AUREN YARJEJENIYA 2 Romantic Hausa Novel

AUREN YARJEJENIYA 2

AUREN YARJEJENIYA 2

Welcome to our romantic hausa novels page where we shared with you AUREN YARJEJENIYA 2 Romantic Hausa Novel written by mommyn fareesa

AUREN YARJEJENIYA 2 Romantic Hausa Novel

PAGE 02

kamal yatab'e baki yana tunanin tsatstsauran ra'ayi da muguwar Ak'ida irinta Abokin nasu wato big man"wanda hssan sarai junuid da tj sbd dukiyarsa suke tare dashi....yana wannan tunanin leemart da sa'ada sukayi sallama suka shigo d'akin"kamal ya Amsa sallamarsu cikin zumud'i yana fad'in babyn yaya Abdallah yau bakije skul ba ko?"sa'ada na murmushi tace"makara nayi wlh yaya kamal ko yayanma besan banjeba"ta k'are maganar suna zama"sbd su tj sun tashi dg kan kujerun"leemart dai kanta Ak'asa ta kasa nutsuwa sbd irin kallon da kamal ke jifar dashi"Akunyace suka gaidasu itada sa'ada"kafin sa'ada yarinya y'ar 13 yrs tace"Anty leemart zanje waje na jiraki"Amma karki jima kizo muje"kinsan yaya 12 pm yake dawowa gida"idan yagane banje skul ba dukana zaiyi"kanta kawai leemart ta gyad'a mata"sa'ada batayi mgn ba ta fice d'aga cikin d'akin sbd driver nacan na jiransu....


Alh mohd jibo shine mahaifin Abdallah"hamshak'in me dukiya ne"sbd tsohon ministern man fetir ne"kuma d'an kwangilane "yataka makamai masu yawa"hasalinsa d'an garin yola ne"kasuwanci yakawosa kaduna shida k'aninsa usman"Alh mohd kyakykyawan gaske ne farin bafulatani"ya had'u da jamilah Anan kaduna sukayi Auren saurayi da budurwa"suna matuk'ar son junansu"shekaransu biyu da Aure suka haifi d'ansu Abdallah"yanada shekara 3 Aka haifi mohd (khalifa)saidai Ana goyonsa yarasu"dg nan hjy Jamila bata koma haihuwa ba"har k'anin mijinta yayi Aure wato usman"bayan shekara 1 matarsa Aysha ta haifi d'an ta sadeeq bayan shekara 4 ta haifi y'ar ta haleematu Ana kiranta da leemart"cikin ikon Allah leemart nada 5yrs hjy jamilah(Ammi)ta haifi sa'ada"daddy da Ammi da Abdallah suka d'auki son duniya suka Azama sa'ada"wanda lokacin da Aka haifi sa'ada Abdallah nada 20yrs"shine da kansa yasaka mata baby"tayi bala'in shak'uwa dashi"tun kafin zuwan sa'ada duniya Ammi na fama da dangin daddy suna cewa" tagama dashi sbd irin soyayyar dayake nuna mata da kulawa"kwatsam shekara 3 da suka wuce daddy yazoma da Ammi da zancen zai k'ara Aure"lokacin sa'ada nada 10yrs"hankalin Ammi yatashi sosai dataga tuni be k'ara Aureba sai yanzun data fara tsufa"dan lokacin 48yrs gareta"wasu najin dad'i wasu najin bbu dad'i"haka daddy ya Auri tsohuwar bazawara balki"tazo da Agolarta hafsat Agidan"wanda ko wata ukku bata k'ullah ba Agidan daddy yasaki Ammi saki 2 "hankalin ta dana Abdallah yatashi matuk'a"kuma yak'i bata sa'ada"Abdallah yasiya mata had'add'en gida ta koma can da zama itada k'anwarta Anty wasilah wacce mijinta yarasu"Abdallah ya cigaba da kulawa da baby sa'ada"saidai yayima umma balki wata iriyar muguwar tsana"yakuma fahimci itace silar raba Auren Amminsa da dadynsa"dama can bbu ruwanshi da ita da kuma y'arta dake bala'in sonsa"umma balki kuwa dama da Asiri ta shigo gidan"takuma raba daddy da matarsa da Asiri"yanzun burunta shine Abdallah ya Auri y'arta"idan haka bata faruba to taga bayan Abdallah ta gaje komai"gashi Abin mamaki data samu ciki saiya b'are.....


Abdallah tun bayan yagama primary skul daddynsa ya fiddasa k'asar waje yayi karatunsa Acan sai yasami hutu yake zuwa nigeria"tun tashin Abdallah miskiline na gidan gaba"da iyayensa kawai yake sakewa sbd yataso d'an gata kuma d'an hutu"sai bayan An haifi sa'ada sannan Aka rage jidashi"Abdallah yakammala digree nasa na farko dana biyu duk Akan fannin kasuwanci"lokacin yanada 30yrs yadawo gida Nigeria da d'inbun nassarori"mahaifinsa yagina mishi camporny na buga furnitures na gida dana waje"bayan shekara 2 kuma yagina gidan man fetur, yabud'e super market kusan guda 3"Acikin k'ank'anin lokaci Abdallah yazama yong bolonia"yanzun yanada 34yrs Aduniya"shekara guda kenan da had'uwarsa da fatima preety"itama ubanta nada kud'i"preety Asali cikin tv da jarida ta fara ganinsa"kafin tayi k'ok'arin zuwa office nasa Amatsayin zatayi order d'in gado"daga nan ta Amshi number nasa tafara cusa kanta"shi kuma dama indai bakan kasuwanci kazo kuyi mgn ba zai iya zaman Awa guda bece maka komai ba"tun yana disgata da wulak'antata harta samu tashawo kansa"sbd har kuka da rok'onsa takeyi yasota"hakan yak'ara fasa kansa"yanuna mata zai iya Aurenta idan zataji dokokinsa"sbd daddynsa dama na matsa masa da zancen ya Ajiye iyali"preety tayi murna sosai da hakan"saidai mahaifinta yace"saita Ida karatunta kuma mahaifiyarta dabatada lafiya ta sami lafiya sannan zai mata Aure"dan komai sai anyima mamanta"Abdallah be damuba da preety tasanar masa"shi dama sbd daddynsa kawai zaiyi Aure"sbd shi mutum ne me tsananin biyayya ga mahaifansa.....

      Abdallah da kamal tun suna yara suke tare har Abdallah yatafi ingila karatu"shi kuma yayi nasa karatun Anan"wanda kamal d'an jaridane yanzun yana Aiki gidan TV"yayinda tj shima da junuid duka Abokansu ne"sai bayan Abdallah yadawo gida Nigeria sukaga yadda yakoma suka nace masa"

      Abdallah dogone wankan tarwada"kyakykyawan bafulatanin usuli"me cike da kyawun haiba da kamala"yanada bak'ar suma da manyan idanuwansa dayake yawan lumshesu"sbd tsabar cikan gashin girarsa har guda ta kusan had'ewa da y'ar uwarta"yanada dogon hanci dg k'arshe sai yayi d'an fad'i"lips nasa bown ne"be cika yawan mgn sbd dan beson yawan hayaniya"mutum neshi me tsananin kwarjini"yanada zuciya da saurin fushi"saidai beson raini"yanada manyan k'wanji sbd motsa jiki dayakeji"kuma irin murd'add'en jikin nan garesa duk gashi"idan kuwa yana mgn wasu har basuson yadena sbd dad'in muryarsa"mutane da yawa na masa kallon me girman kai"saidai yanada sauk'in kai ga wanda yasan halayensa"Abdallah nada halaye guda 3 masu kyau da mutane suka bashi sheda Akai"na farko yana sallah kan lokacinta"na biyu beyin k'arya zai fad'i gaskiya ko A gaban waye sbd be tsoro be shakka"sai Abu na ukku yana yin kyauta taban mamaki"Abdallah na shaye shaye sanadin b'acin ran rabuwar daddy da Ammi yafara"wanda tj da junuid sune silar fara shaye shaye sa" kuma iyayensa basu sani ba"lokacin da kamal yasani hankalinsa yatashi matuk'a"saidai daya fahimci beshan giya hankalinsa yad'an kwanta"yanadai yimasa nasiha Amma be dena ba"Abdallah be tab'a tsayawaba ya kalli wata y'a mace harya furta mata kalmar so"saidai shi Ayita cewa Ana sonsa yana disgasu"shiyasa beson miye soba"idan yaga namiji yarikice sbd mace ba k'aramin haushinsa yakejiba"musammun da yawan matan dake nuna masa ko baya sonsu to yayi k'azamar hud'da dasu"wanda hakane yasa yake tsanar masu cewa suna sonsa"junuid da tj dai basa zina Amma suna soyayyar shan minti.... Abdallah yahad'u tako ina Akwai izzah da nuna Aji Aduk Inda yashiga"be kuma d'aukar raini"sunan big man kuwa A jami'a friends nasa suka saka mishi shi....


KARANTA: 

Auren Yarjejeniya 4
Auren Yarjejeniya 3
Auren Yarjejeniya 1 

Post a Comment

0 Comments