baba yana bakin kokarinshi Amfi karfinshine saboda yanayin aikin da yake ba na zama bane


Neco din su Zarah ta fito masha Allah ta samu 9 credit ranar zokuga irin farincikin da ta shiga ita da kawarta sai tsallen murna suke Suna cikin murna gidan su Asmy aka Aiko wani yaro aka ce Ana kiran  Zarah 


jekace bana nan  Zarah ta fada tana yamutsa fuska mamansu Asmy ce ta ce je kace gata nan Kallon Zarah tayi ta ce yata jekiga waye ne Ai ba a haka 


to Mama ta fada tare da mikewa ta sanya hijab dinta har kasa ta fito Rungume da hannayenshi ta sameshi A jikin motarshi kirar corolla L E sanye yake cikin shadda ash Bakine amma coculate colour bashi da muni haka bazaka kirashi da kyakyawaba


  karasawa wajen Zarah tayi tana jin dari_d ari Hafiz ko tunda ta fito ya kafeta da idanu ya na kara yabawa da zubi da kyan sura uwa uba kyau irin na Zarah dan tunda ya ganta a wajen safka ya kwallafa rai a kanta


 Dan lokacin da suka haduma arashi akayi yaje unguwar wajen wani abokinshi Hakan yasa ya bi mai napep din Har ya gano gidansu Zarah Inda ya nemu information a kanta kuma ya samu bayanin komai a kanta



 tundaga tarihinta da irin wahalar da take sha sosai ya tausaya mata hakan ya kara sawa yaji soyayyarta a ranshi


 Da faraarshi yayi mata sallama tare da cewa fatan na sameki lafiya sarauniyar mata  


Batasan lokacin da murmushi yazo mata ba ta ce waalaikumussalam yaushe na samu wannan mukami haka Ba nadi ba komai a nadani har sarauniyar mata anma bansaniba wannan mukamin ai sai manya 

ai kin fi ma a kiraki da sarauniyar mata saboda kedin ta musamman ce a cikin mataKasa da kanta zarah tayi ta na wasa da zoben hannunta


 Da farko dai su na na Hafiz maaruf Mahaifina tsohon Dan kasuwane kumamanomi a wannan garin namu nine Third thild dinsa A yanzu na kammala Degree dina a  Umyuk Inda yanzu ina shirin jonawa masters wannan shine takaitaccen tarihina


 Tsaki Zarah taja a ranta ta ce  ji shegen surutu kowa ya tambayesa a fili kuwa cewa tayimasha Allah Nice to meet uh


gyaran murya Hafiz yayi ya ce da farko dai tun ranar da na fara ganinki Naji kin tafi da imani na kuma ina sonki so na aure inason ki zama uwar yayana duba da tarbiyarkihankalinki da nutsuwarki a Gaskiya Zarah ki godewa Allah a zamaninnan samun kamarki sai antona Allah yayi miki komai a rayuwa kina da kyau tarbiya ga kuma ilimin addini both side boko da arabi kafin nazo wajenki saida nasan wacece ke ina fatan za amshi tayin soyayya ta


   uhm Zarah kawai tace tare da cewaGaskiya zan fada maka ka fara zuwa wajen mahaifi na ka nemu izini a wajensa Dan bai bani ikon kula kowaba har sai an nemu izininshi sannan nagode da soyayya


 ta na gama fadar haka ta juya ta shiga gida Dan ta tsani namiji mai yawan surutu 


 Hafiz ko yaji dadi a ranshi tunda da kanta ta ce yabi ta iyayenta hakan ba karamar dama ce ta sameshi ba



 Zarah na komawa gida Nan Tabawa Asmy labarin yanda sukayi ta na Jan tsaki  Dariya asmy tayi mata ta ce Uhm nikan banga makusha a wajensa ba wlh daga gani yana da nutsuwa 



Harararta Zarah tayi ta ce Ke wani ganin baki da hankali ma wlh Haba mutum sai shegen surutu ke nifa sanin kankine bansan surutu  



Chab nikam zanso naga mijinki zarah kowa yazo saikince ga aibunshi Asa Nura ma wannan ba Mate dinki bane amma hakafa kwanaki wani daga katsina yazo wajenki saida kika koreshi Kinga Zarah kiyiwa kanki fada 


Kamar yanda ta fada masa da daddare yaje ya samu mahaifinta a waje Inda Yayi mashi bayanin abunda ke tafe dashi Malam yaji dadi sosai Dan dukda a dare ne baiga fuskarsa ba kasancewar duhu  amma a kalaman yaron yasan yana da nutsuwa


 ce masa yayi ba damuwa zai iya fara zuwa Wajenta hakan sosai yayi wa Hafiz dadi


Washegari Baba saida ya sanya aka masa bincike akan Hafiz kuma aka tabbatar masa da yaro ne mai hankali da nutsuwa hakan yayiwa Baba dadi sosai 



Ranar da daddare ya samu Zarah a daki Inda ya shiga mata nasiha tare da cewa  Kinga Zarah yaron nan da alamu ya na da hankali kuma na bincika an bani kyakyawan zato a kansa zai dinga zuwa wajenki har Allah yasa ku daidaita kanku kinji


Dagowa  tayi kamar zatayi kuka ta ce Bab shit karkice komai Zarah kice Allah ya zaba miki alkhairi Dan ba  abunda nake da burin gani a rayuwa da raina sama da aurenki na kagu naga ranar da zan Aurar dake zarah kema ki huta da wahalar gidannan shi yasa kullum Addua ta da buri na naga ranar Auranki  Allah ya baki miji na gari Wanda zai rikemunke da amana 



kasa da kanta Zarah tayi Bayan Baba ya fita daga dakin saida tayi hawaye ita harga Allah Hafiz dinnan bai mata ba Amma yanda taga Baba yana yabonshi kuma ya nuna yanason alakanta dashi dole ta kula shi ko Dan son farincikin mahaifin nata


Soyayyace da shakuwa ta fara shiga tsakanin Zarah da Hafiz Sosai yake nunawa Zarah soyayya da kulawa a nata bangarenma ta fara sabawa dashi saboda mutum ne mai barkwanci kullum yazo sai ya sanyata Dariya hakan yasa ta fara sabawa dashi Saidai duk wata sayayya ko kudi da zai bata bata taba amsa ba ba yanda baiyi da itaba amma bata amsar abun hannunshi


 ta bangaren Mama Rabi ko bakinciki take da Hafiz dinnan dake zuwa wajen Zarah ba irin Karfar da batayiwa Zarah a wajenshi ba Anma yace Eh yaji ya Gani yana sonta Dan kafin yazo wajen Zarah an bashi labarin Mama Rabi ko ita wacece da samarin da take korarwa Zarah


Washegari Zarah ta tashi da ciwon Mara Wanda hakan ya tabbatar mata da perioud dinta na kusa sosai hankalinta ya tashi Dan duk wata a darura takeyi saboda tsananin wahalar da take sha cikin Sauri ta sanya hijab dinta tare da fitowa ta nufi gidan su Asmy 


 Dan bata mance irin sharrin da Mama Rabi take mata ba akan ciwon marar da take akwai lokacin da tace kilama cikine aka zubar mata ake mata rufe rufe hakan yasa ta maza ta zame tana zuwa gidansu Asmy Bayan ta gaishe da Mama a daddafe ta shiga dakin Asmy Inda ta sameta ta na guga kwancewa tayi kan gadon ta na maida numfashi 



Asmy ce ta ce  Lafiya BestyGyada mata kai Zarah tayi tana ida kwanciya kan gadon ta ce Da sauki dai perioud dina ne zaizo wlh na farajin ciwon Mara Cike da tausaya Asmy ta ce wayyo my Zarah Allah dai ya yaye maki wannan larurar Dan larurace wlh ace duk wata sai ka sha bakar azaba hada su suma  


bata Kara cewa komai ba Zarah saboda murdawar da cikinta ke mata ruwan zafi Asmy ta dauko tare jika tsumma take Dan shafa mata a ciki sannan ta hada mata tea mai zafi ta bata ta sha ciwon sai gaba yake Inda Zarah duk ta firirice ta fara fita hayyacinta kafin ka Ce me sai amai nan ta fara kwararashi Asmy dai Sannu kawai take mata Bayan ta gyara wajen mamansu Ce ta shigo ta ce



 Lafiya Asmau cike da damuwa ta ce Mama perioud din Zarah ne yazo cike da kulawa Mama ta ce wayyo Allah sauwake amshi ki maza ku tafi Asibiti ayi mata allurar ta fada tana mika mata dari biyar amsa tayi tare da kama Zarah dake murkashi 


mai napep ta fara tarowa tukwana ta zo ta kamata suka tafi asibitin da suka saba zuwa suna zuwa nurse din tayi mata allura daman ita ke mata duk wata ita kanta tana tausayawa irin wahalar da yarinyar takesha


 Sai wajen magriba Zarah ta samu kanta Taji ciwon ya lafa Asmy itake jinyarta kamar kowani lokaci harta gama perioud dinta


Yau ta  na zaune tsakar gidansu ta na sintar gashinta aka Aiko akace ana kiranta  to ta amsa 


Mama Rabi na banka mata harara saida ta ida sintar tukwana ta mike tare da sanya Hijab ta fita 

 kamar yanda tayi tunani shi dinne dai murmushi ya sakar mata Itama  ta mayar masa da murmushin yake sun taba Hira sosai kasancewar yamma ce Sai wajen magriba da zai tafi kwalin waya kirar hot10 ya miko mata ya ce


 tata ce saboda su dinga waya ko baya nan nanfa Zarah ta ce bata San wannan zancen ba ba irin yanda baiyi da ita ba akan ta amsa amma takiya saboda bata da shaawar abun hannun namiji kuma Baba ma yayi mata wannan kashedin Hafiz badan ranshi ya soba ya juya


Zarah na dakinta ta na karatu taji Asmy ta Banko kofar batayi aune ba saiji tayi ta Rungumeta cikin farinciki ta ce Sis ki tayamu murna ina applying da Mukayi a wayar Mama kwanaki na A B U zaria to yanzunnan sukayo message sun amshemu sannan daman kinga ita ce first choice dinmu s jamb Ranar Monday ma zamuje muyi PUMB kai sis Kinga farincikin da nake ciki


Wow Zarah ta fada ta ce  Gaskiya ni kaina nayi farinciki Sai kuma tayi sanyi ta ce Sis nadai tayaki murna ammani kinsan bamu da halin da zantafi wata makarantar gaba primary da secondry dinma a yaya na yita ina da burin karatu mai zurfi  amma dole na hakura saboda karatun yanxu na masu da shi ne 



 Lokaci guda asmy ta hade rai Tare da cewa Insha Allah tare zamu tafi yanda muka fara tun daga pri tare haka zamu cigaba har university ai idan babuke nima wlh Saidai na hakura da makarantar kuma bari naje nayiwa Baba Bayani  


sakin firar Zarah tayi ta Kama wata sun jima suna Hira kafin Asmy ta tafi


Babansu Asmy ya samu Baba da maganar makarantar da su Zarah suka samu Inda Baba ya nuna masa baida raayin tura Zarah karatun gaba Aure yake da burin yi mata tayi a gidan mijin ta 


shi kanshi babansu asmy baiji dadiba ace yanda yarinyar nan take da tsabar kokari da baiwa Ta tsaya iya sec Dan shi kanshi yasan Asmau ma Zarah ta taka rawar gani sosai a rayuwarta Dan yasan ba wani kokarin kirki gareta ba Amma tare da Zarah ya sanya itama take dagewa take kokari saboda kunsan ance shi abokin mai sayar da turare Shima kullum cikin kamshi yake gashi yarinyar ya yaba da tarbiyarta 100yasan ko makarantar suka tafi baida shakka a kansu saboda bazata bari Asmy tayi wani abun da bai kamata ba.

Post a Comment

0 Comments