GUDU DA WAIWAYE 1 to 10
MALAM Rabi'u Shema, cikakken bakatsine jinin rumawan asali da ALLAH ya azurta da wani sirrin ƙyau mai fita da kwarjini.
Ya fitone da ga
yankin karamar hukumar Dutsamma dake jihar katsina, a wani ƙauye da ake kira
Shema, danginsa uwa da uba duk sun fitone daga wannan yanki.
Sanadin
ƙaddarar neman na kaine ta dalilin kasuwanci ya tsinci kansa a garin kano, shi
kaÉ—ai ya fara zuwa kafin daga baya ya kawo matarsa mai suna iya ladi.
Ƴaƴansu huɗu a
duniya, maza uku mace É—aya.
A yanzu haka da
shekaru suka shuÉ—a gidan Malam Rabi'u ya zama family house mai É“angarori huÉ—u.
Ginine irin na
mutanen da, shiyyasa ya kasance gida babba da har Æ´aÆ´ansa Uku duk suka sami
gurbin zama da iyalansu a cikinsa.
A yanzu haka dai
ALLAH ya azurtashi da jikoki daga tsatson waÉ—annan Æ´aÆ´a huÉ—u da zasu iya kaiwa
kusan ashirin da huÉ—u, harda Æ´aÆ´an Æ´arsa mace Marwa dake aure acan garin
Dutsamma kuma guda biyu.
Duka Æ´aÆ´an malam
Rabi'u ALLAH baisa sunyi karatun boko ba har suka kai minzalin hankali, amma
sunada ilimin addini gwargwadon iko.
Babban ciki mai
suna Hamza shine ya fara auren matarsa ta farko Ruƙayya, wadda ya koma gida ya
auro ɗiyar zumu, wato ɗiyar gwaggonsa ƙanwar mahaifinsa.
Ruƙayya ta
tare a kano tare da mijinta Hamza annan cikin gidansu, ya gina É—akuna biyune da
bayi ya katange wajen, Ruƙayya tana samun soyayyarsa data iyayensa mai tsafta
harma da ƙannensa.
Sai da Ruƙayya
ta shekara uku a gidan sannan ta samu ciki, bayan ya kai haihuwa ta haife É—iyarta
mace wadda taci suna maryam.
Haihuwar Maryam
da watanni biyu Muktar yazo da batun sake aure.
Hankalin Ruƙayya
ya tashi ƙololuwa, hakama iyayensa suka nuna sam basu yardaba.
Yashiga damuwa
sosai, saboda yanason Suwaiba, kuma harma sunyi alƙawarin aure, da farko yaso
ya haƙuran amma sai ya kasa, yaje can gida Shema ya sanar ma mahaifin Ruƙayya
halin da ake ciki.
Mahaifin
Ruƙayya yazo kano, inda ya wanke Ruƙayya da faɗa tas, sannan ya koma nasiha a
gareta, hakama iyayen Hamza ya samesu ya nuna musu suyi haƙuri su barsa tunda
yanaso, da yaje gefe yana aikata abun banza gara ya auro yarinyar zaifi
kwanciyar hankali.
Badan su iya ladi
sun soba suka amince akai auren Suwaiba da Hamza.
Suwaiba dai
asalin iyayenta Æ´an dawanau ne, amma yanzu suna nan zaune a cikin garin kano,
bata da damuwa sam, dan tunda ta tare gidan Hamza batajin daÉ—in kowa sai shi,
iyayensa da ƴan uwansa basa sonta, ƙiri-ƙiri suke nuna mata fifiko akan
Ruƙayya.
Danne zuciyarta
tayi tamkar bata gani, takuma kwantar da hankalinta tana musu biyayya su duka,
wannan halayyar tatace ta saka suka fara sassauta mata, har itama Ruƙayyar
kanta.
Koda yaushe
zakiga Maryam maƙale da Suwaiba, dan tanada son yaran tsiya, tun Ruƙayya na
ƙwacewa bisa zugar matar Yusha'u harta hakura ganin Suwaiba bata taɓa cutar da
Maryam ɗinba, lokacin ma da Ruƙayya zata yaye maryam sai Suwaiba ta amsheta ta
yayeta, tundaga wannan lokacin kuma zaman Maryam ya koma hannun Suwaiba.
Kawaicin É—an
fari yasa Rukayya ta ƙyale mata.
Cikin hikimar
ALLAH kuma sai Suwaiba da Ruƙayya suka fara laulayin ciki a tare, Rukayya na
biyu, Suwaiba na farko, tare sukaita laulayinsu har ALLAH ya saukesu lafiya,
sai dai Ruƙayyace ta fara haihuwar ɗiyarta mace, taci sunan Rahama, bayan kamar
sati biyu dayin suna sai itama Suwaiba ta haihu, amma ita namijine.
Itama ranar suna
yaronta yaci suna AHMAD, Suwaiba mutum ce mai azabar kawaici, sai yazam har
akan Ahmad halayyarta na nan, dan sam yitake kamar ba É—antaba, dukda kuwa tana
ƙaunarsa sosai, wani lokacin tana zaune zaita kuka amma tai biris dashi, har
sai Ruƙayya ta shigo ta ɗaukesa tana mata faɗa, ko bashi nono sai Ruƙayyan ta
tsaya a kanta wani lokacin.
Wannan kawaicin
da takeyi mai tsanani a kansa yasaka Ruƙayya maida hankalin kula dashi da
Rahama, sai suka taso tamkar wasu tagwaye, idan ka ganshi hannun Suwaiba to
nono zaisha.
Maryam kam ta
zama ƴar ɗakin Suwaiba, itace tamkar uwarta, itama Ruƙayya tana kawaici akanta,
dan bata faÉ—ar koda sunanta kamar yanda itama Suwaiba bata faÉ—ar sunan Ahmad.
Ahaka yaran
suka fara wayo har zuwa yaye, sai zaman Ahmad ya koma wajen Ruƙayya gaba ɗaya,
kamar yanda Maryam take hannun Suwaiba.
A wannan
karon sai Ruƙayya ta fara samun ciki kafin Suwaiba, sai da cikinta yakai kusan
wata bakwai sannan Suwaiba itama ta fara laulayi, a wannan haihuwarma dai Ruƙayya
mace ta haifa, wadda taci suna Sakina.
Su Ahmad sunyi
murna sosai an haifa musu ƙanwa, sai nan nan suke da ita dukdama bawani wayone
dasuba lokacin.
Bayan haihuwar
Sakina da kusan wata taƙwas itama Suwaiba ta haife ƴarta mace, itama taci suna Raheenat.
Ƴaƴa zun fara
cika gidan malam Muktar, dan haka sunayen iyayensu ya fara ɓuya, Ruƙayya ta
koma Ayyah, Suwaiba kuma Gwaggo.
Tun daga kan
Sakina Ayyah (Ruƙayya) bata sake haihuwaba, sai Gwaggo (Suwaiba) ce ta cigaba
da haihuwa, tayi Mudanseer, Abubakar, Fa'iza, Sadiya, sai auta Zainab.
Daganan ne
haihuwar ta tsaya itama, yaransu sun taso kansu a haÉ—e, inba sanar maka akaiba
baka taɓa sanin ƴaƴan wance da wance, tare suka haɗu wajen gina ƴaƴansu a
tarbiyya, sun gina gidansu bisa ƙyaƙykyawan tsari mai birgewa duk da sheɗancin
kishin sauri da suke fuskanta lokuta da dama.
Sai ƙanin
Hamza mai suna Yusha'u, shima dai matarsa É—aya da Æ´aÆ´a biyu, shima a cikin
gidan ya gina nashi É—akin matarsa ke zaune, shima sai ya ja katanga iya sashensa
kamar yanda Hamza yayi, ya auri matarsa mai suna ÆŠausiyya (Gaje) kusan tare da
auren yayansa hamza na biyu, hakanne ya saka Gaje É—aukar kishin duniya ta aza
akan Suwaiba tamkar mijinsh É—aya, dan komai na auren Suwaiba yafi nata.
Taso saka ruÉ—ani
a zaman Suwaiba da Ruƙayya, su haɗe kai su ware Suwaiba a gidan, amma sai
UBANGIJI ya hana hakan, babu irin munafircin da batai musu, sai yazam ko saɓanin
ya shigo tsakaninsu baya wani daÉ—ewa suke fahimtar juna.
Lokacin da
riƙon Maryam ya dawo hannun Suwaiba ba ƙaramin baƙin ciki Gaje ta shigaba,
taita zuga Ruƙayya akan ta amshe Maryam, amma sai ALLAH bai ƙaddara hakanba.
Abinda kuma
yazo ya sake haɗa ƙiyayyarsu Haihuwar namiji da Suwaiba tayi, wato Ahmad, dan
kusan tare itama Gaje ta haihu dasu, sai dai itama mace ta samu kamar Ruƙayya,
wadda taci suna Binta.
Nanma Gaje ta so
ta cusama Ruƙayya ƙiyayyar Ahmad sai hakan bai faruba, dan kuwa Ahmad ma sai ya
dawo hannun Ruƙayyan gaba ɗaya.
Tunda Gaje ta
fuskanci bazatai galabar ɓata zaman Ruƙayya da Suwaiba ba sai ta koma kishi
dasu gaba ɗaya, kullum burinta ta yaya zata ƙuntata musu kota haɗasu faɗa.
Sukam watsar da
lamarinta sukayi tankar basusan da zamanta a gidanba.
Ahaka zaman nasu
yaci gaba da tafiya har Ilyasu É—a na uku wajen su malam Rabi'u yayo nasa auren
shima.
Ilyasu ya auro
matarsa mai suna Sailuba, tunda Sailuba ta tare a gidan sai Gaje ta shiga jan
ra'ayinta da cusa mata tsanar su Ruƙayya (Ayyah) a zuciya, a hankali itama abun
ya fara tasiri a ranta, sun ware kansu su biyu, bakajin cikinsu sam a gidan,
sannu a hankali sai suka fara jan ra'ayin mazansu ma.
Daga nan ne fa
zumincin iyalan malam Rabi'u yaso fara tangal-tangal.
Hankalinsa ya
tashi lokacin da ya fahimci daga inda matsalar ke neman fitowa, dan haka ya
tara Æ´aÆ´ansa duka huÉ—u har Marwanatu autarsu da itama tai aure acan dutsamma.
Ta inda ya
shiga ba tanan yake fitaba wajen banbamesu da masifa akan sheÉ—ancin matansu
dake nan lalata zumincinsu.
Jikinsu kuma duk
sai yayi sanyi, dan tabbas sun fahimci kuskurensu sosai, haƙuri sukaita bama
iyayen nasu.
Iya Ladi tace
ita sam bazata haƙura ba sai Yusha'u da Ilyasu sun ƙara aure, danta fahimci
matsalar daga wajen matansu take.
A take Ilyasu ya
amince zai ƙara auren, amma Yusha'u sai ya bada haƙuri akan shifa baida ra'ayin
sake mata bayan matarsa Gaje.
Iya Ladi tace
aikuwa bai isaba, ƙara aure ya zamar masa tilas, tadai bashi lokaci yaje ya
nema wadda taimar daga lokacin har tsawon shekara uku.
Kwanaki kaÉ—an
dayin wannan Zama, zancen ƙara auren Ilyasu ya taso, zai auri wata yarinya anan
ƙasan layinsu mai suna Zubaida.
Bayan Ilyasu
ya ƙara aure a nanma sai Gaje taita tunzura Sailuba, sam zaman lafiya yaƙi
tsakanin matan Ilyasu saboda munafurcin Gaje.
Haka rayuwar ta
cigaba da tafiya a wannan family, a cikin gida É—aya har kawo yanzu da duk sun
mallaki hankulansu, Æ´aÆ´ansu duk sunyi girma, yayinda tsufa ya kama Malam Rabi'u
sosai, hakama iya ladi, dukda dai ita Alhmdllh jikinta da ƙwari tunda komai
tana iyayima kanta.
Hamza talakane
mai ƙoƙarin neman na yau da gobe, yanada wadatar zuci da bai amince ya zauna
roƙoba, duk wahalar sana'a yana ƙokarin ganin yayi ya samawa iyalansa abinci,
da abinda zai kula da iliminsu, dan ya tashi zuciyarsa nason Æ´aÆ´ansa suyi
karatun boko, amma ga sauran Æ´an uwansa sam ba haka baneba, sun tsani ilimin
boko, a ganinsu watsa tarbiyyar yarane kawai, inda yana da kyau da iyayensu
suma sun sakasu ai..
Hamza yasha
zaunar dasu ya fahimtar dasu banbancin zamanin yanzu da nasu daya shuÉ—e, sai
dai sam sunƙi fahimtarsa, hakanne ya sakashi ƙyalesu kawai.
Shi Æ´aÆ´ansa
Suna zuwa makarantar boko ta gwamnati tamkar sauran yara, sannan da yamma suje
islamiyya, da dare suje allo.
Rayuwa ta
shuÉ—a inda malam Hamza (Baba) ya fara aurar da Æ´aÆ´ansa, Maryam ita aka fara
kaiwa É—akin miji, sai Rahama da suka tashi sa'anni da Ahmad, daga nan sai
Raheenatu.
Shima Yusha'u ya
aurar da Binta, wanda bayan bikin da kwanaki kaÉ—an yace zai kara aure.
Tashin hankali
kenan, da ga mama Gaje, wadda tai tsalle ta dire akan bai isaba, ita tafi
ƙarfin zama da kishiya wlhy.
Rigima tayi
rigima har takai Yusha'u ya saki Gaje da cikinta É—an wata bakwai.
Wannan shine
sanadin barin Gaje gidan, shikuma yayo aurensa.
Daga nanne suka
sami zaman lafiya, kowa ya koma mutunta É—an uwansa a gidan.
Amaryar Yusha'u
ta sinkuto masa É—iya mace bayan shekara É—aya, wadda taci suna Umm-Rumana.
Ƴaƴan Baba Hamza
mata daya aurar Dukansu iyakarsu
sakandire aji uku yake musu auren, dan haka Ahmad ne ya fara wuce aji uku na
sakandire a gidansu.
Ahmad
ƙyaƙyƙyawan yaro mai cikar halittar asalin rumawan katsinawa, komai nasa
mahaifinsane, yanada ƙwazo a makaranta ga rashin hayaniya, dan sam da wahala
kaji ance ga abokin faɗansa, inhar kaga yayi faɗa to ankaisa maƙurane, dan
yanada zafin zuciya idan aka kaishi ƙarshe, sannan idan yay fushi da abu Ayyah
ce kawai ke iya lankwasashi cikin sauƙi.
Dan Ahmad É—an
gatan Ayyah ne sosai, duk abinda kaga Ahmad ya nema ya rasa sai dai idan Ayyah
bata da ƙarfin siyensa, shima kuma saitayi ƙokarin saya masa makamancinsa,
harya fara zama saurayi komai nashi yana É—akinta, tsakaninsa da mahaifiyarsa
kuwa gaisuwace kawai, dan kallonsa ma bata iyayi saboda kunyar É—an fari.
Ya daÉ—e baisan
ba Ayyah ce ta haifesa ba, da yasani kuman ma bai damuba, abinda kawai ke bashi
mamaki kawaicin mahaifiyarsu, dan sam bata sakewa dashi, tun abun bai damunsa
harya ɗan fara damunsa, amma daya ƙara hankali sai ya fuskanci ba sonshi bane
batayi kawai al'adace irinta hausawa, tunda itama Ayyah ai bata kula yayarsu
Maryam, komai sai gwaggo.
Tun Ahmad na
sakandire aji É—aya suka haÉ—u da Samina, an tashi makaranta sun nufo gida shi da
su maryam sai suka iske yara na damben faÉ—a a wani lungu.
Maryam tayi
ƙoƙarin rabasu amma ta gaza, hakan yasa Ahmad ɗaukar ƴar bulala ya tsutstsula
musu a É—uwawu, dole suka rabu kowa na shafa wajen yana kuka.
Yarinya É—aya a
cikinsu sai ta maido faÉ—an akan Ahmad daya dokesu, tsayawa yay kawai yana
kallonta da mamaki, dan alokacin shekarun nata bazasu gaza bakwai ba, inma sun
wuce sai dai Æ´an wattani.
Kuka take kashirɓan
akan saita rama dukan da yay musu, ta kama ƙasan rigarsa ta riƙe tana kai masa
duka da É—an hannunta.
Shi dariyama ta
bashi, dan haka ya tsaya yana kallonta yanayi, ganin da gaske take sai Rahama
ta kamata ta janye tana dungure mata kai, nanko yarinya takuma daddagewa ta
fasa musu kuka harda zagi.
Sunyi mamakin
rashin kunyarta, suka wuce suka barta tana cigaba da zaginsu.
Washe gari sun
taho makaranta suka gamu da yarinyar jiya da ko sunanta basu saniba, tana
ƙyalla ido taga Ahmad saita samu dutse
ta jefa masa, aiko sai akan goshinsa, kafin kace kwabo sai jini.
Dole aka
kaisa ƙyamiz daga nan makaranta, yarinyar kuwa ta tsere gida basu sake
ganintaba.
Bayan kwana huÉ—u
Ahmad ya samu sauƙi ya koma zuwa makaranta, a randa ya koma yakuma yin gamo da
yarinyar nan a hanya ana faÉ—a da ita.
Tsayawa kawai yay
yana kallonta, ya kula batajin magana sam, tana ganinsa ta kwasa da gudu zata
tsere, amma saiya cafkota, kuka ta saka masa da magiyar yayi haƙuri.
Shiko ya zare
mata idanu yana faÉ—in, saiya rama zubar masa da jini da tayi.
Sosai take kuka
tana tsalle da bashi haƙuri, shiko ya tsaya kawai yana kallonta.
Ganin bazata
nutsuba yasashi fadin, “Kinga nutsu na fasa ramawar”.
Tsayawa tai
tana share hawayenta, tace, “Da gaske ka haÆ™ura?”.
Kansa ya É—aga
mata alamar eh.
Hakan ne yasa ta
nutsu, sai kuma takai hannu tana taɓa masa ciwonsa inda aka saka bandejin,
dukta marairaice alamar jin tausayinsa.
Hannun nata ya
janye yana murmushi, yace, “Kinga ai ya warke, yaya sunanki?”.
“Samina” ta
faÉ—a har yanzu hankalinta nakan goshin nasa data fasa.
“Suna mai daÉ—i” ya faÉ—a yana miÆ™ewa riÆ™e
da hannunta, cikin makaranta suka karasa yana tambayarta ajinsu, sashen Æ´an
firamari ya kaita, saida ya kaita har cikin aji, ya É—auki naira É—aya ta
ƙwandala ya bata a cikin kuɗin taransa naira uku da Ayyah ta bashi.
Tun daga wannan
ranar sai yazam kullum Samina saita zo wajen Ahmad, tun su Rahama na mangareta
har suka bari, dan shaƙuwace ta fara shiga tsakaninsu a hankali, harma takai ga
Ahmad yasan gidansu Samina, dan anguwarsu É—aya, sai dai ba layinsu É—ayaba,
tsakanin makarantar su Ahmad da gidansu Samina babu nisa, shiko Ahmad gidansu
da akwai É—an nisa da makarantar.
Haka suka
kasance a tare, idan Samina ta taho makaranta bata shiga sai ta jira Ahmad
yazo, dayake makarantar firamare din kusa take da sakandire É—in, shikuma shine
zai kama hannunta ya rakata har ajinsu yakuma cire ƙwandala ya bata a kuɗinsa
na tara.
Shaƙuwar dake
tsakaninsuce tasa har Ahmad yasan gidansu Samina, wadda ashe bai saniba Æ´ar
uwarsace ta jini.
Dan kuwa Samina
ɗiyar Mama Gaje ce tsohuwar matar Yusha'u ƙanin Hamza daya saki da ciki.
Ashe bayan
fitowarta ta haifi Samina sai tai aure a can garin Bauci, kuma da Samina ta
tafi sannan tana jinjira, haihuwarta biyu acan zaman yaƙi daɗi ta kashe auren
ta dawo kano da Samina, dan wancan mijin ya kwace Æ´aÆ´ansa.
Tunda kowa ya
fahimci hakan a gidan sai ya fara jan Samina jikinsa, yayinda Ahmad yaytama
Kawunsa Yusha'u naci akan ya dawo da mama gaje mahaifiyar Samina gidan dan
ALLAH.
Da taimakon
Ahmad daya kama kafa dasu Iya Ladi Mama Gaje ta sake dawowa gidansu, inda
Samina da Ahmad suka kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya.
A wannan karon
Mama gaje da shirinta ta dawo gidansu Ahmad, dan kuwa sai da ta gama mallake
zuciyar kowa musamman Malam Rabi'u da Iya Ladi.
Dawowarta kuma
gidan ya sake É—aukar sabon salon zama, sai dai kowa na dannewa da kawaici
saboda yanzu akwai Æ´aÆ´a a tsakani.
Da taimakon Ahmad dukan yaran gidansu suka samu shiga makaranta a yanzu,
musamman ganin ita Samina tanayi tunda ba'a gidan ta tashiba.
A haka har
Samina itama ta shigo sakandire É—in dayake maza da matane a haÉ—e, hakan ya saka
shaƙuwarsu ta sake ƙarfi mai ban mamaki, tana aji ɗaya yana aji biyar, amma ko
yaushe suna tare, hakan yasaka abokansa suka fara kiransa da suna Sharukhan
baban soyayya.
Karanta: Bafulatanar Ruga Hausa Novel
GUDU DA WAIWAYE 2
Yakanyi dariya kawai, dan a sannan ba soyayyar
bace a tsakaninsu, duk da dai ta musu kamu basu saniba.
Tun ana yaya da
kawa har abin ya fara rikiɗa yana zama soyayya, soyayyarma mai ƙarfi da
shaƙuwa, kowa ya san da hakan a cikin iyayensu kuma duk da iyayen Ahmad mata
basuso hakaba saboda mugun halin Mama Gaje.
To Amma ya zasuyi
da hukuncin UBANGIJI? Dole suka É—auke idanunsu suka koma musu addu'a da fatan
ALLAH yasa kar Samina tayo gadon halin Uwarta.
Bayan Ahmad
ya kammala sakandire saiya fara bin mahaifinsa kasuwa wajen sana'arsa ta saida
yadikan maza da huluna, amma sai baban yace da hakan ai gara ya koya koda
sana'ar É—inkice ko wani abun.
Ahmad ya aminta
da hakan É—ari bisa É—ari, dan haka yashiga wani shagon koyan É—inki anan bayan
layinsu kusa da makarantar su samina.
kusancin da suka
samune ya kara sake ƙullesu sosai, dan kullum daga gida Ahmad da Samina tare
suke tahowa, saiya rakata makaranta zai dawo shago wajen aikinsa.
Sannan da an
tasosu daga makaranta komi yake a shago sai ya ajiye ya rakata har gida,
wataranma sake biyoshi shagon ta keyi, data shiga gida babu daÉ—ewa zata fito
wajensa su koma tare..
Ƴan shagon kan
musu dariya, musamman da suke ganin sunyi ƙanana, badai za'ace za'ai musu aure
a wannan shekarunba.
Lokacin da Baba
ya fahimci wannan shashancin nasu sai yaytai ma Ahmad É—in faÉ—a, yakuma ce karya
sake ganin Samina ta bishi shago bayan ta dawo makaranta.
Yaji faÉ—an baba
ya dakatar da Samina, amma dukda hakan wataran saita É—an zagaya a É“oye taje,
musamman ranar weekend da babu karatu.
Shekararsa É—aya
a shagon aka yayesa, zuwa lokacin kuma ya kware a aikinsa sosai dan ya nuna
ƙwazo matuƙa.
Ayyah ta fasa É—an
asusunta da takeyi da ribar kayan sana'arta ta siya masa keken É—inki, yayi
murna sosai, hakama yan uwansa sunyi farin ciki, wani É—akin dake cikin gidan
aka fasama kofa ta baya aka saka masa keken É—inkin, sai yazama shike É—inkama
baba yadika ana kaiwa kasuwa a siyar É—inkakku, sai kuma masu kawowa da
yakemawa, harma na mata yana dan jagulawa dukda bai wani ƙwareba saboda dinkin
maza ya koya.
A hankali
hannunsa ya fara faÉ—awa akan dinkin matan ma, kafin kace mi komai ya zama
Alhmdllh, harma yana taimakawa gidansu da abinda ALLAH ya hore masa, gefe kuma
yanama Samina hidima sosai dasu ta karatu da buƙatun yau da kullum.
Ganin yasamu
madogara kuma yana samu Alhmdllh sai yay aniyar komawa karatu.
Kowa ya bashi
goyon baya, dan haka ya shiga kokarin neman gurbi a jami'ar b.u.k.
Ya samu shiga
jami'ar B.U.K, dayake takardunsa sunyi ƙyau sosai, kuma a lokacin tsadar rayuwa
batakai hakaba sosai.
Komawarsa makaranta yasakashi sake zama busy, ko ɗinkima sai yayi da gaske yake samu yaɗanyi, ga kuma aikin yana samu, ganin zai iya korar customers ta wannan hanyar sai ya fara koyama ƙaninsa Mudanseer shima, aiko Alhmdllh Mudanseer ma sai ya maida hankalinsa sosai, sai ya zam yana taimakawa Ahmad ɗin da wasu ayyukan.
Tunda Ahmad
ya shiga rayuwar Samina ya fara canjata sai baba Yusha'u kejin daÉ—i sosai, dan
abubuwa da yawa sai Samina tabar biyema
mahaifiyarta, dan a hannunta ta tashi, lokacin da mama Gaje ta dawo gidansu
Ahmad sai tarbiyyar Samina ya banbanta dana sauran yaran gidan.
DaÉ—in hakan da
Baba Yusha'u ya jine ya sashi zaunar da Æ´an uwansa duka a gaban iyayensu su iya
ladi, aka kuma kira masa Ahmad da Samina, a gaban kowa ya kuma sake damƙa ma
Ahmad amanar kula da Samina, tare da alƙawarin aura masa ita a duk lokacin da
suka kai munzalin girma, ya kumace ko bayan babu ransa bai yarda wannan
alƙawarin ya tashiba.
Murmushi kawai
Ahmad yayi kansa a ƙasa saboda kunya.
Yayinda sauran
Æ´an uwa da tsoffi su malam Rabi'u wannan abu yay musu daÉ—i, dankuwa koba komai
zumincin ƴaƴansu zai ƙara danƙo da ƙarfi.
Albarka kowa ya sakama
abin, tare da addu'ar kaiwa lokacin da rai.
Tun daga wannan
lokacinne kuma Samina bata kula kowanne namiji, kowa yasan an mata miji Ahmad,
hatta da danginsu na Shema kowa yasan hakan.
Mama Gaje dai
batace hakan bai mataba, bakuma taji a ranta zuwa nan gaba idan Samina ta sami
wanda yafi Ahmad zata hanata barin Ahmad ɗinba, idan kuma Ahmad yayi arziƙi
dama ta dawo hannunta, dan kuwa sai yanda tayi dasu Ayyah akansa.
Tunda Ahmad ya
gama secondary ya koya É—inki yana kama Æ´an kuÉ—aÉ—e sai nauyin Samina ya kusan
koma kansa, shine duk wani bukatunta na makaranta, shine dinkinta da bukatun
yau da kullum na É—iya mace, hatta dasu kayan ciki na mata bai gazaba wajen bata
kudin saye.
Wannan hidima
da yake da ita sai ta ƙara saka mata girmansa da ƙaunarsa a zuciyarta, bata da
hira sai ta Ahmad, duk wani namiji a idonta mace ne, Ahmad É—intane kawai take
kallo da gashin arziƙi, shine kuma kawai nagartaccen namiji a idonta.
Bayan samina ta
gama secondary lokacin Ahmad na shekararsa ta ƙarshe a jami'a sai yake bata
shawarar komawa karatu.
Lokacin suna zaune
a ƙofar gidansune a shagon ɗinkinsa suna hira, dama mafi yawan lokuta anan suke
hirar tasu.
Kallonsa tayi da É—an
murmushi ta dukar da kanta ƙasa saboda kunyarsa, cikin muryarta mai cike da
yanga tace, “Haba Hubby, kamar ka manta yanda al'amuran suke a gidannan namu,
idan nace zan cigaba da karatu yanzu a ina baba zai samu kuÉ—in É—aukar nauyina?,
kullum ana haɗa na masara da ƙyar a ina za'a samo na karatu kuma?, sannan a
ziri'ar mu kaf babu macen data taɓa gama secondary sai nifa, shima da
taimakonka, saiko ƙannenmu uku mata da ayanzu suma zasu kammala, iyayenmu ma
bazasu amince naje jami'a ba nima nasani”.
Murmushi Ahmad
dake kallonta da tausayawa yayi, ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idonsa a
kanta, a hankali yace, “Samie na ai komai na ALLAH ne, indai kina da ra'ayin
karatun baki da matsala, dan ba baba zamu dorama wannan nauyinba, nine zan É—auki
nauyin matata da kaina, kinga insha ALLAHU idan ubangiji ya shige mana gaba
sanda zaki kammala ƙila koda karamin aikine na samu, sai maganar aurenmu ko,
kodama baki gamaba inhar aka samu É—an abin rufin asiri sai mu rufama kanmu
asiri a wankemu a miÆ™amu daga ciki kowama ya huta”.
Maganarsa ta
ƙarshe ce ta sakata jan hijjab ɗinta ta rufe fuskarta saboda kunya tana ƴar
dariya.
Shima dariyar
yayi mai sauti yana shafa kansa, yace, “Sorry bazan sake bama matata kunyaba,
ammafa randa aka kaimin ita zan cire kunyarnan dukanta insha ALLAHU”.
Babu shiri Samina
ta tashi ta gudu zuwa gida, duk kiran da Ahmad yake mata akan ta dawo su karasa
magana kasawa tayi, dole ya haƙura ya ƙyaleta.
Daya shiga gidan
suka haɗuma da sauri ta kauda fuska taƙi kallonsa, lokacin suna a tsakar gida
itada su Rumana suna shafa kurkur a fuska.
Murmushi kawai
yay yana É—auke kansa, dan baya wasa da yaran gidan, idan ka cire Samina babu
mai yawan ganin haƙoransa a cikinsu.
Duk sannu sukai
masa, ya amsa kamar yanda ya saba, sai da yazo gab da shiga sashensu ne suka haÉ—a
ido da Samina data saci kallonsa.
Ido É—aya ya kashe
mata yana murmushi, tai saurin É—auke kai
tana murguÉ—a masa baki.
Shigewa yay yana
maijin nishaɗi da ƙarin kaunarta a ransa.
Da daddare
Samina take sanarma mahaifiyarta yanda sukayi da Ahmad.
Mama Gaje da daÉ—i
ya lulluɓe ta washe baki tana rungume Samina.
“Yo Samina wannan
kuwa abin amincewane da guduma, damacefa tazo mana, ai wannan yaro bamusan
abinda zamuce masaba a rayuwa, ALLAH dai ya saka masa da alkairi, yakuma kaimu
lokacin aurenku, dan kuwa Suwaiba ta haifama Ruƙayya, niko Ruƙayya ta rainar
mini”.
Duk da Samina
bata fahimci zaurencen mahaifiyarta na ƙarshen maganarba Babu kunya ta amsa da
amin, dan tana tsananin son Ahmad da har takai batajin kunyar yin duk wani abun
daya shafesa a gaban kowa, iyayensu maza kawai take iya ɗagama ƙafa akan Ahmad.
Hatta kakanninsu
Iya ladi da baba Rabi'u bata jin kunyarsu akan Ahmad.
Sai washe
gari Ahmad ya samu saƙo a rubuce daga wajen Samina akan amsar cigaba da
karatunta.
Yaji daÉ—in hakan
sosai, a ranar kuma ya samu su baba da batun su duka harma da kakanninsu.
Da farko dai
tsoho mai ran ƙarfe malam Rabi'u har yace a'a, danshi kam baiga dabara ba a
wajen nan sam.
Amma sai Ahmad
yayta lallashinsa da nuna masa ra'ayinsa akan matarsa tai karatu mai zurfi,
tunda yanzu suna da dama saita fara kafin shi yaÉ—an samu madogarar da za'ai
hidimar aurensu, in yaso ita saita ƙarasa karatun a gidansa.
Fatan alkairi
yay musu, tunda ya fahimci Ahmad nason lamarin, bai kamata a katse masa
hanzariba matsayinsa na babba namiji a gidan.
Kwana biyu dayin
zancen Ahmad ya amshi takardunta ya tafi dasu makaranta.
Tun daga
ranar Ahmad yashiga faÉ—i tashi wajen ganin ya samawa Samina gurbin karatu,
kasancewarsa mai ƙokari a makarantar yasashi kusanci da mafi yawan malaman
cikinta, ta hanyarsu ya samawa Samina gurbin karatu.
Lokacin da
labarin hakan yazo mata tayi farin ciki harma ta rasa ina zata saka kanta dan
daÉ—i.
Hakama iyayensu
kowa yaji daÉ—i, babu kuma wanda ya nuna rashin dacewar hakan, dan a ganinsu
Ahmad É—in yanada ra'ayin matarsa tasamu karatu mai zurfi shiyyasa ya maida
Saminar makaranta.
Sauran Æ´an
uwantama Æ´ammatan gidan sun tayata murna da wannan cigaba, koba komai suma zasu
saka ran cigaban tunda aka fara daga kanta.
Nauyin
karatun Samina daya dawo kan Ahmad sai ya sa abubuwa suka sake masa yawa, dan
kuÉ—in shigarsa basu kai nauyin É—ukar hidimar da yakeyiba, gashi dai-dai da kuÉ—in
mota wannan sai Samina tazo wajensa take amsa. Ga nauyin karatun Mudanseer ma
shine yake bada mafi yawan ƙarfinsa, dukda mahaifansu na taimakawa tanan ɓan
garen.
Kuma a gefen
hidimar gidama baya zuba ido baneba, yanayin ƙoƙarinsa wajen taimakon
mahaifinsu.
Wannan abubuwan da
sukaimasa yawane ya sakashi fara tunanin faÉ—aÉ—a neman kuÉ—in nasa, akuyarsa da
ya saya Ayyah na kula da ita yace zai saida ya zuba kayan É—inki na saidawa,
saboda akuyar ta haifi yara biyu sai Ayyah ta amince masa aka saida, da kuÉ—in
akuyar yaɗan sayo kayan su zare da wasu ƙananun abubuwa irinsu allura,
almakashi, zips da sauransu ya zuba a shagon, teloli dake cikin gida da masuma
shagunan dake kusa sai sukanzo sukan saya anan, kamar wasa sai ALLAH ya sakama
abin albarka ake ciniki, idan duk suna makaranta sukan É—an É—ebo kayan sayarwar
a ajiye cikin gida, duk wanda yazo saya sai yayi sallama a bashi.
Ahmad bai
tsaya ananba kawai, har komawa yay idan ya taso makaranta ya sari lemuka ya É—ora
a kansa yana zuwa bakin titi saboda motoci masu wucewa, wani lokacin kuma biredi,
ko kayan fruits haka.
Da waÉ—annan
sana'oi da wahalhalu Ahmad ya cigaba da kula da karatunsu shi da Mudanseer da
samina, sauran ƙannensa ma yakan basu gudunmawa, hakama yayunsa dake gidan aure
sukan taimaka masu da abinda ALLAH ya hore musu.
Ahmad ya kammala degree É—insa ya samu yay
bautar ƙasa, daga nan kumane ya dawo zaman gida sosai, dan babu dai maganar
aiki.
Yaci gaba da
sana'oinsa na É—inki da saida kayan É—inki, zuwa yanzu kuma hannunsa ya faÉ—a
sosai ya ƙware, ɗinkuna yake na zamani masu birgewa, duk wasu samari ƴan
kwalisa da Æ´ammata zaka samu É—inkinsu ya fitone daga shagon Ahmad, wanda aka fi
sani da Ahmad sharukhan, idan É—inki yaÉ—an kwanta saiya koma sana'arsa ta sai da
lemo da ruwa, kokuma kayan fruits.
Yanzu dai haka
takai Ahmad yana hayar keke napep ne, yay É—inkinsa da yamma ko dare, da safe
zuwa la'asar yana neman taro da kwabo da adaidaitarsa a gari.
Matsala
ta farko data fara shigowa tsakanin Samina da Ahmad shine, bayan barinsa
makaranta Samina tayi sabbin ƙawaye, sanda yana nan koda yaushe suna tare, sai
dai lokacin karatune zaka samesu ba tareba, duk wanda ma yake mu'amula dasu
yasan suÉ—in masoyan junane.
Samina tun
tana secondary takanyi karatun novels É—in hausa, rayuwar jin daÉ—i da dukiya da
akeyi a novels na ƙayatar da ita, har wani lokacinma takanyi addu'ar ALLAH ya
buɗama Ahmad ɗinta shima yay arziƙi ya gina musu ƙaton gida, ya narka musu
kayan alatu da jin daÉ—i, su ringa hawa motoci na alfarma ita dashi.
A wancan
lokacin burin nata bai taɓa kaita ta nemi canjin Ahmad da masu irin suffar
jaruman littafiba, shiÉ—in dai takema addu'ar ya samu su mora.
Takai koda Samina
ta karanta littafi sam bata wani damuwa da É—aukar darussan rayuwa ko ilimin da
littafin yazo dashi, ita kawai soyayya da kayan ƙawane ke ɗaukar hankalinta da
ƙara faɗaɗa burinta, tama kai inhar buk bana masu ƙazamin arziƙi bane ƴan gayu
batason karantawa, data fara karatun taji ana faÉ—in jarumin littafi nashan
wahalar neman nakansa sai buk ya fitar mata akai ta ajiyeshi, tafi son taji ana
suffanta ƙyawun jaruman littafi tare da dukiyar da tunani bazai iya musaltawa
ba, to takanji kamar tai tsalle ta ganta a buk ɗin saboda shauƙi.
HaÉ—uwarta dasu
Nafy ne ya fara nuna mata hanyar samun cikar wannan burin nata, tun tanajin
haushin kushe mata Ahmad da sukeyi akan talaucinsa har zuciyarta ta fara rawa
da aminta da maganarsu.
Dan kuwa dai
sunyi nasarar fara tsundumata shafe-shafen mayukan bilicin, dukda kuwa tanada
haskenta gwargwadon iko, sannan Samina ƙyaƙyƙyawace babu laifi.
Ƙananun burikan
Samina sun fara faɗaɗa, dan yanzu kowane biki saita san yanda ta ƙwalkwali
Ahmad kuÉ—in ankonsa. Ada bata kula kowane saurayi sai Ahmad, amma zuwa yanzu
kam ai samari babu iyaka take kulawa, dataga kazo da Æ´ar kalar manyan mutane
babu wani jan aji take miƙa kanta.
Tun Ahmad na
zuba mata idanu akan ƙananun sabbin ɗabi'unta harya kasa haƙuri ya tuhumeta
akan bilicin data fara, ya tabbatar masa shi bama ya ra'ayin farar mace,
yafisonta da kalar fatarta choco color, alokaci haƙuri tabasa, ta shirya masa
ƙaryar ba bilicin baneba, kayan gyaran jikine irin namu na gida take amfani
dashi.
Cayay kosu É—inne
tabar amfani dasu sai sunyi aure ya yarda da ingancinsu.
0 Comments