Rainon Soja Hausa Novel

Rainon Soja Hausa Novel


Barka da zuwa shafinmu na littafan hausa novels inda muka kawo muku Rainon Soja Hausa Novel by maman teddy.

Rainon Soja Hausa Novel

               Free Page 1 

Labari da Rubutawa daga:©Ayshatou Maman-teddy: December 02-12-2023 .....7:30am

#Rainon soja#whispering of love#Book 1#chapter 1#hand salute #travelling .

Wata moto ce ke guda a tsakiyar Æ™walta inda babu gida gaba babu baya sai Falfalan dajin ALLAH.  

Mota ce irin ta haya wanda yake dauke da mutane sun kai Goma zuwa goma sha biyu , kallo É—aya zaka yi masu ka fahimci matafiya ne wanda suka fito daga cikin garin Zaria zasu iso Garin Abuja .  Kowa hankalin sa yana akan hanya banda Mace ÆŠaya wacce tun da suka shigo moton idanun ta ke tsiyayar da Ƙwallah, daga  saman jikin ta kuma yarinya ce Wacce a shekaru ba zata Haura ÆŠaya ba zuwa É—aya da Rabi a Duniya . Tausayin yarinyar nata take jin yana ratsa ta haka zuciyar ta na kuka mata . Juyawa tayi tana kallon mai gidan nata wanda shima jimami ne da kuma tsoro fal a zuciyar sa.  Hajara kina ganin idan muka je Muka koma a halin yanzu Ƴan uwan ki zasu amshe mu? Zasu amince da Auren namu a yanzu kuwa? Hajara ko zamu koma ne.....ÆŠaga masa hannu tayi tana saurin riÆ™o hannun shi kamin cike da Raunanniyar murya ta fara cewa " A'a Salihu " kar ka Æ™ara furta hakan , yanda muka Æ™udurci kawo Zahra dangina Don taga iyayen ta da kakanni a yau babu abun da zai fasu daga yin hakan sai kuma idan Æ™addara ta Gifta .


Ka janye Tsoro ka manta da komai nasan su ma a yanzu sun manta kuma kowa zai yafe mun inshallah.  Fatan mu a yanzu shine Allah yasa mu sauka lafiya . 


"Hummm" . 


Sauke Ajiyar zuciya Salihu yayi kana yakai hannun shi yana ɗaukar ƙaramar yarinyar tasu yana daura ta bisa jikin sa . Ƙurrrr yayi mata da ido kamin yace " Wai Haihuwar ki ce aka ce mun ba alheri a rayuwa ta Zahra , Ni nasan Allah shine mai yin komai shine wanda yasan ƙaddara ba ɗan Adam ba. Ko ina raye ko ina a mace ina rokon ALLAH ya kare mun ke da kariyar sa. Shiru Hajara tayi tana kallon uba da ƴar wanda yake ji tamkar ya haɗa ta da jikin sa ya zamana babu wani abun cutarwar da zai iso gareta . Murmushi take bin su dashi kamin ta juya tana kallon dajikan da suke wucewa.


Kaman wanda aka É—aga moton suka ji tayi sama tayar gaban ta yana fita fittttttt ji kake kwaltan da tayar suna fidda wani irin Æ™ugi Æ™uuuuuuiiiiiiii nan take moton ta É—aga tare da kifowa kif kaman wanda aka dirkake su . A dai dai kuma wannan sa'ilin da babu gida gaba babu gida baya ,sai falfalan dajin ALLAH . Yanda moton tayi Æ™watsa Æ™watsa jini na malala a tsakiyar titin ga hayaÆ™i dake tashi tamkar an kunna Masu fetur da ashana wurin yayi baÆ™iÆ™irin kai daga Ni kasan babu mutum É—aya daga cikin moton nan da ya shura sai dai muce Allah yajiÆ™an wanda suka rigamu gidan Gaskiya. 


**

Nigerian defence academy ( NDA)

#Nd 1 .

Yaran sojoji ne birjik a Æ™ame rana na dukan tsakiyar kan su , amma yanda wurin yayi shiru da yanda sukya a Æ™ame tamkar wanda ruwa yaci yacinye su . Mutumin dake daga nesa ba zai taÉ“a kawowa da akwai mutum ko É—aya a wurin ba,bare kuma sojoji da sun haura 100 É—ari duka a layi . Kasancewar su Nd 1 yasa duka yawancin su yara ne matasa wanda daga secondary ne suka shigo , duk girman yaron dake wannan wuri babu guda É—aya da ya haura 18 . Duka Æ™asa da haka ne sai kuma 18 din , ciki har da masu 15 years yayan manyan kenan masu faÉ—a aji a Æ™asa . Sune suke kawo yaran su tun da yarinta . 


Cike da Wani irin Æ™araji tamkar zai tashi wurin da yaÆ™i Muryar Major É—in su ya katse su yana furta " Hand salute! Daram dam dam....kaji takon su duka ya sauya suna juyawa ga Major É—in a lokaci guda suna É—aga yatsunsu tare da Æ™amewa da Æ™afafun su .  Bin su da kallo yayi dukan su Sanye suke cikin t.shirt na sojoji sai wandon su mai ratsin tambarin su na soja. 


Idanun Major Jibril ne ya sauka akan Wani kyaÆ™yÆ™yawan yaron dake daga can tsakiyar layi , su duka a Æ™ame suke amma shi a wannan lokacin Wayar hannun sa yake latsawa cike da kula murya Æ™asa-Æ™asa yake furta " Mami...Hello . 


Wani irin Tsawa Major Jibril ya daka masa Wanda sai da Hantar cikin Duka yaran ya kaÉ—a yana bada amon Æ™ulululu... Mamaki ne ya kama su Ganin Yanda Aliyou Haidar bai Girgiza ko ya saki wayar tasa tayi Æ™asa ba ,sai ma Æ™ara mannata da yayi da kunnen sa yana furta " Mami I'm in trouble Major Jibril ya na mun magana bye bye .kamin ya jira jin mene Zata furta ya datse kiran da Sauri yana maida Wayar cikin Aljihun sa . 


Cike da shouting da É—aga murya irin na Sojoji Major ya furta " Who are you ? ....kamin ya rufe baki cike da Ƙwarin gwiwa tare da gigiwa irin na Aliyu ya furta" ALI HAIDAR ". yana furta zancen tare da Æ™amewa kaman yanda suka saba yi don respect. Kallon shi Major Jibril yayi kana ya bashi umarnin ya fito wajen layin . Cike da kuzari da Sauri ya fito yana gyara tsayuwar sa , kallo ÆŠaya Major yayi masa yaga tsayayyen namiji ne a gaban sa tun kan ya girma a yanzu ma zaka fahimci hakan , Æ™wayar idanun sa ya kalla ganin rashin tsoron sa yasa shi Furta " Waye Soja a tare da kai ?  . 


Sorry sir 

Fa furta yana kame ma Major É—in , Tambayar ya kara nanata masa karo na biyu  wato a dangin sa Waye soja? Wanda a wannan karon kai tsaye Ali haidar ya basa amsa da my Dad...! Ya furta da Æ™arfi yana Ƙara Æ™ame ma Major Jibril  . Meye sunan Mahaifin ka ? General Saleh Yelwa . Girgiza kai Major Jibril yayi tamkar General ne a gaban sa , don yasan Waye General Yelwa babban sune shine ya basu horo a lokacin tasowar su . 


Kallon Aliyou Haidar yayi kana ya cigaba da cewa " Ya ake yin Hand salute? 


Ok sir . Ya furta yana Sara masa tare da hade Æ™afafun sa . 


Kallon Sauran sojojin abokanan sa yayi shigowan yanzu Nd 1 kana cike da Arrogant voice É—in sa ya fara cewa Hand salute! 


"You raise the right hand smartly in the most direct manner a kuma lokaci guda extending and joining the fingers ...keep the falm plat and facing the body. 


"Yana maganan tare da nuna masu yanda ya kamata suyi don haka Majorn ya sanar dasu a jiya . " 


Komai dai dai ya faÉ—a , Wannan yasa Major kallon sa yana basa horo da ya fita can Rana ya fara tsallen kwaÉ—o shine punishment É—in sa na yau , Gobe ba zai Æ™ara kuskuren da yayi irin na yau ba.  


Ficewa Ali haidar yayi yana nufar inda Major yace yayi tsallan kwaÉ—on , ÆŠan waigawa naga yayi yana kallon wani direction yana murmushi . 


Gani nayi wani Matashin yaro wanda ba zai haura 17 ba yana kallon Aliyu idanun shi sunyi ja na damuwa ga gumin dake karyo masa , damuwa duka sun bayyana ƙarara a fuskar shi . Haɗa ido suka yi da ƙanin nasa yana jifan sa da harara tare da cewa a zuciyar sa " Yaushe Haidar zai daina rashin ji ne? Yau sai ya sani bari ya gama mu koma . Murmushi Aliyu haidar yayi yana furta to menene na dumuwa Yaya Khaleel bafa wuya ne dashi ba . Yanzun xanyi na gama .




Tsallan Æ™wadon ya fara yi su kuma sauran sojojin suna fara fareti . Fiye da Awa É—aya yake aikin tsallan Æ™waÉ—on amma babu alamar gajiya a tare da shi , don shi jin sa yake tamkar training din da suka saba yi ne a gida yake yin sa a yanzu.  Ni Ko nace yo ba dole ba , Mahaifin su soja mahaifiyar su babban Ƴar sanda ce , Wanda a yanzu take da matsayin mataimakiyar Commissioner of police. Hajiya Nafisat Yelwa kenan . Ƙaramar Æ™anwar su kuma jidderh itace take makarantar yara na karatun architecture . Sauran labari zamuji shi a gaba inshallah ku dai ku cigaba da biyo wannan Golden pen din don wannan tafiyar ta musammance .



Ali Are You not tired ?  Baka gaji ba Haidar? Muryar Areef ya katse shi wanda yake fareti dai dai inda Aliyou Haidar yake . Cike da hade gira tamkar wani bad boss yace " Na riga da na saba da ko wani horo na soja tun kamin nazo nan. ÆŠan wannan tsallen kwaÉ—on ba zai gajiyar Dani ba . 


Da kyau! 


Muryar Major Jibril ya katse su wanda basu san yana tsaye da a bayan su ba.  Tabbas wannan yaron yana da jan rai da zuciya kangararriya , haka ake son soja ya kasance , Major yayi maganan a zuciyar sa yana juyawa tare da kallon Manyan sojojin dake bayan sa.  Ina so ku bi mun bayan Ali haidar Yelwa yayi gudu tun daga nan Kaduna jaji har zuwa Zaria ya dawo a Æ™asa ba tsayawa ko Hutawa yanzu . Ok sir ......! Suka yi maganan cike da amsa kuwa . Juyawa Ali haidar yayi yana kai hannun sa tare da miÆ™a yana miÆ™ewa tsaye . Da sauri ya furta " Major idan ba damuwa zan iya É—aukar Helmet da Armor idan ba damuwa da ruwa ma .  Wani irin kallo duka suka bi shi dashi , yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace " Kai ba yaÆ™i aka ce zaka tafi ba , You Are under punishment now , shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi me zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo .......................!



*Ina kuke masoyana nasan yawan ku kun haura irin billions É—in nan kuyi mun share page É—in nan ga mutanen ku nasan Æ™aranci yanda nake da jama'a billions haka kuma Æ™aranci 1 million people.  Ga masu buÆ™atar na tallah masu hajar su Æ™ofa a buÉ—e take zaki zanzare kuÉ—in aljihun ki ayi Miki tallah don samun customers sai ki tuntuÉ“eni ta WhatsApp ga nombibina nan a daga Æ™asa*


*Labarin RAINON SOJA  na kudi ne kar ki fara karantawa tun fari idan kin san baki da kuÉ—in saya don Allah... Book 1 free ne shine wannan ,idan mun gama shi book 2 na kuÉ—i ne kar azo ana ayi haÆ™uri da sauran su , Sannan group din littafin guda uku ne 3 , muna da na Æ™asa shine ₦500 (regular group) sannan aÆ™wai yan tsakiya shine ₦1000 (Vip group)sannan aÆ™wai na sama shine ₦1500 (Special payment)...Zaki iya payment din ki ta wannan account number 60312299 Mohammed A'isha keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta wannan number 1202932 idan Vtu transfer ne ga MTN numbern da zaki tura tanan 01466409 zaku iya fara payment naku tun yanzu don na samu damar sakaki group da wuri kamin mutane suyi yawa kunsan hidimomin da yawa ...to hajiya ta wannan salon tafiyar ta daban ce kar ki bari ayi babu ke a barki a baya .labari ne mai É—auke da darussa yanda yazo a Æ™arshen shekara haka daÉ—in sa ya kasance na musamman kun san alÆ™alamin mmnteddy baya rubuta labari mara ma'ana ato.

Anty Aysha Mamanteddy


KARANTA: JEJI Girl Hausa Novel Complete


Rainon Soja Hausa Novel Page 2

Yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace " Kai ba yaÆ™i aka ce zaka tafi ba , You Are under punishment...shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi? , Amfanin mene Helmet zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo ban yarda ko Hutawa kayi ba . Cike da É—aga murya tamkar saukar Aradu Aliyu ya Æ™ame tare da furta " Yessss sir ". 

Yana furta hakan ya fara cika umarnin Major Jibril yayin da Wani soja dake gaba dasu É—an ND 3 yake bin bayan Aliyu haidar da ya fara gudun sassarfa kaman yanda Major yace dashi . Tun daga jaji yake gudu a wani irin tartsatsin rana gashi ba hulan su ta soja wanda yake tare dukan Rana ,ko ruwa kuma ba'a yarda mishi yasha ba .


A hankali take bin bord É—in da kallo , tana sakin Murmushi tare da kai laÉ“É“anta tana kissing É—in zanen fuskar Aliyuu Haidar . I love You Booo mie. Ta furta tana shafan giran sa wanda yake a tattare ya haÉ—e kaman hadari. 

Ƙamshin turaren da taji ne yasa ta saurin juyowa tana kallon inda Mami ke saukowa cas-cas-cas cikin shigar suit Æ™afarta tasa cover irin na mata , Fuskar ta cikin baÆ™ar gilashi da gani kasan no respect ba zaka taÉ“a cewa itace ke da yara uku maza biyu mace É—aya ba wato jidderh, Khaleel da kuma iyayen kafiya da naci wato Aliyu haidar.  Mami....! Ƙaramin Muryar Jidderh ya katse Ni cike da yarinta tana sakin mawa Mahaifiyar nata fara'a . 

Cikin sauri Mami ta nufo inda take tana rage tsawon ta tare da hugging É—in jidderh tana cewa " Morning my baby love". Ana nan kina kallon Khaleel da Aliyu ? . Yes mami i really miss Booo mie da kuma Ya Khaleel . "Hummmmmm"  Hajiya Nafisat ta sauke Sanyayyar ajiyar zuciya kana ta kai hannun ta tana shafa kan Jidderh cikin sanyi da Muryar rarrashi ta furta " Sorry my lav zasu dawo nan kusa bada jimawa ba '. 

GyaÉ—a ma Mami kai jidderh tayi tana sakin Murmushi haÆ™oranta da wawulo na bayyana wannan yasa Mami dariya tana cewa"Alright muje kiyi breakfast sai na kai ki school daga nan Ni na wuce Office . Hannunta ta kama suna nufar Dinning room.....yanda Mami ke tafiya kadai zaka fahimci zaman gidan Na sojoji ne masu kaki komai oya-oya ake yin shi babu shauÆ™i irin na mata , tun tasowar yaran nasu a haka cikin gidan ya kasance, Daddy Soja Mami Police yar sanda 🫡 . 

Haka suka taso basu san suga iyayen su kullum a tare ba ,idan yau Daddy yana hutu to gobe Mami zakaji an sauya mata wurin aiki ko bata gari , dukan su yaran sun taso cikin horan sojoji ne ,don gidan baki É—aya har ta masu girki cook sojoji ne  , masu kulawa dasu sojoji masu kai su school sojoji Wannan yasa duk horo suke shan baÆ™ar wahala , gashi General Saleh Yelwa ya Æ™udurci son ganin yaran nashi sun zama tamkar shi Wato Sojoji . Wanda a yanzu a lokaci guda Duka su biyun suka fara NDA . A yanzu Aliyuu Haidar shekarunsa sha shida ne Bama ce ya cika ba ,sai Khaleel babba shine gaba da Haidar shi kuma shekarun sa 17-18 don tazaran su ba nesa bane shiyasa kan su yake daya ,sau tari wanda basu sani ba ma kiran tagwaye suke yi masu .

Sai dai Khaleel na fama da shan Wahalar Aliyu saboda Neman magana irin nasa ga kafiya da fusata ga saurin ƙufula da zuciya, a haka kuma yake zafin son Ƙanin nasa . Wannan shine taƙaitaccen labarin Gidan General Saleh Yelwa da iyalan sa . Bari mu Jah gaba muji wani hali Aliyu yake ciki a yanzu .


Tafiya ce suka yi ta mai dogon zango yayin da Ali ya haÉ—a gumi iya gumi a wannan lokacin har sun kai wuraren Gwargwaje sannan suka kuma juyowa zuwa jeji. A tsakiyar wani Æ™aramar jeji ne kan hanya idanun Aliyu da Yaron Captain Lawal suka sauka kan Wata moto da tayi Æ™watsa Æ™watsa a titin wuta na tashi ta sama da Æ™asanta . 

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kalmar da Lawal yayi kenan yayin da Haidar ya cigaba da Gudun sassarfa yana Æ™oÆ™arin wuce moton . Amma kai baka da Hankali Wani irin mara imani ne kai Ali ? Wucewa zaka yi kana ganin halin da Mutanen moton ke ciki . Tsayawa Haidar yayi yana Æ™amewa tare da seniority ya furta " I'm under punishment Sir ". 

Kama kai Lawal yayi kana yace " Mu ceci mutanen nan ka dakata da Wannan Gudun da kake yi haka nan ,idan mun koma xanyi ma Major bayani . Ok sir . Aliyu ya furta yana saurin Æ™arikowa inda moton yake hannun sa yasa duk da Æ™arfen da tayi zafi ga moto ba karama ba . 

Tura moton suka yi da ƙarfin na sojoji suna ɗaga ta , Saurin rufe ido Ali yayi don wannan shine karon shi na farko da ya fara ganin gawa ido da ido a rayuwar sa . A takaice gaba ɗaya moton babu wanda ya shura dukan su sun zama gawa, gashi mutuwar wahala abun ba dadin faɗi da gani sai ka zubda masu da Hawaye jini ne kawai ke malala.....

Hu'uhhhhmmmmmmm Suka ji wani jan iska da karfi anyi tare da fara tsala ihu irin na yara jarirai . Hasbunallahu wani'imal wakeel ". Lawal ya furta da sauri yana kai hannun sa yana fuzgo yarinyar da take maÆ™ale jikin mahaifiyar ta , har ta fara sanÆ™arewa. 

Aliyu Ruwa ruwa Aliyu Ruwa kawo ruwa .! Yana maganan hankalin sa a tashe da kuma yanda yarinyar ke ihu iya Æ™arfin ta numfashin ta na kokarin É—aukewa.  

Kallon Sa Aliyu yayi kana yace " Ai Major yace ba zan taho da ruwa ba ko ka manta ne ? . 

Ba tare da ya tsaya ba Aliyu amsa ba ya fara gudu da yarinyar a hannun sa ,hakan yasa Aliyu shima bin bayan sa don su nemi ruwa su bata a wannan falfalan hanyar jejin da babu gida babu gida baya ,itako yarinya Æ™iwuya ne yayi mata yawa ganin bata san fuskokin ba. Wannan yasa ta take kuka har da shirin riÉ—ewa . 

Sir Lawal ka daka ta gudun nan , wannan ihun yarinyar yayi yawa kaman mun sato ta? . Cak Lawal ya dakata da gudun yana kallon Aliyu kamin ya juya yana kallon kyaÆ™yÆ™yawar fuskar yar lukutar yarinyar wanda nan take ya furta " Laaa Aliyu kalla? Kai take kallo tayi shiru Aliyuu kalli dariya ma take yi maka yanzu . ÆŠaga gira Aliyu yayi yana zuba ma yarinyar Manyan idanun sa da suke warwaje na rashin tsoro , Ganin yanda take Wangale masa baki kaman ba itace mai kukan ba ko kuma ta san shi yasa shima jin wani irin yanayi lokaci É—aya na shigar sa gami da yarinyar . Amshe ta Ali zata yi shiru a hannun ka yanzu . 

Ba musu Aliyuu ya miÆ™a hannun sa yana amsan Yarinyar da take ta Wangale bakin nata tana dariya tare da miÆ™a masa hannayen ta duka na yara . Lawal ne ya bude baki zai masa magana da nuna masa yanda zai riÆ™e yarinyar don ya lura bai ma iya daukar yara ba , Kawai caraf yaga ya É—aga yarinyar yana É—aura ta bisa wuyan sa tare da riÆ™e hannayen ta a sama . Zamu iya tafiya YallaÉ“ai.! Yayi mganan cike da amsa kuwa da Æ™amewa , cikin sauri Lawal yace " Kai Ali mu aje wannan duk abin a gyefe yanzu ina zamu kai yarinyar nan.  ? 

Shiru Aliyu yayi masa yayin da Lawal ya cigaba da cewa " mu tafi Barack da ita.  Mu sanar mawa Major.  

A'a gidan General Saleh Yelwa zan kaita yanzu.  Ko mun dare zan dawo barack . A'a kana fa bisa laifi ne ,idan ka tafi zaka iya samun wata matsalar, sannan kuma dole mu nemi abun hawa don yarinyar a gajiye take . Gudu Haidar ya fara yi mai sassarfa kana ya yi gaba tare da daga murya yana cewa " Sai na dawo YallaÉ“ai". 

Ali Meye haka nake gani? Wacece wannan a saman wuyar ka ka É—auro? . Muryar Mami ya katse shi cike da amsa kuwa take maganan cikin É—aga murya don kallo É—aya tayi masa jikin ta sam bai bata ba . 

Mami abani ruwa na bata . Meye sunan ta ? Kuma Meye na kawo mana ita cikin gidan nan? . 

Ban san sunan ta ba , Amma na kawo ta gare ki ne , domin ki sanya mata sunan da ya dace . Ki kuma raine ta.  Yanda yake maganan idanun sa kafe akan Mami yasa ta Fahimtar bafa wasa yake yi ba ,don dama shi ba ma'abocin yin shirme bane sam baya wasa . You're very stupid Ali..! Baka da hankali . Ka dauko yarinya nayi mata raino , ko ku kan ku a haka kuka taso ban raine ku ba ,kuma har yau kulawa da ku ake yi , shine ka dauko yarinya wai na raine ta? Har na sa mata sun .....Kai Ali talk to me openly about this child, a ina ka same ta Wacece ita? . 

Wannan shine tambayar da ya kamata ki fara yi mun tun farko Mami , duk da bani a mood din zan baki amsan yanzu , i need massage.  Where's Jamima? . Yanda yake maganan kaman House boss din gidan yasa ta , cewa sannu Mai gida General Saleh Yelwa, ina magana kana maganan a kira maka wacce zata matsa maka jiki ? Aliyu zan cire duk wata Sangarta da soyayyar da nake maka na aje ta a gyefe a yanzu faÉ—a mun Wacece wannan Yarinyar......? 

Mami idan na faÉ—a Miki Wacece ita , zaki raine ta ki kula da ita tamkar yanda kike yi mana koma fiye da namu so nake ki raine da hannun ki akasin mu da sojoji suka raine mu , ki ake wannan aikin naki ki zama cikakkiyar House wife matar gida don ki kula da Ma'eesha sunan dana sanya mata kenan Mami.....Kai yi mun shiru Ali , bana son Shashanci tambayar da nake maka daban amsan da kake bani da ban , to Bara kaji Wannan yarinyar ba zan raine ta ba , ba kuma zata zauna a cikin gidan nan ba . Ka dauko yarinya kaman Aljana ji ta fa tana wuru² da ido kai Ali fice mun da yarinyar nan yanzu. A'a mami zan zauna da ita , zan fasa cika duk wani mafarki na har ta girma . 

Kallon sa Mami tayi cike da rashin fahimta ta furta " Ban fahimce ka ba ban gane inda ka nufa ba Aliyu.

Takowa yayi yana Fuskantar Mami da itama shi take kallo yana ƙara gyara zaman yarinyar dake bisa wuyan sa , Yes Mami zan Aje aikin soja na naɗan wani lokaci, zan raini Ma'eesha har ta girma , zata taso ne a hannu na Wato RAINON SOJA...................!



Har yanzu muna sharan fage ne ba'a fara chakwakiyar ba a cikin littafin rainon soja kudai ku cigaba biyo alkalamin nawa wannan salon sa na daban ne . Kar kuman ta wurin yi mun sharing zuwa masoya na na duniya baki daya.

Post a Comment

0 Comments