Soldiers Family Book 2 Hausa Novel

 

Soldiers Family Book 2 Hausa Novel

Soldiers Family Book 2 Hausa Novel

Page 13&14

Ko da suka K'arasa acan suka Sami gimbiya halila bayan tayi musu duk abunda yadace kana tayi musu sallama ta tafi...bawan Allah bai tashi ba saida yashafe awa biyar 5hr Yana baccin wahala kamun ya farka, mama na gefenshi ta zabga uban tagumi tana kallanshi ganin yabud'e idonshi Yana k'ok'arin tashi zaune yasa mama temaka mishi ya tashi tare da d'aukomai ruwa tabashi tana fad'ar sannu Abba gashi kawanke bakinka sekaci abunci...shidai da Ido kawai yake binta Kuma beyi abunda tace ba ganin hakan yasa mama zuba ruwan ahannunta takuskure bakinta tare da janyo hannunshi shima ta zuba mishi, ba musu ko yayi yadda tayi sai da ya wanke bakinshi sosai kana tabashi abinci aiko kamar jira yakeyi yakarb'e dasauri yafaraci...Ido mama tazuba masa sai da ya cinye tass kana tabashi ruwa yasha abun mamaki sai kawai taga yana Mata murmushi itamayi yimasa tayi kana tafita gunsu biba...tin daga wannan ranar mama ke kula da Dan tsohonnan Kuma betab'a yunk'urin gudu ba ko cutadda ita Kuma duk zamanda suke shibetab'a ganin su mero ba ko gimbiya halila dake kawo musu ziyara Shi mama kawai yake gani itace cinshi da shanshi har sallah ma yanzu sukeyi tare abun gwanin Sha,awa tad'aukeshi kamar mahaifinta..!

 

 

Dubai

 

Fitowarshi kenan daga wanka Yana goge jikinshi yajiyo sallamar Suhaif daga perlon jallabiya ya janyo ya saka tare da boxes d'inshi kana yace ya shigo shiko ya zauna gefen gado Yana shafa manshi...shigowa Suhaif yayi ya tsaya Yana kallonshi jin anshigo anyi tsaye kuma ba,ayi magana ba ya sakashi d'agowa yana duban k'ofar Ido yak'ara bud'ewa sosai Yana kallonshi ganin idonshi cike tab da k'wallah...Baki yabud'e zaiyi magana sai kawai Suhaif ya fad'a jikinshi tare da Æ™anÆ™ameshi yana sakin marayen kuka..hankali tashe Alyasat ya shiga shafa bayanshi yana me karanta duk addu,ar da tazo bakinshi domin yasan tabbas ba lafiya ba?...bai hanashi ba kuma bece komai ba sai da yayi me isarsa kana ya d'ago yana kallonshi cikin muryarshi data disashe saboda kuka yace, "Yaya Sat ammy Yaya sat Miyake faruwa damune da iyayenmu abbe ya Bata ammy takwanta ciwo yanzu kuma abun sekara tsananta yakeyi" kasa Æ™arisawa yayi saboda d'agowar da Alyasat yayi masa da Æ™arfi Yana fad'ar, "me yasami ammy? Wani abunne yafaru? kuka Suhaif yakoma sakawa kamun ya bashi labarin yadda suka sami ammy a yau cikin tashin hankali Alyasat ke maimaita kalmar, "innalillahi wa innailaihhiraji un" yanayi yanajin abunda ya tokare masa zuciya na faÉ—awa sunÉ—au tsawon lokaci ahakan kamun Alyasat ya zaunarda shi, ya buÉ—e baki zaiyi magana kenan Alhassan da Alhusain suka shigo suma ga dukkan alamu kukan sukayi cikin sauri suka Æ™arisa wurinshi tare da rungumarshi atare suna faÉ—ar, "I miss you my lovely bro I miss you so  much please karka tafi kabarmu ammy  batada lpy abbe" shiru yayi saboda hannu da Alyasat ya É—ora mashi abaki Yana girgizamai kai tare da share mai hawayenshi, sunÉ—au tsawon lokaci ahakan kamun suji voice d'inshi yana faÉ—ar, "kuyi haÆ™uri ku dena kuka ku kasance masu ta wakkali ga Allah Subhanahu Wata'alah, aduk abunda ya sameku ku tuna cewa duk wani tsanani yana tare da sauÆ™i muÉ—auka wannan abun dake faruwa ga iyayenmu jarabawace Allah ke mana" shiru yayi yana É—an cizar laÉ“É“anshi (lips) É—inshi kamun yaci gaba da faÉ—ar, "wannan abun Æ™addarar rayuwar suce bamu isa mu canzata ba muzama masu d'aukar k'addara me kyau ko akasin haka kunji ko? kurinÆ™a yi musu addu,a itace abunda suke buÆ™ata agaremu adaidai wannan lokacin, Allah ya warware Mana koma miye Dan Alfarma Sayyidina Rasulillah"...

 

"Ameen ya Allah suka amsa atare" kana yatattarasu duka suka nufi bedroom d'in ammy yadda ya barta hakan suka sameta addu,a sosai suka yiwa mahaifiyar tasu kana suka Kira d'aya daga cikin masu kula da ita domin surik'a kwana tare suko suka fito wannensu zuciyarshi acinkushe.

 

Fita Alyasat yayi izuwa part d'in habibbty Koda yaje bakowa a perlon hakan yasa yanufi bedroom d'inta nan ma batanan wucewa yayi tabaya domin yaduba kotana lambu sai kawai ya hangi Najeeb zai shiga  bedroom d'inshi wata budurwa na biye dashi domin shiko anan yake da d'aki part É—in habibbty mamaki sosai ya kama Alyasat na mi wannan budurwar ta zoyi d'akin Najeeb ba dai cikin Æ™annensu bane to wacece? Wata zuciyar tace masa to Kuma wacece miye ruwanka tinda bakasan abunda ya kawota ba kawai sai ya wucewarsa inda yasamu habibbty acan lambun kuwa..zama yayi akusanta tareda Dora kanshi gefen kafad'arta sai dai bai sakarmata nauyin shiba..shafa kashi tayi kamun tace Alyasat.."uhm ya,amsa atak'aice...shiru tayi nad'an wani lokacin kamun tace ka cigaba da hak'uri kaji Kuma ka kulada kannenka nasan izuwa yanzu kasan abunda ke faruwa da mahaifiyarku ni kai na abun na kwancemun lissafi amma duk tsanani yana tare da sauk'i kaji mijina..kai kawai yad'aga mata domin baiji zai iya magana ba.... murmushi tayi ganin hakan kamun tace, "sai magana ta biyu kana jina kuwa?"

 

Idonshi yad'an bud'e alamar Yana jinta kamun yakoma lumshesu.."hummm me hali baya fasawa ta fad'a aranta afili Kuma sai tace sai zancen aure kasani ya dace kayi aure Alyasat tinda Kaine babba kodan a samu mace agida waddda zata tayaku kula da mahaifiyarku maza hakan bazaiyu ba ya dace a yanzu ace kanada iyali shekara 30 aiba banza bane... tunda tafara magana ya bud'e idanuwanshi Yana saurararta Shi wlh yama manta sam da wani abun wai shi aure sam baya cikin lissafin rayuwarshi toma yayi aure saboda me? Ai wannan abunda habibbty ta fad'a sam bai isa hujjar dolene sai yayi aure ba? Amma zai ba wasu Suhaif dama suyi Idan suna da buk'ata... mik'ewa yayi zebar wurin ba tare da yace komai ba habibbty tayi saurin cewa to Ina zakaje baka bani amsaba..."no habibbty bana buk'ata please kibarni najida matsala na...Yana gama fad'ar hakan yabar wurin

 

Baki habibbty tarike tana fad'ar Allah kawomun d'auki kacanjawa wannan yaro halayya Abu kamar ba mutum ba.

 

Shiko ta inda yafito anan yakoma sai dai yana kawowa dai-dai k'ofar perlon Najeeb wani kalar sauti daya bashi mamaki matuk'a nishi akeyi sosai da gurnani kamar ana sex tare da wasu zantukan dabasa fita sosai harya juya ze wuce seyaji muryar Najeeb yace "ashhhh babyy dad'i ohhhhh" Ido ya zaro  Alyasat yana me tura k'ofar tashi kaÉ—an kaÉ—an cikin Æ™unan rai da tafasar zuciya...

 

Page 15&16

 

__Yana É—ora hannun akan handle d'in k'ofar sewa wata zuciyar tace masa kada kashiga Alyasat bakasan ya zaka sanmesu ba Idan shiÉ—in namijine kuma É—an uwanka itafa? Kawai karbarshi yanzu amma kasan matakin da zaka d'auka akanshi da wannan tunanin yaja baya tare da barin wurin cikin sauri yana fitowa harabar gidan ya hangi Yusuf na Lateep zasu shiga mota hannu suka masa ya k'ara Yana fad'ar, "Ina zakuje?" "Zamu shiga cikine mugaisa da mutane kasan basu gan muba..." Okay kawai yace tare da shiga motar shima zuka shiga cikin stet É—in.

 

Gidan Abba suka fara zuwa anan suka Sami mutanen gidan a perlo suna fira cikin jindaÉ—i hajiya batul ta tarbesu wadda suke kira da hajiya  babba Alhaji Jameel kuwa wato Abba cikin tsonaka yace wato kunga mamanku Ni ko oho ko? Dariya sukayi suna fad'ar, "sorry Abba" tare da zuwa suka rungumarshi gaba d'aya suna dariya Nan suka zauna suka Dan tab'a fira kamun sufita tareda nufar wani gidan.

 

Gidan baffa suku shiga wanti Alhaji Imran suna Zaid nafitowa Yana bala,I da Ameer akan yad'auki motarshi yafita shima gaya yafito cikin kakinshi na sojo ga dukkan alamu fita zeyi....Yana ganinsu yace yawwa ya sat kaga Ameer yad'auki motana yafita dashi yanzu Kuma nemana fa akeyi a Barack Idan nayi Magana mama ta ga laifina ya fad'a cikin ƙunan Rai domin Zaid akwai zuciya..."Ina yaje? Kuna inatashi? cewar Lateep...nima fa bansan inda yakai tashiba.."it's okay jeki bedroom D'ina acikin bedside akwai car keys aciki kad'auki d'aya Kuma kabar mishi waccan motar kamun muwuce zansiyama wata kahad'a da wannan okay? Cewar Alyasat...wani irin tsalle Zaid yayi tareda rungumarshi Yana ihun murna shikam alyasat cikin sauri ya cireshi daga jikinshi Yana harararshi irin zaka fasamun kunne d'innan.

 

Dariya sukayi su Yusuf kana suka shiga cikin perlon inda sukaga mama na waya zaunawa sukayi sai da tak'arasa kana suka gaidata...ta Amma tana kallon Alyasat kamun tace son ya jikin ammy? Dasauki mama...to Allah yabata lafiya?...suka amsa da ameen kana tace, "akawo musu abinci" sukace sun koshi Amma Bata yadda ba seda tazuba musu abunci tadanka ta tsaresu seda sukaci kana sukayi nata sallama suka tafi.

 

Gidan Alhaji Naseer suka nufa inda sukace daga can zasu fitane wani uzzurin daya taso musu zuwa gobe ko dadare sai su je inda Basu jeba...Koda suka shiga perlon gidan ba kowa se Muhibbat kawai dake kallo tana sanye da wasu Yan iskan Kaya duk Rabin jikinta awaje nonuwanta duk awaje nipple d'inne kawai arufe se wani iyayi takeyi...zama suka itako tataso tana gaidasu cikin kissa da kwarkwasa duk suka amsa suna d'auke kansu musamman Yusuf akwai saurin Sha,awa yanzu ne zata dagula masa lissafi danma Allah ya temakesu dukkansu ukku basa biyar Mata... Alyasat ta kallah daya d'auke kai kamar bai sanda wata halitta awurin ba tace, "Yaya sat sannu da zuwa..." Amma ko kallon gefenda take beyiba balle tasan ze amsa...ganin ya had'e rai tamau yasa Yusuf fad'ar, "Anty Billy fa?" "Tana kitchen barana kirata..."Idan kikaje karki dawo perlon Nan ahakan  kinemi kayan kirki kisaka wlh ko na k'ara ganinki da wannan banzar shigar Sena karyaki cewar Lateep dominshi kaifi d'aya ne....kamunma tayi wani motsi sukaga Alyasat ya mik'e da sauri ya bar perlon domin yasan muddin yaci gaba da tsayuwa zai iya karya yarinyarnan....Yana fita Anty Billy na shigowa perlon suka gaisa sosai da ita kana sukabar gidan gaba d'aya....suna fita habibbty tasaka kuka kamar uwarta ta mutu da k'yar Anty Billy ta lallaÉ“ata kamun tace tayi hak'uri wannan karon da dadynta yadawo zatasaka yayi magana da habibbty domin a d'aura musu aure Koda bayaso..wannan zanjen kuwa bakaramin dad'i yayiwa muhibbat ba hakan yasa tasaki jikinta kamar ba,itace me rusar kuka yanzuba..!

 

 

Ghana

 

 

Rayuwa sukeyi me tsabta acikin jejinnan kamar ya da ubanta wata irin shakuwa tashiga tsakanin mama da wannan dattijon datake Kira Abba dudda bayada wani abun dazece yasan kanshi amma fa duk abunda ya keyi da zaran ya duba bega mama ba yanzu ne zai tada hankalinshi duk ya koma wani iri wani lokacin har k'wallah yakeyi sai ya ganta hankalinshi ke kwanciya fahimtar hakan yasa mama ta dena bin su Biba Idan zaduje Nemo musu abunci sedai biyu suje biyu suzauna taredasu inda mama ce kawai ke kallon Sanu tareda wasu mutanen ammafa abbanta ita kad'ai yake gani.

 

Lokaci yaja sosai daga kwanaki zuwa watanni daga watanni zuwa shekaru ayanzu kusan shekara 4 kenan su mama suke rayuwa awannan jeji Kuma ba abunda suka nema suka rasa duk wani abun Jin dad'i da farin ciki gimbiya halila na k'ok'ari wurin Sana musushi itada abbanta kama daga abinci me kyau gar situru Wanda Kuma su mero na Nan tareda ita har wannan lokacin Kuma Basu tab'a gajiyawaba kowani abun Wanda ze bakantawa mama Kuma har izuwa wannan lokacin su bibibo d'inta Basu dawo ba awannan shekara 4 mama tazama cikakkiyar budurwa Yar shekara 17 Wanda girmanta ketafiya danasu mero domin tarik'a ganinsu kamar kansu d'aya sabida zatafi Jin dad'in zamadasu.

 

Kyawunta kuwa yak'ara bayyana domin wani irin kyau ne da ita na ban mamaki duk da su dasuke aljani mamakin kawu mama sukeyi duk da kuwa ba fara bace Allah yayi Mata Kira me d'aukar hankalin duk wani lafiyayyen namiji tanada manyan nonuwanta masu matuk'ar girma da Sha,awa Kuma atsaye suke kikam cike Tabb da k'irjinta akewaye duk yadda tasaka riga kawai sekaga tsinin nipple d'inta acikinta abun nabawa gimbiya halila mamaki Amma Bata damuba ganin inda suke rayuwa ba Wanda ze iya zuwa wurin balle ya cutadda ita gakuma masu gadinta wato su mero ikon Allah

 

Idan akazo zancen hips kuwa abun ba,a magana domin fad'in hips d'inta kad'ai abun kallo ne gakuma tudun duwawu domin koyaya tajuya sesun mitsa kamar ita keme juyasu abun gwanin d'aukar hankali irin duwawun nanne masu yiwa maza kwalele abun tubar kallah Masha Allah.

 

 

Abuja

 

Jalaludeen ne kezaune cikin office d'inshi wani soja tsaye agabanshi Yana fad'ar.. shikenan yallabai Sir yadda kace hakan za,ayi Dan kyakkyawa balaraben wato jalaludeen yayi murmushi kamun yace bakomai fa Usman zamu temaka musu insha Allah kace gobe insha Allah zamu shugo Ghana Allah yabamu nasara akansu.. ameen y Allah Sr Usman yasara masa kana yafita...shiko wayarshi dake k'ara yad'auka ganin sunan dake yawo ajikin g.n.r Yusuf murmushi yayi kamun yad'auki wayar da sallama d'auke abakinshi...bangaren Yusuf kuwa Jin yad'auka yace Yaya jalal inawuni y Nigeria? Lpy qalau Yusuf y London? "Alhmdllh Yaya jalal ai Muna Dubai munzo duba jikin ammy ne...ayya Dan Allah kugaisarmunda da ita kunji Kuna Idan kakoma gida kahad'a Ni da ita naganta please my bro nayi kewarta yafad'a cikin sanyin halinshi...."numfashi Yusuf yaja zeyi magana lateep ya girgizamai Kai alamar karya gayamai komai domin jalaludeen akwai saka Abu arai suko sun rigada sunsani domin Alyasat yagaya musu komi ganin hakan yasa yace to shikenan Idan munkoma gidan Zan Bata..Masha Allah Ina Yan uwanka jiyadai munyi wayada lateep Amma alyasat nakwana biyu banjishiba Kona Kira wayarshi baya tafiya... okay barana bashi Muna tare yafad'a tareda bawa alyasat wayar....k'anena yada shariya hakan? Cewar jalaludeen... lumshe Ido alyasat yayi Yana saurarar muryar yayan nasu kamun yace sorry my bro inata kiranka bana samune...ayya duk Kuna lpy ko? Eh lpy qalau ya jalal...Masha Allah kayimana addu,a gobe zamu shiga k'asar Ghana wani aikin wasu Yan ta addane suka harbi shugaban k'asar Ghana shine suka nemi temakon Nigeria akan wannan Al,amaren to dai sunnemi alfarman na jagoranci tafiyar Kuma zamuje gobe insha Allah...wani irin fad'uwar gaba Alyasat yaji tinda Jalaludeen ya anbaci k'asar Ghana bawai yasan k'asar bane kawai hakan ya tsinci kanshi da wannan fad'uwar gaban har abun yakasa b'oyuwa agareshi cikin rauni yace Yaya jalal karkaje  please...."hello hello Alyasat kana jina...saurin karb'a wayar Lateep yayi Yana dubansa kamun yakashe Yana fad'ar miyada zakace karyaje bro? Shiru yayi Yana sauke numfashi kamar Wanda yayi gasar tsere kamun yace I don't know kawai banaso yajene..to akanme? Yak'ara jefo masa tambayar...shiru yayi kamar bejishiba tareda mayarda idonshi ya lumshe..da Ido yusif yayi masa alamar yabarshi kawai.

 

Jalaludeen kuwa ganin wayar tayanke yasa yayi murmushi kawai tareda ajiye wayar domin Yana tinanin matsalar network ne...washe gari da safe sukayi Shirin barin Nigeria cikin jiragensu na yaki domin ko cikin garin bazasu shigaba harse sun farauto wannan Yan ta addan shiyasa kai tsaye jikin jejukan k'asar Ghana suka fara sintiri da jiragensu..!

 

Page 17&18

 

__"tinda suka shiga k'asar Ghana suke sintiri ajejuka Amma basuga wani abunda suke tinaniba kawai se general jalaludeen yace asaki wuta kawai arika Harbin k'asa daga can saman girgin Koda sun buya zasu fito

 

Aiko ahakan suka sakarwa jejuka wuta ciki kuwa hadda Wanda su mama kezaune su mero na waje suna Sha,aninsu sukaga wannan abun Basu damuba tinda sunsan ba,abunda bindiga zata musu Amma me azabure dija tamik'e tana fad'ar munshiga ukku inmu bazata tab'amuba ai mama da abbanta bil,adama ne tana gama fad'ar hakan tayi hanyar bukkarsu agiguce yayinda su Biba ke Mara Mata baya karo sukaci da mama tafito aguje se huci take tana ihun bazata yaddaba anharbar Mata abbanta k'ok'arin riketa sukeyi Amma inna seda takai tsakiyar filin jejin tana ihu tana d'aukar duwatsuna tana jifar jiragen gaya suko se ruwan wuta sukeyi....su Biba kuwa Jin tace anharbi abbanta yasa suka runtuma cikin bukkar

 

itako Niya taje sanarda gimbiya halila abunda kefaruwa gabad'ayansu ba Wanda yakoma takan mama Sam sun Sha,afa dacewa wajefa tayi Kuma wannan ta,adin kan iyasamuta.

 

Itako masifa kawai takeyi tana jifarsu wani sojane yahangeta tareda setata da bindiga yasako mata harbi akuma Dede wannan lokacin bibibo da k'awarta suka iso wurin domin dawowarsu kenan cikin azabar sauri maheerah ta gotarda ita yayinda maheer yacika yayi simtim sabida fishi atake yarikid'a yazama wani wurgegen maciji me azabar girma da tsawo  wani irin k'ugi yafara tareda cilla jelarsa yakanannad'e jirginnan dashi tareda wutsiloshi k k'asa kad'an yarage ya isarda makasha kan wani dutse gimbiya halila tadakamai tsawa tana dakatardashi.

 

""Maheer kasaukoda jirginnan ahankali karkabari wani yacutu ajikinsu...shiru yayi Yana kallonta shibe ajiye jirginba Kuma be sakeshiba....suko su jalaludeen dasukaga mutuwa afili tinda sukayi Ido 4 da wannan shirgegen macijin suke salati tareda kalmar shahada cikin tashin hankali da firgicinda Basu tab'a riskar kansu acikiba ganin macijin bekashesuba Kuma be barsuba se kawai suka fara addu,a duk wadda tazo bakinsu...cikin bada umurni gimbiya halila tace kasaukesu nace zaraah tana lpy ba,abunda yasameta...se a lokacin yasauke wani huci me mugun zafi wanda da,akwai mutin akusanbakinshi a lokacin ba abunda ze Hana zafinnan kasheshi...walwale jelar yafarayi ahankali seda yasauke jirgin se kawai yaji muryar mama na fad'ar bibibo kada kasakesu sesun bitomunda Wanda ya hirbi abbana acikinsu domin bazan yafeba Sena dau fansa wlh...Ido duk suka k'walalo Jin wannan dadd'ar murya nafad'ar Kar asakesu captain Usman yace wannan akwai sheda niyar yarinya koma wacece muryarta da Dad'i Amma zuciyarta ba Iman...shiru yayi sabida hararar da jalaludeen ya zabga masa....shiko bibibo Jin abunda tace yasaka bayan saukesu seya Kara kanannad'e su da jelarsa ta yadda ba Wanda ze iya fita daga cikinsu....shuru wurin ya d'auka nawani Dan lokaci domin duka sauran jiragen sunfece ganin wannan tashin hankalin.

 

Gimbiya halila ce tadafa mama dake mak'ale jikin maheerah tace zaraan Abba kiyi hak'uri yasaukesu inyaso bawanda zebar jejennan acikinsu se abbanki yasamu lpy...shiru tayi batace komaiba seda maheerah tace k'awata kin yadda? Eh tafad'a ahnkali kamun bibibo yashiga zare jelarsa yasake jirgin.. rikid'a gimbiya halila tayi tadawo bil adama sak dashigar gidan sarauta kana ta umurci su bibibo suzo amatsayin mutane ba dabbobi ba hakako akayi Amma duk wannan abun da,akeyi su jalaludeen basa gani sedai sunajin maganar mama dawani sauti mekamada rugugi Amma basajin mi,akecewa seda duk suka zama mutane kana gimbiya halila tak'arasa Dede k'ofar jirgjn tace kufito daga waje...tana rufe bakinta wani soja yajanyo bindiga murmushi tayi kamun tace ba,anfaninda zatayima anan kawai kufito inkuwa kunfiso nabarku dasu shikenan Sena tafi....tinkamun tak'arasa duk suka shiga fitowa seda suka fito dukkansu kana sukaja suka tsaya suna kallon kyawawan mutanen dake gabansu...maheerah taja hannun mama suka K'arasa kusansu kana tace saka makon harbe harben dakukayi kun harbe abban wannan yarinyar itama kunso harbeta wannan dalilinne yasa Dan uwana yaso hallakaku Amma antynmu tanema muku alfarma sabida hakan doline yanzu kuzauna taredamu harya samu lpy inafatar kun fahimta?

 

Shiru duk sukayi secan jalaludeen yace afuwa muke nema Dan Allah kugafarcemu dudda cewa shigowa jije damukayi yanada dalilinshi Amma sam bamuyi tinanin zamu cutarda waniba Amma Dan kuyafe Mana duk acikin larabci yake zancen domin Sam besan dawane yare zeyi sumafimtaba yadda zasufi ganewa se Kuma akayi sa,a sunajin larabcib...murmushi gimbiya halila tayi kamun tace bakomai narigada nasan abunda kukazoyi Kuma zankaiku har inda way'anda kuke nema suka buya Amma kamunnan zaku D'an zauna Koda zuwa gobe ne muga yadda jikinshi yayi seku tafi...to mungode sosai cewar jalaludeen kamun Usman yace zamu iya ganin Wanda muka raunata kodan munemi yafiyarshi..."eh bakomai zaku iya gimbiya halila tafad'a tana kallon dija alamar tafitoda abban mama bukkarsu tashiga kamun tafitodashi kuwa tuni su mero sunbaza shimfidd'o Wanda su dai su jalaludeen basuga ta inda sukafitodasuba kawaidai sunga suna shimfid'awa....fitowa sukayi rik'edashi subuyu suka samu wuri suka zaunardashi kana maheerah tace gashinan....gabaki d'aya suka juya suna duban Dan kyakkyawa balaraben dake zaune awurin.

 

Ido jalaludeen yazaro Yana fad'ar *abbee* duk kallonshi sukamayi shiko se nuna wannan tsohon yakeyi Yama kasa magana Yana neman K'arasawa wurinshi asukwane

 

 Usman ne yarikeshi Yana girgizamai Kai alamar karyaje shiko gabaki d'aya hankalinshi baya taredashi ganin hakan yasa gimbiya halila cewa Usman yasakeshi d'in Aiko Yana sakeshi yaruga aguje Yana fad'ar abbe dama kana Raye abbe miyazodakai k'asar Ghana mikakeyi anan abbe na kallanni kaga abbe jalaludeen D'inka nefa abbe nine jalal...ganin abbe nabinshida Ido kawai bece komaiba sema kwab'e fuska dayayi Yana duban mama...itako cikin sauri tazo wurinshi tareda Kama hannunshi da akaharba tana kallo tareda yimai sannnu Dan tuni su mero suncire masa harsashen.

 

Meda dubanshi yayiga gimbiya halila domin yaga tadanfi sauk'i sabida maheer dai kofuskar rahama babu ataredashi dama Dama ma maheerah cikin rauni yake fad'ar Dan Allah miyasamu abbe na? waya kawoshinan? suwayeku Dan Allah kufiddani aduhu please?

 

Ganin duk yarud'e yasa gimbiya halila fad'ar ""kwantarda hankalinka bawan Allah zamu gayama Amma dafari kagaya mana yakakedashi?

 

""Shid'in fa abbe nane k'anen mahaifinane uwa d'aya uba d'aya yab'ata shekaru da dama anata nemanshi Amma ba,asameshi Kuma tin daga Dubai abun mmki segashi a Ghana Dan Allah kunyimun bayani yadda Zan fahimta?

 

Shiru gimbiya halila tayi nad'an wani lokacin Ashe bincikene takeyi taga Idan abunda yafad'a gaskiya ne seda ta tabbatar da gaskiya yafad'a kana tace shikenan barakaji yadda muka sameshi Nan tabashi labarin tindaga had'uwar da su mama sukayi dashi har kawo yanzu kana tace dama Kuma way'annan ne muke jura kafin mukarya sihirin Kuma cikin ikon Allah gasu sundawo

 

 kallonta tamaida ga maheer tace bibibon zaraah kaga aikinda zaraah tad'auko inafatar zaka amunce kuyi wannan jahadin kodan farin cikin zaraan ka...shiru bibibo yayi nadan wani lokacin kamun yadubi mama alamar neman K'arin bayani itako marairaice face d'inta tayi kamar zatayi kuka tace please bibibo inaso abbana yayi magana... shikenan zanyi bincike akan sihirin zuwa gobe Yana Kama fad'ar hakan yabar wurin... jalaludeen kuwa k'wallah yashafe kamun yadubi mama yace Allah yasaka Miki da aljannah k'anwata dakeda way'annan bayi nasa.. ameen y Allah Mama tace tana murmushi domin hakan kawai taji yakwanta Mata bakuma k'aramun dad'i tajiba d'aya kiratada k'anwarsa.!

 

Dubai

 

Anty Billy tuni tayiwa dady zancen auren muhibbat da alyasat Kuma yaji dad'in hakan sosai inda yasamu habibbty da zancen sedai tace bazatayiwa alyasat zancenba se lokacin daya bukaci aure Dan kanshi wannan dalilinne yasaka akarufe zancen izuwa lokacinda zezoda zancen auren.

 

 

Zaune yake a bedroom d'inshi Yana kallo a CCTV daya jona abaki d'aya ila ihirin pert d'in samarin gidan abubuwa yake gani kala2 wasu subashi mmki wasu Kuma subashi haushi zancendai najeeb na neman Mata hakanne domin baccin wannan yarinyar yak'ara zuwa dasu maban banta matan

 

 yauko abunda yake kallone kebashi mmki matuk'a muhibbat ce kwance akan shareef tana wasada sumar kirjinshi shiko se wani lumshe Ido yakeyi Yana tura hannu cikin rigarta tareda damk'o breast d'inta Yana murzasu cikin shauk'i ganin abun nasu naneman zarta misaline yakashe dasauri Yana mek'ewa tsaye sintiri kawai yakeyi a bedroom d'inshi shin Mike shirin faruwada ahalinsu ne? Yaya dakanshi ze lalata k'anwarshi? aikoba mahaifansu d'aya ba ita d'in jininsuce miyasa shareef zeyi hakan? Dama muhibbat tasan maza kenan kumama yayunta innalillahi wa innailaihhiraji un abunda yaketa maimaitawa kenan kamun yakwashi wayoyinshi yafita.!


Ghana

 

Zaune suke dukkansu afilin inda bukkarsu mama take sunacin abunci dudda basusan daga Ina yafitoba amma karamcin way'annan bayin Allah yayi musu dad'i sosai...mama kuwa tana zaune tana bawa abbanta abaki Yana kallonta itako se murmushi takeyi jalaludeen ma yakasa cin nashi kallonsu kawai yakeyi tareda tsananin mmki aranshi... Maherr da tind'azu yake tsaye awunrin Yana kallon yadda mamarsa ke farin ciki sekawai abun yayi masa dad'i se yanzu yayi gyaran murya tareda K'arasawa wurinsu d'auke da sallama abakinshi..!

 

Page 19&20

 

Free page yak'are daga wannan kiyi hanzari kinemi naki domin karki Bari abaki lbr

__"amsawa sukayi duk suna kallanshi kana yasamu wuri yazauna kusan mama yace""uwar gijiyata nayi bince akan sihirin sedai kamar yadda anty halila tace doline sedake zamu karyashi nisawa yayi kamun yasake cewa aikin Yana cikin ruwa acan akajefashi Kuma gudu yakeyi yadda wannan sihirin ke gudu hakan abbanki zeyita yawo aduniya batareda sanin takamammen inda zashiba ajiya nasaka antsayarda aikin inda zamu samu sauk'in kamashi sedaifa bawanda ze iya fiddashi acikin ruwannan se bil adama sabida hakan Idan kinshirya semuje.....kamun tayi magana jalaludeen yayi saurin cewa aa kabari Ni muje ai wannan tayi k'arama kartasaka kanta ahad'ari...murmushi gimbiya halila tayi kamun tace ba Wanda ze iya wannan se ita domin tana tattareda abunda bakadashi sabida hakan kabari suje kawai kaide kayi musu fatan nasara...nisawa yayi kamun yace shikenan Allah yabasu sa,a akan abunda zasuje nema... ameen y Allah duk suka amsa kana mama tamik'e tana cewa bibibo suje mik'ewa shima yayi kana maheerah ma tamik'e sukabar wurin seya rage daga gimbiya halila sesu mero datawagar sojojinsu jalaludeen..!

 

Dubai

 

Alyasat nafita yawuce part d'in yusif aperlo yasameshi zaune Yana aiki a computer d'inshi zama yayi kusadashi tareda jingina bayanshi jikin kujerar batareda yace komaiba tinanin yake aranshi wannan wanne irin Bala,I ne ace y'ay'a family d'aya Amma suna neman junansu Idan son muhibbat shareef keyi baze auretaba itako dake fad'ar tana sanshi Ashe duka karyace Aiko zeyi maganinsu....tinaninshi ne yakatse lokacinda yaji yusif nakiran sunanshi yad'ago shima Yana dubanshi..."Miyake faruwa ne bro Naga kayi shiru se tinani kakeyi? Dan yamutsa face d'inshi yayi kamun yace no bakomai kawai inasan komawa London ne kamun mudawo bikinnan daza,ayi kaga daganan semu dawo aikinan Baki d'aya ko?

 

Shiru yusif yayi nadan wani lokacin kana yace hakan zeyu kuwa? "Eh mana kodama bazeyuba nibazan cigabada zama acanba domin gidannan namu akwai matsaloli sosai gaskiya doline murik'a saka Ido gudun faruwar wani mummunan abun...nisawa yusif yayi yace hakane bro to kodai kaga abunda kefaruwa ne acikin stet d'innan?

 

Da mmki alyasat ke dubanshi kamun yace wani abunne yafaru?

 

"Humm zokaga yusif yafad'a Yana nuna masa abunda ke cikin computer d'inshi...Ido alyasat yad'an bud'e kamun yadafe kanshi domin abunda yagani yabashi mmki sosai dudda yaga wani shima Amma beyi tinanin abun yake hakanba...ganin yayi shiru bece komaiba ne yasa yusif fad'ar yanzu minene abunyi?

 

 

"Humm zamuyi maganinsu soon bro daga hakan bek'ara cewa komaiba..ganin hakan yasa yusif fad'ar tashi muje mud'auko wani mlm danayi magana dashi akan rashin lpyr ammy tind'azu yace mun suntaso nasan izuwa yanzu jirginsu yakusa sauka daga saudia zezo...dobanshi kawai alyasat yatsayayi Yana tinani aranshi inama ace dukan soldiers family kamar yusif suke sedai Kash kowada kalar nashi ha layyar....seda yusif yarik'o hannunshi kana yamik'e suka Kira lateep sukabar gidan..!

 

 

Ghana

 

 

Suna fita suka d'auke mama tareda shiga keta jejuka da ita basuzarce ko inaba se wani k'aton teku Wanda mutin be Isa yace ga tsawon ruwan ko fad'insu ba balle ayi zancen ganin karshensu seda sukakai Dede wani katon dutse da ruwa kifita cikinshi suna gangarawa kana bibibo ya ajiye mama tareda fad'awa cikin ruwan itako maheerah tana tsaye tareda ita duk wani aljani Idan yazo wucewa yahangi mama seya kawo Mata Hari sedai daga zarar sun k'araso duba d'aya suke Mata sukoma bashiri (komiyasa hakan)

 

Yad'auki tsawon lokaci acikin ruwan kamun ya k'walawa maheerah Kira Yana fad'ar yasamu ganin sihirin tashigo da Mama Aiko ko bakinshi be rufeba tarik'e mama suka nutsa aciki can kasan ruwan wani katon ledane aka nannad'e kamar ball ko tarewarda maheer yayiwa abun yakasa tsayi wuri d'aya cikin k'araji yacewa Mahira tanunawa mama tad'auka domin masu tsaronshi gab sukeda k'arasowa wurin...tana nunawa mama tasaka hannu biyu tareda bismillah tad'auko Amma me tana rikonshi aka fara janta kamar igiyar ruwar zata tafida ita ganin hakan yasa sukayi saurin fitowada ita ta gab'ar ruwan suna fitowa maheer yace tadoka abun ak'asa Idan tayi hakan baze k'ara komawa cikin ruwaba Kuma kowa ze iya k'arasa aikin

 

Hakako tayi domin dagewa tayida iya k'arfinta tadokashi k'asa aitana dokashi itama ana wullata cikin ruwan hakan sukaga anjefata kamar walk'iya kamun maheer yayi wani yunk'urin tuni maheerah tabi bayanta Amma se tamaula ruwan keyida ita sunaneman hallakata dak'arfi gaske Mahira tasamu nasarar cabkota kana tafitoda ita Amma tuni tasuma...seda suka B'ata lokaci sosai wurin ganin sun ceci rayuwarta seda ta farfad'o dudda batadawo normal ba kana suka shiga kiciciniyar walwale wannan sihiri wani irin mird'ewane akamasa wani abun cikin wani hakan sukayita banye abubuwa daga karshe suna Kai karshen kullin sekawai sukaga guntun takalmine dawani Kashi se dunkulin jini da babyn roba mekamada wancan dattijon sak...suna gama bud'ewa maheerah tak'ona kayan.

 

 

Aiko zunbur abban mama dake kwance tin bayan tafiyarsu yamik'e tsaye kamar Wanda aka tsikara duk seda suka bishi da kallo arazane Amma Banda gimbiya halila daketa famar murmushi...shiko rik'e kanshi yayi dake juya Mashi sosai kana yayi baya luuuuu ze Fad'i cikin sauri jalaludeen yataroshi yafad'a jikinshi... d'agowa yayi Yana kallon gimbiya halila kamar zeyi kuka se kawai ta girgizamai Kai alamar karyayi...shiru yayi Yana duban abbe nasu yakai kusan minti 5 ahakan kamun gimbiya halila tacewa mero takawo ruwa ba musu kuwa mero takawo mikawa jalaludeen tayi tana fad'ar kayi addu,a tukunnah kashafa masa a fuska...hakanko akayi bayan yakarb'a yayi addu,ar kamar yadda tace kana yashafa masa a fuska atake yasauke ajiyar zuciya me k'arfi kana yafara bud'e idonshi da salati d'auke abakinshi yabud'e su tarr akan fuskar jalaludeen...yunkurawa yayi zetashi jalaludeen yatemaka masa yatashi kana shiga k'arewa wurin kallo cikin sauri jalaludeen yace abbe.

 

""Na,am jalal inamuke anan mimukeyi anan? Ina alyasat?

 

"Alhmdllh alhmdllh alhmdllh shine kawai abunda kefitowa daga bakin jalaludeen yabud'e baki zeyi magana kenan su bibibo suka bayyana awurin yanad'auka mama...cikin sauri gimbiya halila tamik'e Wanda sukayi atare itada jalaludeen miyasa meta maheer? Cewar gimbiya halila...karkidamu tajigatane sabida matsalar da kasamu Amma komai lpy insha Allah..to alhmdllh tafad'a tareda bashi wuri ya kwantarda ita... maheerah ce tashiga Basu lbrn abunda yafaru acan dakuma yadda sukayida abunda suka d'auko...shidai jalaludeen inbanda tasbihi ga ubangiji ba,abunda yakeyi...yayinda gimbiya halila tayi musu Adda,a sosai dakuma fatan alkhairi taname jinjinawa kannen nata dasuka kasance bayan sallah nagani

 

 

""Nisawa tayi tana fad'ar aiki yayi kyau sosai maheer domin abban zaraah yasamu lpy.. dukkansu murmushi sukayi hadda jalaludeen shiko abbe biye kawai yakedasu Yana kallo domin Sam besan inda kalamansu suka nufaba Kuma bayajin hausa garama jalal yad'an ji sabida zamanshi Nigeria

 

Ganin irin kallonda yake musune yasa gimbiya halila fad'ar sannu bawan Allah nasandai dukkanmu Nan baka sannumuba bancin wannan

 

 

Tanuna jalaludeen dake zaune kusanshi d'aga Mata Kai yayi domin da larabci take magana shiyasa yafahimceta... cigaba tayida fad'ar to abunda yafaru gaskiya wannan yarinyar itace silar had'uwarmu dakai tanuna mama dake kwance kana tabashi lbrn tin lokacin da mama ta tahad'u dashi har izuwa kawo yanzu da sihirin yabar jikinshi shera 4 kenan..seda takai karshe kana tace kaji yadda akayi muka sameka har zuwan wannan bawan Allah yace Kai abbanshine..

 

Shiru kawai abbe yayi Yana sauraronta idonshi suncika Tabb da k'walla Yama kasace komai se aikin kallon mama yake

 

 

Jalaludeen kuwa se murmushi yakeyi seda gimbiya halila tace kagaya masa yadda kuka rasashi domin hankalinshi yak'ara kwanciya Nan ko jalaludeen yabashi lbr iya abunda yasani na b'atanshi dakuma tashin hankalin da ahalinsu suka shiga Amma ya boye masa cinwon ammy...awannan Karon kuka sosai abbe keyi bawanda yahanashi domin dukkansu sunsan abunda ciwo sosai arabakada ahalinka natsawon shekaru...ana cikin wannan halinne mama tafarka tana turo baki gaba tana Kiran bibibo

 

 

*SOLDIERS FAMILY* complete ne ga duk me buk'atar complete akwai ak'asa 💃

 

 

 

Murmushi sukayi atare kana bibibo tarik'ata tatashi zaune kamun yace uwar gijiyata abbanki fa yasamu lpy...wani irin k'walalo Ido mama tayi kamun tasaka ihun murna tamik'e aguje taje gun abbe dake zaune Yana kallonta sekawai Tafad'a jikinshi tana abbana kawarkeko? Bazaka Kara ciwoba insha Allah yanzu mikakeso abbana naje nasaka Biba takawoma? Jin yayi shiru Kuma biyi Mata yadda yasaba ba seta d'ago tana dubanshi taga shid'in ma ita yake kallo kunya taji takamata atake Kuma jikinta yayi sanyi data tuna yafa samu lpy kardai ace yamantata janye jikinta tayi daga nashi zata Mike sekawai taji yamaidata Yana shafa bayanta hawaye nazuba a idonshi  godiya yakesan yimata Amma yakasa furta komai se aikin shafa bayanta yakeyi Yana hawaye Koda ba,a bashi lbrn ta ba iya yadda tayi yanzu da,akace yasamu lpy ya,Isa yanuna masa tsananin sonda take masa shiko mizeyiwa wannan yarinya yabiyata aduniya...sunjima ahakan sosai kamun yad'agata Yana fad'ar ngd ngd ngd sosai y'ata Allah yayimiki albarka Allah yabaki ingattacciyar rayuwa Allah yabaki Ni,imar duniya data lahira Allah yabaki miji nagari Wanda zekulada rayuwarki cikin amunci... dukkansu da ameen suka amsa kana wurin ya keceda fira kowana bada lbrn abunda yasani kamun haduwarshi da wani..!

 

 

Dubai

 

Suna kan hanyar zuwa d'aukar mlm Abba yakirasu yace suzo yadawo ance suna nemanshi...to kawai sukace tareda K'arasawa suka d'auko mlm pert d'in ammy sukakaishi inda sukace suhaif da alhusain sukaishi inda ammy zasuje suga Abba...hakanko akayi bayan sunje gun Abba sunjima awurinshi suna tattaunawa bayan sungama kana suka fito kowannen ji yakeyi kamar ancire masa k'aya ajiki ahakan suka Isa pert d'in ammy suka samu mlm nazaune shida su Al Hassan domin yaduba ammy har an mayarda ita d'aki wuri suka samu suka zauna..

 

Kana mlm yashiga yimusu bayi ""agaskiya ciwon mahaifiyarku ba komai bane face babbak'un aljanu sune aka izo Mata Kuma akowacce Rana ta duniya tsafi sukeyi ajikinta domin ba,abuk'atar tawarke Kuma Basu tashi kashetaba ba,ba,abunda zance muku anan illa kudage da addu,a Kuma akwai wasu addu,oi dazan Baku zaku Rika yimatasu da maganin dazan,arika yimata wanka ana shafe mata jikinta sedaifa kusani abune me matuk'ar wahala rabatada way'annan hatsabiban alajanun shiyasa nace kudageda addu,a....nisawa suhaif yayi kana yace shikenan mlm mungode sosai Kuma insha Allah zamuyi yadda kace.

 

To allah yabata lpy...duk suka amsa da ameen shidai alyasat Yama kasa magana domin inba lugudeba Babu abunda zuciyarshi keyi tinani yakeyi wayayiwa mahaifiyashi wannan mummunan abun? Mita aikata agaresu da har za,acutarda ita? Atake yaji komai na stet d'in yafara tsanarshi domin inba nanba to wazemata wannan mugun aikin lallai shakka Babu duk Allah yatoni asirin Wanda yayi Mata wannan abun to sedai uwarsa ta haifi wani wlh...wannan tinanin dayakeyi shine yusif keyi hakama su Al,Hassan lateep dabaya boyone kawai yafitarda nashi Ali bayan sunyiwa mlm rakiya sundawo kallonshi duka sukayi Jin yafad'i abunda ke zukatansu kamun sumeke zuwa Shirin masalachi domin yau jimu,a.

 

 

Dukkansu sunshirya cikin manyan Kaya na larabawa jallabiya ce ajikinsu da hirami sunyi kyau matuk'a kamar kasacesu kagudu...shidai gogan natse yagame fuska kamar besan minene dariyaba lateep ne yakalleshi kamun yace kaikam matarka nada aiki bro wannan cin magani hakan humm lallai zatasha fama...dariya suka saka atareda yusif yace Kai bro wato bama shine zesha famaba ita? Eh mana lateep yafad'a Yana k'ara kallon alyasat d'aya Kara yaderai kamar besan dashi sukeba...maganar lateep ce tamakale jin ana sanarwar an d'aura auren shareef da muhibbat se najeeb da yusra sadeeq da Maryam se Kuma sulaiman da ashnah dukkansu akan sadaki dubu d'ari Allah yabasu zama lpy..

 

Se a lokacin wani k'ayataccen murmushi ya bayyana akan kyakkyawar fuskarshi Yana shafa kwantaccen sajenda yayiwa fuskarshi kawanya..shiko lateep da yusif dariya sukayi lokaci d'aya ganin yadda fuskar dake mutuk'e yanzu tawayeda anuri ahakan suka nufi gidan zuciyarsu fyass..!

 

 

Ghana

 

 

Shiru wurin yad'auka suna saurarar gimbiya halila inda take cewa abbe""""bawan Allah bawai baka zaraah ne bamasanyiba aa zaraah amanace awurunmu bamasan abunda zesakata kuka arayuwarta domin muma wani gefene ita na rayuwarmu zamu iya isko zaraah aduk inda take afad'in duniya sedai abunda ka,iya zuwa yadawo ne bamaso tinda har aka,iya yima wannan aika aikar acikin jinsinku tofa ko zaraah wata Rana zasu iya cewa sucutarda ita....

 

""Idan ko hakan taru Sena k'ararda ahalin duk Wanda yayi gangancin yin hakan cewar bibibo dake cika Yana batsewa..

 

""Nafahimceku Kuma insha Allah baza,asamu matsala ba inaso na inganta rayuwarta acikin mutane Yan uwanta tinda rayuwa ajinsinku bazeyuba Kuma nabaku dama na Kuma amunce ga duk Wanda yayi yunk'urin cutarda ita m

Kuhukuntashi... shikenan zance yazo karshe cewar maheerah dukkansu murmushi sukayi Banda jalaludeen daya Lula duniyar tinani Wai sune kezauneda aljanu suna magana Baki da Baki kamar mutane Yan uwansu lallai inbaka mutuba kallo bek'are makaba aduniya.

 

Kallo mama bibibo yayi yace uwar gijiyata aizakibi abbanki ko? "Eh tafad'a ahnkali kamun tace to kufa? Dariya yayi kamun yayi magana maheerah tace duk inda kike a fad'in duniya Muna taredake k'awata iyarai da mutuwa..Aiko tawashe Baki tana dariya ahakan suka shiga jirginsu se garin Abuja inda jalaludeen yabar wasu daga cikin tawagarsu subi gimbiya halila takaisu gun way'anda sukazo nema ajeji captain Usman ne yajagoranci tafiyar..

 

Bayan saukarsu Abuja akashiga yiwasu abbe shirshiryen tafiya shida mama domin basuda passport da visa...cikin kwana ukku aka gama komai inda jirginsu yad'aga zuwa *Dubai* k'arfe 4pm jirginsu yasauka Al Hassan ne kawai yasanda zuwan nasu domin Shi kad'ai jalaludeen yagayawa Aiko yayi kuka yayi farin ciki marar misal tuwa Shi kad'ai yaje dokosu tin a filin jirgin dayaga abbensu ya rungumarshi Yana kukan farin ciki dakyar abbe ya,iya Raba jikinshi danashi kana yarungumi jalaludeen daganan suka shiga mota zuwa gida mama da abbe ne abaya jalaludeen kuwa na gefen Al,Hassan ahakan suka shigo cikin stet d'in Wanda tin daga babban Gert d'in shigowa stet d'in mama taware idonta tana kallon abunda idanuwanta kegani wasu irin miyagun halittune masu ban tsoro da firgici kowanne Yana sintiri asama da makamai ahannunsu kamar masu Shirin yak'i wani mugun launi da kallar stet d'in kebadawa kamar hadari ya had'u irin me Baki da jaa d'innan Kuma be saukoda ruwaba...cikin mmkin wannan tashin hankalin datake gani suke tafe har suka K'arasa bakin pert d'in habibbty duk suka fito nan ma kallon abunda ke faruwa tsakanin pert d'innan biyu takeyi wannan dasuka tsaya dakuma wani dakecan gaba Wanda ba pert d'in kowa bane Sena ammy wasu kalar launuka kefita daka kowanne part acikinsu gakuma wasu halittun nanma abun tsoro ahakan abbe yarik'e hannunta ganin tayi tsaye suka shiga cikin perlon habibbty..!

 

 

Tofa wannan wanne irin abune ke faruwa acikin wannan stet?

 

Shin minene alak'ar dake tsakanin mama dasu gimbiya halila?

 

Ina dangin mahaifin mama suke?

 

Shin suwaye kena hannun acikin wannan mummunan abun da,akejifar ahalin habeeb shuraim dashi wato abbe?

 

 

Wanne irin zama mama zatayi acikin wannan stet d'in me tattareda abubuwan mmki da Al ajabi bugu da Kari kartawan sojojin gidan taza Kaya atsakaninsu?

 

Duk kubiyoni acikin *SOLDIERS FAMILY* Pat 2 danjin yadda zata Kaya

Karanta: Life Partner Hausa Novel Part 2 Complete

Post a Comment

0 Comments