Kanwar Maza Hausa Novel

Kanwar Maza Hausa Novel

Barkanku da isowa shafin littattafan hausa novels inda zaku karanta littafin Kanwar Maza Hausa Novel wanda Aisha Adam (Ayshercool) ta wallafah.

Kanwar Maza Hausa Novel

Page 1: Daji Ajiyar Allah! La'asar sakaliya, a lokacin da hasken rana ya fara disashewa, ta doshi yamma za ta faɗi, duhun magariba na ƙoƙarin shigowa ya maye ragowar hasken da ranar ta bari kan ta ƙarasa faɗuwa.

Gamayyar bishiyoyi ne, dogaye da da madaidaita, haɗe da ciyayi da ga mabanbantan tushe, suka haɗu suka yiwa dajin ƙawanya. Zai iya kasancewa abin sha'awa ga wanda ya zo yawon buɗe ido, idan har bai san mai dajin ya ƙunsa ba.

Ga wanda ya san abin da ya ƙunsa kuwa, zai kasance wuri mafi razani, firgici da kuma tashin hankali.

Gudu take yi a tsakanin rayuwa da mutuwa, tana rungume da wani zani a ƙirjinta, babu yadda za ayi daga nesa ka gane me ta rungumo haka take wannan uban gudun.

Ƙafafuwanta babu takalmi, jikinta babu mayafi, duk da yanayin garin babu zafi, amma laɓɓanta sun bushe tamkar dutsen da ya shekara ruwa bai zuba a kansa ba, babu alamar tana gane in da take jefa ƙafarta. Duk da wannan mawuyacin hali da take ciki, ta bawa abin da take rungume da shi muhimmanci sosai da sosai.

Cikin rashin sani, tayi karo da wani abu da ita kanta ba ta kai ga tantance ko meye ba, sai dai ƙarfi da nauyin abun ya sanya ta faɗi ƙasa, take ta saki wani marayan kuka, a lokacin da jini ya fara zuba daga ƙeyarta.

Sai a lokacin abin da take rungume da shi ya tsala kuka, saboda firgitar da ya yi shima.

Jariri ne ɗanyen goyo, cibinsa ko faɗuwa bai yi ba, jikinsa duk busashshen ƙazantar haihuwa da alama yaron ya kwan biyu, amma ko ruwa bai taɓa gani ba balle a wanke wannan ƙazantar!.

*************

Cikin garin Kano, unguwar É—orayi tinga, misalin Æ™arfe huÉ—u na yammacin ranar Alhamis, wani matsakaicin gida ne, cikin rukunin gidajen dake É—an Æ™aramin layin,  kallo É—aya zaka yi wa gidajen, ka san na masu Æ™aramin Æ™arfi ne, duba da yanayin kwatoci da kuma kasancewar gidajen awon igiya, ba magudanan ruwa, babu layuka masu kyau, kowa da in da fuskar gidansa ta kalla, haka zalika kowa in da ya ga dama yake sako kwatar gidansa, wasu da gyara wasu babu, ga gidajen 'yan Æ™anana tamkar wani zai hau kan wani.

 

"Wai ba zaki fito ki je mini aiken ba, har sai gawayin ya ƙare tukuna?" Cewar wata matashiyar dattijuwa, da take zaune a gaban kurfoti, hannunta riƙe da mafici tana firfitawa, gefe ga farantin silba ɗauke da garin tuwon masara a kai.

 

Wata  yarinya ce ta fito daga wani É—akin da yake bayan matar, hannunta É—aya riÆ™e da hijjabinta, É—aya kuma sai matsar hawaye take yi.

 

Matar ta kalleta ta ce "Kukan me  ki ke yi?"

 

Aikuwa kamar mai jiran ƙiris, cikin sangarta yarinyar ta ce "Ba Huzaifa bane ba ya....

 

"Ni yi mini shiru, haka dai kuka iya faÉ—a kamar kuna ganin hanjin junanku, idan na hana ki zuwa in da yake ai ba zaki hanu ba, maza ki É—au kuÉ—in nan ki je mini gidan Laure, ta baki kuka ta sittin, daddawa ta arba'in sai manja na naira É—ari ki kawo mini canjin, na yi maza in kaÉ—a miyar nan kan magariba".

 

Kwaɓe fuska yarinyar ta yi ta ce "Wai yau ma miyar kuka za ayi Innalillahi wa innalillahi raji'un"

 

Baki buÉ—e ta bi Yarinyar da kallo, cikin hasala ta ce "Idan na kaÉ—a kukar kar ki sha, zaki É—au kuÉ—in ki fita ko sai na yi fatali da kanki a wurin?"

 

Ta durƙusa ta ɗau kuɗin, ta zura hijjabinta ta nufi hanyar fita, a ranta tana jin gara ace yau babu abin da zasu ci, da wannan tuwon kamar na ibada.

 

Cike da kashedi matar ta ce "Idan kin ga dama kuma ki je ki zauna, kar ki yi sauri kiga yadda zan yi da ke, ko ki biyewa yara ki tsaya shashanci a hanya"

 

Ba to ko waiwayo ba, ta yi gaba abinta tana kalle-kalle.

 

Gidansu ƙawarta Habiba ta fara biyawa, ta tarar da maman Habiba a tsakar gida ana yi mata kitso, ta durƙusa ta gaida Maman Habiba, sannan ta ce mata wurin Habiba ta zo.

Habiba ta fito daga ɗakinsu tana kallonta tana murmushi, ta ƙaraso in da take tsaye ta ce "Ruma ina zuwa ne?"

 

Cikin muryar RaÉ—a Ruma ta ce "Dan Allah Habiba aron tayar Sani zaki bani, Mama ce ta aikeni so nake nayi sauri na je na dawo".

 

Habiba ta ce "Kaii, Ruma kin san Sani yafi kashi É—oyi, kar na baki ki je ki salwantar da ita, daga ni har ke mu shiga uku".

 

Ruma cikin ƙwarin gwiwa ta ce "Wallahi ba zata salwanta ba, ke dai ki aramini, so nake na yi gudu na ne na dawo".

 

Habiba ta ja Ruma soron gidansu, ta duba saman kejin kajin da ke cikin É—an tsukakken zauren gidan, ta É—aukowa Ruma tayar Sani ta bata ta ce "Dan Allah Ruma ki kula, kar wani abu ya samu tayar nan, ki yi maza mi garata ki je ki dawo"

 

Ruma tayi murmushi ta ce "Kar ki damu, yanzu zan fyalla naje na dawo, ina son tayar nan ta sani dama ya bar mini, 'yar dandaɓasa da ita, yanzu zaki ga naje na dawo".

 

Habiba tayi murmushi ta ce "To shikenan, yi sauri kafin ya dawo".

 

Ruma ta dafe kan taya, ta garata ta dinga zura gudu ta lunguna kamar wata namiji ba mace, ba ta tsaya da gara tayar ba har sai da ta isa gidan Laure.

Ta yo sayayyarta ta gama, ta fito ta kuma garo taya zata tafi gida, can ta hango wasu 'yan makarantar allonsu, a ƙofar gidan Hanne mai markaɗe suna 'yanta, ba tare da ta tuna da kashedin Mama ba, ta ajiye kayan aiken da canjin haɗi da tayar da ta aro, ta shiga aka hau 'yanta da ita.

 

Kasancewar ƙwararriya ce a harkar shagala da iya rinto, nan da nan wasa ya ɗau zafi, ganin tana ta cinyesu a 'yantar ta hanyar rinto, sai wasa ya koma faɗa, daga nan aka hau dambe, a wurin Ruma ta kifar wa da wata markaɗenta ga ta da ƙarfi kamar doki. Da ƙyar wani mutum ya raba faɗan, Ruma ta haɗa yaran mutane ta zane musu jiki, sai da mutumin yayi mata barazanar zai gayawa yayanta, sannan ta haƙura da damben.

 

Yarinyar da suka yi damben, ganin an musu asarar markaɗe, an kifar ga duka, ya sanya ita da ƙannenta suka fasawa Ruma Manjan da ta sayo wa Mama, suka kwashe canjin aiken, suka farke ledar aiken suka gudu, daddawar ma sai da ƙyar ta tsinto wasu, an fasa ledar kuka duk ta watse.

 

Ta kwashi sauran kayan, ta tafi gida, tana tafe tana tunanin wace ƙaryar za ta jirgawa Mama, dan ta kaucewa faɗanta, dan a duniya ba ta son faɗan Mama, gefe guda kuma tana tunanin irin dukan da zata naɗawa Safiya idan suka haɗu a makaranta allo, saboda abin da suka yi mta.

Lokacin da Ruma ta isa gida tuni an fara kiraye-kirayen sallar magariba, domin wasu masallatan har sun tayar, sai a lokacin ta sake shan jinin jikinta, tsoro ya ziyarce ta.

 

A soro ta rakuɓe tana leƙa cikin gidan, ta hango Mama a gindin rariya tana alwala, Mama ta ɗaga ido tayi mata kallo ɗaya, ta mayar da kai ta cigaba da alwalarta.

 

Cikin sanÉ—a Ruma ta shiga tana satar kallon Mama, ta ji mai Maman za tace mata, amma ta ji ba tace mata komai ba.

Ta lallaɓa ta ajiye abin da yayi saura na aiken, ita ma ta faɗa banɗaki tayi alwala.

Ta lallaɓo falo, ta tsaya a bayan Mama ta tayar da sallar ita ma.

Mama ta idar, ta tashi ta fita tsakar gida, ta duba abin da Ruma ta kawo mata na aiken, taga irin aika aikar da Ruman ta yo.

Ta dawo falon tana jiran Ruma ta idar da salla ta dirar amata, amma Ruma ta ƙi idarwa, ta hau nafifilin babu gaira babu dalili, matar da wataran sallar ma sai Mama ta haɗa .mata da duka take yi, amma yau sai gashi har da nafila.

 

Can da Mama taga abin nata bana ƙare bane ba, sallar taƙi ƙarewa, ta damƙo wuyanta ta baya ta zaunar da ita, ta kalleta cikin haɗe fuska ta ce "Gidan uban wa ki ka je dana aike ki?"

 

Cikin tsoro Ruma ta girgiza kai ta ce "Ba ko ina Mama"

 

"Ƙarya kike yi, zaki gaya mini ko sai na murɗe miki wuya, tun la'asar na aike ki amma sai magariba kika shigo mini, gidan uban wa kika je?"

 

Cikin zazzare ido Ruma take jujjya kai tana rantse-rantsen rashin gaskiya, "Wallahi Mama ban je ko ina ba"

 

Cikin tsananin Fushi, Mama ta ce "Ba zaki gaya mini ba!"

 

"Mama wallahi dagaske nake"

 

"Assalamu alaikum" aka yi sallama a tsakar gida.

 

Mama ta amsa sallamar tana huci, wani matashin saurayi ne ya shigo É—akin, yana faÉ—in Mama na dawo".

 

Mama ta ce "Sannu da zuwa"

 

Ya amsa da yauwa, ya dubi Mama dake tsaye a kan Ruma, Ruma sai wulƙita ido take, kamar ta zagi sarki.

 

"Mama meyafaru ne?" Yayi Maganar yana son jin ba'asi.

 

Cikin ɗacin rai Mama ta ce "Saboda tsabar iskanci na yarinyar nan, nan da gidan Laure, ta je ta sayo mini kayan miya, tun bayan la'asar sai yanzu ta shigo mini gida, babu aiken babu dalilinsa, kuma babu canjina, nayi-nayi ta gaya mini in da ta tsaya amma taƙi faɗa sai rantse-rantse take yi".

 

Ya kalli Ruma ya ce "Ba zaki faÉ—i inda kika tsaya ba, kuma ina canjin? Ko zuwa ki ka yi ki ka kashe mata kuÉ—i tunda kin saba"

 

Cikin tsiwa da rashin kunya, Ruma ta ce "Ban sani ba, kai kuma waye ya saka da kai, zaƙin zaƙafere mai gida feraye kabewa, ai ba da kai ake yi.....

Kan ta ƙarasa Mama ta rufe bakin nata da duka, da sai da tayi zaton bakinta ya fashe.

 

Ja da baya tayi da sauri, ta dafe bakinta tana yarfe hannu, saboda ta ji zafin dukan nan sosai da sosai.

 

Ya jinjina kai ya ce "Mama ƙyaleta, ba dai bata da kunya ba, kar ki wahalar da kanki, ki bari mai sunan Baba ko Haidar su shigo, sai su tuhumar miki ita".

 

Jin abin da ya faɗa ya sanya Ruma ta yi wata irin zabura, ta ce "wallahi Mama gaskiya na gaya miki, dan girman Allah kar ki gaya musu, canjin ne suka zube a hanya, na faɗi ƙasa man jan ya fashe dan Allah kar ki gaya musu".

 

"Wallahi Mama ƙarya take yi, kin san dai ƙaryarta ba ta salla, ki tuhumeta bari mai sunan Baban ya dawo zaki ci ubanki".

 

Cike da gamsuwa Mama ta ce "Ai hakan za ayi tun da ba ta da mutunci"

 

Ya fakaici idon Mama ya yiwa Ruma gwalo.

 

"Mama kin ganshi ko yana mini dariya, dan Allah kiyi haƙuri"

 

Banza Mama tayi da ita, ta bawa Huzaifa kuÉ—i ya kuma yi mata wani cefanen.

 

Rumaisa ta koma gefe tayi tagumi, zuciyarta na ta zullumin halin da zata iya shiga, idan har aka sanarwa da Mai sunan Baba ko Haidar abin da ta yi, gashi ko giyar wake ta sha ta san ba zata iya gayawa Mama haƙiƙanin abin da ya faru ba.

Salati kawai take yi, tana roƙon Allah ya rufa mata asiri, kar Mama ta gaya musu, ƙasan zuciyarta kuma tana yi wa Huzaifa Allah ya isa da ya bawa Mama shawarar ta haɗata da su Haidar.

 

Ta na tsaka da tunanin, ta jiyo Mama da Huzaifa suna hirarsu a tsakar gida, kamar ba ita ta gama faÉ—a ba.

Suna yi mama tana ƙarasa aikin miyarta.

Sallama aka yi a tsakar gida, Ruma ta rikice, dan kusan muryoyinsu duk kusan iri É—aya ne, ta É—an nutsu ne da ta tuna mai sallamar muryarsa ba ta kai ta su Haidar fashewa ba, kuma shi dama sanyin hali ne da shi.

 

Jiyo Mama tayi tana faÉ—in "Fodiyo, an dawo"

"Eh Mama, ya gidan?"

 

"Alhamdilillah, sannu ka je ka watsa ruwa kafin nan na gama miya"

 

Usman da Mama ke kira da Fodiyo ya ce "To Mama, ga wannan" yayi maganar yana ajiye mata leda.

 

Miƙewa Ruma tayi tana leƙa window, tana son gane me ye a cikin ledar da Fodiyo ya kawo.

A ranta ta ce "Allah ya sa kifi ya kawo, idan kifi ne a bani kasona, dan idan aka saka a wannan baƙar miyar ban sha.

 

Ba ta kai ga gano meye a ledar ba, idanunta suka sauka a cikin na dodonta, da ya shigo gidan ko sallama bai yi ba, gani tayi tamkar yayi mata wani irin mugun kallo, ko dan dai a tsorace take ne oho.

Mai sunan Baban Mama kenan, Umar faruk.

Cikin takunsa na ƙasaita ya ƙaraso tsakiyar tsakar gidan, sannan ya yi sallama.

 

Hannu Ruma ta ɗora a ka, muryarta ƙasa_ƙasa ta ce "Na shiga uku, yau kashina ya bushe ƙayau idan ya san me nayi".

 

Tun daga sallamar da ya yi, bai cewa kowa komai ba, shi ma ya ajiyewa Mama ledar da ke nasa hannunsa, ya wuce É—akinsu.

Bai jima ba ya fito tsakar gida, ya É—au buta zai yi alwala.

Ruma ce ta fito kamar munafuka, ta É—an risuna ta ce "Yaya Faruk sannu da zuwa"

 

ÆŠaga ido ya yi ya kalleta, bai amsa ba ya mayar da kansa ya cigaba da alwala.

 

Cikinta ya É—uri ruwa, ta É—au tsintsiya ta tafi falon Mama ta hau shara a daren, kai da gani ka san sharar ba ta domin Allah bace ba.

Huzaifa ya faki Idon Mama ya bi Rumaisa falon, ya dinga leƙata yana tuntsura mata dariya.

 

Ba dan tana cikin yanayi na tashin hankali ba, babu abin da zai hana su kafsa faɗa da Huzaifa a daren nan, amma ta san biyewa Huzaifa su yi faɗa alhalin Faruk yana gidan nan, wata babbar matsalar ce, mai zaman kanta, dan ƙarshe sai tayi kuka.

 

"Ba zaki fito ki É—ebi Abinci ki ci ba?" Mama tayi maganar cikin É—aga murya, yadda za ta jiyota.

 

Daga ɗaki Ruma ta ce 'Mama na ƙoshi"

 

A ƙufule Mama ta ce "To uban me ki ka ajiye da zaki ci, ba zaki fito ki ci Abinci ba?"

 

Ruma ta É—an tura baki tayi shiru.

 

Usman ya ce "Ai kin san kin yi maƙiyin nata tuwo, mussaman miyar kuka da ma wata miyar ce ba wannan ba, ƙila ta ci"

 

Mama ta ce "Abin da nake da shi ba shi zan dafa na bata ba, zan fasa girki ne dan ba ta cin tuwon?".

 

Cikin kakkausar muryarsa Umar ya ce "Ki ƙyaleta, tun da a cikinta zata zuba, ta kwana da yunwa mana".

 

Mama ta gyaÉ—a kai ta ce "Ai shikenan"

 

Muryarsa kawai da ta jiyo, sai da ta sake shiga cikin tashin hankali, tsananta addurta ta yi, a kan Allah ya rufa mata asiri kar Mama ta gaya masa ta yi mata laifi.

 

'yan mazan nan suka kewaye Mama, suna ta hira kowa da abin da yake ce mata, banda mai sunan Baba, da  yake duba wayarsa, ba tare da ya tanka musu ba.

 

Jin suna ta hira, Mama ba ta gaya masa tayi laifi ba, ya sanya take ta murna, tayi maza ta yi sallar isha'i ta shimfiÉ—a katifar ta ta kwanta.

Ta cigaba da Addu'a a cikin zuciyarta.

 

"Assalamu alaikum" aka yi sallama a tsakar gidan.

 

Suka amsa baki É—aya, Suka zubawa yaran da suka shigo ido mace da namiji.

Duk da akwai wutar lantarki da fari Mama ba ta gane yaran ba sai daga baya.

 

Suka gaida Mama da su Umar, Mama ta kallesu ta ce "Habiba ya aka yi me?"

 

Habiba ta ce "Ruma tana nan?"

 

Umar yayi caraf ya ce "Yaya aka yi?"

 

Kasancewar sa mutum mai tsanain kwarjini, sai da Habiba ta É—an ruÉ—e sannan ta ce "Dama É—azu ne da aka aiketa ta zo ta ce na bata aron taya, zata jewa Mama aike, to tayar ta Sani ce, ta ce zata dawo da ita kuma haryanzu shiru".

 

Mama cikin mamaki ta ce "Taya kuma?"

Habiba ta jinjina mata kai.

 

Gaba É—aya Ruma ta manta da ta je ta aro taya, sai yanzu da ta ji maganar Habiba, dan tun da aka kwashi damben nan a nan ta yasar da tayar ta yo gida.

ÆŠora hannu tayi a ka ta ce "Na shiga uku, Habiba shikenan kin kasheni".

 

Mama ta ce "Kina ina zo nan, mara kan gado, babu yadda ban yi dake ba a kan ki gaya mini in da kika tsaya, amma kika ce ke baki tsaya ko ina ba, ashe yawon aron taya kika tafi ko, ko ina sai kin nuna hali ƘANWAR MAZA, ina ke ina taya ban da hauka, zaki fito ki basu abarsu ko kuwa?"

 

Jikinta na tsuma ta fito ta tsaya daga bakin ƙofar falon Mama, tana satar kallon Umar, amma taga kamar ma bai san me ake yi ba.

 

"Ma.m.maama.. wallahi dan nayi sauri ne, ya sanya na aro tayar, kuma wallahi na manta na barota a wajen gidan Hanne mai markaÉ—e".

 

Mama ta riƙe haɓa kawai, tama rasa me zata ce gaba ɗaya.

 

Huzaifa ya ce "Wannan yarinyar idan kina da rabon yin hankali Allah ya shiryeki, ina ke ina taya kina mace?"

 

Mama ta kalli in da Habiba take tsaye ita da ƙaninta ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, tun da ta fita nima nake zaman jiranta, ban aiketa ta je ta karɓi kayan kowa ba, da safe in Allah ya yarda zan turata ta je ta dubo muku" Mama tayi ta basu haƙuri, suka juya suka tafi.

 

Mama ta zauna ta dasa mita, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, su Usman na tayata, ita kuwa Ruma da ta san ba ta da gaskiya, sai ta ƙule a kan katifarta, zuciyarta sai bugawa take tana jiran jin me Yaya Umar zai ce, amma shiru bai ce komai ba.

 

Har suka watse daga tsakar gida, Mama ta shigo ɗakin, ta sameta ta rufe ido tana baccin ƙarya, still Mama ta cigaba da mita, sai da Ruma ta ji kamar ta tashi ta barwa Mama ɗakin ta huta, saboda Mama mitarta ba ta ƙarewa sam, gefe guda tana yiwa Allah godiya da Dodonta bai yi magana ba.

 

Wani irin bacci ne mai daÉ—in gaske yayi awon gaba da ita. A cikin baccin nata babu zato babu tsammani sai ji tayi an yi sama da ita da hannu É—aya.

 

"Wayyo Allana, Innalillahi wa innalillahi raji'un, warin hannuna na hagu zai karye Mama!" Sai da ya dungurar da ita a tsakar gida, suka yi ido huÉ—u, ta ga wanda yayi mata wannan aikin.

Jikinta ne ya hau kyarma, dan idonsa kawai idan ransa a É“ace yake abin tsoro ne.

 

A ƙasan zuciyarta ta ce 'Shikenan tawa ta ƙare, Allah ya sa na cika da kyau da imani!.

Kanwar Maza Hausa Novel Page 2

Kasa É—auke idanunta tayi daga kallonsa, saboda azabar firgici da razanar da ta yi.

Ya janyo kujera ya zauna a gabanta, ya ɗan ƙura mata ido, sannan cikin kaushin murya ya ce "Gidan uban wa kika tafi da ta aikeki, tun la'asar ba ki dawo ba sai magariba?" Yayi Maganar yana tsareta da ido.

Kasancewar akwai wutar lantarki, ya sanya fes take kallon fuskarsa da idonsa.

 

"Ba magana nake yi miki ba, ki ka tsare ni da ido?" Ya daka mata tsawa.

 

Zabura tayi ta yinƙura za ta yi magana,amma ya sake cewa "Kuma wallahi kika yi mini ƙarya sai na ci ubanki a daren nan"

 

Jiki na rawa ta fara zayyane masa yadda aka yi tun bayan fitarta.

 

Huzaifa tun da  yaga Yaya Umar ya shiga É—akin Mama ya jiyo kukan Rumaisa, ya sha jinin jikinsa, dan ya san yau sai yadda Allah ya yi.

Mama kuwa girgiza kai kawai ta yi, jin Yadda Ruma take faɗar gaskiya saɓanin ɗazu da ta yi mata ƙarya.

 

Umar ya ce "Namiji ce ke da zaki tafi aron taya?" Ta sunkuyar da kai tayi shiru.

 

"Kuma me nace miki a kan dambe a hanya, karya ce ke?"

 

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

 

Ya É—ora da cewa "Wato ke duk wani abu da za'a gaya miki sai dai ya shiga ta kunnenki na dama, ya fita ta hagu ko?"

 

Ita dai tayi shiru tana rarraba ido.

 

"Kyaci ubanki, tashi ki kama kunnenki tun da ba zaki yi hankali ba".

 

Maraicewa tayi zata fara yi masa magiya, amma da yayi mata wani mugun kallo, ba shiri ta miƙe ta durƙusa ta hau kamun kunne.

 

Gaba ɗaya Huzaifa ji yayi bai ji daɗi ba, maimakon a hukuntata tun a lokacin amma sai da aka bari ta fara bacci, za a sakata kamun kunne, ya tsaya ta ƙofa yana leƙen tsakar gidan ya san yanzu zata galabaita, gashi babu wanda ya isa ya hana Yaya Umar abin da yayi niyya sai Hassan ɗin sa wato Abubakar Sadik, shi kuma baya nan.

 

Umar ya nutsu yana duba litattafansa, Rumaisa kuwa sai tangaÉ—i take tana neman ta faÉ—i, amma yayi banza da ita, dan ta san idan ta faÉ—i ko ta tashi ba zata iya É—aukar wani hukuncin ba.

Tun tana kuka ƙasa-ƙasa har ta fara yi da ƙarfi, saboda azabar gajiyar da ta yi.

"Tashi" ya faÉ—a ba tare da ya kalleta ba. Ta É—ago duk ta haÉ—a uban gumi, ga hawaye da majina duk a fuskarta.

 

"Kukan uban me kike yi?"

 

Cikin kuka ta ce 'Yaya na gaji ne, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba, na tuba"

 

"Da alama haryanzu baki yi laushi ba, yi zaman babur tun da kin gaji da kamun kunne"

 

Babu kalar izayar da Yaya Umar bai yi mata ba a daren, har Sai da Mama ta ji babu daÉ—i a ranta, amma tuna cewar yarinyar ba 'yar goyo bace ba, ya sanya tayi banza ta cigaba da laziminta.

 

Aliyu ne ya fito daga ɗakinsu, cikin damuwa ya ce "Dan Allah Yaya kayi haƙuri ka ƙyaleta haka ta je ta kwanta dare yayi, wallahi ta horu, kuma ga gobe in Allah ya kaimu da makaranta".

 

A fusace Umar ya kalleshi ya ce "Ka ɓace mini daga gabana ko sai na haɗa da kai?" Ran Aliyu ba ƙaramin ɓaci yayi ba, kawai ya girgiza kai ya shiga banɗaki.

 

Sai da ya tabbatar da ta galabaita sannan ya ce ta zauna ta huta, shi kuma ya tashi ya fita.

 

Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, saboda jin cinyoyinta take kamar babu nama a cikinsu sai rodi, saboda azabar sagewa da suka yi, ƙashin bayanta ma ban da azabar ciwo babu abin da yake yi mata.

 

Yaya Umar na fita, Huzaifa ya ƙaraso in da take yana mata sannu cikin tausayawa kamar ba shi ne ya gama bawa Mama shawarar ta haɗata da Yaya Umar ba.

 

Ya je ya ɗebo ruwa ya bata, ta karɓa ta kafa kai tana sha tana kuka. Ta gama sha, ya karɓi kofin ya ajiye yana goge mata hawayen fuskarta.

 

"Uban me kake a nan wurin?" Basu ji dawowar Yaya Umar ba, sai maganarsa kawai suka ji, suka yi tsuru-tsuru.

 

"Zaka tashi ko sai na haÉ—a da kai?" Jiki na rawa Huzaifa ya tashi, ya koma É—akinsu.

 

Ya kalli Ruma da ke ta ajiyar zuciya, ya tabbatar ta galabaita, ya san yanzu haka jikinta na ciwo, ya jefa mata leda a jikinta ya ce "Maza É—auki ki shanye"

 

Jiki na rawa ta ɗau ledar, doguwar jarka ce cike da youghurt mai sanyi a ciki, ta ɗaga kai ta sha rabi, yana tsaye yana kallonta, ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Na ƙoshi".

 

Jin bai ce komai ba ne ya sanya ta ɗago ta kalleshi, ganin yana mata wani irin kallo ne, ya sanya ta cigaba da sha tana yamutsa fuska, da ƙyar ta shanye, ta ajiye robar tana jiran umarni na gaba.

 

"wuce ki je ki kwanta"

 

Da ƙyar da yinƙura ta tashi, ƙafafuwanta na ta rawa saboda ciwo, ta shiga ɗaki.

Tana shiga ta tarar da Mama na salla, ta faÉ—a kan katifa tana kuka.

Mama har ta idar da sallar ba tace mata komai ba, ta cigaba da kukanta har bacci ya É—auke ta.

 

Cikin bacci ta ji Mama na É—ala mata duka a cinyarta "Tashi" duk da yadda ta ji zafin dukan, amma ta buÉ—e idonta a hankali ta kalli Mama, ba tare da ta ce komai ba.

 

"Saboda tsabar rashin hankali, ki kwanta ki yi fitsari a kwance, ke ba jaririya ba ba 'yar yaye ba" jin abin da Mama ta faɗa ne ya sanya ta miƙe zumbur, ta ganta luntsum a cikin fitsari.

 

Waro ido ta yi ta ce "Na shiga uku, wallahi na zata a mafarki ne, dan Allah kiyi haƙuri"

 

Mama cikin É“acin rai ta girgiza kai ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, zaki tashi ki fita kije ki gyara jikinki ko kuwa?"

 

Sannu a hankali ta sauka daga kan katifar, saboda yadda jikinta ko ina yake yi mata ciwo, saboda punishment É—in da Yaya Umar ya sanya ta.

Da ta fita tsakar gida da rarrafe ta ƙarasa banɗaki, ta wanke jikinta ta dawo ta canza kaya, ta jingine katifar tayi kwanciyarta a ƙasa.

 

Har ga Allah, tana jin yadda fitsarin ya matseta, amma ta ji gandar tashi, saboda bacci take ji sosai, ga kuma ciwo da jikinta yake yi, dan haka ta cigaba da baccinta, da ta ganta a banÉ—aki ta zaci a gaskene ta saki fitsarinta.

Tana jin yadda Mama ke ta mita, amma ita ko a jikinta, wani nannauyan baccin ne ma yayi awon gaba da ita.

 

Da Asuba ma an kai ruwa rana kan Mama ta samu Rumaisa ta tashi ta yi salla, dan sai da ta yi iƙirarin haɗata da Yaya Umar sannan ta tashi ta yi sallar.

Ta idar da salla Mama tayi mata maganar shirin makaranta, amma ta tura baki ta ce "Ai kina gani jiya mai sunan Baba yana azabtar da ni baki hana shi, ni bani da lafiya, ba zani ba cinyata kamar an mini É—orin karaya haka nake ji na"

 

Mama ta yi mata shiru ta cigaba da laziminta, Huzaifa ne ya fara shigowa É—akin Mama ya gaisheta, suka gaisa ya tambayi Mama mai za'a É—ora na karin kumallo?.

 

Mama ta ce "Bari gari yayi haske, sai a sayo gasara, ka cewa Yasir ya feraye maka dankali, sai a soya"

 

Huzaifa ya jinjina kai ya miƙe, har zai fita idonsa ya sauka a kan katifar Rumaisa, ya ɗan yi turus ya dubi Mama ya ce "Mama ba dai fitsarin kwance yarinyar nan tayi ba?"

 

"Gashi kuwa kana gani, ai Yarinyar nan sai addu'a kawai".

 

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, su Balama an yi asarar kunnuwa, ba sai ki saka ta fitar miki da ita daga ɗaki ba, sai ɗakin ya fara wari tukuna, abinka da fitsarin gardiya bana jariri ba, tashi shashasha" ya ƙarasa maganar yana zuba wa Rumaisa duka a ƙafa.

A gigice ta tashi zaune ta raba ido, tayi zaton Mama ce ta daketa, amma taga Huzaifa a kanta.

 

"Me nayi maka zaka dakeni?" Tayi maganar a ƙule.

 

"An dake ki ɗin, tashi ki fitar mata da wannan katifar daga ɗaki, mai abin kunya ƙatuwa da ke kina fitsarin kwance"

 

"Ba zan fita da ita É—in ba, uban shishshigi ko ina ruwanka, tun da ba a kan ka nayi ba, kuma ruwa ne ya zube ba fitsari nayi ba".

 

"Au Mama ƙarya take yi miki kenan, ba zaki tashi ba?"

 

Cikin tsiwa ta ce "Ba zan tashi ba"

 

miƙa hannu yayi, ya janyota ya ɗagata, ya ce "Wallahi sai kin fita da katifar nan kin wanke kayan da kika yi tsiyar a kan su". Idan da sabo Mama ta saba da wannan halin nasu na faɗace-faɗace, gashi Huzaifa ya bawa Rumaisa kusan shekaru shida, amma faɗa kamar suna ganin hanjin junansu.

 

Mama ta sharesu ta ƙi ko kallon in da suke, Rumaisa ta dinga turjewa tana kwarara ihu.

Basu yi aune ba suka ga Yaya Umar a tsakiyar É—akin, take suka yi cirko-cirko suna kallonsa.

 

Cikin kaushin murya ya ce "Meye haka karnuka ne ku?"

 

Suka girgiza kai a tare.

 

"Me kai mata take wannan ihun, da idon Mama bai sanya kun daina ba?".

 

"Fitsari ta yi a kwance, shi ne nace ta fita da kayan"

 

Cikin mamaki Umar ya kalleta ya ce "Fitsarin kwance kuma? Kina me kika yi fitsari?"

 

Cikin rauni ta ce "Wallahi Yaya tsautsayi ne, kasa tashi nayi"

 

"Tsautsayin uban wa? Kwashe kayan ki fita ki wanke ƙazamar banza kawai".

 

Haka ta ja katifar ta fita da ita tsakar gida, ta kwaso kayan da ta yi wa fitsari ta hau wanki.

 

Huzaifa ya faki idon Yaya Umar ya dinga yi mata dariya.

Duk wanda ya fito tsakar gida ya ga katifar Rumaisa sai ya ce me ya fito da katifar, Huzaifa sai yayi farat ya gaya musu ai fitsarin kwance ta yi.

 

Tausayinta ne ya kama Usman, ganin yadda take kuka, kuma ba ta saba yin fitsarin kwance ba, ya je ya karɓi kayan ya tayata.

Kowa da abin da yake faÉ—a a kan Ruma, wasu na mata Addu'a shiriya wasu kuma na yi mata faÉ—a har da zagi.

Tamkar gidan 'yan mata, haka zaratan samarin nan suka kama aikin gida, wasu na wanke-wanke, wasu shara da Abin karyawa, kan gari ya ƙarasa haske, hatta ruwan da Rumaisa zata yi wanka, an dafa ta haɗa ta yi wanka.

 

Haka suka jeru a tsakar gida, tare da Mama suna karyawa, Rumaisa kuwa sai shan kunun take da ƙyar tana yamutsa fuska.

Can ta kalli Mama ta ce "Mama Kununa bai ji suga ba, yayi tsami da yawa".

 

Haushi ya kama Mama ta ce "Amma a gabanki aka zazzage sugan kowa ya ɗiba ko? Kuma kin san ya ƙare"

 

Ta ture kofin kunun ta ce "Nifa dama kunun nan gudawa yake sani, gashi bai ji suga ba, ni cikina ma har ya fara ciwo"

 

Umar kawai ya girgiza kai, Rumaisa ba zata taɓa zaman mintuna goma lafiya ba, ba tare da tayi abin da za a yi mata magana ba.

Haidar ya kalleta, ya zura hannu a Aljihunsa ya É—auko É—ari biyu ya bata ya ce "Jeki wurin Mamuda ya baki buredi da suga, akwai ruwan zafi sai ki haÉ—a shayi ki sha"

 

Washe baki tayi, ta ce "Allah dai ya biya da aljanna, gadanga na Mama" ta É—au kofin kununta ta turawa Mama kunun ta ce "Mama ki shanye kunun na bar miki" tayi waje.

 

***

Da ƙyar ta ƙarasa makaranta yau, saboda ciwon cinyoyi da take yi, sakamakon horon da Yaya Umar ya bata a daren jiya.

 

"Ruma hatsari kika yi ne?" Cewar wata matashiyar yarinya sa'ar Ruman, gannin yadda take tafiya da ƙyar.

 

Ta haÉ—e rai ta ce "Me kika gani?"

 

"Gani nayi kina tafiya da ƙyar, kamar wadda ta warke daga karaya"

 

Cikin gatse Ruma ta ce "Eh, tirela ce tabi ta kaina, da ta wuce na taso na taho"

 

"A'a Allah ya baki haƙuri"

 

Duk da yadda jikinta babu daɗi, hakan bai hanata faɗace-faɗace da neman rigima ba, dan idan ba tayi hakan ba ace lafiyarta ƙalau ba.

 

Bayan an tashi ba ta tsaya ko ina ba ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da katifarta a tsakar gida kamar yadda ta barta.

 

"Mama yanzu dan Allah a nan aka bar mini katifata, sai anyi baƙi sun tambayi ba'asi ace fitsarin kwance nayi?"

 

"Au ba ke kika yi ba, ni nayi kenan?"

 

Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama ta ce "Haba Mama, kema fa kin san tsautsayi ne, rabona da fitsarin kwance tun ina jairiya, tun ban fi wata huɗu ba na daina fitsarin kwance" wani irin kallo Mama tayi mata, jin uwar ƙaryar da ta saki.

 

Mama ta ce "Tashi ki cire Uniform, kiyi wanka ki zo kiyi salla, ki tsefe wannan kan naki, ƙazamar banza da yake ban yi magana ba, baki ga dama kin mayar da kai kin tsefe ba, kuma wallahi ya kai gobe in Allah ya kaimu baki gama tsifar nan ba, sai na zaneki".

Hannu ta saka ta shafa kanta, ƙanann kitso ne a kanta, a ƙalla guda arba'in da ɗoriya, Mama ta bata kuɗi ta je ayi mata kitson hannu guda biyar, saboda ba ta son tsifa, amma ta karɓi kuɗi a wurin Yaya Usman ta je aka yi mata ƙanana.

Ta san yau ko Mama zata kwaɗanta ta ta cinye ba zata iya gama wannan tsifar ba, haka nan ta tashi ta je ta yi wanka, ta yi alwala ta saka wasu kayan. Ganin Mama ta tada salla, ta leƙa Window ta ga Usman da sallaya a hannu zai tafi masallacin juma'a, ta ɗau hijjabinta ta bi bayansa.

Sai da ta fito ƙofar gida sannan ya kalleta ya ce "Ina zaki?"

 

"Masallaci mana" ta bashi amsa.

 

"Kin tambayi Mama?"

 

Ta gyaÉ—a masa kai alamar eh.

 

Ya ce "Shikenan muje" ya sanyata a gaba suka tafi masallaci.

 

Mama ta daÉ—e tana yiwa Rumaisa Addu'a bayan ta idar da salla, kullum cikin Addu'a take yi mata, amma tana girma tamkar ana sake turata, ko alamar hankali babu a tare da Rumaisa.

 

Da suka dawo daga masallaci tana kallon Rumaisa, ba ta ce mata uffan ba, Rumaisa sai raragefe take yi, tana sauraron ko Mama zata yi mata magana amma taga ta shareta.

 

Ba tare da ta yi tsifar ba, ta ci Abincin ranarta tare da Yaya Aliyu, ya siyo kifi É—auri biyu, ya bawa Mama É—aya ya ce gashi nan duka gidan, É—auri É—aya kuma suka ci shi da Rumaisa.

 

Bayan sallar la'asar, ta É—au allonta ta tafi makarantar allo.

Tana zuwa Habiba ta tare ta da harara, tare da sheda mata cewar Sani ya ce sai ya yi mata dukan tsiya, idan ba ta biya shi tayarsa ba.

Tsaki Rumaisa tayi ta ce "To, ya kasheni ya huta mana, tayar banza da ta wofi, shi bai san tsautsayi ba"

 

A ƙufule Habiba ta ce "Au hakama zaki ce? Ki zo girma da arziki na ara miki tayar, amma ki je ki ɓatar ko a jikinki?"

 

"To tayar da kuÉ—i ya saya? Idan da kuÉ—i ya saya ya faÉ—i kuÉ—inta, yayyena su biya shi"

 

Habiba da ta gama fusata ta ce "Dalla can, uwar meye a gidan naku, banda gayyar maza da tsiya, sai ka ce wata uwar kuka ajiye, har kike a faÉ—i kuÉ—in tayar a biya"

 

"Ku kun ajiye wata uwar É—in ne, da kuna da wani abun ai babarku ba zata sayar da fanke da safe ba" Tayi maganar tana murguÉ—a baki.

 

Cikin rawar murya Habiba ta ce "Kar ki sake ki zagar mana uwa"

 

"Ni ban zagi babarku ba, ni dai na san fanke take sayarwa, fanken naku ma mai Shegiyar tsada, ƙanana kamar ƙuli-ƙuli, dan ranar Yasir ya ce har kiyashi ya gani a cikin fanken" kan Rumaisa ta rufe bakinta, tuni Habiba ta shaƙo hijjabinta, zata rufeta da duka.

Abinka dai mai nema a duhu, balle ya samu a sarari, nan Rumaisa ta zage ƙwanji ta tabattarwa da Habiba ita ɗin ƘANWAR MAZA ce.

Abin takaici da malami a gefe yana biyawa wasu allo suka harƙe da dambe.

A fusace ya miƙe ya saka bulala ya zane musu jiki, musamman Rumaisa, tsabar masifarta ya sanya baya son ta a ajinsa, kullum cikin rigima take, ga allonta sai yayi wata ba tayi wani rubutun ba, ga daƙiƙanci da surutu.

 

Idan da abin da Rumaisa ta tsana bai wuce duka ba, ta ji zafin dukan bulalar da Malam Ashiru yayi mata  ba kaÉ—an ba, dan haka ta koma gefe tayi shiru tana kuka. Ta rasa meya sanya ya tsaneta haka.

 

Habiba kuwa da ƙawayenta, suka ƙudiri aniyar idan aka tashi sai sun naɗawa Rumaisa duka saboda suna jin haushinta suma, a kan damben da aka yi a ƙofar gidan mai markaɗe ranar Alhamis, gashi ta zagi fanken babar ƙawarsu.

 

Ana tashi cike da takaicin dukan da Malam yayi musu, Rumaisa ta É—au allonta ta nufi gida, sai share hawaye take. Sai dai yau babu tsokana a hanya, babu neman magana saboda bayanta sai raÉ—aÉ—i yake na dukan da malam yayi mata, gashi ba ta warke daga ciwon jikin punishment É—in Yaya Umar ba.

Babu tsammani ta tarar da su Habiba a wani lungu suna jiran isowarta.

Turus tayi tana binsu da kallo kamar ba ta sansu ba.

 

Babu ko ɗar ta cigaba da tafiya tana yinƙurin ratse su ta wuce.

 

Shan gabanta Habiba ta yi ta ce "Ke kin isa ki tafi, ba dai ni kika zaga ba, kika kuma zagi babarmu ba, wallahi yau sai kin gane kuskurenki, kuma wallahi Sani ma ya ce sai kin biya shi tayarsa.

ÆŠaya daga cikin yaran ta ce "Ai wallahi yau sai kin daku, haka nima ranar kika zubar mini da markaÉ—e, zaki gane baki da wayo".

 

Bin su Rumaisa take da ido, sai kurari suke amma an rasa wadda zata kaiwa Rumaisa duka.

Sake yinƙurin wucewa tayi, amma Habiba ta janyo Rumaisa ta baya, yaran suka fara kai mata duka.

Tayi kukan kura, ta É—aga allonta saukewa Habiba allonta a fuska, wani uban ihu Habiba ta kurma, jin danshi a hancinta.

Tamkar namiji a filin dambe, haka Rumaisa ta zage ita kaɗai ta dinga dukan yaran nan, yadda ta dunƙule hannu tana kai naushi, kai ba ka ce 'ya mace bace.

 

Da ƙyar da siɗin goshi wani mutum ya rabasu, saboda Rumaisa akwai taurin kai, zuciyarta a bushe ana rabasu tana cigaba da kai duka.

Ta É—au allonta ta nufi gida, tana ta huci, duk da dukan da tayi musu sai dai jikinta duk yayi tsami ita ma. Dama ga jikin nata babu daÉ—i ji Sai dai kash, tuni wasu daga cikin yayyen yaran maza suka samu labari, suka yi gaba zasu datse Rumaisa a hanya, su zaneta.

 

KARANTA: Littattafan Hausa Novel Complete

Kanwar Maza Hausa Novel Page 3

'yan matasan yaran maza sun girmi Rumaisa, kuma duk da haka ƙarfin namiji da na mace ba ɗaya bane ba.

Tana cikin tafiya ta ji ana ke!ke! Ta tsaya waiwaya ta ga da wa ake.

 

tawagar yara ta gani sun nufota gadan-gadan, tana ganinsu ta san masu dukanta ne, sam bata karaya ba, maimakon ta gudu sai ta durƙusa ta fara kwasar duwatsu, ta shirya duk wanda ya kawo kai, sai ta ƙwale masa kai da dutse.

 

Amma a haka sai da wasu daga cikin su suka cim mata.

 

Sani Yayan Habiba, ya na zuwa ya kwarfeta da ƙafarsa ta faɗi ƙasa, wani danƙo ya ɗauko a aljihunsa, ya fara dukanta da shi, duka take kai masa ko ta ina da allonta har ta samu ta tashi tsaye da ƙyar a kan ƙafafuwanta.

 

Ta yi kukan kura ta kafa masa haƙora a kafaɗarsa, tsananin azabar zafi ya sanya ya kurma wani uban ihu ya ja da baya, dan har ƙashinsa ya ji haƙoram Ruma, sai ka ce mayya.

 

Ganin ta gigita Sani, wasu daga abokan nasa kuma suna fama da raɗaɗin jifan da suka sha, ya sanya ta durƙusa ta ɗauki takalminta da hijjabinta a hannu, ta tsula da gudun tsiya.

Rufa mata baya yaran suka yi, suna a taro ta, amma kamar walƙiya haka take sheƙa da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba sai da ta kai filin ball ɗin su Yaya Aliyu. Suna tsaka da ball, sai ratsa cikin ƙartin mazan nan take sai gata a tsakiyar filin da maza ke uban gudu suna ball, ta cinma Aliyu a tsakiyar filin ƙwallon ta rirriƙe shi.

 

Mamaki ne ya kama shi, ganin hijjabinta a hannu, kanta sai hula idanunta duk sun yo waje, tana ta haki tana waige-waige.

 

Riƙeta yayi yana tanbayarta lafiya? Wasu daga cikin abokansa suma suka tsaya suna tambayarta ko lafiya, amma taƙi magana sai ajiyar zuciya take yi.

 

Aliyu ya ja ta gefe, ya sanya mata hijjabinta, ya kalleta a tsanake ya ce 'Menene?" Shiru ta yi bata yi magana ba sai sauke numfashi take.

 

Haushi ne ya fara kama shi ya ce "Dan ubanki menene, me aka yi miki kika biyoni nan cikin maza?" Yayi mata maganar a hasale.

 

Fara gaya masa abin da ya faru tayi, kuka ya ƙwace mata.

ÆŠan shiru yayi sannan ya ce "Amma ina fatan baki yi kukan a gaban yaran ba?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Kin taimaki kanki, dan da kin yi musu kuka wallahi sai na ƙara miki".

 

Cikin shesheƙa ta ce "Ban yi ba"

 

Aliyu ya ce "Bari na canza kayana muje, É—aya bayan É—aya ki rakani gidajensu sai naci uban yaran nan, dani suke zancen"

 

Ya zaunar da ita a gefe, aka cigaba da tambayarsa meya sami Rumaisa ya ce musu babu komai, su cigaba da ball É—in su, shi zai tafi.

 

Su Sani kuwa tun da Allah ya sanya Ruma ta ɓace musu, suka haƙura da binta, amma suka yi alwashin sai sun kuma saka ranar da zasu naɗa mata duka, dan tayi musu ɓarna sosai.

 

Suna tafe a hanya, Aliyu ya ce "Ke amma ba a banza zan je rama miki ba, sai idan ki yadda zaki wanke mini kayan ball É—ina da takalmina".

 

Cikin hanzari ta ce "Eh na yadda, zan wanke maka"

ya ce "To shikenan"

 

Ya sakata a gaba har ƙofar gidan su Habiba, Aliyu ya aika yaro yace a kira masa Sani.

Sani ya zata a cikin abokansa ne wani yake nemansa, yana ta fama da kafaɗarsa saboda cizon da Rumaisa tayi masa, sai ka ce an sare shi da manjagara a wurin ba haƙorin ɗan Adam ba, ga Habiba ita ma sai kuka take, leɓe yayi suntum ya kusa haɗewa da hancinta, bakin yaƙi rufuwa saboda dukan da ta sha da allo a fuska, sai da bakin ya fashe, banda dukan da ta yi mata a ka da allon, da take jin tamkar an mata rawani da tukunyar ƙarfe saboda nauyin da kanta zuwa fuskarta yayi mata, ba ta iya banbance a wani sashi na fuskarta hancinta da bakinta suke.

 

Sani ne ya fito yana waige-waige, yana neman wanda ya aiko a kirashi, Aliyu yayi caraf ya danƙe shi.

Zazzare ido Sani ya hau yi, Aliyu ya ce "Kai, kaine ka tattaro abokan ka ka daki Ruma ko?"

 

Cikin fitsara Sani ya ce "Nima ƙanwata ta daka, kuma ta ɓatar mini da tayata".

 

"Kuma saboda kai mahaukaci ne, sai ka tattaro abokan ka maza su daketa, saboda baka da tarbiyya ko? Meyasa ba ka bari ƙanwarta ka ta rama da kanta ba?".

 

Fizge-fizge Sani ya fara, yana yiwa Aliyu rashin kunya, aikuwa Aliyu ya dinga kifa masa mari, har sai da bakin Sani ya mutu, fuskarsa duk tayi ja. Ya saka shi a gaba zuwa gidan abokansa da suka yi yinƙurin dukan Rumaisa.

Duk da irin É“arnar da Ruman ta musu da duwatsu, hakan bai hana Aliyu kama yaran É—aya bayan É—aya ya zane musu jikinsu ba, sannan ya saka Ruma a gaba yana rarrashinta suka tafi gida.

Ko da suka je gida, yanayin Ruman Mama ta kalla ta ga kamar ba ta da gaskiya, amma ta share ba ta kula ta ba, dan idan ta biye wa halin Rumaisa kullum sai ta daketa.

 

Da daddare bayan sallar isha'i duk suna zaune a tsakar gida, Rumaisa na ta tunanin me zata ci yau, dan yau ma maÆ™iyin na ta Mama tayi, wato tuwo, Allah ya sani yau ba ta jin za ta iya cin wannan tuwon, gashi haryanzu ranta a É“ace yake a kan abin da ya faru, dan marin da Yaya Aliyu ya yiwa Sani bai gamsar da ita ba, ji take ba zata huce ba sai ta fasa masa kai, ko ta hankaÉ—a shi kwata, ga  kuma tuwon nan da Mama tayi ya sake Æ™ara mata É“acin rai.

 

Yasir ne yayi sallama, hannunsa riƙe da leda, duk suka amsa masa, banda Rumaisa da ta yi zurfi a tunani.

In da Rumaisa take ya ƙarasa, ya jijjiga kanta ya ce "Ke tunanin me kike?"

HaÉ—e rai ta yi ta ce "Meye kuma na dakar mini kai?"

 

Yasir ya ce "To kwalba uwar sharri, ni ban dakar miki kai ba"

 

Tsaki ta yi ta ce "Ai na saba in dai ƙarya ce"

 

Dire mata baƙar ledar yayi a cinyarta, ya wuce ɗakinsu.

BuÉ—e ledar tayi ta kwance, gurasa ce fal ta masu tsire a ciki.

 

Murmushi ta yi ta É—aga murya ta ce "Na gode rabin ran"

 

Daga É—aki ya ce "Ko ba rabin rai ba, tun da na baki abin duniya ba, uwar son zuciya"

 

Rumaisa ta ce "kai dai Allah yayi maka albarka, kamar ka san ba son wannan tuwon nake ba, tunani kawai nake me zan ci? Wannan tuwon ne yake toshe mini kai bana gane karatu sosai, Allah dai ya biyaka rabin raina "

 

Murmushi Yasir yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.

 

Ya gama abin da yake ya fito tsakar gida, zamansa yayi dai-dai da shigowar dodonsu, wato Yaya Umar.

Cikin muryarsa ta ƙasaita yayi sallama.

Duk suka amsa masa, ba tare da ya kula kowa ba, ya ajiyewa Rumaisa leda da indomie ya ce "Tashi ki dafa mini" tabbas ba dan Mai sunan Baba ne ba ba zata yi ba, ita a rayuwarta tana son ko aiki zaka sanyata, ka lallaɓata shi kuwa mai sunan Baba bai san wannan ba, ya bada umarni a bi kawai ya sani mutum ya ƙi kuma jikinsa ya gaya masa.

 

Haka ta tashi ta je ta kunna wuta ta É—ora masa.

 

Rumaisa na tsaka da aiki, suka ji sallama, kai da jin yadda aka yi sallamar, ka san babu alheri a tare da mai sallamar.

Mama ta amsa tana faÉ—in maraba.

 

Jin yanayin yadda aka yi sallamar ne ya sanya Rumaisa faÉ—uwar gaba, ta tsaya cak tana sauraron abin da zai biyo baya, dan ta san babu wanda zai aikata abin da za a zo ana musu wannan sallamar a daren nan idan ba ita ba.

Mama tayi wa matar nuni da tabarma dan ta zauna, amma matar ta ce "A'a ba ma sai ma zauna ba, ai abin bana zama bane na"

 

Ɗan zuro kai Ruma tayi daga Kitchen, domin taga wacece, tozali tayi da Habiba da ƙaninta Sani.

Ita ba zuwansu ne ya ɗaga mata hankali ba, babu tantama ta san ƙararta aka kawo, amma tashin hankalin ta, Mai sunan Baba yana nan.

 

"Ban sani ba ko ke ce ki ka sanya 'yar ki ta dinga abin da ta ga dama a cikin unguwar nan, saboda tsabar rashin mutunci da rashin ta ido, ta kama mini 'ya ta daka, kalli fuskar Habiba, kuma duk da haka bai isheta ba, ta É—auko yayanta suka biyo Sani gida shima suka daka, haka ake yi fisabilillahi wallahi sai da na biya na kai ta chemist aka yi mata allura.

Dawowata gida kenan bana nan kawai na tarar da yarinya baki ya haye, ya fashe ta riƙe kai sai kuka take, shima Sani kalli fuskarsa duk shatin mari tsakani da Allah Wannan adalci ne?" Ta ƙarasa maganar tana haska fuskar Habiba. Fuska ta kumbura suntum, bakin ko rufuwa baya yi, leɓen sama ya ɗage ya kusa danganawa da hancinta, duk dadashi a waje.

Duk da halin da Rumaisa take ciki na fargaba, amma sai da ta ƙunshe baki tayi dariya ƙasa-ƙasa, saboda yadda fuskar Habiba ta koma kamar an naushi fura.

 

Jiki a sanyaye Mama ta ce "Dan Allah dan annabi kiyi haƙuri, yaran yanzu ne sai addu'a kawai, kin ga ni ban ma san tayi ba, daga ita har yayan nata babu wanda ya zo ya gaya mini, ban ma san waye ba a cikin yayyan nata ba, amma kiyi haƙuri".

 

Haidar yayi gyaran murya ya ce "Mama nine, su meyasa yaran ba a tambayesu me suka yi mata ba, hijjabi a hannu suka biyota da bulalai zasu daka.....

 

"Rufe mini baki ban tambayeka ba" Mama ta dakatar da haidar cikin tsawa.

 

Mama tayi ta bawa Babar su Habiba haƙuri, amma ba kunya babarsu Habiba ta ce "An bar yara babu tarbiyya su yi ta abin da suka ga dama, saboda tana taƙamar ita ƙanwar maza ce, sai tayi ta isakancin da ta ga dama, sai ta kashewa yarinyar fuska ta cuceni, wallahi ban da ana maƙota da sai na kai maganar wurin hukuma, dan ba zan yadda ba, ita ta dakar mini 'ya, shi kuma ya zo ya zage ƙwanji a kan ɗana".

 

Cikin muryarsa mai ban tsoro da babu alamar wasa a cikinta ya ce "Ke ya isheki haka malama, ke kamar ba uwa ba, kawai ki zo gaban mace kina cewa 'ya'yanta basu da tarbiyya, tana baki haƙuri kina cigaba da ƙanan maganganu, kar Allah ya sanya ki haƙura ɗin, ki kai duk in da zaki kai ki je ki faɗa, kuma ko yau wani ya kuma yinƙurin taɓa Rumaisa a unguwar nan, sai mun nuna wa duniya ƙanwar maza ce, fice ki bawa mutane wuri"

Mama zata yi magana, amma mai sunan Baba ya haÉ—e rai, ya girgiza mata kai, tare da nunawa Babarsu Habiba hanyar fita.

 

Jiki na rawa ta saka su Sani a gaba suka fice, duk girma da ƙanƙantar mutum, babu wanda Umar baya yi masa kwarjini.

 

Sai da ya tabattar sun tafi, sannan ya dubi ƙofar Kitchen ɗin ya ce "Ke kuma fito nan munafuka" aikuwa kamar munafukar ta fito tana sunkuyar da kai ƙasa.

 

Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Muna zaman zamanmu lafiya aka haifeki, shegiya kamar rainon iblis, duk gidan nan babu mai fita ya ɗauko magana sai ke, tana zaman zamanta kin saka an zo har cikin gida ana gaya mata maganganun banza saboda ke, kai ma saboda hauka dan me zaka biye mata ku je kuna dukan 'ya'yan mutane? Waye ya aiketa ta tsokane su?".

 

Ran Aliyu ya ɓaci, ya harzuƙa ya ce "Bafa maganar hauka a nan, yarinyar nan hijjabi a hannu suka biyota, ba dan filin ball ɗin mu na hanya ba, haka zasu haɗu su yi mata duka, yara maza ba mata ba, har sun fara dukanta baiwarsu ce ita, ko kuma ce musu aka yi ba ta da gata?.

 

"Shut up! Ita ka san me tayi musu, wannan Yarinyar da rashin jin tsiya, ai gara su zane ta gobe ba ta kuma ba, ki cigaba da zuwa ki na janyo mata magana, wallahi ba zaki É—ora mata hawan jini a banza ba, da ki cigaba da É—auko mata magana ana zuwa ana gaya mata maganar banza, gara na takeki na murÉ—e miki wuya ki mutu kowa ma ya huta".

 

Tun da Mai sunan Baba ya fara sababi, Sentence ɗinsa na ƙarshe ne ya baƙanta mata rai, wai ya murɗe mata wuya ta mutu su huta. Ta yi shiru ya gama bala'insa ya ce ta wuce ta cigaba da yi masa aikinsa, ya fice.

 

Rumaisa tana aikin tana kuka, wato ma ba'a sonta, wai da suna zaman zamansu aka haifeta, ta hana mahaifiyarsu kwanciyar hankali.

 

Usman ne yayi tsaki ya ce "Wallahi Mama É—an nan naki yana da matsala, na yi shiru ne kar na tanka masa yayi mini tijara, amma ba damar yarinya ta motsa sai faÉ—a, ke Ruma" ya kirata.

Ta goge hawayenta, ta fito daga Kitchen É—in.

 

Ya kalleta ya ce "Duk shegen da ya takaleki kar ki raga masa, ki ci uabnsa idan yafi ƙarfin ki muna nan, yaran unguwar nan marasa mutunci, ki ka zama nusara raina ki zasu yi, duk ɗan da ya miki ki ci ubansa ko mace ko namiji mun tsaya miki".

 

Mama ta ce "Zinnuraini, kai ne kake zigata ta É—auko magana?".

 

"A'a Mama bance ta ɗauko magana ba, amma duk wanda yayi mata, ta rama babu nusari a cikinmu, ƙanwarmu ba zata zama nusara ba, mu ci uban mutum ya zo kawo ƙara mu ƙara masa"

 

Martanin Yaya Usman ne ya É—an sanya hankalin Rumaisa ya kwanta, ta kammala yiwa Yaya Umar aikinsa ta je ta nemi wuri ta kwanta, ko gurasar da Yasir ya bata ba ta ci ba.

Tana kwance lamo a kan katifarta, ta ji muryar Huzaifa a kanta yana cewa ki cigaba da É—auko magana, ai gara ya murÉ—e miki wuyan ki mutu kowa ma ya huta da tijararki da rashin hankali.

Banza ta yi masa, kamar ba da ita yake ba, dan idan ta ce zata biyewa Huzaifa faɗa za suyi, kuma a kowane lokaci mai sunan Baba na iya shigowa, yadda yake a ƙule da ita ta san sai jikinta ya gaya mata, idan ya dawo ya tarar suna faɗa da Huzaifa.

 

Da safe bayan gaisuwa ba abin da ya haÉ—ata da mutan gidan, tana kwamce a É—aki, 'yan mazan suka gyara komai na gidan, suka É—ora abin kari. Ko ta kan abincin safen ba ta bi ba, ta saye gurasarta a hijjabi, ta É—au allonta ta tafi makarantar allo.

 

Sai dai ashe tuni labari ya iske shugaban makarantar su, a kan faÉ—an da suka yi jiya, malam babba ya tara su ya ce sai ya zane su.

Idon Rumaisa yayi tsilli-tsilli, dan kusa bulalar malam Babba akwai É—an karen zafi.

Kan Malam Babba ya kai ga zuwa ya yanke musu hukunci, ta zari allonta ta kwasa da gudu, ya tsaya yana ƙwala mata kira, amma tayi burus ta bar makarantar ta kama hanyar komawa gida, dan a rayuwar Rumaisa ba ta ƙaunar duka ko kaɗan.

 

A soro suka yi karo da Yaya Usman zai fita, ya tsaya yana kallonta, har zata wuce ya ce "Wai me kika dawo yi ne gidan nan yanzu, ina Makarantar kuma?"

 

Ta tura baki ta ce "Kashi nake ji shine na dawo gida"

 

Tsaki yayi ya ce "Haka dai kika iya, wannan uban cin da kike yi, ba dole kullum ki kasance cikin zawo ba, baki da aiki sai kashi da tusar tsiya" banza tayi masa ta raɓe shi ta wuce tana murguɗa masa baki, ba tare da ya sani ba.

 

Ta shiga cikin gidan tana ciccin  magani, ihuu tayi, tare da tsalle ta nufi in da wani dogon matashi ke zaune, mai tsananin kama da Yaya Umar, sai dai banbancinsu, Yaya Umar fari ne shi kuma bai kai shi haske ba, sannan shi wannan fuskarsa É—auke take da murmushi saÉ“anin fuskar Yaya Umar.

 

Babu tunanin komai, ta faÉ—a jikinsa tana murmushi.

Shima rungumeta yayi yana murmushi ya ce "Autar Mama, tun É—azu zaman jiran dawowarki nake yi".

 

"Babban Yaya, yaushe ka dawo?"

 

"Tun É—azu na dawo, nace kina ina aka ce kin tafi makarantar allo".

 

"Wayyo daÉ—i, yaushe rabon da na ganka, gaba É—aya gidan babu daÉ—i, kowa ya tsane ni, har da cewa na ishesu wai kamar su murÉ—e mini kai su huta".

 

Waro ido yayi ya ce "Wane mara ta idon ne yayi wannan iƙrarin a gidan nan?" Ta waiwaya sannan a hankali cikin raɗa ta ce "Waye banda ƙaninka, ya tsaneni wallahi".

 

Yayi murmushi ya ce "Ai ba wanda ya isa ya taɓa mini auta ina raye, ai gani a gidan na dawo".

 

Wani matashin ne ya sake fitowa, yana faÉ—in "Iya rigima, ya halinki?"

 

Sake waro ido ta yi ta ce "Yaya Abdallah".

 

Ya amsa da "Na'am uwar rikici".

 

"HaÉ—a baki kuka yi duk kuka dawo yau kenan?"

 

Abdallah ya ce "Eh haka ne, su Baba Atine suna ta gaisheki, sun ce ke ba kya zumunci"

 

Ta taɓe baki ta ce "Waye zai barni na je garin, ai ni ina son zumunci kai ni ne ba ayi" Gaba ɗaya sai ta manta da damuwarta, ta shantake suna hira.

Sai da aka jima sannan ta shiga É—aki ta ajiye allonta.

 

Sabgoginta ta shiga yi, ta zage ta ce ita zata yi wa su Babban Yaya girki, abincinta zasu ci.

Aikuwa faɗa ya kaure, Huzaifa ya ce ba zasu ci jagwalgwalonta ba su zasu yi girkinsu, ƙarshe Yaya Sadik ya ce na Rumaisa zai ci.

 

Zuwa Azahar gida ya ɗinke kowa ya hallara a falon Mama suna cin Abincin rana, Sadik sai jinjinawa ƙoƙarin Rumaisa yake ta yadda ta iya girki mai yawa haka, Huzaifa da Yasir kuwa sai kushewa suke yi.

 

Zaratan maza ne su bakwai sai Rumaisa, Mama a hankali take binsu É—aya bayan É—aya da kallo, tana tuna baya.

 

Hadiza shine sunan Mama na gaskiya, haifaffiyar garin Kano ce, unguwar mandawari. A nan ta taso tayi karatun boko da islamiyya, sai dai tana aji uku na Sakandire, ta haÉ—u da mahaifinsu Rumaisa, Muhammad Aminu a nan unguwar sabon sara, amma asalinsa É—an garin Katsina ne, yana zuwa gidan wan mahaifinsa ne a Kano yana koyan harkar kasuwanci, a nan suka haÉ—u suka yi aure, kan Hadiza ta gama makarantar sakandare.

 

Haihuwar fari Mama ta haifi tagwaye Abubakar Sadik da Umar faruk sune 'ya'yanta na fari, Sai ta kuma haihuwar Usman, sai Aliyu, Abdallah da Huzaifa, Yasir ne kawai ba ɗan ta ba, ɗan ƙanwar mahaifinsu Rumaisa ne, ta haife shi da kwana kaɗan Allah ya yi mata rasuwa, a lokacin Mama tana shayar da Huzaifa sai ta haɗa su ta shayar da su tare, ba zaka taɓa cewa ba 'yan biyu bane ba, ko ba ita ce ta haifesu ba.

Mama gaba É—aya tayi tunanin ta daina haihuwa, saboda galibi bai fin shekara biyu uku a tsakanin yaran take haihuwa, amma bayan haihuwar Huzaifa sai da ya shekara takwas, kawai ta daina ganin al'ada, sai ga cikin Rumaisa.

Tun da Allah ya sa ta haifi Rumaisa, kowa ya É—auki soyayya ya É—ora mata, kasancewarta kallabi a tsakanin rawuna, kowa babban burinsa ya faranta mata.

Mahaifinsu Rumaisa, mutum ne mai matuƙar kulawa da son iyalinsa, kasancewar Ruma ce kaɗai 'yar sa mace yafi kowa ji da ita, ba shi da magana sai ta Rumaisa, Akwai tsananin ƙauna da shaƙuwa a tsakanin Ruma da mahaifinsu, dan kusan tafi son sa a kan Mama, saboda Mama akwai faɗa, Abba kuwa lallaɓata yake. kwatsam Allah ya yi masa rasuwa tana da shekaru uku kacal a duniya, bayan yayi gajeriyar rashin lafiya.

Bayan rasuwar sa sai da Rumaisa tayi cuta kamar ba zata rayu ba, saboda alhini. Dangin mahaifin su Rumaisa suna da zumunci sosai, sun so a rarraba musu yaran su riƙe su, amma Mama ta ce ba ta son a raba nata kan yaranta, dan haka ta ce su ƙyale mata su.

Haka tayi ta É—awainiya, 'yan uwa da abokan arziki suna taimaka mata da abin da zasu iya

Tasowar Rumaisa a cikin 'yan mazan nan, wannan ya É—auka wannan ya sauke ya sanya ta taso tamkar namijin ita ma. Ba ta jin magana ga rashin tsoro, ga tsiwa da É—an karen surutu da iyayi, gashi lokacin da take tasowa girma ya fara kama Mama duk tayi sanyi, dan haka ta mayar da Mama kamar wata kakarta ba uwa ba.

Mutum É—aya take tsoro shi ne Baban Mama, Yaya umar mai sunan baban Mama, Allah yayi masa kwarjini shi ko irin wasan nan na yarinta baya yi, ba shi da abokai, ga tsare gida ba shi da fara'a ko walwala baya son shiga mutane sam, idan kaga an taka masa burki kai tsaye to Yaya Sadik ne. Mama tana matukar girmama shi saboda sunan mahaifinta da yake da shi.

Yanzu Rumaisa tana aji huÉ—u na Firamare, Abubakar yana Dutse yana karatu,  babu wanda yake da cikakken Æ™arfin É—aukar É—awainiyar gidan gaba É—aya, amma kowa babban burinsa ya nemo ya kai gida, komai suka samu mahaifiyarsu da Æ™anwarsu kawai suke tunani.

 

"Hajiya Mama, ya naga kina ta kallonmu ne kamar da baƙo a cikinmu".

 

Mama tayi murmushi ta ce "Allah nake yiwa godiya, da ya sanya duk ku ɗin nan nawa ne, Allah ya dafa muku ya ƙara haɗa mini kanku"

 

Suka amsa da "Amin"

Yasir ya ce "Mamanmu, maganin kukanmu Allah ya ƙara hore mana, mu gantataki fiye da kowace irin uwa a duniya"

 

Huzaifa ya ce "Hmm kamar gaske, nan fa kake zuwa da abin duniyarka ka hanata, ka hana kowa ka bawa waccan  yarinyar mai kama da Akushin"

 

Murguɗa baki tayi tana fari da ido ta ce "Tubarkallah zuƙul-zuƙul maye ya ci kansa da kansa, wallahi ni bana kama da Akushi, son kowa ƙin wanda ya rasa"

 

"Ke dalla ware, meye son kowa ƙin wanda ya rasa, aba Kamar gurguwar akuya" Yasir yayi maganar yana dariya.

 

Haushi ne ya kamata ta buÉ—e baki za tayi rashin mutunci, ta sanya idonta a cikin na Umar, ta haÉ—a maganar da zata yi, da lomar abincin ta haÉ—iye.

 

Suka gama cin abincin, Yasir ya kwashe kwanuka, ya fara ƙoƙarin wankewa, Huzaifa ya shigo da tsintsiya zai share ɗakin, Umar ya ce ya ajiye tsintsiyar ya bawa Rumaisa ta share.

Haushi ne Yakamata ta lura tun da aka kawo ƙararta ya tsaneta, dama can ba wani shiga shirginta yake yi ba.

Bayan ta kammala sharar ta nemi wuri za ta kwanta Mama ta kalli kan Rumaisa, da ta fara tsifa, tayi rabi ta bar rabi ta ce "Fita ki bar mini É—aki, karki sake shigowa sai kin gama wannan tsifar.

 

Fitowa ta yi ta na tura baki, tana nema ta yi kuka.

"Autar Mama, meya ɓata miki rai ne?" Cewar Yaya Abubakar da yake ƙoƙarin shiga ɗaki.

Dama ƙiris ta ke jira, dan haka ta fara kuka "Ba mama ce ta koreni daga ɗakinta ba, wai sai na gama tsefe kaina ba, ni mama ta tsaneni".

 

Girgiza kai ya yi ya ce "Yi haƙuri ki daina kukan, bari na zo na tayaki tsifar"

Haka suka zauna ya samu kibiya ya tsefe mata kan tsaf, suka wanke gashin, ya ce da safe zai bata kuÉ—in kitso.

Mama ta na kallonsu ba ta kula su ba, ta cigaba da sabgoginta.

 

Abdallah yana ta dube-dube a kitchen, ya ci karo da allon Rumaisa, duk gefensa ya karye, ga rubutun jiki yayi baƙi ƙirin, ba ta sake wani ba.

Ya fito da allon a hannunsa ya ce "Ruma, wannan allon naki yaushe zaki yi wani rubutun?" Ta haÉ—e rai ta ce "To ban iya ba, sai na iya zan wanke".

 

"Haka dai, ba kya ja a ko ina, daga arabin har bokon, Allah ya sa su zaneki idan ki ka je sati mai zuwa, baki wanke allon kin yi wani rubutun ba, gandamemiya da ke amma haryanzu a izifi biyu ki ke"

Sai da yayi wannan maganar ta tuna yadda malam Babba ya dinga ƙwala mata kira amma ta gudo gida, yanzu sati mai zuwa ta yaya zata je makarantar allon? Kuma muddin abin da ta yiwa malam ya zo gidan nan, ta san ta kaɗe".

 

"Astagfrillah, ni 'ya su meyasa haka ne, garin in gujewa wani hukuncin sai na faÉ—a wani tarkon, ya zan yi da raina?

KARANTA: 

Post a Comment

0 Comments