Auren Yarjejeniya 11-12


Bakin Sirri Hausa Novel Complete

Barka da zuwa shafin mu na hausa novels inda ayau ma muka kawo muku littafin auren yarjejeniya 11-12 na Mommyn Fareesa.

Auren Yarjejeniya 11-12

PAGE 12
"lafiya kuma kike kuka?"na zata kun shirya keda mutumin dana hango kunata mgn"cewar lawisa tana k'ok'arin zama kan kujera"wane shiryawa zanyi da wannan me girman kan lawisa?"mena masa da zafi Arayuwa daya zab'i cutar dani da tursasani da iko Akaina?"wai meyace miki ne?"tana share hawayenta ta sanar mata komai harda labarin shima Abinda yashafesa duk ta sanar mata"Amamakin ummu sai taga lawisa na murmushi tace"Alhmdllh! wannan shine mafita kawai k'awata"haba lawisa wace irin mgn ce wannan,kinsan mekike fad'a kuwa??"bansan mutum ba da halayensa zan Amince muyi irin wannan Auren "bayan kuma irin wannan Auren haramun ne lawisa"kece dai ke bakisan saba"Amma Ai kafin ku had'u kinji Ana fad'in sunansa"dan duk wanda yakwana garin nan bazaice besan big man ba"Aganina ki bashi kwana 2 sannan ki kirashi ki sanar masa kin Amince"in har kin sanarwa mubashshir yace"bai shirya Aurenki yanzun ba"kuma kin sanar masa mafitar da Aka samu"sai ki sanarwa big man yaturo kodan ki gujewa Auren wanda bakyaso besonki"Aganina gara ki hak'ura da wannan Auren kiyi Addu'ar zab'in Alkhairi"ki kumayi istahara "dukda dai kinyi Addu'a mama nayi damu da masu k'aunarki"Aganina Auren nan shine mafi Alkhairi ma k'awata"dadai burun mak'iyanki yacika gara kin jure komai Abdallah zai miki"kuma wlh nasan sai sunyi mamakin irin wanda zaki Aura"to Amma lawisa Ayi Auren Azo kuma yasakeni kinga tsugunne be k'areba?" hmm! Amma idan kun rabu ga wanda zaki Aura ko"sannan ko mubashshir yace"beyi wlh kinfi k'arfin kiyi kwantai"kuma bafa dg yin Auren zai sakekiba sai bayan shekara d'aya da rabi ko biyu inaga ko?"gaskiya nidai hankalina be kwanta dana Amsaba"ina tausayin mama lawisa"kuma idan beda halin kirkifa?"sannan nifa bawai rayuwar Aure zamuyiba koda hakan yafaru"kowa d'akinsa daban bbu ruwan kowa da kowa"murmushi lawisa tayi tace"ina zaton shima haka zaice miki"Amma yanzun kifara tambayar mubashshir"idan be shiryaba ki masa bayanin komai"idan kun had'u shine da kansa zai fad'a masa wannan sharad'in idan ya Amince shikenan"zancen bincike kuma Abba zan saka umma tayiwa mgn Ayi" insha Allah bbu wata damuwa"saidai karki yarda kisanarwa kowa manufar wannan Auren"ki nunawa duniya son juna kukeyi"saidai idan har na Amince d'in ko?"sannan muddin be nuna son juna muke ba koda na Amince tofa nima bazan nunaba"Allah dai yazab'a mafi Alkhairi"shima Ai yaka mata yayi Aure kodan sbd d'aukakar dayake da ita"nasan shiyasa mahaifin nasa ya matsa yayi Auren"tab'e baki ummu tayi tana fad'in wannan banzar dakika gani ta mana tsaye itace zai Aura"harda cemun wai karna koma ce mata yarinya sbd ta girmeni"dariya lawisa ta kamayi"sbd ita harga Allah taji dad'in wannan Abu"kuma bata yiwa big man wani mummunan zato kan Auren ba"sannan ita dama bata wani son mubashshir ya Auri ummu sbd basuma daceba"saidai yanda ta hangosu d'azun suna mgn ga kayansu kala d'aya sai ta gansu tamkar wasu masoya"dukda lawisa na yarinya dan ummu ta girmeta da shekara 1"Amma tayi kaifin tunani da hangoma ummu Amfanin ta Amince ta Auri mutum kamar Abdallah....ki tashi muje yamma tayi"cewar ummu tana saka card d'in da big man ya Ajiye mata Acikin hand bag nata"suka jera suka bar wajen....big man ransa fari k'ar yatsaya gefen motarsa yana kallon preety yace"ki koma gida zamuyi waya"wannan yarinyar itace zamuyi Aure da ita sbd bin umarnin mahaifina"idan An kwana biyu lokacin mommy tasami lafiya kin Ida karatunki zan saketa muyi Aure"Amma baby....Amma what? na riga na gama mgn"itama tanada wanda takeso"and last one kinsan bansan surutu da k'ananun mgn ko?"hakane"is good"banaso ki sanarwa kowa komai kina jina?"muddin naji labarin nan wani waje zan iya fasa Auren ki"be jira Amsar taba yashiga mota batare daya koma kallontaba"ta tab'e baki ta nufi motarta itama ta shiga tabar wajen.....
    shiru Abdallah yayi yana tunani yasan dai dole ta Amince dan wannan shine mafita"zuwa sadda zata nemesa sannan sati gudan ya Ida cika saiya sanarwa daddy ya fidda"can kuma yasaki murmushi sbd tunawa da yayi da irin uk'ubar daya tanada dazai mata sbd rashin kunyar datake masa"zai sakata ta masa ladabi kotaso ko kar taso....da wannan tunanin suka iso gida"bayan ya fito dg cikin motar "Aharaban gidan ya hango sadeeq da sa'ada suna karatu"d'auke kansa yayi yacigaba da tafiya cikin nutsuwa"fuskarsa Ad'aure kamar koda yaushe yashigo cikin parlourn"Amamakin sa ya sami hafsat da wani saurayi zaune suna fira"yashige mata sosai...yatsina fuska big man yayi"yaya Abdallah sannu da zuwa"ta fad'a cikin fad'uwar gaba"be Amsaba yatsaya cak! yana binsu da wani irin shegen kallo yace"waye wannan??"Amm....dama d'an uwanmu ne"tsaki yaja ya kalli saurayin yana fad'in get out"duk ranar daka koma shigowa zaka san ka shigo da hujjja"ya fad'a yana jan tsaki"saurayin jikinsa har kirma yakeyi dan sosai yaji shakkar Abdallah" ya mik'e tsaye zai fita"yayinda kan hafsat ke Ak'asa"umma balki ta fito dg cikin kitchen da warmers Ahannunta"da sauri ta dubi sayyeed ta kuma dubi Abdallah dake tsaye yana danna waya yayi bala'in had'e rai"wai tafiya zakayine sayyeed?"Eh hjy zan wuce sai Anjima"be jira cewar taba yafita dukda tana kiransa....bazai koma dawowa ba sbd na hanashi zuwa"nan gidan matan Aure ne"be kamata baligi kamarsa yana shigowa yana shigewa wannan Abarba"ya fad'a yana nuna hafsat"yana kai Aya Azancen yatafi cikin izzah "umma balki tabishi da mugun kallon tsana domin tasan mgn cikin mgn yagaya mata sbd Abinda tayima sadeeq jiya"kuma tunda taji daddy beyi mata zancen Abdallah be fidda wacce yakeso ba"tasan tabbas ya fitar"saidai tasha Alwashin kota halin k'ak'a sai taga bayansa ta mallake komai na gidan"taja wata iriyar kwafa ta nufi dining Area"ita kanta hafsat bataso korarsa da yayiba"sbd tanaso tasamu ta Auri sayyeed d'in d'an k'awar umma balki ne.....
    
 kwance Abdallah yake samqn katafaren royel bed nasa"ya lumshe sexy eyes nasa"yana shafa gashin dake kwance samqn faffad'an k'irjinsa"yana d'aure da towel"tunanin Abinda zaiyiwa wannan cakuri cicin cikon benci yakeyi idan ta shigo gidansa"dukda yana tunanin bazaima kaita gidansa daya gama ginawa last 6month ba"saidai yakaita wani gidan Acikin gidajensa"bud'e lumsassun idanuwansa yayi sbd jin wayarsa na ringing"yatab'e baki sbd ganin kamal ne"d'auka yayi yak'i mgn"hmm! dama su hjy ne zasuyi order d'in kayan Auren wata"inaso na shigo da dare muyi mgn"okay Allah yakaimu"dg haka Abdallah ya yanke wayar"yatashi tsaye yanufi bath room....
       
da misalin k'arfe 8: 45 pm"big man ne da kamal tsaye A haraban gidan bayan sun gama mgn game da kayan da sukayi waya kansu d'azun"kamal ya kalli big man cikin marairaice murya yace"pls ka rakani gidansu my leemart" inaso na ganta sbd nayi bacci cikin nutsuwa....kallon bakada hankali big man yajefasa dashi kafin yace"mudena y'ar haka dakai"karma kaja yarinya ta rainani wlh"wannan zubda girman badaniba"kaida kaji zaka iya sai kayi tayi"kamal yatab'e baki yace"kaji dashi wlh"yanzun dai ka hak'ura da takalar ummulkhairy ko?"yatsina fuska yayi yace"wace haka?"kafini sani"tamace Agaidaka Ai"wani kallo Abdallah yamasa yana tab'e baki yace"banfi 6 hours da rabuwa da itaba"kadena k'arya"dan nasan wannan matsiwaciyar baza tace Agaidani ba"hmm ! kaidai kasani wato har yanzun kana shiga harkanta kenan?"meza'a fasa?"Ai ba yanzun zatayi kukan sanina ba Arayuwa sai nan gaba idan na Aureta"ta hakane kawai zan takata na jata k'asa yadda naga dama"yak'are maganar yana d'age kafad'a irin ko'a jikinsa d'in nan"kamal ya dubesa cikin mamaki yace"mekake nufi Abdallah?"kodai soyayyar k'arya ka k'ullah da itane?"banza yamasa yana danna waya"saida yagama shan k'amshin sa kafin yace"AURE zamuyi da ita Amma na YARJEJENIYA"what?"kasan mekake fad'a kuwa?"kaga dan Allah karka kamun matsala mana"kanata wani zaro ido da razana sai kace wani Abun furgici ne yafaru"jiya daka tsaya ka saurareni dana sanar maka Abinda daddy yafadamun"kaji tsoron Allah Abdallah! dan Allah kasanar mun gaskiyar meke faruwa?"bazan fad'a ba saida safe... rik'e gefen jallabiyarsa kamal yayi yana fad'in wlh saika fad'amun kaji na rantse"shikenan bazan fad'a ba kaje kayi kaffarah"haba Abokina pls ka sanarmun sbd soyayyar da kakema preety"had'e rai Abdallah yayi yaja tsaki yana fad'in na rasa wane irin mahinmanci kabama soyayya Arayuwarka kamal??"cikani na fad'a maka"dan Allah karka tafi"idan tafiya zanyi bana jin komai nace maka tafiyar zanyi"yak'are maganar yana fara yiwa kamal bayanin komai....dg k'arshe yace"taimakonta nayi Akan Amata Auren dole kuma bbu zancen rabuwa da wanda zata Aura"Amma ni idan nagama saitata zan saketa"haba big man! da iliminka da komai zaka Aikata haka?"babufa kyau irin wannan Auren"sannan karka tursasa y'ar mutane idan bataso kabarta mana.....babu wannan zancen dole ta Amince!kuma na tsara wannan Auren ne da ita sbd na takata yadda na gadama"idan na sai tata na koya mata yadda Ake iya mgn da manya saina saketa"saidai inaso kasani muddin kasanarwa Ammi wlh sainayi sanadin daka rasa leemart har Abada kuwa"wani murmushi me ma'anoni da yawa kamal yasaki yana fad'in bazan sanar mata ba huta rantsuwa"saidai inaso kasani ba'asan Inda rana ke fad'uwa ba"kuma bbu wanda yasan me gobe zata haifar?" Amma idan harta Amince bazaka kwanta da itaba idan Anyi Auren ko?"yatsina fuska big man yayi yana fad'in gaskiya ka cuceni" Allah ya isa dakayi wannan banzan tunanin"ni banga Abinda zan kwanta Ajikin taba?"Allah ko?"to shikenan Allah yakaimu bakwai"Aikai dutsene ko?"banza Abdallah yamasa yana tunani"dan shifa yama manta da Ana yin wani sex idan Anyi Aure sai yanzun yatuna"shifa be tab'a zama yaji yana jin sha'awar mace ba"saidai kawai duk sadda yayi mafarki yayi wanka"shi kansa har yana zargin kodai bashida lafiya ne??harka fara tunaninta tun kafin tazo?"wani wawan punch big man yakai masa"ya goce yana dariya yayi gaba"shi kuma yatab'e baki ya wuce ciki.....Muhadu a dinner karfe 8 na dare insha Allah !!

KARANTA:

Munafukin Miji Hausa Novel
Wuta A Masaka 1 By Ayshercool
Auren yarjejeniya 11-12
KWARTON GIDA HAUSA NOVEL 
AUREN YARJEJENIYA 4
AUREN YARJEJENIYA 3
AUREN YARJEJENIYA 2
how to download Hausa novel 
kuruciyar minal 1 to 10 
Gidan Uncle page 30 to 40
Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 46 By Hafsat Bature
bafulatanar ruga hausa novel complete by maman teddy 
Wayyo gindina hausa novel



Post a Comment

0 Comments