Gidan Sarauta Complete Hausa Novel
GIDAN SARAUTA Page 1
Bismillahir rahmanir Rahim,in the name of Allah,the most gracious and the most merciful
Assalamualaikum my fellow Sisters and Brothers in Islam,may Allah bless you all.as I'm starting my new book I ask Allah subhanahu wata'ala to guide me through and make it successful till the end
Amin ya Allah....
Littafinnan nan is a fiction duk wanda taga yayi kama da labarin rayuwarta ko shi to suyi hakuri don Allah akasi akasamu bawai anyi dagangan bane
MASARAUTAR ZAZZAU
Katuwar masarauta ce dabazan iya misalta muku girmanta ba wanda inka shiga cikinta garine guda donko tako ina kai kawo akeyi kama daga bayi dakuma kuyangu kowa da potion din aikinsa wasu na bangaren girki,wasu suna tsaye matsayin dogaraye wasu kuma na fannikan gidan suna gudanar musu da aikin daya kamata.....
Masarautace babba wanda ke daukeda bangararruka daban daban hakanan takunshi kofofi kala kala,masarautace mekyau don tundaga wajenta zaka gane an xuba kudi gurin tsara gurin intsaya inamuku bayanin wannan masarauta wani bata lokacin ne don nasan kunsan kyauwun masarauta barin ma ace na zaria......
Tafiya yakeyi ahankali kamar bazai taka kasa ba,kaman wanda tsoron kasan yakeji yana sanye cikin kananan kaya black T-shirt da Black jeans tunda yake tafiyar yake wuce dogaraye dake tsaye amma cikinsu babu wanda yabashi girmamawan daya kamata sema kuskus da wasu suka shigayi suna gulma,ko kallo basu ishe shi ba in fact kanshi kasa yake har yakarasa wani madaidaicin kofa wanda ina iya cewa daganin side din yana daya daga cikin bangare marar kyau cikin masarautar baki daya, tunda yadoso gurin banga halaman kuyangu ba gurin shiru kaman wanda anyi mutuwa ahankali yatura kofar yashiga tareda rufo kofar....
wata yar kofa yashiga wanda itakadaine nagani acikin compound din sauran kuma fili ne yar kankanuwa wanda ke dauke da tarkace sekuma wani gefen murhu ne da dan tukwane na girki,seta dan gefe kadan kayan wanke wanke ne ah ahjiye masu datti da alama dai nan gurin ahalin gidan ke wanke wanke dakuma girki kaman yanda yataho kanshi na kasa haka ma yanzu still kanshi na kasan ko sallama babu yashiga gidan wasu yan mata biyu na hango suna zaune ah tsakiyar parlourn sun zabga uban tagumi parlourn kuwa ko kujeru babu cikinta kafet din dake shinfidema tayi daka daka daita,takode duk tafita hayyacinta karasawa yayi gabansu tareda cewa yajikin Ummi?....
Dayar ne datake matukar kama dashi tace"to Yaya Almustapha dasauki za ace"....
wucesu yayi yashiga dakin batareda yace komai ba,karewa dakin kallo nashiga yi shima kafet ce irinta parlourn tayi daka daka daita sewata katuwar katifa da wata dattijuwa ke kwance akai ko motsi batayi da alama katifar ma taci duniya...
Zama yayi ah dede setin kan dattijuwar tare da sa hannu yana taba temperature din jikinta idanunta biyu amma bata magana sede binshi da idanu datakeyi,rike hannunta yayi sosai cikin nashi ahankali cikin muryarshi me sanyi dakyar yace "Sannu Ummi",batace komai ba kuma bawai daman yayi expecting tayi maganar bane tunda yasan batayi din yajima zaune gurin yana kallonta kamin daga baya yajingina kanshi da jikin gini tareda lumshe idanunshi.....
Afiya kanwarshi ce tashigo tareda zama gefenshi,yaji shigowanta don haka yabude idanunshi yadaurasu kanta Yaya Almustapha bamuci abinci ba yunwa mukeji....
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace kayan abincin sun kare ne?....
Jijjiga mishi Kai tayi alamar eh,tashi yayi batareda yace mata komai ba yafita komawa gun yar uwarta Amira tayi don tana da tabbacin yafita nema musu abunda zasu sama bakinsu ne,yau kimanin shekaru 15 kenan ace dai tun da suka dan yi wayau amma babu wanda suka sani amatsayin ubansu dayawuce Yayansu Almustspha,shine cinsu hakana shine shansu,biyan kudin makarantarsu ne kawai baya musu shima sabida akwai makaranta free cikin masarautar both islamiya da boko dukda kuwa har suka kare karatunsu na firamare da kuma secondary dasuke yanzu ss2 kullum ana cikin tsangwamarsu dayi musu gori,kaf rayuwarsu basu san miye jin dadi ba se wahala,basu da walwala,basu san miye farin cikin rayuwa ba,sunsan ance ubansu ne sarki ubansu ne ke mulkar garin zariya sede sunanshi kawai sukeji basu taba ganinshi ba dukda kuwa suna muhalli daya,basu san dadin uba ba don ko neman su betabayiba hakana bedamu da sanin ko suna existing ko baswayiba shiyasa sometimes idan common bayi da kuyangu namusu wulakanci basu taba damuwa tunda wanda yayi sanadiyar zuwansu duniyar kuma me gidan be damu dasuba bare har yasa wasu suga mutuncinsu.....
Amira ne tadubi Afiya tace Sis,nitunda nake bantaba ganin me irin rayuwarmu ba hakana bantaba ganin me rashin sa'a irinmu ba,anya kuwa dagaskene mu 'ya'yan Sarki Abdulrahman ne,anya ba tsinto mu akayi aka kawomu gidan nan tareda mahaifiyar mu suka taimaki rayuwarmu ba.....
Afiya rasa abunda zatacema yar uwar tata tayi se hawayene daya fara ambaliya ah idanunta, Amira kuwa bazama ta iya kukan ba don inda sabo tasaba,tayi kukan tagaji har hawayenta sundaina wahal dakansu tunda basu taba samun me lallashinsu ba,kara numfasawa Amiran tayi tareda kura ma ceiling ido tana
Jin sautin kukan yar uwartata har cikin ranta.......
Sunfi awa suna zaune ah haka sega Almustaphan yadawo rikeda yellow and black leda ah hannunshi,karba sukayi suna mishi godiya"kuyi anfanida wannan kafin nasamu kudi insayo kayan abincin"....
To Yaya,mungode juyawa yayi yafita batareda yace musu komaiba,duba ledar Amiran tayi shinkafar gidace yasiyo da alama kwano daya ne se taliya guda biyu dakuma mai ah leda,"bari mudafa shinkafar da wake tunda ga mai kuma akwai sauran yaji ko, takarashe maganar tana duban yar uwarta don neman karin bayani...
Eh kawai Afiyan tace mata yayinda Amiran ta dauki ledar tafita don fara gudanar da aiki...
Tunda Almustapha yafita ah masarautar yarasa ina zeje yazauna yaji ko ransa zatayi masa dadi...
Gidane madaidaici wanda bazaka ganshi kace talaka ke zama cikinsa ba haka na bazaka ce gidan masu kudi baneba sede ace ma masu gidan middle class people ma'ana irin muhallin masu rufin asiri,wanda basu rasa ci ba bare sha hakama sutura suna dashi dede gwargwardo......
Shiga nayi daga cikin gidan inda naga bangare uku ah jere ne sede na tsakiyan yafi girma sena gefe biyun Kuma duk girman su dayane sekuma daga can nesa nahango boysquaters dakuma dakin me gadi dayake daga bakin kofa kusa da gate,balaifi filin gidanma ya hadu don anyi interlocking dinsa yayinda andan yi shuke shuken flowers ta gefe sekuma can gefen hagu dam ne agefe da tank ah sama anyi decking aka daura akai se parking space dake dauke da motoci guda uku masu kyau cikinta......
Daya daga cikin bangaren nashiga wanda su biyu girman su daya wata tsohuwa nahango zaune kan kafet yayinda wata yar budurwa ke kwance kan cinyarta tsohuwar na tsefe mata kitson kanta tundaga nesa ka hango gashin sekaji yaburgeka tsabar kyaunshi dakuma tsayinshi,yarinyarne cikeda shagwaba wash Hajja dazafi dai......
Yihakuri Me suna nadaina miki dazafi turo yar bakinta tayi gaba sannan tace to kokefa,dariya Hajjan tayi sannan tace kede ba a raba ki da raki wallahi suna cikin haka ne suka jiyo sallama daga waje ansawa Hajjan tayi yayinda Asiya tacigaba da kallonta ana mata tsifa....
"Aa Mubaraq yau kataso da wuri kenan?"....
Saurayin da aka Kira da Mubaraq yasamu guri yazauna yana cire hulanshi
"eh wallahi Hajja kinsan yau juma'a daga massallaci nataso senaji yunwa nikeji Kuma yau banda niyar cin abinci ah waje"....
Tabune baki Hajjan tayi tana "Uhmm,aikadinga fama kuwa tunda mutum shi bazai nemi mata yayi aureba har yaushe"....
Yar dariya yayi don yasan ya cakalota yau, karki damu Hajja nima nadamu nayi lokacine beyi ba...
Harararshi tayi...
"aikullum maganar kenan mutum shekaru sunja ancemaka shekaru talatin da biyu wasane?"
Sosa Kai yayi Yana ayi hakuri Hajja za asan nayi,kaikasani dai...
Selokacin ma ya lura da Asiya dake kwance anamata tsifa,cikeda bacin rai yace wannan din Kam Asiya ce ko?....
Se lokacin tadago tadube shi,wani tsawa ya dirar mata wanda har Hajja seda ta zabura"ke wato baki da kunya ko?"...
Iye,ba magana nake miki ba minti na nawa da shigowa amma ko kallon inda nake bakiyi ba sabida ke figagga tashi kibani guri banason kallonki....
Tsaki Hajja tayi tana ya isheka,kana shirin cire mana dodon kunne be ishekaba harsaika korar min mesuna ko bakaga tsifa nake mata bane ba?...
Amma dai Hajja kinsan abunda take bata kyautawa ko intana mana mu na cikin gida wataran ana waje zatayimawa bekamata ana barin taba...
Kamin shiru nace,kadebo gajiya zakazo ka takurama yarinya kakira wance tasaba ma bautar tayimaka mana tunda dai kasan wannan din bayi zatayiba nifa banason anatakura ma jikokina wallahi,kuda kuke yara wayamuku haka? ....
Zuciyarshi tafarfasa yakeyi amma babu yanda yaiya da Hajja inbahaka ba seta hadashi da Daddy abun yakoma wani abu daban don haka yabuga tsaki yatashi yashige ciki Asiya kuwa tayi lukwi ajikin Hajja kamar munafuka.....
Dakin Mommy yashiga batanan seyawuce kitchen don acan yayi tsanmanin samunta itada 'Yar lelen nata,tunkan ya Isa yakejiyo kamshin girki yakaure ko Ina murmushi yasaki yayinda yakarasa cikin kitchen din yana sanda rungume Mommyn yayi tabaya Yana Mommyna wani delicious kike girka mana haka?....
"Mubaraq you'll never change,you always behave like a seven year old child"...
Murmushi yasaki mekarama kyaukyawar fuskarsa annuri yakarbi wukan dake hannun nata ya ajiye gefe sannan yakamo hannun duka yayi kissing"Mommy nihar zan girma ne ah idanunki?, I'm always your little boy and I'll always be".jijjiga Kai tayi tare da jan cheeks nashi to naughty Boy kabarni nayi aiki Daddynku yakusa dawowa.....
Dariya yarinyar dake gefe tasaki wanda akallo daya dana mata bazata wuce sa'ar Asiya ba,yankan fruits take abunta ahankali Kuma cikin nutsuwa Ina wuni Yaya Mubaraq,tayi maganar ahankali cikin yar siriruwar muryarta.....
Lafiya Lau Ma'ulele ya aiki?....
Alhamdulillah,yanaka yau ka dawo dawuri....
Kede bari yar kanwata yunwa ne yagudo dani naji nan duniya babu girkin wanda nakeson ci sena Mommy da Ma'ulele,dariya tayi sosai na yanda yayi maganan tun tana nuna batason sunan dayake kiranta dashi harta hakura don ta lura bayida niyar bari.......
Karasa yanka last pineapple din tayi tareda ajiye knife din....
Mezan kawo maka kaci to?....
Duk abunda ya sauwaka,to Big Brother consider it done....
Dan Bata rai Mommyn tayi tana Ina Asiyan itabazatazo takai maka ba ko baka ga aiki mukeyibane mudin....
Mommy kinsan Hajja ae...
Jijjiga Kai Mommyn tayi batasake cewa komai ba inda Asmaun tace yanzu zankai mishi indawo mukarasa.....
To Yar albarka sekindawo,haka tazauna tahada mishi abincin kan tray sannan tafice takai mishi side dinsu inda yayunsu biyu ma nanan biyun Kuma basu dawoba don haka seda takuma Karo abincin dakuma cokala kamin takoma gurin Mommyn don su karasa tanajin Hajja nata mita yarinya se shegen wayon tsiya dason nuna tafi kowa sanin yakamata,kekuma Zainab Kita biye musu wataran seta sa yayanta sun rabaki da naki Ya'yan tukunnan, murmushi Mommyn tayi tanaji sannan tace Husna karkibari maganar Hajja tamiki zafi kinsanta se ahankali....
Asmau da hawaye yacika idanunta tayi karfin halin rikesu tana Mommy karki damu inda sabo ai munsaba yanzu Kam......
Shafa kanta Mommyn tayi sannan tace Allah yamiki albarka kiyi mugama kada Ummi taneme ki acan bakyanan.....
To kawae tace mata inda suka cigaba da gudanar da aiki seda suka gama tas sannan suka kai na mahaifinsu side dinshi kamin tatafi side dinsu.....
Ah parlour tasamu mahaifiyarta nama kanwarta Munira kitso wanda suke matukar kama se Munir twin brother din Muniran dake can gaban TV yana game.....
Munir wai yau babu islamiya ne katasa TV agaba?....
Befasayin game dinba yace Adda Asmeey anbamu hutu jiya nafadamiki ae sede inkin mata....
Murmushi tayi ehto kilan mantawan nayi.....
Kinmanta Kam don inajin sanda yake fada miki cewar mahaifiyartata,Ya Hajja suke?...
Lafiyansu kalau Ummi,yanzu muka gama girkin Daddy yakusa dawowa murmushi Ummin tayi sannan tace to sannu da kokari sekishiga ki watsa ruwa ko?.....
To Ummi Ina Sadiq ne baya side dinsu....
Yayi wani gun kenan tunda baki sameshiba inkinyi wankan kidan wankemin jikin autana tana bacci ah daki banason tacigaba da baccin nan laasar takusa....
To shikenan cewar Asma'u din sannan tatashi tashige dakinta babu bata lokaci tashiga tube kaya.....
*Asalinsu*....
Alhaji Muhammad Dan asalin katsina ne daga wata kauye batagarawa wanda nanne asalin iyayensa sede as time goes on and yanayin budewar rayuwa se suka koma cikin birnin katsina da zama inda yayi karatunshi kama daga firamare har secondary daga nanne kuma yasamu gurbin karatu ah jami'ar Ahmadu Bello University Zaria inda yakaranci Business administration bayan ya kamalla karatunsa da service ne yasamu aiki cikin garin zariya inda nanne yazame masa gurin zama se in yasamu sarari ne yake zuwa duba iyayensa can cikin garin katsina....
Wani zuwa dayayi gida ne Hajja da mahaifinsa suka matsa masa maganar aure to anan ne yace musu shibaida zabi ah yanzu don besaka maganar aure ah gabanshiba tukunnan amma insun takura suna iya sama mishi mata cikin Yan uwa haka kuwa akayi ba ajima ba akasaka bikinsu da Zainabu kyaukyawar yarinya mai dattaku haka ta tare ah gidan daya saya ah zariya suna zaman lafiya abunsu har Allah ya azurtasu da yara hudu maza Uku se Mace daya Mubaraq 32yrs ne dansu nafari se Aliyu 28yrs se Musa 25yrs sekuma Halima 21yrs wanda ah yanzu haka tayi aure tana gidan mijinta ba a Jima dayin bikin ba.......
Tun auren su Alhaji Muhammad basu taba samun matsalaba tsakaninsa da matarsa ba hakanan bata rageshi da komaiba sede Alhaji Muhammad yakasance mutum matafiyi meyawan tafiya kan harkokin kasuwancinsa don shiyasa ka agaba,koda yagama karatunshi bewani dogara da gwamnati ba don anashi ganin sudin basu da tabbas.....
Ayawan tafiye tafiyenshi ne Allah ya hadashi da Maryam ah Gombe bafulatanar Gombe kyaukyawa da hankali wanda hali irin natane yajashi zuwa gareta yakai ga maganar aure tunda ya tunkari mahaifiyarsa da maganar auren yafara samun matsala don daru ta tada baza ayi ma Zainab kishiya ba me tamishi dazaice zaimata kishiya....
babu Hajja, Zainab bata rageni da komai ba kawai Allah ne yadauramin son wancan baiwar Allahn Kuma naga inada dama shiyasa nakeson auren ta,daru sosai akasha da Hajja seda Kawu ya taka Mata birki sannan Muhammad yasamu sa'ida dukda hakan bawai tasauko bane alokacin Halima nada shekaru biyar koda ya tunkari Zainab da maganar aure bata nuna bacin ranta ba fatan alkhairi tayimishi dukda kuwa taji wani iri aranta amma tasan bazata iya hanashi ba tunda Allah ya halasta masa Kuma Allah yaga zuciyarta tana kula da mijinta dede gwargwado tasan bata rageshi dakomaiba.....
Haka akasa ranar aure bayan sunkai tambaya gurin iyayen Halima sumakuma seda sukayi bincike sannan suka bayar da yarsu,anyi aure da shagalin biki sannan aka kawo amarya zaman lafiya suke da Zainab hakana Maryam na girmamata tunda tasan ah girme ta girmeta sannan Matar tasan yakamata kusan kaman ah tare suka samu ciki ma don tsakanin Asma'u da Asiya wata daya ne da yan kwanaki, Asiya aka fara haifa sannan Asma'u yara biyun tare suka taso gwanin shaaawa don kuwa wasu sukan dauka yan biyune ma sabida suna kama dukdama bawani kama sosai bane kaman jini zaace...
Sede Asma'u tafi Asiya kyau da haske kasancewar itan mahaifiyarta tadauko ah haske dakuma tsayin gashi da yanayin jiki da komai,daga idanu,hanci,baki komai na mahaifiyarta tadauko, Asiyan ma nada kyau don ba acemata mummuna ba sannan suma tushen fillon ne tunda gaba da baya fulani ne......
Tunda suka taso kusan Kaya kala daya ake sayamusu komai ma tare akeyi masu makaranta tare suke zuwa da dai sauransu sede sun ban banta ah hali sabida Asma'u sanyin hali ne da ita batada hayaniya ga nutsuwa ga kokari dasanin meya dace,ga girmama na gaba da ita,gatada shiga ran jama'a duk wanda yazauna da ita seya so sake hada hanya da ita shiyasa tazama Yar gata acikin gidan kowa yayinta yakeyi don akwaeta dason aiki dakuma tarairayar yan uwanta sabanin Asiya da takeda rawar Kai dason jiki, batason aiki kwata kwata sannan bata damu da girmama nagaba da itaba ga rashin manners of approach dukda kuwa Itama akwae kwazo da son karatu don duk rashin jinta when it comes to studies tana maida hankalinta wannan banbancin ne yasa kowa bawai yacika shiga harkanta bane sede suyi da Asma'u,Asiya mesunan Hajja ce don haka tazamo mafi soyuwa agurin Hajja don ko tabata batason ayi wani abun da takeyin ma harda zugin Hajja don bakaramin daure mata gindi tayi ba sannan Asiya da Asma'u sunason junansu amma Asiya takan tsangwami Asma'u din ganin anfi ji da ita..........
Hajja kuwa bawai tanason Maryam bane haryanzu don gaisuwarta ma dakyar take amsawa shiyasa ko bayan rasuwar Kawu data dawo gidan ah bangaren Hajiya zainab tasauka hakan nan tasama Asma'u ido da sauran yaran bata cika shiga jikinsu ba kaman sauran jikokinta don Yayan Ummin ma biyarne Asmau 18,Sadiq,Munir Munira se ikram autar ta....
Ayanzu haka Asma'u da Asiya sungama matakin sakandire sunajiran admission yafito sunyi applying Ahmadu Bello University Zaria.....
Asma'u takasance meson girki da gyare gyaren guri hakanan Hajiya Zainab shiyasa tasu tazamo daya,kullum tana manne da ita tana koyan samfarin girki kala kala....
Mubaraq yagama karatunsa tun tuni yanzu yana PHD ne ma at the same time Yana lecturing ah makarantar Ahmadu Bellon faculty of engineering,yayinda Aliyu shima yagama nashi karatun Yana taimakawa Alhaji Muhammad wurin tafiyar da kasuwancin sa don tuni yabar aikin gwamnati kuma yana samu sosai alhamdulillah tunda Yana fulfilling all his familys needs harma yataimakama na waje....
Wannan kenan.....
GIDAN SARAUTA page 2
Tunda yabar masarautar yarasa ina zaije shiba abokiba don anashi duniyar besan me ake kira da aboki bama tunda tun tasowarshi betaba experiencing wannan relationship din ba.he always mind his ways and live his life alone,to koma yanason huldar abokan takan wazai so yazama abokinshi?....
Tafiya yake ahankali kaman me tsoron kasa duk wanda ze kalli Imam yakamata yagane akwai jinin sarauta attattaredashi sabida halaye irin nashi narashin son yin magana dama yanda yake tafiyar da al amuransa seda ya tabbatar yayi nesa da katangar masarautar sannan yasamu guri yazauna tareda lumshe idanunshi sa hannu yayi ah aljihun shi yaga babu kudi sawayayi ah dayan aljihun sannan yasamu wata kodaddiyar dari biyu wanda tagama cin duniya....
Furzar da iska yayi daga bakinshi sannan yasake lumshe idanunshi masu daukan hankalin yan mata,maganin Ummin sa yakusa karewa besan yazaiyi ba besan inazai samo kudiba shine tunaninshi don duk wata dabara ta Kare mai ah yanzu.......
Duba wrist watch dinshi yayi sannan yaga time ahankali yakuma tashi yacigaba da trecking seda yaji yagaji sosai sannan yatari machine me machine dinne yatsaya yana kare masa kallo sannan yabuga tsaki yaja machine dinsa yayi gaba yana cewa Allah ya sauwake se akacemaka ko fatara ta kamani se in dauke ka,toni ba dan iska irin ka bane ba.....bin me machine din yayi da kallo batareda yace komai ba sannan ahankali yasaka hannunsa cikin aljihunsa yacigaba da tafiya sanda ya Isa kasuwan ma laaasar tayi likis,yasani duk duniya babu me kin kyamatarsa se Mallam Hudu agurinsa ne kawai yakesamun sauki donnhaka straight shagonsa yawuce seya samu guri abakin kofa yazauna batareda yace komai ba tundaga nesa Mallam Hudu yahangoshi se ya saki murmushi yasan halin abunshi amma shima yau tsiya yake shirin yi mishi don haka yacigaba da harkokinsa yayi kaman besan da zuwansa ba shiko Imam maganar ne bazai iyayi ba,yace yazo dinne bazaiyiba don nauyi bakin sa ke masa haka yacigaba da zama ah gurin har maghrib ah lokacin ne Mallam Hudun yafito don rufe shagon yakauda Kai kaman beganshi ba seda ya rufe har ya juya yafara tafiya se yaga ko yabar Imam ba maganan zeyiba tunda daman halinsa ne don haka yajuyo yana Yareema mekakeyi anan?.....
Murmushi kawai Imam din yayi sannan yamika ma Mallam Hudun hannu sukayi musabiha kafin dakyar yace Ina wuni...
Lafiya Lau ya jikin Hajiya?...
Seda suka fara tafiya sannan dakyar yabudi baki yace "dasauki",wanda alokacin har Mallam Hudu yafidda ran samun ansa,zanje massallaci yanzu gobe sekazo za akawomin kaya ah Daf seka saukeminsu se inbaka kudi in Allah yakaimu.....
Jijjiga Kai yayi alamar to sannan yajuya yatafi, murmushi Mallam Hudun yayi sannan yace zanga ranar da bakinka ze budu Yarima don kuwa rashin maganar ka nadaya daga cikin abubuwan dasuke cutar dakai da yan uwanka sannan ahankali yakuma cewa Allah ga bayinka nan cikin wani irin hankali da bantaba ganin wani cikin sa ba,ya Allah ka duba musu ka kawo musu dauki.....
Yakarashe addu'ar da Amin sannan yawuce massallaci don kada ya rasa jam'i.......
*****
Makeken parlour ne nagaske wanda yake dauke da kayan sarauta tako Ina tundaga bakin kofar zakaji hancinka na ziyartar wani kamshi medan karen dadi sannan tundaga kofar shiga wannan bangaren zaka gane cewa me bangaren bata wasa bace dubada yanda kuyangu ke da hada hada gurin ganin sun cinma aikin su babu wanda zaka gani ah zaune kokuma ah tsaye batareda yana gudanar dawani aikiba.......
Wata dattijuwa nahango zaune kan kujera irin ta sarauta tadan kishingida jikin kujera yayinda bayi sunkai shida suna zagaye da ita suna mata fifita yayinda biyu nazaune ah gabanta daya nagyara fruits yayinda dayan na bata tana ci ahankali daka gansu kasan ah tsorace suke baswa son suyi wani mistake ayi musu hukunci don haka kowa taka tsantsan yakeyi.....
Ana cikin hakane sega wata tashigo cikin sauri tareda zubewa gaban Matar tana takawarki lafiya Magajiya, Allah yaja da tsawon kwana....
Amin duka sauran bayin suka ansa yayinda jakadiya tacigaba da magana ..
"Ranki shi dade yau me martaba beci abinci ba haka aka dawo dashi",dasauri Magajiya tatashi tazauna,wani abinci ne aka sarrafa mishin?".......
Shiru jakadiya tayi don tana tsoron bada ansa don tasan sauran,ba tambayar ki nikeba Jakadiya?kinyimin shiru kina zazzare idanu awani dalili?....
Cikin in ina jakadayi tace"Wainar masa ce da miyan ganye"...
Dafe Kai Magajiya tayi ranta na tafarfasa jitake kaman tarufe jakadiya da duka sede babu hali tunda dattijuwa ce duk rashin imanin ta bazata bugu wacce ta girme mata ah shekaru ba don haka tace waya girka?.....
Aliya ce sabuwar me girkin me martaba da aka canza,wani harara Magajiya ta daka mata sannan tace amma ai na fada miki kifada mata dokokin abincinsa ba koban fada Miki ba?....
Wallahi kinfada uwargijiyata akasi akasamu wai tamanta ne.....
Duba daya daga cikin bayin tayi tace Surayya je
Kikira min Sarkin gidan yari da Sarkin mazga yanzunnan,tasake duban wata daga cikinsu tace kekuma laure jeki kiramin Aliyar yanzunnan,to Magajiya nansuka fice cikin sauri don aiwatar da abunda akasakasu.....
Baa Jima ba segasu sundawo dukansu duban Sarkin mazga tayi tace ga Aliya tayi laifi ayi Mata hukunci da bulala ishirin sannan Sarkin gidan yari yasata ah gidan yari cikin kuka Aliya tashiga bada hakuri amma ko kallon inda take Magajiya batayiba sema duban jakadiya da tayi tace kinemi wata tamaye gurbin ta sannan aka kara irin wannan kuskuren hardake zan hukunta tunda yakamata kina duba irin ayuukan dasukeyi bawai ayitayin duk abunda akaga dama ba.....
To uwargijiyata in Sha Allahu za a kiyaye nan gaba.......
nan ta tashi tafice jiki na bari.....
****..
Tunda suka tashi suka wanke yan kwanikan dasukayi anfani dashi da dare yayinda Amira tashiga shirin tafiya makaranta Afiya Kuma tafara share sharen gidan......
Seda tagama shirin sannan tayima yar uwarta sallama tanacewa seki shirya in an fito break se indawo ke kije tunda Yaya Almustapha baya gida....
To Amira,amma nikam da kinbi tanawa ma damunyi zaman mu tunda komunje dinma kusan kullum se an koro mu ance mutafi muje muyi aiki shiyasama ni Kinga nadaina damun kaina....
Afiya nasan da hakan sede kinsan makaranta nada anfani ah garemu kiduba halin da Umma take ciki yakamata muyi kokari muzama wani abu sabida mufidda mahaifiyar mu awannan halin.....
Hakane kuma to sekin dawo din Allah yadauramu akansu karsu zo yau batakai ga rufe bakinta ba sega laure jakadiya tazo tana hararar su tareda toshe hancinta waiku don jaraba kullum sai kunsa anzo wuri medan Karen kazantar nan ankiraku?.....
Afiya nashirin yin magana Amira tayi saurin rike hannunta alamun tayi shiru..
Laure wake kiranmu?.....
Tsaki Lauren tayi sannan tace shafa kiji ai tambayar rainin wayaune ma wannan wazai kiraku inba Gimbiya ba....
To muna zuwa cewar Amiran.....
Juyawa laure tayi tana yar wakokinta sannan tace kada ma mutum yazo mana yaga abunda zaifaru dashi.....
Murmushi Amiran tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tacire hijabin makarantar kamin tasamu kayanta tasaka sannan tace tashi mutafi.....
Babu inda zanje nikam don bazai yuyu mubar Umma itakadaiba yar kwafa Amiran tayi sannan tace sekace yau kika saba barinta kinsandai ko bakije ba se anbiyoki anci miki mutunci sannan ah tasa ki gaba gwanda muje Umma Kuma Allah zecigaba da Kare Mana ita kaman yanda yasaba haka Afiya na kunkuni ta tashi suka tafi side din Gimbiya Hamida wacce wai abaki sukejin Yar uwarsu ce ta jini,yayarsu mahaifi daya......
Koda suka karasa bangarenta samunta sukayi kwance kan gado tarungume pillow tana waya se wani murmushi takeyi tana yauki....
Sunfi minti arbain ah tsaye still tana wayan seda tagama sannan tayi wurgi da wayan tareda tashi tazauna,harara tazuba musu
"tun yaushe kuke dakin nan?"...
Tun dazu cewar Amira....
Ku bakusan mutum nawaya ku fita bane ko gulma da munafurcine yasaku tsayawa don jin abunda nike fada?....
To duk iskancina bekai na matsiyacin Yayanku ba me lalata da 'ya'yan mutane.....
Ran Afiya ya baci tanashirin magana Amira tadamke hannunta kamin Amiran tace kiyi hakuri Gimbiya bazamu sakeba...
"Better"...
To your normal work as usual Kuma daga yau kada kuyarda insake sawa ah kiraku don na lahira seyafiku jin dadi wallahi.......
Dasauri Amira tashiga bandaki don hada mata ruwan wanka yayinda Afiya na yamutsa fuska ta isa ga wurin kayan Gimibiyan tamika mata towel seda ta daura sannan tashiga bayi lokacin har Amiran tagama hada mata ruwan wanka don haka tazo tajona yar uwarta suka kama gyaran dakin Gimbiya Hameedan saida suka gama tas kowa ranshi ba dadi sannan Afiya tafita zuwa bangaren kitchen don karbo breakfast din Gimbiya yayinda Amiran tashiga taimakawa Gimbiya wurin gyara jikinta bayan tafito haka aikin kenan kullum su suke mata komai harta tausa da bata abinci sannan suyita mata fiffita har saitace ya Isa........
*****
*London*
Kwance yake kan makeken gadonshi yayinda 'yan mata biyu ke kwance jikinshi kowa da irin harkar da take yimishi hankali kwance shikuma se karban sakwwnni yakeyi suna cikin badalar su ne wayarsa tashiga ringing jiki ba kwari yace
Can someone disconnect that call for goodness sake!ynda yayi maganar seda ya tsorata duka matan turawa biyun Justina dake kusa da bedside drawer da wayan ke kai tayi saurin daukan wayar yayinda dayar tacigaba da yamutsashi yana ta surutai, tunkan tayi disconnecting har ya katse call din sekawae ta mayar kafin tasake ankara wayar tasake daukar ruri ture joy yayi daga jikinshi yana huci tareda jan gashin justina"didn't I ask you to disconnect that damn call?"....
Kokarin kwace kanta tashigayi tana"I'm sorry Prince"...
Wurgi yayi da ita Itama yana"get out of my room now!"....
Jikina bari suka tashi sukafice dukansu still wayar na ringing se sake Kira akeyi Kamar kayan jaraba,tsaki yasaki tareda shafa kanshi sannan yadauki wayar tareda picking call din......
Yarima inaka shigane inata kiranka baka dauka?....
Wani kululun bakin ciki yakeji because he's busy enjoying with those girls amma Magajiya ta bata mishi budget cikeda bacin rai yace Mama darene fa kinsan by this time yakamata Ina bacci amma kika kirani ko awani dalili oho!.....
Cikin sauke murya Magajiya tace haba autana shikenan ban isa inkira Baby boy dina ba inason jin muryarsa,kasan dai nayi kewarka ko?....
Turo baki yayi kaman wanda yana gabanta, I'm sorry Mama just that kinbata min budget dina ne,sorry to Son,ya kake,yaya London da makaranta inafatan komai na tafiya smoothly....
Gyara kwanciya yayi kan makeken bed dinshi don ya lura yasamu opportunity yanzu because he's running out of cash daman yanata tunanin taya zai tunkari Mai martaba da maganar tunda ko sati biyu baiyiba daya turomasa 2million ah account dinshi itakuma uwartasa bayason kiranta sabida kullum inyakiradin maganar yadawo gida takeyimishi......
shagwabe murya yayi inafa smoothly Mama babu cash and you know kudi is everything right, I'm nothing without money.....
Lokaci guda hankalinta yatashi tace dagaske baka da kudi shine baka Kira ka fadamini ba Sulaiman....
To ai kedinne Mama dana kiraki seki fara maganar dawowana gida shiyasa banson Kira amma wallahi banida kudi. ..
Dan kwafa tayi sannan tace zanturoma kudi amma maganar zuwa gida yazama dole Yarima rabonka da gida kusan shekaru biyar ahaka kakeson abaka sarautar kodanma Kai daman wan Babanka ka dauko bakason abun kwata kwata toka rufamin asiri Kaine hope dina Yarima babu wanda nakeson yagaji sarauta Kamar ka inkuma baka dawo kusa damu kafara gudanar da duties dinkaba bana tunanin Mai martaba zeji dadin haka......
Yamutsa fuska Yarima yayi,to ai Kinga matsalar ni Mama banason sarautarnan kema kinsani bama nina cancanta ba tunda I'm the Youngest son,no one deserves the throne other than Brother Almustapha yakarashe maganar yana magiya....
Kai! Magajiya tayi wata irin tsawa wanda saida Yarima Sulaiman ya tsorata harcikin dodon kunnensa sannan ahankali yatashi daga kwance yazauna akan gadonshi.....
Cikin bacin rai Magajiya tace idan har nasake jin irin wannan maganar ah bakin ka ranka bazai maka dadi ba wallahi ko sunan yaron nan nasake ji abakinka ranka inyayi dubu seya baci and I warn you for the last time kafin satinnan yakare ka tattaro naka ya naka kadawo Nigeria inbahaka ba nidakai ne acikin gidannan sannan takatse wayar tana hucin takaici.....
Furzar da iska yayi ah hankali sannan yayi wulli da wayar"Damn it,I told her I'm not after the throne meyasa baza abarni in huta ba miyasa baza a bar mutum ya shakata ma rayuwarsa ba,I don't want to be caged in there.i want to be a free Man,I mean a free Man!"yakarashe maganar yana tsakin takaici yasan Magajiya she will not take her words back tunda tace yatafin as a command dole yatafin if not shikanshi bazai ji da dadinba don haka yasama ranshi dole yakoma Nigeria cikin satinnan din......
****
Yau tunsafe bayan tagama taya Ummi ayyuka tashige daki ta dale gado don karanta wani littafi da Aisha tadameta takaranta wai ya hadu sosai,aikuwa littafin bakaramin tafiya da hankalinta yayi ba waishi *ALKAWARI BAYAN RAI* na *SUMAYYA ABDULKADIR* tana ganin masu karanta Hausa novel amatsayin marasa aikin yi dakuma bata lokaci seyau ta tabbatar ba bata lokacinsu sukeba tunda gashi tunda tafara da safe bata iya ajiyewa sallah ne kadai ke tadata daga kan gadon sekuma in Ummi tai Kiranta each and every page takaranta she'll be yearning to know what will happen next se yanzu Allah yabata ikon gamawa....
Lumshe idanunta tayi ahankali tana tunano abubuwan dasuka faru cikin littafin,towai daman haka soyayya yake?
haka mutum yakeji when he's in love,haka yake reacting dakuma sacrificing...
dan shiru tayi nadan dakiku sannan ta lumshe idanunta,when will she fall in love and who will she fall for,ya yake? will she be lucky to get the love in return kokuma son maso wani zatayi,ya gayen ze zama dogo ne ko guntu, fari ko Baki, kyaukyawa ko mummuni duka babu wanda tasani dan ware hannun ta tayi ahankali sannan tafurta "only God knows,but I hope he'll be dashingly handsome in everyway"......
Murmushi ne yasubuce mata sekuma taji kunyar kanta, ahankali tadan bugi kanta"Ya Allah what am I thinking?"....
Jitayi Munir namata sallama ah kofar dakinta don haka ta ansa sannan yace Mommy na kiranki....
Wurgi tayi da pillow dinta sannan tace to inazuwa, Allah sarki yau Mommy tunsafe bata ganni ba dole tanemeni.. .
******
*****
Yauma kaman jiya yaje kasuwa shagon
Mallam Hudu seyasake neman guri yazauna batareda yayi magana ba murmushi Baba Hudun yayi sannan yafito yasamo shi zaune,dan dafa shi yayi sannan yace daga makaranta ka fito ne?......
"Ina wuni",yagaishe shi ciki sanyayyar muryarsa...
Lafiya Lau Yarima,yajikin Hajiyan?,murmushi kawai yama Baba Hudun batareda yace komai ba suna nan tsaye sega motar kawo Kaya ta zo nan Almustapha yashiga aiki najido kayan yana shigar dasu shagon inda sabo yasaba don wannan shine aikin da Baba Hudun kesashi yi har yadan samu abun rikewa ah hannunshi yakuma saima kannensa abunda zasu sa ma bakin salatinsu dukda ma wani sa'in yakan dauki kyautan kayan abinci yabasu,sede ba kullum za ayi maka ba dole watarana mutum ze gaji shiyasa shima Almustaphan yakeson yin aikin yasan yasamu da guminshi ne bawai yazama maroqi ba seda yagama kwashe uban kayayyakin sannan mallam Hudun yamasa sannu tareda cewa to ga kudin ka nan Yarima.....
Lumshe idanu Almustapha yayi bayason wannan sunan kwata kwata inda Mallam Hudun yasan yanda yakeji inya kirashi da wannan sunan dakoda wasa bazai taba koda kwatanta kiranshi da sunan ba sede duk yanda yakeji din bekai girman darajar Mallam Hudun dayake gani ba don haka bazai iya budan baki yace masa bayason sunan ba....
Dukar dakansa yayi kaman bazaice komai ba se can sannan yace ka ajiye kudin agunka kawai zanturo Amira, murmushi Mallam Hudun yayi sannan yace to amma dai katafi musu dawannan yanzun nan Mallam Hudun yajuya cikin shagon yadauko taliya da macaroni bibbiyu yasaka mishi ah leda hadeda ledan maggi da Onga roll daya se Mai kwalba daya yace to gashi ka Kai musu ko kafin Amiran tazo.....
Karba yayi batareda yace komai ba sannan yabar gurin mallam Hudun da kallon tausayi yabishi dashi sannan ya jijjiga kanshi yakoma cikin shagon nashi.....
Waishin wanene Almustapha?
Menene asalinsa,menene labarin masarautar Zazzau,meyasamu Ummi?,meye dalilin dayasa Almustapha suke cikin wannan yanayin?....
Kucigaba da bin Zeeneert don jin yaza akayata....
GIDAN SARAUTA Page 3
*ASALINSU*....
Sarki Sulaiman babban sarki ne acikin Nigeria da babu yankin dazakaje ba asan dashiba tsabar tashen da mulkinsa yayi dama kuma adalcinshi ga talakawanshi,asalin iyayenshi nomads ne(Wanda akafi sani da fulanin daji) tun kakanni wanda basu da takaitaccen gurin zama suna yawo ne depending on the weather tayanda zasu samu su ciyar da dabobbbinsu dama su kansu ahakan ne har Allah yasauke su acikin garin Zaria wanda tun alokacin ba abakin komai take ba don mutane tsirarru ne kawai agarin.tunda sukazo garin Zaria suka ji dadin zama agarin se suka kasa yin gaba suka kafa gida da kasuwancin su wanda ahakan ya bunkasa har suka saba da mutanen gari akazama daya. with time population na karuwa ah garin har garin Zaria yafara zama babban guri alokacin da Allah yadauki ran Sarkin garin bashi da magajin daza abama sarauta don haka akanemi wanda yacancanta aka bama wanda shine mahaifin sarki Sulaiman shima bayan shekaru tsufa taxo se mulki yadawo hannun sarki sulaimanu wanda alokacinshi bakaramin taka rawar gani yayiba don ganin yayi wani abun alfahari ah yankin Zaria haka rayuwa tacigaba, Sarki Sulaiman yazama abun soyuwa ga kowa bama a zaria kadai ba ah kasar Nigeria bakidayan ta.matar shi daya kwallin kwall wanda tunda ya aureta basu samu haihuwa ba har na tsawon shekaru takwas hakan Kuma besa yakara aureba dukdama irin takuramasa da jama'a sukeyi da irin hakurinshi dama Kuma addu'a dasukeyi gakuma subjects nayimusu Allah yabama Zuwaira ciki kaman da wasa bakaramin farin ciki sukayiba lokacin har yar kwarya kwaryar walima seda akayi sanda Zuwaira tahaihu 'da namiji tasamu nanma murna sosai akayi ranar suna akasama yaro suna Almustapha wanda mutanen gari ke kiranshi da Yarima tun haihuwarshi Zuwaira da Mai martaba suka dauki son duniya suka daura ma yaron komai yace yanaso za ayimishi har tasowanshi, Almustapha yazamanto me kiriniya da son yawace yawace da freedom,tun yana shekara biyar akeson fara koya mishi swordfighting da hawan doki amma kwata kwata bayaso sabida baida passion for sarauta kwata kwata wannan abun baidamu su Sarki ba se suka barshi ah tunaninsu yarinta ne with time zefara dakanshi, Yarima Almustapha nada shekara bakwai Allah yasake bama Zuwaira ciki wannan karan anyi murna sosai don harta fidda rai ga haihuwa sede murnar batakai na lokacin haihuwar Almustapha ba
haka akayi suna lafiya akasama yaro Abdulrahman tunda aka haifi Abdulrahman yazama abun so acikin masarautar sabida yaron akwai shiga rai haka Almustapha yadauki son duniya yadaurama tilon kaninshi komai yasamu na Abdulrahman haka Abdulrahman dinma yataso yanason dan uwanshi komai tare sukeyi hakanan Almustapha bayason laifin kaninshi komai yana shigan masa sede abunda ya banbantasu Abdulrahman na matukar son sarauta tun yana shekara biyar yake koyon fada dason hawan doki daduk wani activities na sarauta,gashi da kwazo da kaifin basira gakuma son manyance alokacin ne Kuma akafara matsama Almustapha yadinga koyon abubuwa sede ranshi bayaso ko anfara koya mishi seya gudu akwae ranar da sarki Sulaiman yakirashi yayi mashi fada sosai wanda hakan betaba faruwa ba yayi kuka sosai sannan yadau alwashin fara yin abunda mahaifinshi keso don bayason bacin ransu kwata kwata don haka yafara participating dukda kuwa ranshi bayaso,bakaramin dadi Mai martaba yajiba ga canzawan 'dan nashi sekuma yawanci karfin koyon yakoma kan Almustapha aka daina bama Abdulrahman din attention sosai wanda hakan bakaramin sosa mai rai yayiba sede be nuna ba saboda shi yarone dabai cika tada hayaniya ba bekuma cika nuna damuwarshi ah fili ba sede yakebe gefe yayi kukansa me isansa yashare hawayensa, Abdulrahman yakasance yaro meson rubuce rubuce barinma akan abunda yafaru dashi dakuma abunda yakeso tunda yafara wayau yakan zauna yazana kanshi ah zaune akan kujerar sarauta kokuma yana tsaye rikeda sword jikinshi da kayan alfarma shiyasa koda yalura bazai samu sarautar ba anfison abaman Yayanshi seya rubuta cikin diary dinsa how he felt and the rest.....
Almustapha cikin yan watannin daya biyo baya yalura Abdulrahman yadaina sakewa kaman da don haka yatambayeshi amma besamu ansa daga gareshiba don haka yashiga bincike wanda ahakan ne har ya karanta diary din bakaramin kuka yayi ba ranar sabida irin son da yakema kaninshi Allah ne kadai yasani,duk wani abu dazai bata mishi rai baso yakeyiba jin yaron yake har cikin ranshi don haka ya daukar ma kanshi alkawari tun ranar babu Mai mulkar garin Zazzau bayan mahaifinsu inba Abdulrahman ba don haka sanda yagama junior secondary school dinshi yadage yanason tafiya Madina wata Islamic school karatu anyin gwagwarmaya kafin Mai martaba ya yarda aikuwa tunda Almustapha yatafi besake waiwayen gidaba seda yagama secondary school sannan ne yace yanason yakarasa karatunshi ah waje......
Mai martaba yalura Almustapha bayason karatu ah gidane kwata kwata don haka seya kyaleshi shikuma Abdulrahman duk karatunsa agida yayi kama daga primary har secondary school sannan yakanyi participating wurin taimakon mahaifinsa halarta wasu abubuwan dakuma ziyarta garuruwa dakuma solving problems na talakawansu in the absence of his Brother wannan dalilin ne yasa kowa yafi sonshi Kuma suke jida shi ahaka har yasamu gurbin karatu ah jami'ar Ahmadu Bello wanda alokacin ba'a jima da budetaba sosai yamaida hankalinshi kan karatunshi Kuma hakan behanashi cigaba da ayuukan dayasaba ba.....
Sanda Almustapha yagama kammala karatunshi yajona Masters Mai martaba har America yaje don dawo dashi amma fir yaki yanuna karara shifa bazai dawo ba indai har zaa matsa masa kan maganar sarauta......
Bakaramin tashin hankali da bacin rai mai martaba yashiga ba sannan yace babu shi babu Almustapha sannan duk wanda yasan yana da dangantaka dashi to yatabbatar ya yanke da Almustapha tunda shida ya haifeshima ya yafeshi hankalin Zuwaira bakaramin tashi yayiba da shikanshi Abdulrahman din, yana mamakin miyasa Yayanshi zekai wannan gandun sede dukansu babu wanda ya Isa ya karya dokan Mai martaba sabida umarni ne daga gareshi sedaga bayane jakadiya take fadama Abdulrahman din Almustapha yayi sacrificing throne dinne for him tunda yalura yanaso Itama saudaya yataba fada mata wanda hakan yasamu asaline sabida irin shakuwarsu,duk wata shawara awurinta yakenema, bakaramin kuka Abdulrahman yayiba sannan yaso fadama Mai martaba amma jakadiya takisam tace amana ne Almustapha yabata shidinma don ya cancanta yasani ne shiyasa tafada mishi haka Kuma inhar Yayanshi na iya yimishi haka mezai hana yacika burinshi tunda talakawama shi sukeso ba wansa ba dakyar yabar maganar, Mai martaba kuwa tunda yadawo daga America hope dinshi kan Abdulrahman yakoma wanda shikuma Abdulrahman din be zuba mai kasa ah idoba ahaka yakarasa karatunshi sannan akafara maganar nema mishi auren Magajiya yar gidan waziri dukda dai bawai yanaso bane sede bazai iya duban mahaifinshi yace bayason zabinshiba ahaka akayi auren sannan suna zaman lafiya da Magajiya sede akwaita da mulki da isa gata dason sarauta batada sassauci ga bayinta kwatakwata bata daukesu abakin komai ba,laifi kadan bawa zaiyi ayi masa hukunci metsauri ashekarar aurensu tasamu ciki wanda akullum bata dawani buri daya wuce taga ta haifi 'Da namiji wanda zai gaji sarautar zazzau ahaka har cikin yacika wata tara akazo gandun haihuwa sekuma Allah da ikon shi yabata santa leluwar budurwa bakaramin bakin ciki taji ba don bahaka tasoba taso ace ita tahaifi air to the throne dukdama ita kadaice Matarsa sede tasan gidan sarauta yanzunnan se ah matsa ya kara aure haka ta rungumi yarta tanasonta dukda kuwa ba macen taso haihuwa ba amma ai 'da 'dane sannan wahalar haihuwar duk dayane Gimbiya HUMAIRA nada shekara uku Allah yasake bama Magajiya wani cikin wannan karan murnar tafi takowanne lokaci don kuwa kowa yana tsanmanin za ahaiho namijine sede Allah da ikon shi batasamu 'da namijin ba seta Kuma haihuwar mace Halima,tundaga wannan lokacin Magajiya tafara shige shige don aganinta zama be ganta ba inbata samu 'Da namiji ba. bayan shekara biyu se Allah yasake bata ciki wanda alokacin bokanta ya tabbatar mata cewa 'Da namiji zata haifa sede Allah dayafi komai seyabata mamaki tasake samun 'Ya mace kuka kam tayishi ranar kaman zatayi yaya sannan tacima boka mutunci don aganinta yacuceta yayi mata karya ahaka tacigaba da rainon 'Ya'yanta mata wanda tun tasowarsu takoyamusu rashin daukar Dan Adam da daraja don kuwa bayi ba ahannun Magajiya kadai suke wahala ba harma ah hannun 'ya'yan Magajiya alokacin ne kuma Allah yadauki ran sarki Sulaiman adalilin wata yar ciwo dayayi na kwana biyu wanda yazo da ajali tunda yafara rashin lafiya yakecewa anemo masa Almustapha,acemasa ya yafemasa duniya da lahira sede kash Allah beyi haduwarsuba.....
Tabbas anyi rashi bama agarin Zazzau ba kadai agabakidaya kasar Nigeria kowa ya jijjiga da rasuwar bawan Allan,haka aka yimashi sallah aka kaishi gidansa na gaskiya daganan aka rada Abdulrahmanu matsayin sarki wanda Ina iya cemuku harma yafi mahaifinsa aiki dakuma yin adalci tsakanin mutanensa wannan yasa kowa kesonshi da girmama shi cikin shekara uku yagama shiga ran kowa sannan babu inda baya shiga don halarta taro na sarakuna bama ah Nigeria kadai ba har neighbouring countries dinmu sannan tunda yahau mulki yake neman dan uwansa sede shiru babu labarinsu kwata kwata,awannan lokacin ne aka gaiyaceshi zuwa wata taro na sarakunan kasashe baki daya ah *Chad* nan yakama hanya yatafi inda anan ne Allah ya hada shi da Yar Sarkin Chad yagani yace yanaso inda yanemi aurenta babu bata lokaci akabashi ita dubada irin mutunci da girma irin nasa tunda Magajiya taji labarin auren Khairiya da Abdulrahman hankalinta bakaramin tashi yayiba, hankalinta bekara tashibama seda tayi ido hudu da Khairiya babu inda taragu daga kyau har mulki da kudi gashi kuwa Mai martaba yadauki son duniya yadaura mata don jida ita yake Kamar kwai banawasaba gashi Itama tazo tanashiga ran jama'a dubada hali irin nata compared to Magajiya me wulakanta bayi ita da take tasu ma,shekaranta daya dazuwa gidan tasamu ciki har Allah yasauketa lafiya tasamu santalelen 'danta namiji ranar murna agurin Maimartaba Allah ne kadai yasani daga Khairiya yayi sama yana juyi da ita cikin daki gaban kuyangu tsabar farin ciki sannan yadauki 'Dan yana karemasa kallo tareda yi masa addu'a,samun guri yayi yazauna bayan bayin sunbasu guri sannan ya janyo Khairiyan zuwa jikinsa.....
I'm very grateful for this gift Khairiya, I'll forever be thankful to you,kinbani kyautar dabansan irin godiyan dazanyi miki ba...Dan furzar da iska yayi sannan yasake dubanta
"the owner of the throne is back Khairiya, Almustapha is back!and the throne belongs to him".....
Murmushi tayi tareda Kara shigewa jikinshi don tasan irin son dayake ma Yayanshi kullum maganarsa shine Allah yabashi 'Da namiji yasamishi suna Almustapha sannan yadaurashi akan kujerar Almustapha dayabari......
Allah ya rayamana shi Abban Almustapha....
Kissing forehead dinta yayi ahankali sannan yace ...
"Amin Ummin Almustapha,kinfara koyon yarenmu sosai yanzu, you're a great learner"....
Murmushi tasakar Mai me melting heart dinshi sannan tace....
And the credit goes to you....
Murmushi kawai yayi yana karema yaron kallo kwata kwata baya gajiya da kallon yaron hakanan bayason barin yaro seyake ganin kaman inyasakeshi ze sake guduwa kaman yanda Yayanshi yagudu yabarshi......
Kallon ta yayi sannan yakalli yaron "he look exactly like his mother, I'm jeolous Khairiya"...
Dan Jan hancinshi tayi "don't be jeolous because he'll be like you one day"....
Yar dariya yayi "anyi one one kenan"......
Uhmm Mana....
ahaka akayi suna akasama yaro Almustapha anyi bikin suna sosai,anyi sadaka anci ansha awannan ranar sannan ba ataba yin taro agarin zazzauba irin na ranar sunan Almustapha.......
Magajiya kuwa ko barka bataje tayima Khairiya ba kowa yaganta yasan tana bakin ciki da wannan haihuwar haka 'ya'yanta ma tabi tasamusu tsanar 'Dan uwansu tun yana yaronshi sannan tundaga wannan lokacin tashiga makirci yau tahada ma Khairiya wannan gobe tahada mata wancan sede babu wanda tayi succeeding aciki, Almustapha nada shekara hudu Magajiya tasamu ciki shima haihuwar Mace tasake samu inda sukasamata Hamida bayan shekara biyu sega wani cikin Kuma wannan karan se Allah yabata 'Da namiji inda suka sa maisunan marigayi sarki Sulaiman Maimartaba yayi farin ciki da haihuwar acewarsa Almustapha yasamu abokin wasa dukdama duk haihuwar da Magajiya takeyi yakan nuna farin cikinsa don kuwa Mata ma 'ya'ya ne Kuma yana kula dasu dede gwargwado and duk abunda sukeso anayi musu......
Tunda Magajiya tasamu Sulaiman tasaka ma ranta cewa shine zai gaji sarautar Zazzau dukyanda za ayi setayi yanda zatayi tahana Almustapha mulkan garin zazzau koda kuwa hakan na nufin ta kaudashi daga duniya ne sede she won't go directly by doing that sede inhar the other way din yaki tafiya yanda tasone.....
Sulaiman yataso yanason dan uwanshi Almustapha, he's just a free boy baya dason bin maganar mahaifiyarshi se abunda ranshi keso yakeyi Sulaiman nada shekara biyar Almustapha nada goma shabiyu duk wani harkansu tare sukeyi sannan Almustapha nakula dashi yanda yakamata sede Almustapha mutum ne dabaya magana miskiline gashi da shariya becika damuwa da alamuran mutaneba ga sarauta da jinkai ga kyau duk wanda yasaka ido akan yaron seyaji yaburgeshi manya da yara kowa girmama shi yakeyi acikin masarautar dama garin baki daya awannan lokacin ne Magajiya tafara shirin gudanar da aikinta don kuwa ta lura sam Almustapha baya kama da Mai Martaba ko kadan uwarsa yadauko don kuwa daka ganshi kaga ba jinin Nigeria bane ba dukda kuwa bawai wani haske ne dashi ba amma yanayin fatarshi da gashin shi kadai ze baka amsa......
ranar Almustapha yadawo daga lambu kenan dayanma yashiga dakin mahaifiyarshi yasamu guri yazauna....
Kallonshi tayi sannan tace harka dawo daga lambun ne yau?.....
Uhm kawai yace Mata, murmushi tayi sannan tace Mallam Hudu bebaka unripe mango ka kawomin ba?....
"Bebaniba Ummi"..
Kuyangun dake mata fifitane sukace kilan yamanta ne Aunty....
Nima tunanina kenan Hindatu Kuma wallahi yau inbanci mangoron nanba zan iya zazzabi,Yar dariya Hindatun tayi sannan tace ba akai ga haka ba bari zanje inkarbo miki yanzunnan inyaso Jamila tafara miki tausan kafin nadawo.....
To Hindatu Allah yamiki albarka, nan kuwa Hindatu tafice aguje don karbowa Jamila nashirin barin yin fifitar Almustaphan yadaga mata hannu alamun tabari sannan yataso ahankali cikin takunshi na kasaita yazauna kusa da kafafun Maman nashi yana yimata tausan ahankali sannan yana dan satan kallon cikin ta don yaga Kamar yadan kumbura murmushi tayi lura da kallon cikin dataga yanayi sannan tariko hannunshi ahankali tadaura akan cikinta "you'll be a Brother soon Yarima"....
Lumshe idanunshi yayi ahankali don bakaramin dadin news din yajiba sannan yadan saki murmushi,yanason kanne yanaso ace shima yanada kannenshi uwa daya uba daya it feels good sabida yagaji da wulakancin Magajiya da Yayanta duksanda taganshi da Sulaiman seta cimishi mutunci wurin yayyunsa matakam baya samun sauki har humaira da Halima sukayi aure baya tunanin maganar kirkita taba hadasu .......
Cire hannunshi yayi acikin nata sannan yarungumeta batareda yace komaiba,tasan rungumar na nuna farin cikinshi ne,tasan halinshi sarai bazai taba magana ba ko shakka babu Almustapha mahaifinta yadauko wurin miskilanci da sarauta dakuma mahaifin shi dan ko sarki Abdulrahman ma ba bayaba wajen kasaita suna nan zaune ahaka har Hindatu tadawo da unripe mango ah yanke karban plate din yayi yanabama Ummin nashi ah baki tanaci suna haka ne wata baiwa tashigo wai ai tayi bako daga Chad tayi mamaki sosai don ah iya saninta babu wani dan gidansu datasani dayace zaizo mata amma seta zari mayafinta tafita anan ne tayi arba da bakon dabatasanshi bama kwata kwata gaisuwa sukayi cikin yarensu na Chad sannan yace mata daga Chad yazo aikine ah Zaria baida gurin sauka Kuma yajima dasanin cewa tayi aure anan shine yace bari yazo su gaisa....
Godiya tamishi sosai da ziyara sannan ta tambayeshi mutanen Chad duk yace mata kalau suke sannan tace akarasadashi gurin Mai martaba sugaisa ace bakontane daga Chad zedan kwana biyu anan.......
0 Comments