Barka da zuwa shafinmu na hausa novels inda muka kawo muku Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 46 By Hafsat Bature.
Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 46 By Hafsat Bature
KURKUKUN ƘADDARA
E46
Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji
PRISONERS
Launin ja, tun daga kan fuskokinsu zaka shaida irin tsantsar farin cikin da suke aciki, tun kafin ma su sanya kayan ajikinsu har sun fara Imagining irin kyan da zasu yi musu, tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, daga ƙasan Uniform ɗin nasu, wasu haɗaɗɗun rigunan sanyi ne masu dan banzan kyau, launin bright rust red da kuma dark brown, sai faman ɗaɗɗaga rigunan suke yi suna kallonsu, sun rasa bakin magana saboda tsabar murna, ga wasu hats haɗaɗɗun hulunan gayu na mata dana maza masu kyan gaske, Ƙasan akwatin gaba ɗaya sabbin takalmansu ne kala bibbiyu, zubin anckle boots da kuma slippers, Yara fa sun zama ƴan gayu, kaf saida suka zazzage kayan akwatin suna ta kallonsu suna yaba kyawunsu haɗi da nuna irin farin cikin da su ka yi.
Tsohuwa tace su buɗe ɗayan kwatin su duba kayan dake acikin shi, tasan zasu Yi farin ciki, akwai wata ƴar kyauta data sanya musu aciki, taban mamaki, Jin wannan maganar yasa suka tattara uniforms din da komai na akwatin farko suka maidasu ciki suka datse shi, cike da zumuɗi Angel ta buɗe musu akwati na biyu, a danƙare yake da kaya, abu na farko da suka fara Cin karo dashi, hankys ne launin ja da baƙi, mai ɗauke da sunayen kowannan su, sun yi matuƙar Yi musu kyau, Hada mayukan gyaran Jiki dana gyaran gashi, da Set na kayan gyaran akaifa, ga wasu ribboms na ɗaure gashi, Yawanci duk basu san yadda zasu yi amfani dasu ba, amma tunda ga angel sunsan zata Yi musu bayanin komai.
“Tsohuwa, kince akwai gift da kika sanya mana, Ta na ina? Ko su ne waÉ—annan kayan”? Angel ce tai mata tambayar tana kallonta,
Tsohuwa tace”Ku duba daga can Æ™asan akwatin zaku same ta” Jiki na rawa suka É—aÉ—É—aga kayan har suka taddo wrapping sheet É—in dake nannade da wani abu, wanda shape É—inshi daga sama round ne mai faÉ—i, Æ™asa kuma ya É—an tsuke, kallon juna suka yi cikin Æ™agara da son ganin menene aka nannaÉ—e haka, kowa ya baza ido suna jiran ganin menene, A tsanake angel ta soma warware wrapping sheet É—in awani slow, Sai da ta taddo Æ™arshen shi ta yakice paper É—in da aka nannaÉ—e shi, A hankali take bin shi da kallo, Su azeeza duk suka zazzaro idanuwansu ganin wani abun ban mamaki da basu ta6a gani ba, shin kunsan menene? Nasan Kun Æ™osa kuji, To ba komai bane face*MADUBI,*
wani irin farin Cikine ya bayyana akan fuskar angel da ƙarfi ta ambaci sunanshi MIRROR, yayin da take kallon kyakkyawar fuskarta wadda yaushe rabon da taga suffar face dinta tun tana atare da daddynta tsawon shekara huɗu da watanni yama kusa ci ka 5yrs,
Ya burge ta sosai, madubin Round shaped ne mai matuÆ™ar É—aukar ido, Yadda kasan Æ´an Æ™auyen ido sama, Haka suka kewaye madubin Suna Kallon fuskokinsu, sun saki baki kamar lehen sakarai, In ka cire mutun É—aya wanda Yaja gefe É—aya kamar baya maraba da ganin sabon abunda basu ta6a gani ba, su kuwa sai ihu suke Yi suna Murnar ganin fuskokinsu kamar suyi hauka, ÆŠakin nasu ya cika da Hayaniyar su, abun nema ya samu, Tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, Sun tasa madubin gaba Na tsawon lokaci, sai faÉ—i suke wai dama haka fuskokinmu suke? azeeza tace Wai Allah na, dama haka nake da kyau? Komai na fuskata É—an Æ™arami mai kyau, Hanna tace”Nima fa kyakkyawace, Idanuwana farare Æ™yal, ga dogon hanci, ” deeja tace”duk da ban kai ku kyau ba, amma Nima ba daga baya ba, Manyan kyau ne dani,” tana rufe baki yasmin tace”ni matsalata idanuwana Æ´an mitsi mitsi kamar zasu shige ciki, hancina luluyayye, har Æ™wara bakina ma, ” gaba É—aya suka kwashe da dariya hada tsohuwa, parveen dai ta Æ™ura wa madubin ido ita da Rubina sai kallon fuskokinsu suke yi kamar zasu lashe su, har sai da haris Yakai hannu ya danÆ™washi kawunansu tukunna suka zabura, suna faman wurga mashi harara,
“Idan kun gama kallon Æ™urallan ku bamu abun muma mu duba kyawun fuskokinmu” Wani irin kallo parveen tai mishi tare da cewa”shawara kyauta haris, Ka haÆ™ura da duba abun nan, saboda Ina jiye maka tsoron munin fuskarka da zaka gani, zai iya sawa zuciyarka ta buga” kafin haris ya bata amsa deeja ta riga shi cewa”Ki Iya bakin ki Parveen, Ƙarya kike kice wai haris bai da kyau, don kawai yana da duhun fata ne, kuma ahakan Ba Æ™aramin kyakkyawa bane, kawai kina yi mishi baÆ™in Ciki ne,” takai Æ™arshen maganar tana jifarta da harara, hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayi ma haris ba, koba komai deeja ta yabe shi, abunda ma ya Æ™ara burgeshi, da kanta ta ruÆ™o madubin daga hannun angel ta kanga mashi saitin fuskarshi, Atare suka haÉ—a faces É—insu suna kallon juna ta cikin madubin sai dariya suke saki,
Satar kallon danish angel tai don taga a wani yanayi yake ciki, Yana zuÆ™unne a tsakaninsu javed da mubeen, yaÉ—an duÆ™ar da kanshi Æ™as, Yayin da idanuwanshi suke akan yatsun hannun shi, Aranta tace Shi kuma haka zai Æ™are! Kowa Yana kallon fuskarshi acikin mirror, banda shi, wama ya sani ko aljani ne, shiyasa yake tsoron Ya haska fuskar shi Cikin madubi, Amma dai zanso Ya kar6i mirror É—in nan kodan yaga irin baiwar kyan da Allah yae mishi…….” kasa Æ™arasa maganar tai ganin yana Æ™oÆ™arin É—ago da kanshi da alama yaji ajikinshi ana kallonshi,
da sauri ta duÆ™ar da nata kan Æ™asa tana faman tsuke baki, koda ya É—ago Bai ci sa’ar haÉ—a ido da ita ba, Sai suka haÉ—a ido da Haris Ya sakar mishi murmushi yana faÉ—in” Deeja bani abun nan in haska ma Sarkin kyau fuskarshi, Nasan yau danish ko bacci bazai iya yi ba idan har yayi tozali da kyakkyawar fuskarshi,” Ya Æ™arasa maganar tare da sanya hannu Ya ruÆ™o madubin, Ya É—an yunÆ™ura ya miÆ™e ya nufi danish, sai dai kafin ya Æ™arasa danish yae saurin kifa kanshi saman gwiwarshi, bubbuga bayanshi haris yae tare da cewa
“Kar ka bani kunya mana, Kowa ya share ka sai ni na damu dakai, pls bro Ka É—ago ka kalli fuskarka,” batare daya É—ago da kanshi ba yace”Haris i can’t bana son ganin shi, pls ka janye shi daga saiti na, zai iya affecting lafiyata,”
jin wannan maganar ta Danish yasa duk suka É—ago da idanuwansu suna kallon shi, Lamarin ya É—aure musu kai,
Deeja tace”But why danish? Kowa fa ya duba fuskarshi Kuma lafiya lou ba wani abu daya cutar damu, sai kai zaka Æ™i kallon fuskarka? Javed yace “Haba danish idan ma saboda abunda ya faru a tsakanin mu dakai ne yasa kace ba za ka duba abun nan ba, Ina mai baka haÆ™uri just for today a matsayin mu na Æ´an uwa mu kalli fuskokinmu acikin baÆ™on abun nan,”
Lamarin yae matuÆ™ar É—aure musu kai, sai roÆ™onshi suke yi suna yi mishi magiya akan ya kalli madubi amma É—an tahalikin nan yaÆ™i É—agowa, rai aÉ—an 6ace Haris Ya damÆ™i sumar kanshi da niyar ya É—ago da kanshi Ya tursasa mishi akan ya kalli madubin, aikuwa rai a6ace danish ya bangaje haris Madubin dake hannun shi ya kubce zai kife Æ™asa, Jiki Na kerma Ƴan matan su kayi sauri ruÆ™o shi, Ran haris ya Æ™ara 6aci ya shiga zazzaga mishi masifa, deeja tace”Su rabu da shi, dama baya atare dasu, Shi kaÉ—ai yasan dalilin shi na Æ™in kallon madubin, danish ba abun yarda bane, Tsohuwa dai tana atsaye tana binsu da kallo bata tanka musu ba, duk wanda yai magana idonta na akan la66ansa.
Naufal yace” Ku ku ka damu da shi, ae gaya nan ya baku kunya, Kar Allah yasa ya kalli madubin, don ma ya samu ana lalla6a shi ne, Kuma wlh da ace Madubin nan ya fashe silar hankaÉ—e haris da kayi, Da ka ji ajikinka, shashasha” yana huci yai maganar,
“Ni dai A iya sani na, Aljanu ne basu son kallon madubi ko su gifta Ta wurin da aka ajiye shi, idan su ka yi suffar mutane saboda baya 6oye ainihin suffarsu ta jinni, na ta6a kallon wani film da irin hakan ta faru, ina da tabbacin cewa danish Ba cikakken mutun bane, Yana da alaÆ™a da aljanu,” Angel ce tai wannan tunanin acikin ranta,
Gyaran muryar da tsohuwa tayi musu ne yasa suka É—ago suna kallonta, Banda Danish daya kifa kanshi saman gwiwowinsa.
“Ku Æ™yale shi, Idan ya nu na baya son abu to ku daina Æ™oÆ™arin tursasa shi, kuma kada hakan yasa ku zarge shi, Danish É—an uwan ku ne, tamkar uba yake agare ku shi da Haris, Tun É—azu Na lura da irin wariyar da ku ke É—an nuna mishi, shin meya faru atsakaninku ne? Ko wani zai iya faÉ—a mini”? Tai tambayar tana bin faces É—insu da kallo, Deeja ce ta kwashe duk abunda ya faru tsakaninsu tun daga kan batool daya bi cikin toilet ya ruÆ™o hannunta ya damÆ™a ma giant ita, har izuwa irin bugun da suka yi mishi, da kuma yanke alaÆ™ar da suka yi da shi” tun kafin deeja takai Æ™arshen maganarta, tsohuwa ta soma girgiza kanta, Yayin da idanuwanta ke akan Danish daya kifa kanshi, duk sun lura da irin damuwar dake akan fuskar tsohuwa, magana ta soma yi cikin nuna 6acin ranta ga abunda suka yi mishi
“Kada ku kuskura ku Æ™ara É—aga hannu kuce zaku ta6a lafiyar jikin shi, bama shi kaÉ—ai ba, Kowa ma, Nayi mamakin jin cewa kun haÉ—a kai kun bugeshi sai kace wani jaki, ko a shekaru Danish Ya É—are maku amma ahaka kuka rufe ido kuka jibge shi kamar bawan ku, ina hankalin ku ya tafi ne? Musamman ke angel,” tai maganar tana nuna angel da sandar hannunta, Yatsina fuska angel tae tare da cewa”Ae ni ban ta6a shi ba, lokacin da suka jibge shi, Na suma bana ahayyacina kuma da ace idona biyu saina 6alla hannun shi daya ruÆ™e batool, saboda baida tausayi mugu ne shi, inaji ina gani Ya raba ni da batool É—ita, tana kuka ina kuka” daÆ™yar angel ta karasa maganar tare da É—aura kanta saman laps É—inta tana shessheÆ™ar kuka tunawa da irin abunda ya faru aranar, gashi har yau babu alamun za’a dawo musu da Æ´ar uwarsu,
Deeja tace”Har ga Allah danish ya Æ™ona mana rai, yayi mana abunda bazamu ta6a mantawa ba, tabbas shi dan uwanmu ne amma baya atare damu, akwai wata mummunar manufa atare dashi, In ba haka ba meyasa duk irin shaÆ™uwar dake a tsakanin shi da batool bai duba wannan ba, ya rasa dame zai saka mata saida sharri, ae wlh duk abunda ya faru da batool alhakinta na akan wuyanshi, Kuma jira muke ta dawo muga awani hali take aciki, kafin mu Æ™arasa yanke mishi hukunci” Daga cikin zuciyarta take magana, fuskarta babu alamun wasa, tsohuwa sai jinjina kai take yi, Tana kallonta, sai da takai Æ™arshen maganarta tukunna tace”Aikuwa indai kuka ce zaku Cigaba da ta6a lafiyar jikin shi da rabon wata rana ku rasa madafarku, nayi mamaki da Danish ya Æ™yale ku har kuka jibgeshi, bayan yana da Æ™arfin da zai Iya rama abunda ku ka yi mishi, amma saboda Æ™aunar da yake yi maku sai baiyi hakan ba, Saboda baya son wani acikin ku ya cutu, baku da masoyi a duniyar nan daya wuce Danish, shi tamkar jagora ne acikin rayuwarku, ku daina raina shi, akwai ranar da zaiyi maku amfani, amma muddin kuka ce zaku cigaba da nuna mashi wariya acikunku, to tabbas kuwa xakuyi danasani mara amfani…….” Tunda tsohuwa ta soma kora musu jawabi, suka kasa kunne suna sauraronta, batare da suna fahimtar taÆ™ameman abunda take son ganar dasu ba, donsu ana su tunanin basu ga amfanin da zai iya yi musu ba, in banda ya hau gado ya naÉ—e kamar wani basarake,
“Ba lallai ne ku fahimce ni ba, saboda na karanci hakan akan fuskokinku, Shawarace nake baku kyauta, Bana so ku yi danasani Anan gaba, ” har suna haÉ—a baki wurin furta Kalmar danasani, deeja tace akan me zamu yi danasani? Bata bata amsa ba, tace”Ku tattara kayayyakin nan ku maidasu cikin akwatin, Ku rufe shi, sannan Ku kawar dasu gefe inaso muyi magana daku kafin in tafi” da sauri Su haris suka mayar da kayan da suka curo cikin akwatin suka datse shi, tare da jansu gefe É—aya suka jingine su jikin table É—in dakinsu,
bayan sun dawo Tsohuwa ta basu umarnin su miƙe tsaye, Gaba ɗayansu suka yunƙura tare da miƙewa suna kallonta, duk sun ƙagara da suji me take son faɗa musu,
ÆŠaya bayan É—aya take binsu da kallo na É—an wani lokaci kafin ta soma magana cikin muryarta ta tsoffi,
“Tsawon shekara da shekaru Ina Rainon Yara agidan kurkukun Æ™addara, Ban ta6a samun Yaran da suka kwanta min araina ba naji ina Æ™aunarsu har cikin zuciyata irin ku É—in nan ba, Kun ciri tuta, domin kuwa kun kafa tarihi acikin rayuwar tsohuwa tamira…….” murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Inka cire mutun huÉ—u, Angel, deeja, Haris da Danish, Babu walwala attare dasu,
“Naso ace ina da hanyar da zan Iya taimaka maku, saboda Æ™aunarku da nake yi sai dai kash bani da damar yin hakan, Amma ina fatan nan gaba idan muna da tsawaicin kwana mu sake haÉ—uwa daku, duk da nasan zaiyi wuya ………” Kallon kallo suka shiga yiwa junansu, Kamar sun fara fahimtar inda zancenta ya dosa,
“Tsawon lokaci Ina atare daku, Duk da ban amfane ku da komai ba, Amma nafi waÉ—anda su ka yi silar zuwan ku kurkukun nan, Na raini wasunku tun suna Æ™anana tun basusan kansu ba, har suka fara tasawa suna rarrafawa yanzu gasunan sun girma gwanin ban sha’awa, wannan abun farin Ciki ne kuma abun ayaba mini ne, ga wanda yasan ya dace” tai maganar fuskarta É—auke da murmushi, bayin Allah duk jikinsu yai sanyi, Sai kallon suke yi,
“Acikin ku akwai waÉ—anda suke Yi mini kallon muguwa maÆ™aryaciya, Mara amfani, Akwai ma wadda tace dani da tukunyar fulawar dake acikin toilet dinku bamu da banbanci, ” duÆ™ar da kai Æ™asa angel tai, Cikin jin Nauyin maganar da tsohuwa tayi,
“Ba za ku ta6a sanin amfani na ba, sai ranar da bana atare daku, A ranar zaku tuna da irin mahimmancin da nake dashi acikin rayuwarku, kuma a wannan lokacin zaku yi danasanin rashina atare daku, Amma bana son hakan ya karya zuciyoyinku, Inaso ku Æ™arfafa ma juna gwiwa kusanwa ranku cewa, ko babu ni, ko babu wani acikin Æ´an uwanku xaku Iya rayuwa! Domin kuwa ba’a halicci duniya don mu dawwama acikinta ba, dole ne akwai ranar da kowa zai barta, ko muna so ko bama so…….” dakatawa ta É—anyi da yin maganar idanuwanta sunyi jawur a yayin da take kallonsu.
“Abunda yasa na buÆ™aci abaku waÉ—annan sabbin kayan saboda Inaso nima wata rana ku tuna dani acikin rayuwarku, A Æ™alla dai nayi muku abun kirki……..” bata Æ™arasa maganar ba, sakamakon shessheÆ™ar kukan da suka fara, Batasan ya akai suka É—agota ba tunkafin ma takarasa zance, girgiza kai ta É—anyi tana murmushi tace”Jikokina kenan, meyasa zaku karaya tun yanzu? Haba Kar muyi haka daku, kada ku bari hawayen ku su xuba, akwai ranar da zasu yi maku amfani,”
“Dan Allah ki fahimtar damu me kike son faÉ—a mana? Gaba É—aya kin jefa mu acikin ruÉ—ani” azeeza ce tayi magana,
“Bankwana nake Yi muku! ” wani irin bugu zuciyarsu tayi, Tsabar tashin hankali ne ya bayyana akan fuskokinsu, Sam sun kasa furta komai,
“Dama na faÉ—a maku cewa, Ni mai raino ce, a Æ™a’idar aikin masu raino na gidan kurkukun Æ™addara, da zarar yaran da yake raino sun mallakin hankalinsu, to za’a canza wanda zai dinga kula da su ne,”
A matuƙar ruɗe suke kallonta, Wasu har sun fara matse ƙwaalla, ashe basu ji komai ba,
“Zanje naci gaba da rainon Æ™annanku masu taso wa, Ku kuma Za’a canza muku sabuwar da zata cigaba da jagorantar rayuwarku, sai dai fa zaku ga banbancin domin kuwa, Ni ba komai bace akanta, bansani ba kota kawo muku ziyara…..” Cikin sanyin murya danish ya bata amsa da cewa”tazo, namanta ban fada musu bane”
Tsohuwa tace”Bakowa bace face TSOHUWA ZAFREEN! Ita É—in takasance É—aya daga Cikin shuwagabannin dake ruÆ™e da gidan kurkukun Æ™addara! Kaifi É—aya ce, zuciyarta bata da banbanci da dutse, a rashin tausayi Cikin kaso É—ari tana da casa’in da tara…..” tashin hankalin da ba’a sama shi date!! Tuni gwiwowinsu sun jima da sagewa, Zuciyarsu ta tsorata sosai, tunkafin ma suyi toxali da tsohuwa zafreen, Kusan atare Æ´an matan suka zube saman gwiwowinsu, banda angel da mazan,
Sai kuka suke yi suna rokonta akan karta bari akawo musu tsohuwa zafreen, Idan ma yazama dole ta rabu dasu to ta taimaka ta hana akawo musu ita, abarsu suyi rayuwarsu batare da kowa ba, zasu Iya kula da kansu,”
Cikin raunin murya tsohuwa tace”Ae ni bani da ikon da zan hana tsohuwa zafreen zuwa wurinku, Saboda A matsayi ko Æ™afarta ban kama ba, wani abun É—aure kai ma, Ita da kanta ta nemi da abata sashen ku don taci gaba da kula daku, saboda ita ba cikin ma’aikata take ba, Shugaba ce Ra’ayin kanta ne zuwa wurinku, kai Danish ae ka ganta, Tana da babban muÆ™ami, agaban rigarta taurari uku ne, idan baku san ma’anarsu ba, bari in sanar maku, duk wanda kuka gani da Star uku agaban rigarshi To shugabane na gidan kurkuku, A mataki na ma’aikatan prison daga star É—aya yake farawa zuwa star biyu kafin ka samu taurari ukun nan, Idan kuka duba Jikin rigata babu star ko É—aya saboda bani da wani matsayi agidan kurkukun Æ™addara, Raino kawai nake yi”
Cikin shesshekar kuka su parveen suke faÉ—in wayyo Allah mun shiga uku mun bani mun lalace, tsohuwa dan Allah kada ki rabu damu wlh zamuyi biyayya, zamu biki sau da Æ™afa, Tun yanzu mun gane kuskuranmu…..”
haÆ™iÆ™a sunyi matuÆ™ar bata tausayi sai dai ba yadda zatayi, haka Allah ya riga daya Æ™addara musu rayuwarsu, amma fa zasu ci baÆ™ar wahalar da ba lallai bane su Iya rayuwa, Angel duk tafi su shiga damuwa, ita gani take hada Æ™arin donta Æ™etare Iyakar data faÉ—a mata na cewa duk ranar da ta kuskura ta yi leÆ™an asiri to bazasu sake ganinta ba, amma kuma ae koda ta dura tagar bata ga komai ba, sai ma wahalar da tasha, sai dai idan ko dama Æ™arya tayi mata data faÉ—i hakan tun da ta saba canza magana,” numfasawa tayi tare da kallon tsohuwa tace.
“Idan ma saboda sa’in sar da muke Yi atsakanina dake ne yasa zaki tafi ki barmu, ina mai baki haÆ™uri, zan ma iya zuÆ™unnawa saman gwiwowina akan in roke ki, dan Allah badan halin mu ba, kiyi haÆ™uri ki cigaba da zama damu…..” da sauri tsohuwa ta É—aura idanuwanta kan wadda tayi maganar, tayi mamaki ganin angel ce, idanuwanta sun Cicciko tab da kwalla duk da basu zuba ba,
Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta tuntsire da ita, Jikinta har jijjiga yake yi saboda tsabar yadda take yin dariya kamar zata kife ƙasa, Duk suka ƙura mata luhu luhun idanuwansu da suka canza launi saboda kukan da suka sha,
Daga bisani tsohuwa ta dakata da yin dariyar tana kallon angel tace”Unaisa kenan, Ban ta6a tunanin zaki Iya furta hakan da kanki ba, lallai kun tsorata da tsohuwa zafreen tunkafin zuwanta, to agaskiya dai ba taimakon da zan Iya yi maku, shawarar da zan baku shine, koda gigin wasa kada ku kuskura tana magana kuna kallon cikin idanuwanta, na farko kenan, sa’an nan, ba’a sa’insa da ita, musamman ke unaisa, Kina da gangancin ya6awa mutun magana, ina mai gargaÉ—in ki da ki kiyayi harshenki, wurin Yi mata magana, abu na Æ™arshe da zan fada maku, idan tana awuri ba’a tsegumi, ko Æ™yafcen ido, da yafu ce, Har kisa tana iya yi, idan har akai hakan agabanta, idan har kuna son ku ci ribar zaba da zafreen, to kuyi mata biyayya tamkar zaku bauta mata, idan ta bada Umarni, Jiki na rawa kuyi gaggawar yi mata shi, babu musu, idan har baku kiyayi abunda na fada muku ba, tabbas zaku yiwa mutuwar ku kutse tunkafin lokacinku yayi, ” wani irin wahalallan yawu kowannan su Ya haÉ—iya, wasu har sun fara jin zazza6i ajikinsu, sun tsorata da tsohuwar nan da za’a kawo musu,
“Ba lallai bane, kullum ku dinga ganinta, kamar yadda kuka saba ganina jefi jefi, saboda ita É—aya ce daga Cikin shuwagabannin kurkukun, zaima yi wuya a sati ku ganta, Zata iya É—aukar tsawon kwanaki bata leÆ™o ku ba, Ta inda zaku samu sauki kenan, domin kuwa baiyanarta ba alkhairi bane……”
Muryar su azeeza ce ta katse mata hanzarinta,
“Tsohuwa yanzu shikenan tafiya zakiyi kibarmu? Fuskokinsu sharkaf da hawaye hada majina,
DaÆ™yar ta Æ™aÆ™alo murmushi akan fuskarta tace”Æ™warai kuwa tafiya zan yi in barku, babu tabbacin zamu Æ™ara haÉ—uwa, ni dai shawarata agare ku shine, Ku daina gaba da junanku, ku hada kanku, kuma ku kawar da idon ku ga duk wani abu da É—an uwanku Danish zaiyi, ku daina fushi dashi, hakan zai iya haddasa mashi matsala acikin zuciyarshi,” ajiyar zuciya ta É—an sauke kafin ta É—ago suka haÉ—a ido da angel,
“Jikata unaisa, Baki ya mutu, tsohuwa zata tafi ki huta da ganin mummunar fuskarta, meyasa banga kina farin Ciki ba”? Tai tambayar tana sakin Æ´ar dariya, angel kuwa fuskarta aÉ—aure take, ta tsuke baki, baiwar Allah damuwa ce danÆ™are akan fuskarta, ” a hankali tsohuwa take buga sandar hannunta, wanda ke nuni da cewa akwai wani abu da hakan ke nufi, sai dai basu fahimci dalilin dayasa take bubbuga sandar ba, dakatawa ta É—anyi still idonta na akan angel taci gaba da cewa
“Ƙaramarsu babbarsu, ki cigaba da taimakon su kamar yadda kika saba, Inajin daÉ—in hakan sosai, haÆ™ika zuwanki cikin rayuwarsu tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, ki haÉ—a ka Æ´an uwanki, kada ki bari wani abu Æ™alilan ya shiga tsakaninki da waninsu, kuso junanku, ku sama ma kanku farin ciki, duk runtsi duk wuya kada kuyi kuskuren da zaisa ku raba kawunanku, idan har kuna son cimma burinku, Inaso ku É—auka cewa ku kamar
*MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MAKU FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARKU, TABBAS KUNA DA DAMA*
Amma fa dole sai kun yarda da kanku, kun haÉ—a hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare daku, Sa’annan
*KU NE MAKULLAN DA ZAKU BUÆŠE TA*
Nasan a yanzu bazaku ta6a fahimtar kalamaina ba, sai nan da wani lokaci, Aranar da kuka fita hayyacinku, wasu ma basa araye, To awannan lokacin ne zaku gane me nake nufi…………”
(Idan Allah yakaimu na Kammala Free pages of Takun farko, zan É—auki hutu, kafin acigaba da middle step, saboda in samu natsuwa kafin in dasa, ba jimawa zanyi ba, Æ´ar tazarace, Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun Æ™addara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za’ayi adding naka a paid group kuma za’a sanyaka a comment section, Sa’annan Ba’a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne Kuma yaja ma kanshi zamu É—auki mataki*
*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuÉ—in zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika É—auko hoton reciept ka tura mana*
KARANTA:
Gidan Uncle page 30 to 40
0 Comments