Barka da zuwa shafin mu na hausa novels inda ayau ma muka kawo muku littafin munafukin miji hausa novel.
Munafukin Miji Hausa Novel
A rikice Ridayya take kallon Mama, da alama ta kasa yarda da kuma fahimtar zancen nata. Mama ta ce "Wallahi tallahi bani da haɗi da wani Zameer, ba dangin iya babu na baba, ai asali da tushen shi yana ƙauye da ina jin? Almajiri ne sosai a nan makarantar almajirai ta Malam Iro, tun yana ƙarami dai da kashinsa a gindi aka kawo shi, ba kowa zai san ba ɗan Kano bane, tunanin kowa mune iyayensa"
Bakin Mama Ridayya ke kallo, ta kasa sanin ainahin inda zata zuba kalaman nata, har ta fahimta daidai. Da ƙyar ta buɗe baki ta ce "Mama kin gane wa nake magana akai anya? Mijina fa Zameer ɗan'ki"
"A'a gyara kalman bakinki, ban yi cikinsa ba balle na haifa na ba ki shi ki aura, bai kuma sha nonona ba, lafiya ras nake da alama kece tunaninki ya yi ƙaura daga kwakwalwarki, nutsuwarki ta bar gangar jikinki, Zameer Almajirin Malam Iro ne" Ridayya ta fara kallon Mama dishi-dishi hawayen da suka jima da yin hijira daga idanunta suka fara bin fuskarta ba tare data shirya zubar su ba, bakinta na ɓari da ƙyar take iya motsa bakin saboda ƙonan fuskar daya kame tare da tattare wa waje guda.
"Me ya sa Mama? Me ya sa kika É“oye wa iyayena gaskiyar al'amarin? Kun rufe ni kun cuce ni"
Mama ta buga cinya ta ce "A'a a hir ɗinki wallahi kar ki kuma cewa mun cuce ki, idan akwai wanda ya cuce ki bai shige iyayenki ba, da suka kasa yin bincike a kan wanda za ki aura, sai kuma zuciyarki data zama kurma akan Zameer ɗin, don me ake cewa a yi bincike kafin aure? Ai saboda irin haka ka je ka auri ɗan fashi ko kidnapa babu uban wanda ya sani, kinga ni fice mini daga gida kada ki saka bakina ya yi tsini" Kuka Ridayya take kamar ranta zai fita wannan wanne irin lamari ne? Ikon Allah da ƘUDIRAR ALLAH ke riƙe da rayuwarta a yanzu. Waye Mijinta? Ina ne garinsu mene mafita? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un.
"Mama kin cutar da rayuwata ki sani Allah ba sai bar ki ba, na san ba za ki so a yi wa ɗiyarki dake gidana haka ba, domin aure ba abin wasa bane" Sheƙeƙe Mama ke kallon Ridayya kafin ta ce "Wacce ƴar rawa ce a gidan ki?"
"Khairiyya!"
Ta bata amsa a raunace ƙirjinta na ɗaga wa sama, kamar wacce Asthma ke shirin kama ta. Mama ta ce "Tab, wata aba ce haka kuma? Bani da wata yarinya mai irin wannan sunan nikam" Dam! Ƙirjin Ridayya ya bada sauti juwa na ɗaukar ta, ta sulale a wajan tana riƙe da ƙirjinta sunan Allah take son kira ta gagara furta komai. Ganin haka ya saka Mama figar hannunta ta ce "A'a ba za ki mace mini a gidana ki ja mini jarfa da zunɗe, ke da can ba ki yi tunani da nazarin wanda kike tare da shi ba sai yanzu da masifa ta faɗa miki? Ni duk wani Almajiri nawa ne ba ruwana da sanin waye shi" Ta hankaɗa Ridayya waje ta rufe ƙofar gidan. Tana faɗin
"Yaran zamani da masifar kwaɗayin abin hannun samari, da shegen iyayi da kinibibi da kunga namiji yana murza shadda ya kafa hula kyakkawa da shi sai ku liƙe masa? Ba kusan kura ce da fatar a kuya ba, yawanci cima zaunane masu burin tsiya, su kuma iyayinki ganin Allah ya rufa musu asiri suka bashi ke da tunanin ya cancanta, ko kuma tunaninsu arziƙi gare shi?" Ta yi ƙwafa tana komawa tare da zama ta ci-gaba da yanka albasa da kabejin awarar daren da take yi almajirai da ƴan unguwa na siye, ta girgiza kai ta ce "Ai bada kuɗi ne kawai arziƙi ba, hadda miji na gari a wannan zamanin arziƙi ne, ni kuma mene nawa? Kuɗi kawai ya biya ni ya ce na yi masa komai a matsayin uwa" Haka kurum ta ji kamar bata kyauta ba na ɓoye gaskiyar waye Zameer da ta yi, kila a kyau masu sonta wanda suka fishi nagarta da komai, idan ta tuna kuɗi ya bata fa sai ta ji ko a jikinta. Ta share batun Ridayya tare da ci-gaba da aikin gabanta domin a yanzu bata da wani abu daya dameta.
Ƙafafuwanta kawai take cillawa ba tare da sanin inda take saka su ba, wani irin duhu ne ya mamayewa idanunta jiri na ɗaukar ta tare da ƙoƙarin yasar da tsamurarren jikin nata, har ta ƙarasa tsakiyar titi bata sani ba, dukda irin horn da masu abeben hawa suke mata. Wawan burkin da aka ja, da kuma sauke mata lafiyayyen marin da aka yi ya saka ta dawo cikin hayyacinta mutumin daya fito daga cikin mota ba shiri ya ce
"Ke wacce irin mara tunani ce da za ki zo tsakiyar titi kamar kin samu hanyar gidan ubanki, e?" Wani ya leƙo daga mota ya ce
"Da ka yi mata afuwa bana jin data da cikakken hankali fa, ko babu komai a girme ta girmeka sai ta ci albarkacin hakan" Cikin kumfar baki ya ce
"Matsalar ta ce wannan kuma hauka ai bani na ja mata, irin su ne masu yawa mutane bala'i"
Murmushi Ridayya ta yi idanunta akan mutumin ta ce "Rashin adalci da ka yi mini daka hana motarka bi ta kai na, wallahi farin cikina a yanzu bai shige mutuwata ba, inama baka dakatar dani ba? Ina ma ka take ni ka yi gaba abinka, babu mai ce maka don me, mai gata shi ake nema wa ƴanci" Ya yi tsaki yana komawa mota ya ce "zafin talauci hauka ne? Kowa idan masifar yunwa ta masa yawa sai ya nemi kashe kansa aikin banza aikin wofi, wahala ku ta ganku" Ya yi wa matarsa key tare da barin wajan, Ridayya ta bisa da kallo domin kamar ba Hausa yake mata ba, laɓɓansa kawai take kallo ta kasa fahimta. Ɗaya mutumin mai bawa Ridayya wancan haƙuri ya dinga kallon Ridayya, yarda maganarta ke fita a hankali a kuma taushashe da yarda take marairaice fuska a shagwaɓe ya saka ya fahimci yarinya ce masifar wahalar rayuwa ce ta mayar da ita haka. Daga gefe guda yana mamakin wasu mutanen da basu iya taimako ba sai gori da arziƙi kamar iyalan ƙaruna.
Ya fito daga motar ya ce "Sannu baiwar Allah kamar kina buƙatar taimako?" Ta yi masa ƙuri da idanunta ta kasa furta komai saboda kwarjinin da ya yi mata. A hankali ya zaro kuɗi a aljihu ya miƙa mata ya ce
"Gashi kya ci abinci"
Kamar ƙaramar yarinya ta maƙale kafaɗa, ita yanzu ba kuɗi take buƙata ba, wanda zai ja ta ya rungume ta ya rarrashe ta, shi take so. Yin duniya taƙi amsa, sai kallonsa take kamar zata bisa, ya zaro card ɗinsa da number shi ya ce
"Ki kira ni, when you need my help ok?" Ta amsa ya juya a hankali ya ji ta ce
"Abbiey!"
"What? What did you say?" Ta juya da sauri ta bar wajan, ya yi murmushi a fili ya ce
"Ikon Allah" kuɗin daya fito da su ya bada sadaƙa da nufin Allah ya bata lafiya ya kawo mata sauƙi cikin lamuranta. Mota ya shiga daman akan hanyar barinsa garin yake.
Ridayya bata nufi hanyar gidan mijinta ba, tafiya ta cigaban da yi bakinta na motsa wa kamar bai magana, harta ƙarasa gidan Baffa, yanayin yadda taga gidan ya saka ƙirjinta bada wani ƙyakƙyawar sauti, bai yi kama da gidan da mutane suke rayuwa tare da wanzuwa a cikinsa ba, ya dinga kallon cikin gidan daga waje babu mota ko ɗaya sai uwar ƙura duk flowers ɗin sun bushe sun mutu murus ya zama kamar kofai. Ta runtse idanunta sunan Allah take son kira amma ta kasa, me ya sa sai yanzu take buƙatar jin ra'ayin Mami a kan lamarin aure da yardar ta? Me ya sa Mami bata taɓa janta a jiki ba? Me ya sa sai yanzu take son rayuwa da Maminta. _When all is gone...!_
Hannu ta sak ta dinga bubbuga ƙofar gate ɗin a raunace ta ce "Baffa ka buɗe mini ƙofa na dawo, Mamina na dawo gani na zo ba zan ƙara zaɓar kowa a kan ku ba, Mamina buɗe mini ni ce Ridayya" ƙofar take bubbuga wa sosai ta ce "Bakwa jina ko? Yunwa na ke ji Mami shi ya sa muryar tawa babu ƙarfi, Mamina zan ƙara haihuwa za ki samu jika, Baffana wai ka dawo ashe kana nan" Shiru ba amsa, ta dinga buga wa da iyakar ƙarfinta. Ta matsa ɗaya ɓarin ta ƙura wa side ɗin Ustaz idanu tana tuna sanda yake bata abinci ya goyata tana tuna yadda duk wani motsinta yake kan idanunsa. Ta rufe ido tana sauke ajjiyar zuciya a cikin raunatacciyar muryarta mai tsananin sanyi ta ce.
"Abbiey, i miss You"
Waje ta nema ta zauna da nufin ta jira su dawo ko unguwa suka je, sai dai Ridayya bata san sun yi tafiyar da babu waiwaye balle batun dawowa a cikinta ba, sun je inda ko wanne mai raye sai ya ke ko baya su, sun je gidan gaskiya. Tana ta zaune ko motsi bata yi saboda galabaita ga cikinta daya fara motsi alamar yana cikin wata na huɗu yanzu yana buƙatar ɗaukin gaggawa, a nan wajan bacci ya ɗauketa. Ita yanzu ba kowan kowa ba ce, but an unprivileged woman
Lagas/ Ikeja
Birnin Legas, ko kuma Birnin Ikko, shi ne babban birnin Jihar Legas da ke Najeriya. Legas yana É—aya daga cikin birane mafi girma da yawan jama'a a Afirka da ma duniya bakiÉ—aya. Legas ne birni na biyu mafi girma a Afirka, kuma na bakwai a duniya.
Government Residence Area (GRA). Unguwa ce babba mazuna manyan mutane.
Idanunsa a lumshe yake sauraran maganganun da ake yi ta cikin wayar dake saman kujera wacce ya sanya a handsfree. Yadda yake sauke ajjiyar zuciya a hankali yana tura hannunsu cikin kansa za a É—auka bashi ke yin wayar ba, É—an gajeren tsaki ya ja a fili yana haÉ—e yatsun hannunsa wanda suka bada wasu sauti kafin a hankali ya buÉ—e sanyayan idanunsa masu kaifi da wani kwantaccen sirri a cikin su. Cikin gajiya da maganar mutumin ya ce
"Enough" Ya faɗa cikin kakkausar murya yana mai sauke numfashi da ƙyar saboda nauyin ƙirjinsa da yake ji. Ta cikin wayar aka ce.
"Be patient Ustaz Bilal, ka ɗauki ƙaddara watanni nawa da faruwar hatsarin nan mun yi iyinmu mun faɗa maka gabaɗaya mutanen ciki sun ƙone" Ustaz Bilal ya manta da waye yake waya cikin hargowa ya dakawa DSS (Department of State Security) tsawa ya ce
"Liar, wanne irin hatsari ne a ce kowa ya rasu, my own family? Kana nufin na rasa kowa, e? Mene amfanin (IPO) a cikin police ne?"
DSS ɗin ya ce "Investigating Police Officer" Ustaz ya jinjina kai ya ce "Good, to ya ƙara bincikawa familyna suna raye kar ka sake kira na muddin bada Baffa za ka haɗa ni ko Junaid ba" Ya kashe wayar yana miƙewa tsaya, Nasir ya dinga bin Ustaz Bilal da kallo a ɗan tsorace domin bai taɓa ganin zallar masifar Ustaz irin yau ba, ana cewa masifaffe ne bai taɓa gani ba amma yau shi kam zai bada labarin haka. Ya miƙe ya ce
"Md komai ya yi zafi maganinsa Allah, ka yarda da ƙaddara ka yarda cewa dukkan mai rai mamaci ne, ka yarda cewa aljalinsu ne ya zo lokacin ɗaya, mutuwa wajibi ce hisabi gaskiya ne, rayuwa ƙarya ce kuma wa'adi ce, ina iliminka ina da tauhinka"
"Yana gidan ubanka, na ce yana gidan Ubanka Nasir tsahirta mini" Nasir ya ja baya yana gwaloido ya ce "Asstagafirullah, yau Ustaz da zagi? Wallahi dole na saka Hajiya ta yi maka aure" Ustaz Bilal ya yi kamar zai shiga ɗakinsa yana zuwa dab da Nasir ya saka hannu ya damƙo shi tare da jansa har bakin ƙofa, ya cilla shi tare da rufe ƙofar yana dafe kansa ya ce "Haihuwa za ka saka a yi mini ba aure ba, stupid".
Nasir ya dinga dariya, koba komai yau ya ja Ustaz da magana a ƙasan zuciyarsa kuma yana mai tausayinsa domin duk wani bincike ya nuna Ustaz Muhammad-Bilal ya yi rashin ahhalinsa yana buƙatar mai kula da shi, ba kowa yanzu Ustaz ke buƙata ba face Mata wajan zata kula da shi, amma shi ganin kansa yake tamkar waliyyi bai taɓa jin ko da wasa Bilal ya yi maganar mace ba, balle kuma aure ko bashi da lafiya ne Ohho ko irin first love ɗin nan bai taɓa gwada yi ba.
Nasir yana ƙoƙarin ficewa mota na shigowa cikin gidan, ya ware Idanu ya ce "Wonder shall never ends, wa nake gani kamar Baita?"
Murmushi ya yi yana buÉ—e idanu tare da watsa hannu alamar oho maka. Nasir ya daki kafaÉ—ar Baita ya ce "Let's keep a joke aside, when did you came?"
"Jiya" Baita ya ce a taƙaice yana kallon Nasir, sai kuma ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na tashi, wani abu na son fusgarsa da son ɗarsa abun da bai shirya ba. Allah Allah yake ya ƙarasa wajan Ustaz babban amininsa ya yi sharing damuwarsa da shi. "Shi ne ba waya? Ko chat?" Baita ya ɗaga kafaɗa ya ce "Bazata" gaba ya yi abinsa ya ce "Ustaz fa? Md"
"Kamar ka shiga, don baya cikin nutsuwarsa wallahi yau ko Bank bai je ba" Baita ya tsaya cak tare da jin abinda yake faruwa da Ustaz É—in, don dama yana ta kiran wayarsa bai É—auka ba. Nasir ya san Baita ba zai magana ba hakan ya sa ya ce "He lost his entire family in an accident" Baita ya zaro ido sai kuma ya runtse da kyau yanzu da me zai ji da rarrashin Ustaz Bilal ko kuma da matsalar yarinyar da ta tsaya masa curr a rai?
Iskar hadarin dake kaɗawa ya sanya Ridayya farkawa daga bacci wahalar daya ɗauke ta, ba tare data shirya ba. Ta miƙe da sauri tana murza idanunta tare da kallon gate ɗin gidansu har yanzu basu dawo ba? Ta juya taga duhu ya fara a hankali ta ce "Ko sai yaushe za su dawo? Mamina, Baffa gobe zan dawo na ganku kun ji?" Ta ja ƙafa ta nufi gidanta ta mance da cewa yanzu ba mallakin mijinta bane. A ƙofar gida ta samu Zameer a zaune ya wanka wani voyel mai laushi har farar singlet ɗin ciki ana gani ya yi kyau, gefensa kuma leda ce sarai ya ganta ya share ya ta nufi ƙofa sai ta tsaya ganin gidan a garƙame da kwaɗo. Ta juya ta kalle shi ta rasa dalilin daya sanya yau ko kyansa bata gani ba, duk yadda ta kai da danne zuciyarta wajan ganin bata ji zafinsa ba. "Ka buɗe mini?"
"Daga ina kike?" Ya tambaye ta yana miƙewa tsaye tare da mayar da wayarsa zuwa cikin aljihu, ta kafe shi da ido taƙi magana. Daram! Ya ji zuciyarsa ta buga, ba tare da sanin dalili ko hujjar hakan ba, abu ɗaya ya fahimta, rashin tsoro da tausayin da suke shimfiɗe a idanun Ridayya yau babu su, tarwai yake kallon cikin idanunta, ya rufe ido ya buɗe wannan kwantacciyar soyayyar babu ita idan har yaren soyayyar daya karanta idanunsa sun faɗa masa daidai. "Daga ina kike? Kar ki bari na maimaita maganata idan ba haka ba, za ki mamamkina"
"Mamaki na nawa kuma ZAMEER?" Ya zaro ido jin ta ce Zameer yau Ridayya ta kalli cikin ƙwayar idanunsa ba shakka ba tausayi, da wannan soyayyarta ta, kai tsaye gatsal ta ce Zameer? "Sunana kika kira Ridayya, sunana Ridayya" Still idanunta a cikin nasa ta ce "Kenan daidai na faɗa ashe, Zameer ko?" Ya shanye mamakin ya san fushi ta yi yana mata daɗin baki zata sakko, sai dai ko a fushi Ridayya bata taɓa tsare shi da wannan rikirkitattun idanun nata ba sai yau.
"Daga ina kike?" Kai tsaye ta ce "Gidan iyayena, gobe ma zan koma don ban tarar da su ba" Ya yi wani murmushi ya ce "Opps sorry, ai na manta ban faÉ—a miki ba iyayenki duka sun mutu babu kowa da ya yi saura hatta wannan farin mutmin Bilal ko? Shi ma ya mutu?" Murmushi ta yi dukda jiriri ta ji yana kwasarta ta ce "Tom, buÉ—e mini gidan" Don ita ta san babu yadda za a yi kowa nata ya mutu yabar cikin wannan rayuwar.
"Na faɗa miki Baffa mota ta bi ta kansu ta, an ce ma kansa ya gutsire kuma huta ta babbake su kamar yadda ake babbaka taya....," Saukar wani lafiyayyen mari Zameer ya ji a fuskarsa, tunda yake a duniya ba a taɓa marinsa ba, marin daya shige shi irin yau ba, ya juya ya sake juyawa yaga babu wanda wake gani a gabansa sai Ridayya. "Ke! Wa kika ga ya mare ni ya gudu?" Kai tsaye ta ce "Ni ce, kuma ban gudu ba" Ta faɗa tana shigewa gidan Zainaba. Zameer ya bi Ridayya da kallo domin ya san ba zata taɓa marinsa ba, ƙarya kawai ta yi kansa har wani za fi ya ɗauka.
Zainaba na zaune kamar daga sama taga Ridayya ta shigo a rikice domin ta ɗauka Zameer ya biyo ta, bata taɓa tunanin zata yi wa Zameer ko da tsawa ba amma sai gashi har mari, ba zata taɓa cewa ga sanda ta mari Zameer ba. A gigice Zainaba ta bawa Ridayya ruwa ta sha, ta bata abinci amma taƙi ci hannunta ƙanƙame da card ɗin da mutumin ya bata. "Tunda ba za ki ci abincin ba, kwanta ki huta idan kin tashi sai ki yi wanka"
"Ina son Zameer ya sake ni, hallayarsa bata irin mijin da nake so ba ce" Wani farin ciki ya mamaye zuciyar Zainaba amma ta É“oye ta ce "Saki kuma? To idan ya sake ki ina za ki?" Ta ce "Wajan Baffa da Mami ko Abbiyena" Zainaba ta jinjina kai ta ce "Kuma zai sake kin?"
Wani irin kallo Ridayya ta yi wa Zainaba sai kuma ta yi murmushi ta ce "Wallahi wallahi Allah na gama zama da Zameer wallahi sai ya sake ni" Zainaba ta yi hamdala tana ƙoƙarin tashi Ridayya ta ce "Zauna na ƙarasa miki labarina wanda na fara, zan baki gabaɗaya labarin a daren nan, domin daga gobe ba za ki ƙara gani na ba" Zainaba ta gyara zama sosai, Usman mijin Zainaba da sauri ya dawo ƙofar ɗaki ya zauna cike da zumuɗin jin cigaban labarin Ridayya. Ridayya ta lumshe idanunta a hankali ta ci gaba da bawa Zainaba labarin.....
Back to story
Baffa ya saki babyn tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa, Bilal ya yi saurin tare ta, ta faɗa hannunsa ya yi saurin rungume ta a ƙirjinsa saboda jin ta tsala ihu. Gabaɗaya suka kalli Baffa wanda har lokacin babyn yake kallo wacce take ƙirjinsa ya yi girgiza kai ya ce
"Bana ƙaunarta wannan ba ƴata ba ce a kaf zuri'ar Mai ran ƙarfe babu baƙin mutun babu mai munin wannan jaririyar, ni Alhaji Mansur Rano bani na yi cikin wannan yarinyar ba a nemi ubanta wani wajan....
KARANTA:
Gidan Uncle page 30 to 40
0 Comments