Budurcina Hausa Novel by Maman Teddy
New Hausa Novel Written by Aunty Aysha Mamanteddy
Dedication
This book is dedicated to the Almighty ALLAH my creator who in his infinite mercy on me make me to be born in this world in the family of Prof Muhammad Bamalli and my beloved mother Haj Safiya.
Finally this book is also dedicated to my darling husband Alh Usman Umar Tukur Love you always
About Maman teddy - The Author
Da dama na tambayar wacece Maman Teddy A taaice dai Aysha Mohammed Maman Teddy haifaffiyar Garin Zariya ce a Jihar Kaduna. A nan take rayuwa tun daga uruciya har zuwa girmanta A matakin karatu tana da shaidar karatu kan ilimin haa magunguna wanda ta samu a shekarar 2014 Sannan ta yi Polytechnic a Zaria while now she is biologist wato dai ta samu warewa kan ilimin halittu Shes is a teacher, business woman and advertiser tana yi wa mutane talla game da kasuwancin su ta bangare da dama musamman a social media da sauran wuraren kasuwancinta.
Tsokaci
Cike da Wani irin mahaukacin Gudu take Bin lungu da Saon layin da zai Sada ta da gidan su Yarinya ce arama wacce A shekaru ba zata Haura Goma zuwa goma Sha aya ba a Duniya Kuma irin gajerun nan yar gijif can asa sai dai atuwa ce yar lukuta amma duk da wannan iba nata bai hanata yin wannan gudu ba don gudu take dashi kaman mene idan ta fara shi duk laifin da ta Aikata babu mai iya kamata sai dai a acimmata a gida
Tun daga Wajen Soron gidan su kake jin muryoyin mutane da Dama suna fain Phania ce Kai wannan yarinya tana ja ma Uwar ta masifa cewan aya daga cikin matan Gidan Wato Mubashshira Muryar Rahmatu ne ya katse na Mubashshira tana cewa Aa Ai uwar ta zata arika dama tun da ta haifo ta ta kawo ta Duniya take jinya Har yau bata sake lapiya ba kun ga kowa ya watse Kar yanzu ta shigo ta zage mu tasss don ba mutunci ne da Phania ba
Duk wannan surutun da suke yi a kunnen Phania wacce ta tsaya daga jikin soron gidan tana hango su amma idanun su sun rufe da munafurci Matan dake tsakar gidan su kusan Bawai ne har da Mubashshira wacce take Amarya ce bata dae da zuwa gidan ba
Cike da iriwa da Rashin ji irin na Phania ta kutsa kan ta zuwa cikin gidan tana fain Rahmatu Kin ga inda nake samun matsala daku nan Kome ne zamuyi ina yawon faa maku kuyi shi amma kar ku sake Umma ta taji wani Abu Yanzu kin zo bakin tagar ta kina maganganu akan kai na To Na gode ma ALLAH duk rashin jina baa taa kamani da aton warto ba Ko ana lalube Ni a lungu
Saurin kallon ta Rahmatu tayi kana tace Yau kuma sharrin naki kan wane ya faa Phania
Wani irin dariya Phania tayi kana tace Umma ta tana yawon faa mun wannan magana biyu Na farko Shine Phania arya da cuta babu kyau kar kiyi shi Phania don haka Yanzu ga yar Ki can Inna da Salihu a akin isihu Wannan shine Dalilin da yasa ku ka ga ina gudu don na ceto Miki martabar ki dana yar ki garin gudu na zubda ma Atiku mai kayan yaji da Tumatur shine har an biyo Ni gida tun kamin nazo To kun dai ji Ga Inna can a akin Isihu Innalillahi wainna ilaihir rajiunCewan Rahmatu tana kama kai tare da matse Idanu irin na makiran matan gida kamin tace Yanzu Phania sharrin naki har ta kai ga Yi ma Inna Haba Phania shekarun ki nawa suke amma gaba aya kin addabi rayuwar mu
Aa Kar kuyi saurin cewa haka Muryar Daya daga matan gidan Luba ya katse su tana mai cigaba da cewa Phania kin san karya ba kyau ko Me yasa kika ce Kinga Inna a dakin Isihu wanda kowa yasan halin sa tun daga farkon layin nan har wajen ta bai bar masu talle ba matan Aure bare kuma ammata Phania faa mun abubuwan da Umman ki take faa Miki a kullum da kika ce
Kallon Luba Phania tayi kana cike da Haukar yarinta da uruciya tace BUDURCINA
Wannan kaan ne kuma tsokaci akan littafina na Budurcina wanda zai fara zuwa maku nan ba da jimawa ba inshallah
Aunty Aysha Mamanteddy
Karanta: The Sexy Boss Hausa Novel Book
0 Comments