Rana Daya Book 3 Chapter 2

Rana Daya Book 3 Chapter 2

Barka da isowa wannan shafin namu na littafan hausa novels inda muka kawo muku littafin rana daya book 3 chapter 2 halima k/mashi.

Rana Daya Book 3 Chapter 2

Yace Hajiya, Ki saurare ni zan yi mikI bayani yanda za ki fahimta' Ta mike tana fadin, "Kana bata min lokaci, ga shi can ana kiran magariba. Ni kawai cewa na yi ka saki waccan abin", Ta nuna Salma wadda ke durkushe a kan Kafafunta, tun gurin da aka titsiye ta Kafatunta sun yi sanyi sun sage, har ba ta san ta yi motsi mai karti don azabar da suke yi mata.

Shatima ya ce, "Hajiya.Ta sake katse shi, Bana son jin komai daga gare ka, sakinta kawai na ce ka yi. Ba zan fahimci komai ba Alhaji ya fado Takin babu sallama, ya amshi zancen Hajiya da cewa,"Wa za a saki?"

Shatima ya mike da sauri tare da fadin, Alhamdu lillahil.

Alhaji Musa ya ce,Zauna Babana, zauna kar ka sake faduwa. Alhaji ya isa gaban danshi da sauri ya kama shi, ya zaunar tareda fadin, "Zauna abinka

Shatima ya zauna cikin farin ciki, tare da ci gaba da yi wa Allah godiya.

Hajiya ta yi matukar girgiza, mamaki ya cika ta da ganin Alhaji. A zuciyarta ta ce,

"To wa ya fada ma Alhaji?"

Alhaji ya dube ta rai bace, fuska daure, "Yanzu Hajiya Amina kin yi daidai kenan? Ki taso tun daga zaria da sunan gaida mara lafiya don ki samu lada, amma ki buge da tada husuma cikin gidan danki?

Ina hankali da tunaninki suka shige? To wa kike fadin a saki ma?"Ya kalli Alhaji Musa, Dubi wani abin kunya don Allah, Alhaji Musa ya ce ga wadda za a ce ta yi abin kunya nan. Kin zo gidan"yarki gaban kishiyoyi, gidan suruki kin tada hankali? Wannan abin fadin da me yayi kama? To da kin yi sanadin rayuwarshi, me za ki Ce?"

Hajiya cikin borin kunya ta ce, "Ni ban tada wata husuma ba. wane munafuki ne ma ya kira Alhajin?"

Ta kai Karshen maganar tare da kure Mustapha da ido. Shatima ya ce, "Alhaji, don Allah ku zauna, nidai na gode wa Allah da ya turo mini ku a daidai wannan lokacin.

Don Allah ku taimaka min ku zauna don a warware wanna matsalar. Domin duk wata matsala a duniya ana warware ta ne ta hanyar zama a tattauna ba ta hanyar tashin hankali ba, ba kuma ta hayaniya ba.

Alhaji yace "'Mu yi sallar magariba tukunna ko?" Hajiya ta ce, "Ni fa kawai a yita ta kare, ya saki *yar can mu kama gabanmu". Ta fada tare da nuna Salma.

Duk suka dubi gurin da Salman ta ke a tsugunne, sai lokacin Alhaji ya ga Salma din.

Hajiya ta ci gaba da fadin, "Ni fa duk wannan abin lafiyarsa ni ke yi ma wa, ku ba za ku fahimta bane an fada min cewa uwar yarinyar nan ta je ta kai sunan Shatima an tsaface shi don ya dinga kashe musu kudi.

An hada asirin da yawun bakinta, an yi surkulle an ba shi ya ci. Kuma asirin ya ci shi domin ga shi yanzu duka yaushe aka yi auren ma ya sa ta a makaranta mai tsadar gaske, kullum sai ya ba ta dubu da dari biyar.

Ita na haifar ma shi kenan?" Salma ta fashe da sabon kuka tana fadin. "Na rantse da Allah Hajiya, Innarmu ba ta zuwa gurin masu asiri.

Ko Babanmu da yake da ciwon Barin jiki cewa tayi yi kar a kai shi grin masu maganin gargajiya ciwonshi na asibiti ne kar su bata masa jinya su ce wani ne ya yi masa asiri. Allah na rantse ba mu taba yi wa Yaya asiri ba.

Allah ma ba zai barmu ba, domin shi taimakonmu ya yi. Na sani ban kai Yaya Shatima ya aure ni ba, mu tsoro ma muka ji da ya ce shi zai aure ni. Ga ma Yaya din a tambaye shi, ko ruwan gidanmu bai taba sha ba bare har ma mu ba shi nama ya ci"

Ta saki ajiyar zuciya, sannan ta karasa maganar a hankali, Ko yanzun da nike matarshi bai ci abincina ya kai sau goma ba. Cewa yake ni ban iya girki ba"

Ta jero shesshekar kuka a tare, sannan ta ci gaba da gunjin kuka.Alhaji ya kalli Hajiya, To ke da ki ka ce an fada miki, wane ne ya fada miki din?"

"Hajiya Azumi ta yo min tambaya a gurin malamai, kuma ta ce guri biyu ta je duk bakinsu daya, Alhaji ya kalli Alhaji Musa ya ce, "Ka ji ko?

Imaninta ta saida a gurin makaryatan bokaye. To da izinin wa ki ka je?" Ta zaro ido cikin firgici, ta ce,

"A'a Alhaji, Niba zuwa nayi ba. Ina fada maka Hajiya Azumi na aika shatima ya amshe zancen da cewa,

Alhaji,kamar yanda Salma ta fada ne, ko ruwan gidansu ban taba sha ba. Hajiya ma da ta yarda da wanna karyar ta so ta yarda ne.

Domin ta fi kowa sanin yanayina domin ba kowane abu ni ke iya ci ba, kuma kudi da Hajiya take magana ina ba salma, ita ce ma ba ta samu gatansu ba, komai na sauran matana ya fi na Salma.

Gida da Hajiya ke magana haya ce na kama musu, ba siya na yi ba don ko alakar aure ba ta hada ni da 'yar suba ina yi musu.

Taimako irin wannan ban san adadin da na yi ba, Munnir ya san haka ba sai na zo na ce hajiya, ko Alhaji na taimaki wasu ba. Haka ko a hanya na sha kashe rigimar kudi da aljihuna in wucce Ba ina fada ba ne don alfahari ko gori ba, ina son a fahimce ni.

Maganar kudj wane magulmaci ne ya fada?"

Aliya ta ce, "Ai na sani kudin nama ne ka ke bata, mu kuma kana saka mana nama a fridge. Na fadama Hajiya"

Shatima ya kalli Alhaji,

"Ga su nan rago na dubu talatin-talatin nike siya musu su uku, kowacce a gyara a saka mata a fridge ga kaji guda goma-goma na wata daidai kenan, amma cikinsu na Amna ne kawai

ya kai watan. Su kafin haka nasu ya fare, ita ko Salma dubu daya a wata, dubu talatin, sannan bana sai mata kaza. In na siyo gasasshiya har da su nike saye. Haka kuma akwai kudin kati da nike saka musu duk sati, ita ko ko wayar ma ba ta mallaka ba bare kudin kati ya je mata

Shatima ya dubi Hajiya,

"Zancen makaranta kuwa,alkawari na dauka tsakanina da mahaliccina cewa, zan taimake ta tun kafin in yanke shawarar zan aure ta

Ya numfasa sannan ya kalli Mama,

"Akwai abin da ba ku sani ba. Babu son Salma ko digo a cikin zuciyata, so na soyayya dai sam babu wannan. Na auri salma ne don in taimaki rayuwarta ta yi karatu. Ta so in aura mata wani ne, in mata kayan daki don ta cika burin Babanta.

Ni kuma na aure ta don ta cika duk burikan guda biyu ne. Zan iya zama da Salma har karshen rayuwarmu, in kuma da zuri'a a tsakaninmu har mu samu rabo, ba zanyi Ki ba. Amma ba don so ba.

In kuma tana bukatar rabuwa da ni yayin da burinta ya cika, zan iya sahale mata ta je ta auri wanda ta ke so, yake sonta.

Ban fadi haka don cin fuska ga Salma ba, sai don hakan shine gaskiya, kuma Hajiya ta gane cewa,Salma ba su yi min asiri ba salma kanta a sunkuye wasu zafafan hawaye ke zuba a idanunta masu radadi.

Tun da aka soma rigimar bata tsinci kanta cikin bakin cikin da ya kai na yanzun nan ba. Kalaman Shatima sun yi tsauri, kuma sun yima zuciyarta daci, sannan sun yi ma kwakwalwarta nauyi.

Har ma ta ji da ma ya bi umarnin mahaifiyarsa ya sake ta din zai fiye mata jin wadannan munanan kalaman da suka fito daga bakinsa.

Ta soma rainon zuciyarta, har ta soma koyon sonshi, da tantance su.

PREVIOUS: Rana Daya Book 3 Chapter 1 

Post a Comment

0 Comments