Kanwar Maza Hausa Novel
Page 1: Daji Ajiyar Allah! La'asar sakaliya, a lokacin da hasken
rana ya fara disashewa, ta doshi yamma za ta faɗi, duhun magariba na ƙoƙarin
shigowa ya maye ragowar hasken da ranar ta bari kan ta ƙarasa faɗuwa.
Gamayyar bishiyoyi ne, dogaye da da madaidaita, haÉ—e
da ciyayi da ga mabanbantan tushe, suka haɗu suka yiwa dajin ƙawanya.
Zai iya kasancewa abin sha'awa ga wanda ya zo yawon buÉ—e ido, idan har
bai san mai dajin ya ƙunsa ba.
Ga wanda ya san abin da ya ƙunsa kuwa, zai kasance wuri mafi razani,
firgici da kuma tashin hankali.
Gudu take yi a tsakanin rayuwa da mutuwa, tana rungume da
wani zani a ƙirjinta, babu yadda za ayi daga nesa ka gane me ta rungumo
haka take wannan uban gudun.
Ƙafafuwanta babu takalmi, jikinta babu mayafi, duk da yanayin
garin babu zafi, amma laɓɓanta sun bushe tamkar dutsen da ya
shekara ruwa bai zuba a kansa ba, babu alamar tana gane in da take jefa ƙafarta.
Duk da wannan mawuyacin hali da take ciki, ta bawa abin da take rungume da shi
muhimmanci sosai da sosai.
Cikin rashin sani, tayi karo da wani abu da ita kanta ba ta
kai ga tantance ko meye ba, sai dai ƙarfi da nauyin abun ya sanya ta faɗi
ƙasa,
take ta saki wani marayan kuka, a lokacin da jini ya fara zuba daga ƙeyarta.
Sai a lokacin abin da take rungume da shi ya tsala kuka,
saboda firgitar da ya yi shima.
Jariri ne ɗanyen goyo, cibinsa ko faɗuwa bai yi ba, jikinsa duk busashshen ƙazantar haihuwa da alama yaron ya kwan biyu, amma ko ruwa bai taɓa gani ba balle a wanke wannan ƙazantar!.
*************
Cikin garin Kano, unguwar ɗorayi tinga, misalin ƙarfe
huÉ—u
na yammacin ranar Alhamis, wani matsakaicin gida ne, cikin rukunin gidajen dake
É—an
ƙaramin
layin, kallo ɗaya zaka yi wa gidajen, ka san na masu ƙaramin
ƙarfi
ne, duba da yanayin kwatoci da kuma kasancewar gidajen awon igiya, ba magudanan
ruwa, babu layuka masu kyau, kowa da in da fuskar gidansa ta kalla, haka zalika
kowa in da ya ga dama yake sako kwatar gidansa, wasu da gyara wasu babu, ga
gidajen 'yan ƙanana tamkar wani zai hau kan wani.
"Wai ba zaki fito ki je mini aiken ba, har sai gawayin
ya ƙare
tukuna?" Cewar wata matashiyar dattijuwa, da take zaune a gaban kurfoti,
hannunta riƙe da mafici tana firfitawa, gefe ga farantin silba ɗauke
da garin tuwon masara a kai.
Wata yarinya ce ta fito daga wani É—akin
da yake bayan matar, hannunta ɗaya riƙe da hijjabinta, ɗaya kuma sai
matsar hawaye take yi.
Matar ta kalleta ta ce "Kukan me ki ke
yi?"
Aikuwa kamar mai jiran ƙiris, cikin sangarta yarinyar ta ce
"Ba Huzaifa bane ba ya....
"Ni yi mini shiru, haka dai kuka iya faÉ—a
kamar kuna ganin hanjin junanku, idan na hana ki zuwa in da yake ai ba zaki
hanu ba, maza ki É—au kuÉ—in nan ki je mini gidan Laure, ta baki
kuka ta sittin, daddawa ta arba'in sai manja na naira É—ari ki kawo mini
canjin, na yi maza in kaÉ—a miyar nan kan magariba".
Kwaɓe fuska yarinyar ta yi ta ce "Wai
yau ma miyar kuka za ayi Innalillahi wa innalillahi raji'un"
Baki buÉ—e ta bi Yarinyar da kallo, cikin hasala
ta ce "Idan na kaÉ—a kukar kar ki sha, zaki É—au
kuÉ—in
ki fita ko sai na yi fatali da kanki a wurin?"
Ta durƙusa ta ɗau kuɗin, ta zura hijjabinta ta nufi hanyar
fita, a ranta tana jin gara ace yau babu abin da zasu ci, da wannan tuwon kamar
na ibada.
Cike da kashedi matar ta ce "Idan kin ga dama kuma ki
je ki zauna, kar ki yi sauri kiga yadda zan yi da ke, ko ki biyewa yara ki
tsaya shashanci a hanya"
Ba to ko waiwayo ba, ta yi gaba abinta tana kalle-kalle.
Gidansu ƙawarta Habiba ta fara biyawa, ta tarar
da maman Habiba a tsakar gida ana yi mata kitso, ta durƙusa ta gaida
Maman Habiba, sannan ta ce mata wurin Habiba ta zo.
Habiba ta fito daga ɗakinsu tana kallonta tana murmushi, ta ƙaraso
in da take tsaye ta ce "Ruma ina zuwa ne?"
Cikin muryar RaÉ—a Ruma ta ce "Dan Allah Habiba aron
tayar Sani zaki bani, Mama ce ta aikeni so nake nayi sauri na je na dawo".
Habiba ta ce "Kaii, Ruma kin san Sani yafi kashi É—oyi,
kar na baki ki je ki salwantar da ita, daga ni har ke mu shiga uku".
Ruma cikin ƙwarin gwiwa ta ce "Wallahi ba zata
salwanta ba, ke dai ki aramini, so nake na yi gudu na ne na dawo".
Habiba ta ja Ruma soron gidansu, ta duba saman kejin kajin
da ke cikin É—an tsukakken zauren gidan, ta É—aukowa Ruma tayar Sani ta bata ta ce
"Dan Allah Ruma ki kula, kar wani abu ya samu tayar nan, ki yi maza mi
garata ki je ki dawo"
Ruma tayi murmushi ta ce "Kar ki damu, yanzu zan fyalla
naje na dawo, ina son tayar nan ta sani dama ya bar mini, 'yar dandaɓasa
da ita, yanzu zaki ga naje na dawo".
Habiba tayi murmushi ta ce "To shikenan, yi sauri kafin
ya dawo".
Ruma ta dafe kan taya, ta garata ta dinga zura gudu ta
lunguna kamar wata namiji ba mace, ba ta tsaya da gara tayar ba har sai da ta
isa gidan Laure.
Ta yo sayayyarta ta gama, ta fito ta kuma garo taya zata
tafi gida, can ta hango wasu 'yan makarantar allonsu, a ƙofar gidan Hanne
mai markaÉ—e suna 'yanta, ba tare da ta tuna da kashedin Mama ba, ta
ajiye kayan aiken da canjin haÉ—i da tayar da ta aro, ta shiga aka hau
'yanta da ita.
Kasancewar ƙwararriya ce a harkar shagala da iya
rinto, nan da nan wasa ya É—au zafi, ganin tana ta cinyesu a 'yantar
ta hanyar rinto, sai wasa ya koma faÉ—a, daga nan aka hau dambe, a wurin Ruma
ta kifar wa da wata markaɗenta ga ta da ƙarfi kamar doki.
Da ƙyar
wani mutum ya raba faÉ—an, Ruma ta haÉ—a yaran mutane
ta zane musu jiki, sai da mutumin yayi mata barazanar zai gayawa yayanta,
sannan ta haƙura da damben.
Yarinyar da suka yi damben, ganin an musu asarar markaÉ—e,
an kifar ga duka, ya sanya ita da ƙannenta suka fasawa Ruma Manjan da ta
sayo wa Mama, suka kwashe canjin aiken, suka farke ledar aiken suka gudu,
daddawar ma sai da ƙyar ta tsinto wasu, an fasa ledar kuka duk ta watse.
Ta kwashi sauran kayan, ta tafi gida, tana tafe tana tunanin
wace ƙaryar za ta jirgawa Mama, dan ta kaucewa faɗanta,
dan a duniya ba ta son faÉ—an Mama, gefe guda kuma tana tunanin
irin dukan da zata naÉ—awa Safiya idan suka haÉ—u
a makaranta allo, saboda abin da suka yi mta.
Lokacin da Ruma ta isa gida tuni an fara kiraye-kirayen
sallar magariba, domin wasu masallatan har sun tayar, sai a lokacin ta sake
shan jinin jikinta, tsoro ya ziyarce ta.
A soro ta rakuɓe tana leƙa cikin gidan, ta hango Mama a gindin
rariya tana alwala, Mama ta É—aga ido tayi mata kallo É—aya,
ta mayar da kai ta cigaba da alwalarta.
Cikin sanÉ—a Ruma ta shiga tana satar kallon Mama,
ta ji mai Maman za tace mata, amma ta ji ba tace mata komai ba.
Ta lallaɓa ta ajiye abin da yayi saura na aiken,
ita ma ta faÉ—a banÉ—aki tayi alwala.
Ta lallaɓo falo, ta tsaya a bayan Mama ta tayar
da sallar ita ma.
Mama ta idar, ta tashi ta fita tsakar gida, ta duba abin da
Ruma ta kawo mata na aiken, taga irin aika aikar da Ruman ta yo.
Ta dawo falon tana jiran Ruma ta idar da salla ta dirar amata,
amma Ruma ta ƙi idarwa, ta hau nafifilin babu gaira babu dalili, matar da
wataran sallar ma sai Mama ta haÉ—a .mata da duka take yi, amma yau sai
gashi har da nafila.
Can da Mama taga abin nata bana ƙare bane ba,
sallar taƙi ƙarewa, ta damƙo wuyanta ta baya ta zaunar da ita, ta
kalleta cikin haÉ—e fuska ta ce "Gidan uban wa ki ka je dana aike ki?"
Cikin tsoro Ruma ta girgiza kai ta ce "Ba ko ina
Mama"
"Ƙarya kike yi, zaki gaya mini ko sai na
murÉ—e
miki wuya, tun la'asar na aike ki amma sai magariba kika shigo mini, gidan uban
wa kika je?"
Cikin zazzare ido Ruma take jujjya kai tana rantse-rantsen
rashin gaskiya, "Wallahi Mama ban je ko ina ba"
Cikin tsananin Fushi, Mama ta ce "Ba zaki gaya mini
ba!"
"Mama wallahi dagaske nake"
"Assalamu alaikum" aka yi sallama a tsakar gida.
Mama ta amsa sallamar tana huci, wani matashin saurayi ne ya
shigo É—akin, yana faÉ—in Mama na dawo".
Mama ta ce "Sannu da zuwa"
Ya amsa da yauwa, ya dubi Mama dake tsaye a kan Ruma, Ruma
sai wulƙita ido take, kamar ta zagi sarki.
"Mama meyafaru ne?" Yayi Maganar yana son jin
ba'asi.
Cikin É—acin rai Mama ta ce "Saboda tsabar
iskanci na yarinyar nan, nan da gidan Laure, ta je ta sayo mini kayan miya, tun
bayan la'asar sai yanzu ta shigo mini gida, babu aiken babu dalilinsa, kuma
babu canjina, nayi-nayi ta gaya mini in da ta tsaya amma taƙi
faÉ—a
sai rantse-rantse take yi".
Ya kalli Ruma ya ce "Ba zaki faÉ—i inda kika
tsaya ba, kuma ina canjin? Ko zuwa ki ka yi ki ka kashe mata kuÉ—i
tunda kin saba"
Cikin tsiwa da rashin kunya, Ruma ta ce "Ban sani ba,
kai kuma waye ya saka da kai, zaƙin zaƙafere mai gida feraye kabewa, ai ba da
kai ake yi.....
Kan ta ƙarasa Mama ta rufe bakin nata da duka,
da sai da tayi zaton bakinta ya fashe.
Ja da baya tayi da sauri, ta dafe bakinta tana yarfe hannu,
saboda ta ji zafin dukan nan sosai da sosai.
Ya jinjina kai ya ce "Mama ƙyaleta, ba dai
bata da kunya ba, kar ki wahalar da kanki, ki bari mai sunan Baba ko Haidar su
shigo, sai su tuhumar miki ita".
Jin abin da ya faÉ—a ya sanya Ruma ta yi wata irin zabura,
ta ce "wallahi Mama gaskiya na gaya miki, dan girman Allah kar ki gaya
musu, canjin ne suka zube a hanya, na faɗi ƙasa man jan ya fashe dan Allah kar ki
gaya musu".
"Wallahi Mama ƙarya take yi, kin san dai ƙaryarta
ba ta salla, ki tuhumeta bari mai sunan Baban ya dawo zaki ci ubanki".
Cike da gamsuwa Mama ta ce "Ai hakan za ayi tun da ba
ta da mutunci"
Ya fakaici idon Mama ya yiwa Ruma gwalo.
"Mama kin ganshi ko yana mini dariya, dan Allah kiyi haƙuri"
Banza Mama tayi da ita, ta bawa Huzaifa kuÉ—i
ya kuma yi mata wani cefanen.
Rumaisa ta koma gefe tayi tagumi, zuciyarta na ta zullumin
halin da zata iya shiga, idan har aka sanarwa da Mai sunan Baba ko Haidar abin
da ta yi, gashi ko giyar wake ta sha ta san ba zata iya gayawa Mama haƙiƙanin
abin da ya faru ba.
Salati kawai take yi, tana roƙon Allah ya rufa mata asiri, kar Mama ta
gaya musu, ƙasan zuciyarta kuma tana yi wa Huzaifa Allah ya isa da ya bawa
Mama shawarar ta haÉ—ata da su Haidar.
Ta na tsaka da tunanin, ta jiyo Mama da Huzaifa suna hirarsu
a tsakar gida, kamar ba ita ta gama faÉ—a ba.
Suna yi mama tana ƙarasa aikin miyarta.
Sallama aka yi a tsakar gida, Ruma ta rikice, dan kusan
muryoyinsu duk kusan iri É—aya ne, ta É—an nutsu ne da
ta tuna mai sallamar muryarsa ba ta kai ta su Haidar fashewa ba, kuma shi dama
sanyin hali ne da shi.
Jiyo Mama tayi tana faÉ—in "Fodiyo, an dawo"
"Eh Mama, ya gidan?"
"Alhamdilillah, sannu ka je ka watsa ruwa kafin nan na
gama miya"
Usman da Mama ke kira da Fodiyo ya ce "To Mama, ga
wannan" yayi maganar yana ajiye mata leda.
Miƙewa Ruma tayi tana leƙa
window, tana son gane me ye a cikin ledar da Fodiyo ya kawo.
A ranta ta ce "Allah ya sa kifi ya kawo, idan kifi ne a
bani kasona, dan idan aka saka a wannan baƙar miyar ban sha.
Ba ta kai ga gano meye a ledar ba, idanunta suka sauka a
cikin na dodonta, da ya shigo gidan ko sallama bai yi ba, gani tayi tamkar yayi
mata wani irin mugun kallo, ko dan dai a tsorace take ne oho.
Mai sunan Baban Mama kenan, Umar faruk.
Cikin takunsa na ƙasaita ya ƙaraso tsakiyar tsakar gidan, sannan ya
yi sallama.
Hannu Ruma ta ɗora a ka, muryarta ƙasa_ƙasa
ta ce "Na shiga uku, yau kashina ya bushe ƙayau idan ya san me nayi".
Tun daga sallamar da ya yi, bai cewa kowa komai ba, shi ma
ya ajiyewa Mama ledar da ke nasa hannunsa, ya wuce É—akinsu.
Bai jima ba ya fito tsakar gida, ya É—au buta zai yi
alwala.
Ruma ce ta fito kamar munafuka, ta É—an risuna ta ce
"Yaya Faruk sannu da zuwa"
ÆŠaga ido ya yi ya kalleta, bai amsa ba ya mayar da kansa ya
cigaba da alwala.
Cikinta ya É—uri ruwa, ta É—au tsintsiya ta
tafi falon Mama ta hau shara a daren, kai da gani ka san sharar ba ta domin
Allah bace ba.
Huzaifa ya faki Idon Mama ya bi Rumaisa falon, ya dinga leƙata
yana tuntsura mata dariya.
Ba dan tana cikin yanayi na tashin hankali ba, babu abin da
zai hana su kafsa faÉ—a da Huzaifa a daren nan, amma ta san
biyewa Huzaifa su yi faÉ—a alhalin Faruk yana gidan nan, wata
babbar matsalar ce, mai zaman kanta, dan ƙarshe sai tayi kuka.
"Ba zaki fito ki É—ebi Abinci ki ci ba?" Mama tayi
maganar cikin É—aga murya, yadda za ta jiyota.
Daga ɗaki Ruma ta ce 'Mama na ƙoshi"
A ƙufule Mama ta ce "To uban me ki ka
ajiye da zaki ci, ba zaki fito ki ci Abinci ba?"
Ruma ta É—an tura baki tayi shiru.
Usman ya ce "Ai kin san kin yi maƙiyin
nata tuwo, mussaman miyar kuka da ma wata miyar ce ba wannan ba, ƙila
ta ci"
Mama ta ce "Abin da nake da shi ba shi zan dafa na bata
ba, zan fasa girki ne dan ba ta cin tuwon?".
Cikin kakkausar muryarsa Umar ya ce "Ki ƙyaleta,
tun da a cikinta zata zuba, ta kwana da yunwa mana".
Mama ta gyaÉ—a kai ta ce "Ai shikenan"
Muryarsa kawai da ta jiyo, sai da ta sake shiga cikin tashin
hankali, tsananta addurta ta yi, a kan Allah ya rufa mata asiri kar Mama ta
gaya masa ta yi mata laifi.
'yan mazan nan suka kewaye Mama, suna ta hira kowa da abin
da yake ce mata, banda mai sunan Baba, da yake duba wayarsa, ba tare da ya
tanka musu ba.
Jin suna ta hira, Mama ba ta gaya masa tayi laifi ba, ya
sanya take ta murna, tayi maza ta yi sallar isha'i ta shimfiÉ—a
katifar ta ta kwanta.
Ta cigaba da Addu'a a cikin zuciyarta.
"Assalamu alaikum" aka yi sallama a tsakar gidan.
Suka amsa baki É—aya, Suka zubawa yaran da suka shigo ido
mace da namiji.
Duk da akwai wutar lantarki da fari Mama ba ta gane yaran ba
sai daga baya.
Suka gaida Mama da su Umar, Mama ta kallesu ta ce
"Habiba ya aka yi me?"
Habiba ta ce "Ruma tana nan?"
Umar yayi caraf ya ce "Yaya aka yi?"
Kasancewar sa mutum mai tsanain kwarjini, sai da Habiba ta É—an
ruÉ—e
sannan ta ce "Dama É—azu ne da aka aiketa ta zo ta ce na bata
aron taya, zata jewa Mama aike, to tayar ta Sani ce, ta ce zata dawo da ita
kuma haryanzu shiru".
Mama cikin mamaki ta ce "Taya kuma?"
Habiba ta jinjina mata kai.
Gaba É—aya Ruma ta manta da ta je ta aro taya,
sai yanzu da ta ji maganar Habiba, dan tun da aka kwashi damben nan a nan ta
yasar da tayar ta yo gida.
ÆŠora hannu tayi a ka ta ce "Na shiga uku, Habiba shikenan
kin kasheni".
Mama ta ce "Kina ina zo nan, mara kan gado, babu yadda
ban yi dake ba a kan ki gaya mini in da kika tsaya, amma kika ce ke baki tsaya
ko ina ba, ashe yawon aron taya kika tafi ko, ko ina sai kin nuna hali ƘANWAR
MAZA, ina ke ina taya ban da hauka, zaki fito ki basu abarsu ko kuwa?"
Jikinta na tsuma ta fito ta tsaya daga bakin ƙofar
falon Mama, tana satar kallon Umar, amma taga kamar ma bai san me ake yi ba.
"Ma.m.maama.. wallahi dan nayi sauri ne, ya sanya na
aro tayar, kuma wallahi na manta na barota a wajen gidan Hanne mai markaÉ—e".
Mama ta riƙe haɓa kawai, tama rasa me zata ce gaba ɗaya.
Huzaifa ya ce "Wannan yarinyar idan kina da rabon yin
hankali Allah ya shiryeki, ina ke ina taya kina mace?"
Mama ta kalli in da Habiba take tsaye ita da ƙaninta
ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, tun da ta fita nima nake zaman
jiranta, ban aiketa ta je ta karɓi kayan kowa ba, da safe in Allah ya
yarda zan turata ta je ta dubo muku" Mama tayi ta basu haƙuri,
suka juya suka tafi.
Mama ta zauna ta dasa mita, ta in da ta shiga ba ta nan take
fita ba, su Usman na tayata, ita kuwa Ruma da ta san ba ta da gaskiya, sai ta ƙule
a kan katifarta, zuciyarta sai bugawa take tana jiran jin me Yaya Umar zai ce,
amma shiru bai ce komai ba.
Har suka watse daga tsakar gida, Mama ta shigo É—akin,
ta sameta ta rufe ido tana baccin ƙarya, still Mama ta cigaba da mita, sai
da Ruma ta ji kamar ta tashi ta barwa Mama ɗakin ta huta, saboda Mama mitarta ba ta ƙarewa
sam, gefe guda tana yiwa Allah godiya da Dodonta bai yi magana ba.
Wani irin bacci ne mai daÉ—in gaske yayi awon gaba da ita. A cikin
baccin nata babu zato babu tsammani sai ji tayi an yi sama da ita da hannu É—aya.
"Wayyo Allana, Innalillahi wa innalillahi raji'un,
warin hannuna na hagu zai karye Mama!" Sai da ya dungurar da ita a tsakar
gida, suka yi ido huÉ—u, ta ga wanda yayi mata wannan aikin.
Jikinta ne ya hau kyarma, dan idonsa kawai idan ransa a É“ace
yake abin tsoro ne.
A ƙasan zuciyarta ta ce 'Shikenan tawa ta ƙare, Allah ya sa na cika da kyau da imani!.
Kanwar Maza Hausa Novel Page 2
Kasa É—auke idanunta tayi daga kallonsa, saboda
azabar firgici da razanar da ta yi.
Ya janyo kujera ya zauna a gabanta, ya É—an
ƙura
mata ido, sannan cikin kaushin murya ya ce "Gidan uban wa kika tafi da ta
aikeki, tun la'asar ba ki dawo ba sai magariba?" Yayi Maganar yana tsareta
da ido.
Kasancewar akwai wutar lantarki, ya sanya fes take kallon
fuskarsa da idonsa.
"Ba magana nake yi miki ba, ki ka tsare ni da
ido?" Ya daka mata tsawa.
Zabura tayi ta yinƙura za ta yi magana,amma ya sake cewa
"Kuma wallahi kika yi mini ƙarya sai na ci ubanki a daren nan"
Jiki na rawa ta fara zayyane masa yadda aka yi tun bayan
fitarta.
Huzaifa tun da yaga Yaya Umar ya shiga É—akin
Mama ya jiyo kukan Rumaisa, ya sha jinin jikinsa, dan ya san yau sai yadda
Allah ya yi.
Mama kuwa girgiza kai kawai ta yi, jin Yadda Ruma take faÉ—ar
gaskiya saɓanin ɗazu da ta yi mata ƙarya.
Umar ya ce "Namiji ce ke da zaki tafi aron taya?"
Ta sunkuyar da kai tayi shiru.
"Kuma me nace miki a kan dambe a hanya, karya ce
ke?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Ya É—ora da cewa "Wato ke duk wani abu
da za'a gaya miki sai dai ya shiga ta kunnenki na dama, ya fita ta hagu
ko?"
Ita dai tayi shiru tana rarraba ido.
"Kyaci ubanki, tashi ki kama kunnenki tun da ba zaki yi
hankali ba".
Maraicewa tayi zata fara yi masa magiya, amma da yayi mata
wani mugun kallo, ba shiri ta miƙe ta durƙusa ta hau kamun kunne.
Gaba É—aya Huzaifa ji yayi bai ji daÉ—i
ba, maimakon a hukuntata tun a lokacin amma sai da aka bari ta fara bacci, za a
sakata kamun kunne, ya tsaya ta ƙofa yana leƙen tsakar gidan
ya san yanzu zata galabaita, gashi babu wanda ya isa ya hana Yaya Umar abin da
yayi niyya sai Hassan É—in sa wato Abubakar Sadik, shi kuma baya
nan.
Umar ya nutsu yana duba litattafansa, Rumaisa kuwa sai tangaÉ—i
take tana neman ta faÉ—i, amma yayi banza da ita, dan ta san
idan ta faÉ—i ko ta tashi ba zata iya É—aukar wani hukuncin ba.
Tun tana kuka ƙasa-ƙasa har ta fara yi da ƙarfi,
saboda azabar gajiyar da ta yi.
"Tashi" ya faÉ—a ba tare da ya kalleta ba. Ta É—ago
duk ta haÉ—a uban gumi, ga hawaye da majina duk a fuskarta.
"Kukan uban me kike yi?"
Cikin kuka ta ce 'Yaya na gaji ne, dan Allah kayi haƙuri
ba zan sake ba, na tuba"
"Da alama haryanzu baki yi laushi ba, yi zaman babur
tun da kin gaji da kamun kunne"
Babu kalar izayar da Yaya Umar bai yi mata ba a daren, har
Sai da Mama ta ji babu daÉ—i a ranta, amma tuna cewar yarinyar ba
'yar goyo bace ba, ya sanya tayi banza ta cigaba da laziminta.
Aliyu ne ya fito daga É—akinsu, cikin damuwa ya ce "Dan
Allah Yaya kayi haƙuri ka ƙyaleta haka ta je ta kwanta dare yayi,
wallahi ta horu, kuma ga gobe in Allah ya kaimu da makaranta".
A fusace Umar ya kalleshi ya ce "Ka É“ace
mini daga gabana ko sai na haɗa da kai?" Ran Aliyu ba ƙaramin
É“aci
yayi ba, kawai ya girgiza kai ya shiga banÉ—aki.
Sai da ya tabbatar da ta galabaita sannan ya ce ta zauna ta
huta, shi kuma ya tashi ya fita.
Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, saboda jin cinyoyinta
take kamar babu nama a cikinsu sai rodi, saboda azabar sagewa da suka yi, ƙashin
bayanta ma ban da azabar ciwo babu abin da yake yi mata.
Yaya Umar na fita, Huzaifa ya ƙaraso in da take yana mata sannu cikin
tausayawa kamar ba shi ne ya gama bawa Mama shawarar ta haÉ—ata
da Yaya Umar ba.
Ya je ya ɗebo ruwa ya bata, ta karɓa
ta kafa kai tana sha tana kuka. Ta gama sha, ya karɓi kofin ya ajiye
yana goge mata hawayen fuskarta.
"Uban me kake a nan wurin?" Basu ji dawowar Yaya
Umar ba, sai maganarsa kawai suka ji, suka yi tsuru-tsuru.
"Zaka tashi ko sai na haÉ—a da kai?" Jiki na rawa Huzaifa ya
tashi, ya koma É—akinsu.
Ya kalli Ruma da ke ta ajiyar zuciya, ya tabbatar ta
galabaita, ya san yanzu haka jikinta na ciwo, ya jefa mata leda a jikinta ya ce
"Maza É—auki ki shanye"
Jiki na rawa ta É—au ledar, doguwar jarka ce cike da
youghurt mai sanyi a ciki, ta É—aga kai ta sha rabi, yana tsaye yana
kallonta, ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Na ƙoshi".
Jin bai ce komai ba ne ya sanya ta É—ago ta kalleshi,
ganin yana mata wani irin kallo ne, ya sanya ta cigaba da sha tana yamutsa
fuska, da ƙyar ta shanye, ta ajiye robar tana jiran umarni na gaba.
"wuce ki je ki kwanta"
Da ƙyar da yinƙura ta tashi, ƙafafuwanta na ta
rawa saboda ciwo, ta shiga É—aki.
Tana shiga ta tarar da Mama na salla, ta faÉ—a
kan katifa tana kuka.
Mama har ta idar da sallar ba tace mata komai ba, ta cigaba
da kukanta har bacci ya É—auke ta.
Cikin bacci ta ji Mama na É—ala mata duka a cinyarta "Tashi"
duk da yadda ta ji zafin dukan, amma ta buÉ—e idonta a hankali ta kalli Mama, ba
tare da ta ce komai ba.
"Saboda tsabar rashin hankali, ki kwanta ki yi fitsari
a kwance, ke ba jaririya ba ba 'yar yaye ba" jin abin da Mama ta faÉ—a
ne ya sanya ta miƙe zumbur, ta ganta luntsum a cikin fitsari.
Waro ido ta yi ta ce "Na shiga uku, wallahi na zata a
mafarki ne, dan Allah kiyi haƙuri"
Mama cikin É“acin rai ta girgiza kai ta ce
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, zaki tashi ki fita kije ki gyara
jikinki ko kuwa?"
Sannu a hankali ta sauka daga kan katifar, saboda yadda
jikinta ko ina yake yi mata ciwo, saboda punishment É—in da Yaya Umar
ya sanya ta.
Da ta fita tsakar gida da rarrafe ta ƙarasa banɗaki,
ta wanke jikinta ta dawo ta canza kaya, ta jingine katifar tayi kwanciyarta a ƙasa.
Har ga Allah, tana jin yadda fitsarin ya matseta, amma ta ji
gandar tashi, saboda bacci take ji sosai, ga kuma ciwo da jikinta yake yi, dan
haka ta cigaba da baccinta, da ta ganta a banÉ—aki ta zaci a gaskene ta saki
fitsarinta.
Tana jin yadda Mama ke ta mita, amma ita ko a jikinta, wani
nannauyan baccin ne ma yayi awon gaba da ita.
Da Asuba ma an kai ruwa rana kan Mama ta samu Rumaisa ta
tashi ta yi salla, dan sai da ta yi iƙirarin haɗata da Yaya Umar sannan ta tashi ta yi
sallar.
Ta idar da salla Mama tayi mata maganar shirin makaranta,
amma ta tura baki ta ce "Ai kina gani jiya mai sunan Baba yana azabtar da
ni baki hana shi, ni bani da lafiya, ba zani ba cinyata kamar an mini É—orin
karaya haka nake ji na"
Mama ta yi mata shiru ta cigaba da laziminta, Huzaifa ne ya
fara shigowa É—akin Mama ya gaisheta, suka gaisa ya tambayi Mama mai za'a É—ora
na karin kumallo?.
Mama ta ce "Bari gari yayi haske, sai a sayo gasara, ka
cewa Yasir ya feraye maka dankali, sai a soya"
Huzaifa ya jinjina kai ya miƙe, har zai fita idonsa ya sauka a kan
katifar Rumaisa, ya É—an yi turus ya dubi Mama ya ce
"Mama ba dai fitsarin kwance yarinyar nan tayi ba?"
"Gashi kuwa kana gani, ai Yarinyar nan sai addu'a
kawai".
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, su Balama an yi
asarar kunnuwa, ba sai ki saka ta fitar miki da ita daga É—aki
ba, sai É—akin ya fara wari tukuna, abinka da fitsarin gardiya bana
jariri ba, tashi shashasha" ya ƙarasa maganar yana zuba wa Rumaisa duka
a ƙafa.
A gigice ta tashi zaune ta raba ido, tayi zaton Mama ce ta
daketa, amma taga Huzaifa a kanta.
"Me nayi maka zaka dakeni?" Tayi maganar a ƙule.
"An dake ki É—in, tashi ki fitar mata da wannan
katifar daga ɗaki, mai abin kunya ƙatuwa da ke kina fitsarin kwance"
"Ba zan fita da ita É—in ba, uban shishshigi ko ina ruwanka,
tun da ba a kan ka nayi ba, kuma ruwa ne ya zube ba fitsari nayi ba".
"Au Mama ƙarya take yi miki kenan, ba zaki tashi
ba?"
Cikin tsiwa ta ce "Ba zan tashi ba"
miƙa hannu yayi, ya janyota ya ɗagata,
ya ce "Wallahi sai kin fita da katifar nan kin wanke kayan da kika yi
tsiyar a kan su". Idan da sabo Mama ta saba da wannan halin nasu na faÉ—ace-faÉ—ace,
gashi Huzaifa ya bawa Rumaisa kusan shekaru shida, amma faÉ—a
kamar suna ganin hanjin junansu.
Mama ta sharesu ta ƙi ko kallon in da suke, Rumaisa ta dinga
turjewa tana kwarara ihu.
Basu yi aune ba suka ga Yaya Umar a tsakiyar É—akin,
take suka yi cirko-cirko suna kallonsa.
Cikin kaushin murya ya ce "Meye haka karnuka ne
ku?"
Suka girgiza kai a tare.
"Me kai mata take wannan ihun, da idon Mama bai sanya
kun daina ba?".
"Fitsari ta yi a kwance, shi ne nace ta fita da
kayan"
Cikin mamaki Umar ya kalleta ya ce "Fitsarin kwance
kuma? Kina me kika yi fitsari?"
Cikin rauni ta ce "Wallahi Yaya tsautsayi ne, kasa
tashi nayi"
"Tsautsayin uban wa? Kwashe kayan ki fita ki wanke ƙazamar
banza kawai".
Haka ta ja katifar ta fita da ita tsakar gida, ta kwaso
kayan da ta yi wa fitsari ta hau wanki.
Huzaifa ya faki idon Yaya Umar ya dinga yi mata dariya.
Duk wanda ya fito tsakar gida ya ga katifar Rumaisa sai ya
ce me ya fito da katifar, Huzaifa sai yayi farat ya gaya musu ai fitsarin
kwance ta yi.
Tausayinta ne ya kama Usman, ganin yadda take kuka, kuma ba
ta saba yin fitsarin kwance ba, ya je ya karɓi kayan ya tayata.
Kowa da abin da yake faÉ—a a kan Ruma, wasu na mata Addu'a
shiriya wasu kuma na yi mata faÉ—a har da zagi.
Tamkar gidan 'yan mata, haka zaratan samarin nan suka kama
aikin gida, wasu na wanke-wanke, wasu shara da Abin karyawa, kan gari ya ƙarasa
haske, hatta ruwan da Rumaisa zata yi wanka, an dafa ta haÉ—a
ta yi wanka.
Haka suka jeru a tsakar gida, tare da Mama suna karyawa,
Rumaisa kuwa sai shan kunun take da ƙyar tana yamutsa fuska.
Can ta kalli Mama ta ce "Mama Kununa bai ji suga ba,
yayi tsami da yawa".
Haushi ya kama Mama ta ce "Amma a gabanki aka zazzage
sugan kowa ya ɗiba ko? Kuma kin san ya ƙare"
Ta ture kofin kunun ta ce "Nifa dama kunun nan gudawa
yake sani, gashi bai ji suga ba, ni cikina ma har ya fara ciwo"
Umar kawai ya girgiza kai, Rumaisa ba zata taɓa
zaman mintuna goma lafiya ba, ba tare da tayi abin da za a yi mata magana ba.
Haidar ya kalleta, ya zura hannu a Aljihunsa ya É—auko
É—ari
biyu ya bata ya ce "Jeki wurin Mamuda ya baki buredi da suga, akwai ruwan
zafi sai ki haÉ—a shayi ki sha"
Washe baki tayi, ta ce "Allah dai ya biya da aljanna,
gadanga na Mama" ta É—au kofin kununta ta turawa Mama kunun ta
ce "Mama ki shanye kunun na bar miki" tayi waje.
***
Da ƙyar ta ƙarasa makaranta yau, saboda ciwon
cinyoyi da take yi, sakamakon horon da Yaya Umar ya bata a daren jiya.
"Ruma hatsari kika yi ne?" Cewar wata matashiyar
yarinya sa'ar Ruman, gannin yadda take tafiya da ƙyar.
Ta haÉ—e rai ta ce "Me kika gani?"
"Gani nayi kina tafiya da ƙyar, kamar wadda
ta warke daga karaya"
Cikin gatse Ruma ta ce "Eh, tirela ce tabi ta kaina, da
ta wuce na taso na taho"
"A'a Allah ya baki haƙuri"
Duk da yadda jikinta babu daÉ—i, hakan bai hanata faÉ—ace-faÉ—ace
da neman rigima ba, dan idan ba tayi hakan ba ace lafiyarta ƙalau
ba.
Bayan an tashi ba ta tsaya ko ina ba ta tafi gida, tana zuwa
ta tarar da katifarta a tsakar gida kamar yadda ta barta.
"Mama yanzu dan Allah a nan aka bar mini katifata, sai
anyi baƙi sun tambayi ba'asi ace fitsarin kwance nayi?"
"Au ba ke kika yi ba, ni nayi kenan?"
Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama ta ce
"Haba Mama, kema fa kin san tsautsayi ne, rabona da fitsarin kwance tun
ina jairiya, tun ban fi wata huÉ—u ba na daina fitsarin kwance" wani
irin kallo Mama tayi mata, jin uwar ƙaryar da ta saki.
Mama ta ce "Tashi ki cire Uniform, kiyi wanka ki zo
kiyi salla, ki tsefe wannan kan naki, ƙazamar banza da yake ban yi magana ba,
baki ga dama kin mayar da kai kin tsefe ba, kuma wallahi ya kai gobe in Allah
ya kaimu baki gama tsifar nan ba, sai na zaneki".
Hannu ta saka ta shafa kanta, ƙanann kitso ne a kanta, a ƙalla
guda arba'in da É—oriya, Mama ta bata kuÉ—i ta je ayi mata kitson hannu guda
biyar, saboda ba ta son tsifa, amma ta karɓi kuɗi a wurin Yaya Usman ta je aka yi mata ƙanana.
Ta san yau ko Mama zata kwaÉ—anta ta ta cinye ba zata iya gama wannan
tsifar ba, haka nan ta tashi ta je ta yi wanka, ta yi alwala ta saka wasu
kayan. Ganin Mama ta tada salla, ta leƙa Window ta ga Usman da sallaya a hannu
zai tafi masallacin juma'a, ta É—au hijjabinta ta bi bayansa.
Sai da ta fito ƙofar gida sannan ya kalleta ya ce "Ina
zaki?"
"Masallaci mana" ta bashi amsa.
"Kin tambayi Mama?"
Ta gyaÉ—a masa kai alamar eh.
Ya ce "Shikenan muje" ya sanyata a gaba suka tafi
masallaci.
Mama ta daÉ—e tana yiwa Rumaisa Addu'a bayan ta idar
da salla, kullum cikin Addu'a take yi mata, amma tana girma tamkar ana sake
turata, ko alamar hankali babu a tare da Rumaisa.
Da suka dawo daga masallaci tana kallon Rumaisa, ba ta ce
mata uffan ba, Rumaisa sai raragefe take yi, tana sauraron ko Mama zata yi mata
magana amma taga ta shareta.
Ba tare da ta yi tsifar ba, ta ci Abincin ranarta tare da
Yaya Aliyu, ya siyo kifi É—auri biyu, ya bawa Mama É—aya
ya ce gashi nan duka gidan, É—auri É—aya kuma suka ci shi da Rumaisa.
Bayan sallar la'asar, ta É—au allonta ta tafi makarantar allo.
Tana zuwa Habiba ta tare ta da harara, tare da sheda mata
cewar Sani ya ce sai ya yi mata dukan tsiya, idan ba ta biya shi tayarsa ba.
Tsaki Rumaisa tayi ta ce "To, ya kasheni ya huta mana,
tayar banza da ta wofi, shi bai san tsautsayi ba"
A ƙufule Habiba ta ce "Au hakama zaki
ce? Ki zo girma da arziki na ara miki tayar, amma ki je ki É“atar
ko a jikinki?"
"To tayar da kuÉ—i ya saya? Idan da kuÉ—i
ya saya ya faÉ—i kuÉ—inta, yayyena su biya shi"
Habiba da ta gama fusata ta ce "Dalla can, uwar meye a
gidan naku, banda gayyar maza da tsiya, sai ka ce wata uwar kuka ajiye, har
kike a faÉ—i kuÉ—in tayar a biya"
"Ku kun ajiye wata uwar É—in ne, da kuna da wani abun ai babarku
ba zata sayar da fanke da safe ba" Tayi maganar tana murguÉ—a
baki.
Cikin rawar murya Habiba ta ce "Kar ki sake ki zagar
mana uwa"
"Ni ban zagi babarku ba, ni dai na san fanke take
sayarwa, fanken naku ma mai Shegiyar tsada, ƙanana kamar ƙuli-ƙuli,
dan ranar Yasir ya ce har kiyashi ya gani a cikin fanken" kan Rumaisa ta
rufe bakinta, tuni Habiba ta shaƙo hijjabinta, zata rufeta da duka.
Abinka dai mai nema a duhu, balle ya samu a sarari, nan
Rumaisa ta zage ƙwanji ta tabattarwa da Habiba ita ɗin ƘANWAR
MAZA ce.
Abin takaici da malami a gefe yana biyawa wasu allo suka harƙe
da dambe.
A fusace ya miƙe ya saka bulala ya zane musu jiki,
musamman Rumaisa, tsabar masifarta ya sanya baya son ta a ajinsa, kullum cikin
rigima take, ga allonta sai yayi wata ba tayi wani rubutun ba, ga daƙiƙanci
da surutu.
Idan da abin da Rumaisa ta tsana bai wuce duka ba, ta ji
zafin dukan bulalar da Malam Ashiru yayi mata ba kaÉ—an ba, dan haka
ta koma gefe tayi shiru tana kuka. Ta rasa meya sanya ya tsaneta haka.
Habiba kuwa da ƙawayenta, suka ƙudiri aniyar
idan aka tashi sai sun naÉ—awa Rumaisa duka saboda suna jin
haushinta suma, a kan damben da aka yi a ƙofar gidan mai markaɗe
ranar Alhamis, gashi ta zagi fanken babar ƙawarsu.
Ana tashi cike da takaicin dukan da Malam yayi musu, Rumaisa
ta É—au
allonta ta nufi gida, sai share hawaye take. Sai dai yau babu tsokana a hanya,
babu neman magana saboda bayanta sai raÉ—aÉ—i yake na dukan da malam yayi mata,
gashi ba ta warke daga ciwon jikin punishment É—in Yaya Umar ba.
Babu tsammani ta tarar da su Habiba a wani lungu suna jiran
isowarta.
Turus tayi tana binsu da kallo kamar ba ta sansu ba.
Babu ko ɗar ta cigaba da tafiya tana yinƙurin
ratse su ta wuce.
Shan gabanta Habiba ta yi ta ce "Ke kin isa ki tafi, ba
dai ni kika zaga ba, kika kuma zagi babarmu ba, wallahi yau sai kin gane
kuskurenki, kuma wallahi Sani ma ya ce sai kin biya shi tayarsa.
ÆŠaya daga cikin yaran ta ce "Ai wallahi yau sai kin daku,
haka nima ranar kika zubar mini da markaÉ—e, zaki gane baki da wayo".
Bin su Rumaisa take da ido, sai kurari suke amma an rasa
wadda zata kaiwa Rumaisa duka.
Sake yinƙurin wucewa tayi, amma Habiba ta janyo
Rumaisa ta baya, yaran suka fara kai mata duka.
Tayi kukan kura, ta É—aga allonta saukewa Habiba allonta a
fuska, wani uban ihu Habiba ta kurma, jin danshi a hancinta.
Tamkar namiji a filin dambe, haka Rumaisa ta zage ita kaÉ—ai
ta dinga dukan yaran nan, yadda ta dunƙule hannu tana kai naushi, kai ba ka ce
'ya mace bace.
Da ƙyar da siɗin goshi wani mutum ya rabasu, saboda
Rumaisa akwai taurin kai, zuciyarta a bushe ana rabasu tana cigaba da kai duka.
Ta É—au allonta ta nufi gida, tana ta huci, duk da dukan da tayi musu sai dai jikinta duk yayi tsami ita ma. Dama ga jikin nata babu daÉ—i ji Sai dai kash, tuni wasu daga cikin yayyen yaran maza suka samu labari, suka yi gaba zasu datse Rumaisa a hanya, su zaneta.
Kanwar Maza Hausa Novel Page 3
'yan matasan yaran maza sun girmi Rumaisa, kuma duk da haka ƙarfin
namiji da na mace ba É—aya bane ba.
Tana cikin tafiya ta ji ana ke!ke! Ta tsaya waiwaya ta ga da
wa ake.
tawagar yara ta gani sun nufota gadan-gadan, tana ganinsu ta
san masu dukanta ne, sam bata karaya ba, maimakon ta gudu sai ta durƙusa
ta fara kwasar duwatsu, ta shirya duk wanda ya kawo kai, sai ta ƙwale
masa kai da dutse.
Amma a haka sai da wasu daga cikin su suka cim mata.
Sani Yayan Habiba, ya na zuwa ya kwarfeta da ƙafarsa
ta faɗi ƙasa, wani danƙo ya ɗauko a aljihunsa, ya fara dukanta da
shi, duka take kai masa ko ta ina da allonta har ta samu ta tashi tsaye da ƙyar
a kan ƙafafuwanta.
Ta yi kukan kura ta kafa masa haƙora a kafaɗarsa,
tsananin azabar zafi ya sanya ya kurma wani uban ihu ya ja da baya, dan har ƙashinsa
ya ji haƙoram Ruma, sai ka ce mayya.
Ganin ta gigita Sani, wasu daga abokan nasa kuma suna fama
da raɗaɗin jifan da suka sha, ya sanya ta durƙusa ta ɗauki
takalminta da hijjabinta a hannu, ta tsula da gudun tsiya.
Rufa mata baya yaran suka yi, suna a taro ta, amma kamar walƙiya
haka take sheƙa da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba sai da ta kai filin ball ɗin
su Yaya Aliyu. Suna tsaka da ball, sai ratsa cikin ƙartin mazan nan
take sai gata a tsakiyar filin da maza ke uban gudu suna ball, ta cinma Aliyu a
tsakiyar filin ƙwallon ta rirriƙe shi.
Mamaki ne ya kama shi, ganin hijjabinta a hannu, kanta sai
hula idanunta duk sun yo waje, tana ta haki tana waige-waige.
Riƙeta yayi yana tanbayarta lafiya? Wasu
daga cikin abokansa suma suka tsaya suna tambayarta ko lafiya, amma taƙi
magana sai ajiyar zuciya take yi.
Aliyu ya ja ta gefe, ya sanya mata hijjabinta, ya kalleta a
tsanake ya ce 'Menene?" Shiru ta yi bata yi magana ba sai sauke numfashi
take.
Haushi ne ya fara kama shi ya ce "Dan ubanki menene, me
aka yi miki kika biyoni nan cikin maza?" Yayi mata maganar a hasale.
Fara gaya masa abin da ya faru tayi, kuka ya ƙwace
mata.
ÆŠan shiru yayi sannan ya ce "Amma ina fatan baki yi kukan
a gaban yaran ba?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Kin taimaki kanki, dan da kin yi musu kuka wallahi sai
na ƙara
miki".
Cikin shesheƙa ta ce "Ban yi ba"
Aliyu ya ce "Bari na canza kayana muje, É—aya
bayan É—aya ki rakani gidajensu sai naci uban yaran nan, dani suke
zancen"
Ya zaunar da ita a gefe, aka cigaba da tambayarsa meya sami
Rumaisa ya ce musu babu komai, su cigaba da ball É—in su, shi zai tafi.
Su Sani kuwa tun da Allah ya sanya Ruma ta É“ace
musu, suka haƙura da binta, amma suka yi alwashin sai sun kuma saka ranar da
zasu naÉ—a mata duka, dan tayi musu É“arna sosai.
Suna tafe a hanya, Aliyu ya ce "Ke amma ba a banza zan
je rama miki ba, sai idan ki yadda zaki wanke mini kayan ball É—ina
da takalmina".
Cikin hanzari ta ce "Eh na yadda, zan wanke maka"
ya ce "To shikenan"
Ya sakata a gaba har ƙofar gidan su Habiba, Aliyu ya aika yaro
yace a kira masa Sani.
Sani ya zata a cikin abokansa ne wani yake nemansa, yana ta
fama da kafaÉ—arsa saboda cizon da Rumaisa tayi masa, sai ka ce an sare shi
da manjagara a wurin ba haƙorin ɗan Adam ba, ga Habiba ita ma sai kuka
take, leɓe yayi suntum ya kusa haɗewa da hancinta, bakin yaƙi
rufuwa saboda dukan da ta sha da allo a fuska, sai da bakin ya fashe, banda
dukan da ta yi mata a ka da allon, da take jin tamkar an mata rawani da
tukunyar ƙarfe saboda nauyin da kanta zuwa fuskarta yayi mata, ba ta iya
banbance a wani sashi na fuskarta hancinta da bakinta suke.
Sani ne ya fito yana waige-waige, yana neman wanda ya aiko a
kirashi, Aliyu yayi caraf ya danƙe shi.
Zazzare ido Sani ya hau yi, Aliyu ya ce "Kai, kaine ka
tattaro abokan ka ka daki Ruma ko?"
Cikin fitsara Sani ya ce "Nima ƙanwata ta daka,
kuma ta É“atar mini da tayata".
"Kuma saboda kai mahaukaci ne, sai ka tattaro abokan ka
maza su daketa, saboda baka da tarbiyya ko? Meyasa ba ka bari ƙanwarta
ka ta rama da kanta ba?".
Fizge-fizge Sani ya fara, yana yiwa Aliyu rashin kunya,
aikuwa Aliyu ya dinga kifa masa mari, har sai da bakin Sani ya mutu, fuskarsa
duk tayi ja. Ya saka shi a gaba zuwa gidan abokansa da suka yi yinƙurin
dukan Rumaisa.
Duk da irin É“arnar da Ruman ta musu da duwatsu, hakan
bai hana Aliyu kama yaran É—aya bayan É—aya ya zane musu jikinsu ba, sannan ya
saka Ruma a gaba yana rarrashinta suka tafi gida.
Ko da suka je gida, yanayin Ruman Mama ta kalla ta ga kamar
ba ta da gaskiya, amma ta share ba ta kula ta ba, dan idan ta biye wa halin
Rumaisa kullum sai ta daketa.
Da daddare bayan sallar isha'i duk suna zaune a tsakar gida,
Rumaisa na ta tunanin me zata ci yau, dan yau ma maƙiyin na ta Mama
tayi, wato tuwo, Allah ya sani yau ba ta jin za ta iya cin wannan tuwon, gashi
haryanzu ranta a É“ace yake a kan abin da ya faru, dan marin da Yaya Aliyu ya
yiwa Sani bai gamsar da ita ba, ji take ba zata huce ba sai ta fasa masa kai,
ko ta hankaÉ—a shi kwata, ga kuma tuwon nan da Mama tayi ya
sake ƙara mata ɓacin rai.
Yasir ne yayi sallama, hannunsa riƙe da leda, duk
suka amsa masa, banda Rumaisa da ta yi zurfi a tunani.
In da Rumaisa take ya ƙarasa, ya jijjiga kanta ya ce "Ke
tunanin me kike?"
HaÉ—e rai ta yi ta ce "Meye kuma na
dakar mini kai?"
Yasir ya ce "To kwalba uwar sharri, ni ban dakar miki
kai ba"
Tsaki ta yi ta ce "Ai na saba in dai ƙarya
ce"
Dire mata baƙar ledar yayi a cinyarta, ya wuce ɗakinsu.
BuÉ—e ledar tayi ta kwance, gurasa ce fal ta
masu tsire a ciki.
Murmushi ta yi ta É—aga murya ta ce "Na gode rabin
ran"
Daga É—aki ya ce "Ko ba rabin rai ba, tun
da na baki abin duniya ba, uwar son zuciya"
Rumaisa ta ce "kai dai Allah yayi maka albarka, kamar
ka san ba son wannan tuwon nake ba, tunani kawai nake me zan ci? Wannan tuwon
ne yake toshe mini kai bana gane karatu sosai, Allah dai ya biyaka rabin raina
"
Murmushi Yasir yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Ya gama abin da yake ya fito tsakar gida, zamansa yayi
dai-dai da shigowar dodonsu, wato Yaya Umar.
Cikin muryarsa ta ƙasaita yayi sallama.
Duk suka amsa masa, ba tare da ya kula kowa ba, ya ajiyewa
Rumaisa leda da indomie ya ce "Tashi ki dafa mini" tabbas ba dan Mai
sunan Baba ne ba ba zata yi ba, ita a rayuwarta tana son ko aiki zaka sanyata,
ka lallaɓata shi kuwa mai sunan Baba bai san wannan ba, ya bada umarni
a bi kawai ya sani mutum ya ƙi kuma jikinsa ya gaya masa.
Haka ta tashi ta je ta kunna wuta ta É—ora masa.
Rumaisa na tsaka da aiki, suka ji sallama, kai da jin yadda
aka yi sallamar, ka san babu alheri a tare da mai sallamar.
Mama ta amsa tana faÉ—in maraba.
Jin yanayin yadda aka yi sallamar ne ya sanya Rumaisa faÉ—uwar
gaba, ta tsaya cak tana sauraron abin da zai biyo baya, dan ta san babu wanda
zai aikata abin da za a zo ana musu wannan sallamar a daren nan idan ba ita ba.
Mama tayi wa matar nuni da tabarma dan ta zauna, amma matar
ta ce "A'a ba ma sai ma zauna ba, ai abin bana zama bane na"
ÆŠan zuro kai Ruma tayi daga Kitchen, domin taga wacece, tozali
tayi da Habiba da ƙaninta Sani.
Ita ba zuwansu ne ya É—aga mata hankali ba, babu tantama ta san
ƙararta
aka kawo, amma tashin hankalin ta, Mai sunan Baba yana nan.
"Ban sani ba ko ke ce ki ka sanya 'yar ki ta dinga abin
da ta ga dama a cikin unguwar nan, saboda tsabar rashin mutunci da rashin ta
ido, ta kama mini 'ya ta daka, kalli fuskar Habiba, kuma duk da haka bai isheta
ba, ta É—auko yayanta suka biyo Sani gida shima suka daka, haka ake yi
fisabilillahi wallahi sai da na biya na kai ta chemist aka yi mata allura.
Dawowata gida kenan bana nan kawai na tarar da yarinya baki
ya haye, ya fashe ta riƙe kai sai kuka take, shima Sani kalli
fuskarsa duk shatin mari tsakani da Allah Wannan adalci ne?" Ta ƙarasa
maganar tana haska fuskar Habiba. Fuska ta kumbura suntum, bakin ko rufuwa baya
yi, leɓen sama ya ɗage ya kusa danganawa da hancinta, duk
dadashi a waje.
Duk da halin da Rumaisa take ciki na fargaba, amma sai da ta
ƙunshe
baki tayi dariya ƙasa-ƙasa, saboda yadda fuskar Habiba ta koma
kamar an naushi fura.
Jiki a sanyaye Mama ta ce "Dan Allah dan annabi kiyi haƙuri,
yaran yanzu ne sai addu'a kawai, kin ga ni ban ma san tayi ba, daga ita har
yayan nata babu wanda ya zo ya gaya mini, ban ma san waye ba a cikin yayyan
nata ba, amma kiyi haƙuri".
Haidar yayi gyaran murya ya ce "Mama nine, su meyasa
yaran ba a tambayesu me suka yi mata ba, hijjabi a hannu suka biyota da bulalai
zasu daka.....
"Rufe mini baki ban tambayeka ba" Mama ta dakatar
da haidar cikin tsawa.
Mama tayi ta bawa Babar su Habiba haƙuri, amma ba
kunya babarsu Habiba ta ce "An bar yara babu tarbiyya su yi ta abin da
suka ga dama, saboda tana taƙamar ita ƙanwar maza ce, sai tayi ta isakancin da
ta ga dama, sai ta kashewa yarinyar fuska ta cuceni, wallahi ban da ana maƙota
da sai na kai maganar wurin hukuma, dan ba zan yadda ba, ita ta dakar mini 'ya,
shi kuma ya zo ya zage ƙwanji a kan ɗana".
Cikin muryarsa mai ban tsoro da babu alamar wasa a cikinta
ya ce "Ke ya isheki haka malama, ke kamar ba uwa ba, kawai ki zo gaban
mace kina cewa 'ya'yanta basu da tarbiyya, tana baki haƙuri kina cigaba
da ƙanan
maganganu, kar Allah ya sanya ki haƙura ɗin, ki kai duk in da zaki kai ki je ki
faÉ—a,
kuma ko yau wani ya kuma yinƙurin taɓa Rumaisa a unguwar nan, sai mun nuna wa
duniya ƙanwar maza ce, fice ki bawa mutane wuri"
Mama zata yi magana, amma mai sunan Baba ya haÉ—e
rai, ya girgiza mata kai, tare da nunawa Babarsu Habiba hanyar fita.
Jiki na rawa ta saka su Sani a gaba suka fice, duk girma da ƙanƙantar
mutum, babu wanda Umar baya yi masa kwarjini.
Sai da ya tabattar sun tafi, sannan ya dubi ƙofar
Kitchen É—in ya ce "Ke kuma fito nan munafuka" aikuwa kamar
munafukar ta fito tana sunkuyar da kai ƙasa.
Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Muna
zaman zamanmu lafiya aka haifeki, shegiya kamar rainon iblis, duk gidan nan
babu mai fita ya É—auko magana sai ke, tana zaman zamanta kin saka an zo har
cikin gida ana gaya mata maganganun banza saboda ke, kai ma saboda hauka dan me
zaka biye mata ku je kuna dukan 'ya'yan mutane? Waye ya aiketa ta tsokane
su?".
Ran Aliyu ya ɓaci, ya harzuƙa ya ce
"Bafa maganar hauka a nan, yarinyar nan hijjabi a hannu suka biyota, ba
dan filin ball É—in mu na hanya ba, haka zasu haÉ—u su yi mata duka, yara maza ba mata ba,
har sun fara dukanta baiwarsu ce ita, ko kuma ce musu aka yi ba ta da gata?.
"Shut up! Ita ka san me tayi musu, wannan Yarinyar da
rashin jin tsiya, ai gara su zane ta gobe ba ta kuma ba, ki cigaba da zuwa ki
na janyo mata magana, wallahi ba zaki É—ora mata hawan jini a banza ba, da ki
cigaba da É—auko mata magana ana zuwa ana gaya mata maganar banza, gara na
takeki na murÉ—e miki wuya ki mutu kowa ma ya huta".
Tun da Mai sunan Baba ya fara sababi, Sentence É—insa
na ƙarshe
ne ya baƙanta mata rai, wai ya murɗe mata wuya ta mutu su huta. Ta yi shiru
ya gama bala'insa ya ce ta wuce ta cigaba da yi masa aikinsa, ya fice.
Rumaisa tana aikin tana kuka, wato ma ba'a sonta, wai da
suna zaman zamansu aka haifeta, ta hana mahaifiyarsu kwanciyar hankali.
Usman ne yayi tsaki ya ce "Wallahi Mama É—an
nan naki yana da matsala, na yi shiru ne kar na tanka masa yayi mini tijara,
amma ba damar yarinya ta motsa sai faÉ—a, ke Ruma" ya kirata.
Ta goge hawayenta, ta fito daga Kitchen É—in.
Ya kalleta ya ce "Duk shegen da ya takaleki kar ki raga
masa, ki ci uabnsa idan yafi ƙarfin ki muna nan, yaran unguwar nan
marasa mutunci, ki ka zama nusara raina ki zasu yi, duk É—an da ya miki ki
ci ubansa ko mace ko namiji mun tsaya miki".
Mama ta ce "Zinnuraini, kai ne kake zigata ta É—auko
magana?".
"A'a Mama bance ta É—auko magana ba, amma duk wanda yayi
mata, ta rama babu nusari a cikinmu, ƙanwarmu ba zata zama nusara ba, mu ci
uban mutum ya zo kawo ƙara mu ƙara masa"
Martanin Yaya Usman ne ya É—an sanya hankalin Rumaisa ya kwanta, ta
kammala yiwa Yaya Umar aikinsa ta je ta nemi wuri ta kwanta, ko gurasar da
Yasir ya bata ba ta ci ba.
Tana kwance lamo a kan katifarta, ta ji muryar Huzaifa a
kanta yana cewa ki cigaba da É—auko magana, ai gara ya murÉ—e
miki wuyan ki mutu kowa ma ya huta da tijararki da rashin hankali.
Banza ta yi masa, kamar ba da ita yake ba, dan idan ta ce
zata biyewa Huzaifa faÉ—a za suyi, kuma a kowane lokaci mai
sunan Baba na iya shigowa, yadda yake a ƙule da ita ta san sai jikinta ya gaya
mata, idan ya dawo ya tarar suna faÉ—a da Huzaifa.
Da safe bayan gaisuwa ba abin da ya haÉ—ata
da mutan gidan, tana kwamce a É—aki, 'yan mazan suka gyara komai na
gidan, suka É—ora abin kari. Ko ta kan abincin safen ba ta bi ba, ta saye
gurasarta a hijjabi, ta É—au allonta ta tafi makarantar allo.
Sai dai ashe tuni labari ya iske shugaban makarantar su, a
kan faÉ—an da suka yi jiya, malam babba ya tara su ya ce sai ya zane
su.
Idon Rumaisa yayi tsilli-tsilli, dan kusa bulalar malam
Babba akwai É—an karen zafi.
Kan Malam Babba ya kai ga zuwa ya yanke musu hukunci, ta
zari allonta ta kwasa da gudu, ya tsaya yana ƙwala mata kira, amma tayi burus ta bar makarantar
ta kama hanyar komawa gida, dan a rayuwar Rumaisa ba ta ƙaunar duka ko kaɗan.
A soro suka yi karo da Yaya Usman zai fita, ya tsaya yana
kallonta, har zata wuce ya ce "Wai me kika dawo yi ne gidan nan yanzu, ina
Makarantar kuma?"
Ta tura baki ta ce "Kashi nake ji shine na dawo
gida"
Tsaki yayi ya ce "Haka dai kika iya, wannan uban cin da
kike yi, ba dole kullum ki kasance cikin zawo ba, baki da aiki sai kashi da
tusar tsiya" banza tayi masa ta raɓe shi ta wuce tana murguɗa
masa baki, ba tare da ya sani ba.
Ta shiga cikin gidan tana ciccin magani,
ihuu tayi, tare da tsalle ta nufi in da wani dogon matashi ke zaune, mai
tsananin kama da Yaya Umar, sai dai banbancinsu, Yaya Umar fari ne shi kuma bai
kai shi haske ba, sannan shi wannan fuskarsa ɗauke take da murmushi saɓanin
fuskar Yaya Umar.
Babu tunanin komai, ta faÉ—a jikinsa tana murmushi.
Shima rungumeta yayi yana murmushi ya ce "Autar Mama,
tun É—azu zaman jiran dawowarki nake yi".
"Babban Yaya, yaushe ka dawo?"
"Tun É—azu na dawo, nace kina ina aka ce kin
tafi makarantar allo".
"Wayyo daÉ—i, yaushe rabon da na ganka, gaba É—aya
gidan babu daÉ—i, kowa ya tsane ni, har da cewa na ishesu wai kamar su murÉ—e
mini kai su huta".
Waro ido yayi ya ce "Wane mara ta idon ne yayi wannan iƙrarin
a gidan nan?" Ta waiwaya sannan a hankali cikin raÉ—a ta ce
"Waye banda ƙaninka, ya tsaneni wallahi".
Yayi murmushi ya ce "Ai ba wanda ya isa ya taɓa
mini auta ina raye, ai gani a gidan na dawo".
Wani matashin ne ya sake fitowa, yana faÉ—in
"Iya rigima, ya halinki?"
Sake waro ido ta yi ta ce "Yaya Abdallah".
Ya amsa da "Na'am uwar rikici".
"HaÉ—a baki kuka yi duk kuka dawo yau
kenan?"
Abdallah ya ce "Eh haka ne, su Baba Atine suna ta
gaisheki, sun ce ke ba kya zumunci"
Ta taɓe baki ta ce "Waye zai barni na je
garin, ai ni ina son zumunci kai ni ne ba ayi" Gaba É—aya
sai ta manta da damuwarta, ta shantake suna hira.
Sai da aka jima sannan ta shiga É—aki ta ajiye
allonta.
Sabgoginta ta shiga yi, ta zage ta ce ita zata yi wa su
Babban Yaya girki, abincinta zasu ci.
Aikuwa faÉ—a ya kaure, Huzaifa ya ce ba zasu ci
jagwalgwalonta ba su zasu yi girkinsu, ƙarshe Yaya Sadik ya ce na Rumaisa zai
ci.
Zuwa Azahar gida ya É—inke kowa ya hallara a falon Mama suna
cin Abincin rana, Sadik sai jinjinawa ƙoƙarin Rumaisa yake ta yadda ta iya girki
mai yawa haka, Huzaifa da Yasir kuwa sai kushewa suke yi.
Zaratan maza ne su bakwai sai Rumaisa, Mama a hankali take
binsu É—aya bayan É—aya da kallo, tana tuna baya.
Hadiza shine sunan Mama na gaskiya, haifaffiyar garin Kano
ce, unguwar mandawari. A nan ta taso tayi karatun boko da islamiyya, sai dai
tana aji uku na Sakandire, ta haÉ—u da mahaifinsu Rumaisa, Muhammad Aminu
a nan unguwar sabon sara, amma asalinsa É—an garin Katsina ne, yana zuwa gidan wan
mahaifinsa ne a Kano yana koyan harkar kasuwanci, a nan suka haÉ—u
suka yi aure, kan Hadiza ta gama makarantar sakandare.
Haihuwar fari Mama ta haifi tagwaye Abubakar Sadik da Umar
faruk sune 'ya'yanta na fari, Sai ta kuma haihuwar Usman, sai Aliyu, Abdallah
da Huzaifa, Yasir ne kawai ba ɗan ta ba, ɗan ƙanwar mahaifinsu Rumaisa ne, ta haife
shi da kwana kaÉ—an Allah ya yi mata rasuwa, a lokacin Mama tana shayar da
Huzaifa sai ta haɗa su ta shayar da su tare, ba zaka taɓa cewa ba 'yan
biyu bane ba, ko ba ita ce ta haifesu ba.
Mama gaba É—aya tayi tunanin ta daina haihuwa,
saboda galibi bai fin shekara biyu uku a tsakanin yaran take haihuwa, amma
bayan haihuwar Huzaifa sai da ya shekara takwas, kawai ta daina ganin al'ada,
sai ga cikin Rumaisa.
Tun da Allah ya sa ta haifi Rumaisa, kowa ya É—auki
soyayya ya É—ora mata, kasancewarta kallabi a tsakanin rawuna, kowa babban
burinsa ya faranta mata.
Mahaifinsu Rumaisa, mutum ne mai matuƙar kulawa da son
iyalinsa, kasancewar Ruma ce kaÉ—ai 'yar sa mace yafi kowa ji da ita, ba
shi da magana sai ta Rumaisa, Akwai tsananin ƙauna da shaƙuwa a tsakanin
Ruma da mahaifinsu, dan kusan tafi son sa a kan Mama, saboda Mama akwai faÉ—a,
Abba kuwa lallaɓata yake. kwatsam Allah ya yi masa rasuwa tana da shekaru uku
kacal a duniya, bayan yayi gajeriyar rashin lafiya.
Bayan rasuwar sa sai da Rumaisa tayi cuta kamar ba zata rayu
ba, saboda alhini. Dangin mahaifin su Rumaisa suna da zumunci sosai, sun so a
rarraba musu yaran su riƙe su, amma Mama ta ce ba ta son a raba
nata kan yaranta, dan haka ta ce su ƙyale mata su.
Haka tayi ta É—awainiya, 'yan uwa da abokan arziki suna
taimaka mata da abin da zasu iya
Tasowar Rumaisa a cikin 'yan mazan nan, wannan ya É—auka
wannan ya sauke ya sanya ta taso tamkar namijin ita ma. Ba ta jin magana ga
rashin tsoro, ga tsiwa da É—an karen surutu da iyayi, gashi lokacin
da take tasowa girma ya fara kama Mama duk tayi sanyi, dan haka ta mayar da
Mama kamar wata kakarta ba uwa ba.
Mutum É—aya take tsoro shi ne Baban Mama, Yaya
umar mai sunan baban Mama, Allah yayi masa kwarjini shi ko irin wasan nan na
yarinta baya yi, ba shi da abokai, ga tsare gida ba shi da fara'a ko walwala
baya son shiga mutane sam, idan kaga an taka masa burki kai tsaye to Yaya Sadik
ne. Mama tana matukar girmama shi saboda sunan mahaifinta da yake da shi.
Yanzu Rumaisa tana aji huÉ—u na Firamare, Abubakar yana Dutse yana
karatu, babu wanda yake da cikakken ƙarfin ɗaukar
É—awainiyar
gidan gaba É—aya, amma kowa babban burinsa ya nemo ya kai gida, komai suka
samu mahaifiyarsu da ƙanwarsu kawai suke tunani.
"Hajiya Mama, ya naga kina ta kallonmu ne kamar da baƙo
a cikinmu".
Mama tayi murmushi ta ce "Allah nake yiwa godiya, da ya
sanya duk ku ɗin nan nawa ne, Allah ya dafa muku ya ƙara haɗa
mini kanku"
Suka amsa da "Amin"
Yasir ya ce "Mamanmu, maganin kukanmu Allah ya ƙara
hore mana, mu gantataki fiye da kowace irin uwa a duniya"
Huzaifa ya ce "Hmm kamar gaske, nan fa kake zuwa da
abin duniyarka ka hanata, ka hana kowa ka bawa waccan yarinyar
mai kama da Akushin"
MurguÉ—a baki tayi tana fari da ido ta ce
"Tubarkallah zuƙul-zuƙul maye ya ci kansa da kansa, wallahi ni
bana kama da Akushi, son kowa ƙin wanda ya rasa"
"Ke dalla ware, meye son kowa ƙin wanda ya
rasa, aba Kamar gurguwar akuya" Yasir yayi maganar yana dariya.
Haushi ne ya kamata ta buÉ—e baki za tayi rashin mutunci, ta sanya
idonta a cikin na Umar, ta haÉ—a maganar da zata yi, da lomar abincin
ta haÉ—iye.
Suka gama cin abincin, Yasir ya kwashe kwanuka, ya fara ƙoƙarin
wankewa, Huzaifa ya shigo da tsintsiya zai share É—akin, Umar ya ce ya ajiye tsintsiyar ya
bawa Rumaisa ta share.
Haushi ne Yakamata ta lura tun da aka kawo ƙararta
ya tsaneta, dama can ba wani shiga shirginta yake yi ba.
Bayan ta kammala sharar ta nemi wuri za ta kwanta Mama ta
kalli kan Rumaisa, da ta fara tsifa, tayi rabi ta bar rabi ta ce "Fita ki
bar mini É—aki, karki sake shigowa sai kin gama wannan tsifar.
Fitowa ta yi ta na tura baki, tana nema ta yi kuka.
"Autar Mama, meya É“ata miki rai ne?" Cewar Yaya
Abubakar da yake ƙoƙarin shiga ɗaki.
Dama ƙiris ta ke jira, dan haka ta fara kuka
"Ba mama ce ta koreni daga É—akinta ba, wai sai na gama tsefe kaina
ba, ni mama ta tsaneni".
Girgiza kai ya yi ya ce "Yi haƙuri ki daina
kukan, bari na zo na tayaki tsifar"
Haka suka zauna ya samu kibiya ya tsefe mata kan tsaf, suka
wanke gashin, ya ce da safe zai bata kuÉ—in kitso.
Mama ta na kallonsu ba ta kula su ba, ta cigaba da
sabgoginta.
Abdallah yana ta dube-dube a kitchen, ya ci karo da allon
Rumaisa, duk gefensa ya karye, ga rubutun jiki yayi baƙi ƙirin,
ba ta sake wani ba.
Ya fito da allon a hannunsa ya ce "Ruma, wannan allon
naki yaushe zaki yi wani rubutun?" Ta haÉ—e rai ta ce "To ban iya ba, sai na
iya zan wanke".
"Haka dai, ba kya ja a ko ina, daga arabin har bokon,
Allah ya sa su zaneki idan ki ka je sati mai zuwa, baki wanke allon kin yi wani
rubutun ba, gandamemiya da ke amma haryanzu a izifi biyu ki ke"
Sai da yayi wannan maganar ta tuna yadda malam Babba ya
dinga ƙwala mata kira amma ta gudo gida, yanzu sati mai zuwa ta yaya
zata je makarantar allon? Kuma muddin abin da ta yiwa malam ya zo gidan nan, ta
san ta kaÉ—e".
"Astagfrillah, ni 'ya su meyasa haka ne, garin in gujewa wani hukuncin sai na faÉ—a wani tarkon, ya zan yi da raina?
0 Comments