Noor Albi Hausa Novel by Mamuhgee
Bismillahir-rahmanir Raheem
Kokarin komawa ta zauna Kan kujerar robar Dake gaban
wheelchair dinda mahaifinta yake zaune akai tayi bayan ta aje cup din data Gama
basa magani abaki Kan qaramin table din Dake gurin ta dago idanuwanta ahankali
cikin nutsuwa ta kallesa batareda tace komaiba ta tsawon mintina biyu kafin ta
Dan motsa Bakinta cikin wata nutsuwar ta sakar Masa murmushinda yake narkarda
zuciyarsa da tsananin tausayinta da qaunarta Dan kuwa yanajin radadi da zafin
dukkanin murmushinta Wanda yariga yasan ba komai cikinsa face damuwa,
kadaici,maraici da rashin uwa dakuma rashin uba dukda shi uban gashi a raye
Amma tamkar baya raye yake Dan baida wani abun dayake iya yimata bayan nuna
Mata zallar qaunarta daga zaune sai kwance.
Ganin irin kallon dayake matane Wanda koyaushe yake nuna
gazawarsa amatsayi na uba
Ita Kuma Bata taba yimasa kallon ya Gaza din sbd tasan hakan
qaddararsu ce su duka tun daga kan mahaifiyarta da Bata Raye har Momy wadda
take ganin itace tafi cutatuwa ato kowane bangare na rayuwarsu.
Sauke idanuwanta tayi daga kallonsa tareda Kai hannu ta zari
tissue Mai Dan yawa tahau goge Masa gefen rigarsa da ruwan maganin masu kala
suka zuba ta sauke siririn numfashi ahankali ta bude Baki ta furta"
Abba!!
Kadaina kallon kanka da yanayinka amatsayin ka cancanta
hakan sbd abunda yafaru,
Kadaina kallon kanka amatsayin Wanda ya lalata rayuwar yarsa
yakasa Mata komai bayan Kaine komai nawa,
Nice rabon haihuwata da zuwana duniya ya tarwatsa kwanciyar
hankalin rayuwark......
Rintse idanuwa da yayi cikin Jin dacin zancenta yayi
daidai da dafata da akai da hannuwa biyu a kafadarta Dan hanata qarasa zancen.
Ahankali ta sauke ajiyar zuciya batareda ta dagoba
ta Dan sake sauke numfashi Mai sanyi da rashin sauti kafin
ta waiwayo da kyakkyawar fuskarta
idanuwanta basu sauka Kan Yar uwarta Kuma Antynta data
dafata sai akan Momy suka fara sauka wadda ke tsaye bayan Anty SA'ADAH din
kyakkyawar fuskarta ta Kamar yanda tasanta tun tashinta a daure Babu sakewa
Babu fushi sai yanayinta dake sake nuni da har lokacin kallon Rabon daya lalata
rayuwarta data yarta take Mata.
Ahankali ta dauke kallonta daga kanta tana Mai Dan Sunkuyar
da kanta ahankali tareda miqewa tsaye daga gurin ta raba gefen Anty
Sa'adah ta koma bayanta ta tsaya cikin tattausan muryanta batareda tasake
kallon momynba cike da biyayya tace"
Barka da safiya Momy.
Kamar yanda tasani tun tasowarta harzuwa shekarunta na yanzu
datake dasu Momy Bata taba amsa gaisuwartaba wanda hakan sabone agareta Kuma
baya damunta Kamar yanda ko so daya Bata taba tsallake ranar gashetaba Dan kuwa
Bata taba ganin laifi ko Jin haushin momynba,
Kallon uwa Kuma mariqiya take Mata tareda wani girmanta Mai
tsanani datake gani.
Qarasowa cikin palon gabaki daya momyn tayi cikin tafiyar
nutsuwa ta Isa Kan kujerar dake gurin ta zauna sai alokacin ta kallesa dakyau
murya natse tace"
Barka da safiya!
Shiru sukayi dukkaninsu sbd sanin ba wani iya mgn Abban
keyiba musamman da kwana biyun jikin nasa ke Dan sake rikicewa duk da tsawon
shekaru masu yawa daya debo daga zaunen da kwancen.
Saida yamata kallon mintuna kamar yanda yasaba yimata kullum
kafin ya iya daga kansa ahankali cikin wani irin yanayi na sanyi da jikin
dayake Dan ji.
Numfashi Mai sanyi ta sauke ahankali kafin ta dauke kallonta
daga kansa cikin sanyin murya tace"
Dr Abbakar yakira akan Yana hanyar qarasowa kana tunanin
hakan zai.....
Dakatawa tayi da maganar Tareda yin shiru kafin ta Dan
waiwaya ahankali ta kalli inda Sa'adah ke tsaye batareda tace komaiba
Suna ganin hakan suka nufa kofa itace agaba jikinta na qara
bayyanarda sanyinta Amma taurin zuciyarta na sake boye hakan.
Kai tsaye dakin anty Sa'adah din Sa'adahn ta jata suka shiga
ta nuna Mata bakin gado da ido tana cewa"
Zauna anan Ina zuwa.
Fita tayi ta nufa kicin ta duba abincin da akai Karin safiya
dashi taga sauran doyar Dake cikin kular da alama ba'aciba
Ta dauka plate ta zuba Mata farar doyar tareda soyayyar jar
miyar dataji albasa ta bude Dan qaramin fridge dinsu daya Dan tsufa Amma Yana
aiki ta dauko Mata pure water daya masu sanyi ta nufo dakin ta qarasa har
gefenta ta zauna ahankali tareda Kiran sunanta cikin tattausan lafazin dake
nuni da irin tsananin son datakewa Yar uwar tata Wanda bayan Momy data haifeta
Babu Wanda takeso kamarta.
*_LAYLAH_* Takira sunanta cikin kulawa da sautin Mai Dan
girma Kai tsaye tace"
Ahakan Zaki zama likitan kina skipping lokacin cin abinci?
Cinye ki tashi kije ki gyara palon Abba kafin baqinsa suzo.
Kamar yanda yake dabiarta dagowa tayi ta kalli Anty Sa'adah
din kadan tareda Dan yaqen guntun murmushi tana daukan plate din tafara cin
abincinta a natse.
Qura Mata ido anty Sa'adah tayi tana qarewa kyakkyawar
fuskarta zuwa yanayin sanyi da nutsuwarta kallo,
Duk yanda kakai qarshe da sanin halin mutum da yanayinsa
bazaka taba iya gane halinda zuciyar *_ZAINAB LAYLAH_* take cikiba,
Yarinyace Mai tsananin zurfin ciki da wata irin juriya da
tawakkali,
Bata bayyanarda fushi ko bacin Rai,
Batada hayaniyar da zaka Kuma gane farin cikinta
Abu daya ke bayyanarda halinda zuciyarta ke ciki ko
yanayinta shine murmushinta Wanda shine abinda ke bayyanarda zallar 'dacin
datake ciki.
Mahaifinta yayi auren sirri da Yar uwar dangin nesa sosai ta
Babban amininsa da baida tamkarsa sun taso tare sun girma tare tarin
Arziki,suna da daukaka ya rage kusancinsu sbd nisa da aminin nasa yai Masa
bawai Dan sun rabu ba haryanxu suna tare matuqar Aminin nasa Yana qasar,
Yayi auren sirri ne da Yar uwar dangi ta Aminin nasa
batareda sanin matarsaba wadda dukkanin yardarta,soyayyarta,kaunarta da gatanta
suna kansa sbd tsananin yardarta dashi dari bisa dari,
Bata taba zarginsaba ko kawo tunanin zai iya cin amanarta ko
ha'intarta takowane bangare musamman sbd sunada 'yarsu daya tak dasuke tsananin
so da kauna Sa'adah.,
Saida ya shekara shida da auren ZAINAB cikin sirri Da
tsananin so da kauna Mai qarfi da baya iya rabuwa da ita kafin Allah yabata
cikin dayayi sanadiyar fitowar auren.
Batada labarin aurensa saidai tasamu labarin hadarin daya
samu Mai tsananin gaske akan hanyarsa takai Matar asibiti tana nakuda a jahar
daba tasuba,
Akaron farko da wani babban alamari ya jijjiga izzarta
datake ganin tanada ita a zuviyar mijinta duk wata yardarta da soyayyarsa ta
rushe tareda wani irin kunci daya cike zuciyarta tsawon shekarunda take dakonsa
har yanzu,
Batasan auren mijintaba saidai gawar matarsa tagani da
lafiyayyar jaririya da aka bar Mata wadda kallo daya takasa Mata sbd batason
shedan ya ribaci zuciyarta ta cutatarda 'dan kowa,
Bata taba son 'yar ba wadda taci sunan mahaifiyarta Kuma
sunanta wato *ZAINAB*
Bata taba sontaba kamar yanda Bata taba Jin qintaba,
Bata kallonta sbd kada ta cutatar da ita,
Ita ba jahila bace tasan Babu haqqi akan yarinyar na
abundaya faru saidai Kuma takasa Hana zuciyarta yimata kallon Itace asalin
dalilin tarwatsewar rayuwarsu duka sbd rabon haihuwartane yayi sanadin komai,
Tun accident din abban yarasa qafafunsa a zaune yake cikin
kujera daga zaune sai kwance tsawon shekarunda sukaja masu tsayi sosai,
Bai taba ganin laifin momy ba Amma Kuma Bai taba daina
rokontaba daga kwancen akan ta samu wani fili kadan a zuciyarta da zata saka
Masa Laylah sbd batada kowa saishi shikuma Haka tasa qaddarar tazo baida wani
Abu dazai iyayi Mata amatsayin uba,
Rayuwar Laylah rayuwace Mai cikeda zallan kadaici da
maraici,
Tunda tafara wayo taga yanda Momy Bata taba kallontaba bare
amsa ko gaisuwarta Amma Kuma Bata taba hantarartaba saita taso cikin juriya da
rungumar rayuwar ahakan tareda yarda da cewa tabbas itace sakamakon cin Amana
da haincin da akaiwa Momy Wanda ya rusa rayuwarta da kwanciyar hankalinta na
gidan aurenta Dan kuwa tun lokacin Momy ta Rasa miji tunda yakoma baida wani
amfani agareta da yarta tun daga kan auratayya har Kan sauran haqqoqin.,
Da wannan zuciyarta take kasa Jin 'dacin Momy sbd takowane
sashe tabbas itace mummanar qaddarar data Bata rayuwarsu shiyasa ta sadaukar da
kanta da rayuwarta gurin bautawa Momy da anty Sa'adah ko zata iya biyansu ta
wani sashen da abinda abbanta da mahaifiyarta da Bata Raye sukai musu,
A rayuwarta cinta da Shanta tareda karatunta momynce ta
dauka nauyi abisaga aikin wahalar datake musu tun bayan data girma aka sallami
Mai aikin data raineta harta girma ragamar aikin gidan tadawo hannunta tun daga
kan girki da tsaftar gidan,
Sam rayuwar Momy a baude take wanzuwar laylah a rayuwarta
sbd tuni ta Rasa annashuwa da dariyarta harma da murmushinta,
Rayuwarta Takoma ta wata irin cunkusashiya kasancewarta
cikin mutane masu tsananin riqo a zuciya shiyasa duk tsawon shekarun Bata
tabajin sassaucin abunda takejiba akan al'amarin.
Babban abunda yake tattareda rayuwar Layla na nutsuwa da
kwanciyar hankali shine tsananin kauna da soyayyar da mahaifinta ke Mata Mai
tsanani da wadda 'yar uwarta Anty Sa'adah ke Mata Dan kuwa anty Sa'adah itace
gatanta a fili da boye sbd itace ta tsaya Kai da qafa agurin mahaifiyarta ta
roqu alfarmar bawa laylan damar karatu bisaga neman alfarmar zata karba ragamar
aikin gidan,
Da wannan Laylah tasamu tayi karatu a makarantar gwamnati
Mai dama dama harta samu ilimin bokon datake dashi sabanin ita Sa'adah datai
karatun private school Mai kyau,
Anty Sa'adah ce gatanta a duk abinda ya danganci haqqin dake
rataye akan iyayenta na kula da ita shiyasa koyaushe Abba ya bude idanuwansa
akan Sa'adah yake Mata godiya cikin ganin qimarta itada momyn sbd koma yayane
da dukiyar momyn Sa'adah ke yiwa Laylah hidima Wanda itama momyn rufin asirine
kawai na 'yar kasuwancin buga buga datake Dan tallatawa rayuwar yarta da abban
da yarsa dasuka zamar Mata wani babban jarabawan rayuwa.
Mahaifiyarta ta rasu tabarta a ranarda ta haifeta Dan Haka
batasan wani shaquwaba ko sake tayi Wasa tareda wani,
Mahaifintane Kuma kwance ta bude ido tagansa,
Anty Sa'adah Kuma kallon wadda ke tallafe da rayuwarta take
Mata duk da a zuciyarta matsayi da girman kaunar datakewa anty Sa'adahn daban
ne.
#MAMUH#
NOOR ALBI
Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama
jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin
mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda
sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya
zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon
'da amatsayin nata mijin?_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda
soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da
shauqinsa na musamman ne_
NOOR ALBI 3
Tana zaune tsakar gidan tsaye bakin kicin tana wanke hannu a
fanfo Dr Abbakar yafito ya fice Tai Masa asauka lfya cikin biyayyarta
Ya amsa Mata cikin kulawa shima ya fice.
Qarasa wanke hannayenta tayi sbd miyar abincin da anty
Sa'adah ta zubar a Palo batareda sani ba tagama kashewa shine take wanke
hannun,
Kofar palon abban ta nufa Kai tsaye tashiga da sallama
Har lokacin Yana yanda Dr Abbakar yafita yabarsa cikin
zurfin tunanin abinda ke addabar zuciyarsa da shawarar dayake nanatawa kansa
akan ya yanke Dan inganta rayuwar yarsa ko baya Raye ko Yana raye
Tabbas idan tana qarqashin inuwar Amininsa Kuma Aminin
mahaifiyarta zata samu gata da kulawa tareda samun Amintacciyar rayuwar
kwanciyar hankali.
Kai tsaye gurinda flask din abincinsa yake ta nufa tafara
daukan flask din ta bude wani tiririn zafi da qamshin kunun alkama da gyada ya
ringa fitowa daga ciki
Ta dauki dauki cup daya cikin cups din Dake gurin wainda aka
Ware musu aka Bata na Abban
Ta tsiyaya kunun Mai Dan yawa aciki kafin ta maida sauran ta
rufe ta dauki kofin ta baro gurin bayan ta jefa cokali aciki tana juyawa
ahankali ahankali Dan ya huce ta nufi gurin Abban tana kallon yanayinsa da a
fili qarara yake nuna yayi nisa a tunani.
Aje kofin tayi tafara tura kujerarsa zuwa bakin windo bayan
tasake yaye musu labule sbd iska Dan yanzu tana basa kunun zufa zai taso Masa.
Janyo tata kujerar tayi ta zauna gabansa tareda aje tissue
gefensu ta dago fararen idanuwanta ta kallesa cikin kulawa shima ita yake kallo
Ahankali tasaki wani irin murmushin dayasa Abban rufe idanuwansa ahankali sbd
murmushinta bakomai yake bayyanawa ba sai zallar tausayinta.
Saida ta tabbatarda ya huce ba zafi kunun ta dauka tafara
basa ahankali da spoon ta nufa bakinsa,
Sam bayajin yunwar Shan komai ayanzu sbd damuwar dayake
cikinta sosai,
Jin inda lafiyarsa ta dosa ya wargaza duk wani Dan sauran
qwarin gwiwarsa da dukkanin jarumtarsa
Tunaninsa 'daya yanzu yanda zai Fadawa *_TURAKI_* buqatarsa
Dan kuwa wannan babban abune Mai girma zai roqa agurinsa duk da girman banbanci
masu tarin yawa dasuke cike a tsakani.
Sbd kawar da sabuwar damuwar da hanata shiga wani sabon
halin yasa hakanan take basa abincin Yana sha tanayi tana goge Masa da tissue
ahaka yakesha har
sukai nisa yakusa shanyewa.
Cikin nutsuwa ta Dan kallesa kafin ta bude Baki kamar ko
yaushe da taqaitaccen sauti tace"
Koma menene sakamakon asibitinka
Bana cire Rai ga falalan ubangiji akan samun sauki da
lafiyarka.
Karka saka sabuwan damuwa
Ko ahakan Ina godiya ga ubangiji daya bani ikon tasowa nayi
rayi rayuwa da mahaifina.
Kallonta yake da idanuwansa dasuke jajir har lokacin
zuciyarsa na sake zurfafa da tunani.
Tas tagama basa kunun ta dauko maganinsa shima tabasa kafin
ta goge Masa ta dauko wani Dan turarensa da baya yanke musu Abdullahi ke siyowa
ta 'dan fesa Masa kadan sbd abdullahi din yamasa wanka kafin zuwan dr Abbakar
Tana gamawa ta fice Dan yau tana Dan da ayyuka
Ga wankin Momy ma ta Tara gwara na anty Sa'adah ta rage Mata
jiya tayi abunta da kanta.
Harta fita Jin zafi a garin yasa tadawo ta turo kujerarsa ta
fito dashi tsakar gidan Dan Tasha iska musamman dayake yamma tafarayi ba rana.
Wankin kayan Momy tafara a natse sai kayan anty Sa'adah
kadan Wanda anty Sa'adah din Bata qarasa ba jiyan tana cikin Yi anty Sa'adah ta
fito ta zaune gefen Abban daukeda takardunta na makarantar jami'a datakeyi tana
karatu Dan tanada test a satin.
Sama sama take karatun tanayi tana Jan laylan da surutu duk
da tasaba Laylah ba wani surutun zataiba musamman ma datake aiki Amma dai Haka
sukeyin surutun sama sama tana yiwa Laylan bayanin wasu abubuwan dake cikin
handout dinta tunda ita Layla Bata karatu tunda tagama secondary School last
year shikenan iya inda nata karatun zai tsay kenan Kuma
Dan Momy tariga tafadawa Sa'adah da Abban hakan,
Bazata iya qarawa daga Nan
Tayi iya abinda taji zata iya
Idan akwai Wanda zai iya daukan karantun nata acikinsu biyun
bismillarsu zasu iya dorawa daga Nan,
Shi dai Abba yasan baqar maganace tafada Masa Amma ko ahakan
ya gode Mata Dan Koda laylan makarantar datai ta gwamnati ce yaga alamar tasamu
ilimin Dan Haka shi ahakanma ya gode matuqa.
Sallamar momyn ce data dawo daga fitar datai tasaka Anty
Sa'adah kallon kofa ita Kuma Laylah sauke kanta tayi qasa tana cigaba da wankin
sbd sanin fuskartace abinda yafi komai tada zafi da ciwon Dake qunshe cikin ran
momyn na shekaru yasa so da dama ita da kanta take dauke kanta da duk inda
momyn zata kalleta din.
Kallon abban Dake zaune zugum idanuwansa a rufe yanajinsu
sbd ganin yanda rayuwar yaransa biyu takeda banbanci Mai girma.
Direct Palo take neman shigewa Sa'adah tace Mata"
Momy zafi ake sosai fa gashi kin dawo kilama kin gaji.
Matuqar Laylah ko abba na guri bakajin muryarta cikin sakewa
ko walwala Dan Haka batareda ta juyoba ta qarasa ciki tana cewa"
Bari nayi sallar la'asar saina fito ai.
Tana shigewa ciki Laylah ta tsame hannuwanta daga ruwan
wankin ta dauraye tareda gogewa ta miqe taje ta dauko babbar daddumar da momyn
ke zama akai ta dawo ta Kama kujeran abbanta ta matsar dashi gefe kusada ita
sosai kafin ta shimfidawa momyn daddumar ta dauko Mata ruwa da abincinta duk ta
aje Mata akai kafin ta koma ta juyarda kayan wankinta dayan gefen tana
fuskantar abbanta sbd bawa momyn baya kamar yanda yake tun yarinta.
Wankinta taci gaba dayi har lokacin Sa'adah na janta da
labari Amma tunda momy ta fito tayi tsit bayan motsin wankinta Babu abinda ke
tashi sai qarar cokalinda momyn kecin abinci
Sa'adah ma datasan Laylah bazata Kuma maganaba Kuma saitayi
shiru tamaida firarta gurin momyn.
Kusa rayuwar gidan gabaki dayansu Sa'adah ce kawai wadda
Allah yabawa ikon gudanar da rayuwarta cikin walwala da sakewa tareda
wadataccen kwanciyar hankali da nutsuwa harma da farin ciki sbd Sam bata dauka
komai tasakawa rantaba,
Abban nema so da dama batada shaquwa dashi Sam Sam sbd farko
datana yarinya abunda yafaru yaso cusa Mata tsanar mahaifin nata Amma Kuma
qaunarta da 'yar uwarta da batada kowa saishi dakuma yanda shima Bai boye
qaunar Laylah din ba ko a idanuwansa yasa takasa riqe komai aranta saima Suka
dawo tausayinsu yayi rinjaye akan Jin zafin cin amanar da yayiwa momynta da
mahaifiyar Laylah din Dan Haka tana qaunarsa saidai ba wani shaquwa a tsakaninsu
musamman dayake Mata kallon wadda sbd itane mahaifiyarta take taimakonsu take
riqe dasu duk da hakan ta wani bangaren itama Yana farin ciki da ingantacciyar
rayuwar farin ciki da kwanciyar hankalin datake.
Sai gab da magriba tagama wankin lokacin tuni Momy tayi
baquwa suka shige ciki Dan hakama wankin nata yayi sauri cikin tayita tashi
kaiwa baquwar momyn ruwa da abinci.
Jin anfara Kiran sallar magriba yasa ta aje shanyar datake
ta goge hannuwanta dasukai sanyi ta nufi gurin Abban da idanuwansa suke zuru
dan dama hakan suke rayuwar kullum.
Maidasa ciki tayi tasaki labulai sbd sauro tana kokarin
fitowa saiga abdullahi yashigo tace"
Anyi sallah Yaya abdullahi shima Abban sai yayi.
Eh dama shine nashigo Dan dubawa.
Ficewa tayi shikuma ya qarasa ciki yaja Abban zuwa toilet
din dake dakinsa Dan Koda Abban na buqatan toilet.
Har aka gama sallah Bata Gama shanyarba Saida aka sallame
tagama ta tattara gurin ta share ta tsaftacesa ta watsa ruwa tayo tata alwalar
ta nufi ciki ta wuce dakinta direct tasaka wata baqar jallabiya ta tada sallah.
Bayan tagama sallar dakin Anty Sa'adah taje ta dauka Qur'an
ta nufi palon abbansu ta zauna gefensa tafara karatun al qur'an din cikin
zuciyarta har akai sallar ishai anan palon tayi sallah bayan tagama taga alamar
shima sallar yakeyi Dan Haka Kai tsaye ta nufa abincinsa ta zubo ta tareda zuba
Masa ruwa a wani kofin ta daukosu tareda magani tadawo gabansa.
Tana Gama basa komai ta gyara Masa koina abdullahi yazo ya
daukesa daga kan kujera ya maidasa Kan gadonsa Tai Masa addua ta fice shima
abdullahin tare suka fito taja Masa kofa.
gurin Anty Sa'adah ta nufa Dan karatun dare datake koya Mata
na littafan addini.
Acan takai kusan karfe goma na dare suna karatun kafin ta harhadawa anty Sa'adah dakin ta gyara Mata shimfidar gadonta dasuka zauna Baki taje ta dauko Mata ruwan dare datake yawan tashi Sha ta aje Mata kafin ta fito taje ta rufe gidan da koina ta nufi nata dakin tayi Shirin kwanciya tayi addua ta kwanta.
Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama
jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin
mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!
KARANTA: Zafin Kai Hausa Novel Complete By Mamuhgee
NOOR ALBI 2
Ajiyar zuciya anty Sa'adah ta sauke lokacinda taga laylan na
aje plate din gefe daya alamar ta koshi
Ta dauki ruwan dake da sanyi sosai
Saikuma ta maida ta aje Dan batashan ruwa Mai sanyi sosai
sbd lafiyarta na daya daga cikin abubuwan datake kiyayewa badan kantaba sai Dan
kula da Abban da gidan gabaki daya Dan kuwa idan ta kwanta ciwo komai cak yake
tsayawa a gidan duk da ba wani babban gida bane ko gidan taro su kadaine agidan
Wanda yakeda iya nasa girman na masu rufin asiri.
Miqewa tsaye tayi batareda ta kalli Anty Sa'adah ba ta nufi
kofa daukeda plate din da ruwan cikin sanyi tana cewa"
Zanje nafara aikin abincin Rana
Lokaci yafara ja.
Ficewa tayi tabar Anty Sa'adah na bin bayanta da kallon
Kamar koyaushe cikin jin qauna irin ta jini dakuma tsantsar burgewa da laylan
ke Bata akoda yaushe Dan kuwa Babu abinda Layla ta baro mahaifiyarta tun daga
kalar fatar,da jikin,da tafiyar dama sanyi da nutsuwa Wanda hakan kesa Koda
mugun kallo Momy Bata kaunar kallon fuskarta sai da dalili Wanda kallo daya
take Mata ta dauke Kai,
Ita kanta anty Sa'adah so daya taga fuskar mahaifiyar Laylah
Shine lokacinda sukaje asibiti tareda momyn da aka Kira
cewan Abban yasamu hadari aka kaisu har gadon mahaifiyar Laylah alokacinda ta
haifeta,
Kallon mintuna masu tsayi Momy tayiwa ZAINAB da jaririyarta
kafin suka juya suka fice Bata sake ganin fuskarba har yau saidai Akan fuskar
Laylah.
Wayarta ta dauko ta Danna Kiran umma Jamila yayar Momy Wanda
ke ji da Sa'adah din itama Kamar itace ta haifeta sbd ita Bata taba haihuwaba.
Dan madaidaicin kicin dinsu ta Isa ta ajiye plate din
hannunta tareda Dora ruwan data dawo dasu akan fridge su huce kafin tasha
Ta tattara kayan da akai amfani dasu tafara wankewa cikin
Dan sauri sbd lokaci yaja Mata sosai.
Tana gamawa ta goge kayan ta saka a kwando ta dauko tukunya
ta kunna lafiyayyan risho dinsu babba ta Dora abincin Rana ta fito ta nufi
palon gidan Wanda yake daukeda dakin Momy a gefe saina anty Sa'adah a gefensa
sai nata daga can gurin hanyar fitowa palon.
Tsaf tagyare palon ta nufi dakin Momy ta gyaro takoma dakin
anty Sa'adah ta gyara kafin ta fito ta nufi palon abbansu Dake dayan gefen tashiga
da sallama duk da tasan suna daga kurya Momy na magana dashi Wanda sai babban
al'amarine kesa Momy magana dashi Dan haryanxu babu Wanda yasani akan akwai
aure tsakaninsu haryanxu kokuwa zaman rufawa Kai asiri suke? itadai abinda
tasani a gidan shine zaman alfarma take.
Gyaran palon takeyi cikin nutsuwa saiga momyn ta fito ta
fice har lokacin Bata dagoba Saida tagama gyarawa kafin ta nufi dakin Abban da
sallama idanuwanta akansa ta qaraso tafara gyaran dakin duk da Babu inda dauda
ko rashin tsafta yake a dakin kullum tana gyarawa hakama kullum sai Abdullahi
yazo yayiwa Abban wanka da wasu abubuwan tareda wankin kayansa.
Daga zaunen dayake kansa a langabe gefe ya zuba Mata ido
cikin yanayin Mai tsananin 'daci da damuwa tareda tausayinta Mai tsanani,
Akan idonsa 'yarsa da zainab ta taso cikin bauta da rashin
walwala,
Ta taso cikin kadaici da maraici,
Badan Sa'adah ta tallafi rayuwarta ba da zuciyarsa bazata
iya kawo yanzu tana daukan tsananin baqin ciki da damuwarta ba
Shiyasa har abada bazai daina godewa Sa'adah da momyn ba ko
Yayane dai sun tallafa rayuwarta alokacinda baya iya tsinana Mata komai
amatsayinsa na mahaifinta...
Saidai babbar gagarumar damuwarsa shine shin wane Hali zata
shiga idan babusa?
Tayaya zatai rayuwa Kamar kowa tasamu farin ciki?
Ya tabbatarda rashinsa zai qarasa juyarda duniyartane gabaki
daya sbd har abada zata qare a bauta da wahalar gidan Dan kuwa kowane lokaci
Sa'adah Dake tallafarta zatai aure ta tafi tabarta.
Hawayene suke bin gefen fuskarsa suna gangarowa zuwa kan
kafadarsa da kayansa
Zuciyarsa na tsananin quna cikeda damuwa.
Ajikinta taji kukan mahaifin nata
Ta waiwayo ahankali a natse ta kallesa da idanuwanta da ako
yaushe suke hasko Masa mahaifiyarta ya rintse ido hawayensa na tsananta gudu
alamar kukane Mai tsanani yakeyi na zuciya Dan baida lafiyar fitar sautin kukan
ne.
Qarasowa tayi gabansa a natse cikin sanyi ta zauna tareda
Dan sauke kanta qasa tsawon mintuna batareda tace komaiba,
Tissue dage gefe ta zaro guda uku ta dago fararen idanuwanta
dasukai ja take batareda hawaye sun taru cikinsu ba kokuma suka gangaro ta
zubawa Abban takai hannu ahankali tafara share hawayensa Wanda hakan yasa
hawayen nasa Suka sake barkewa ba kakkautawa,
Yanajin radadi da zafin Zuciya ba damar furtawa kokuma
bayyanawa,
So yake ya bude Baki yasaka Mata albarka tareda Bata hakurin
yanda quruciyarta da yarintarta take neman qarewa agurin dawainiya dashi.
Batace komaiba sai share hawayensa datakeyi ahankali tana
kallonsa
Yasan bazatai maganaba sbd Yana iya hango tsananin dacin da
zuciyarta ke cikk a ganinsa hakan
Dan Haka yafara kokarin danne kukansa Yana Dan sauke kansa
daqyar sbd wani lokacin kasa kallonta yakeyi sbd nauyi duk da Yana matsayi na
uba.
Ahankali ahankali take qarasa goge hawayensa har zuwa Kan
rigarsa Sama sama cikin nutsuwa.
Damqe tissue din tayi a tafin hannunta bayan ta Gama goge
Masa ta sake dagowa ahankali cikin sanyi da nutsuwa ta kallesa tsananin
qaunarsa na bayyanuwa akan fuskarta ta bude Baki a natse tace"
Har abada bazan daina sake fada maka ba laifinka bane,
Qaddararmu ce mu duka ahaka,
Allah Bai dauki ran mahaifiyataba sbd wannan al'amarin
Ya karba ranta ne sbd lokacinta yayi,
Kadaina kallon kanka a matsayin uba daya Gaza,
Kallonka ko ahaka Yana bani nutsuwa da qarin qarfin
tawakkali ga ubangiji.
Ka cire damuwar yanayin zamana da rayuwata sbd ban taba
ganin laifin kowaba agame da hakan,
Idan Dole anason ganin laifin wani
Nice Mai laifin,
Sbd rabon haihuwata ne,
Rabon zuwana duniyane yaxo ta hanyar tarwatsa rayuwarku ku
duka,
Ahakan har abada bazan taba daina yiwa Momy addu'a ba sbd
koma yayane Bata barni nayi rayuwar titi ba ta barni Ina rayuwa a qarqashin
inuwarta data 'yarta
Hakan ma ya isa ka godewa Allah.
Rintse idanuwa yayi Yana Dan daga Mata hannu kadan akan ta
Kama.
Kama hannun nasa tayi ta damqe Suka sauke ajiyar zuciya
atare kowanne Yana kallon Dan uwansa.
Saidataga yadan kawar da damuwar kafin ta saki hannunsa ta
qarasa gyara dakin tadawo gabansa ta dauki ruwa ta zuba a cup takai bakinsa
tana basa
Wasu na shigewa wasu na zubowa tana gogewa da tissue.
Tana Gama basa ruwan tasake goge Masa jiki kafin ta fice
daga dakin ta koma kicin gurin aikin abincin data Dora.
Qarfe daya da rabi tagama komai tasake gyara koina kafin ta
nufi dakinta Dake da Dan qaramin toilet aciki tayi wanka tareda alwalar sallar
azahar ta fito tafara yin sallah kafin ta shirya cikin doguwar rigar atampa
Wanda anty Sa'adah ta Bata Dan kuwa kaf suturarta kayan anty Sa'adah ne,
Bata taba saka sabon Kaya a rayuwartaba sai kayanda anty
Sa'adah tasaka tacire tabata
Duk da bayan kusan shekaru takwas zuwa Tara da anty Sa'adah
ta Bata akwai banbancin jiki Dan anty Sa'adah ba ramammiya bace hakama bawani
qibane da itaba saidai batada tsayi
Sabanin itakuma datake da Dan tsayi daidai
Hakama batada jiki Amma tafi anty Sa'adah nonuwa sbd anty Sa'adah
jikinne kawai da ita batada nono ko kadan,
Wasu kayan idan anty Sa'adah din ta Bata tana kaita gurin
wata tela Dake anguwar a rage Mata wasu Kuma hakanan take yawo cikinsu harta
tsufa.
Fitowa tayi ta nufi kicin ta dauko abincinsu Momy da anty
Sa'adah tafara kawo palo Dan Nan sukecin abincin.
Kicin Takoma acan taci nata sama sama tana gamawa ta nufi
palon abbansu sbd ganin lokacin Shan maganinsa yayi.
Da sallama tashiga palon Kai tsaye
Saitaga baqi
Bakuma kowa bane face Dr Abbakar wanda yake babban Orthopedic
likitane yasan Abban ne shiyasa har lokacin shine yake riqe da ragamar kula da
Abban dakyau hakama da kansa yake Dan duddubasa ata bangaren paralyze dinsa
daya saka gefen jikinsa baya Aiki sosai duk da dayan gefen ba laifi Yana aiki
Kuma ahakan danma ya tsaya tsayin dakane akan nemawa Abban
lafiya shiyasa ba wani sosaineba rashin aikin gefen dan wani zubin ba'a
ganewama.
Tareda Abdullahi babban Yaron Abban Wanda har lokacin
halacci yasa yake tareda dashi Yana taimakawa gurin hidamar kulawa dashi,
Kusan duk wasu hidimar asibiti madai shine yake jagoran
saidai Laylah tabisa abaya.
Ganinsu kowanne fuska ba wani walwala yasata juyawa Takoma
ahankali bayan tagaida Dr Abbakar din cikin nustuwa.
Bayanta dukkaninsu sukabi da kallo har Dr Abbakar din Wanda
yariga yasan damuwar Abba ba akan rashin kyawun results dinsa dasuka fito na
asibiti akan yarsa ne wadda yakejin ko yayane idan Yana Raye tana abun kallo da
dogaro Koda Baida wata moriya agareta dagashi har ita suna debewa juna kewa da
baqin ciki.
Ajiyar zuciya Dr Abbakar yayi shima cikeda tausayin Abban
dama laylan
Ya dago ya kalli abdullahi ya miqa Masa wasu takardu
yace"
Malam Abdullahi karba wannan Dan Allah kaimun mota Ina
fitowa.
Karba yayi cikin girmamawa jiki a sanyaye ya fice.
Bayan fitar Abdullahi sake sauke numfashi Dr Abbakar yayi
tareda kallon Abba da yayi nisa cikin tunani fuskarsa Babu wani alama dayake
bayyanarda yanayin da zuciyarsa take ciki,
Zuwa yanzu zuciyarsa tafara riqewa da tawakkalin tabbas
komai kaddarowar ubangijine,
Duk kaunar dayakewa 'yarsa yasan idan lokacinsa yayi Allah
bazai barsaba,
Hakama Babu wata qaddarar da Allah ya sauko Mata dazai iya
sauya Mata,
Results dinsa sun nuna infection daya shiga qashinsa tun
farko farkon hadarin da ba'a yanke qafafunba sunyi yawanda harsun fara shiga
jininsa,
Tabbas yasan yanda yakeji ajikinsa lokacinsa yakusa zuwa
Saidai duk ya kalli Layla da rayuwarda zai barta aciki
hankalinsa tashi yakeyi yabar jikinsa,
Tsoro da fargaba tareda kukane suke lullubesa aduk lokacinda
yayi tunanin hakan.
Alhaji MAHMOUD tabbas rikicewar lafiyarka a Yan lokutan Nan
sunada babbar nasaba da damuwa da kuncin dakake Tarawa aranka,
Da zaga sassauta damuwa da tunani kasamu hutun zuciya Dana
qwaqwalwa ko yayane za'a ringa samun sauki ko yayane.
Sunkuyar da Kai Abban yayi ahankali cikin irin yanayinsa na
masu ciwo irin nasa batareda ya iya ko dago idanuwansa ya kalli Dr Abbakar din
ba.
Shiru sukai tsawon mintuna kafin Dr Abbakar din ya miqe
tsaye Yana kallon abban cikin kulawa yace"
Zan tafi gobe zandawo zamu sake dibar sample ajikinka
Inshallah saimu gwada wani awon mugani,
Allah yaqaro lfy.
Juyawa yayi ya fice daga dakin har lokacin Abban Bai motsaba
Yana yanda yake.
Ahankali idanuwansa suka sauya zuwa ja jikinsa na daukan zafi na wani irin zazzabi Mai qarfi daya saukar Masa atake saidai zuciyarsa ta riqe yakasa tunanin komai saina Mutum daya daya fado Masa a Rai wato babban Amininsa Wanda shikadaine zai iya magance babban abunda yazo ya tokare ransa tsawon shekaru wato damuwar Laylah.
0 Comments