Barka da zuwa shafinmu na hausa novel inda ayau muka kawo muku littafin Juya ta Haihu Hausa Novel Complete.
Juya ta Haihu Hausa Novel Complete
Shafi na farko 1
Fitowar ta daga wanka daga dan karamin bayin dake chan lungun gidan su tana gyara daurin zanin wankan nata tana chewa ‘mama na fito, nakai miki naki ruwan chiki ne kema kiti wankan koh sakiji saukin zafin nnan da akeyi yau , dattijuwar da bata wuche shekaru 47 ba amman saboda talauchi da yanayin rayuwa zakache ta kusa 60, tana tsugunne gefen wasu duwatsu uku da aka jera domin girki da itache tana hura wuta tache ‘uhm uhm Nahla, bari idan na gama girkin nnan se nayi wankan kawai gaba daya, dan yanzu idan kikache zaki ansa ki karasa girkin wankan naki ai ya tashi a na banza, wacche aka kira da Nahla tache yawwa mamata kinfi kowa sona daman na sani , bari naja miki na sirki daga rijiya sena ajiye miki a gefe kinga na rage miki wahalan debowa, mama tache gwanda dan koda kin shirya daman sekin debo min harda wanda zan wanko bandakin dashi idan na gama, duk sukayi dariya, Nahla ta dauka bokitan karfe biyu dake kusa da rijiya ta karasa dasu ta chikasu sannan takai ka ajye mata kusa da bayin ta wuche daki domin shiryawa.
Tana shiga dakin ta ta dakko wani kwando dake dauke da kayan shafan ta ta dakko mai shafawa ta zauna kan yageggen ledan dake gefen katifar yan boarding din dake dakin tana shafawa mama ta leko tache, nidai ina mamakin wannan irin hali naki, ache duk zafin da ake a duniyan nnan inhar kikayi wanka sekin shafa vaseline, bata karasa magana ba sukaji sallaman Abi yana chewa hakannan mahaifiyar ta take itama, sudai suji fatarsu na danko da taushi kaman balanbalan dinda aka chikawa ruwa shiyake sakasu farin chiki, duk zafi kuwa haka Ammah take shafa mai itama, Nahla jin an anbata mahaifiyarta ta tashi ta fito tana washe baki tana tambayar baban nata ‘dagaske Abi, Ashe Ammi na gado bata karasa ba Abi ya daka mata tsawa yache ji shashanchi Dan Allah batula, bata karasa shiryawa ba amma daga jin anyi magannan uwarta ta fito, ya kara mata tsawa yache kin wuche kin karasa shiryawa koh sena saba miki, idan kinga dama kuma ki mulke man dukkan shi a jikin ki kaman danwake ki huta.
Nahla ta koma chikin dakin ta tana share hawayen ta da suka fara gangarowa fuskar ta, batasan meyasa duk sanda babanta ya dakkoh magannan mamanta koh ta tambayesa akan asalin mahaifitarta se ran abi ya bachi ba, duk sanda ta tambayesa ya bata labatin mahaifiyar tata seya koreta chikin tsawa , fushi, da fada, bayan abin nata koh da wasa baya daga mata murya ballantana ya mata tsawa, tana chikin shiryawa taji Abi nache mata mamana idan kin karasa inason magana dake, tasan baze wuche dan ya lallasheta ba saboda daga muryan sa da yayi mata, tunanin haka yasata murmushi tache toh Abi gani nnan fitowa.
Nahla ta dai san che Hajiya batula ba itache ta haifeta ba dan tana shekara 9 mahaifiyarta tache mata zatayi tafiya itada babban yayanta dakeda shekara 17 a lokachin, bayan tafiyanta da wata uku baba ya kawo hajiya batul yache mata daga yanzu ita zata dinga kirada mama, itache mamarta, kuma tindaga lokachin take jinta kamar itanche ta haifeta, tunda Hajiya Ammah ta tafi da danta kuwa yau shekara 9 kennan babu su babu labarin su.
JUYA TA HAIHU Chapter 2
Tana fitowa daga dakin da sauri sauri tache baba magannan urgent ne yanzu koh zaa iya bari sena dawo daga aiki, kaga yau zan ansa albashi kuma dashi zamu chika na sake jamb da kuma biyan kudin jami’a dazan shiga wannan shekaran, baba yache ba yanzu naganki kin dawo daga gidan mai chanji ba,daman baki karasa aikin bane kika fito yawo’ tache aa na gama nasu aiki na dayan gidan da nakewa aiki ne yanzu zanje nayi wanke wanken yanma da shara su sunada mai gyara chikin gidan ni kuma nake wanke wanke da sharan bayan gidan nasu, baba yache yaushe kika nemi wani aikin banda na gidan mai chanji nahla, mama che ta ansa da chewa aa alhaji kadai manta ne ammah na fada maka lokachin data samu, gidan chanjin da duk aikinsu da wankin gidan nnan ita keyi tun safe bata dawowa sai yanma a karshe suke biyan ta dubu 7 a wata, wannan kuwa wanke wanken safe da yamma kadai 20k zata anso yau inshaallahu, ai kaga idan ta anso ta hada da na chan data ansa safiyar yau semu ajye dubu 25 ma bokon mudan saya kashi mu lasa da sauran dubu ukun daze rage, baba na kallon yarsa dake kwankwadar farau farau din kokon safe da mama tayi chikin muryan tausayi da rauni yache kiyi hakuri Mamana Allah be bani arzikin share kukanki ba a duniyan nnan, be ajye magana ba ta rungumesa tache babana ban chanchanchi hakurin nnan da kake bani ba, babu abin da kayimin banda nuna kulawa da soyayyarka a gareni garin nema mana abunchi da kudin da zamu raayuda idonka ya samu matsala, nidai ya kamata na gode maka irin kokarin da kayi akanmu nida mama, mama tache toh dai kar ayi latti kije ki gama aikin ki ki dawo ga tuwon tsaki nnan zan tuka mana, idan kin dawo kyachi tache toh mama harta kai kofa baba yache nahla idan kin tashi dawowa ga naira 100 ki sayo min panadol tun jiya kannan kemin chiwo, tache toh sannan ta wuche.
Tana fita mama ta sauke ajiyar zuchiya tache alhaji yau wata biyar kennan rabonka dakasha magannin idonkan nnan kuma na tabbata komin panadol da zakasha baze dena.
KARANTA: Kanwar Maza Hausa Novel
JUYA TA HAIHU Chapter 3
Da sallama ta shigo gida lokachin daidai an tada sallan magrib, taga Abiinta zaune akan tabarma yana sallah, ahankali ta jawo wani iche ta saka a gabansa tamasa sutura kafin ta tsallaka ta shige dakinta ta ajye ledan ta shige bayi tayi alola sannan itama tayi sallah, tana idar da azkar bayan sallah ta wuche tsakar gida ta gaida mama da Abi tache Abi chiwon kanne ya hanaka zuwa massalahi yau? Mama tache idonsane ya tasar masa kuma bayan fitanki , baba yache ina maganin mamana tache baba bara na dakkoh ta tashi taje debo ledojin dakinta mama tache dadai kachi tuwon kafin kasha maganin zefi aiki , Nahla tache mama yau da Abi da keh dani dadi zamuchi a gidannan , tana murmushi tache sun kara min dubu 5 akan kudin aiki Abi shine nache yau sekasha fura kachi kaza son ranka a gidannan kema haka mama, ta dakkoh paranti ta ajye sannan ta dakkoh wani roba ta fara dama furan mama tache ikon Allah yau saboda an biyaki harda dan kari a sama shine zaki kashe kudin kaman bakida abunyi dashi tache mama tsakani da Allah yachi ache munchi nama a gidannan yau fin shekara da wata nawa kennan Abina bechi nama ba kullun idan aka samu dan kudi se a ajye na biyan bashi koh sayan abunda zamuchi yau rana daya dai mu manta da bashi koh makarantana koh wani abun rayuwa muchi nama muji dadi Abi yache me kukewa kus kus ne keda mamanki nahla ta dauka roban data dama furan a chiki ta kawo ta ajye gaban Abi sannan ta koma ta debo ruwa a buta ta kawo wani roban tache Abi wanke hannunka kaaji, ba tuwon da zakachi yau, yayi murmushi yache kaman kaza nakeji kamshin ta, tache Abi baka gani ne yache wlh idon ne ya dan tashi Amman nasan zuwa gobe ze washe inshaallahu tache koh goben kawai zamuje asibitin ne yache aa inashan panadol ze washe nache miki ta kallesa sannan ta sauke ajiyar zuchiya tasan chewa kudine bubu shiyasa bayason zuwa asibitin don idon ba karamin kudi suke kashewa ba, tache toh Abi naji bara na juye mana a paranti se muchi, mama ta wanko hannunta itama ta zauna tache halan ni bandani zaachi shiyasa banji kinche na karaso ba nahla tayi dariya tache aa ni na isa na hanaki wache ni base na fasa chi ba idan baze isa ba duk sukayi dariya nahla ta zubawa baba da mama fura a cup ta basu sannan suka fara chi suna yushe gamo da kaza.
Abi yache mamata nache zanyi magana dake kafin ki fita aiki dazu koh, tache eh Abi haka kache, yache inaga lokachi yayi da zan fada miki dalilin tafiyan mamanki da kuma inda ta koma.
Nahla taji gabanta ya fadi batasan dadi zata jiba koh akasin haka, tasan chewa Abinta, duk sanda yayi magannan mahaifiyarta se yyi bakin chiki, kuma hakannan taji hankalinta be kwanta ba, ta bude baki tache baba ai base kayi magannata ba idan bakaso bazan kara tambayn ka ba inshaallahu, ita kanta mama seda taji gabanta ya fadi saboda tasan magannan tsohuwar matar nasa ba magana ne da yake sonyiba amma se tai shiru kawai, baba yache aa inaji a jikina che lokachin fada miki yayi bamusan meze faru gobe ba dan haka gwanda na fada miki kawai.
Nahla dai tayi shiru bata kara chewa komai ba baba ya fara magana chikin rauni, yache shekaru 30 baya da suka wuche nabar garin mu Soha dake kasar egypt na koma babbar birnin cairo domin neman abunyi na nemi gadi saboda a lokachin ban samu gatan zuwa jami’a ba ballantana na samu aikin gomnati,
A gidan da nake gadi muka haduda mamanku muka fara shiri, a hankali a hankali soyyyah mai karfi ta shiga tsakanin mu, mamarki a lokachin ta kusa gama jami’a tache min zata fadawa mahaifinta chewa ta samu wanda takeson aura, bayan ta fada masa chewa mai gadin gidan su wato ni kennan takeso aure se ran iyyenta ya bachi har yakai ga an sallameni daga aikin sannan baban ya mata hadi da dan abokin sa, da mamanki taji labarin chewa zaa aura mata wanda baniba se kawai ta gudu tazo wajena sabida lokachin soyyayyan dake taakannin mu yyi karfi dayawa muka gudu kawai mukabar egypt muka dawo nigeria mukayi aure, nima kuma ban sake waywayan gida ba saboda yawanchi a danginmu da mutun ya gama secondary barinma na miji toh kawai duniya yake shga neman kudi baa sake ganinsa.
Bayn mun dawo Nigeria na sake neman gadi a wani gidan inda suka bamu dakin mai gadi a nnan mukayita raayuwa chiki talauchi da kunchi, bayn shekara daya mamanku ta haifo yayanki Ahmadu, dayake mamarku a chikin gata ta taso haka kullun a chikin kunchi take, se kuma allah yasa duk wani abu danasaka a gaba danyi na samun kudi bana wani samun albarka a chiki iyaka abunda zamu saka a baki kadai yake kawowa.
Bayan shekaru 9 ina gadi a gidan uban gidana mamarki ta haifo ki se uban gidana ya bani wannan gida nashi kyauta ya kuma hadani da jari yache na koma na fara wani business koh zan samu kula da iyalaina sosai dan har a lokachin ma shiyke biywa Ahmadu kudin makaranta. Haka muka tashi nazo na bude shago a chikin kasuwa na fara sayeda sayarwa a hankali sai Allah yasa albarka a chiki, kwatasm wani rana se gobara ta tashi a yankin da shagunan mu keh chiki komai na jarin nawa ya kone tass dan ban dade da bunkasa shagon da riban da na samu a chiki ba gobaran ya faru lokachin baki wuche shekaru 4 ba daga nnan kuma muka kara shiga chikin wani talauchin mamarki kuma a lokachin hakurinta ya fara karewa.
Bayn kinyi shekara 8 yayar mamarki ta kirata take fada mata chewa babansu na kwanche gadin asibiti babu lfy likitochi sunche baze tshi ba kuma shi baban natayache yanason ganinta kafin ya koma ga ubangiji a lokachin ne tache zata koma gida, nache toh taje ita kadai tache aa sedai ta tafi da danta na miji, nache mata gaki yarta mache ai idan zata tafi da daya daga chikin ku keh ya kamata ta tafida tache wai aa wahala da aiki zaki bata a hanya shi kuma y girma ze iya yiwa kansa komai, a haka dai ta tafi da ita da Ahmadu, bayan tagiyanta da wata daya kawai seta turomin da sako chewa tayi nadamar aurena da barin rayuwarta mai kwanchiyar hankali da dukiya da tay a baya saboda so sannan tana bukatar takardan ta dan bazata iya dawowa ta chigaba da wahala ba kuma Ahmadu ta daukesa dan shi yafi bukatan karatu a chan kuma yan uwanta zasu taimaka mata yyi karatu har jami’a.
Babu ynda na iya haka na sawwake mata na chigaba da kula dake har lokachinda na auro batul.
Masoya JUYA TA HAIHU na gide da comments a chapter 2 irin comments dinda marubuchiya keson ji kennan ku chigaba da fada min abunda kuke tunani koh kukeson sani a littafin, dakuma bada karfin gwiwanku suwa gareni
Nagode.
0 Comments