The Billionaire's Maid Hausa Novel

The Billionaire's Maid Hausa Novel

The Billionaire's Maid Hausa Novel (Ƴar Aikin billionaire), Sabon littafine Wanda shahararriyar marubuciya littafan hausa Maman teddy ta wallafah.

The Billionaire's Maid Hausa Novel

Zaune take jaÉ“asss a cikin Æ™untatattacen tsakar gidan nasu ,wanda ya matse babu girma ,gashi da Alama gida ne na yawa , don sasa² ne ,amma a har haÉ—e , bin ta da kallo nayi ina sake Æ™are mata Kallon tsaf inda naganta gari guda , Mace sabceciya a tsaye , ga tsawo ga Æ™iba, gashi komai da take yi da Æ™arfin ta take yin shi , fuskan nan yayi baÆ™inÆ™irin ga Æ™uraje (pimples) da suka ci shi tammm kai da gani kasan na tsaban Æ™azanta ne , Kayan Wanki kam a gaban ta yanda kasan wankin gidan ne ta tattaro su gaba ki É—aya zata Wanke ,nan kuwa tsaban Kayan ta ne don bata tashi Wanki sai taga ta juya bata da rigar sawa bare hijabi, kayan nan gaba É—aya sun cika gidan da hamami da kuma tsamin dauÉ—a.

Girgiza kawai take yi Tana gyaÉ—a kai tare da bin WaÆ™ar M.Sharif da ta Æ™ure shi yana tashi ta cikin m.p dake gaban ta , inda take bin baitin waÆ™ar Asma'u Ma'u .....Ji kike Muryar ta cikin Æ™araji ya amsa tana cewa “ Gaaaannni.....Sai kuma can ta cigaba da bin waÆ™en tana cewa “ Asma'u Ma'u sunana in ka kira ,daÉ—i ya rufe Ni banda kamar ka a zuciya....” Ni kaine nawa tauraro ka haska...kai nai nunawa iyaye sun kai Barka, bana canzawa ko za'a mini duka, kai ke sanyawa kullum inyo dariya hahahaha! Kawai sai ta wani fashe da dariya tana kai hannu tare da ÆŠaukar Sabulu tana sillawa a daddaunar hijabin ta tana dirza iya Æ™arfin ta.

Ma'u! Ma'uuuuu.....Muryar Mahaifiyar ta ya katse ta dake fitowa daga Madafi (kitchen) Wanda gaba É—ayan shi da Lange Lange aka yi shi . Ina sam ma'u bata ma san Ana yi ba , Wannan yasa Baba ÆŠan lami dake shigowa kallon Mama Hauwa yana cewa “ Ina zata san kina yi , Ai Ba zata sani ba , don ta faÉ—a halarar Aure , sai dai kuma kashhh gashi ko mashin shini babu ....Muryar Hausi ne ya katse su wato matar sa inda take taya shi da cewa “ Waye zai zo wurin tabbatacciya mara kunya , ai babu mai zuwa a haka zata zauna ta zama guzuma, gashi nan tun Æ™awayen ta na Aure aka zo Æ™anni yanzu Æ™annin Æ™annin ta ke yi , amma kullum babu Abin da ta iya sai Masifa da Jaraba da cin zalin É—in Æ´aÆ´an mutane! 

Wannan magana na Hausi duka shi ya sauka a kunnen Asma'u Ma'u, Cikin sauri Tasaka hannun ta tana kashe Mp tare da juyowa tana kallon Umman ta Wanda bata ce komai ba , sai sadda kai da tayi Æ™asa ,mace mai haÆ™uri don tabbas da Ma'u ita ta biyo to da babu wanda zai ji muryar ta a cikin tsakar gidan. 

Hausi me kika ce? Ƙanni na suna Aure kike magana? To ki iya bakin ki , don kin Sanni sarai wallahi ba kirki ne dani ba , sannan idan ban shiga gonar ka ba bana so ka shigo tawa , idan kuma ba haka ba ,zan kyata maki rigar mutunci gida biyu Wallahi! Sannan da kike maganar Ƙanni na sunyi Aure ba dai Æ´aÆ´anki kike magana ba Su Asabe ,wanda kullum kika je gidan mijin babu daÉ—i , tuwo ne dai yanzu ma ba'a iya tuÆ™a na masara an koma na Dawa, Sai kuma Haule da kullum mijin ke dukan shegiya duk ya sauya mata halittu, yarinya da kumarmatun ta kika miÆ™a masa yanxu kuwa kika ganta sai dai haÆ™ora a gaba , don har wani gantso tayi wanda a gidan uban ta da ake cin tuwo duk dare bata dashi , to don ban yi Aure ba har Abin ke ki fito ma kiyi magana ne , Hmmm ...., Sai ta caÉ“e baki tana cigaba da cewa “ ko da yake Auren wuri kika yi masu don a ce yaran ki na Aure Ni kuma ma'u gani a cikin gida , to sai mene yanzu a haka na fisu sutura cikar sura ta Æ´a mace! 

Cikin Sanyin murya irin na Umma Hauwa ta kuma kiran sunan Æ´ar ta ta tana cewa “ Ma'u.....” wannan yaba Baba ÆŠan lami damar cewa “ Eh a haka babu komai suna lemar Aure ne , kuma kullum lada suke samu wurin ALLAH . To Ni kace zunubi nake samu mana , tun da ina a gaban iyaye na....... Kamin ta rufe baki ne kaji gyaran Muryar malam Da yake shigowa yana faÉ—in “ Mama na yau ma dai ÆŠin dake ne ko?” . 

Saurin miÆ™ewa Asma'u Ma'u tayi tana Nufo inda mahaifin nata yake yana shigowa da sandar sa a hannu yana É—an lalube alamu baya gani da Æ™yau na tsufa . 

A'a Baba malam , Ni sukola ma nake yi , ka dawo Ciki ka huta kenan?  Ta furta tana riÆ™o masa hannu tana kokarin nufa dashi ÆŠakin Umma Hauwa,wacce take tsaye tayi tagumi , Muryar Malam ne ya katse ta yana cewa “ A'a Ni hayaniya na jiyo ina daga zaure ina Æ™ara ma Yara karatu , Kuma indai naji hayaniya a cikin wannan gida nasan da kene Mama na”. Kamin Ma'u tayi magana Hausi tace“ Aikuwa kaima kasani dai , yarinya sam bata biyo Uwa da Uba ba ”. Shiru Ma'u tayi sai dai galla ma Hausi harara da take yi , don idan Malam na Wuri bata iya magana ko me za'a ce da ita . 

Muryar malam ne ya katse ta cike da girma , yana Furta “ To to to! Yi haÆ™uri Hausi,don Allah kiyi haÆ™uri kin san Mamana tun tana Æ™arama kiyi HaÆ™uri Don Allah . 

Juyawa Hausi tayi tana cewa “ Ai dama kullum wallahi arziÆ™in ku wannan yarinya take ci da ba don haka ba....hmmmm kawai sai ta ja Æ™wafa tana girgiza kai tana Wucewa, nan shima  Baba ÆŠan lami ya biyo bayan ta . 

Mama na kina ina ne? Malam ya furta yana waige waige . Na'am Baba Gani nan . Mama na , ki kama kanki fa, Duka nan iyayen ki ne kina jina ko? . GyaÉ—a kai ma'u tayi kana ya cigaba da cewa “ Yanzu mene kike yi anan?”. Sukola Baba, to maza kiyi ki tashi kar na kuma sake jin Muryar ki kinji na faÉ—a Miki ?”. To! Ta furta tana isa inda Kayan ta suke tsubire tana kama wankin ta , Shi kuwa malam Nufar inda Almajiransa suke yayi ,yayin da Umma Hauwa ta koma cikin madafin tana gyara itacen da suke ci a hankali ”. 

SCOT LAND 1:00am. Kaiwa da komowa take yi a tsakiyar falon inda takaici da baÆ™in ciki duk ya addabi zuciyar ta . Tsaye take daga ita sai Kayan barci tana aikin  Kallon inda Mijin nata Abu Zarri yake zaune , Fuskar sa a murtiÆ™e babu alamun wasa ,don idan kun barni zan iya ce maku Abu Zarri bai kama da mutane masu sakin fuska da Walwala ba . Mamaki ne ya kamani ganin yanda ya baje a tsakiyar falon nasa yana Shan Sigari , irin masu kaurin nan na cikaƙƙun marasa kirki ”. Abu Zarri Ya kamata ka buÉ—e Idanun ka , ka san Abin da kake yi ba me Æ™yau bane. Kana da mata da Yarinya ace Ba zaka dawo gidan ka na Aure ba sai 1 na dare ? Sannan ka Zauna kana buÆ™ar mun Sigari a tsakiyar falo , wallahi an cuce Ni haÉ—ani da aka yi Aure da kai , don baka Sona! . Wow! That's very good, yayi Æ™yau da kika fahimci hakan , yanzu zaki iya sanar masu Ammie da kin gaji da zama dani Phania sai su rabaki dani..........Ya Æ™are maganar yana hura mata iskar HayaÆ™in taba. 

Rintse ido Phania tayi tana jin wani Abu na tokare mata a Æ™irji , baka isa ba Abu Zarri kai ka same su kayi masu wannan baya ni, daga nan duk abin da ka yanke yayi Æ™yau ”. 

Alright, kin zaÉ“i cigaba da zama dani kenan , Ni kuwa da nayi Wani mu'amalar Aure dake na gwammaci na samu sugar mummies naji daÉ—in su don sun fi mun ke É—ari bisa ÆŠari . Ka tuna da ALLAH Abu Zarri ”. Phania ta furta tana bin sa da kallo mai cike da Æ™unar rai . Shut up your mouth! Yayi maganar yana daka mata tsawa tare da wurgi da sigarin hannun sa , ke kina da bakin magana Phania, kin manta wacece ke? I know you since we're child . Tun muna primary abokanai na suke Æ™waÆ™ular ki a school toilet,so don't forget this in ur memory.....nasan ki fiye da yanda kowa ya san ki a duniyar nan , shigowar ki Rayuwata Æ™addarata ce Phania , Tir da Samun mace irin ki , tun kina yarinya Kin gama Lalata Rayuwar ki a hannun Arna ma ba musulmai ba.  Sannan yanzu kike tsammanin jin daÉ—i daga gare Ni Wuce ki bani Wuri.........................!

#Mrs Usm #Mmnteddy Dm for your advertisement 08081202932.#free page!

KARANTA:  Juya ta Haihu Hausa Novel Complete

Post a Comment

0 Comments