Life Partner Hausa Novel Part 2
Thanks to Almighty Allah for giving me ability and power to start the other part of the book _SHARIKHAYATI_ many thanks to my follwers fans and Family i luv u all
Kwance Ummi ta sameta ta rufo da blanket jin motsi yasa tayi saurin goge hawayen idanta ta tashi ta zauna Ummi ta zauna gefenta cike da damuwa ta ce U havent eat dear dan turo baki tayi ta ce Na koshi Ummi shiru Ummi tayi tana kallanta ganin yadda ta kara mungun rama akan da ta sauke ajiyar zuciya ta ce To me zakici Tayi saurin girgiza kai ta ce Banasan abinci kuma Ummi ta ce Me zakici to idan ba abinci ba or do u need tea Ta girgiza kai Ummi ta ce Conflask Ta kara girgiza kai ta ce Awara nakeso Ummi ta ce To bari na bawa Saudatu ta samo maki tashi muje kasa dan noke kafada tayi kamar zatai kuka ta ce Ummi bacci nakesan yi Ummi ta kamo hannunta ta ce Sai kiyi a kasan ai zakuyi sallama da Mummy ne beside that ma banasan kina zama ke kadai dan kwalinta Ummi ta daura mata sannan ta kama hannunta suka fito a dakin Very slowly ta dinga bin Umminta har suka sauko a steps din Mummy dake kallansu ta ce Lafiya dai Ummi?
Ta ce Wai Awara zata ci gefen Mummy Rafiah ta zauna ta ce Mummy tafiya zakiyi Mummy ta kamo hannunta ta ce Insha Allah ina jiran driver ne but kullum zan dinga zuwa kallanki harki samu sauki sosai abinda nakeso dake shine ki daina kukan nan idan Allah ya rubuta abu zai faru babu mahalukin daya isa canzashi shi kuma Yusuf ki watsar da kashin sa ki saki jikinki ki daina damuwa dashi banda hauka irin naki ma mutum yaci amanarki haka amma ki zauna kina kuka akansa share hawayen idanta tayi tana kallan Mummy ta ce Ni bana san shi kuma i hate seeing him ko mai kamarsa banasan na gani what is making me to cry is Fashewa tayi da kuka ta kasa karasawa Mummy ta bata side hug ta ce Dan ya barki da ciki a kanki aka fara Ke dai ki kula da kanki ki haife abinda yake jikinkin ki kawai ina guje masa ran da zai zo yana blaming abinda kika haifa dan dansa ne wallahi babu me rabani dashi duk duniyar nan saina wulakantashi kamar yadda yayi mana sai na sa shi kuka da kunci na har abada kuma da ba nasa bane kece uwarsa kece ubansa ita dai Rafiah sai share hawayen idanta take bayan haka ta zame akan sofa ta kwanta akan carpet ta rufe idanta tana addua wani zafi da takaici take ji deep down her ba dan ba dan ba da tayi addua Allah yasa cikin ya bare itama ta hutawa rayuwarta.
Bayan 10 minutes Saudatu ta shigo da warmer a hannunta Ummi dake zaune suna hira da Mummy ta ce Kin samu Saudatu ta ce Ehh na samu Ummi ta daga Rafiah ta ce Dear ga Awaran an kawo maki a hankali ta bude idanuwanta tana kallan Ummi ta ce Im sleepy Ummi ta ce I know try and eat ko kadan ma tin safe bakici komai ba gyara zama tayi ta jingina da jikin kujera sannan ta bude warmer din fork Saudatu ta mike mata ta fara cin Awaran daga Ummi har Mummy kallanta suke kai kace tayi sati bataci komai ba na bakinta baya karewa take saka wani su kam hakan yayi musu dadi indai zataci ai komai zaizo da sauki kusan rabin warmer din ta cinye sannan ta rufe ta ajiye a gefenta ta ce Anjima zanci wannan Ummi ta danyi murmushi tana kallanta ta ce Ba wanda zai ta6a daga haka ta kwanta ta limshe ido nan da nan bacci me nauyi ya dauketa Ba jimawa driver yazo daukar Mummy a hanyarsu zuwa gida yake fada mata Jawad ya dawo with surprise Mummy ta ce Har sunyi landing ya ce Wallahi Hajiya kafin naje daukoshi wani abokinshi ya kawo shi gida Mummy ta ce Inaga dai sanda ya kirani yayi rabin tafiyar
Anty Amina ce zaune a parlorn Ummanta tana shan exotic lokacilokaci takan kalli Anty Rahama dake ta trying number Anty Khadija amma yaki shiga Anty Amina tayi murmushi ta ce Maman Leemah wai menene damuwarki akan Khadija ne Naga randa abin ya faru munyi magana da ita tace sun bar kasar Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce Duk tasu Anty Amina ta ce Ehh mana ni lokacin kaina ya dau caji ban gaya miki ba ga zaman dole na asibiti.
Anty Rahama ta ce Amma tace tayi aure a Kaduna da mijin ta wuce kenan Anty Amina tayi dariya ta ce Kema kinsan ba zata harshi ba ai mijin da aka zautarwa hankali ya bar matarsa da manyan yayansa ya aureta ta ina zata barshi ai suna caan ko wacce kasa Allah masani amma dai ni banga abin tada hankali dan baki sameta a waya ba ina dai burinmu ya cika shikenan sai mu barta ta sha iska Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce Hakane kuma Allah ya raka taki gona daga haka suka tafa Anty Amina ta ce Atooh haushinama yarinyar da tai ciki koba komai zasu danganta dan da Yusuf Anty Rahama ta mata wani kallo ta ce Taab ai kuwa wannan yayar uwartan ba yarda zatai ba lokacinfa da mukaje da Yah Muhammad gidan Yusuf wuka ta dauka tana nemansa daki daki wai saita kashe shi nasan dai ko zafin haushine ya sata haka baxa dai ta bari ya kar6i abinda Rafiah zata haifa ba ke nifa mamaki abin ya bani banyi tinanin wannan figigiyar zata daukar ciki da wuri ba gaki nan zabgegiya dake shekara kusan 5 ba labari nan da nan Anty Amina ta hade fuska ta ce Dan Allah kimin cikin nan idan zaki iya ba dai Allah ke bayar ba nayi maganin harna gaji babu labari kema naga a shekaru 22 da kikai gidan mijinki ya dya kawai kika haifa Anty Rahama ta ce
Amma dai na haifi dayar ko to dan Allah kema kiyi zuciya ki haifo ko nakashashshe ne Anty Amina ta mike ta ce Sai dai ke ki haifo gashi mun fara gani kin haifo mai cuta cushion Anty Rahama ta cilla mata cikin 6acin rai ta ce Ki shiga hankalinki Amina karki kara kiramin Ikleemah da mai cuta fitowa Umma tayi a daki taja Anty Rahama tana bata hakuri suka shiga ciki bayan nan ta fito ta rarrashi Anty Amina ma wai ai sai ace basu da hadin kai kuma abin kunya ne suyi fada a junansu ita dai Anty Amina baki kawai ta ta6e taci gaba da shan exotic dinta
Fuskarsa dauke da murmushi ya shigo parlorn Mummy ta juyo tana kallansa ta ce Mutanen Cyprus ya dan shafa tulin gashin dake kansa ya ce Ina yini Mummy ta ce Lafiya kalau have a seat ashe harka dawo ya ce Ehh kusan awana 1 ma fatan na sameku lafiya Ta ce Alhamdulilah mikewa yayi yana kallanta ya ce Zan answer call ne ta ce Alright no problem daga haka ya fita a parlorn part din Maminsa ya shige hade da sallama Abi na zaune a gefen Mami sai Ikram dake kan carpet a zaune Jawad ya danyi kasa da kansa ya ce Ashe ka dawo na dauka zaka kirani na dauko ka Abi ya ce U dont have to worry son kai da ka dawo a tafiya Sadeeq ya daukoni kan kujera Jawad ya zauna yana kallan TV Abi ya kalli Mami data dan hade fuska ya ce To meyasa bakije yau ba.
Ta juyo tana kallansa ta ce Naga dai an sallameta har sun koma gida gidanma kullum zan dinga zuwa kenan Abi ya sauke ajiyar zuciya ya ce U have to go asibiti da ban gida da ban dont make me repeat my self kije kawai ki duba ta tashi yayi ya fita a parlorn Mami ta bishi da wani irin kallo Jawad dake kallanta ya ce Whats going on Mami Dan karamin tsaki taja ta ce Ina kana da labarin auran Rafiah wanda akayi bayan kwana biyu da tafiyarka ba karamin bugawa zuciyarsa tayi ba ya daga mata kai yana kallanta Mami ta ta6e baki sannan ta ce Shes divorced with shock ya juyo yana kallanta ya ce Divorced ta ce Saki ba ya saketa saki daya innalillahi Jawad ya dinga furtawa yana kallan mahaifiyarsa Mami ta ta6e baki ta ce Wallahi sakin wulakanci daya bata takardar ya bar gidan shida matarsa har yau baa san inda yake ba ya tafi ya barta da karamin ciki inka ganta kamar ka hureta ta fadi ni cewa nayi ma da zubar da cikin sukai yarinyar dako 18 bata cuka ba sanda naje sunanta Ikram dina tafi shekara 1 kasa daina kallan Mami yayi lokaci daya yaji komai nasa ya tsaya musamman data ambaci ciki Mami ta gyara zamanta ta ce Ni gani nake saboda cutarta ya gujeta yanzu a zamanin nan yaushe zaka auri mata mai ciwan zuciya duk wata fa sai sun kar6i magani ga uban tsada shi kuwa inaga yayi na Allah yace ya gaji ba dan ubanta nada dukiya ba inaga gidan da zasu zauna ma sai ya gagaresu Tashi Jawad yayi ya shige daki yana rufo kofar idanuwansa suka cika da hawaye bai bari sun zuba ba saima murmushi da yayi ya dauki key din motarsa dake kan mirror din dakin jin an bude dakin yayi saurin juyawa Mami ta ce Ya muna magana zaka tashi ka barni ba excuse ya ce Na tina akwai inda zanje ne ta ce Ina Ya dan shafa kansa yana kallanta ya ce Wajen aiki akwai papers din da zan kai musu wanda na taho dasu Mami ta ta6e baki ta zauna bakin gado ta ce Haka dai kullum aiki aiki idan dai kayi aure barin wannan kotun zakayi ka nemi wata a hankali ya ce Ohk saina dawo daga haka ya fita a dakin
Driving kawai yake amma gaba daya tinaninsa ya tafi wajen Rafiah minti 10 ya kaishi kofar gidan yayi parking a waje sannan ya fito walking gently ya tura gate din ganinsa yasa Mustapha ya kara bude kofar yana masa sannu da zuwa daga masa hannu yayi ya nufi entrance din gidan yana murda handle din yaji kofar a bude ya shiga parlorn da sallama Saudatu dake jera dinner akan dinning ta ce Ina wuni ya ce Lafiya kalau Ummi na nan Ta ce Ehh bari in mata magana upstairs ta nufa ta kwankwasa dakin Ummi bayan an bata izini ta bude dakin ta shiga da sallama Rafiah na kwance akan gado Ummi na rarrashinta dan wani saban kuka ta kafa musu tinda ta tashi a bacci Ummi ta kalli Saudatu dake tsaye gefe ta ce Kin gama abincin ne Ta ce Ehh na gama kinyi bako ne a kasa Ummi ta ce Bako kuma at this time Babbane Saudatu ta girgiza kai ta ce Ehh babbane dogo dan fari haka yana da gashi me yawa a kansa sosai zuciyar Rafiah ya buga dan tinaninta ko Yusuf ne ta ruko hannun Ummi kamar zatai kuka ta ce Dan Allah karkije Ummi Ummi ta ce Why Rafiah bari na gani ko waye daga haka ta zame hannunta ta nufi kofa ta fita saukowa akan gadon Rafiah tayi tana kallan Saudatu ta ce Fari ne Saudatu dake tsaye tana kallanta ta ce Aa amma dai ba zaa ce masa baki ba ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta kwanta dan tasan Yusuf yana daya daga cikin mutanen da zaa kira su asalin farare a hankali Saudatu ta ce Allah ya baki lafiya daga haka ta fice a dakin Tana saukowa ta sami Jawad da Ummi suna gaisawa yana mata jajen abinda ya faru Ummi ta danyi murmushi ta ce Toya zamuyi haka Allah ya tsara mana da munsan haka zai faru ko auran baza ai ba to amma Allah shi yake tsara komai a duk lokacin daya so Jawad da kansa ke kasa ya ce Hakane Ummi ta ce Bari na turo ta ku gaisa daga haka ta mike ta wuce upstairs kwance ta sameta tayi shiru ta kurawa window ido Ummi ta kamo hannunta ta ce Daughter kifta idanta ta danyi sannan ta kalli Ummi ta ce Who was d visitor
Mum Ummi ta ce Ahmad ne kije ku gaisa tsayawa tayi tana kallanta bata dai ce komai ba Ummi ta ce I mean Jawad a hankali ta ce Ohh daga haka ta mike hijab Ummi ta dauko mata tasa sannan ta ce U wash ur face duk idanki ya kumbura a hankali ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta goge idanta with clean towel sannan ta fito daga haka ta fita a dakin ta wuce downstairs tin tana sakkowa yake kallanta ko kiftawa babu ita dai kanta na kasa ta karaso parlorn da sallama zama tayi akan carpet ta ce Ina yini ya ce Fine how are u then Silently ta ce Same Jawad yayi shiru yana kallanta dago kanta tayi suka hada ido tayi saurin dauke kanta a hankali taji muryarshi ya ce Ya karfin jiki Ta goge hawayen idanta ta ce Alhamdulilah tinda ta rife bakinta hawaye suka dinga sakko mata tana sharewa da hijab dinta Jawad ya danyi kasa da murya ya ce Destiny kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa so u dont have to cry one day one time u will laugh fashewa tayi da kuka ta ce I will never laugh again Ya Jawad to laugh for what Kasan zafin da nake ji deep down me ni kadai nasan abinda nake ji so nobody should tell me i will laugh one day daga haka ta kifa kanta akan gwiwowinta kallanta ya dinga yi daga inda yake zaune jiin ta sausauta kukan da take ya ce May be shi din ba alkhairi bane a tattare dake Allah ya raba ku ne saboda ki samu wanda ya fishi alkhairi just erase all ur bond together with him ki manta dashi a rayuwanki so dont cry for him pls ta share idanta ba tare data kalleshi ba ta ce I have to cry Yayah he divorced me without any reason ya azabtar dani a gidanshi ban gayawa kowa ba after all ya tafi ya barni da cikinshi sarkewa muryarta tayi hakan yasa tayi shiru tana kuka kasa kasa Jawad ya ce No u dont have to ai shi da na kowa ne i can take care of the unborn child and still after his birth so u forget about that man i beg u a hankali kawai ta daga masa kai ya ce Promise u wont cry again ta ce Yes ya ce Yes what Ta ce I cant make a promise to u nasan sai nayi saboda yin kukan kadai zai yi preventing dina from heart attack inajin dadi idan nayi Jawad ya limshe idanuwansa ya ce To kiyi kadan dagowa tayi tana kallansa yana bude idanuwansa tayi saurin sunkuyar da kanta ya ce I think i have to go kiyiwa Ummi sallama Allah ya kara maki lafiya silently ta ce Ameen nagode daga haka ya mike ya fita a parlorn ta bishi da kallo yana fita compound aka bude gate motar Sadeeq ta shigo compound din sosai Mami ta hade rai tana dalla masa harara yayi karfin halin ya karasa parking lot din yana kallanta ya ce Dama na gama abinda nake ne shine Wucewa tayi ta barshi nan wajen a tsaye ya juyo yana kallan Sadeeq da fitowanshi a motar kenan ya ce Till u come back daga haka ya nufi hanyar gate Sadeeq ya bishi da kallo
_08103810398_
_ _
_MY LIFE PARTNER_
_Part 2_
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
_We are here to Educate Motivate and Entertain our Readers_
_By FATIMA _
_2_
Shiru Rafiah tayi ganin Mami ta shigo parlorn ta mike a hankali tana goge hawayen idanta ta ce Sannu da zuwa Mami ta zauna kan kujera kamar bazata amsa ba sai kuma ta ce Sannu ya karfin jiki silently ta ce Naji sauki Mami ta dago kai tana kallanta ta ce A hakan Rafiah ta daga mata kai sai kuma ta ta6e baki ta ce Aike da jin sauki sai kin haife wannan jarabar ta cikinki bayan haka kin samu me auranki shine zaki ce kin fara samun sauki dan mace ta zamu zama agidan miji ma wani falala ne kinga idan kika kara fitowa ai ciwo ya koma baya kara goge hawayen idanta tayi ta dan turo baki ta ce Niba aure kuma zan sake yi ba daga haka ta nufi upstairs Mami ta mike ta ce To kya gaisheta daman jikinki nazo dubawa daga haka ta mike ta fice a parlorn Rafiah ta bita da harara Very gentle ta dinga taka steps din harta gama hawa ta shige dakinta ta rufo kofa har zata kwanta aka bude kofar dakin Abdul ya karaso yana kallanta ya ce Sannu ta ce Thank u ya ce We just came back with Abba na siyo maki grapes da Apple and shawarma dan murmushi kawai tayi dan ita yanzu ta tsani komai idan ba danwake ba kwanciya tayi tana kallansa ta ce So much thanks bro nagode gyara mata blanket din jikinta yayi ya ce Allah ya baki lafiya ta ce Ameen ganin ta limshe ido yasa ya mike ya fita a dakin ya jawo mata kofa a hankali Ammi ce zaune a parlornta Sameer na gefenta a zaune gaba daya jikinsa yayi sanyi jin abinda danuwansa ya aikata shida yake murna zai dawo gida yaga yan uwansa cikin farin ciki amma kuma yaji abunda ko a mafarki bazai yarda ba Ammi ta dan goge hawayen idanta ta ce Yarinyar nan ta sha wahala Muhammad idan ka ganta gaba daya ta rame Sameer ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce Allah ya kyauta kenan bai gayawa kowa inda zaije ba Ammi ta ce Ba wanda ya sani wadanda ya kamata su sani su suka daukeshi suka tafi dashi nasan Yusuf dina bazai iya butulci da wulakanta mace haka ba wallahi Sameer akwai abinda yake faruwa kamo hannunta Sameer yayi ya ce Stop crying pls mother in sha Allah wata rana zai dawo na miki alkawarin zan kula da yarinyar da kuma abinda zata haifa Ammi ta kara share hawayen idanta ta ce Allah ya baka iko zamuyi ta addua Allah ya bayyana shi a hankali ya ce Ameen yanzu dare yayi kuma na dawo da ciwan kai gobe insha Allah zanje na dubata Ammi ta ce Allah ya kaimu goben ya ce Ameen amma dan Allah ki daina kuka
Karfe 12 na dare Jawad ya dawo gida bayan yayi parking sai daya tabbatar gate man ya rufe gate sannan ya nufi entrance din gidan yana murda handle din kofar yaji a kulle ya ciro wayarsa a pocket dinsa yayi dialing phone din Sadeeq bugu biyu ya dauka hade da sallama Jawad ya ce Open the door for me na parlorn Abi da to kawai ya amsa sannan yayi hanging call din few minutes Sadeeq ya bude masa kofar ya shigo sannan Sadeeq ya rufe kofar ya koma dakinsa har zai shige dakinsa Abi ya bude kofar part din Mami ya ce Whos that Jawad ya juyo a hankali ya ce Its me Abi ya ce Ya sai yanzu zaka dawomin gida Ahmad is exactly past 12 now kafin yayi magana Mami ta fito tana masa wani kallo ta ce Gashi nan saiya gaya maka gidan ubanwa yaje daya kai dare haka bai dawo ba tin bayan isha dana je gidansu yarinyar nan na samu shi yana fita daga nan ko gidan uwarsa wa ya tafi ban sani ba Abi dake kallansa ya ce Where have u been Ahmad Kaje gidan su Fatima ne a hankali ya ce Ehh but i left there since 8 naje wajen Aliyu ne baya nan shine naje asibiti wajen Umar anyi admitting dinsa ne anan na zauna sai yanzu Abi ya sauke ajiyar zuciya ya ce Allah ya sauwake daga haka ya koma ciki Mami dake tsaye tana kallansa ta ce Kai ko tsoro bakyaji a tattaraka ubanka yana dan siyasa a hankali ya ce Ba abinda zai faru by God grace Mami ta wurga masa harara ta ce Aini gara kayi auranka ka barmin gida idan yaso ka kai karfe 1 baka koma ba wacce ka aura ne dai sai dai tayi hakuri dan murmushi yayi yana kallanta ya ce Sai da safe daga haka ya shiga dakinsa ta bishi da harara
Washegari ya kama Monday da safe Ummi ta gama hada komai da taimakon Saudatu bayan ta shirya ta shiga dakin Rafiah ta sameta a kwance tana bacci rufo kofar tayi ta koma dakinta Abba dake zaune yana rubutu ya ce Haka zaki fita ki barta at this condition kenan Dagowa tayi tana kallansa ta ce Im not staying long 2 hours lectures kawai zan musu sai meeting daza muyi amma idan kace na zauna ba damuwa Abba ya ajiye pen din hannunsa ya ce No idan kinga dai ba matsala kije kawai amma kinsan tana bukatar me kula da ita ko Ummi ta ce I knew amma ga Saudatu ai komai takeso zata bata Abba ya ce Ohk Allah ya kiyaye ta ce Ameen 2 days per week kawai nake da lectures din ya ce Alright a dawo lafiya Ummi ta nufi kofar fita ta ce Allah yasa daga haka ta fita a dakin bayan ta sauko kasa ta zauna akan kujera tayi kiran Saudatu cike da ladabi yarinyar ta karaso ta zauna a kan carpet ta ce Gani Ummi Ummi ta ce Zan je aiki ne idan Rafiah ta tashi ki bata tea first after then akwai dan wake cikin warmer idan zata ci kuma karta taita kwanciyar nan dan Allah idan kin gama abinda kike zaki iya zama da ita Saudatu tayi kasa da kanta tana murmushi ta ce To Ummi insha Allah a dawo lafiya Ummi ta ce Allah yasa daga haka ta mike ta fita a parlorn
Karfe 10 Rafiah ta tashi ta dinga bin dakin da kallo kafin ta mike a hankali ta zauna yau kam Alhamdulilah jikinta ba zafi sosai kuma batajin ciwo a ko ina mikewa tayi ta dauki towel ta shiga toilet kusan 15 minutes tayi taking a ciki kafin ta fito da towel daure a kirjinta ta zauna gaban mirror Yusuf kawai ta tuna a lokacin dan mostly idan ta fito a wanka shi yake tsayawa a bayanta ya taje mata kai ya taya ta shiryawa jin kirjinta na bugawa yasa ta limshe idanta tana addua bayan minti 2 ta bude idanta sannan ta shafe jikinta ta mike ta bar wajen doguwar riga na atampa ta saka sannan ta daura dankwalinta ta shafa white powder sai lip gloss sosai tayi mungun kyau duk da ramar da tayi ta jawo phone dinta dake kan gado ta kira Mummy sosai sukai waya kuma jin muryarta yasa hankalin Mummy ya kara kwanciya bayan sunyi sallama ta ajiye phone din sannan ta fara gyara gadon Tana cikin gyaran Saudatu ta bude kofar ta danyi murmushi ganinta ta ce Anty Rafiah bari na gyara miki Rafiah ta girgiza kai ta ce Aa Saudat bari nayi kawai Saudatu ta danyi shiru tana kallanta sai kuma ta ce Bari na kawo miki tea ta ce No zan sakko kasa yanzu Abbana ya fita ne Saudatu ta girgiza kai ta ce Gaskiya banga fitan shi ba amma Ummi ta fita ta ce Ehh jiya tacemin zata koma aiki yau fita Saudatu tayi a dakin tana murmushi ita kanta dadi taji ganin Rafiah a haka ta wuce kitchen ta fara hada mata danwaken kamar yadda taga Ummi nayi Bayan Rafiah ta gama gyara dakin ta shiga dakin Abbanta da sallama ya dago yana kallanta ya ce Mother ta danyi murmushi ta zauna gefenshi ta ce Abbana murmushi yayi shima yana kallanta ya ce Alhamdulilah jiki ya fara sauki ta ce Good morning ya ce Morning how are u dear a hankali ta ce Banajin komai yanzu Abba thanks for the care hannunta ya kama suna shaking tayi saurin sunkuyar da kanta tana murmushi Abba ya ce Allah ya kara miki lafiya a hankali ta ce Ameen sannan ta mike tana kallan warmers din dake gefensa ta ce Abba u havent eat ya ce Yanzu zan gama naci Mamana daga haka ta danyi murmushi ta fita a dakin ya bita da kallo cike da tausayi Tana sauka downstairs ta samu Saudatu ta hada mata komai ta zauna akan carpet ta ce Sannu da kokari Saudatu ta ce Haba dai Anty Rafiah ai indai ke zanyiwa abu zan iya yini inayi ba tare dana gaji ba Rafiah na murmushi ta ce To banaso kina kirana da Anty just Rafiah pls Saudatu ta ce Wallahi bazan iya ba ta ce Zaki iya kin ta6a ganin inda ka cewa wadda ka girma Anty Ta ce Ehh mana nidai koma menene bazan fasa fada ba ya karfin jiki Ta ce Yau kam Alhamdulilah kawai inajin weakness ne Saudatu ta danyi murmushi ta ce Dama haka zakiji saboda cikin dake jikinki Rafiah ta dan kalleta ta ce How do you know that taya kika san hakan ta ce Nima nayi kuma naji Rafiah ta dan zaro ido tana kallanta ta ce Kin ta6a aure Ta ce Ehh tin ina shekara 13 aka min aure a garinmu inaga shekarana 14 da watanni na samu ciki ina da tsohon ciki Allah yayi wa mijina rasuwa a ranar daya rasu ranar nima na haihu amma dan yazo ba rai ni kuma tawa kaddarar kenan Rafiah ta ajiye spoon din hannunta tana kallanta ta ce Subhanallah Allah ya jikansu Saudatu ta ce Ameen amma tin daga lokacin ban sake aure ba naci gaba da karatuna na islamiyya har nayi sauka shine wata kawar mahaifiyata ta samar min aiki anan nidai shekaruna 19 a duniya amma wallahi ban ta6a haduwa da mutanen kirki irinku ba Umminku Abbanku kema da Abdul ba wanda ya ta6a min abinda zanji ba dadi Allah ya saka da alkhairi ya biya ku da gidan Allah Rafiah ta danyi murmushi ta ce Ameen
Suna zaune suna dan hira aka danna bell Saudatu ta gyara hijabinta zata bude kofa Rafiah ta ce Wait Saudat ki fara tambayar waye Saudatu ta ce Waye Sameer ya ce Nine jin muryar namiji yasa ta mike ta dauka hijab dinta akan kujera ta saka sannan Saudatu ta bude kofar Sameer dake tsaye yayi folding hannayensa ya shigo parlorn yana kallan Rafiah ya zauna itama zama tayi kasa ta ce Sannu da zuwa ya ce Yauwa sannu Saudatu ta ce Ina kwana ya ce Lafiya kalau ya mai jiki Ta ce Alhamdulilah daga haka ta wuce kitchen ta kawo masa drinks da cup sai table water Rafiah dai na kallanta harta ajiye ta bar wajen a hankali ta dan kalleshi ta ce Ina kwana ya ce Lafiya kalau ya karfin jiki Ta ce Da sauki sosai ya ce Allah ya kara sauki shiru duk sukayi na kusan minti 5 Sameer yayi breaking silent din ta hanyar cewa Allah ya baki lafiya jiya da daddare nayi landing Mother told me all what happened Allah yasa haka shine mafi alkhairi a hankali ta ce Ameen nagode ya ce God knows best Fatima shi yasan dalilin daya sa hakan ta faru but i think hakan ya faru ne saboda shi din ba alkhairi bane a tattare dake may be u will find someone better than Yusuf so forget all what happened im there for u insha Allah i will take care of the Baby before and after his birth Sameer ya karashe maganar yana kallanta kin dagowa tayi ta kalleshi jin abinda yace is very similar to Jawdas speech Sameer ya sauke ajiyar zuciya ya ce Allah ya raba lafiya a hankali ta ce Ameen nagode mikewa yayi yana kallanta ya ce Im going ba tare data kalleshi ba ta ce Ko in kawo maka tea Ya ce No im going with this daga haka ya dauki Fanta daya ya rike a hannu ya ce Ammi tace sunyi waya da Ummi wai bata nan ko ta ce Yes shes out ya ce Ohk i will come back ltr ta ce Till u come Allah ya kiyaye daga haka ta tura kofar bayan ya fita hijabin jikinta ta cire ta dauko danwakenta akan dinning taci gaba da ci tana kallan TV
_08103810398_
I appreciate all ur calls and messages nagode sosai da sosai im more than healthy now
_ _
_MY LIFE PARTNER_
_Part 2_
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
_We are here to Educate Motivate and Entertain our Readers_
_By FATIMA _
_3_
Da yamma Rafiah na zaune a parlor tayi pillow da cinyar Ummi aka danna bell Ummi ta dan kalleta ta ce Open the door Rafiah mikewa tayi a hankali tasa Himar dinta sannan ta bude kofar murmushi ta danyi ganin Ammi a tsaye Khairiyya ta rungumeta calmly ta ce I missed u Anty a hankali Rafiah ta ce I missed u namesake daga haka ta matsa gefe Ammi ta shigo With smile Ummi ta cire glasses din idanta ta ce Sannu da zuwa Hajiya Ammi ta zauna akan sofa tana kallan Rafiah dake tsaye ta ce Sannu jiki ya fara sauki ko Ummi ta ce Sosai wallahi sai godiyar Allah sake hannun Rafiah Khairiyya tayi ta ce Ina yini Ummi ta ce Lafiya kalau Khairi how are u Khairiyya ta ce Fine Ummi zama duk sukayi a kan carpet Ammi ta kalli Ummi ta ce Amma ta rage aman ko Ummi ta ce Ehh yau dai tinda ta tashi ba tai ba jikinma da sauki sosai Ammi ta ce Allah ya kara mata lafiya ya kuma bata hakurin jurewa Ummi ta ce Ameen Cikin few Minutes Saudatu ta jerawa Ammi abinci da abinsha duk cikinsu ba wanda ya ci Khairiyya ce kawai ta sha Mango juice bayan sun dan jima Ammi ta kara musu sannu suka wuce sosai itama taji dadin ganin jikin Rafiah
A haka rayuwar Rafiah ta dinga tafiya wata rana ta tashi garau wata rana taita amai harda zazza6i duk bayan kwana biyu Jawad ya kanzo ya dubata ba laifi yanzu tayi sabo dashi ba kadan ba tin tana kin gaya masa abinda takesan ci harta fara fada masa wata rana ma a waya zata kirashi idan kuwa ta kira ko me yake sai ya bari ya kawo mata abinda ta bukata kullum kara kwantar mata da hankali yake yana nuna mata misalai kala kala wanda suka faru kuma a yanzu komai ya zama tarihi A yanzu a gidansa yake kwana abinci kawai yake zuwa yaci idan yaga dama shima dan mostly idan yaje gaishesu baya wani cin abinci Mami kuwa komawarsa gidansa ba karamin dadi ya mata ba hankalinta kwance ya fiye mata yazo ya gaisheta ya tafi kayan Babies yake saya sosai yana tarasu cikin wani akwati sai da yaga ya cika sannan ya daina sayan kayan gaba daya unisex ya saya saboda baisan me zata haifa ba Bangaren Sameer ma baiyi kasa a gwiwa ba yakan zo ya duba Rafiah time to time shima duk abinda yasan tana so saiya kawo mata ita dai kawai kulashi take amma harga Allah batasan zuwan sa gidan bata so ta sake sakin jiki da dangin Yusuf yawanci Jawad yana haduwa da Sameer a gidan idan ya tambayi Rafiah sai tace wani dan uwan Yusuf ne ba wani shiri suke da Sameer ba ko gaisuwa randa bata kansu basa yi Rafiah kuwa tin sanda cikinta ya girma take zama da hijab idan ta cire hijabi to tana tare da Ummi ne ko Mummy ko kuma Saudat amma ko Abba ne yazo yini zatai tana yawo da hijab a jikinta musamman da cikin ya shiga wata 8 kullum fadansu da Ummi ta tashi tayi aiki dan tinda ta daina laulayi Ummi ta raba musu aikin gida ita da Saudat wani lokacin harda kuka take karasawa sabida gajiya ga ciwan baya da yake daminta sosai amma hakan baisa Ummi ta daga mata kafa ba gaba daya ta kara ramewa tayi fari akan da
kwanciya tayi akan gado tana sauke ajiyar zuciya toilet dinta ta gama wankewa shine ta mike ta dan huta tana jin an bude kofar dakinta ta juya tana kallan me shigowa Ummi ce ta shigo da shirinta na zuwa aiki ta zauna gefen Rafiah dake kwance ta ce Kin sharemin parlorn Girgiza kai tayi kamar zatai kuka ta ce Banyi ba wallahi na gaji Ummi Ummi ta mike tana kallanta ya ce U dont have to ki tashi kije ki gyara parlorn nan sannan kuyi abinci idan kinga dama kuma ki gudu ki barta tayi ita kadai idan kin huta kuma ki wanke innerwears dinki da kika jera min su a toilet dan bazan wanke ba hawayen idanta ta share bata ce komai ba Ummi ta nufi kofar fita ta ce Sai na dawo tana fita Rafiah ta jawo phone dinta ta kira Mummy bayan ta daga tayi sallama da kyar ta amsa tana danne kukan dake cinta Mummy da hankalinta ya fara tashi ta ce Lafiya Fatima Meya faru ne Cikin muryar kuka ta ce Kinga Ummi bata daina sani aiki ba kuma bayana ciwo yake bazan iya ba wallahi daga haka ta fashe da kuka Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce To kiyi shiru ki daina kuka kiyi abinda zaki iya sauran ki bar mata shi zanzo yau da yamma ban san meyasa Zainab ke haka ba wallahi aiki ai kina yi amma wallahi baza kiyi abinda yafi karfin kuba dama caan ba lafiya ba balle kuma ga larura zanzo da yamma idan ta dawo to kawai tace tayi hanging call din da kyar ta mike ta zauna ta kurawa kananun kafafuwanta ido ganin yadda suka kumbura ta zira su kasa gently ta sauko akan gadon sannan ta dauki hijab dinta ta saka koda ta sakko kasa kwanciya tayi akan kujera sai sauke numfashi take daki daki tana nan zaune Saudatu ta fito a kitchen tana murmushi ta ce Anty Rafiah lafiya dai Ta ce Ehh hutawa nake daga haka ta turo baki ta gyara kwanciya akan kujera ta limshe ido bacci ne me shegen nauyi ya dauke ta sai karfe 12 ta tashi tana kallon agogo tayi sauri ta dauko tsintsiya sannan ta dawo ta fara share parlorn tana gamawa kuwa batai mopping ba Ummi ta shigo tayi parking Rafiah ta kalli Saudatu dake dariya kasa kasa ta ce Dan Allah kice mata banda lafiya har amai nayi zanje na kwanta daga haka ta wuce sama da sauri
1 month ltr
Tsaye suke duk tasu a kofar room din da Rafiah ke ciki kana ganinsu kasan suna cikin babban tashin hankali musamman Ummi data kasa controlling tears dinta tausayin Rafiah kawai take idan ta tuno azabar haihuwa Mummy dai na jingine da pillers din wajen ta limshe idanuwanta banda salatin Rafiah da kiran Ummi da take ba abinda su ke jiyowa Abba dai na tsaye yana ta addua sai kaiwa yake yana kawowa a area din wajen bayan few minutes Dr Hisham ya fito a room din Ummi ta mike da sauri tana kallansa ta ce How is she Dr Ya ce Alhamdulilah kenan amma gaskiya ba zata iya haihuwa da kanta ba zamuyi mata CS but sai mijinta yayi signing Ummi ta share hawayen idanta ta zauna Abba ya ce Let me sign Dr Dr Hisham ya girgiza kai yana kallan Abba ya ce U cant sign both yallaboi mijinta zai fara signing sai kuma kai a fusace Mummy ta juyo tana kallansa ta ce Wane irin miji kake magana bayan ga mahaifinta nan shekara nawa ana kawota asibitin nan kunfi kowa sanin danginta mijin da shekara daya baa san inda yake ba idan baza kuyi abinda ya dace ba mu kaita wani asibiti mana sauke idansa Dr Hisham yayi ya ce Kiyi hakuri Madam rules din aiki ne ba wai nina fada ba daga haka ya kalli Abba ya ce Muje sai kayi signing din daga haka Abba yabi bayansa zuwa office cikin 20 minutes aka gama komai aka shiryata ko magana bata iya yi sai kallon Ummi da take hawaye na sakko mata har aka turata cikin dakin gaba daya jikinsu ya gama sanyi musamman Ummi da hawaye ya ki daina sakko mata addua babu irin wacce batayi
Kusan 1 and half hour suna tsaye a wajen sannan Dr Hisham ya fito Abba ya kura masa ido yana kallansa ya danyi murmushi yana kallan Abba ya ce It was successful Sir an samu cute baby girl ajiyar zuciya suka sauke a tare duk suka amsa da Alhamdulilah Abba ya ce Can we see her Ya ce Not yet za a mata allura ne bayan awa daya zata tashi but u can see the baby zasu kawo muku ita soon daga haka ya wuce office dinsa yana cire hand gloves din hannunsa Kafin a fito da Baby Mummy ta yiwa mutane sunfi 30 waya cewa tayi jika bayan minti 10 nurse din ta fito da Baby a hannunta sai kamshi take saboda yadda aka gyarata sosai Ummi tayi saurin mikewa ta kar6eta sannan ta bude fuskar Babyn dake rufe da towel sai da zuciyarta ya tsinke ganin kamannin Yusuf karara ta sauke ajiyar zuciya ta mikawa Abba Babyn shima same thing abinda ya gani ya danyi murmushi ya kai bakinshi saitin kunnen Babyn ya mata kiran sallah hade da addua hanging wayar Mummy tayi ta kar6a Babyn tana murmushi ta ce Gata kamar shashashan ubanta kuwa Abba dai ya kalli Ummi ya ce Bari naje sallah na dawo ta ce Safe Mummy ta ta6e baki ta ce Wallahi da ana canza halitta dana canza miki kamannin Yusuf dan bai kamata ki dauko kamarsa ba baki sanshi ba bai sanki ba banda ma hukunci na Allah taya zakiyi kama da Yusuf uban me ya tsinana miki a rayuwa goge dan hawayen idanta tayi ta ce Allah ya taimakeshi watarana yazo yana kirarin shine mahaifinki wallahi saina yaga masa rigar rashin mutunci sai ya kwammace bai sanni a rayuwa ba balle dangi na Ummi dai bata ce komai ba tasa tissue ta goge hawayen daya ke kokarin gangaro mata Dakin da Rafiah take kwance suka shiga bacci take sosai banda numfashi babu abinda take saukewa Ummi ta kamo hannunta tana kallanta ta ce Allah ya baki lpy daughter Mummy ta ajiye Babyn a gadonta ta zauna gefen Rafiah tana mata addua Kafin ta tashi mutane sunzo ganin Baby makwabtan Mummy da Ummi sai kuma friends din Ummi Anty Amina da yan gidansu sai daga baya suka zo Ammi kam ita ce farkon zuwa ita da Sameer Mami ma tazo sai murmushi take tana yaba kyan yarinyar kamar da gaske duk da itama batasan Yusuf sosai ba amma taga kamanninsa da Babyn Sameer dai ya dinga kallan Babyn dake kwance tana bacci bayan 5 minutes Rafiah ta fara motsa karfarta duk occupants din dakin suka dawo kallonta ta fara bude ido a hankali tana salati Ummi ta mike tana kallanta ta ce Rafiah kokarin tashi take amma ta kasa Mummy ta dagata ta zauna ta ce Sannu kinajin ciwo ne A hankali ta nuna mata dai dai inda aka mata surgery din Mummy ta ce Sannu limshe idanuwanta tayi ta budesu sannan ta fara bin katon dakin da kallo kowa na dakin take kalla amma bata ga Jawad ba he once told her that duk lokacin data haihu tana bude idanta zata ganshi a gefe but he is absent now suna hada ido da Mami tayi saurin kawar da kanta gefe the same thing daya faru lokacin data kalli Umman su Anty Amina Ikleemah na zaune kan carpet tana ta danna phone dinta jin Mummy ta ta6a ta yasa hankalinta ya dawo waje daya ta sauke ajiyar zuciya kawai Mummy ta ce U didnt ask for ur Baby daughter sauke kanta ta kara yi tana wasa da ring din hannunta Mummy ta ce Bari na dauko miki ita kan gadon Babyn ta koma ta dauko Babyn sai kallon towel din da Babyn ke ciki take Mummy ta mika mata ita ta ce Congratulation for having her Allah ya kare miki ita daga sharrin masu sharri zaro ido Rafiah tayi ganin fuskar Babyn her eyes lips the fair skin nose gaba daya is exact as Yusufs own fashewa tayi ta kuka ta rungume Babyn a jikinta kam kam tana fadin Why didnt u resemble me Habibty i was the one who take care of u since from the day i got u i suffered for 9 months i cried several times because of u dear isnt all this a prove to resemble me dear bana bacci da kyau bana ci da kyau just because of u meyasa ni baki yi kama dani ba share hawayenta tayi ta kara kurawa Babyn ido sai kuma ta kara rungumeta ta ce Anywhere i luv u Habeebty ba wanda zai miki irin son da zan maki a duniya i still remain ur mum and Dad nice komai naki a rayuwa if anyones to blame hes mistaken dear im only yours ke tawa ce ni kadai na i luv u Habeebty ta kara rungumeta tana kuka sosai da sosai duk jikin mutanen dakin sai yayi sanyi musamman Ammi data kasa tsayuwa sai ficewa tayi a dakin
_08103810398_
_ _
_MY LIFE PARTNER_
_Part 2_
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
_We are here to Educate Motivate and Entertain our Readers_
_By FATIMA _
_4_
Kar6an Babyn Mummy tayi a hannunta ta ce Stop crying like this daughter ke daya kamata ki godewa Allah kuma hannunta tasa ta share hawayen daya sakko mata Mummy ta zauna gefenta bayan ta kwantar da Babyn ta ce Calm down and rest dear what do u want to eat a hankali ta ce Kunu zan sha Mummy ta jawo basket din da Ammi ta kawo ta dauko flask ta zuba mata kunu cikin mug sannan ta mika mata a hankali ta kar6a tana kallan Umminta dake zaune tayi shiru ta ce Thank u mothers Kwanan Rafiah uku a asibiti aka sallameta kuma har suka koma gida Jawad baizo ba sakamakon tafiyar da aka sa shi yayi a wajen aiki tin kwana daya da Rafiah ta haihu Mummy ta gaya masa hankalinsa ya kasa kwanciya komai yake a wajen hes in a hurry so yake ya gama komai ya koma kano a ranar amma hakan bai samu ba dolensa ya kara kwana biyu Da yamma Rafiah na zaune a dakin Ummi tana breastfeeding Babynta aka turo kofar ta juyo tana kallan direction din kofar Ummi ta shigo da flask a hannunta ta ajiye a gefensu tana kallanta ta ce Hope u are not in any pain yace idan kinajin ciwo we should let him know ta girgiza kai a hankali ta ce Ni banajin komai kawai dai wajen ne yake dan zogi Ummi ta ce Kina shafa maganin ne Ta ce Eh Ummi ta ce To idan kun gama ki kawota gun Gwaggo sai ki huta a hankali ta ce Ohk zan kawota Ummi ta mike ta ce Abinci fa Tayi saurin girgiza kai sannan ta ce Not now daga haka Ummi ta fita ta jawo musu kofar few minutes ta gama ta kwantar da Babyn a gefenta ta kwanta itama jawota tayi very close to her ta rungumeta ta limshe ido nan da nan duk sukai bacci ganin shirushiru basu fito ba yasa Ummi ta koma sama duba su saboda yadda Gwaggo ta matsa a kawo mata Babyn tana shiga dakin ta samesu suna bacci Ummi ta kura musu ido cike da tausayi sai kuma tayi murmushi ta juya she never thought Rafiah zata so dan da zata haifa haka tana sauka kasa Gwaggo ta ce Ina jaririyar ne Zainab idan baa so a bani ba sai na hakura ba ni dama ba ita nazo dubawa ba jikata nazo gani na mata ya jiki Ummi ta danyi murmushi ta ce Hajiya Gawggo na samu sunyi bacci ne kuma idan zan daukota zata tashi ne Gwaggo ta ta6e baki tana kallan Mummy da Anty Salma ta ce To sai a kira uban Rafiah ya maidani Bauchi yau tinda dama daga cewa anyi haihuwa yaje ya daukomu muga ya gashi kusan awana 1 ban dauki yar a hannuna ba Mummy ta ce Gobe fa zaku koma Gwaggo ai zaki dauketa harki gaji Gwaggo ta mike ta ce Ba sai nama dauketa ba yar da akace da ubanta take kama gara dai na ciccibi ita Rafian tinda itama bata fi a dauketa ba Har Mummy zatai magana Anty Salma tayi mata alamar tayi shiru
Anty Anina ce kwance a parlorn ta ita da Anty Rahama suna hira kamar an tsikareta ta mike ta ce Ni kuwa Khadija tasan Rafiah ta haihu Anty Rahama ta girgiza kai ta ce Ta ina zata sani dama bamu zamu gaya mata ba kuma kusan shekara bama waya da ita ta ina zata sani to Anty Amina ta gyara zama ta ce Bakisan Khadija ba kenan zata iya sa ayi mata bincike idan kuma taga dama zata watsar dasu ne kawai Anty Rahama ta ce Shiyafi mata sauki wannan gaskiya yarinyar akwai kyau kam kinga dazu da Yah Muhammad ya daukota har ta danyi kiba wannan da namiji ne cewa zaai kakinta Yusuf yayi Anty Amina ta ta6e baki ta ce Dama ai shine me kyau din ita dai Rafiah fara ce amma bazata hada kanta da Yusuf ba kwata kwata basu dace ba Anty Rahama tayi dariya ta ce Basu dace ba kam gashi ai sun rabu shiru Anty Amina tayi jin an bude kofar parlor Ikleemarh ta shigo ta zauna gefensu tana turo baki Anty Rahama ta mike ta ce Waya ta6a ki Kuka ne ya kwace mata ta ce Ba wannan kanwar Kakan su Rafian bace naje wucewa ta dinga zagina wai harda cewa nima na kwaso ciwo ai naga su suka fara ciwon kafin nayi Anty Rahama ta ce Share hawayenki ai ciwo yanzu suka fara gani ciwo ya wuce wata biyu a sako yarinya tazo gida ta haihu miji bai zo ba
Kukan Babyn ne ya tasheta daga baccin da take ta mike a firgice tana kallan Babyn dagota tayi ta rungumeta tana share hawayen idanta daga dan baccin nan data kwanta mafarkin Yusuf tayi yazo yana ce mata ta bashi Babynsa ta limshe idanuwanta tana girgiza kai ta ce Its impossible shes only mine daga haka ta gyara Babyna jikinta tana kallan idanta dake bude silently ta ce Ni kadai kika sani Habeebty nine mamanki nine babanki kinji inma akwai wani mahaifinki a duniya to Ya Jawad ne hawayen idanta ta share ta sakko a kan gadon still holding her baby ta bude press dinta ta ciro wayarta ta kunna raban data kunna ta tin ana gobe zata haihu yau kwana 4 kenan Ameera ma ta wayar Ummi suke waya bayan wayar ta kunnu tasa hannu zata bude lock din kiran Jawad ya shigo ta dan turo baki sannan tayi picking call din Jawad yayi sallama shiru bata amsa ba ya sake sallama nan ma shiru a hankali yake jiyo sound din kukanta ya danyi murmushi ya ce I apologize dear im on my knees pls do forgive me dan turo baki tayi ta ce Where have u been Yaya Ya ce Kaduna but im now in Kano yanzu ina gidana zanyi wanka saina zo hope my Baby is fine a hankali ta ce Yes when will u come Ya ce Just few minutes from now ta danyi murmushi ta ce Sai kazo to ya ce Alright dear hanging call din tayi ta goge hawayen idanta sannan tasa hijab ta dauki babyn suka fito tin suna sakkowa a stairs Gwaggo ke kallansu bayan ta karaso ta ce Ke ba haka ake bafa kinbi kin kankame ya ko kunya bakyaji yar fari ce fa Rafiah ta danyi murmushi ta ajiyeta akan cinyar Gwaggo sannan ta juya zata shiga kitchen Ummi ta ce Kinci abincin ne Ta ce Zanci daga haka ta shige kitchen Mummy ne da Anty Salma sai Saudatu suna hada girkin dare Rafiah ta dan tsaya gefe tama rasa ta ina zata fara Anty Salma dake kallanta ta ce Lafiya dai Rafiah Mummy ta juyo tana kallanta itama girgiza kanta ta danyi ta ce No ba komai Mummy ta ce Ko kinasan wani abu ta kara girgiza kai Mummy dai ta fahimci tana san abu amma ta kasa fada ne hannunta ta wanke a sink sannan ta kalli Rafiah ta ce Muje parlorn Abbanku bin bayan Mummy tayi a hankali har suka shiga parlorn bayan sun zauna ta ce Tell me whats wrong with you what do u want sauke kanta tayi kasa a hankali ta ce Dama Yayane yace wai yana hanya Mumny ta ce Wane Yaya ko Sameer ta girgiza kanta a hankali ta ce Ya Jawad Mummy dake kallanta ta ce Yaushe ya dawo Ta ce Dazu yacemin yana gidansa wai daga nan zai taho nan Mummy ta dinga kallanta kafin ta ce Ohk sai a kawo mishi abinci nan daga haka ta mike ta fita a parlor Rafiah ta bita da kallo ta jima zaune anan parlor ita kadai horn din mota data ji ne yasa ta mike ta leka ta window ganin motar Jawad yasa ta danyi murmushi ta koma ta zauna Yana parking ya fito a motar da key dinsa a hannu ya sha farar shadda yayi wani kyau sosai sai kamshi yake a hankali ya dinga takawa zuwa entrance din gidan bayan ya danna bell yaja ya tsaya a gefe Ummi ce kadai da Gawggo a parlor sai Saudatu da shigowanta kenen ta wuce ta bude kofar a hankali ta ce Bismillah Jawad ya shigo parlorn kansa a kasa kan carpet ya zauna yana murmushi Ummi ta ce Jawad ne Yaushe ka dawo Ya ce Dazu Ummi ina yini ta ce Lafiya kalau Jawad how is work Ya ce Alhamdulilah ashe an samu Baby girl Ummi ta ce Wallahi gata nan a kwance tana ta bacci kallan dan karamin bed din babyn yayi kafin ya ce Allah ya raya ta da imani Ummi ta ce Ameen kallan Gwaggo yayi data zuba masa ido tin shigowarsa ya ce Ina yini Hajiya ta ce Lafiya kalau yaro kai din dan wane gida ne Ummi ta ce Yaran Hajiya Hadiza ne Gwaggo ta ce Kishiyar Halima kike fada Ta ce Ehh shine babba Gwaggo ta ce Ba shakka gashi nan kamar honorable mahaifinsa yayi aure ne Ummi ta mike ta ce Aa baiyi ba tukunna Saudat kaishi parlorn Abba Saudat dake goge kan dinning table ta ce Toh mikewa yayi yabi bayanta har suka shiga parlorn ta juya ta fita a hankali ya ce Nagode kan carpet ya zauna ya dauko wayarsa a pocket yayi dailing number Rafiah harta gama ringing bata dauka ba ajiye wayar yayi ya dan juya hangota yayi ta kifa kanta akan dinning table ya mike a hankali yana murmushi ya karasa inda take zaune ya ce How are u dear kin kulashi tayi ya kamo hannunta ya ce Pls get up dear ko so kike nayi miki kneel down Dago kanta tayi a hankali ta ce U dont have to but u broke the promise u made to me murmushi yayi yana kallan face dinta ya ce Aina ce maki a wajen aiki ne aka turani amma kinsan da babu abinda zai hanani zuwa clinic ranar now how are u feeling A hankali ta ce Fine ya kai hannunsa face dinta ya share mata guntun hawayen daya sakko ta sauke kanta kasa ta ce And u are not happy for seeing me ya dan zaro ido yana murmushi ya ce Who told u i am more than happy Fatima wasa taci gaba dayi da fingers dinta tana murmushi ya koma kan carpet ya zauna yana kallanta ya ce Most i tell u to bring her for me ko rowa zakimin ta tashi a hankali ta ce No ni ai bana rowa daga haka ta fita a parlor a corridor ta tsaya ta leka parlorn taga Ummi ce kadai ta fito calmly ba tare data kalleta ba ta dauki Babyn ta koma parlorn Abba gefen Jawad ta zauna ta mika masa Babyn ya kar6a kallan fuskarsa kawai take lokacin daya kar6a Babyn ya dago kansa yana kallanta ya ce Shes so cute Allah ya raya mana cikin addinin islama shiru tayi ta fara goge hawayen idanta ya kamo hannunta ya ce Why is it that kuka baya maki wahala Fatima u waste ur tears too much what makes u to cry tell me now cikin muryar kuka ta ce Ni shine batai kama dani ba ya danyi murmushi yana kallan yadda take tura masa baki as if shiya halicci Babyn ya ce So u thank God and stop crying dear mu godewa Allah daya bamu this cute angel is she not cute ta daga masa kai ta ce She is ya ce Kamar ke ba kinma fita kyau just that ta fiki hanci ta dan ta6e baki ta ce Inma kace bani da kyau ni ina ruwana daga haka ta fara kokarin tashi a gefenshi ya kamo hannunta yana murmushi ya ce No dont go pls dear kin fita kyau kawai na fada ne do u think zance ta fiki kyau ne bayan kena fara sani na kuma fara Shiru yayi ganin yadda take kallansa yaja hancinta ya ce My stubborn Rafiah ta kauda kanta gefe ta ce Let me bring food for u daga haka ta tashi ya bita da kallo
_08103810398_
httpsmfacebookcomZamaniwritesassociation
_ _
_MY LIFE PARTNER_
_Part 2_
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
_We are here to Educate Motivate and Entertain our Readers_
_By FATIMA _
_5_
Bayan few minutes Rafiah ta dawo da tray a hannunta me dauke da snacks sai exotic da glass cup a gefe calmly ta ajiye a gabansa ta ce Here it is Yaya Jawad ya danyi murmushi yana kallanta ya ce Thanks mikewa tayi yayi saurin riko hannunta ta zauna gefensa ya ce Ina zaki je ta ce Abinci zan kawo maka ya ce No wannan ma ya isa ta juyo tana kallansa ta ce Kace fa baka ci komai ba Ya ce Ai zanci wannan ta dan matsa baya a hankali ta ce Alright kara matsowa yayi gefenta ya kamo hannunta ya kalli Babyn dake bacci hankali kwance sannan ya kara kallanta ya ce Are u with me Fatima Ta daga masa kai a hankali silently ya ce I just want to tell u that right from the day i met u i love the way u smile the way u laugh and u know what Girgiza masa kai tayi kanta a kasa tana kallan hannunta dake cikin nasa limshe ido yayi ya tattaro courage dinsa ya ce I notice that it was lo Shiru yayi jin an bude kofar parlorn tayi saurin jaa baya tana kallan Mummy dake kallansu ta ce Meye haka Jawad Kansa ya dan shafa ya ce Ehh dama abu ne ya fada mata a ido shine na hure mata Mummy ta zauna akan kujera ba tare data kalli Rafiah ba ta ce Yayi kyau when did u came back Ya ce Ban jima ba banma je gida ba but daga nan can zan wuce ta ce Ohk ya danyi kasa da murya ya ce Congratulations once again for the cute Baby ta ce Thank u baza kaci abinci bane Ya ce No wannan dinma ya isa sai lokacin Mummy ta kalli Rafiah dake zaune gefe tana jujjuya ring din hannunta ta ce Kar6eta ki bashi waje yaci abinci mikewa tayi a hankali ta kar6i Babyn sannan ta nufi hanyar fita a parlorn Mummy ta mike tabi bayanta ta ce Idan ka gama zamu wuce tare ya ce Ohk to daga haka taja masa kofar Cikin minti kadan ya gama cin abinda zai ci ya mike yasa phone dinsa a pocket sannan ya wuce sink ya wanke hannu ya dawo ya dauka key din motarsa a parlor ya tarar da duk ilahirin gidan amma banda Rafiah ya dan durkusa ya ce Zan tafi Ummi Allah ya raya da imani Ummi dake murmushi ta ce Ameen Gwaggo ta ce To ni tinda nazo banga Hadiza tazo barka ba dama kuma Da sauri Ummi ta ce Tazo mana Gwaggo tin muna asibiti ai tazo Jawad ya mike ya nufi kofar fita Ummi ta ce Allah ya kiyaye Mummy da Anty Salma suka mike sannan sukai musu sallama suka tafi Har suka isa gida Mummy da Anty Salma hirarsu suke shi dai yana ta driving but zuciyarsa ya tafi wani tinani daban what if Mami taga ya sauke su fa ta kuma tabbatar tare suke dan karamin tsaki yaja yaci gaba da tuki Mummy ta dan kallesa ta ce Lafiya da tsaki haka Ya ce Ba komai ta6e baki tayi taci gaba da bawa Anty Salma labarin yadda Rafiah ta sha wahala a rainon cikinta Dai dai kofar gida Jawad yayi parking Mummy ta ce Ya zaka dire mu anan young man Ya dan shafa tilin gashin dake kansa ya ce Eh zan fita an jima kadan thats why Mummy tayi masa wani kallo ta ce Ko kana tsoron uwarka ba daga haka ta fito a motar Anty Salma ma ta fito suka wuce ciki sai bayan shigarsu da minti 10 sannan ya gyara motar ya danna horn bayan an bude gate ya shigar da motar yayi parking sannan ya fito ya nufi entrance din gidan Ikram ce kadai zaune a parlor tana kallo ta mike a hankali ganinsa ta ce Yaya sannu da dawowa ya ce Thank u Mami fa Ta ce Tana kitchen daga haka ya wuce kitchen walking gently a bakin gas ya sameta tsaye tana gauraya pepper chicken din da take ya rungumeta ta baya yana murmushi ya ce Mami ta danyi murmushi ta ce Ahmad saukar yaushe Ya ce Yanzun nan aiki kike Ta ce Kai nake yiwa pepper chicken naga basan cin abincin gidanmu kake ba kaga koka tafi dashi sai kai warming dinsa ai kana da microwave ko Ya ce Yes i have thank u mother ta ce To kayi wanka kafin na karasa ya ce Alright to daga haka ya fita a kitchen din ya nufi dakinsa na da ba kowa a dakin amma a gyare tsaf tsaf ya cire rigar jikinsa ya dauki towel ya shiga toilet.
Karanta: Budurcina Hausa Novel by Maman Teddy
0 Comments