Igiyar Zato Hausa Novel Complete
IGIYAR ZATO NA NANA HAFSAT MISS XOXO
In the name of Allah the Gracious the Merciful
SHAFI NA DAYA
ZARIA
2004
Zaune nake a dan tsukukun gefan kofar dakin mu Gaba na kuwa wani tsohon kwano ne dake dauke da sandararren tuwon dawa da miyar kuka koriya shar da ita ina ci ina korawa da ruwan bunu marar sukari can gefe na kuwa su Alawiyya ne da Hinde sun barbaje suna afka lomar taliya yar mirji data sha manja sun yayyan ka tumatir da albasa a akai Kuka na na hadiye ina kokarin karasa cin tuwon gaba na don sauri nake yi zan kai wa yayan mu abinci dake can tsallaken gaban gidan mu can yake bakanikan ci Fitowar babar su Alawiyya ne yasanya ni hanzarin mikewa Na dauke kwanon gaba na Ai kuwa muna hada idanu ta zabga min harara wadda tazame mata jiki kullum sai ta min
Mayya Aniyar ki ta biki Kurwar mu kur wallahi anyi gado awajen uwa Da shegen idanu kamar na ungulu
Nai shigewa ta daki Na baro Babar su Alawiyya wacce ake kira da Bintalo tana zuba min kwandon zagi Na danne bacin rai na na dubi Innar mu dake tsintar hatsi a tire nace
Innaar mu bari naje na kai wa yaya abincin sa
Na karasa magana hade da daukar wata fashasshiyar kular abincin mu wadda itace me kyau acikin kwanukan mu da ake zubawa yayanmu abinci Innar mu tayi murmushi tana gyarawa autar mu kwanciya dake baccin ta hankali kwance gefan zaninta ta sunce ta ciro naira hamsin wadda itace dama a kullin zanin duk ta kanannade ta mikomin
Ungo ki taho da man gyadan ashirin sai yajin goma ki biya ta gurin ladiyo mai koko ki sayo koko da kosai na ashirin
Rissinawa nayi hannu biyu na karbi kudin idanuwa na suka kawo ruwa cikin tsantsar tausayi nace
Innar mu to ke mezaki ci Kinbar mana tuwon ni da yaya Najib koko da kosan kuma na Aminatu ne
Banasan sakarci sanda naci abincin idanuwan ki biyu
Girgiza kai nayi alamun aa Kafin na janyo kodadden koren hijabi na daya zama tamkar na gado na zura shi cike da tausayin innar mu Uwa kenan gwara muci ita ta zauna da yunwa har sai mun gama sanwar rana Sallama nayi mata na fito kai na a kasa na wuce ta gaban bintalo ai kuwa ban gama maganar ta a zuci ba ta zubamin rankwashi ji kake kwas
Su Alawiyya da Hindatu suka tuntsire da dariya suna gasamin magana share hawaye na nayi domin inda sabo na saba da irin rayuwar gidan mu Dakyar na karasa sauka daga benen gidan mu mune a saman karshe mu dasu Bintalo da Usaiba maman su Larai wato dakuna na uku acikin dakuna tara dake gidan Domin kaf layinmu da unguwoyin gaban mu babu wanda bai san gidan mu ba wanda akewa laqabi da Gidan Mata Tara
HAYIN RIGASA MECHANICS
Ina tafe a hanya ina bitar haddar Suratul Yasin da zaa karba anjima a islamiyyar mu Sauri nake yi na karasa na kai wa yaya abincin sa Cikin nutsuwa na karasa wurin aikin su Na gaggayshe da abokanan aikin su kafin na wuce wajen daya ke zama Can karkashin wata mota na hango shi yana gyara notinan taya Yayi dumu dumu da bakin man fetur Cike da murmushi na karasa wajen sa Cikin nutsuwa da girmamawa na dan durkusar da kaina yadda zai iya jiwo murya ta nace
Yayan mu Sannu da aiki Ga abincin ka
Naam Batoul Sannun mu Ya innar mu da auta
Lapia lou Yayan mu Bari naje nayo cefane
Ina gama fada na mike daga tsugunnan da nake Yaya ya zura hannu a aljihu yana lalibo kudi Nera sittin ya ciro duk sun dunkule da junan ya miko min naira arbain ya maida ashirin din cikin aljihun sa Na danne kukan daya tahomin ina kokarin mayar da kai na gefe dan kada Yayanmu ya gano yanayi na
Yayanmu ALLAH ya kara budi Me zan siyo aciki
Jia kin tambayeni kudin Omo ko To kiciri goma ki sayo omon Naira talatin din sai ki sayo abunda babu a gidan
Gyada kai nayi Ina tunanin abunda babu
Shikenan zan sayo maggi mai tauraro na goma sai albasa da tumatir na sauran ashirin din Nagode Allah ya saka da alkhairi ya kara budi Na tafi Yaya sai ka dawo
Sallama mukai dashi alokacin yana kokarin bude kular dumamen tuwon jia dana kawo masa Allah sarki Yayan mu bai ci komai ba ya fita daga gida tun asubah Hanyar karamar kasuwar sayar da kayan masarufin unguwar mu na nufa Nan na hadu da Fadila babbar kawata tana sauri itama da alama cefanon zata yo Dan daga murya nai yadda zata iya jiyo ni na shiga rafka mata kira ina hadawa da sassarfa don cinmata
Fadilah Fadila
Juyowa tayi da sauri tana kallo na fuskar ta dauke da murmushi Karasawa nayi ina haki Ta dan dafa ni tana bubbuga bayana
Sannu tawaje na daga ina kike
Wallahi daga gida amman na biya na kaiwa Yayan mu abincin sa
Murmushi tayi hade da sakalo hannuwan ta ta wuyana muka ci gaba da tafiya a haka Har muka karasa wajen Falalu mai kayan miya Mutum hudu ne a gaban mu Dan haka muka koma daga gefe muna hira Fadila ta sauke nannauyar ajiyar zucia tana yar carafke da duwatsun hannun ta
Tawaje na nakasa cire Yaya Najib a rai na
Na muskuta kusa da ita ina mai kallon kwayar idanun ta dake fitar da hawaye Na kasa gane wane irin so takeyiwa Yayan mu gashi a gidan su an hanata kula shi ko nace Umman su ta hane ta da kula Yayan mu saboda su sunada rufin asiri mu kuma talakawa ne wanda bamuda tabbacin cin yau ko na gobe Mahaifiyar ta irin iyayen nanne masu son yayan su su shiga babban gidah Gashi Yayan namu a babban ajin sakandire na biyu yake ko karewa bai yi ba ya dena zuwa ya koma sanaar kanikanci mechanics ta haka yake dauke mana wasu hidindimun na gidah dana makaranta duk kuwa da ta gwamnati muke yi Ajiyar zuciar nima na sauke cikin bata baki da kwantar mata da hankali nace
Kawata kenan dan Allah ki kara hakuri ki fawwalawa ALLAH lamurran ki na rantse maki da ALLAH idan har Yayan mu mijin ki ne to babu shakka sai anyi auren ku Sannan ki sani Yayan mu fa har yanzu kinga ba gama makaranta yayi ba ko ince ya dakatar da zuwa makaranta saboda muna cikin halin rashi Muma kuma duka duka yanzu muke a karamin aji na biyu Kinga kuwa akwai sauran lokaci Saura aji hudu mu gama makaranta muma Kuma ma ai shekarun mu bana zamu cika sha hurhudu fa 14 Dan dai ma kece kawai kina son sa ne amman naga shekaru hudu fa ya bamu
Nagama fada Ina murmushi Fadila ta rafka min hararar wasa tana tsuke baki hade da sakin tsaki
Wai an gaya miki kowa irin akidarsa ce da ke Ke wannan yadama amman ni gaskia inason Yaya Najib kuma zan iya salwantar da komai don zama mallakin sa
Tabe baki nayi ina sake cuno shi gaba narasa meyasa take son Yaya Najib ko yaushe tasan so oho Kuma ma dai ni abokan Yayan mu wallahi kallon yara nake musu Ina cikin zancen zuci ashe har layi yazo kanmu Fadila ta mike ta sayo kayan miyan sai gani nai ta miko min bakar leda cike da kayan miya Na bita da kallon karin bayani Duk kuwa da nasan hakan ba farau bane awajen mu Amman gaskia ni kunya nake ji duk sanda tayi haka duk kuwa da nasan tasan mu ba masu hali bane
Dalla tashi mu tafi kin kuramin idanuwan ki irin na Ashwariyya rai
Daria nayi domin duk sanda ta tanka idona da irin na Ashwariyya abun daria yake bani Domin nasan ni dai ba jinsin indiyawa bace amman sosai mutane kemin kallon ruwa biyu ce ni Saboda kyau da tsarin halitta da ALLAH yayoni dashi wanda kwata kwata nafi yan gidan mu da yan dakin mu kyau A takai ce dai kamanni na daban Na kan sha kuka na a duk sanda Bintalo ko sauran matan gidan mu suka tasani a gaba suna zagi na da aibata ni koda yake wasunsu a gurin mazajen su suke jin cewar wai ni ba yar baban mu bace Ni shegiya ce Nima nakan zauna wani sain na tambayi kai na ya akai na fita zakka a gidan mu Amma kuma me Ai ALLAH shine mamallakin kowa da komai a haka ya yoni badan ya tsane ni ba Cikin tafiya tunanin da nai fatata tai wani mugun radadi sakamon zazzafan mintsilin da Fadila ta sakarmin a dantsen hannu na na dama
Hararar wasa na jefa mata hade da mika mata hannu na ta ja ni na tashi tsaye Shagon Habulele store muka je na siyo maggi da da mai da omon da zan wanke uniform dina Ganin harda rarar canji da na samu sakamakon kayan miyan da Fadila ta siya mana hakan yasanya na tsaya na sai mana kifin talatin bayan na siyo koko da kosan autar mu Dadi kashe ni yau zamu ci dadi A hanya naita yiwa Fadila godiar alkairin da take mana Saboda kayan miyan yau data siya mana zai yi na nera dari wanda idan har mun cancana shi zai mana sati munashan lagwada Har kofar gidah Fadila ta rakani saboda gidan su na gaba da namu Shigewa nai cikin gida fuska ta dauke da murmushi Banbi takan surutan su Bintalo ba nai hayewa ta sama dakin mu na shige baki na dauke da sallama
Autar mu ce kawai xaune akan shamilalliyar katifar mu wadda kallo daya zakai mata kasan tayi shekaru a haka Sai kwanukan mu a gefe nacin abinci Gefe daya kuma kullin kayan mu ne a daddaure kamar kayan wanki Tamkar dai a kurkin kaji Domin kwata kwata dakin mu bai fi girman taku hudu na auni ba Gashi mune a karshe babu wundo kullum kamar dafamu akeyi Idan lokacin kwanciya yayi Labulen dakin mu a jeme yake shima Tun kafin a haifi autar mu makociyar mu inda Innar mu ke wankau a gidan itace ta baiwa Innar mu lokacin banfi shekaru takwas a duniya ba Kallon Autar mu na sake yi ganin yadda ta dukunku ne tana sharbar kuka da jan majina kusa da ita na je na janyo ta jiki na ina bubbuga bayan ta
Autar mu menene
Cikin rawar murya hade da jan majina tace dani
Yaya Kashi ne ya matse ni naje bandaki don kasayar dashi Ashe wai Kawu ila ya shigar da ruwan wankan sa shine yai ta mun masifa na fito ko yashigo yaci ubana Lokacin kuma ciki na ne yake ciwo Koda na fito sai ya shiga ya dakko bokitin ya juye min ruwan a kai na Sannan ya kwallama innar mu kira kan ta biyashi ruwan sa tunda na bata ruwan da warin kashi na Kuma wallahi Yaya ni ko hanyar ruwan banyi ba Wai lallai sai tabi layin tuka tuka borehole ta debo masa bazai yi amfani da ruwan rijiyar gidan nan ba Kuma yaita zagin ta yana runkwashi na akai
Ta kafarsa fada hade da fashewa da kuka Nima kukan na shiga rerawa ina mai yin addua a zucia ta kan ALLAH ya yaye mana wannan kuncin rayuwar da muke fama da ita shekara da shekaru
Yanzu ina Innar mu
Ta tafi gangare debo masa ruwan
Hawayen dake yar tsere a fuska ta na goge Sannan na mike na fice ina jaddadawa autar mu da taci koko da kosan dana siyo mata kafin mu dawo Ficewa nayi cikin sauri nayi gangare inda tuka tukar borehole yake Can na hango Innar mu a layi ta dan tsugunna tana duban wasu yara dake wasan yar galagala a gefe Da sauri na nufi wajen ta
Innar mu
Juyowa tayi ta dube ni fuskar ta dauke da murmushi dan sam bata bata ranta a duk lokacin dasu Baba Ilah suka sauke mata kwandon rashin mutunci Saboda batason kimar su ta rage a idanun mu Saboda kannen uba da yayyun sa suma iyaye ne agare mu
Batoul
Naam Innar mu Kije gidah zan taho da ruwan
Kada kai tayi Sannan ta mike tana nunamin bokitin baba ilan Tana tafe tana hada hanya saboda yunwa ga masifar su Baba ila da kullum da ita muke tashi Mutum uku ne a gabana da haka da haka har layi yazo kai na Na debo taf sannan na tafi gidah Har cikin bandaki na kai masa Sannan na haye sama abu na Autar mu na gefe tana cin koko da kosan ta Innar mu kuma tana yayyanka tumatir da albasa Zama nai a bakin kofa ina bubbuga kugu na sakamakon ciwon dayake min
Wash Allah Na
Sannu Batoul
Sannun mu Innar mu Yawwa kayan miyan Fadila ce ta siya mana nayi karambani na sayo kifi da kudin da Yaya ya bani
Babu komai Batoul Allah sarki Fadila angode mata Allah ya saka mata da alkhairi
Ameen Innar mu
Ba adau lokaci ba Innar mu ta gama abincin ranar mu aka zubawa Yayan mu a roba autar mu takai masa Mu kuma muka hadu muka ci namu a babban tire domin haka muke cin abincin mu a tare ko Yayan mu yananan dashi ake haduwa aci Na tattare dakin na share na kintsa komai sannan na debi uniform dina na makaranta da na autar mu nai kasa na wanke tas banbi takan bakaken maganganun dasu Alawiyya ke gasamin ba
Nasan mai karatu zai yi mamakin irin halin rayuwar da muke ciki a gidan mu tamkar gidan haya dake tattare da yaruka kala kala Toh zan baku takaitaccen tarihin mu
ASALIN MU
TAKAITACCEN TARIHIN MU
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE BILLYN ABDUL
DAURIN GOROHAFSAT RANO
IGIYAR ZATO MISS XOXO
_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN_
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin
07067124863
_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_
09032345899
_Sayen nagari maida kui gida masoyan asali_
Mucigaba da shakatawa da wannan KAFIN A FARA KAFTA WASAN
MX
915 639 PM 234 809 521 5215 ZAFAFA BIYAR NA KUDINEIDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARINGIDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER
KARANTA: Nihaad Hausa Novel Complete
IGZ
SHAFI NA UKU
Zo nan dan uban ki
Wani abu ya tokare min a wuya na Na rasa mai yasa ala dole sai sun zagi Abban mu aduk lokacin da zasu mana fada Jiki ba karfi na karasa kusa dashi na tsugunna tamkar mai neman gafara
Gani Kawu
Da alama bai masan meyasa ya kira ni ba Domin sai cixan lebe yake alamun tunani Babu abinda nayi masa wallahi Kawai dai neman yadda zai dake ni yake yi ko tozarta Innar mu
Ruwan tuka tuka zaki ebo mani kwarankwatsa idan kika dade baki kawo ba sai na lahira yafi ki jin dadi
Na kara kasa da kai na ina kukan zuci duk ga yara nan ciki harda almajiran gidan amman babu wanda zai ebo masa ruwan sai ni Ga yunwa dake addabar ciki na sai kukan agaji yake Rankwashi ya sakar min a kai na nai saurin dafe wajen
Toh kawu a me zan ebo maka
Tambaya ta kike Lalle figegiyar mahaifiyar ku ta kara lalata ku
Mikewa yayi daga kan bokitin da yake zaune ya shiga zundumawa Innar mu kira ba kakkautawa
Ke Kaltume Kaltume kina ina ne Zaki fito ko sai na raunata shegiyar yar nan taki
Innar mu dake sallar nafila tai hanzarin sallamewa cikin sauri tafi to tana dafe kirji
Kawun su ya akai Lefi ta maka Dan Allah kayi mata hakuri
A dai dai lokacin Usaiba tai kukan kura ta cakumi Bintalo tana yage dankwalin kanta Tun daxu suke fada
Shegiya mai kan kwakwido
Cewar Usaiba ta fadawa Bintalo tana tsurtar da yawu a gefan Bintalo Bintalo ta kece da daria tana nuna Usaiba da hannu
Shegiya wada tamkar a kife ki da kwando da ido aciki munafuka
Baba ila yaja tsaki yana nuna su da hannu
Ku fitar min a hanya ko nai sanadin barin mutum anan gidan
Innar mu dake saukowa daga bene tafara girgiza kanta tana mai cewa da baba ila
Kayi musu hakuri sharrin shedan ne
Kawu ila ya kece da daria hade da tafa hannaye kamar mace Cikin kasakantaccen kallo ya dubi Innar mu
Toh munafuka algunguma Saidinawa ana ruwa kuna irgawa masu bacci da ido daya
Innar mu tayi shiru kanta a kasa Bintalo ta buga zanin ta tana sakin guda
Kuji min annamimiya Ke har kina da bakin magana Dangin mayu uwar shegiya acike nake da ke wallahi kika kuskura wata kalma tafito daga bakin ki sai na daka shegiyar yar ki
Innar mu tayi shiru kanta a kasa na goge hawayen da ya fara tsere a fuska ta Wai shin yaushe zamu dandani farin ciki ne Wannan wacce irin musibace ace yan uwan mahaifin ka na jini su dinga kyamatar ka suna laantar ka
Ya ALLAH ka nuna min ranar da zan mai dawa su Kawu ila martani domin nagaji da rashin kauna da tozarcin da suke mana shekara da shekaru Ameen ya hayyu ya qayyum
Na fada a zuciata ina mikewa tsaye
Bokitin da ya mike akan sa na dauka na fice cikin sauri Usaiba dake gefe ta ja tsaki tai hayewar ta sama tana mai jifan su da munanan kalamai Har naje tuka tuka na dawo ina jiyo muryar kawu ila yana zuba magana da alama da Innar mu yake domin ina jiyo ta tana bashi hakuri A soro na tsaya ina mai baje kunnuwana don jiyo zancen su
Ki jawa shegiyar yar ki kunne dan billahil azim idan ta sake nanata hali irin na yau sai nayi maganin ta Kina jina ko
Innar mu tai hanzarin kada kanta alamar Eh kafin tace
Toh Kawun su Insha Allahu ba zata kara ba ayi mata uzuri
Hawaye na na goge ina takaicin banyi komai ba amman kusan kullum sai an laqaba min sharri kawai don Innar mu ta kaskantar da kanta taba su hakuri shi yasa duk wata bolar su akan mu suke zuba ta Shin a haka zamu dawwama cikin bakin ciki Cikin zucia ta na shiga nanata
Ya Raheem saadneey min kullu amr
Har bandaki na kai masa ruwan sannan na koma bakin kofar dakin sa
Kawu Ga ruwan na kawo
Annamimiya Bace min daga bakin kofa
Jiki ba kwari na mike nai hayewa ta saman mu Cin karo nayi da Alawiyya ta yaba jambaki a baki tana kwarkwasa Bintalo dake gefen ta tana gyara mata mayafi tai bake bake a matattakalar benen da zan wuce Na tsaya ina jiran ta wuce
Meye kike bin ta da kallo Zaki kasa da idanun ki ko sai na zuba miki mari
Matsawa nayi nesa dasu kai na a kasa Kawu Dawood ya fito daga dakin su yana aswaki shi gaskia ba shida hayaniya irin tasu Kawu ila Kawai dai shi matar sa ce zata nemo abinci ko da kuwa bara za tayo babu inda zashi kullum yana kwance a daki tunda aka kore shi daga wajen aikin sa cikin tabe baki ya dubi Bintalo
Hayaniyar menene haka kuke yi
Hayaniyar da akai ai da yawa wacce daga ciki
Ya tofar da yawu ya cigaba da kuskure bakin sa kafin yace
Hayaniyar yanzu Meyasa waccen yarinyar ke rakube a gefen ku Ki bata hanya ta wuce mana
Oh shegiyar can Take Alawiyya tai a kafa ta kuma nemi ta bangaje ni kan naki matsa mata ta wuce
Ware idanuwa nayi jin sharrin da Bintalo ta hadamun Cikin rawar murya nace
Kawu Dawood wallahi ban aikata ko daya daga ci
Wuce ki tafi
Ya fadamin batare da yaji karashen magana ta ba rabawa nayi ta gefan su na wuce dakin mu Ina shiga na tarar da Innar mu tana lazimi autar mu kuma tana aikin da aka basu a makaranta Kayan makaranta na nacire na daura zani wanka kawai nakeso nayi idan naci abinci Kwanon gabanta Innar mu ta matso dashi kusa dani budewa nayi ina murmushi garin kwaki ne da mai da yaji Na wanko hannu na a tukunyar bayan mu sannan na fara handama shi a baka bayan nayi bismillah Ina gama cinyewa nai hamdala nacaccen hijabi na na zura na dauki robar sosan wankan mu da sabulu irin danyaka dinnan na naira ashirin Na hada da bokiti na sauka kasa don yin wanka Da mutum acikin bandakin hakan ya sanya na zauna a dandamalin kitchen din kasa wanda matan Kawu ila ke amfani dashi Bude kofar bandakin akai na daga kai na don ganin wanda zai fito Innatuwa ce tafuto wato matar Kawu Khamis sai baje hanci take yi da alamun kashi tagama kasayarwa
Shiga nayi bayan nayi adduar shiga bandaki Wanka nayo nima na dan karkace na sau kashi na wanda dakyar yake fitowa sakamakon garin da naci saman mu na haye na shafa mai hade da sanya kayana dake karkashin kwallar mu hijabin islamiyya na zura na dau yan littafan da muke yi nayiwa Innar mu sallama kan sai na dawo Tare da yiwa autar mu kashedin kar tayi latti Saboda manya mu karfe uku muke tafiya yara kuma sai karfe hudu
Ta gidan su Fadila na biya a bakin gate din su muka hadu da ita tana sanya hijabi Tana gani na ta dashare hakora nayi murmushi ina tsaye a bakin kofa
Tawan
Fadila ta fadamin tana mikomin jakar ta karfa nayi na rike ina jujjuya littafan hannu na
bestie ya kike Kice yau baki makara ba kenan
Daria tayi tana harara ta
Dalla na dinga makarar kenan Yauwa na taho miki da lessons din da akai mana yau Idan aka fita free period sai na koya miki
Nagode bestie Allah ya bar zumuncin mu har gaban abadan
Ameeen
A tare muka tafi hannuwan mu saqale dana juna Idan ka ganmu dole ne mu birge ka saboda yadda muke ba amintar mu hakkin ta hakika Fadila ta xarce aminiya ta zama hamimiya kuma yar uwata ta jini mai son cigaba na duk karatun da ake musu a makarantar su sai ta koya min sannan tanada lesson teacher dake zuwa har gidah ya koya mata karatu ranar asabar da lahadi shima dik sai ta koya min Bangaren Islamia ma duk abunda bata gane ba ina koya mata kasancewar ni ce monitan ajin mu sannan nafi kowa kokari da hazaka ba yabon kai ba Idan kayan dadi suka yi a gidan su sai ta kawomin nata rabon bama boyewa junan mu komai mun kasance muna bawa junan mu shawara duk sanda hakan ya kama
Akan hanya muka hadu da Haysam wato daya daga cikin samarin dake nacin so na Ina ganin sa na bata fuska na shiga zame hannu na daga na Fadila saboda nasan dole sai ta tsaya tasa munyi magana dashi ala dole Haysam matashi ne mai jini a jika dan shekaru goma sha tara yanada kyau da kamala sannan da ne ga Alhaji kabeer wafa wato manajan chanjin kudi na bangaren Zaria Banason Haysam saboda dan masu kudi ne ni kuma yar talakawa ce bayaga haka ma banason kula kulen samari ga kuma sharadin Yayan mu daya hanani kula kowannen su Saboda na tsaya na fuskan ci karatu na sosai Tundaga nesa Haysam ya tsuramin ido yana bin kallo na tundaga kan yan yatsun kafata zuwa kirji na da fuska ta
Dan iska
Na fada ina cuno baki na gaba ina sake kokarin kwace hannu na daga na Fadila ganin yadda take masa murmushi alamin ya matso kusa ga ni Kin sakin hannu na tayi Hakan yasanya Haysam tunkaro mu yana taune leben sa na kasa
Batoul
Yakira sunana yana sakin murmushi na kauda kai na gefe ina sake hade fuska ta Ganin hakan ya sanya shi mai da kallon sa ga Fadila
Aminiyar mu ya kike
Lapia lou saurayin mu Ya gidah
Alhamdulillah fa Islamiyya zaku ne
Ya tambayeta yana mai sake maida kallon sa fuska ta
Eh wallahi can zamu
Nazo nayi rakiya
Meze hana Bismillah
Jerawa mukai dashi muna tafiya Fadila na tsakiyar mu suna hira lokaci zuwa lokaci yakan sako sunana ko zanyi magana Ni kuwa shiru nayi naki tankawa har muka karasa makaranta Sallama su kai da Fadila ya tafi gidah mu kuma muka shjga ciki
Ki dena abunda kike Allah Menene makusar Haysam Meyasa bakya son sa Akan wane dalilin zaki dinga garashi tamkar taya Haba Batoul Ki dena yiwa samarin ki haka Allah Wasu ma ido rufe suke neman masoyan ke kuwa kin samu damar ki a hannu kina neman ta kubce miki kiyi tunani tawan
Bestie kenan Dukaduka shekarun mu nawa Sannan ko ajin farko na siniya sukul bamu shiga ba bayaga haka Haysam dan masu hannu da shuni ne Banason hada kai na da wanda suka fini a komai har a addinan ce a har kullum so ake ka kalli na kasa da kai ba wanda yake saman ka ba ya kere ka Sannan sahibin ki ma wato Yayan mu ya hana ni kula samari
Fadila ta fadada murmushin ta jin na ambaci masoyin ta
Hakane kuma Toh Allah ya zaba mana mafificin alkhairin sa Ameen
Ameen
Aji muka shige aka fara tilawar karatu kafin Ya Sayyadi ya shigo Haka dai mukai ta tilawa sannan aka kada kararrawar sallar laasar Sallah muka fita muka yo sannan muka koma aji Malam yabi daliban ajin mu daya bayan daya ya karbi haddar suratul Yasin da Ashmawi Ya fita sai Malamin dake mana Bulughul Maram da Buhgayatul Muslimeen ya kara mana daga karshe mukai Sira da kuma Usulul Thalatha
Haka dai rayuwa ta cigaba da garawa Safiya ta zama rana Rana ta zama yammaci Yammaci ya zama dare Lalle Allah qadirun ne ala manyashau Yau da dadi gobe babu A haka dai akai mana hutun karshen aji a daddafe muka je Shema kauyen su Innar mu ni da autar mu mu kai hutu Anai sauran kwana ki biyu zaa koma makaranta muka dawo Dan kudin da muka samo a Shema dasu Innar mu ta yanka mana sabon inifom aka dinka mana ta sai mana takalma na makaranta da safa yar gwanjo Takuma yi mana dan tsince tsincen kayan abinci Ciki har da rabin buhun gawayi da taliya yar aune dari ukun kai kuma ta auno kananzir da manja nera darin kai kuma ta bani kan na ajiye mana kudin birek ne na makaranta ni da autar mu har tsawon kwana ki uku Dama gashi ni na shiga babba aji na uku na jiniya sakandire Autar mu kuma ta shiga ajin firamare na uku Haka dai muka shiga rufawa juna asiri don ciyar da kan mu
Ranar wata asabar muka tashi da tashin hankali Domin ogan su Yayan mu wato mai wurin kanikancin su ya sayar da wajen ga wani mutumi inda zaa mayar da wajen filin yin biki na kudi dake katon waje ne Gefe kuma wajen wanke mota Yayan mu yaci kuka ko ince munci kuka duk kanin mu Innar mu kuwa muryar ta har dashe wa tayi tsabar kuka Kasa zuwa makaranta muka yi ni da autar mu Yayan mu mai share mana kukan mu yanzu shima abun a taimaka masa ne Tsawon kwana ki uku muka dauka bama zuwa makaranta Islamiyya kuwa munma ajiye babinta a gefe domin bamu da tabbacin samun kudin biyan islamiyyar na wata wata Yayan mu ya buga koina amma babu aikin yi domin duk inda yaje nema sai ace sai ya kawo takardar kammala sakandire tukun
Da dare tare muka hadu muka ci kwadin tafasa da Innar mu ta samo a gidan da take wankau Sannan muka dora da taliya da mai da yaji Innar mu ne gefe tana jin rediyo Mu kuma mu da Yayan mu muna hirar mu Har lokacin bacci yayi Yaya ya dauki yar taburmar sa da net ya daura a tsukukun kofar dakin mu ya kwanta lokaci daya bacci yai awun gaba dashi Cikin dare fitsari ya ishe ni na mike daga kwancen da nake daure da zani na zira hijabi na dauki cocilan mu na shiga haska gabana dashi a hankali na tsalle Yayan mu na sauka bandakin kasa na shiga zurara fitsari na ahankali ina rufe bakina sakamakon bahaguwar hammar da naketa saki wadda kallo daya zaka min kasan bacci ne a idanu na Ina gamawa nai tsarki na fito daga bandakin baki na dauke da addua Ina hawa bene mu kai kicibus da Islaha kanwar Bintalo wadda tazo daga kauyen su Ta kasance tana mutuwar son Yayan mu Gashi Yayan namu ko kallon ta bayayi idan suka hada idanu ya zabga mata harara Hango Yayan mu nai ya tattare kayan kwanciyar sa zai fita waje Da alamun takura masa tashiga yi Ni dai daki nai shigewa A hankali a hankali nake jiyo nacin da Islaha ke yiwa Yayan mu
Sakarmin hannu dalla malama
Da sauri na fito daga daki ina kallon yadda Islaha ta rike hannun Yayan mu dumudumu acikin nata Sai zabga mata harara yake yi yana kokarin kwace hannun sa taki sakin sa A dai dai lokacin Bintalo tafito daga daki kallo daya tayi musu ta daura hannuwan ta akai cikin sakin wata irin shegiyar kara tace
ihuuuuuu Gardiiiiiiiiii
Ai bata rufe baki ba mutan gidan mu suka fara firfitowa daga dakunan su kankace me Anyi cincirondo kowa yana kallon su Yayan mu Islaha daure da zani ba dankwali a kanta Shi kuma Yayan mu sanye yake da wando dogo babu riga ajikin sa sakamakon zazzafan zafin da ake zubawa yasa tun da zai kwanta ya cire yashiga cikin net
Innalillahi wainna ilaihir rajiun
Itace kalmar da Yayan mu yake ta furtawa lokaci daya hawaye suka shiga yar tsere a fuskar sa Nima na goge nawa hawayen tare da tsugunnawa sakamakon rawar da kafafuna suka shiga yi sun kasa daukar gangar jiki na tsabar tashin hankali Na dubi Bintalo dake sakin wani makirin murmushi tana tafa hannuwa
Shege wan shegiya dan shegiya An tsotsa a mama ai dole a nuna hali Toh karshen tukatuka tik Allah ya kama ka Tun ranar da yarinyar nan tazo gidan nan kake bibiyar t
Bata karasa ba Innar mu tayi hanzarin shiga tsakanin su Ta kwace hannun Yayan mu daga na Islaha cikin rawar baki da jiki tace
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE BILLYN ABDUL
DAURIN GOROHAFSAT RANO
IGIYAR ZATO MISS XOXO
_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN_
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin
07067124863
_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_
09032345899
_Sayen nagari maida kui gida masoyan asali_
Mucigaba da shakatawa da wannan KAFIN A FARA KAFTA WASAN
MX
915 639 PM 234 809 521 5215 _IGIYAR ZATO__
_NA_
_NANA HAFSAT_
_MISS XOXO_
_ZAFAFA2020_
_SABON TAKU_
_SHAFI NA BIYU_
ASALIN MU
TAKAITACCEN TARIHIN MU
GWANI IDRIS NAJIBULLAH
Marigayi Gwani Idris Najibullah shine sunan mahaifin baban mu Tare da matar sa Malama Halimatu Alkali Ya kasance Malami a garin na kaduna matar sa wato mahaifiyar su baban mu ita kadai ce mai dakin sa ALLAH ya albarkace su da yaya shida Kawu Ishaq Kawu Dawood Gwaggo Aminatu Kawu Khamis Sai mahaifin mu Salis Sai Kawu ilyas wanda ake kira da baba ila shine karamin cikin su Dukkanin yan dakin nasu a Zaria suke gidan mu daya Banda Gwaggo Aminatu wadda ke aure a Kaduna Gidan da muke ciki a Zaria gida ne na gado wanda iyayen mu suka hada karfi da karfe suka siya Dakuna tara ne acikin sa kowanne guda daya daya ne ba ciki da parlor Sai dakin baba ila dake kasa shine mai ciki da parlor Dukkanin yan uwan mahaifin mu a gidan suke da zama da matan su Gidah ne mai hawa biyu mune a saman karshe dake dakuna uku ne Muna cikin daya sauran biyun kuma Bintalo da yayan ta na daya Sai Usaiba mahaifiyar su Larai da Talatuwa Usaiba matar Kawu Ishaq ta farko sai amaryar sa Rabiatu ita takansace juya ce bata haihuwa sannan a dakin kasa take Dakuna uku na kasan mu kuma Kawu Dawood ne da matar sa Hafsatu sai yan biyun su Fareed da Fareedah Sai Kawu Khamis da matar sa Innatuwa da Yayan su maza biyu kanana wato Yushau da Bala Sai dakin karshen saman nasu wanda Rabiatu take ciki wato matar Kawu Ishaq ta biyu Sai Kawu ila wanda ke dakunan kasan karshe shi da matan sa Ummita da Hajara dakin farko mai ciki da parlor Ummitan ce aciki wato matar sa tafarko Ita da tawagar yayanta su biyar dake yawan haihuwa take yi akubi akubi Sai daki dayan karshe na amaryar sa Hajara wadda ya aure ta bayan rasuwar mahaifin mu Takasance tanada tsohon ciki wadda zata iya haife shi a kowanne lokaci saboda ya tsufa
Marigayi Malam Salis Idris Najibullah shine mahaifin mu Malama Kaltume Rabiu shine sunan mahaifiyar mu Mahaifin mu kafin rasuwar sa ya kasance yanada mata biyu Innar mu Kaltume sai Baba Zarau wacce ake kira da Bintalo Mahaifin mu dan asalin cikin garin Kaduna ne almajiran ta takawo su shida yan uwan sa Zaria Anan kuma ALLAH yayi zasuyi aure su hayayyafa Mahaifin mu lokacin da suka fara sanaar tashi zuwa garin katsina anan Allah yayo zai gamu da mahaifiyar mu a kauyen Shema Mahaifiya ta irin fulanin nanne na jaubawa Mahaifin mu kuwa bahaushe ne gaba da baya Domin kakan su ma kafin Allah yayi mai rasuwa ance a garin kano yake Baba Bintalo yar uwar mahaifin mu ce da kakanta da mahaifin baban mu uwa suka hada uba kuma kowanne da nasa Auren nasu ma auren hadi ne ko nace auren zumunci ne mahaifiyar mu kuwa itace matar sa ta ladan noma wato auren saurayi da budurwa Mu bakwai ne awajen mahaifin mu dakin mu mu uku ne Yaya Najibulla wanda yaci sunan kakan baban mu ana kiran sa da Najib Sai ni FadimatuzZahrau wadda ake kira na da Batoul Naci sunan mahaifiyar maman mu wadda ALLAH yayiwa rasuwa tun ina yar kankanuwa Sai autar mu Aminatu Wadda taci sunan Yayar mahaifin mu dake garin Kaduna Sai yayan Bintalo guda hudu Yaya Zabbau wacce ke aure a kauyen kode dake lahadin makole a Kano Sai Alawiyyah da Hindatu wacce muke kira da Hinde Sai autar su Hauwa
Nasan mai karatu zai yi mamakin yawan gidan mu da kuma ahalin dake cikin sa Toh kamar yadda kuka gani a baya Gidan Mata Tara gida ne mai dakuna guda tara Sannan gidah ne wanda mahaifin mu da yan uwan sa su hudu suka hadu suka siya tun kafin a haife mu
Mahaifin mu marigayi Malam Salis ya rasu ne shekaru bakwai da suka wuce lokacin autar mu Aminatu na jaririya ya rasu ne akan hanyar sa ta zuwa gidah sakamakon hatsarin mota daya rutsa dasu wata jibgegiyar gingimari ce tabi takan mashin din da yake kai alokacin yayo cefanen sunan kanwar mu Aminatu Tundaga lokacin rayuwar mu ta canza zuwa halin rashi da kuma kunci
Ashe haka kanne da yayyun uba suke Tabbas mun shiga garari na rayuwa domin duk juya mana baya su kayi abincin da zaa ci da rasuwar ma sai makwabta ne suke temakawa su bayar sai da Gwaggo Aminatu tazo daga kaduna ne ta fuskanci halin da muke ciki ta bamu hakuri sannan ta bayar akayo mana cefanen kayan abinci Hakika Gwaggo Aminatu ita kadai ce mai kirki acikin yan uwan mahaifi mu itace keyin mai yiwuwa don ganin ta tallafa mana ta tsaya har aka raba mana gado mahaifin mu bashi da wata kadara fyace gidan da suka hada kudi suka saya shi da yan uwan sa inda mahaifiyar mu da Bintalo kowanne ya kasance yanada rabo biyu biyu tanada mata hudu mu kuma namiji daya mata biyu wato biyu kenan muma Kowanne bangare daga cikin mu ya tashi da daki daya daya Sai daki daya wanda Rabiatu take ciki wato matar Kawu Ishaq ta biyu shine ya zamto a tuminin takabar su Innar mu Nasan zakuyi mamakin toh aina Yaya Najib yake kwana ko Toh Yayanmu yana daura net a tsukukun kofar dakin mu ya kwanta a kan yar tabarmar sa wani lokacin kuma yakan kwana a langa langar makarantar almajiran dake kallon kofar gidan mu
Tunda mahaifin mu ya rasu mu kai sallama da farin ciki Innar mu ta kanyi wankau a gidajen masu hannu da shuni saboda rufin asirin mu Yaya Najib kuma ya kasance yana kanikanci don samo mana abunda zamu afa a baka Ni da autar mu kuma mu kadai ne keyin makaranta itama ta gwamnati wanda Yaya Najib da yanayi ya dakatar saboda bamuda halin da duk kanin mu zamu dinga zuwa makaranta duk kuwa da ta gwamnati ce Amman akwai tsarabe tsaraben kudin fom nera talatin duk wata ga kudin littafi da fensir Hakan yasanya Yayanmu dakatar da zuwa makaranta ya fara sanaar kanikanci dan kare mana mutuncin mu sannan muna zuwa Islamiyya duk wata naira hamsin itama yayan mu ne ke biya mana kudin Duk kuncin rayuwar nan muka dai ne muka shige ta banda Bintalo da Yayan ta domin ita su Baba ila suna taimaka mata Hakan yasanya na qudri niyyar tsayawa tsayin daka don yin karatu sosai Saboda inaso nayi amfani da damata na cika mana burikan mu Hakika ALLAH ya yoni da saurin daukar karatu da kaifin basira komai yawan karatu cikin sauki nake gane shi na kuma hadde shi Shiysa haddar AlQurani da muke baya min wahala cikin kankanin lokaci nake haddace ta akai na
Tabbas ALLAH ya yoni da zatin halitta da kyakkyawar sura Idan ka kalle ni dole ne ka sake kallo na duk kuwa da kankancin shekaru na amman halittar jiki na a tsare take koina ya cika sannan na kasance mai wata irin kalar fata ni ba fara can ba ba kuma baka chakulet ba Na kasance tsaka tsaki wadda turawa ke kira da brown skin Inada tsawo sosai TubarkAllah Idanuwana farare ne tas da su kamar ruwan madara kwayar idanu na kuwa burawun ce sosai sai yalwar gashin gira domin saura kadan su hade da juna baki na dan mitsitsi ne jawur dashi kai kace jambaki na shafa hanci na dogo ne sosai ga kuma tawadar ALLAH a gefan hancin wanda ya kara kyawun fuska ta Inada yalwataccen gashin kai tubarkAllah tamkar ni na kera abuna har gadon bayana yake zuwa Shekaru na goma sha hudu a dunia inada saoina sosai a gidan mu Wanda suke kulakulen samari kamar tinkiyoyi Idan kaga layin da ake a kofar gidan mu za kwi mamaki Na kasance ina da dinbin samari Sai dai basa kulani saboda rashin ganin fuskar hakan Sannan Yayan mu ya hanani kula kowanne daga cikin su Hakan ba damu na yayi ba domin nima banida raayin kula samari yanxu Nafison sai nayi karatu sosai kuma inada burin auren wanda ya girmemi ni sosai domin agani na sunfi hankali da nutsuwa
Duk abokanan Yaya Najib kallon yara nake musu har a sujjada nake rokon ALLAH karya sa na auri wanda ya girme mini da shekaru biyar nafuson na auri wanda ya bani shekaru goma da yan kai saboda wasu dalilai na dana barwa zucia ta A karamin aji na biyu nake a jiniya sakandire wadda ake kira da gwanmen gels jiniya sakandire sukul shekaru na sha hudu a duniya banida burin da nake so na karanta irin karantar bangaren zallar ingilishi Kuma har farfesa nake so na zama a fannin
Gidan mu ya kasance mai dakuma tara aciki kuma Idan ka lissafa matan auren dake ciki su tara ne Hakan shi yasanya yan layin mu dama unguwoyin gaban mu yiwa laqabi da gidan mu Gidan Mata Tara
Wannan shine takaitaccen tarihin gidan mu dama nawa a takaice
WASHEGARI
Tun asubar fari dana tashi ban koma ba bandaki nai hanzarin shiga nayo wanka na saboda bandaki daya ne kawai a gidan mu kuma har layi ake yi akan sa Ina gama wanka na na tado autar mu itama na sabe mata jikin ta Innar mu ma tayo nata bayan mun gama kintsawa Uniform dinmu na zaro mana a karkashin kwallar da muke ajiye kwanukan abincin mu Domin anan nake mana ninkin guga sai na zura su a leda na dora kwallar akai sai kuga kuma sun ninku tamkar an goge shi Rogowar dumamen shinkafar jia muka ci na koma gefe ina azkhar Innar mu kuma tagama nata tuni ta kunna yar rediyon ta tana jin labaran jamus Autar mu kuma ta kishingide tana bacci daria taba ni yadda ta kanannade tana baccin ta da yar ledar littattafan ta a hannu Gyara mata kwanciyar nai yadda zata ji dadin baccin ta Haka dai nai ta jira har rediyon hannun Innar mu suka sanar da karfe bakwai da kwata Mikewa nayi na dan diga turaren dan duwalar da shi kadai ne turaren mu na shafe jikina dashi Tashin autar mu nayi ta kara wanko bakin ta da fuskar ta Innar mu dake gefe ta miko min naira talatin
Ungo ki dau ashirin din ki barwa auta goman ALLAH ya bada saar karatu mai amfani
Rissinawa nayi na karba cike da girmamawa
Mungode Innar mu ALLAH ya kara budi
Innar mu mungode
Autar mu tafada tana rufe bakin ta sakamon hammar data taho mata da alama baccin bai gama sakin ta ba
Haka dai na tasa keyar ta muka fara sauka a bene a lokacin su Alawiyya ke wanka kamshin soyayyan kwai sai tashi yake daga dakin su Da alama dashi zasu tafi makaranta Nida autar mu ne kawai ke yin makarantar gwamnati Su Alawiyya firabet suke zuwa duk tam dubu daya da dari biyar Makarantar su daya da Fadila babbar kawata Ina ta jan hannun autar mu muka tafi makaranta har ajin su na kaita sannan na wuce namu ajin Koda aka fito birek awara da wainar fulawa na siya mana ni da autar mu Goman ta kuma muka sai ruwan biyar da alawa Ana tashin mu muka dauki hanyar gidah Muna tafe a hanya ina bitar haddar Ashmawin da zaa karba an jima a islamiyya Tun a kofar zauren kofar gidan mu muke jiyo hayaniyya kai na na dafe da hannun dama ina girgiza shi shin yau ko da suwa ake dambatuwa oho Muna shiga na jiyo muryar usaibatu maman su Larai tana lailayo ashar tana durawa Bintalo Nan dai suka hau gumirzin fada Baba ila dake tsakar gidah ya janyo bokitin karfe ya zauna akai yana duban su da kallo Sunne kai nayi a kasa na fara hawa bene muryar Baba ila na jiyo yana doka wa suna na kira
Batoul Ke Batoul
Gaba na ya fadi jikake ras Shin menayi ni kuma Cikin rawar baki da jiki na fara komawa kasa ina nanata
Naam KawuGani
_______
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE BILLYN ABDUL
DAURIN GOROHAFSAT RANO
IGIYAR ZATO MISS XOXO
_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN_
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin
07067124863
_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_
09032345899
_Sayen nagari maida kui gida masoyan asali_
Mucigaba da shakatawa da wannan KAFIN A FARA KAFTA WASAN
MX
915 639 PM 234 809 521 5215 ZAFAFA BIYAR NA KUDINEIDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARINGIDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER
07067124863
Ko kuma
09032345899
ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbikarku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING
httpsyoutubeLxY42ErBf_8
_SHAFI NA HUDU_
Ya ishe ki Bintalo Banason tashin hankali shiya sa bana biyewa ayi dani idan hayaniya ta kaure a tsakani Saboda haka kada ki kara sheganta min yara yayana yan halak ne Allah ya isar mana idan har kika kara aibata su Banda bina da yayana da sharri ba abinda kika iya Allah ya tsare mu daga miyagun halayen ki
Tunda Innar mu tafara magana har ta gama gaba daya kowanne acikin yan gidan mu mamaki ne dankare a zukatan mu idanuwa muka zuba mata ni kam harda kyakkyaftawa ko mafarki nake domin tunda nake bantaba ganin Innar mu ta maida wa wani martani ba fyace yau Da alamun an kaita mukura dadi ne ya mamaye ni ganin tafara samawa kanta yanci Na dubi Bintalo yadda ta daskare a wajen tana kikkifta idanuwa da alamun maganganun da Innar mu tayi sun shammace ta Cikin tunanin dana tafi na sake jiyo Innar mu tana yiwa Yayan mu magana
Wannan yaron Saboda dan fari ne Inaso ka gayawa kowa yadda ku kai da yarinyar nan data bika da sharri
Innar mu wallahi kawai ina kwance a cikin net na jiyo ana kiran sunana Sai kawai na mike tsaye ina kallon gabana ganin mai kiran nawa Ashe ita ce Tasa hannu kenan zata bude min net din na mike tsaye gaba daya na tattare tabamar tawa da net din zan koma langalangar almajirai Toh a lokacin ma na hango Batoul ta dawo daga kasa da alamun bandaki taje Bayan shigar Batoul daki ke da wuya kawai naji ta riko min hannu nai nai ta sake ni taki Nasa dayan hannu na kenan zan fincike sai Bintalo tafito daga dakin ta tana kurma ihun gardi Wallahil azim hakan akayi Daman tasha tara ta a koina ne tana gayamin kalaman so Gata nan a tsaye idan karya nai mata
Bintalo tayi kukan kura tana girgiza jiki agaban kowa
Sittin ta Ubangiji karya kake yi Waya san sau nawa kake lalata ya
Karya kike yi Bintalo wallahi tallahi wannan yaron baya kula wata ya mace ma ballanta na har yakai ga lalata Allah ya isa wallahi Kin kai ni karshe Bintalo
Innar mu ta karasa fada tana sharce hawayen bakin ciki Kawu ila dake jingine da kafar bene ya ja tsaki yana komawa dakin sa Kawu Dawood ne yai kokarin cewar
Toh ita yarinyar tafada da bakin ta abunda ya faru Sai musan hukuncin da zamu dauka ko kuwa
Su Kawu Khamis suka daga kai alamun Eh hakan yayi Kawu Dawood ya sake maida kansa ga Islaha da kanta ke a kasa tana lankwasa yan yatsun ta yace
Ke gaya mana gaskiyar lamari shin abunda yace shine gaskiya ko kuwa karyane shi ya kira ki
Bintalo tasa kafa ta take ta Islaha alamun tace Eh shine ya kirata A hankali Islaha ta goge hawayen dake kwarara a idanun ta cikin rawar baki tace
Eh Kawu Hakika Yaya Najib shine ya kira ni Tun ba yau ba yakeson yai lallalata da ni
Bintalo ta saki wata uwar guda kai kace amarya aka kawo Cikin buga zanin ta hade da tafa hannuwa tace
Alhamdulillah yanzu naji zance Daman na gaya muku shine ya neme ta
Yayan mu ya saki wani marayan kuka mai kona zucia wanda kowa ya saurara sai ya tausaya masa Cike da rawar baki ya tsugunna a gaban Islaha yana duban idanun ta Wadda tai saurin kauda kai gefe
IsIslIslaha ki dubi girman Allah ki sanar da su gaskiyar lamari zamu mutu zamu koma ga Allah Allah yana kallon ki shin ni na kira ki ko kuwa kece kika neme ni
Islaha tayi shiru tana goge hawayen nadama Yayan mu ya sake tambayar ta har sau uku nan ma dai amsar daya dince dai tabashi Kawu Dawood yai gyaran murya kafin yace
Toh shikenan yanzu dai a barwa wayewar gari komai Ke Islaha kiyi hakuri hakan ba zata sake faruwa ba Kai kuma Najibulla kaje langa langar ka kwana zuwa safiya zamu yanke maka hukunci Allah ya kyauta
Wani kukane ya kufce min jin abunda Kawu Dawood yace Na dubi Islaha jiki na rawa nace
Kiji tsoran Allah Islaha karki ga kwarjinin Bintalo ki fadi gaskiyar lamari
Dakata shegiya waya ce ki tsoma bakin ki Zatai muku karya ne Zaki matsa ko sai na sharara miki mari Ai wallahi Idan naji hukuncin da aka dauka masa bai min ba wallahi zakuji sammaci a kotu
Cewar Bintalo Ta karasa fada tana jan hannun Islaha Innar mu dake gefe ta sharce hawayen fuskar ta Sannan ta dubi Yayan mu cikin sakin murmushin dayafi kuka ciwo tace dashi
Kayi hakuri wannan yaron Kai dai ka cigaba da fawwalawa Allah lamurran ka zamu tayaka da addua Wallahi komai nisan dare gari zai waye Allah zai bayyana mai gaskiya
Tana gama fada ta shige daki Nabi bayanta ina fashewa da kuka Tsabar bakin ciki Yayan mu ko kayan shimfidar sa bai dauka ba ya fice daga gidan Daganan kowa ya watse Ana jiran safiya tayi aji hukuncin da zasu yanke wa Yayan mu
WAYEWAR GARI
Taliyar jia na shekawa ruwan zafi muka ci A roba na zubawa Yayan mu na tafi kai masa Yana zaune a bakin kofar langalangar kansa a kife
Yayan mu
Na fada ina mai ajiye robar abincin a gaban sa dago kansa yai Na tsorata kwarai matuka da ganin yanayin sa Jijiyoyin kansa sun fito sunyi rudurudu dasu idanuwan sa sun kada sunyi jajir dasu lokaci daya ya zabge ya jeme tamkar wanda yayi shekararren ciwo Murmushi ya kakaro yana mai kokarin danne damuwar sa
Naam Batoul
Barka da safiya Yayan mu
Barkan mu Yasu Innar mu
Lapia lou Alhamdulillah
Ga abinci nan Yaya ka daure kaci
Wallahi cikina a cushe yake Amman zan ci
Yauwa Yayan mu Allah ya maka sakayya Ya fidda kai daga sharrin su
Ameen ya Allah
Mikewa nai na barshi yana kokarin bude filet din da aka rufe robar dashi Ina shiga gidah na kwaso kayan wanke wanke na sauko kasa na wanke tas Na koma na hada gawayi na dora ruwan zafi Tsabar munafunci ko makaranta babu wanda yaje acikin yaran gidan mu kowanne jira yake yaji hukuncin da zaa yanke wa Yayan mu Ta sama na hango Kawunnin mu suna ta shiga parlorn Kawu ila daya bayan daya Anan duk suka hallara Kasancewar nanne kadai mai parlor kuma wadatacce wanda zai dauke su Kawu Ishaq Kawu Dawood Kawu Khamis Sai shi Kawu ila din Daki na ruga na zauna hade da janyo carbin Innar mu na shiga yin lazimin Allah ya dora Yayan mu akan su Allah yasa su yanke masa hukunci sassauka
Can parlorn Kawu ila kuwa hallara su kai Sai da sukai yar caftar su wanda dole ne idan suka hadu sai sunyi fada Tukun sannan daga baya Kawu Ishaq kasancewar shine babban su hakan yasanya yayi gyaran murya kafin yace
Toh kamar yadda kuka sani abunda ya taramu anan yau hukunci ne wanda zamu yankewa Najibulla Shin tayaya kuke ganin zaa warware bakin zaren Wane irin mataki ko hukunci zamu yankewa yaron nan Kun san dai sarai Bintalo ba yadda zatai ba idan taji abunda muka yanke bai yi mata ba
Kawu Dawood dake sakace hakoran sa da tsinke ya ajiye a gefe kafin ya sauke nannauyar ajiyar zucia
A yanke masa hukunci dai dai da laifin sa akuma yi masa sassauka A nawa fahimtar wannan matsala da aka samu a tsakanin su abune wanda ke a boye wanda babu wanda yasan tabbacin gaskiyar yadda komai yake
Ya karasa fada yana maida kallon sa ga Kawu Khamis Kawu Khamis ya sau siririn tsaki
Hakane amma ni ina ganin kawai daga shi har ita su bar gidan nan Hakane kawai zai kawo karshen matsalar nan Amman muddin yana nan suna zaune tare a wuri daya to dole sai an sake maimaita rana irin ta jiya Amma ya kuke gani
Kawu ila dake kishingide tun daxu yana kallon su sunata magana sai a lokacin ya dan gyara zaman sa cikin cigaba da fifita da mificin dake hannun sa yace
Bangane ba Khamis Su je ina kenan
Kawu Khamis ya bude baki kenan zai yi magana Kawu Ishaq ya tari numfashin sa
Idan na gane abunda kake nufi kana nufin ita ta tafi kauyen su shi kuma ya koma wani wajen da zama Maana kenan yabar nan Zaria ko
Kawu Khamis ya jaddada kai Baba ila ya gyara zaman sa da alamun sun tabo masa inda yake masa kaikayi
Wannan shine daidai Tun ba yau ba nakeson shegen yaron can ya bar gidan nan Domin naga alamun shi ke tsayawa uwar sa take yiwa mutane ganigani A yau ba sai gobe ba dan tselen uwa zai bar gidan nan
Ya karasa fada sauran na babbaka daria banda Kawu Dawood Domin shi Kawu ila yafi su rufin asiri Don har shagon kayan masarufi yake dashi a gangare Sannan mahaifin matar sa yanada kudi babu laipi Kunsan yaro da kudi abokin manya ko kaine kafu kowa kudi a dangin ku dakayi magana daya ta zauna kenan babu mai musawa Shi yasa kowanne hukunci ya zartar da shi suke amfani Kawu Dawood ne kawai baya shiga harkar sa sakamakon rashin jituwa da basa yi Mikewa Kawu Dawood yai Yayi hayewar sa sama Nan yabar su Kawu ila dasu Kawu Khamis suna zantawa
Karfe sha daya saura kwata na karasa tuwon dawar da Innar mu tasani Ina kwashe wa na dora ruwan miya gaba daya zucia ta babu dadi nake jinta domin idan ka cire mahaifin mu daya rasu da kuma Innar mu toh duk duniya babu wanda nake so irin Yayan mu da autar mu Hakika ALLAH ne kawai gatan mu Amma Yayan mu yana iyakar kokarin sa ganin muna cikin farin ciki ya zamto mana makara dau duka Hawaye ne na goge hade da saurin mikewa tsaye jin muryar Kawu ila yana dokawa sunana kira
Naam Kawu gani nan
Na fada ina mai zura hijabi na Ko takalmi ban tsaya sawa ba sanin masifar Kawu ila Ai kuwa ina sauka kasan ya zabga min harara yana nuna ni da dan yatsan hannun sa guda daya na hannun dama
Wato tsabar raini ina kiran ki tun daxu kina jina shine sai yanzu zaki sakko
Kayi hakuri Kawu wallahi banji ba sai yanzu
Okay wato karya na shirga miki kenan Zo nan dan uban ki Shegiya mai idanuwa irin na jemagu
TubarkAllah
Na fada a zuciya ta Ina mai karasawa kusa dashi a tsorace Tuni hawaye suka fara wanke min fuska Kyakkyawan rankwashi ya sakarmin a kwanyar kai Cikin radadi na shiga sosa kai na ina hawaye yaran dake wajen suka shiga babbaka daria cike harda Hinde dake wanke wanke Na goge hawaye na baki na na rawa nace dashi.
KARANTA: Tame Gari Complete Hausa Novel
0 Comments