Wuta A Masaka 1 By Ayshercool

Bakin Sirri Hausa Novel Complete

Bakin Sirri Hausa Novel Complete

Wuta A Masaka 1: Da misalin ƙarfe goma na dare, Gari yayi shiru, wasu daga cikin al'umma sun adana kawunansu a cikin gidajensu, domin hutawa rayukansu hidindimun da akayi da Rana.

Sedai a ɓangare guda kuma sautin kiɗane ke tashi a wani ƙaton ɗakin taro, mutane nata shiga da fita kamar Rana, se kaiwa ake ana komowa da Abinci da abin sha kala kala, da gani base ka tambaya ba kasan bikine ake na masu hannu da shuni, duba da haɗuwa da tsaruwar ɗakin taron, da kuma kalar mutanen dake zarya a gurin, da uwa uba danƙara danƙaran motocin dake fake a harabar gurin taron.


Ango da amarya na kan high table suna kallon wanda suka halarci bikin nasu, Yayin da ƙawayen amarya da abokan ango, dangi 'yan uwa da abikan arziki keta cashewa a filin rawa, anata bajinta gurin zuba musu kuɗi, dj se ƙara zigasu yake suna ɓarin kuɗi yayin da matan keta cashewa.


MC ne ya fara magana ta speaker yace "Masha Allah, gaskiya na yadda wannan bikine na masu arziki, madalla ƙawayen amarya da abokan ango ina godiya da wannan bajinta da ku ka nuna, da kuma kara da ku ka yiwa Amarya da ango, sedai ana tsaka da wannan shagali na samu sanarwar, isowar wasu hamshaƙan jiga jigan baƙi da suka amsa gayyata domin tayamu nishaɗi a wannan biki na 'ya'yan gata, wannan baƙin ba kowanne bane face DJ Sultan, tare da 'yan tawagarsa na rawa, ciki hadda wannan tauraruwar taku, wadda ludayinta ke kan dawo, tauraruwarta ke haskawa a cikin manyan yara da suka yadda da kansu wajen iya cashewa, wato gimbiya Amira, nasani ga dukkan wanda suka saba zuwa guraren taron biki, birthday da makamantan su, da duk wanda yasan dj Sultan da tawagarsu nasan sun san wannan gimbiya, kai ga wanda bema santa ba yau ze santa, zatazo ta baje mana baiwarta ta nishaɗantar damu, ina fatan kuma zaku nuna mana farincikinku ta hanyar nuna bajintarku, DJ idan ka shirya, Sultan da jama'arka muna buƙatar ganinku akan stage"


Wata waƙa aka saka me sanyi, wasu mazane suka dinga fitowa, suna sanye da baƙaƙen wanduna da fararen riguna, bayanta an rubuta Dj Sultan, sekuma sunayen su a ƙasa, su huɗu haka suka zo suka jeru a tsakiyar filin, suka sunkuyar da kai, kamar masu jiran umarnin wani, sumarsu duk ta sha dying, kowanne da kalar askinsa, wanine ya kuma shigowa filin shima, sanye da shiga irin tasu, ga uwar suma akansa se ƙyalli take ya tsaya a cikinsu suka zama su Biyar.


Mutane sun zuba ido  suna jiran ganin gimbiya Amira, kowa ya zuba ido wasu tyni sun zaro wayoyi zasu É—auka, amma aka shafe wasu mintuna bata bayyana ba, se jan rai da ake yi, har wasu suka fara Æ™osawa.


lokaci ɗaya aka canza waƙa, aka saka wani kiɗa me sauti da ɗaukar hankali, Ta wata ƙofa ta fito, sanye da crazy jeans, da baƙar riga, ta ɗaure kanta da siririn ɗan kwali ta zubo kitson gashin doki da tayihar ɗuwawunta, ƙafarta sanye cikin wani uban takalmi kamar na sojoji, tana da matsakaicin tsayi, idanunta kamar na Japanese, tana da dogon hanci, sedai ba fara ce tas ba, tana da shape ɗin jiki me kyau, dan kayan sun zauna a jikinta sun kamata tsam tsam a jikinta, kana ganin duk wani shape na jikinta, kallo ɗaya zaka yi mata kaga yarinya ce ɗanya, dan dudu ba zatafi shekaru sha shida zuwa sha bakwai ba, amma tana da jiki me kyau da ɗaukar hankali.


Yanayin tafiyar da take, yana tafiya daidai da sautin kiÉ—an dake tashi, shewa mutanen hall É—in suka shiga yi, suna tafa mata dan yadda take tafiyar cike da É—aukar hankali da burgewa, tsakiyar mazan nan taje ta tsaya, tana tsayuwa suka É—ago kansu daga sunkuyarwar da sukayi.


Wani irin kiɗa aka saki, aikuwa suka fara rawa a tare, sedai yadda Amiran take rawa kamar ba jikin ɗan Adam ba, Kamar me jikin roba, tafi mazan nan iya sarrafa jikinta cikin ƙwarewa da jan hankali, duk inda ta karya jikinta kota lanƙwasa haka mazan nan keyi, duk wani tsalle da juyi haka itama ke yinsa, attach ɗin kanta na bajewa.


Nan da nan hall ya É—au shewa, masu video nayi Masu hotuna nayi, nan aka shiga É“arin kuÉ—i akan Amira.


Sunyi rawa kala kala Babu alamar Amira ta gaji da rawar nan, suka nishaÉ—antar da mutane sosai, agogon hannunta ta kalla, ta silale daga kan stage É—in, se nemanta akayi aka rasa.


"Mungode mungode, DJ Sultan da tawagarsa, jinjinar ban girma ga Gimbiya Amira, munagodiya da wannan gudunmawar da aka bamu, Muna fatan Allah ya maida gimbiyarmu gida lafiya"


Amira kuwa zuwa tayi ta canza shiga, ta saka doguwar riga akan kayanta, kamar ba ita tayi wannan uwar rawar ba.


Zagayawa tayi inda dj suke zaune, tace  "Sultan, yau mun samu kuÉ—i sosai, bani 10k zan hau Mota, senaji alert"


Sultan ya kalleta Yace "ke Amira, har 10k?"


"Eh ko ba zaka bayar bane?"


Sultan yace "A'a, ni na isa ince bazan bayar ba? Ni a wa?"


"Dalla ka hanzarta ka bani, zan tafi gida inje mu fafata, kuma fitar yau tayi kyau, dan mun samu kuÉ—i wallahi maga ba dai dai ba zanyi dirar mikiya a Chamber inyi rashin mutunci"


Sultan yai murmushi yace "ki huta gimbiya, bame miki ba daidai ba ai girmanki ne, in bake babu mu" ya ƙarasa maganar Tare Da ƙirgo kuɗi ya bata.


Yayin da aka cigaba da shagalin biki, ita kuma ta silale tai waje abunta, agogon hannunta ta kalla, sha biyu saura na dare, kuma gurin bikin ma basu da niyyar tashi yanzu.


Cikin hanzari ta fita titi, duk babu masu abun hawa, se  É—aiÉ—aiku, ji take tamkar ta rufe ido ta ganta a gida, dan ta san yau da drama.


Wata uwar ƙatuwar motace ta alfarma tayi parking a gabanta, aka sauke glass ɗin motar.


Wani Babban mutum ne a ciki, wanda a ƙalla ze kai shekaru hamsin da biyar, ya kalli Amira Yace "Baby ina zuwane muje in sauke ki?"


Ƙare masa kallo tayi, ta ɗauke kanta.


"Haba Me kyau, be kamata kiyi ta tsayuwa a gurin nan ga dare ba, ina zakiyi".


"Hausawa zanje" ta bashi amsa.


"Ok shigo in saukeki Mana"


Ba tunanin komai, Amira ta buɗe gaban motar ta shige abunta, wani sanyi da ƙamshin turaren jikinsa sun gauraye cikin motar.


Ya fara jan motar a hankali, ya kalleta Yace "Gimbiya Amira, kinci sunan naki gimbiya fa, gaskiya kin nishaÉ—antar damu sosai, na daÉ—e banga 'yar baiwa ba kamarki"


ÆŠauke kai tayi kamar bata san meyake cewa ba, ya É—an kalleta Yace "magana fa nake Gimbiya"


Maimakonsa ta bashi amsa, se tace "Idan kaje zoo road zan sayi abu"


"Meye abun?"


"In munje ka gani" ta bashi amsa


Yaita surutunsa amma taƙi Magana, suna zuwa gurin masu gasa kaji tace "yawwa ɗanyi parking, zan sai kaza"


Yace "haba Amira, aiba girmanki bane, bari inje in siyo miki"


Bata kuma cewa komai ba, ya fita daga motar, ya ɗan jima sannan ya dawo motar, hannunsa ɗauke da manyan ledoji, ɗaya na kaza ɗaya kuma na abun sha, ya miƙa Mata.


Tasa hannu ta karɓe tace tagode.


Tai tayi masa kwatance har sukazo bakin wani layi, ta kalleshi tace "Nagode fa a nan zan sauka"


"Ahh haba dai, mu ƙarasa inga gidannaki mana"


Ta kalleshi tace "gidana kuma? Kaga a nan zan sauka zan ƙarasa"


"Amma Yakamata muyi exchanging number, sannan ai Yakamata muyi sallama"


Amira tace "Yallaɓai wace sallama kuma?"


Ya wani matso daf da ita yana ƙasa da murya Yace "haba Gimbiya, wannan ai ƙwalele ne, duk yadda kikaje kikayi wannan karairayar kice zamu rabu ba sallama haba Baby"


Yai maganar yana ƙoƙarin naniƙar Ameera, hannu tasa zata buɗe motar amma taji a rufe, ta juyo a fusace tace "malam ka buɗemin in fita, bana son iskanci fa"


"Wane irin bakya son iskanci, nifa bana son wani kame kame, meye na wani damuwa ko ɓoye ɓoye, bayan kin nuna wace ke, kinyi talla na biyo kuma kiƙi siyarwa, kinga in dai kuɗine baki da Matsala, zan kashe miki ko nawa ne"


KARANTA: Auren Yarjejeniya 11-12


Zaro ido tayi tace "dagaske?".


Da sauri ya jinjina kai Yace  "Æ™warai dagakse mana"


Kamar abun arziki ta zira hannu a rigarta, ba zato ba tsammani ta zaro wata 'yar ƙaramar wuƙa, se ƙyalli take ta kalleshi tace "Wallahi, idan har baka buɗemin motar nan na fita ba, sena yanka wannan ubsn tumbin naka da wuƙar nan, kuma in toshe duk wata hanya da za'a gane nina yi".


Zaro ido yayi Yace 'ke kina mace kike yawo da wuƙa haka, har kike iƙrarin zaki kasheni?"...... Tohfa readers gashi dai nadawo hutu Ayau Ina fatan nasameku Lafiya...in littafin yayi muku tom sai nace muku Muhadu a breakfast din gobe Insha Allah.

KARANTA:


Post a Comment

0 Comments