Kyalkyalin Kauna Hausa Novel

kyalkyalin kauna hausa novel


Kyalkyalin Kauna Hausa Novel

EPISODE 1️

Wuraren 1:30 na dare yay parking motanshi wata mahaukaciyan faran Benz gaban wani babban club wanda da kyar yasamu yay parking motan kasancewa yau Friday yau mutane na zuwa club sosai dan weekend start yau gobe ba aiki hakama jibi, dudda girman wajen parking na club din yayi girman wani kauye hakan baisa yasami space ba tsabagen motocin dasuke nan sa’a ma yayi yana zuwa wani mota na fita saisa da awajen street din layin zaiyi parking, kashe mota yayi yafito, wani kyakkyawan dan saurayi ne fari dashi mai suffan fulani fulani da akalla zaiyi 34-35 years yana sanye da jeans da riga masu kyan gaske designers, 

yamaida motan yarufe yafara tafiya yana duba wayanshi dayaji sako yashigo yana dubawa yana tafiya zuwa entrance din shiga dawasu jibga jibgan security hudu ke wajen da bindigogi da bakaken kaya zaka dauka basamudaye ne suna ganinshi kai tsaye suka mammatsa suna gaidashi. “Welcome sir” gyadamusu kai yayi yawuce yashiga ciki, wani lafiyayyen security door ne awajen dakana gani kasan wannan ba anyhow ur common club bane dan ita kanta kofar abin kallo ce. Security door din ne yay magana yace “welcome ur access card please” dan gajeren tsaki yasaki yana tura hannunshi a aljihu yace “I hope ban manta da card dina a mota bama” yay maganan yana karasa tura hannun aljihu luckily yaji katin yaciro ya manna jikin kofan da nan da nan tai acknowledging katin kofan tace 

“Welcome to Xperince” kofan yabudu yashiga ciki, wani kalan hadadden club ne da gabaki daya baimada naija settings, kashiga ciki zaka dauka kana asalin kasar waje ne, duk wani wanda ya isa a club din nan zaka ganshi har yau ba’ayi irinshi a Abuja ba, matane a tsaye a stage strippers suna poll dance waka na tashi, ga maza ga mata wasu a zazzaune wasu a tsaye ana rawa ana spraying dollars kowa na having good time kawai, masu shan giya nayi, masu shakan cocaine nayi, ga customize azul na yawo ta ko’ina ana kaiwa wayanda sukai ordern su, gawasu kalan shisha da babu irinsu a nigeria anan xperince ne kawai ake samu, ga vape anasha suma, idan kashigo club din nan kai karan kanka kasan ana barin kudi, ga security guys daban daban in different corner and spot tsaitsaye da communicative devices a kunnensu kagansu zaka dauka gumaka ne kaman basa numfashi sabida yanda suka tsaya kikam akwana daban daban, wucewa yayi yahau lift zuwa second floor, direct gaban wani office yayi da wasu kattin security guda biyu ke tsaye awajen kai tsaye yakallesu yace “Pablo na ciki?” 

Cikeda girmamawa sukace “yes sir yana ciki” direct hannu yasa yabude kofan yashiga ciki batare dayay knocking ba, wani kalan mahaukacin office ne dayake nan kaman nawani shugaban kasa ga sanyin AC dake tashi aciki kaman kankara, wani kyakkyawan guy ne zaune akan kujeran cikin office din yana sanye dawani Armani white shirt da short nashi daya tsayamai iya knees nashi, kafanshi sanye dawani white nike socks mai tsayi yasaka wani black customize Dior sandals na maza dayay complimenting kayan jikinshi yana aiki da Mac book din dake gabanshi yana typing dasauri dasauri yatsunshi kaman machine idanunshi nakan laptop din har lokacin bai dago yakalli wanda yashigo cikin office din ba, hakan yasa wanda yashigo yaja kujeran dake facing nashi yazauna yana kallonshi kaman wanda yaga wani abu dabai taba gani ba, 

Tundaga kan kafafunshi dayake iya hangowa dan transparent glass office table ne awajen yake kallo harzuwa kan yatsunshi dayake typing dasu, Pablo nada wani kalan yatsu dogaye masu kyau yanda yakeda tsawo haka yatsunshi keda dan tsayi, dogone shi sosai fatanshi baki ne irin baki sidik din nan, ko kadan baida rama wani kalan full gallant man ne dayakeda jikin every women dream, yanada broad fashashen kirji da abs kana ganinshi kasan wannan gym product ne dan he’s really working out and it’s so obvious, yanada wani kalan lips pink yirrrr sosai abin sai yawani kalan haska black face nashi ga dogon hanci kaman kan biro daya bama face nashi wani kalan definite look, 

Yanada manyan fararen idanu dakuma cikan gashin gira black sosai, yanada gashin saje gyararre mai kyau dayakai zuwa gemunshi dayadan tara gashin gemun kadan kuma acike black dake shinning tsabagen jin gyara, yanada cikan gashin suman kai dasuke nan a kwance kanshi wani kalan wavy hair ne dake shinning sosai suka karamai kyau sai kunnenshi daya a huje yasaka wani dan karamin circled earring na gold guda daya, shi kanshi dan saurayin dake kallonshi wani zubin mamaki yake dan inda ace Maheer mace ne yanda samari zasu dinga layi hala tundaga gidansu har bakin anguwa gashi Allah yamai wani kalan mahaukacin farin jini da kwarjini sai kuma uban bakin hali da murdadden hali da Allah yamai.

 

 

Batare daya janye idanunshi dagakan abinda yakeyi ba cikin wata kalan murya dake nan adikile irin muryan nan na no nonsense person ba wasa kokuma fara’a yace “how is my shipment Nas?” Firgigit saurayin daya kira da Nas ya farga daga duniyan tunani dakuma kallon Maheer dayake yadan sosa kanshi yace “I spoke to the captain gobe around 1500hrs zasu iso port na lagos so anything jibi shipment dinmu zai iso nan I assure you Escobar!” Sai a sannan yadago kanshi ahankali yadaurasu akan Nas tareda folding hannunshi a kirji kaman mai nazarin wani abu, murmushi Nas yayi yajaye idanunshi da dan sauri daga kallon da Maheer kemai yakalli about 40grams na cocaine dake kan table din da akai packaging ga wata yar karaman farin roba da aka zuba cocain yar kadan aciki taster yakai hannunshi yadauki yar roban yana budewa yace “coke din nan fa Pablo? Na waye”? Danne hancinshi daya yayi yashaki cocaine din jikinshi nawani kalan tsuma yana kyarma yace “Ya Allah!” Ya maida roban yarufe ya ijiye yana dan mika yace “amman wannan coke din wacce ta iso jiya ne daga Mexico ko dan wlh tayi dadi, har cikin bargon kashina najita, Wallahi tasa kyankyasan kwakwalwata sun watse dukansu sun fara tafiya suna gudu kaman an watsa musu fiyafiya” yay maganan yana murmushi yana daukan roban yana kokarin kara bude roban ya shaki na biyu Maheer yamai wani mugun kallo dayasa ya rufe ya maida ya ijiye roban dasauri yace “you don’t get high on duty nasani Oga!” Cikin wani kalan karisma Maheer yace “good” sannan yacigaba da aikin dayake yi daidai nan wata waya kirar iphone 14 pro max amman customize na gold dake kan table na wajen tashiga ruri kallon screen din Maheer yayi saikuma yadauke kanshi yacigaba da aikin dayakeyi hakan yasa Nas da kanshi yadan fara juyawa sabida yar kankanuwan coke din daya shaka yakalli screen din dan murmushi yayi yakalli Maheer yace “wai yaushe Boss zata dawo ne”? Batare da Maheer yakalleshi ba yace “bakada number ta ne”? Dasauri Nas yace “amman ai the whole empire ansan kaine favorite nata dan haka nasan tafada maka” batare daya kalleshi ba yace “tashi kabarmin office dina” dasauri Nas yace “Boss is obsess with you wlh, you yelled at her, imagine you even Bosses her around Pablo kaman kaine Mai empire dudda dai nasan you guys are partners in business yanzu but ai ita takawoka kaman yanda takawomu muma what’s so special about you dakai kadai takeji take kuma gani dudda akwai maza dai dai sama da maza dari biyu dake mata aiki banda external ones dake kawo Mata hari”? Yay maganan yana kallon Maheer dayay kaman baimasan wani na magana awajen ba, jaye idanunshi yayi yana kara kallon wayan da kusan this is the fifth call yake shigowa wayan kenan daga same number dayay saving da Hajiya, knocking kofan akayi hakan yasa Maheer yadago kanshi batare dayay magana ba yadanna wani boturi akan kujeranshi hakan yasa aka bude kofan aka shigo Manager club din ne yashigo yana sanye da suit black looking smart, cike da girmamawa yakaraso cikin office din yagaida Maheer yace “Sir we need XTC (Ecstasy akafi kiranki, ko methylenedioxymethamphetamine MDMA) saikuma Liquid X (Gamma-hydroxybutyrate GHB)

duk angama da wayanda aka fito dasu yau, kusan guest namu na yau yafi na kowani Friday” dasauri Nas yace “ba last dose of Liquid X aka fito dashi yauba”? Ahankali Maheer yamike tareda jaye kujeran dayake zaune kai baya, bindigar dake kan kujeran kiran Glock 17 Gen 4 yadauka yasoke abayan wandonshi sannan yafara tafiya kaman wani sarki da isa da takama dasauri suka biyoshi abaya kaman fadawa bude office din yayi yafita yahau stairs duk suna biyedashi zuwa sama wanda nan ne supply room na komi yake a club din dakuma kitchen,  kwali biyun XTC yabawa manager yace “lemme make the Liquid X come back in the next 30min” dasauri Manager yace “da kanka yallabai zaka hada mana yau”? Murmushi Nas yayi yace “chemist kake gani anan” murmushi Manager yayi yawuce yafita shikuma Maheer yay wani kitchen dakeda fadi sosai kana ganin kitchen din kasan kwayoyi kawai ake hadawa awajen wani black apron yadauka yadaura asaman kayan dake jikinshi yadauki tukunya yana tara ruwa hakan yasa Nas yasami waje yazauna kan kujera yanabin Maheer din da kallo danshi ko zaa kasheshi dudda shima ya dade a harkan amman bai iya hada daidai da burkutu nan nan ba, Maheer, Maheer sheggen yaro kake gani awajen nan saisa baya ganin laifin Boss data gama mutuwa akanshi dudda suna boyewa but yasan akwai something that is definitely going on tsakaninsu zai iya rantsewa cin juna suke dan Boss tai Kane kane akanshi saisa har yau baitaba ganin Maheer da wata budurwa aduniyan nan ba dudda kusan 30yrs kenan dayasan Maheer, bayama mata magana apart from Boss, ga yaron shegen kwaro ne duk randa Maheer yabar business din nan to empire din nan ta tashi aiki wlh dan kasuwan mutuwa zatayi mut ko abinda yasa Boss keji dashi kenan oho dan Maheer shine business din nan business din nan shine Maheer, ba abanza akamai lakabi da PABLO ESCOBAR ba the biggest drug lord in history, zai iya fadin this aduk inda yashiga ayanzu dai the biggest Drug lord in the whole Africa as a continent is Maheer Escobar na Africa!!!

 

 

Yana cikin tunanin wayanshi yay kara hakan yasa da sauri yakai hannunshi gaban aljihun riganshi yazaro wayan ganin Boss yasa dasauri yakalli Maheer da hankalinshi kekan abinda yake dafawa a kitchen sannan yakai wayan kunne cikeda girmamawa yace “ranki shi dade Boss, Hajiyar mu Maman mu kuma gatanmu” dan shiru yayi yana sauraron maganan da akeyi daga ta dayan bangaren sai chan yadago kai yace “eh gani nan tareda shi yana dama Liquid X ne a kitchen” yay shiru yana sauraron maganan da ake saikuma yatashi yataho cikin kitchen din bama Maheer wayan yayi yace “gashi za’ayi magana dakai” kallon wayan Maheer yayi awulakance kaman baiso yay magana, kaman wanda magana kemai wahala yace “waye”? Wani kalan murmushin kunma rainamin wayau Nas yayi yace “Boss ce Oga takira, Hajiya ce” cikeda halin wulakancin nan nashi yadauke kai yacigaba da juya substance din dake wuta, baki Nas yasaki yana kallon Maheer, almost 1min yabata tsabagen wulakanci sannan yace “tell her am busy” maida wayan kunne Nas yayi yace “Boss kinji shi ko” dan shiru yayi saikuma yace “okay” zaro wayan yayi daga kunnenshi yadanna speaker sannan yace “Boss wayan na speaker” wata muryan yar matace da bazata wuce 45-46yrs ba dan tadan manyanta dagajin muryan authoritatively tace “Naseer ijiye wayan kawuce kafita inaso nai magana dashi” dasauri Nas yadan juya idanu yace “okay Boss” Nas yafada da girmamawa sannan ya ijiye wayan kan table dake wajen yajuya yafita daga kitchen din yarufo kofa.

 

Kusan 1min da fitanshi sannan matan ta sauke ijiyan zuciya ahankali cikeda asalin lallashi tace “wai Pablo so kake kahaukatani kai mesa kacika mugun hali ne? Tunda nasa kafa nafita nabar garin nan kaki kulani, kaki amsa WhatsApp message, text massage dakuma calls dina wai mesa kake wahalar dani ne eh, kanamin fizge fizge kana ciccimini magani agaban su Nas so kake su rainani kaman yanda ka rainani sabida babu abinda baka sani nawa bako” tai shiru tana sauke ijiyan zuciya jin still baiyi magana ba kuma tasan yana jinta rass maganan ce dai bazaimata ba, kaman zata haukace dan kanajin yanayin maganan ta kasan she’s really pain tace “wai mema namaka ne kaketa shareni? Damuwan ka tahanani sukuni nazo Las Vegas nama kasa natsuwa nayi finalizing deal din danazo yi dasu El Chapo, Maheer!” Takira sunanshi da karfi dayasa ahankali ya tsayar da juya liquid na tukunyan dayakeyi for the first time yakalli wayan batare dayace komi ba, cikeda lallashi kaman zata fashe da kuka tace “nine fa your Mami tunda nake dakai nataba offending naka? Kataba fadamin kanason wani abu ban maka ba? Komi nawa dana rayuwata na hannnunka there’s nothing dabaka sani game dani ba, I love you so much babyna dan Allah kayakuri kadaina fushi dani wlh zuciyata zata buga Mah…….” Saikuma tafashe da kuka sosai dayasa yadauke kanshi danshi ya tsani yaga anamai kuka abin na kashemai jiki ahankali yakai hannunshi yakashe gas din yawuce ya wanke hannunshi tsaf gaban tap sannan yadawo gaban wayan yana kallon wayan yanajin sautin kukanta kaman bazaiyi magana ba akufule yace “I hate cry” cikin sigan kuka dasauri matan tace “Toh you refuse to talk to me saisa nakemaka kukan” kaman bazaice komi ba cikeda isa yace “wat am I doing now?” Dan murmushi matan tayi mai sauti tace “miskilin yaro kawai Allah ya shiryamin kai, sabida nacema nadawo yakamata muyi aure shine kake wannan fushin” shiru yayi kaman bazaiyi magana ba yana juye liquid din awasu fancy goruna, idan da sabo tasaba da shariyan shi  dan halinshi ne saida yagama juyewa tass sannan yajuyo yakalli wayan anatse yace “I hate marriage cus it’s nonsense and kinsan da haka” dasauri Hajiya tace “kwarai nafi kowa sani, amman inaso kagane wani abu, kar abinda iyayenka sukama yasa kazo ka tsani aure gabaki daya I love you Maheer tun kana dan kankanin ka nake sonka you know that, na raineka da so, soyayyanka yasa naki aure dudda inada manyan mutanen dake nemana nadinga rainon ka harka girma kawowa yau, nasan bazaka taba so wata ba wannan tunanin ma baya raina dan I know who u are Maheer, I groom you kazama abinda kazama yau nasanka ciki da bai kawai inaso kazama mijina ne sunana should be link to yours forever, I want to bear your child dudda nawuce menopause yanzu but zamuje muga Dr a dubai he knows wat to do, please Maheer help me banson in mutu ba yaro ban aje maimun addu’a aduniya ba, inaso na haifi yaro ko yarinya da jininka ke gudana ajikinta this is my only wish”  dan gajeren tsaki yaja mai kara dan conversation din wani kalan mugun batamai rai yake adikile yace “this will be the last time I will say this to you Maryam!” Yakira sunanta direct da saida taji gabanta yafadi ahankali yace “bazan taba aure ba! And I don’t want children! Infact I hate babies, I hate children, idan kika shiryamin wata magana daban you can call but for now kije kisha iska”. Batare daya katse wayan ba yanaji tana hello hello yashiga cire apron na jikinshi ya yar akasan wajen yawuce yay hanyar kofa bude kofan yayi yafita Nas dake zaune awajen wajen yace “kai ina wayata?” Wucewa Maheer yayi batare daya kalleshi ba sanin halinshi yasa yakoma kitchen din yadauki wayanshi yasa a aljihu sannan yadauki liquid X din daya hada yafita dashi dan kaiwa manager yasan anachan clients na nema.

EPISODE 2️

Wuraren 4:22 wata mota yar daidai kiran toyota Camry tai parking gaban wani babban gida haka da kana ganin ginin kasan asalin ginin da ne daya kwan biyu saidai kofar gidan fes fes babu wani makusa awajen ko datti, parking motan akayi aka bude kofan aka fito anatse wani babban mutum ke fitowa daga motan dake sanye da kayan polisawa dasuka nuna asalin natsuwan shi dakuma manyantan shi acikinsu dan akalla mutumin bazai wuce shekaru 45 aduniya ba dan baida wani jikin tsufa hakanan he look young and fit sosai sai natsuwa da rashin wasa akan fuskanshi, from mere appearance kasan irin strict men din nan ne, maida kofan motan yayi yarufe sannan ya tsaya chak yana bin ko’ina da kallo, gabas yamma kudu da arewa kaman kai nazarin wani abu sannan ahankali yasa hannu yatura kofan gate din gidan yashiga cikin gidan, Babban gida ne sosai da cikin gidan nema zai kara maka confirming cewa old gida ne wannan, babban gida ne  mai katoton compound asalin irin ginin da dakunan ajere suke bawai flat flat bane, sai katoton bishiyan kashu dake tsakar gidan dakuma wata yar karaman yarinya yar kimanin shekaru 4 zuwa 5 dake zaune a tsakar gidan ita kadai kan tabarma ga plate na tuwo agabanta da ba’a zuba miya ba tana kallon tuwon tana kuka mara sauti tana goge hawayen da bayan hannunta kanta babu dan kwali sai gashi dake mata lilo sabida iska dake kadawa yarinyar black beauty da ita kana ganinta kaga bakar bafulatana, anatse yake tafiya harya karasa gaban tabarman ya tsaya akanta, cikin kuka yarinyar ta kalli bakin cover shoe dake gabanta dake kyalli shinning mai wankin takalmi sannan tadago fuskanta ahankali sama takalleshi dasauri tace “Babaa” saikuma ta tashi dasauri tana ture tuwon ta rungumeshi awani kalan shagwabe, for the first time mutumin yasaki murmushi yasa hannu yadauketa yace “Nanan Baba yaya jikin”? Cikin magananta irin na yara amman tana fita tsaf tace “na warke Baba” hannunshi yakai yakama habanta yana kallonta yana kara kallon kwayan idanunta dasuke jikeda hawaye yace “mesa kike kuka”? Sake fashemai da kuka tayi kaman jira take ashagwabe tace “Baba ni baranci tuwo ba ni yoghurt zansha” dan murmushi yayi yaduka yasauketa ahankali yace “dauko hulanki kizo muje to nasiya miki” wani kalan tsalle tayi tareda shiga dakin wajen da gudu yabita da kallo yanadan murmushi ko second daya batayi ba tafito rikeda dan karamin hijabinta tana bashi karba yayi yaduka yana saka mata yace “ke kadai bakije islamiyya ba Allah kaimu gobe zakije dan kinji sauki” yana maganan ya idasa saka mata yadauketa yajuya da ita suka fice daidai nan wata mata da kana ganinta kasan ita ta haifi yarinyar da dan sandan ya fitada ita sabida yanda sukai kama ta leko daidai suna fita murmushi tayi ta koma kitchen din tana kallon wata yar dattijuwan mata dake tuka tuwo a babban tukunya tukunya Lamba biyar kaman na gidan biki irin family pot din nan tace “hala ubanta yafita da fitinanniyan”? Yar dariya Matan tayi tace “kaman kin sani Yaya” dan dariya matan tayi tace “tunda Nana tai yar kyandar nan gabaki dayan mu bamu huta gidan nan ba ai Allah kaimu gobe wlh kobaku turata makaranta ba ninan zan dauketa na kaita da kaina dan bata zama mana agida gobe fitinanniyan yarinya kawai mai hali irin na ubanta” dariya dukansu sukayi, Yaya tace “wai kin sake kiran Yasmeen kuwa? Kemadai kinsan idan mahaifinta yasan har yanzu bata dawo gida ba balle taje islamiyya yau kene zakisha fadanshi Ammi” dan yatsine fuska matan da aka kira da Ammi tayi tace “to nakira nakira bata dauka ba nasan duk yanda akayi tana hanya wani abun ne halan ya tsareta, akanme zaihau yimini fada shi da kanshi fa yadauketa yakaita wajen matan abokinshi dan takoyi girke girke sai yahauni da fada dantai latti” baki Yaya tasaki tana kallon Ammi tace “ohh ba shakka jibi yanda kike magana Ammi saikace bakisan halin mijinki akan yaran nan nashi ba, mutumin da yake tsaye kan yaranshi koke uwarsu baki isa ki gwadamai kinfishi sanin wani abu game dasu ba nidai sake kiranta dan wlh yau yafara masifan nan nashi na yan sanda babu abinda yashafeni wlh, ban lekowa ma balle nasa baki nabada hakuri, itakuma Hajjo bazata dawo daga gidan suna bane tadaisan yanzun nan da Malam da mijin nata zasu dawo daga kasuwa ko”? Ammi data fito da waya tana kokarin kiran number datai saving da Yasmeen ne tace “ai yanzun nan zakiga Hajjo dazu da muka leka mata gidan batace ana la’asar zata dawo ba” wayan takai kunne yagama ringing still shima ba’a dagaba cikeda damuwa tace “wlh bata dagaba” baki Yaya ta tabe tace “nidai turomin kwanukan nan kigani mu kwashe tuwon nan na shige daka” turamata kwanukan tayi tashiga kwashewa ita kuma Ammi na kwasa tana fito dasu tana ijiyewa kan tabarma daidai an bude gate an shigo tadaga kanta, mijin nata ne yashigo da Nana a hannunshi dake rikeda goran yoghurt din Habib, shikuma yarike wata yar leda da yoghurt guda uku keciki yakaraso bata ledan yayi yace “gashi kirabama yara idan sun dawo” murmushi tayi tace “sannu da zuwa Baban Nana, ya aikin” ahankali yace “Alhamdulillah” takalli Nana dake kiciniyar bude yoghurt din tace “kawota na bude miki” makema Maman nata kafada tayi tabama Babanta tace “ni Babana ne zai budemin” kwafa Ammi tayi tace “nida kene agidan nan” murmushi Baban kawai yayi yabude yabata wani kalan zama ta gyara tanasha hakan yasa yakalli Matar tashi yace “Yasmeen da Farida fa suna islamiyya”? Dan kallonshi tayi itadai tunda yake bata taba ganin uba da baya wasa da lamarin yaranshi irin mijinta ba, anatse tace “Farida dasu Sa’a duka suna islamiyya” dasauri yace “Yasmeen fa”? Ahankali tace “har yanzu bata dawo daga wajen Maman Intee ba, kuma ina kiranta bata dauka, maybe basu gama aiki dawuri bane” take yanayin fuskanshi ya chanza, duk wani walwala da annuri na kan fuskanshi bacewa yayi bat, hannunshi yatura cikin aljihu dasauri yaciro wayanshi kiran Infinix zero number dayay saving da Yasmeen yay dialing saidai harta katse ba’a dagaba, dasauri yamaida wayan aljihu yajuya hakan yasa Ammi tabishi dasauri tace “ina zaka kuma Baban Nanah ko kayan aiki baka cire ba fa”? Batare daya juyo yakalleta ba yace “zanje gidan Maman Intee, nagayamata anything 3:30 tasallami Yasmeen sabida kafin hudu tadawo gida ta shirya tawuce islamiyya” hannu yasa zai bude gate karaf Ammi tarike hannunshi hakan yasa yajuyo yakalli fuskanta,  anatse tace “dan Allah calm down, nasan ko’ina Yasmeen take yanzu haka tana hanyan dawowa gida ko kaje zakusha bambam ne, you are being over protective dayawa over this girls Baban Nanah, Yasmeen is a big girl remember?” Tai maganan tana kallon kwayan idanunshi Anatse trying to calm him down tace “Yasmeen is 20 yanzu, she’s not more yarinyar 12yrs old da zaka kasa ka tsare akanta haka please kadawo gida ka chanza kaya nakawo maka tuwo kaci Yasmeen zata dawo yanzun na. Besides yaune rana na farko data makara tunda tafara zuwa koyan su cake din nan awajen Maman Intee da kaine da kanka kasata please kazo kai wanka kahuta” tunda take maganan kallonta yake kaman mai nazarin wani abu kaman kuma baraiyi magana ba sai chan cikeda ihu dakuma fada ya nuna kanshi yace “are you telling me nazo na zauna na natsu y’ata daya kamata tadawo gida since bata dawo ba har zuwa yanzu kusan 5:15 yanzu? Kin zaci yanda baki sonsu baki damu da su ba haka nima nake? Diyarki daya kamata 3:50 ko 3:45 tana gida baki ganta ba baraki saka hijabi kibi hanya ba kin zauna agida ko ajikinki yanzu zanbi sahun ta kuma kinaso ki hanani what is your problem Hajara?” Yay maganan da tsawa cikin fushi da saida Yaya ta leko daga kitchen ta tabe baki takoma ciki abinta ita daman tasan za’ayi haka, cikin fushi yace “kina banzan tar mini da yara kina wulakanta mini su, nashigo gida na tarar da y’ata my sick little girl da duka duka yaushe taji sauki daga kyanda tana kuka she wants yoghurt baraki iya siyamata ba idan ma baki da kudin ne baraki ara ba in yaso nadawo saina biya amman no kin barmin ita tana kuka ita kadai a tsakar gida ke kina kitchen ko ajikinki, tun yanzu da raina da lafiyata kina neman maidamini da yara marayu” baki Ammi tasaki tana kallonshi takasa cewa komi kawai ganin ta inda yake shiga batanan yake fitaba balbaleta kawai yake da masifa, hannunshi ya fizge yace “when it comes to yarana don’t ever, I mean it don’t ever try to tell me wat to do or wat not to do” yawuce azuciya yabude gate yafita, sanin duk inda take yanzu tana hanya kuma bayaso yasha bambam da ita yasa yashiga tafiya da kafa bai dauki motanshi ba zuwa bakin junction na anguwan su yana kallon titi.

 

 

Wata yar yarinya ce yar doguwa kadan dan bawani tsayin kirki ne da ita ba at the same time kuma ba gajera bace kana ganinta kasan bazata wuce shekaru 20 aduniya ba, wani kalan coffee skin ne da ita irin wayanda ake cema glass skin dinan, kana ganinta kaga mahaifiyarta Ammi saidai Ammi tafita duhu ita batakai Ammi duhu ba, tana sanye da hijabi dark blue mai hula daya kaimata har kasa anma hijabin hannu data fito da hannun data rike wata yar simple jaka da shi baki, wani flat takalmi ne akafanta baki irin na yan 1500 din nan masu hanci daya kara haska kananun kafanta da babu safa, dudda hijabinta mai hulane kana ganin tulin gashin kanta da some suka kwanta agoshi ta sabida dan zufan datayi na tafiyan datakeyi akasa, tanada wasu kalan manyan idanu da kwayan idanunta are complete gray kaman idanuwan yar tsuntsuwa, ga cikan bakin gashin gira dana idanu sai dan karamin dogon hancinta da lips dinta yan dis so pink dasu kaman na jiririyan da aka haifa yau, tana tsaye akan titin  tana juye juyen da kalle kalle da kai trying ta tsallaka titi dan titin is so busy gashi two sided titi ne kasancewan yamma kowa na kokarin komawa gida.

 

 

“Yasmeen!” Kaman daga sama taji muryan Babanta na kiranta dasauri takalli saitin inda taji muryan gabanta nadan faduwa tana zaro idanunta fiki fiki kaman wata zabiya looking so calm and scared atare, hannu Baba yadaga mata alamun ta tsaya inda take hakan yasa anatse ta gyadamai kai tana hadiye miyan dataji ya katse abakinta kirjinta na bugawa still ganin Baba, tsallaka titin Baba yayi ahankali yakarasa daidai inda take yana kallonta ahankali dakuma sauri tana dari dari tace “Baba ina wuni” batare daya amsaba yakai hannunshi yakama hannunta kaman wata yar karaman yarinyan 5yrs yashiga dadduba titin sannan ya tsallako da ita yana tafiya da ita suka shiga layinsu ko kunyan jama’an anguwan su baijiba gam yarike hannunta yanda kasan yasaki hannun zaa dauketa ne suka shiga tafiya tana binshi ahankali kanta akasa har zuwa gida. Bude gate yayi tashiga sannan yashigo shima tareda sakin hannunta yamaida kofan yarufe sannan yace.

 

 

Yace “ya akayi kikayi latti baki dawo ba” wani kalan ijiyan zuciya tasauke kana ganinta kasan itama duk atsorace take yanda kirjinta ke bugawa har a idanunta kake gani lips nata har rawa rawa suke tace “Baba bansamu keke bane kwata kwata shine nadawo akafa” cikin fushi kaman zai rufeta da duka yace “maisa baki kirani kingayamin baki samu keke ba?” Dan hawayen datake rikewa ne ya sauko mata dukta rude tashiga tura hannunta cikin jakan hannunta taciro wata yar techno phone rakani toilet tanunamai tace “Baba wayana yafada cikin zobon damuka yi ne, shine Maman Intee tace nabude naje nasa a shinkafa, saida zan tafi nadauko nahada na kunna ta kunnu amman anata kirana bana iya dauka har Mama ma takirani ban iya na dauka ba Baba kayakuri dan Allah” takarashe maganan tana sauke kanta kasa hawaye na saukowa daga idanunta yana sauka akasa gabanta faduwa kawai yake sabida tsoro, dan ijiyan zuciya Baba yasauke yana kallonta still yace “bani wayan” dasauri ta mikamai, karba yayi yace “wuce kije kicire kaya kiyi wanka kici abinci” gyadamai kai tayi tajuya ahankali tawuce, dakinsu tashiga Nana tabiyota dan aduniya Nanah nason Yasmeen sama da kowa na gidan, dan Yasmeen nakawo mata kayan dadi dasauri tace “Anty Yasmeen sorry Baba yasa kinyi kuka, nace kidawo ni kidaina kuka idan ana miki fada” wani kalan murmushi Yasmeen tayi takai bayan hannunta  tagoge fuskanta da sauri tace “nadaina” sannan tazauna kan katifar su dasauri itama Nanah tazo tazauna kusada ita tace “Anty Yasmeen Baba yasayamini yoghurt kuma narage miki nawa bari nakawo miki” ganin zata tashi yasa Yasmeen dasauri tarike mata hannu tace “tsaya tukunna” tace “yajiki kin warke nakawo miki cake da zobo” dasauri Nana tasauka dagakan gadon tana tsalle sosai Yasmeen tabude jakan data dawo dashi taciro cupcake guda daya tabata da zobo na gora daidai nan Ammi tashigo dakin ganinsu yasa Ammi tace “sai yashigo yaga baki wankan dayace kije kiyi ba kika zauna kika biyewa Nanah” dasauri ta tashi hakan yasa Ammi takalli Nana data shiga bude ledan cake din tace “kidaici ahankali dan kika fara zawo da ubanki zan barki nasan bazaiji kyashin wanke kashin yaranshi ba” dariya Nana tahauyi tana kallon Ammi cikeda yarinta tace “Ammi ai Baba na wankemin kashi idan nayi a po yakuma je bayi ya zubar tuntuni” tsaki Ammi tayi tawuce tafita daga dakin itakuma Yasmeen tadaura zani tasa hula akai tafito waje bucket tadauka na ruwa takai bayi sannan tadawo dakin Yaya tashiga tasameta zaune a tsakar falo tana cin tuwo tace “Yaya ina yini” kallonta Yaya tayi tareda washe baki tace “sannu yar nan jibi duk kinbi kin zuru zuru sabida fitinar ubanki Allah dai ya kyauta, Allah yakawo miki karshen fitinan mahaifin nan naki kisami miji ki aure ki barmai gida sai muga zai dinga bikin gidan mijinki ne yana bibiyan lamarinkj, jeki wankan ki kafin yafito yamiki wani sabon fadan” murmushi tayi tamike tsaye tafice Yaya tabita da kallo yarinya har yarinya amman fitinan ubanta yasa har yau ko mashinshini batadashi saisa ita tayi alkawari duk iskancin Baba yayi amman wlh barata bari yahana Sa’anta sakat ba, idan saurayinta yazo zance turata zatayi Sa’adatu ce kadai diyarka mace dan haka barata bari ya cuci rayuwanta ba shidai nashi yaran Yasmeen da Farida da Nanah karama yacigaba da musu haka sukai kwantai yakada su a nono yasha atoh, tana cikin tunanin taji sallaman yaran gidan an dawo daga islamiyya hakan yasa ta leko, yaran Hajjo ne agaba dan sune kananun yaran gidan dama su hudu manyan biyu maza sai mata yan shekaru 7-7 yanbiyu Hasana da Husaina, sai yaranta biyu maza Aliyu da Bashir dasuke nan sa’onnin Farida 15 yrs, sai Sa’adatu data girme Yasmeen da shekara daya ita she is 21, dukansu anatse suke ganin motan Baba awaje ansan yana gida, gabaki dayansu dakin Ammi sukayi dan zuwa gaida Baba.

 

 

 

Yana zaune a falo bayan yayi wanka dan shi adakinshi akwai bayi yana sanye da farar jallabiya suka shigo atare dukansu sukace “Baba sannu da zuwa ya aiki” binsu yayi da kallo one by one kaman mai nazarin abu kafin yayi murmushi yace “Alhamdulillah” kafin ahankali yace “kuje Ammi taraba muku yoghurt dinku sai ayi shirin salla” atare dukansu suka tattashi karaf idanunshi yasauka kan jelan gashin Sa’a daya fito dan kitson gaba ne akanta babu wasa akan muryanshi yace “Sa’adatu” adan daburce tajuyo tace “Na’am Baba” wani kalan mugun kallo yamata yace “me gashin nan ke nufi daya fito” dasauri takai hannunta tana maida gashin dukta rude tace “wlh Baba bansan yafito bane bazan karaba” mugun kallo yamata yace “next time kisaka hula kafin ki daura hijabi akai, gashi suturce shi ake kinajina” dasauri tace “eh naji Baba” “tafi” yafadi ahankali.

Karanta: Yar Waye Complete Hausa Novel

Post a Comment

0 Comments