Barka da zuwa shafinmu na Hausa Novels!A yau, mun kawo muku cikakken littafin Bakin Sirri wanda Jiddah S. Mapi ta rubuta.
Ku kasance tare da mu don karanta wannan littafi mai kayatarwa, Bakin Sirri Hausa Novel Complete
Bakin Sirri Hausa Novel Complete
Shirya komai sukayi gidan sai ƙamshi yake yi, wanka tayi Abdul ya taya ta suka shiryata tayi matuƙar kyau cikin atamfa, kallonta yayi yace "unty sweety atamfa yana miki kyau sosai"
murmushi kawai tayi tace "Abdul idan nayi aure tare zamu tafi ko? bazan iya barinka a gida inacan gidan wani ba, mun saba sosai mun shaƙu da juna"
murmushi yayi yace "unty sweety ance idan kinyi aure mun rabu ba zamu zama kamar da ba, please ki ɗan ɗaga auren nan, kece ƙawata kece yayata meyasa zakiyi nesa dani?"
hanu ta mika mishi alaman yazo, mika mata hanunshi yayi ta janyoshi jikinta tace "karka damu zan roki momy ta rinƙa barinka kana zuwa hutu a gidana kaji? amma ba zan iya ɗaga auren nan ba, zanso nayi aure na haifi ƴata nasa takwaran momy, duk da banga mijin da zan aura ba amma nasan zaimin insha Allah"
murmushi yayi yace "Allah yasa kiyi farin ciki a gidanki kamar yadda muke yi anan"
"Ameen kanina"
sakinshi tayi tace "6 yayi yanzu zasu shigo naga sakon momy"
turare ya fesa mata shima ya fesa kafin sukaji karan buÉ—e kofa, muryan momy sukaji tana amsa sallama, kallonshi tayi "sunzo"
lekawa yayi ta window yace "kwarai sunzo bari naga angon"
baiga wani matashi a wajen ba, da sauri yace "unty sweety tsoho ne mijin mun shiga uku"
da sauri ta bige kanshi tana lekawa, ganin babu saurayi tace "wayyo Allah na shiga uku Abdul wallahi ba zan fita ba, da alama wannan tsohon ne"
hanunta ya rike yace "muje idan tsohon ne saina É“ata komai, kinga wancan shocking É—in? jona mishi zanyi a jiki har sai ya daina motsi"
dariya tayi tace "yawwa kanina shiyasa nake sonka Amma kada su momy su gane"
momy ce ta kira wayanta tana É—agawa tace "ku fito sunzo"
Abdul ne ya rike hanunta suka fito tare, ta rufe kanta zuwa fuskanta da mayafin, murmushi sukeyi su duka, sun zauna akan kujera suna kallonta, a gefen momy Abdul ya zaunar da ita, momy tace "ki gaishesu"
a hankali tace "ina wuni?"
cikin fara'a suka amsa da "lafiya"
kanta a kasa mutumin yace "sannu Æ´ata" a hankali tace "yawwa"
Abdul ne ya kaikayata, da sauri ta janye kafarta, mutumin babban mutum ne, kana ganinshi kasan yaji kuÉ—i cikin nutsuwa da magana irin ta manya masu kamala yace "sunana Alhaji Ahmad Dikko, niÉ—an asalin garin Adamawa ne aikine ya kawoni nan Abuja, sai kuma Allah ya haÉ—ani da Abbanki wato Alhaji Abeed, ganin yadda yake kula da mutane yake bawa kowa respect yasa nace idan akwai Æ´arshi ina nemawa É—ana aurenta, ya amince yace ba komai hakan yasa na kira É—ana wanda yake zaune acan kasar London nace yazo gida maza-maza anyi mishi mata, hakan yasa ya dawo yau ma saukanshi nigeria" kallon kofa yayi yace "gashi nan ma ya karaso dama waya yake yi a waje"
Abdul ne ya fara kallonshi kyakkyawan saurayi ne, a kunnenta yace "wallahi ya haÉ—u harma ya kusa ya fiki haÉ—uwa"
bigeshi tayi tana cigaba da sunkuyar da kai, matar dake zaune tace "ki buÉ—e fuskanki kiganshi Æ´ata, idan ya miki"
a hankali ta zame mayafin sukayi ido huÉ—u dashi, yana zaune a kasa yanason shima ya kalleta, waro ido tayi ganin wanda suka haÉ—u É—azu ya kusan bigeta da mota ne, da sauri tace "kaine?" shima tambayan da yayi mata kenan, momy cikin mamaki tace "kunsan juna ne dama?"
shiru sukayi, Amminshi tace "kin sanshi?"
"yaune ya kusan bigeni da mota saida wata ta taimaka min"
da sauri momy tace "shine baki gayamin ba?"
"kiyi hakuri momy hankalina yana kan neman Abdul ne shiyasa"
"wace yarinya ce ta taimaka miki?"
bankaÉ—o kofan É—akin akayi da karfi har saida suka tsorata su duka suka kalli kofa, cikin fusata tace "Abdul? waye Abdul a gidannan? Abdul?"
momy kallonta tayi daga sama har kasa, gabanta taji ya faÉ—i da sauri ta mike tace "ke baki iya sallama bane?"
kallo É—aya tayi mata kafin ta watsar taci gaba da kiran sunan Abdul, a tsorace yace "nine"
cikin rashin tsoro ta karaso inda yake riga dogo ne a jikinta da É—an karamin mayafi sai takalmi irin na maza canvas ta É—aure igiyoyin, cikin zafin rai taje gabanshi ta rike hanunshi "muje inada magana da kai"
jan hanunshi tayi zasu fita sweety ta tsaya a gabanta, itama cikin É“acin rai tace "me zaki gaya mishi wanda ba zaki iya faÉ—a a gaban family É—inshi ba?"
kallon banza tayi mata kafin tace "bana magana da butulu wacce bata iya godiya akan Alkhairin da akayi mata ba saide tayi magana akan sharri, da wannan mara kunyan yaron nake magana bada ke ba kin gane?"
jan tayi sweety ta rike hanunta tace "baki isa ki shigo har cikin gidanmu kice zakiyi mana rashin kunya ba zaifi miki kyau ki saki hanunshi"
kallon cikin idonta tayi "idan naki fa?"
Amal dake tsaye a wajen ta kasa yin komai sai kallon yarinyar take, sam batada kunya ga taurin kan tsiya, a hankali tace "ya isa haka, meya miki da zaki fita dashi?"
"zaifi kyau idan kin tambayi É—anki dan inada tabbacin baki bashi tarbiyya me kyau ba..."
hanu sweety ta É—aga zata mareta da karfi ta rike hanun ta murÉ—a tana kallonta "karki fara wannan kuskuren"
kallon Abdul tayi wanda ya zuba mata ido a tsorace, cikin fusata tace "meya haÉ—aka da kanina?"
a hankali yace "wani kaninki?"
"ka fini saninshi meya haÉ—aka da Areef Anas?
zazzare ido ya fara, cikin tsawa tace "zaka faÉ—a min ko saina wanke ka da mari?"
bakinshi yana rawa yace "ba...ban.."
mari me zafi ta ɗaukeshi dashi, duk mutanen wajen saida suka zaro ido suna kallonta, har saida mayafinta ya zame akanta, gaban amal ne ya faɗi ganin yadda tulin gashin yarinyar ya warware ya bazo gadon bayanta, cikin masifa tace "zaka faɗa min ko saina saɓa maka?"
"ban mishi komai ba"
wani marin ta kuma É—auke shi dashi, hanu tasa ta fara dukanshi tako ina, wannan matashin dake tsaye buÉ—e baki kawai yayi yana ganin abin mamaki, Amminshi dake tsaye tace "Yazeed ka hanata mana, ko dai mahaukaciya ce?"
girgiza kai yayi "ban sani ba Ammi"
itama sweety ta tsorata bayan momy taje ta É“uya, kowa yana yin baya a tsorace, Yazeed ne yaje wajen yana janye Abdul, kallonta yayi yana mamakin karfinta domin ta rikeshi da iya karfinta tana dukanshi, ganin ba zai iya kwace Abdul É—in ba ya fara rike hanunta yana hanata dukan, da kyar ya haÉ—a hannayenta duk biyu ya rike, sai fizgewa take ya riketa kam kam kafin ya fara janta zuwa waje, inda sukayi parking na motocinsu ya kaita, tana huci tana cewa "ka...ka...ka sakeni"
saida ya buÉ—e motan ya turata ciki kafin ya zagaya ya shiga, tana kokarin buÉ—e marfin ta fita ya rufe da key, hon yayi aka buÉ—e mishi da sauri ya fita da ita a gidan, baisan ma inda zai kaita ba kawai tafiya yake yanaso suyi nisa da gidan, jingina kanta tayi da jikin kofan motan ta fara kuka, da kaÉ—an kaÉ—an yake juyawa yana kallonta, a ranshi yace "ko dai da gaske tanada hauka?"
ganin yadda ta barbaza gashinta tabar takalminta a gidan ya nemi gefen hanya yayi parking, buɗe mata yayi yace "fita kibarmin mota, kuma wallahi idan kika koma gidan can saina kakkaryaki, sannan kika sake kika taɓa matar da zan aura saina..."
shiru yayi dan ta jima da fita a motan tunda yace ta fita, bayanta yake bi da kallo tana tafiya tana sharan hawaye, fesar da iskan bakinshi yayi kafin yace "omg wannan meke damunta? anya nayi daidai da zan barta ta tafi cikin wannan halin?"
da sauri ya kunna motan ya bita, a gabanta ya tsaya ya fito yana kallonta, juyawa tayi zata tafi ya kuma bin inda juya É—in ya tsaya, share hawaye take, hanunta kawai ya rike ya maidata motan, buÉ—e mata yayi taki shiga, yace "idan baki shiga ba zan shigar dake"
a hankali ta shiga ta zauna, shima shiga yayi, ya mika mata goran ruwa, fizgewa tayi tasha rabi sannan ta aje sauran, gyaran gashinta tayi sannan ta gyara mayafin taci gaba da kallon hanya, bini bini yake juyawa yana kallonta, saida suka hau titi yace "ina zan kaiki?"
da hanu ta nuna mishi ya fara bi har suka isa unguwansu, a bakin kofansu tace "ya isa"
murmushi yayi yace "to malama ki rage masifa kinji? duk abinda yayi miki nasiha zakiyi mishi ba wai duka ba, kinji?"
gyaÉ—a kai kawai tayi kafin ta buÉ—e motan ta fita, harta isa bakin kofa sannan ta juyo ido huÉ—u sukayi tace "na gode"
murmushi yayi yana ganinta ga buÉ—e get ta shiga ciki, jan motan yayi ya tafi.
sweety sai duba kofan shigowa take har yanzu shiru baizo ba, bataji daÉ—i ba sam a ranta, aina ya tsaya? ba dai da wannan yarinyar yake tare ba har yanzu? rike Abdull tayi tana shafa mishi pain relief a goshi, ammin Yazeed tace "wannan yarinyar batada kunya, ace kizo har gidan mutane ki daki É—a a gaban uwarshi? nidai nasan sai yaya da kani ne suke iya haka a gaban iyayensu amma wannan anyi marar kunyar yarinya"
shiru momy tayi tana kallon sweety da take hurawa Abdul ciwon da yaji a goshi, Abeed ma sai kallonsu yake yana mamakin abinda yasa tazo har gida tayi mishi wannan dukan, hakuri ya baiwa su ammi da Abba kafin yace "zamuyi magana insha Allah ina mai baku hakuri dan Allah"
atare sukace "ba komai Allah dai ya kiyaye gaba"
Ameen.
tafiya sukayi abeed ya zauna akan kujera yayi shiru yana huci, da alama ranshi ya É“aci sosai, momy dake tsaye tazo gefenshi ta zauna, hanunshi ta rike tace "kayi hakuri"
kallonta yayi "meyasa kike bani hakuri? bacin ba kece kikamin laifi ba"
shiru tayi kafin tace "sabida naga ranka ya É“aci sosai"
a fusace yace "koma wacece wannan yarinyar sai nayi maganinta, ta É“ata rana mafi muhimmanci a rayuwar Æ´aÆ´ana, bansan abinda Abdul yayi mata ba amma tayi babban kuskure data shigo har cikin gida ta dakeshi, saina É—au mataki akanta"
"na baka goyon baya kayi mata duk abinda zakayi dan nima ta É“ata min rai, batada kunya, amma mu fara bincikan É—anmu me yayi mata har tayi mishi wannan hukuncin"
"koma me yayi mata ai bai cancanci tazo har cikin gida ta samemu da baƙi tayi wannan rashin mutuncin ba, yanzu me ɓakin zasuyi zato? kikasan me zasuce yasa tayi wannan hukuncin? kina gani fa har yanzu Yazeed ɗin bai dawo ba, wallahi duk wanda ya ɓatawa ƴaƴana shima saina ɓata mishi sau dubu" tashi yayi yabarsu a wajen, dafe goshi tayi, sweety ta rungume abdul tana lallashinshi sai kuka yake, kallonshi momy tayi kafin tace "me kayi mata?"
sweety tace "haba momy kina ganin dukan da tayi mishi da wanne zaiji? da wannan tambayan ko zafin dukan?"
"bake na tambaya ba shi nake tambaya "me kayi mata?"
cikin kuka yace "ban mata komai ba"
"karya kake kayi mata waye Areef É—in?"
"kaninta ne kuma É—an class namu"
"to meya haÉ—aka dashi?"
shiru yayi yana kukan, zaro sucket na caji tayi kafin tace "zaka faÉ—amin ko sai nayi maka wanda yafi nata?"
rikeshi sweety tayi tana kareshi daga kallon momyn, cikin kuka yace "shine baya mana magana kullum shine shahid yace mu bashi wani abu a gora, shine muka gwarwaya ruwan da ruwan cikin goranshi, da yasha shine ya fita a class har aka tashi bamu ganshi ba, shine muke nemanshi har aka fara ruwa, dana fara kuka sai shahid yace na daina kuka muyi karya muce ba abinda mukayi mishi"
salati ta fara tana tafa hannu "Abdul shine abinda zakamin?"
"momy kiyi hakuri dan Allah"....
KARANTA:
Gidan Uncle page 30 to 40
0 Comments